HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 10/Jumadal Akhirah/1440H
daidai da 15/FABARAIRU/ 2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ALIYU DAN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
TAWAKKALI GA ALLAH TA'ALAH
(التوكل على الله تعالى)
Shehin Malami
wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy–Allah ya tsare shi- ya yi
hudubar juma'a mai taken: TAWAKKALI GA ALLAH TA'ALAH,Wanda kuma
a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Godiya
ta tabbata ga Allah Mabuwayi Mai yawan gafara,
Mai hakuri abin godiya. Ga Ubangijinmu ne -Mabuwayi da daukaka- falala
take, da yabo mai kyau, da ni'imomi na zahiri dana boye, ba mu iya kididdige
yabo a gare shi, Shi kamar yadda ya yi yabo ne ga kanSa.
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin
tarayya, Masanin abinda suke a cikin kiraza.
Kuma
ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne ManzonSa,
wanda Allah ya turo shi domin rahama ga Talikai.
Ya
Allah ka yi dadin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka
Muhammadu da iyalansa da sahabbansa, salati da sallama masu dawwama, har zuwa
ranar tayarwa da hisabi.
Bayan
haka
Ku
yi takawar Allah, ta hanyar aikata kyawawan ayyuka, da kauracewa munana, domin
hakan shine hanyar samun yardar Allah (سبحانه), da rabauta da samun darajoji a cikin
Aljannoni, da gyaruwan halaye, a cikin wannan rayuwar, da kuma bayan mutuwa.
Ya
ku Musulmai
Ko
yaushe, ku tuna Rahamar da Allah ya muku, a lokacin da ya zubo ni'imominSa
akanku na zahiri da kuma a boye. Kuma ku girmama ni'imar Alkur'ani, da ni'imar
sunnar Annabi mai yin bayani da fassara ga wannan Littafi Mabuwayi, saboda
Allah ya daukaka Mutum ne da su, izuwa ga matsayin da yafi daukaka, Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma kada ku yi rauni,
kuma kada ku yi bakin ciki, domin ku ne mafiya daukaka, idan kun kasance masu
imani" [Ali-imrana: 139].
Kuma Allah
(Subhanahu) ya ce: "A'aha! Lallai hakika, littafin masu
da'a yana wuri madaukaki (na illiyuna)" [Mudaffina: 18].
Kuma Allah
Ta'alah ya ce: "Kun
kasance mafi alherin al'ummah, wanda aka fitar ga Mutane, kuna umurni da
alheri, kuma kuna hani da abin ki, kuma kuna imani da Allah" [Ali-imrana:
110], don haka, Daukakar Mutum da kimarsa da alkhairinsa da matsayinsa suna
kasancewa ne da akidarsa ta Musulunci, da kuma irin ayyukansa na kwarai,
wadanda da su ne, yake kasancewa salihi, mai kawo gyara a cikin wannan rayuwar.
ALKUR'ANI
MAI GIRMA, DA SUNNAR ANNABI MUHAMMADU saw, Allah ya raya zukata da su, kuma
Allah ya warkar da kiraza da su, daga cututtuka, kuma ya bada basira da su daga
makanta, kuma da su yake gusar da nau'ukan shirka da bata da kafirci da ilhadi,
kuma yake tsarkake hankula da zukata da
su daga cutukan sha'awowi da shubuhohi, wadanda suke canza fidirar addini mikakkiya
da hankula lafiyayyu. Wannan kuma rahama ce daga Allah Mabuwayi da daukaka ga
Mutane.
Kuma bayan
Allah (سبحانه) ya cire
daudodi daga zukata, da munanan halaye, da sifofi ababen zargi, ta hanyar
Alkur'ani da Sunnah, Sai ya cusa imani da rassansa a cikin zukatan, domin imani
da rassansa ba za su samu gindin zama a zuciyar Mutum ba, sai zuciyar ta
wofinta daga abinda yake kishiyantar imanin, saboda kwarya ko masaki ba zai
kasance mai tsarki ba, sai an gusar da najasosi daga cikinsa, Sai kuma a sanya
abubuwa masu tsarki. To ita ma zuciya kwatankwacin masakin take.
Kuma
hakika Allah Ta'alah ya sanar da mu hakan, a farkon surar da Allah ya mayar da
annabinSa Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) manzo da saukarta, saboda ya kasance annabi ne da saukar:
Ikra'a, ya kuma kasance: Manzo, da saukar: Ya Ayyuhal Muddasir, a inda Allah (سبحانه) ya ce: "Ya
wanda ya lulluba da mayafi * ka tashi domin ka yi gargadi * kuma Ubangijinka sai
ka girmama shi * kuma tufafinka sai ka tsarkake shi * Kuma Gumaka sai ka
kaurace muku" [Muddassir: 1-5]. Sai Allah ya umurce shi, a farko, da kiyayar
shirka, da yin gargadi ga masu dogewa akansa, da bayanin muninsa, da girman
ukubobinsa. Sa'annan sai ya umurce shi da girmama Ubangiji Ta'alah ta hanyar
tauhidi da kuma kalmomin yabo. Sa'annan sai ya umurce shi, da yin tsarki, a
farko a dunkule, sa'annan sai aka saukar da hukunce-hukuncensa dalla-dalla a bayan
haka. Kuma ya umurce shi da kaurace wa Gumaka, da kyale su, da barranta daga
masu yin bauta a gare su.
Kuma wadannan
ayoyin kamar fadin Allah Ta'alah ne: "Babu tilastawa a
cikin addini, hakika shiriya ta bayyana daga bata, don haka, wanda ya kafirta
da dagutu, kuma ya yi imani da Allah, to hakika ya yi riko da igiya mai karfi, babu
yankewa a gare ta" [Bakara: 256]. Sai Allah ya fara da bayar
umurnin cewa a kafirce wa Dagutu, domin imani ya tabbatu a cikin zuciya.
Kuma mafi
girman ni'imar Ubangiji ga BawanSa, ita ce Allah ya bashi zuciya lafiyayya,
wanda zai shiryar da shi da ita zuwa ga ILIMI MAI AMFANI, DA AIKI NA KWARAI,
Allah Ta'alah ya ce: "Ranar da dukiya bata amfani, haka
'ya'ya * sai ga wanda yaje wa Allah da zuciya lafiyayya" [Shu'ara'i:
88-89].
Kuma
Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ya Allah, lallai ni ina rokonka tabbatuwa cikin wannan
lamari (Musulunci), da azama akan ayyukan shiriya, kuma ina rokonka godiya ga
ni'imominka, da kyautata ibadarka, kuma ina rokon ka bani harshe mai gaskiya, da
zuciya lafiyayya" Tirmiziy
ya ruwaito shi, da Ibnu-Hibbana daga hadisin Shaddad dan Aus -رضي الله عنه-.
Daukakar
Musulmi, tana ga yin imani, da daukacin ressansa, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma
daukaka ta Allah ne, da ManzonSa, da kuma Muminai, saidai Munafikai ba su sani
ba"
[Munafikuna: 8].
Kaskantuwar
Mutum kuma, tana cikin ayyukan sabo da zunubai, Allah Ta'alah yana cewa: "Lallai
wadanda suke saba wa Allah da ManzonSa, lallai wadannan suna daga cikin mafiya kaskanci" [Mujadala:
20].
Kuma
Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya fada a
cikin ganawarsa da UbangijinSa Madaukaki: "Lallai Kai kana yin hukunci, kai kuma ba a yin hukunci
akanka, kuma lallai wanda ka jibinta baya kaskanta, kuma wanda ka ke ki baya
samun daukaka, saboda albarkaka -Ya Ubangijinmu- ya yawaita, kuma ka daukaka" Ma'abuta littafin sunan suka ruwaito shi.
Kuma ya
tabbata Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce: "Imani rassa saba'in da wani abu ne, mafi kololuwarsu
shine fadin: LA ILAHA ILLAL LAHU, Mafi kankantansu kuma: Gusar da abu mai
cutarwa daga hanya. Itama kunya reshe ne daga imani".
Kuma
Ubangijinmu Tabaraka wa Ta'alah ya shar'anta mana, abinda zai amfanar da mu a
rayuwarmu, da kuma bayan mutuwarmu, ya kuma hane mu aikata abinda zai cutar da
mu a cikin rayuwarmu da kuma bayan mutuwarmu. Kuma shi Mahalicci Mabuwayi da
daukaka, aikin biyayya baya amfanar da shi, kuma saba masa baya cutar da shi,
Allah Ta'alah ya ce: "Lallai Allah hakika Mawadaci ne daga barin
Talikai" [Ankabut: 6].
Kuma yana
daga dalilan KUDURAR ALLAH سبحانه da ILIMINSA da HIKIMARSA
da RAHAMARSA da FALALARSA da KYAUTATAWANSA da BAIWARSA, Yadda ya shar'anta wa
Musulmi ibadodin da zai samu daukaka zuwa ga darajojin kamala, da tsarkaka, da
samun kyan hali da su, domin ya isa izuwa ga abinda aka kaddara masa (na
matakan girma), kuma domin ya rabauta (ya samu sa'ida) a cikin rayuwarsa da
kuma bayan mutuwarsa, Allah Ta'alah yana fada dangane da sifofin Muminai:
"Wadanda suke tsayar da sallah, kuma daga abinda muka
azurta su suna ciyarwa * Wadannan sune muminai na hakika, suna da darajoji a
wurin Ubangijinsu, da wata gafara, da arziki mai karamci" [Anfal:
3-4].
Sai
Ubangiji Mai rahama ya bayyana AYYUKAN ZUKATA, a cikin Alkur'ani da Sunnah,
kamar tsarkake niyya (Ikhlasi) da yakini, da rukunnan imani, da tsoro da fata,
da wasun haka. Kuma Allah a cikin Alkur'ani da Sunnah ya bayyana AYYUKAN GABBAI,
Misalin rukunnan Musulunci, da umurni da kyakkyawa, da hani da mummuna, da
makamantansu. Kuma ya fifita sashen ayyukan akan sashe.
Kuma mafi
girman abinda Musulmi zai kusanci Ubangijinsa da shi, shine ayyukan zukata,
wadanda Allah ya yi umurni da su a cikin Alkur'ani da Sunnah.
Kuma
ayyukan zukata sune ginshiki ga ayyukan gabbai.
Kuma
Musulmai suna samun fifiko da ayyukan zukata, da kuma sanin ma'anoninsu, da
sifantuwa da su, don haka ne Sahabbai -رضي الله عنهم- suka rigayi dukkan Mutane, cikin lamarin ayyukan zukata, kuma
suka samu fifiko a cikinsu. Sa'annan sai Tabi'ai, saboda yadda suka san
cikakken ma'anoninsu, kuma suke aiki da hakikaninsu, kuma saboda cikar
fikihunsu ga harshen Larabci, da cikar tauhidinsu, hasanul Basariy ya ce: "Abubakar, ba ya fi ku ne, saboda yawan azumi da salla ba,
saidai saboda abinda ya tabbatu a cikin zuciyarsa".
Kuma yana daga cikin MAFI GIRMAN AYYUKAN ZUKATA, WADANDA
SUKA FI DAUKAKA: DOGARO KO TAWAKKALI GA ALLAH MABUWAYI DA DAUKAKA, Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma ga Allah, za ku
dogara, idan kun kasance Muminai" [Ma'idah: 23]. don haka,
Tawakkin Bawa ga Allah Ta'alah ibada ne, saboda Allah ya yi umurni da shi, a
cikin wannan ayar, da kuma wasu ayoyin. Ma'ana: Ku fawwala al'amuranku
gabadayansu zuwa gare shi.
Shi kuma
fadinSa (سبحانه): "idan
kun kasance Muminai" ya nuna cewa lallai Tawakkali sharadi ne na
imani, wato imanin yana koruwa a lokacin da tawakkalin ya tafi.
Kuma Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma gaibin sammai da kasa na Allah ne,
kuma zuwa gare shi ake mayar da dukkan al'amura, sai ka bauta masa, kuma ka dogara
akansa" [Hudu: 123]. Sai ya ware tawakkali da ambato, bayan
ambaton ibada (saboda muhimmancinsa).
MENENE
TAWAKKALI GA ALLAH TA'ALAH?
Ma'anar Tawakkali:
Shine Dogaro ga Allah سبحانه cikin lamura
gaba dayansu, na Duniya da Lahira, da gaskiya cikakkiya, da kuma tsarkake niyya
wanda ya barranta daga shakku, da fawwala dukkan al'amura zuwa ga Mahalicci Mai
jin kai Mai iko akan komai, da jin amintuwa da Allah Mai girma, tare da
barrantar zuciya daga jin tana wayo da karfi, da yarda da abinda Allah ya
hukunta wa Bawa na dukkan al'amura. Duk wanda ya samu wannan matsayi na
tawakkali (dogaro ga Allah) to ya samu mafi girman abin nema, kuma Allah ya
hada masa dukkan abin samu, kuma Allah Ta'alah ya jibinci al'amuransa, sai ya
kasance daga cikin Bayin Allah salihai, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai
Majibincina shine Allah wanda ya saukar da wannan littafin, kuma shine yake
jibintar Salihai" [A'araf: 196].
Kuma Allah
Ta'alah ya ce: "Ku saurara! Lallai ne Waliyyan Allah (masoyansa)
babu wani tsoro akansu, kuma su ba za su yi bakin ciki ba * Wadannan da suka yi
imani, kuma suka kasance masu takawa" [Yunus: 62-63].
Kuma Allah
a cikin hadisin kudusiy ya ce: "Ni ina ga yadda Bawana ya yi zatona, kuma lallai ina tare
da shi idan ya ambace ni", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi,
daga hadisin Abu-Hurairah.
Tawakkali
shine mafakar Annabawa -عليهم الصلاة والسلام- wanda yake kare su daga makircin makiyansu.
Kuma
Tawakkali shine karfin da ba a rinjayarsa daga makiya Annabawa -عليهم السلام-, kuma da shi Annabawan a cikin rayuwarsu suke fiskantar
nau'ukan tsanani da bakin ciki, da musibun da suke sauka, sai su rinjayi kowane
tsanani da bacin rai da tawakkali, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma
ka karanta musu labarin Nuhu, a lokacin da ya ce wa Mutanensa, Ya ku Mutanena,
idan matsayina da tunatarwata game da ayoyin Allah sun kasance sun yi nauyi
akanku, to ga Allah na dogara, sai ku tara al'amarinku, ku da abubuwan
shirkinku, sa'annan kada al'amarinku ya kasance rufaffe akanku, sa'annan ku
nemi gamawa da ni, kada ku yi mini jinkiri" [Yunus: 71].
Abdullahi
dan Abbas -رضي الله عنه- ya
ce: "Kalmar HASBUNAL LAHU WA NI'IMAL WAKIL Ma'ana: Allah ya
isar mana, Annabi Ibrahim -عليه
السلام-
ya fade ta, a lokacin da aka jefa shi a cikin wuta"
Bukhariy ya ruwaito.
Kuma Allah
Ta'alah yake fada ga AnnabinSa Muhammadu -صلى الله عليه وسلم-: "To, idan sun juya baya, sai ka ce:
MA'ISHINA SHINE ALLAH, BABU ABIN BAUTAWA FACE SHI. A GARE SHI NA DOGARA, Kuma
shine Ubangijin Al'arshi mai girma" [Taubah: 129].
Kuma Allah
Ta'alah yake fada dangane da annabi Hudu -عليه السلام-: "Lallai ni na dogara ga Allah
Ubangijina kuma Ubangijinku, babu wata dabba face shine Mai riko ga
makwarkwadarta, hakika Ubangina yana kan tafarki madaidaici" [Hudu:
56].
Kuma Allah
Subhanahu ya ce: "Sai Musa ya ce: Ya ku Mutanena! Idan
kun kasance kun yi imani da Allah, to a gare shi kawai za ku dogara, idan kun
kasance Musulmai * Sai suka ce: Ga Allah muka dogara" [Yunus:
84-85].
Kuma Allah
(سبحانه) yake fada dangane da dukkan Manzanninsa:
"Kuma menene a gare mu, ba za mu dogara ga Allah ba,
alhali kuwa ya shiryar da mu ga hanyoyinmu? Kuma lallai ne, mu yi hakuri ga
abinda kuka cutar da mu, kuma ga Allah ne masu dogaro za su dogara"
[Ibrahim: 12].
Don haka,
duk wanda ya tabbatar da ibadar tawakkali ga Allah, to lallai shine mai samun
rabo, abin taimako akan kansa, da kuma makiyansa na daga Aljanu da Mutane.
Wanda kuma
ya tozarta ibadar tawakkali, ba za a taimake shi ba, kuma zai bata, kuma babu
abinda zai amfane shi.
Kuma
tawakkali yana daga cikin sifofin Muminai masu tauhidi, Allah Ta'alah ya ce: :
"Lallai Muminai, sune wadanda suke idan an ambaci Allah,
zukatansu suke firgita, kuma idan an karanta ayoyinSa akansu, su kan kara musu
imani, kuma ga Ubangijinsu suke dogara" [Anfal: 2].
Kuma yana
daga cikin tawakkali, YIN AIKI DA SABUBBAN DA ALLAH YA SHAR'ANTA, da
mu'amalantarsu. Da kuma yin aiki da sabubban da aka sansu ta hanyar jarraba su,
da yin riko da su, tare da rashin dogaro akansu, a'a dogaron zai kasance ne ga
Allah shi kadai.
Saboda
barin sabubba baya cikin tawakkali, kuma sabubban halittu ne na Allah; idan Allahn
ya yi nufi sai ya bata su; ya zama ba su yin wani amfani. Idan kuma ya so sai
ya sanya amfani a cikinsu, don haka al'amarin gaba dayansa na Allah Ta'alah ne.
Kuma
BABBAR SHIRKA a babin tawakkali shine, Mutum ya fawwala al'amarinsa zuwa ga 'dan'uwansa
mahaluki, rayayye ko matacce, sai kuma ya dogara akansa, akan irin abinda halittar
bata da iko a kai, sai Allah Mabuwayi da daukaka, kamar dogaron Mutum ga wani
shehi, da cewa zai gafarta masa zunubansa, ko ya taimake shi akan makiyinsa, ko
zai amsa masa addu'arsa, ko ya dogara akansa, da cewa zai masa ceto. Domin
ceton Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- a ranar kiyamah tana kasancewa ne, ga kowane Musulmi, da kuma
kowane salihi, da izinin Allah. Ko ya dogara ga wata halitta cewa, ita zata
warkar da shi, ko ta masa baiwar 'da, da makamancin haka.
Shi kuma
kaso na biyu na SHIRKA A BABIN TAWAKKALI, Shine shirkar da bata kai ga babbar
shirka ba, wanda kuma ita ce: Ya dogara ga wani cikin wani al'amari daga nau'in
al'amurran da yake da iko akansu, kamar ya dogara akansa cewa, shi zai samar
masa aiki yi, a inda zai iya, sai ya manta da UbangijinSa Mabuwayi da daukaka,
ya yi fatan samu daga 'Dan'uwansa halitta. To wannan nau'i bai kai ga babbar
shirka ba. Kuma wajibin shine ya sanya wannan halittar a matsayin daya daga
cikin sabubban da yake aiki da su, Amma sai ya dogara ga Allah shi kadai, Wani
daga cikin Magabatan kwarai yana cewa: "Wani ba zai yi fatan
samun wani abu daga wurin wani ba, face ya rasa fatansa a inda bukatarsa tafi
tsananta a gare shi".
Amma, bada
wakilci a cikin abinda ake iya na'ibci a cikinsa, misalin saye da sayarwa, to
wannan ya halatta, tare da wajabcin kudurta, cewa lallai wakili baya iya cika
maka muradinka, sai da taimakon Allah, da ikonsa.
Kuma
hakika Allah ya yi alkawarin bayar da mafi girman sakayya akan tawakkali, a
inda yace: "Lallai ne Allah yana son masu tawakkali" [Ali-imrana:
159]. Saboda, duk wanda Allah ya kaunace shi, to zai bashi alkhairori, kuma zai
kiyaye shi daga sharri da ababen ki, Allah Ta'alah ya ce: "Wanda
ya dogara ga Allah, to lallai Allah ne ma'ishinsa" [Dalak:
3]. Wato, UbangijinSa ya isar masa abinda ya dame shi, ya ke bakanta masa, kuma
zai gyara masa al'amuransa a cikin rayuwarsa da bayan mutuwarsa. Wannan kuma
shine mafi girman sakamako da lada. Kuma Allah bai ambaci irin wannan sakamakon
a wata ibadar da ba ta tawakkali ba. Kuma wannan ya ishe tawakkali falala.
Kuma Ahmad
da Ibnu-Majah da Nasa'iy sun ruwaito daga Abu-zarrin, Lallai Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya karanta masa wannan
ayar, sai ya ce masa: "Da dukkan Mutane za su yi riko da
wannan ayar da ta isar musu".
Kuma an
ruwaito daga Ibnu-Abbas -رضي الله عنهما- daga
Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda yake son ya kasance
yafi Mutane karfi, to ya dogara ga Allah", Abdu Ibnu Humaidin ya
ruwaito shi.
Allah
Ta'alah yana cewa: "Kuma ka dogara akan Rayayye wanda ba
ya mutuwa, kuma ka yi tasbihi game da gode masa. Kuma Allah ya isa zama Mai
kididdige laifuffukan BayinSa" [Furkan: 58].
Allah
ya mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma, ,,,.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA
TA BIYU
Godiya
ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai * Mai rahama Mai jin-kai. Ina yin
yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominnsa gaba daya, wadanda muka
sani da wadanda ba mu sani ba.
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin
tarayya Madaukaki Mai girma.
Kuma
ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa Mai
karamci.
Ya Allah
ka yi dadin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da
iyalansa da sahabbansa masu shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici.
Bayan
haka
Ku ji
tsoron Allah iyakar takawarsa, kuma ku yi tawakkali a gare shi, domin duk wanda
ya dogara gare shi zai isar masa.
Ya
ku Bayin Allah
Ku yi riko
da sabubban tawakkali, kuma ku cike matakansa, kuma ku kiyayi abinda yake
kishiyantarsa, ko yake rage cikar kamalarsa, saboda tawakkali shine guzurinku a
cikin wannan rayuwar, kuma dalilin amintuwa a gare ku bayan mutuwarku daga
dukkan azaba da fitina da bakin ciki, Allah Ta'alah ya ce: "Babu
hukunci face daga Allah. a gare shi na dogara, kuma a gare shi masu dogara za
su dogara" [Yusuf: 67].
Kuma Allah
Ta'alah: "Kuma ga Allah ne kadai Muminai za su dogara"
[Ibrahim: 11].
Kuma ku
rika neman arziki na halal, domin a rika karbar ibadodinku, da addu'oinku, kuma
ku nemi shi ta hanyar tawakkali ga Allah Mabuwayi da daukaka, saboda ya zo
cikin hadisi, daga Umar dan Alkhaddab -رضي الله عنه- daga Annabi -صلى الله عليه وسلم-, ya ce: "Da za ku dogara ga Allah, hakikanin tawakkali, da ya
azurta ku, kamar yadda yake azurta tsuntsu, yana fita da safiya da yunwa, sai
ya koma da yammaci a koshe",
Imam Ahmad ya ruwaito shi, da Tirmiziy, kuma ya ce: Hadisi ne hasan sahih.
Ya ku Bayin
Allah!
"Lallai
ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan Annabi, Ya ku wadanda suka yi
imani ku yi salati a gare shi, da sallamar aminci"
[Ahzab: 56].
No comments:
Post a Comment