2018/11/23

ADDINI NASIHA NE 15 RABIYUL aWWAL 1440 Huzaifiy












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 15/RABIYYUL AWWAL/1440H
daidai da 23/NOBENBA/ 2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
ADDINI NASIHA NE
(الدين النصيحة)
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: ADDINI NASIHA NE, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO

Yabo ya tabbata ga Allah; Ma'abucin buwaya da karamci, Wanda ya kagi halitta, Mai yalwar falala da ni'imomi, Ina yin yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa kan ni'imominSa wadanda muka sani, da kuma wadanda bamu sani ba.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Mafi girman buwaya da karamci,
kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne Manzonsa, Wanda Allah ya bashi dunkulallun kalmomi (na jawami'ul kalim).
Ya Allah! ka yi dadin salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, wadanda aka shiryatar da su ga hanyar da ta fi mikewa,

Bayan haka:
Sai ku yi takawar Allah Mabuwayi da daukaka, ta hanyar neman kusanci zuwa gare shi da aikata kyawawan ayyuka, da kuma nisantar ayyukan haramun, saboda babu mai tsira (a wurin Allah) face masu takawa, kuma babu mai tabewa ya yi hasara face masu bin soye-soyen zukata, da masu sakaci.

Ya ku, Musulmai… !!!
Ku yi hisabi ga kayukanku gabanin a muku hisabi, kuma ku farkar da zukatanku daga gafalarsu, kuma ku kame rayuka daga aukawa cikin dadi irin na haramun, kuma ku yi gaggawan tuba, gabanin saukowar ajali, da yankewar guri, da katsewan yin ayyuka, domin kuna ganin saurin tafiyar shekaru, da gaggawar tafiyar kwanaki.
Kuma babu komai a bayan wannan rayuwar face mutuwa, kuma babu komai a bayan mutuwa face shiga gidan ni'ima, ko gidan azaba mai radadi.
Kuma kamar yadda kuke aiki domin duniya mai karewa, to sai ku yi aiki domin lahira mai wanzuwa, Allah Ta'alah ya ce: "Kawai, kuna fifita rayuwa ce ta Duniya * alhalin Lahira itace mafi alheri kuma mafi wanzuwa" [A'alah: 16-17].

Ya ku, Musulmai… !!!
Ku rungumi littafin Ubangijinku, domin daukakarku da rabautarku da gyaruwar lamuranku, duka a cikinsa suke, kuma a cikinsa samun rabonku bayan mutuwarku yake, da kariyarku da tsirarku daga fitintinu wadanda suke yawaita duk lokacin da Kiyamah ta kara kusantowa, fitintinu wadanda suke da sarkakiya a farkon faruwarsu, sai kuma su bayyana su fito sarari a karshen lamuransu; don haka, babu wanda zai tsira daga fitintinu sai wanda yayi riko da Alkur'ani da Sunnah, kuma ya lazimci jama'ar Musulmai;
Sai ku yi tadabburi, ko nemi sanin ma'anar littafin Allah Mabuwayi da daukaka, kuma ku yi aiki da shi, sannan ku haddace abinda addini zai tsayu da shi, na sunnar Manzon Allah صلى الله عليه وسلم, kuma akida ta ingantu da shi, itama ibada ta samu kamala da shi, musamman hadisan da ma'anoninsu ya game hukunce-hukuncen Musulunci, wadanda suka kunshi falaloli, sai ku san ma'anoninsu, domin ku yi riko da su kuma ku yi aiki, domin wannan shine MANHAJIN MAGABATA NA KWARAI, wadanda Allah Ta'alah ya fada, akansu: "Masu rigayen farko daga Muhajirawa da Ansarawa, da wadanda suka bi su da kyautatawa, Allah ya yarda da su, kuma suma sun yarda da shi, kuma ya musu tanadin gidajen Aljannoni, koramu suna gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada, wannan shine rabo mai girma" [Tauba: 100].
Kuma –a wannan matsaya- zan kawo hadisi daya daga cikin dunkulallun magana (Jawami'ul kalim), wanda ya wajaba kowane Musulmi namiji da Musulma suyi aiki da shi, a cikin kowane hali, kuma dole ne mazaje da mata su rika aiki da hadisin matukar akwai rai a cikin jikinsu, Wannan kuma shine, fadinSa –صلى الله عليه وسلم-: "Addini nasiha ne, addini nasiha ne, addini nasiha ne. Sai muka ce: Ga wa Ya Ma'aikin Allah? Ya ce: Ga Allah ne, da littafinSa, da ManzonSa, da kuma shugabannin Musulmai, da kuma sauran gama-garinsu", Muslim ya ruwaito shi, daga hadisin Tamim Ad-dariy (رضي الله عنه). Kuma wasu Maluma dayawa banda Muslim, suma sun ruwaito shi; daga cikin Maluman hadisi.
Kuma hadisi ne mai girman sha'ani, Imam Abu-dawud ya ce: "Fik-hu yana gudana akan hadisai guda biyar; hadisin halal a bayyane yake, haram a bayyane yake, da hadisin babu cuta babu cutarwa, da hadisin: dukkan ayyuka suna tare da niyyoyinsu, da hadisin: addini nasiha ne, da hadisin: Abinda na hane ku, ku nisance shi, wanda kuma na umarce ku, to ku zo da shi gwargwadon iko".
Kuma Alhafiz Abu-Nu'aimin ya ce: "Wannan hadisi ne da yake da sha'ani mai girma, Muhammadu bn Aslam Ad-duwsiy ya ambaci cewa, lallai hadisin addini nasiha ne, daya ne cikin kashi hudu na addini".

Yana daga cikin dalilan da suka nuna cewa; lallai wannan hadisin, wajibi ne ga kowane Musulmi namiji da kuma mace musulma, su yi aiki da shi, koyaushe, Lallai Allah Ta'alah ya dauke wasu ibadodi, ga wasu daga cikin Mutane, saboda wani uzuri, ko saboda wasu sababi, amma bai dauke yin nasiha ba, karkashin kowane uzuri, ko cikin kowane hali, Allah Ta'alah ya ce: "Babu kunci ga Maraunana, kuma babu laifi, ga majinyata, da wadanda basu samu abinda za su ciyar ba, matukar sun yi nasiha ga Allah da ManzonSa, kuma babu wata hanya (ta cutarwa) ga masu kyautatawa, Allah shine Mai yawan gafara, Mai jin-kai" [Tauba: 91].
Sai Allah ya bayyana cewa, ba za a yi uzuri ga wani Musulmi ba, kan yin watsi da nasiha, daidai da kyaftawar ido (koda yana da uzuri).

Sahabbai basu yi tambaya kan ma'anar nasiha ba, saboda sahabban sun san abinda kalmar take nuni akansa na ma'anonin addini mai fadi ta kowace fiska, domin hakikanin nasiha ya kunshi, martabobin addini uku na Musulunci da Imani da Ihsani.
Kawai abinda sahabbai suka tambaya, shine Ga wa ake nasihar, kuma wanene suka cancanceta?

Kuma asalin ma'anar nasiha, shine Tsamo abu ko cire shi daga abubuwan da suka shiga masa domin gurbata shi, a larabci ana cewa; Nasahal asala, wato ya tace zuma, idan Mutum ya tsaftace zumar daga kwansonsa.

Kuma MA'ANAR YIN NASIHA GA ALLAH TA'ALAH ya kunshi, Son Allah, da kan-kan-da-kai a gare shi, da rusuna masa, da mika-wuya ga shari'arsa, domin neman yardarSa da ladanSa, da kuma tsoron fushinSa da azabarSa, Allah Subhanahu ya ce: "Kawai masu imani da ayoyinmu, sune wadanda idan aka fadakar da su da ayoyin, sai su fadi suna masu sujada, kuma suna yin tasbihi game da gode wa Ubangijinsu, alhali ba su yin girman kai * sasanninsu suna nisantar wuraren kwanciya, suna kiran Ubangijinsu bisa ga tsoro da tsammani, kuma suna ciyarwa daga abinda muka azurta su" [Sajada: 15-16].
Kuma AllahTa'alah ya ce: "kuma Masu imani sune masu tsananin so ga Allah" [Bakara: 165].
Kuma Annabi صلى الله عليه وسلم  ya ce: "Ku so Allah daga dukkan zukatanku, saboda abinda yake ciyar da ku da shi, na ni'imomi".

        Kuma mafi girman nasiha ga Allah, itace bauta masa Subhanahu, ba tare an hada shi da abokin tarayya ba, cikin tsarkake niyyah, da aiki da Sunnah da bin shiriyar annabi Muhammadu صلى الله عليه وسلم, da kebance Ubangiji da na'ukan ibadodi dukkansu, kamar addu'a da neman taimako, agaji, da tawakkali, Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce, lallai kawai ina rokon Ubangijina ne, ba zan masa shirki ko hada shi da kowa ba" [Jin: 20].
        Shi kuma Ubangiji Mabuwayi da daukaka ana masa bauta ne, saboda abinda yake da su na sifofin kamala da girma, da kuma yadda ya tsarkaka daga sisfofin tawaya (nakasa), da kuma saboda abinda Allah yake da su na ni'imomi ga halittunSa, da bukatuwan bayi zuwa ga rahamarSa; don haka: Ita ibada sababi ce na samun alherorin Allah, kuma sababi ce na tunkude sharrace-sharrace ga Mutum, a cikin rayuwarsa da kuma bayan mutuwarsa.

        Kuma nasiha ga Allah Tabaraka wa Ta'alah tana kasancewa ta hanyar tabbatar wa Allah abinda ya tabbatar wa kansa a cikin littafinSa, da kuma abinda ManzonSa ya tabbatar masa da su; na sunaye da sifofi, akan abinda magabata na-kwarai suka kasance akansa, Allah ya yarda da su, amin. An ruwaito daga Abu-Umamah رضي الله عنه daga Annabi صلى الله عليه وسلم, Allah Ta'alah ya ce: "Mafi soyuwan abinda bawana ya bauta min da shi, shine yin nasiha a gare ni", Ahmad ya ruwaito shi, da 'Dabaraniy a cikin mu'ujam kabir.

        Kuma ma'anar yin nasiha ga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم itace: son annabi da darajanta shi da girmama sunnarsa, da aiki da umurninsa, da hanuwa da haninsa, da yin bauta wa Allah da shari'arsa, da bibiyar shiriyarsa, da gaskata labarunsa, da yada hadisansa, da yin da'awa zuwa ga addininsa, Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce: Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga Manzo, amma idan kuka bijire, to lallai akansa akwai abinda aka aza masa, kuma akanku akwai abinda aka aza muku, kuma idan kuka masa da'a zaku shiryatu" [Nur: 54].

Kuma ma'anar yin nasiha ga Littafin Allah Ta'alah itace: Girmama Alkur'ani mai karamci, da sonsa, da yin kokari wajen koyan karatunsa da karantar da shi, da neman sanin hukunce-hukuncensa, da yin tilawarsa tilawa ingantacciya, da yin aiki da umurnin Alkur'ani, da barin haninsa, da dawwama kan tilawarsa, da kiyaye harrufansa da iyakokinsa, da sanin tafsirinsa da ma'anoninsa, da abinda aka nufa da shi, da yin tunani cikinsa, da dabi'antuwa da shi, da yin raddi ga wadanda suka karkata wajen fahimtar Alkur'ani da sunnah, tare da ruguza barnace-barnacensu, da tsawatarwa akansu, Allah Subhanahu ya ce: "Lallai wannan Alkur'anin yana shiryatarwa zuwa ga hanyar da tafi kyawu" [Isra'i: 9].

Kuma ma'anar yin nasiha ga Shugabannin Musulmai itace: So musu alheri, da son su yi adalci, da yin farin-ciki idan aikinsu ya yi dace, da nisantar algus a gare su, da kin ha'intarsu, da kuma (uwa uba) kada Mutum ya yi fito-na-fito da su, ko ya taimaki makiya akansu, tare da taimaka musu cikin lamarin gaskiya, da yin biyayya a gare su cikin abinda ba sabo ba, da yin addu'ar dace a gare su, da addu'ar dacewa da gaskiya a cikin hukuncin da suke yi, An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Lallai Allah yana yarje muku abu uku, yana yarje muku, ku yi bauta a gare shi; kada ku hada shi da kowa, kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kada ku rarraba, kuma rika nasiha ga wadanda Allah ya jibinta musu lamuranku", Muslim ya ruwaito shi.
Abdullahi bn Mas'ud رضي الله عنه ya ce: "Lallai abinda kuke kyama alhalin kan jama'a yana hade shine mafi alheri akan abinda kuke so, a halin rarrabuwa".
Kuma an ruwaito dagan Jubair bn Mud'im, daga Annabi صلى الله عليه وسلم ya fada a cikin hudubarsa a masallacin Khaif (dake Minah): "Abu uku zuciyar Mutum Musulmi baya daukar kyashi akansu; Tsantsanta aiki ga Allah, da yin nasiha ga Majibinta lamura (shugabanni), da lazimtar jama'ar Musulmai", Ahmad ya ruwaito shi da Alhakim.
Kuma an ruwaito daga Ma'akil bn Yasar, daga Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Babu Mutumin da Allah zai bashi wani abin kiyo, sai bai kewaye su da nasiharsa ba, face ba zai shiga Aljannah ba", Bukhariy da Muslim da Ahmad suka ruwaito shi.

Ita kuma ma'anar nasiha ga dukkan Musulmai itace: Fadakar da su zuwa ga maslahohinsu, da ilmantar da su lamuran addininsu, da sitirce al'aurarsu, da kokarin toshe ko biya musu bukatu, da nisantar algus ko ha'intarsu, da nisantar yin hasada a gare su, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba" [Ali-imrana: 103], kuma Allah Ta'alah ya ce: "Lallai Muminai 'yan'uwan juna ne", [Hujurat: 10]

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na fadi abinda ku ke ji, kuma ina neman gafarar Allah Mai girma ga Ni da KU da sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,




HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah Masanin abinda ya buya na gaibu, Mai jujjuya zukata, Mai yaye musibun da suka sauka da bakin ciki, Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa gaba daya; wadanda suka gabata da wadanda zasu zo,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Mai yawan gafarar zunubai,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawanSa ne ManzonSa zababbe,
Ya Allah ka kara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa madaukaka, masu takawa.

Bayan haka … !!
Sai ku yi takawar Allah Ta'alah, a asirce, da kuma a bayyane, domin da takawa ne zaku samu mafi kololuwar daukaka, kuma ku rabautu da alkhairori a wannan rayuwar, da kuma bayan mutuwanku,

Ya ku Bayin Allah … !!
Ku yi tunani akan fadin Allah Ta'alah: "Kuma Muminai maza da mata, sashensu majibincin sashe ne, suna yin umurni da kyakkyawa, kuma suna hani da abinda ba a so, kuma suna tsayar da sallah, kuma suna bayar da zakka, kuma suna da'a ga Allah da ManzonSa, wadannan lallai Allah zai yi rahama a gare su, Lallai Allah Mabuwayi ne Mai hikima" [Tauba: 71]. A cikin wannan ayar akwai taimaka wa juna, da tallafar juna, da nasiha wa juna, da agaza wa juna, da 'yan'uwantaka, da jin-kai da rahama da kauna.
        Kuma an ruwaito daga Jarir bn Abdullahi, ya ce: "Na yi mubaya'a ga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم akan tsayar da sallah, da bada zakka, da yin nasiha ga kowane Musulmi", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Kuma Abubakar Almuzaniy ya ce: "Abubakar رضي الله عنه bai fi sauran Sahabban Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yawan azumi ko salla ba, saidai ya yi fice ne da wani abu da ya tabbatu a cikin zuciyarsa",
Ibnu-Ulayyah ya ce: "Abinda ya kasance a zuciyar Abubakar shine, soyayya don Allah Mabuwayi da daukaka, da yin nasiha ga halittarSa".
        Kuma an ruwaito daga Hakim bn Abiy-Yazid, daga Babansa, daga Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: "Idan dayanku ya nemi nasihar dan'uwansa, to ya masa nasiha", Ahmad ya ruwaito shi, da 'Dabaraniy a cikin mu'ujam kabir.
.
        Ya ku Bayin Allah… !!!
        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, ……………………………
,,,          ,,,          ,,,


2018/11/16

TAKAITACCEN TARIHIN MA'AIKATAR SARKI FAHD DA TAKE BUGA KUR'ANI MAI GIRMA, A MADINATUL MUNAWWARAH

TAKAITACCEN TARIHIN MA'AIKATAR SARKI FAHD DA TAKE BUGA KUR'ANI MAI GIRMA, A MADINATUL MUNAWWARAH

Gabatarwa
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya dauki nauyin bada kariya ga littafinSa mai karamci.
Tsira da aminci su kara tabbata ga wanda Kur'ani ya sauka a zuciyarsa, domin ya kasance mai gargadi ga Talikai.
Bayan haka:
Hakika Allah Mabuwayi da daukaka ya datar da shugabannin kasar harami biyu madaukaka kan yin hidima ga littafinSa mai karamci, ta hanyoyi masu tarin yawa, daga cikin manyansu akwai assasa wannan ma'aikatar mai albarka, a zamanin mai hidimar harami biyu tsarkaka wati sarki Fahad bn Abdul'aziz Al-Sa'ud -Allah ya yi masa rahama- wanda ya bude shi a ranar 6/Safar/1405H daidai da 30/10/1984M.
Kuma wannan ma'aikatar a zamanin Mai hidimar harami biyu madaukaka; Sarki Abdullahi bn Abdul'aziz Al-Sa'ud -Allah ya yi masa taufiki- yana samun kulawa mai girma, ta yadda ya wayi gari shine wuri na farko wanda Duniya take koma masa a lamarin Alkur'ani da ilmukansa. Kuma abubuwan da yake fitarwa suka samu karbuwa da son barka daga Musulmai a sasanin Duniya.

Kuma ma'aikatar sha'anonin Muslunci da wakafai da da'awa da fadakarwa ta Wizara, a masarautar larabawa ta Saudiya, ita take aikin kulawa da wannan hukumar ta Mujamma'a, kuma yana da sakateriyar da take gudanar da sha'anoninsa,  kuma take lura da yadda yake gudana.

MANUFOFIN MUJAMMA'A
1 Dab'in Mus-haf madaukaki, da shahararrun riwayoyi a duniyar Musulunci.
2 Daukar sautin tilawar Alkur'ani Mai karamci, da shahararrun riwayoyi a duniyar Musulunci.
3 Tarjamar ma'anonin Alkur'ani Mai girma da tafsirorinsa.
4 Bada kulawa ga ilmomin Alkur'ani Mai girma.
5 Bada kulawa ga sunnar Annabi da tarihinsa.
6 Bada kulawa ga ba'asi da rubuce-rubucen Musulunci.
7 Kokarin biya bukatun Musulmai, na cikin Saudia da wajenta, da abubuwa mabanbanta wanda Ma'aikatar ke fitarwa.
8 Yada ababen da Ma'aikatar ke fitarwa a yanar gizo-gizo, da sauran hanyoyin zamani da ake da su.

CIBIYOYI DA LAJANONI NA ILIMI A KARKASHIN MA'AIKATAR
Ma'aikatar babbar majalisa, wanda Mai girma Ministan sha'anonin Musulunci da wakafai da da'awa da fadakarwa yake shugabantarsa, wanda kuma shine shugaba na kololuwa ga Ma'aikatar.
Kuma Ma'aikatar tana da majalisar ilimi, wanda babban sakataren Ma'aikatar yake shugabantarsa.
Kuma Ma'aikatar tana kunsar CIBIYOYI da LAJANONI na ILIMI da suke tafe:
1 Cibiyar nazarin binciken da suke da alaka da Alkur'ani.
2 Cibiyar tarjamomi.
3 Cibiyar hidimar sunnar Annabi SAW da tarihinsa, da hadin guiwa da Jami'ar Musulunci da take Madinar Annabi.
4 Lajanar ilimi domin bitar Mus-hafin Madinar Annabi.
5 Lajanar kula da daukar sautin karatu.
6 Majalisar tarjamomi.
7 Lajanar gabatar da shawarwari.

BUGAWA DA RABARWA
Matsakaicin abinda Ma'aikatar ke bugawa ya zarta kofi miliyon goma, a kowace shekara daya, daga dukkan abinda Ma'aikatar ke bugawa, wanda yawansu ya haura abu guda 150.
Kuma an fara bugawa da rabarwa ne a shekarar 1405H, daidai da 1984M.
Kuma Ma'aikatar ta mallaki ababen ilimi, kayatarwa, da na ofis, da sauran shirye-shirye, wadanda suke bada tabbacin kyan dukkan abinda Ma'aikatar zata fitar. Kari akan yadda take aiki da tsare-tsaren bada kulawa iri-iri amintattu, a dukkan ayyukanta.

ABINDA MA'AIKATAR TA FITAR
* Fiye da Mus-hafai na Kur'ani ashirin Ma'aikatar tayi dab'i cikin riwayoyi mabanbanta da nau'i na rubutu ko girma da kankanta kala-kala. Tare da Mus-hafai guda takwas da aka rera sautin karatunsu cikin kasetu da faifayin cd.

* Yin tarjamar ma'anonin Alkur'ani Mai girma cikin harshe fiye da hamsin da uku daga cikin harasan Duniya, kanana da manya, da nau'in bugu iri-iri, da rakodin na tarjamomin.
Kuma Ma'aikatar a yanzu tana cigaba da nazarin wasu tarjamomin wadanda zata yi aikin buga su da izinin Allah.

* Tahkikin littafan ilimi masu amfani, a fannonin ilimin Musulunci masu yawa, da aikin dab'insu.

* Samar da shirye-shirye na komfuta dayawa, masu alaka da Kur'ani Mai girma da ilmukansa, a cikin fayafayen komfuta, wasu kuma ana kawo su a shafin intanet na wannan Ma'aikatar.

* Majallar ilimi tatacciya, da taken: MAJALLAR BA'ASI DA NAZARCE-NAZARCE MASU ALAKA DA ALKUR'ANI, mai fitowa sau biyu a kowace shekara, wanda take da manufar bada nashadin binciken ilimi, a fagen Alkur'ani da ilmukansa.

* Kuma ta samar da ba'asi tatattubfiye da 230 a semina guda biyar wanda Ma'aikatar ta tsara su, daga shekarar 1421H, daidai da 2000M.

MA'AIKATA DA LAMARIN HORASWA
Darurrukan Ma'aikata ne suke yin aiki a wannan Ma'aikatar, tsakanin Malami, da ma'aikacin ofishi, ko Mai wata sana'a, wanda yawan 'yan kasar Saudia daga cikinsu ya zarta 80/💯.
Kuma cibiyar bada horaswa ta wannan Ma'aikatar ta kan jibinci aikin bayar da gwanancewa na zango-zango ga samarin da ake neman su samu kwarewa, domin su rika aiki a mabanbantan bangarori; na fitar da Kur'ani, tun daga shirya shi, da aikin dab'insa, da yin rakodin din sautukansa, haka kuma, bangarorin ayyukan gyare-gyare dana ofis mabanbanta.
Kuma wannan cibiyar tana bibiyar Ma'aikatan da suke bakin aikinsu, domin bunkasa kwazonsu.

SHAFIN INTANET NA WANNAN HUKUMAR
www.qurancomplex.org

Wannan shafin na intanet, a yanzu yana yin aiki da harshe guda bakwai. Kuma yana gabatar wa Musulmai nau'ukan ilimin Musulunci masu fadi da zurfi.
Kamar shafin yake kawo dukkanin abinda Ma'aikatar Mujamma'a ta fitar cikin Kur'anai da littatafan da aka yi dab'i, ko shirye-shirye na cikin sauti. Haka kuma nazarce-nazarce da aka yi ba'asinsu a tarukan karawa-juna ilimi wanda Ma'aikatar Mujamma'a ta shirya su. Da tsare-tsare masu tarin yawa, masu alaka da Kur'ani ko ilimukansa.

ADIRESHI
Babbar Sakateriyar Mujamma'a na Sarki Fahd, dake dab'in Mus-hab Mai girma
Masarautar Larabawa ta Saudiya
Madinatul Munawwarah, p o box: 6262
00966 -4- 8615700
Pax:
00966 -4- 8615495 
Adireshin emel:
kfcphq@qurancomplex.org

2018/11/12

مستخلص الدراسة لموضوع المسائل العقدية المتعلقة بالنعم لأبي بكر ح


مستخلص الدراسة
بسم الله، والصلاة والسلام على رسوله الأمين، وعلى آله وصحبه أجمعين. أما بعد:
فإنه ولجمع النصوص في بيان نِعَم الله وآلائه، ثم دراستها دراسة عقدية كانت أطروحتي التي تمت مناقشتها بالجامعة الإسلامية في العام الدراسي 1439-1440هـ وذلك استكمالا لمتطلبات الحصول على درجة العالمية العالية (الدكتوراه) تحت عنوان:
"المسائلُ العقديةُ الْمتعلِّقةُ بالنِّعَمِ -جمعًا ودراسة-". وقد خلُصت إلى نتائج، أبرزها:
      أولا: مسائلُ الربوبية المتعلقة بالنعم يعود قاعدتُها إلى الإيمان بأنّ جميع ما بالخلق من النعم فمِن خلقه تعالى وإيجاده وملكه وتصريفه، {وَمَا بِكُمْ مِنْ نِعْمَةٍ فَمِنَ اللَّهِ}  [النحل: ٥٣]. وكثرة النعم وتواليها مِن أدلة عنايته تعالى بخلقه.
      ثانيا: مسائل الألوهية ترجع إلى توحيده تعالى بأفعال العباد؛ الواقعة بقلوبهم وأقوالهم وأعمالهم، وهي متشعبة، وللإيمان والعمل بموجبها تعلق وارتباط بالنعم.
      ثالثا: الشُّكرُ غايةُ الله في خَلقِه، كالعبادة، على حَدّ قوله: {وَاشْكُرُوا نِعْمَةَ اللَّهِ إِنْ كُنْتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ} [النحل: ١١٤]. وحقيقتُه شاملٌ لأعمال القلوب والجوارح وأقوال القلب واللسان.
      رابعا: أعمال القلوب المتعلقة بالنعم ترجع إلى: معرفة النعم، وقبولها، وشُهودها، والتفكر فيها، وتذكرها وعدم نسيانها، وتعظيم النعم وعدم احتقارها، وكذلك محبة المنعم المتفضل على النعم وتعظيمه، وإحسان الظن بالمنعم تعالى ورجاء حصول خيراته ونعمه، وخوف فواتها وزوالها وتغيرها إلى النقم، والاستبشار بالنعم والفرح بها، ومجانبة طلب المحمدة بها والْمُرَاءَات، ومجانبة الحسد، ومجانبة الفخر والكبر والخيلاء والعجب والغرور بالنعم.
      خامسًا: عبادات الجوارح المتعلقة بالنعم ترجع إلى: الشكر بالأعمال، وإلى التقوى فعلا وتركًا الذي هو برهان الشكر، وفعل سجود الشكر عند حدوث النعم، وإظهار النعم وإراءة أثرها، والالتزام بعدم مظاهرة المجرمين، وجزاء النعمة والإثابة عليها والمكافأة.
      سادسًا: عبادات اللسان المتعلقة بالنعم ترجع إلى: الشكر باللسان وقول كلمة الحمد والثناء على الله بفواضله ونعمه، ومدح الذي لا أحد أحبّ إليه المدح منه، والاعتراف والإقرار بالنعم، والتحدث بالنعم، وقول: ما شاء الله لا قوة إلا بالله عند الإعجاب بالنعم تبريًا مِن الحول والقوة، وسؤال الله النعم وتمامها وشكرَها والنعيم المقيم، والتعوذ بالله مِن زوال النعمة وتحولها، وشكر الناس على الجميل، والدعاء لهم.
      سابعا: توحيد الله في أسمائه وصفاته الذي هو إثباتها لله تعالى كما أثبتَها لنفسه وأثبتَها له رسولُه صلى الله عليه وسلم حسَبَ وُرودها في الكتاب والسنة، له ارتباطٌ وثيقٌ بالنعم والآلاء، لأنّ النعم أثر لصفات جمال الله وبِرّه وإحسانه.
·        لفظتا "المُنْعِم" و"المُفْضِل" عملا بقاعدة عدم تجاوز القرآن والسنة في تسميته تعالى بما لم يُسمّ بها نفسَه ولم يُسمّه بها رسولُه الكريم، ليسا مِن أسمائه تعالى الحسنى، بل المنعم والْمُفضِل داخلان في صفاته تعالى لأنه ذو النَّعماء والإفضال.
·        كما أنّ نِعَمه مرتبطةٌ باسمه تعالى "الرَّبّ" لأنه صاحب الربوبية على خلقه؛ ومرتبطة باسْمَيْه "الله والإله" لأنّ المنعم الحقيقي الخالق هو صاحب استحقاق الألوهية والعبودية على خلقه أجمعين.
·        ارتباطُ النعم ببقية أسماء جمال الله، التي هي: الرحمن الرحيم والبَرّ والرزاق والكريم والرازق والأكرم والمقيت والمعطي والباسط والجواد والمحسن والوهّاب والمنّان واللطيف؛ لأنّ النعم مِن أثر رحمته وبرِّه بعباده ورزقه وإقاتته لهم وإعطائه وبسطه وكرمه وجُوده وإحسانه وهبته ومنِّه ولُطفه بعباده وفضلِه، على قاعدة: (مُطِرْنَا بِفَضْلِ اللهِ وَرَحْمَتِهِ وغير ذلك مِن صفات الجمال، مثل كونه ذا الفضل والطَّوْل والنعماء والجلال والإكرام، وصفات أرحم الراحمين وخير الراحمين وذو الرحمة الواسعة وخير الرازقين وخير الفاتحين التي استلزمت إنعامه وإكرامه وإفضاله العامة والخاصة، في الدين والدنيا والآخرة. والله تعالى يهب لعلم وحكمة، حسب إرادته.
·        ارتباطُ النعم بأسمائه تعالى "الشاكر والحميد والشَّكُور"، لأنَّه المحمود الذي يُثنى عليه ويمدح ويمجَّد ويُشكَر بالقلب واللسان والجوارح، بسبب آلائه ونِعَمه، كما أنه الشَّكُور الذي يَقْبَل القليلَ مِن شُكْر عباده فيُكَثِّر جزاءَه ويوسِّعُه ويضاعفه.   
      ثامنًا: لا صحةَ للإيمان إلا باعتقاد أنّ جميع ما بالخلق مِن النعم فمِن الله وحده؛ خَلْقًا وإيجادًا، ومُلكًا وتصريفًا واختصاصًا، لا شريكَ له في ذلك، كما أنه لا شريكَ له في العبادة. والإيمان يزيد وينقص، ومِن أهم الأسباب الجالبة لمفقود الإيمان، والْمُقوية التي تُنَمِّي موجودَه التفكّر في خلق الله وما فيها مِن مظاهر رحمته بخلقه وبرِّه وإحسانه وعظيم جوده وإفضاله، لأنّ التَّعمق في معرفة أجناس النعم وأنواعها وأفرادها عاملٌ كبير مِن أسباب زيادة الإيمان.
      تاسعًا: كُفرُ النعمة يُعنى به إنكارُها وجحودها وتكذيبها، إنْ كان الواقع فيه: يعتقد أنّ نعمةً ما، أو كلَّها ليسَتْ مِن الله إيجادًا وإعطاءً، أو أنها مِن الآباء والأجداد والقوة، أو أنها مِن عِلم العبد وحِذْقِه وعلمه بوجوه المكاسب، أو غير ذلك إنْ كان يعتقد أنّ ما سبق هو الموجِد للنعمة؛ فنَسَبَها إليه بهذا المعنى: فهو كفرٌ أكبرُ مخرجٌ مِن الملة. أما إنْ نسَبَها إلى استحقاقه وحِذقه وقوته، مع اعتقاد أنّ الله هو الموجد لهذه النعمة، أو نسبها إلى سببٍ لم يجعله الله سبَبًا، كمن ينسب المطر للنجوم مع أنّ الله لم يجعل للنجوم سببية للمطر، فهذا وغيرُه -على الصحيح- كُفرٌ أصغرُ لا يُخرِج صاحبَه مِن الدين.
      عاشرًا: النعمُ كما ارتبطتْ بمسائل الإيمان بالله، في الربوبية والألوهية والأسماء والصفات، فهي أيضًا متعلقةٌ ببقية أركان الإيمان الخمسة؛
§        فالإيمان بالملائكة الكرام قاضٍ بأنّ لله تعالى عليهم نِعَمًا كبرى ترجع إلى: خلقه تعالى إياهم مجبولين على صفات خيِّرة من الإيمان به، ولزوم طاعته على الدوام، وعدم عصيانهم إياه، وتوفيقه تعالى لهم. كما أنّ الملائكة واسطة في إيصال أنواع النعم للخلق في الدنيا وفي القبر وفي الجنة، على حدّ قوله: {فَالْمُدَبِّراتِ أَمْرًا} [النازعات: 5]، وقوله: {وَهُمْ بِأَمْرِهِ يَعْمَلُونَ}  [الأنبياء: ٢٧].
§        ومن الإيمان بالكتب المنزلة التي نزَلَتْ لهداية الخلق، التصديق الجازم والإقرار بكلّ ما جاء فيها مِن ذكر أصول النعم ومتمماتها، التي يُنْعِم بها تعالى في الدنيا والآخرة.
§        ومن علاقة النعم بمسائل الإيمان بالرسل الكرام أنّ الأنبياء والمرسلين هم أعلى أصناف المنعَم عليهم، ثم الصِّدّيقون والشهداء والصالحون. وأُولى نِعَمِه تعالى على هؤلاء الكرام؛ لهم ولأقوامهم هو اجتباؤهم لحمل الأمانة، واختصاصهم بالوحي، وإيتاؤهم النبوة والكتاب وإرسالهم بالرسالة. تليها مِنَنُه التي امتنّ بها عليهم وأَتمها على آحادهم مما هو داخلٌ في باب الميزات والخصائص. وجنسهم أيضًا هو أفضلُ مَن قام بشكر المنعِم تعالى على نعمه، وجانبوا كفران النعم والجحود والبطر والنكران. ثم دعوا أقوامهم إلى تذكر النعم، وإلى شكر المنعم والنعم، وحذّروا مِن كفرانها.
§        ومِن علاقة الإيمان باليوم الآخر بالنعم والآلاء: أنّ النعمة الحقيقية الكاملة هي ما اتصلَتْ بسعادة الأبد، وارتبطَت بفَوز العبد بدخول الجنة والتنعم بما فيها مِن الحصول على رضوان الله تعالى، ورؤية المؤمن وجه الله الكريم وتناول بقية النعم، في جانب المآكل والمشارب والمناكح والمفارش والظلال.
§        القبرُ فيه السؤال عن نعمة الدين والبعثة وعن الرَّبّ المنعِم تعالى، ويترتب على التوفيق للإجابة لها إنعامه تعالى للعبد المؤمن الشاكر، بشتى أنواع النعم، فيكون القبر له روضة من رياض الجنة. وجامع أسباب النعيم في القبر وبعد الخروج منه هما الإيمان بالرب المنعم المتفضل وشكره على آلائه: {مَّا يَفْعَلُ اللَّهُ بِعَذَابِكُمْ إِنْ شَكَرْتُمْ وَآمَنْتُمْ} [النساء: ١٤٧].
§        السؤال بعد البعث وفي الحشر يكون عن جميع نعم الدنيا {ثُمَّ لَتُسْأَلُنَّ يَوْمَئِذٍ عَنِ النَّعِيمِ}  [التكاثر: ٨].
§        غلَب إطلاق "النعيم" الذي فيه اللزوم والثبوت على نِعَم القبر والآخرة؛ لأنها السعادةُ الحقيقيةُ التي لا تمنع ولا تَنقطِع، وفي الحديث: أنّ النَّبِيّ صلى الله عليه وسلم، قَالَ: "يُنَادِي مُنَادٍ: إِنَّ لَكُمْ أَنْ تَصِحُّوا فَلَا تَسْقَمُوا أَبَدًا، وَإِنَّ لَكُمْ أَنْ تَحْيَوْا فَلَا تَمُوتُوا أَبَدًا، وَإِنَّ لَكُمْ أَنْ تَشِبُّوا فَلَا تَهْرَمُوا أَبَدًا، وَإِنَّ لَكُمْ أَنْ تَنْعَمُوا فَلَا تَبْأَسُوا أَبَدًا" ([1]).
§        الجنةُ هي النعمة المطلقة والسعادة الأبدية، ودخولها هو الفوز العظيم والفوز الكبير والملك الكبير، فلا جوعَ فيها ولا ظمَأَ ولا عُري ولا شمسَ ولا زمهريرَ، وإذا غمس فيها أبأَسُ أهل الدنيا أيقَنَ أنه لم تَمُرّ به بُؤْسٌ قط. وفي الآخرة نعمتان جليلتان هما أكبر وأعظم من التنعم بما أُعدّ مِن النعم للمؤمن في الجنة، هما: لذة النظر إلى وجه الله الكريم، ونعمة الحصول على رضوانه تعالى وعدم سخطه أو احتجابه تعالى عن العبد، قال تعالى: {وَرِضْوَانٌ مِّنَ اللَّهِ أَكْبَرُ ذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ} [التوبة: ٧٢]، وعَنِ النَّبِي صلى الله عليه وسلم، قَالَ: «إِذَا دَخَلَ أَهْلُ الْجَنَّةِ الْجَنَّةَ –قَالَ- يَقُولُ اللَّهُ تَبَارَكَ وَتَعَالَى: تُرِيدُونَ شَيْئًا أَزِيدُكُمْ؟ فَيَقُولُونَ: أَلَمْ تُبَيِّضْ وُجُوهَنَا، أَلَمْ تُدْخِلْنَا الْجَنَّةَ، وَتُنَجِّنَا مِنَ النَّارِ؟ -قَالَ- فَيَكْشِفُ الْحِجَابَ، فَمَا أُعْطُوا شَيْئًا أَحَبَّ إِلَيْهِمْ مِنَ النَّظَرِ إِلَى رَبِّهِمْ عز وجل»([2]).
§        إنَّ من علاقة النعم بمسائل الإيمان بالقدر أنّ كل نعمة مع أنها ابتلاء فهي مِن قدر الله؛ خيره وحُلوه التي يبتليها عباده، وقد علِمَها أزلا وأبدًا كما قال: {اللَّهُ أَعْلَمُ حَيْثُ يَجْعَلُ رِسَالَتَهُ} [الأنعام: ١٢٤], وقال الكفار: {أَهَؤُلَاءِ مَنَّ اللَّهُ عَلَيْهِمْ مِنْ بَيْنِنَا أَلَيْسَ اللَّهُ بِأَعْلَمَ بِالشَّاكِرِينَ} [الأنعام: ٥٣]. وقد كتب سبحانه المقدرات جملة وتفصيلا, ضمن ما كتبه القلم وسطَّرها أول ما خلقه الله. كما شاء كونها أزلا وأرادها قبل نفاذها, كما قال عن الهداية: {يَهْدِي مَن يَشَآءُ إِلَى صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ} [البقرة: ١٤٢], وقال عن الرحمة: {وَيَرْحَمُ مَنْ يَشَاءُ} [العنكبوت: ٢١]. وهو تعالى خالق النعم التي يوجدها،  قال سبحانه: {اللَّهُ خَالِقُ كُلِّ شَيْءٍ} [الزمر: ٦٢], ومما يدخل في عمومه النعم.


([1]) أخرجه مسلم، رقم: 2837، وقد تقدم.
([2]) أخرجه مسلم، رقم: 181، وقد تقدم.

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...