HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 17/SAFAR/1440H
daidai da 26/OKTOBA/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEHI HUSAINI BN ABDUL'AZIZ AL-ASSHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA ZAKARIYYA
INA MAFITA?
(فأين المخرج؟)
Shehin Malami wato: Husaini
bn Abdul'aziz Al-as-sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai
taken:
INA
MAFITA,
Wanda
kuma a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata
ga Allah Majibincin Masu takawa, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya
sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, abin bautar halittu
gabadaya.
Kuma ina
shaidawa lallai annabinmu Muhammadu shine mafificin halittu kuma shugaban
annabawa da manzanni.
Ya Allah ka
yi salati da sallama a gare shi, da albarka, da kuma iyalansa da sahabbansa
gaba daya.
Bayan haka
Ya ku Musulmai
Ina muku
wasiyya da ni kaina da irin abinda Allah Mabuwayi da dauka ya mana wasiyya da
shi, a cikin fadinSa:
"Ya ku wadanda suka
yi imani, ku bi Allah da takawa, kuma ku yi imani da ManzonSa, zai baku ninki
biyu na rahamarSa, kuma ya sanya muku wani haske da kuke tafiya da shi, kuma ya
gafarta muku, Lallai Allah Mai gafara ne Mai rahama" [Hadid:
28].
A irin wannan zamani wanda yake
cike da fitintinu musibu kuma suka yawaita, kuma makiya suka yi karfafar mulki
ga al'umar Musulmai, wanda hakan yake haifar da nau'ukan radadi, da tarin kayan
bakin ciki mai yawa, To lallai bukata tana tsananta, kan tunatar da Musulmai
game da tabbatattun mafita na yakini; daga dukkan kowane bakin ciki, da fadakar
da su game da sabuba na hakika wanda za'a kubuta daga dukkan bacin rai da
wahalhalu.
Ya ku Musulmai!
Wannan rayuwa mai karewa
cike take da musibu da ababen wahala, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne, Mun
halitta mutum cikin wahala" [Balad: 4].
Lallai tushe mai girma na
fita daga wadannan musibun da suke cikin wannan rayuwar, da kuma kubuta daga
damuwowinta yana kasancewa ne cikin tabbatar da tsoro ko takawar Allah a boye
da kuma bayyane, da komawa ga Allah da dawowa zuwa ga kusancinsa dare da
wuni , da bada lokaci na gabadaya don girmansa, da kankan-da-kai a gare shi
cikin sauki da tsanani, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wanda ya bi Allah
da takawa, Allah zai sanya masa mafita *.Kuma ya azurta shi daga inda ba ya
zato, kuma wanda ya dogara ga Allah to Allah ya isar masa" [Dalak: 2-3]. Kuma Allah Mabuwayi
da daukaka ya ce: "Kuma wanda ya bi Allah da takawa,
zai sanya masa sauki cikin lamuransa" [Dalak: 4].
Kuma yana daga cikin nau'i
na wannan rusunawar da Kankan-da-kai da mika wuya ga Allah Mabuwayi da daukaka,
Abinda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya shiryatar da wasu sahabbai kuma ya
musu wasiya da shi; ciki da waje, cikin fadi da aiki, da hali da dabi'a; domin ya
shiryar da Abu Musa -Allah ya yarda da shi- da fadinsa a gare shi: (Ka ce: La haula
wala kuwwata illa billahi, domin ita taska ce daga cikin taskokin Aljannah), Bukhari da Muslim
suka rawaito.
Abu-zarrin -Allah ya yarda da
shi- ya ce: (Masoyina -tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi- ya min
wasiya kan na yawaita fadin: La haula wala kuwwata illah billahi).
Lallai fadin لا حول ولا
قوة إلا بالله wasiyya ce madaukakiya kan yin zikiri mai girma, domin kalmominta takaitattu
ne, amma ma'anoninta suna da girma.
Zikiri wanda harshe zai furta
shi, zuciya kuma ta sakankance da shi; wato ta ji cewa: Babu mai taimako
game da tabbatar da maslahohin duniya da lahira face Allah Mabuwayi da daukaka,
domin wanda Allah ya taimaka shine wanda aka taimaka, Wanda kuma ya tabar shine
tababbe.
Zikiri ne wanda Bawa zai
sakankance; cewa bashi da dabara shi ko waninsa na ya fita daga wani hali zuwa
wani halin, kuma bashi da wani karfi bisa ga wani sha'ani daga cikin sha'anoninsa,
ko tabbatar da wata manufa daga cikin manufofinsa face ta hanyar tsoron ALLah
mai karfi Madaukaki Mai girma.
Zikiri ne da Bawa zai
bayyana hakikanin talaucinsa da Kankan-da-kai ga UbangijinSa. kuma ya nuna cewa
yana cikin larura da matsanacin bukatuwa zuwa ga MahaliccinSa Mabuwayi Mai
rinjaye.
Zikiri ne wanda ke fitowa
daga harshen Bawan da zuciyarsa take kadaita Makadaici Mai girman sha'ani.
Wanda kuma daga wurinsa yake neman nasara da galaba da yayewa da mafita; Allah Mai
tsarki da daukaka ya ce: "Allah zai sanya sauki a bayan tsanani" [Dalak: 7].
Zikiri ne wanda da shi ake
samun rabauta da nasara da mafita da kubuta, Allah Madaukakin sarki ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani
idan kuka hadu da wata kungiyar yaki, to ku tabbata, kuma ku ambaci Allah
dayawa, domin tabbas ku samu cin nasara" [Anfal: 45].
Lallai wanna zikiri ne wanda
ya dace kowane Musulmi ya rika furta shi da harshen maganarsa da a cikin
halinsa, saboda kasancewarsa sirrin tauhidi, wanda yake hukunta rusuna wa Mahalicci,
da nuna tarewa gare shi, da kubutar da kai daga jin tana da wata dabara ko
karfi, face ta dogara ga Allah Mabuwayi da daukaka.
Ibnul-kayyim -Allah ya yi
masa rahama- ya ce; ((Wannan kalmar tana da tasiri na ban mamaki, wurin
tafiyar da abubuwa masu tsanani, da dauke wahala da shiga ga wadanda ake tsoro,
da dauke manyan wahalhalu).
Ya ku bayin Allah:
ku saurara ga wannan kissa mai girma wanda hujja ce
mai haske wanda take nuna cewa lallai karfin tauhidin bawa yakan warware bakin
ciki, duk yadda ya kai ga girmama, kuma matsaloli suna warwarewa duk yadda suka
kai ga tsananta.
Wato, kissa ce wanda dayawa daga cikin Malaman
tafsiri suka ambace ta, kuma ta zo ta fiskoki daban–daban, wanda kuma mafi
karancin darajarta a ilimin hadisi ta zama hadisi hasan, Ita ce, lallai Auf dan
Malik Al-ashja'i yana da da wanda ake kiransa Salim, kuma lallai mushirikai sun
kama shi cikin fursunonin yaki, sai ya zo wurin Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce da shi: Ya Manzon Allah: lallai abokan gaba sun kama dana
(cikin kamammun yaki), sannan ya koka masa talauci, sai Manzon Allah -tsira da
amincin Allah su kara tabbata a gare shi- ya ce: "Ba abinda ya wuni a wurin iyalan Muhammadu sai mudu
daya; Sai ka ji tsoron Allah ka yi hakuri, amma ka yawaita fadin: La haula
wala kuwwata illa billahi), A wata ruwaya kuma ya zo cewa Annabi ya umarce
shi, sannan ya umarci uwar 'dan, da su rika fadin hakan, Sai mutumin ya akaita
hakan, ana cikin haka, yayin da yake cikin gidansa, sai ga dansa ya zo masa, alhali
makiyan sun gafala daga gare shi, sai gashi ya samo rakuma; kuma ya zo da su ga
Babansa, dama baban matalauci ne, Sai baban ya je wurin Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ba shi labarin Auf da labarin rakuman, sai Manzon Allah ya
ce da shi: "ka aikata abinda ka so da rakuman, ka
yi abinda kaga dama da wadannan rakumar). Sai
ayar ta sauka wato Fadin Allah: (("Kuma wanda ya bi Allah da takawa, Allah
zai sanya masa mafita *.Kuma ya azurta shi daga inda ba ya zato, kuma wanda ya
dogara ga Allah to Allah ya isar masa" [Dalak: 2-3].
To, Daga nan ne Sahabbai
suka tafi akan wannan wasiyyar, cikin fadinsu da aiki.
Ibnu-Abiddunyah ya ruwaito cewa lallai Abu-Ubaidah
makiya sun katange shi (bashi da mafita) sai Umar ya rubuta takarda zuwa
gare shi: duk abinda ya sauka ga Mutum na tsanani, to Allah zai kawo yayewa
bayan haka, kuma lallai tsanani daya ba zai ci galaba akan sauki biyu ba,
kuma Allah yana cewa: (ku yi hakuri kuma ku
yi dauriya kuma ku yi zaman dako, kuma ku yi takawa , domin ku kai
ga cin nasara) [Ali-imrana: 200].
Lallai wannan ratayuwa ne ga Allah da dogaro a
gare shi, da ambaton Allah a harshe, wanda yake yake tafiyar da bakin
ciki, duk yadda ya kai ga tsananta, sai makomansa ya zama yayewa da samun mafita.
Fudail ya ce: Wallahi da Mutum zai debe tsammani daga halittu ka ji ba ka bukatar
komai daga gare su, to da Majibincin ya baka dukkan abinda kake so.
Ya ku taron Musulmai
Lallai yana daga SABBUBAN KWARANYE BAKIN CIKI, da
gusar da bacin-rai, lallai dan Adam a duk lokacin da yayewar ta yi
jinkiri har ya fara yanke tsammani daga gare shi bayan kuma ya yawaita rokon samun
hakan, da kuma Kankan-da-kai, amma sai bai ga wani alama na amsa addu'ar ba a tare
da shi, to wajibi ne ya koma ya rika zargin kansa, ya sake wani sabon tuba, ta
gaskiya, ya dukufa zuwa ga Allah yana mai tsarkake niyya, yana mai rusunawa ga
Majibinci, tare da yin ikirarin cewa, lallai shi ya cancanci bala'i ya sauka a
gare shi, kuma baya cikin wadanda suke ahalin amsar adu'arsu, ko a
kwaranye bakin cikinsu, saidai yana fatan samun rahamar UbangijinSa
kuma yana neman afuwarSa, to a nan ne lamarin amsar adu'arsa zata zo, da
yayewar bakin cikinsa; saboda Allah Ta'alah yana tare da wadanda zukatansu
suka rusuna zuwa gare shi, domin shi. kamar yadda Malaman magabata
suka tabbatar.
Ya ku Musulmai!
Ku kiyaye irin wannan zikiri mai girma (na LA HAULA
WALA KUWWATA ILLA BILLAHI) a kowani lokaci da yanayi, domin alherorinsa nau'uka
ne daban daban, falalolinsa kuma suna dayawa, Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ba
wani Mutum a doron kasa da zai ce: LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR,
WA SUBHANAL LAHI, WA LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAHI, face an
kankare masa kusakuransa, ko da sun fi kumfan teku yawa", Ahmad
ya rawaito, Tirmizi ya ce Hasan ne, Hakim kuma ya inganta shi kuma Zahabi ya
mar muwafaka.
An karbo daga Ubadah dan As-samit -Allah ya yarda
da da shi- ya ce: "Manzon
Allah –صلى
الله عليه وسلم- ya ce :
"Wanda ya tashi cikin dare sai yace : LA ILAHA ILLALAHU WAHDAHU LA
SHARKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR,
ALHAMDU LILLAHI, WA SUBHANAL LAHI, WA LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR, WALA
HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAHI, sai yace: Ya Allah ka gafarta mini,
ko ya yi adu'a za'a amsa masa, kuma in ya yi alwala ya yi sallah za a
karbi sallarsa", BuKhari ya rawaito shi.
Lallai adu'a ne na alheri ga Bawa, kuma kariya ne
garkuwa ga maslahohinsa, saboda Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-
ya ce: "Wanda ya ce- idan ya zo fita daga
gidansa- Bismillah, TAWAKKALTU ALAL LAHI, LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAHI, wato:
Na dogara ga Allah, babu dabara ko karfi sai gare shi, za a ce da shi: An isar maka, an baka kariya, kuma Shaidan
zai yi nesa da shi). Abu Dauda da Tirmizi ne suka rawaito.
Saboda wannan zikiri ne da yake hukunta mika wuya
ga Allah da mai da lamura zuwa gare shi, da yarda da rusuna wa gare shi, tsarki
ya tabbata a gare shi, kuma yake nuna cewa babu mai iya tunkude lamarinSa, da kuma
cewa, lallai Bawa bai mallaki komai daga cikin lamura ba, domin ragamar
al'amuran suna hannun Allah ne Madaukaki, al'amuran bayi dukansu suna kulle ne da
hukuncinSa da kaddararSa, babu mai tunkude al'amarin Allah, ko bin kadun
hukuncinSa.
Sai kasance ya kai Musulmi, mai natsuwar
zuciya, mai kwanciyan hankali, mai sakankancewa da zuwan yayewan bakin ciki da
samun mafita, domin dukkan abinda ke cikin Duniya yana karkashin iko ne na
Allah.
Dukkan abinda suke cikin wannan Duniyar ko yaya
karfinsu ya kai, ko suka kai ga tsanani, to hakika suna karkashin karfin Allah
ne da umarninSa, da hukuncinSa da kaddararSa, saboda dukkan wani mai karfi mai
rauni ne a wurin Allah Jalla wa alah.
Don haka, Ya kai Bawan Allah! ka shagaltar da kanka
da aikata nau'ukan ayyukan da'a da duk nau'uka na alheri, kuma ka lazimci
ambaton Allah da nau'ukan zikiri daban-daban, a yanayi na sauki da cuta, da
kuma tsanani da yalwa. Saboda ya zo cikin abinda ya inganta daga Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-: "Duk wanda yake son Allah ya
amsa masa adu'a yayin tsanani da bakin ciki, to ya yawaita adu'a lokacin yalwa".
Ka kuma rika aikata aiki na alheri mai yawa, da
falala mai girma, saboda Duniya ba za ta yi dadi ba sai da ambaton Allah, kamar
yadda Lahira kuma ba za ta yi dadi ba sai da afuwarSa, Aljanna kuma ba za ta yi
dadi ba sai da ganinSa.
Ka kasance mai yawan ambaton la haula wala kuwwata illa billahi domin tana taimakawa wajen dauke abubuwa masu nauyi, kuma
tana tunkude abubuwa na ban tsoro da tsanani, da ita ake samun daukaka a
dukkan yanayi.
Allah ne wanda ake neman taimako a gare shi, kuma a
gare shi ake dogaro, babu dabara ko karfi sai ga Allah Mai girma .
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah.
Kuma tsarki ya tabbata ga Allah.
Kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.
Kuma Allah shine mafi girma.
Kuma babu dabara babu karfi, face mun koma ga
Allah.
Ya Allah ka yi salati, da sallama, da albarka ga
annabinmu kuma manzonmu annabi Muhammadu, da kuma iyalansa da sahabbansa
gabadaya.
Ya ku Musulmai
Mumini mai kadaita Allah, mai kiyaye
dokokin Allah, mai lazimtar biyayyarSa da kuma biyayyar ManzonSa –صلى الله عليه وسلم- Allah yana tare da irin wannan bawan da kiyayewanSa na
musamman, Allah Madaukakin sarki yana cewa: "Allah yana tare da wadanda suka yi takawa da kuma wadanda suke su
masu kyautatawa ne", [Nahli: 128].
Wanda kuma Allah ya kasance yana tare da shi to
lallai yana tare da bangaren da ba a yin galaba akansu, da mai kiyayewa wanda ba
ya yin barci, da mai shiryarwan da ba ya bacewa, kamar yadda Katadah ya fada.
Wannan tarayya ne da Allah, wanda take hukuta bada
taimakonSa, da karfafawarSa, da kiyayewa, da agazawa, da fitar bawa daga
zaurukan bakin ciki da wahalhalu masu tsanani.
Kuma duk wanda ya kiyaye Allah, kuma ya rika kulawa
da bayar da hakkokin Allah, to zai sami Allah a gaba gare shi a duk
halin da yake ciki.
Wanda kuma ya tuna Allah a lokacin yalwa to Allah
zai kawo masa dauki a lokacin tsanani, sai ya tseratar da shi daga tsanani,
ya kubutar da shi daga musibu.
Wanda ya mu'amalanci Allah da takawa da
biyayya, cikin neman yardarSa, sai Allah ya masa mu'amala da tausasawa da
kuma taimako a yayin fadawarsa
cikin tsanani; domin ya zo a Hadisil kudusi: "Bawana ba zai gushe ba yana kusanta ta da
nafilfilu har na so shi, idan na so shi sai na kasance jinsa
da yake ji da shi, da kuma ganinsa wada yake gani da shi, da hanunsa wanda
yake damka da shi, da kafarsa wanda yake tafiya da ita, kuma idan ya roke
ni zan ba shi, kuma idan ya nemi tsarina tabbas zantsare shi)
Buhari ne ya rawaito.
Sannan ku sani mafi tsarkin abin da rayuwarmu za ta
mike da shi shagaltuwa da salati da aminci ga Annabi mai girma, ya
Allah ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga bawanka kuma manzon
ka Annabinmu Muhammad , ya Allah ka yarda da Al-kulafa'ur rashidun
Abubakar daUmar da Usman da Aliyu ya Allah ka
gyara halayenmu da halayen musulmai, ya Allah ka yaye bakin ciki ka gusar
da bacin rai , ya Allah ka tsiratar da bayin ka musulmai daga dukkan wata
jarabawa da fitina , ya Allah ka yi maganin makiya musulmai domin su ba za su
gagare ka ba ya mai girma , ya Allah ka kiyaye 'yan
uwan mu musulmai a ko ina ya Allah ka kasan ce mai taimakon su da ba su
nasara ya mabuwayi ya mai karfi, ya Allah ka datar da kadimul
haramaini ash-sharifaini cikin abin da ka ke so kuma ka yarda da
shi ya Allah ka taimaki addini da shi ka daukaka kalmar musulmai da shi,
ya Allah ka gafartawa musulmai maza da musulmai mata rayayyu daga cikin su da
matattu ya Allah ka bamu kyakkyawa anan duniya da kyakkyawa a lahira kuma
ka kare mu daga azabar wuta .
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment