HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 12/JUMADAL ULAH/1440H
daidai da 18/JANAIRU/2019M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. HUSAIN DAN ABDUL'AZIZ AL-ASHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
DA'AWA ZUWA GA KYAUTATAWA
(الدعوة إلى الإحسان)
Shehin Malami wato: Husain
bn Abdul'aziz Al-Sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: KIRA ZUWA GA KYAUTATAWA, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Yana daga KYAWAWAN
LAMURA MASU GIRMA A CIKIN ADDININ MUSULUNCI, TABBATATTU A CIKIN DALILANSU NA
YANKAN SHAKKU: DA'AWA ZUWA GA LAMARIN KYAUTATAWA (الدعوة
إلى الإحسان), da dukkan surori da misalansa mabanbanta, Allah Mabuwayi da
daukaka ya ce: "Lallai Allah, Yana
umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa ma'abucin zumunta" [Nahl: 90].
Kuma Allah (سبحانه)
ya ce: "Kuma ku fadi magana
mai kyau zuwa ga Mutane" [Bakara: 83].
Kuma an ruwaito cikin
hadisi daga Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) lalllai shi ya ce: "Wanda ya kasance ya yi imani da
Allah da kuma ranar karshe, to ya kyautatawa makwabcinsa, kuma wanda ya yi
imani da Allah da kuma ranar karshe, to ya karrama bakonsa", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi.
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم)
yana fada, a
inda yake tabbatar ko yin wasiyya kan riko da wannan dabi'a mai girma, da yin
aiki da wannan ka'ida ko manufa abar karramawa: "Lallai Allah ya
wajabta lamarin kyautatawa ga kowane abu" [Muslim]. Malamai masu sharhi suka ce:
"abin nufi shine a kyautata wa kowane abu". Don haka, ana nufin, a
game komai, kuma a mamaye komai da kyautatawa.
Ya ku taron
Musulmai...
Lallai mabudin rahama shine
kyautatawa, cikin bautar Mahalicci, da yin aiki cikin amfanar da BayinSa, Allah
(سبحانه): "Lallai ne rahamar
Allah a kusa take da masu kyautatawa" [A'araf: 56].
Kuma Musulmi, ya dace ya
lazimci lamarin kyautatawa, cikin aiki da zance, cikin mu'amalolinsa, da kuma
cikin rayuwarsa, don ya rabauta da alfano masu girma, da kuma fa'idodi manya,
domin Ma'abucin kyautatawa yana cikin tarayya da Allah kebantacciya (المعية الخاصة), wanda take
hukunta, samun kiyayewarSa, da karfafawa, da taufiki, da dacewa, Allah Ta'alah
ya ce: "Lallai ne Allah yana tare da wadanda suka yi takawa, da wadanda suke
su masu kyautatawa ne"
[Nahl: 128].
Kuma Allah Mabuwayi da
daukaka yana cewa: "Kuma lallai Allah yana tare da masu kyautatawa" [Ankabut: 69].
Kuma lallai Mai kyautatawa
zai rabautu da samun mafi girman abin nema, wanda shine, Soyayyar Allah Ta'alah
ga BawanSa mai kyautatawa (محبة الله), to a wannan lokacin ne, zai rabauta ba; ba zai tabe ba har
abada, a Duniya da Lahira, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ku kyautata,
domin Allah yana son masu kyautatawa" [Bakara: 195].
'Yan uwa a cikin
imani ...
Da lamarin kyautatawa ne,
ake faranta zukata, kiraza suke yalwata, ake janyo ni'imomi, ake tunkude
azabobi.
Kuma kyautatawa baya yaduwa
a cikin wata al'umma, face gininta ya yi karfi, kuma an kare ta (wato al'ummar)
daga aukawa cikin matsaloli, kuma sun kasance wayayyu madaukaka, wanda suka
wofinta daga gurbatar rayuka da cutukan zuciya. Kuma da haka za su kubuta daga
wutan fitintinu, da sabubban fadace-fadace da musibu. Domin haka ne, umurnin
Ubangiji ga BayinSa ya zo akan lamarin kyautatawa cikin dukkan motsawansu, da yin
rayuwa tare da shi, cikin mu'amalolinsu.
Allah Ta'alah ya ce: "Ka tunkude cuta da
abinda yake mafi kyawu, sai wanda akwai kiyayya a tsakaninka da tsakaninsa ya
kasance kamar Majibinci ne masoyi" [Fussilat: 34].
Kuma Allah Ta'alah ya ce:
"Kuma ka fada wa Bayina su rika fadar kalma wadda take mafi kyau,
lallai ne Shedan yana rura gaba a tsakaninsu" [Isra'i: 53].
Ya ku taron
Musulmai...
Lamarin kyautatawa ta hanyar
bada kyautayi da baza hannu, lamarinsa yana kara karfi ga hakkin ma'abuta
matsayi da mukamai, da dukiyoyi da wadaci, Sai ka yi kwadayin aiki da wannan Ya
wanda Allah ya kyautata maka, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka kyautata,
kamar yadda Allah ya kyautata maka" [Kasas: 77].
Ibnu-Kayyim –رحمه الله- ya ce: "Ba
a janyo ni'imomin Allah, kuma a tunkude azabobinsa, da abinda yafi yin da'a a
gare shi, da kyautatawa halittunSa".
'Yan uwa a cikin
imani ...
Kyautatawar da shari'a ta
kwadaitar akansa yana kunsar dukkan
amfani da kowane nau'i, ga kowane halitta, Mutum ne ko dabba, saidai ladansa
yana banbanta, kuma falalarsa tana kara girma, gwargwadon wadanda aka gabatar
da kyautatawar a gare su, da girman hakkinsu da matsayinsu, kuma mafi kololuwan
wanda ya wajaba a kyautata musu sune iyaye biyu, sa'annan sai makusanta,
sa'annan sai sauran halitta.
Kalmar ihsani (wato kyautatawa)
tana dauke da ma'ana mai kyau, wanda take hukunta maka -Ya kai Musulmi- ka
mu'amalanci waninka da dukkan aiki kyakkyawa, da kuma dadadan maganganu.
Kuma daga cikin kyautatawa
akwai, kyautar da zaka gabatar, da dukiyar da zaka bayar, da wani amfanin da
zaka gabatar, da kalma daddada, da lafazi mai kyau, tare da haduwa mai kyau,
cikin walwala da sakin fiska, da kuma yin sallama.
An tambayi Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
wane lamarin
Musulunci yafi alkhairi? Sai ya ce: "Ka ciyar da abinci, ka karanta
sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi.
Kuma ya inganta daga gare
shi (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce:
"Murmushinka a fiskar dan'uwanka sadaka ne a gare ka".
Kyautatawa bayarwa ne wanda
baya yankewa, da fadada karbar bakunci, ko agazawa na gaskiya, ko taimako a
lokacin bukata.
Ya zo cikin littafin
Sahihul Jami'i, daga Annabi (صلى
الله عليه وسلم) ya ce: "Mutumin da
Allah yafi so, shine wanda yafi amfanar da Mutane, kuma mafi soyuwan ayyuka a
wurin Allah Mabuwayi da daukaka shine, farin cikin da ka sanya ga Musulmi, ko
ka yaye masa wani bakin ciki, ko ka biya masa wani bashi, ko ka kore masa wata
yunwa, Kuma nayi tafiya da 'Dan'uwana cikin wata bukata, lallai shine yafi
soyuwa a gare ni fiye da nayi ibadar i'itikafi a wannan Masallacin -yana nufin
Masallacin Madina- na tsawon wata guda", har karshen hadisin.
Kuma Muslim ya ruwaito
cewa, Lallai Annabi (صلى
الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya kwaranye wani bakin cikin daga
ababen bakin cikin Duniya ga wani Mumini, Allah zai kwaranye masa baki ciki
daga bakin Lahira, Kuma wanda ya saukaka wa Mutumin da yake cikin kunci, Allah
zai saukaka masa a Duniya da Lahira, Wanda ya suturce Musulmi, Allah zai
suturce shi a Duniya da Lahira, Allah yana cikin taimakon Bawa matukar Bawan
yana taimakon 'Dan'uwansa".
Ya ku Bayin
Allah! ...
Kyautatawa shine shigar da
farin ciki ga Musulmi, da bayar da mai kyau, da baiko ga wanda bashi da shi, da
taimakon wanda aka zalunta, da tsamar da Mutum daga bakin ciki, da taimakon
wanda ya fada bala'i, da ziyartar maras lafiya, da ciyar da mai jin yunwa, da
sauran dukkan ababen da za su sanya Mutane cikin farin ciki, da walwala da jin
dadi.
Allah Ta'alah ya ce: "Kuma suna ciyar da
abinci, akan sonsa ga Matalauci da Maraya da Bawa * (Suna cewa:) Muna ciyar da
ku ne, domin Allah, bamu nufin wani sakamako daga wurinku, kuma bamu nufin godiya" [Insan: 8].
Kuma Allah Ta'alah ya ce:
"Kuma suna fifita wdansu akan kawunansu, koda a tare da su akwai lalura
(talauci)"
[Hashr: 9].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mai tafiya
cikin lamarin bazaura da miskini, kamar mai jihadi ne domin daukaka kalmar
Allah, ko kuma kamar mai tsayuwan dare, mai azumin yini", Bukhariy ya ruwaito
shi.
Kuma
Annabi (صلى الله
عليه وسلم) ya ce: "Kuma hakika naga wani Mutum yana
jujjuyawa a gidan Aljannah, sakamakon wata bishiyar da ya yanke daga kan hanya,
ta kasance tana cutar da Mutane", Muslim ya ruwaito shi.
Sai ku kyautata, domin
Allah ya kyautata muku, kuma ya ninninka sakamakonsa a gare ku, "Wadanda suka
kyautata, suna da abu mai kyawu, da kuma kari" [Yunus: 26].
Ina
fadar abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah; sai ku nemi gafararSa,
lallai ne shi ya kasance ga masu komawa
gare shi, Mai yawan gafara.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Bayan haka
Ya ku Musulmai
Lamarin kyautatawa a
Musulunci, baya takaituwa kawai ga Mutane, a'a lamarin a kyautata yana game
wadanda basu magana; na dabbobi, saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم)
yana cewa: "Wata rana Wani Mutum yana tafiya akan wata hanya, kishin
ruwa ya tsananta a gare shi, sai ya samu wata rijiya, sai ya shiga cikinta ya
sha ruwa, sa'annan ya fita, sai ga wani kare yana lallagi yana cin kasa saboda
kishi, Sai Mutumin ya ce: Lallai wannan karen kishi ya tsananta a gare shi,
kwatankwacin yadda ya tsananta a gare ni! Sai ya shiga rijiyar, ya ciko
huffinsa da ruwa, sa'annan ya rike shi da bakinsa, sai ya shayar da karen, Sai
Allah ya gode masa, kuma ya gafarta masa, Sai suka ce: Ya Ma'aikin Allah! Shin muna da wani lada
akan dabbobi? Sai ya ce: Lallai cikin dukkan abu mai rai akwai lada", Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
Sai ku yi salati da sallama
ga