HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 18/RABIYUS-SANIY/1439H
Daidai da 5 /JANAIRU / 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
DR. ABDULMUHSIN DAN MUHAMMADU DAN ABDURRAHMAN ALKASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar da
shi, babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su kara
tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da
takawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku yi riko a cikin musulunci
da igiya mai karfi (ta LA ILAHA ILLAL LAHU).
Ya ku musulmai …
Tauhidi, hakkin Allah ne akan bayinsa, Kuma da tauhidi Allah
ya tayar da ManzanninSa, kuma don shi ya saukar da littatafanSa.
Kuma HAKIKANIN
TAUHIDI shine kadaita Allah a cikin bauta.
Ita kuma BAUTA suna ne da ta game dukkan abinda Allah ke sonsa,
kuma ya yarda da shi, na daga zantuka, da ayyuka, na zahirinsu da na boye; don
haka Zuciya tana da ibadodin da suka kebance ta,
Kuma IBADAR ZUCIYA tafi girma a kan ibadar gabbai,
kuma ibadun zuciya sun fi yawa, kuma sun fi dawwama, kuma shigan ayyukan zuciya
cikin "sunan imani", shine yafi cancanta a kan shigan ayyukan gabbai,
don haka, Addinin da ke tsayuwa a zukata na daga imani; ta fiskar sanin imanin
da aiki da shi, shine ginshikin da ake nufin halittu su samar da shi. Su kuma
sauran ayyuka na zahiri suna biye da shi, kuma suna cike shi. Kuma ayyukan
gabbai basa zama ingantattu karbabbu a wurin Allah, sai idan sun bi ta hanyar
ayyukan zukata; don haka; ayyukan zuciya sune tsantsar bauta tsagwaronta. Kuma
idan ayyukan gabbai na zahiri suka wofanta daga ta'allaka da aikin zuciya sai su
kasance tamkar mataccen jikin da bashi da rai. kuma da gyaruwan zuciya, gangar
jiki ke gyaruwa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kuma lallai a cikin
jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru, to dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ta
baci, to dukkan jiki ya baci, Ita ce: zuciya", Bukhariy da Muslim.
BAYIN ALLAH, wani kan fi wani, saboda fifikon da ake samu na
abinda ke cikin zukatansu, kuma da hakan ayyukansu suke samun fifiko, Kuma
zuciya ita ce, wurin da ganin Ubangiji ke rataya, daga jikin bayinsa, Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai ne Allah,
baya yin dubi ga jikinku, ko surar halittarku, Kawai yana yin dubi ne zuwa ga
zukatanku da ayyukanku", Bukhariy da Muslim.
Yana daga cikin AYYUKAN ZUKATAN DA SUKA FI MUHIMMANCI; KYAUTATA
ZATO GA ALLAH (حسن الظن بالله), domin yana cikin abinda musulunci ya farlanta, kuma
daya ne, daga hakkokin tauhidi, da wajibansa.
MA'ANARSA MAI GAMEWA kuma shi ne; Dukkan zaton da ya allaku,
da kamalar zatin Allah (سبحانه) da kamalar sunayenSa da sifofinSa; saboda kyautata zato ga
Allah, reshe ne na ilimi ko sanin Allah, kuma abinda kyakkyawan zato ya ginu
akansa shine SANIN YALWAR RAHAMAR ALLAH, DA BUWAYARSA DA KYAUTATAWARSA, DA
KUDURARSA, DA ILIMINSA, DA KYAKKYAWAN ZABINSA, To idan ilimin bawa ga hakan ya
zama cikakke, to ba makawa, sai ya haifar masa da kyautata zato ga UbangijinSa.
Kuma ibadar kyautata zato, wani lokacin ta kan samu ne sakamakon halarto da
ma'anar wasu daga cikin sunayen Allah da sifofinSa.
Kuma wanda zuciyarsa ta
dauki hakikanin ma'anonin sunayen Allah da sifofinSa, to sai kyautata zaton da
ke da alaka da kowani suna, da sifa su tsayu a cikin zuciyarsa; saboda kowace
sifa tana da nau'in bautar da ta kebantu da ita, da nau'in kyautata zaton da ya
kebanca ta (sifar).
Kamalar Allah da girmanSa
da kyanSa, da falalolinSa ga halittunSa, suna wajabta a kyautata masa zato (جل وعلا); kuma da hakan
Allah ya umarci bayinSa, a inda ya ce: "Kuma ku kyautata, domin Allah yana
son masu kyautatawa",
[Bakara: 195].
Sufyanus sauriy –رحمه الله- ya ce: "Ma'ana: Ku kyautata
zatonku ga Allah".
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) gabanin wafatinsa ya karfafa wannan
lamari, saboda girman matsayinsa, Jabir dan Abdullahi (رضي الله عنه) ya ce na ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) gabanin rasuwarsa
da yini uku yana cewa: "Kada wani daga cikinku ya mutu, face yana
mai kyautata zatonsa ga Allah (عز وجل)", Muslim ya ruwaito
shi.
Kuma hakika Allah ya yi yabo ga bayinSa masu tawali'u a gare
shi, da cewa suna kyautata zatonsu ga Allah, kuma ya sanya bushararsu ta
gaggawa ita ce, saukake musu bautarsa, kuma ya sanya ta zama taimako a gare su,
Allah (تعالى) ya ce: "Kuma ku nemi taimako da yin hakuri,
da salla, kuma lallai ne ita sallah, mai girma ce, face akan masu tsoron Allah
* wadannan da suke da tabbacin cewa, su masu haduwa ne da Ubangijinsu, kuma
lallai ne zuwa gare shi masu komawa ne", [Bakara: 45-46].
Hakika Manzanni (عليهم السلام) sun samu matsayi madaukaki, ta fiskar
saninsu ga Allah; sai suka fawwala lamuransu zuwa gare shi, suna masu kyautata
zatonsu ga Ubangijinsu;
Ga annabi Ibrahima (عليه السلام) ya yi hijira zuwa
ga dakin Allah, alhalin babu wani mutum a wannan lokacin a garin Makkah, kuma
babu ruwa a garin, (tare da matarsa). A lokacin da annabi Ibrahima ya juya zai
tafi, sai matar ta biyo shi, tana cewa: "Ya kai Ibrahima, ina zaka tafi, ka
barmu a wannan kwarin, wanda babu wani mutum ko wani abu a cikinsa? Sai ta yi
ta gaya masa hakan, dayawa, Sai ya zama baya juyawa zuwa gare ta, Sai ta ce,
Shin Allah ne ya umarce ka, da aikata hakan? Sai ya ce, Na'am. Sai ta ce, To
lallai ba zai tozarta mu ba", Bukhariy ya ruwaito shi. Sai ya zama karshen akibar
kyautata zatonta ga Allah, shine, yadda ruwa mai albarka (na zamzam) ya bulbulo
musu, kuma aka raya wannan daki da bauta, ambaton wannan matar kuma ya wanzu a
duniya, danta Isma'ilu shi kuma ya kasance annabi, kuma daga zurriyarsa aka
samu cika-makon annabawa, kuma jagoran manzanni (محمد صلى الله عليه
وسلم).
Annabi Ya'akubu (عليه السلام) ya yi rashin 'ya'yansa, sai ya yi hakuri,
ya fawwala lamarinsa ga Allah, kuma ya ce: "Abin sani kawai,
ina kai koken bacin raina da bakin cikina zuwa ga Allah", [Yusuf: 86]. Sai
zuciyarsa ta wanzu, cike da kyautata zato ga Allah, da jin cewa shine mafi
alherin masu kiyaye bayi, sannan ya ce: "Kuma akwai tsammanin Allah ya zo min
da su gaba daya, domin shine Masani Mai hikima" [Yusuf: 83]. Kuma ya
fadakar da sauran 'ya'yansa, da irin hakan, a inda ya ce: "Ya ku diyana, sai
ku tafi, ku nemo labarin Yusufa da dan'uwansa, kada ku yanke tsammani daga
rahamar Allah, Lallai ne babu mai yanke tsammani daga rahamar Allah, face
mutane kafirai",
[Yusuf: 87].
'Ya'yan Ya'akuba, (wato, Banu-isra'ila) nau'ukan cutar da ba
za a iya jure musu ba, sun riske su, amma tare da girman ababen bakin ciki, sai
kyautata zato ga Allah ya zama abin fata, da mafita a gare su, Sai annabi musa,
ya ke cewa Mutanensa: "Ku nemi taimakon Allah, ku yi hakuri, domin kasa ta
Allah ne, yana gadar da ita ga wanda yake so, daga cikin bayinsa, kuma
kyakkyawar makoma tana ga masu takawa * Su ka ce: An cutar da mu gabanin ka zo
mana, da kuma bayan zuwanka. Sai ya ce: Ina kyautata zaton Ubangijinku zai
halaka makiyinku, ya halifantar da ku a doron kasa, domin ya ga yaya za ku
aikata",
[A'araf: 128-129].
Sai wahalar ta kara yin tsanani ga Musa (عليه السلام) da wadanda suke
tare da shi, alhalin teku yana gabansu, Fir'auna kuma da rundunarsa, suna ta bayansu,
a lokacin ne, "Sahiban Musa, suka ce, lallai mu, za a riske mu" [Shu'ara'i: 61], Sai
amsar ba'annaben da Allah ya yi magana da shi ta kasance, tana kunshe da
bayanin girman dogararsa ga Allah, da kyautata zaton da ke yi ga UbangijinSa,
Mai iko: "Sai ya ce, A'a! lallai ni, Ubangijina yana tare da ni, kuma zai
shiryar da ni"
[Shu'ara'i: 62]. Sai wahayi ya zo da abinda bai darsu a cikin zuciya ba, "Sai muka yi wahayi
ga Musa, da cewar, Ka doki teku da sandarka, sai tekun ya tsage, kowani tsagi
ya kasance kamar falalen dutse mai girma * kuma muka kusantar da wadancan
mutanen ga wurin * Sai muka tsiratar da Musa da wadanda ke tare da shi gaba
daya * Sa'annan muka dulmuyar da wadancan a cikin teku" [Shu'ara'i: 63-66].
Kuma mafi girman halittu wajen yin bauta ga Allah, da
kyautata zato a gare shi, shine annabinmu Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) saboda mutanensa
sun cutar da shi, amma sai ya wanzu yana mai aminta da wa'adin da Allah ya yi
masa, da jin samun taimakonsa, har Mala'ikan duwatsu yake cewa da shi: "Idan ka so, sai in
tanitse su da duwatsun akh-shabaini biyu; Sai ya ce: A'a, fatata itace, Allah
daga tsatsonsu ya fitar da wadanda za su bauta wa Allah; shi kadai ba tare da
sun hada shi da kowa ba", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma duk tsananin kunci da dufunsa, Annabi, lamarin kyautata
zatonsa ga ubangijinsa baya rabuwa da shi, Ya fita daga garin Makka (lokacin
hijira), akan hanyarsa ya fake a cikin wani kogo, sai kafirai suka riske shi,
sai ga su, a kewayen da ya ke, Amma sai yake ce wa sahibinsa (Abubakar) yana
mai kara karfafar guiwarsa: "Kada, ka yi bakin ciki, lallai Allah yana
tare da mu. Abubakar (رضي الله عنه) ya ce: Na ce, wa Annabi
alhalin ina cikin kogon: DA 'DAYANSU ZAI KALLI KARKASHIN KAFOFINSA BIYU, DA ZAI
GANMU, Sai ya ce: Menene zatonka, ga mutane biyun da Allah shine na ukunsu", Bukhariy ya ruwaito
shi.
Kuma tare da abinda ya hadu
da shi na dangogin cutarwa da bakin ciki da fitar da shi da aka yi daga
garinsa, da kai masa yaki ta kowani wuri, saidai kuma Manzon Allah ya amintu da
cewan wannan addinin zai kai ko-ina, a cikin zamannai, kuma ya kasance yana
cewa: "Wannan lamari –na addini- lallai zai isa ko-ina, kuma Allah ba zai
bar gidar laka ko fata ba, face ya shigar da wannan addinin a cikinsa, da
buwayar mabuwayi ko da kaskancin kaskantacce", Ahmad ya ruwaito shi.
(Wata rana) wani balaraben kauye ya zaro takobi domin ya soke
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) alhalin yana barci, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: ''Sai na farka,
alhalin takobin yana hannunsa a zare, sai ya ce: Wanene zai kare ka daga
hannuna? Sai na ce: Allah ne, har sau uku, amma Annabi bai masa ukuba ba, sai kawai ya zauna", Bukhariy ya ruwaito
shi.
A wurin Imam Ahmad kuma "Sai takobin ya fadi
daga hannunsa".
Sahabbai -in banda Annabawa-, sun fi dukkan halittu yakini;
saboda kyautata zatonsu ga Ubangijinsu, Allah (تعالى) ya ce: "Wadannan da mutane
suka ce musu, lallai mutane sun hade domin cutar da ku, ku ji tsoronsu, sai
hakan ya kara musu imani, kuma suka ce, MUN DOGARA GA ALLAH, KUMA MADALLA DA
ABIN DOGARO",
Ibnud-daginah ya zo wurin
Abubakar (رضي
الله عنه) domin Abubakar ya rika yin sallarsa da karatunsa a asirce, ko
ya mayar wa Abubakar lamarin kula da makwabtakarsa da ya dauki alkawari, sai
kuma ya baiwa kafiran kuraishawa samun ikon kama Abubakar, Sai Abubakar (رضي الله عنه) ya ce: "Lallai ni, ina
mayar maka da makwabtakanka, kuma na yarda da makwabtar Allah (عز وجل)", Bukhariy ya
ruwaito shi.
Umar (رضي الله عنه) ya ce, "Wata rana, Manzon
Allah (صلى الله عليه وسم) ya umarce mu da yin
sadaka, sai umarnin ya zo daidai da zuwan wata dukiya a wurina, Sai na ce: Yau
zan rigayi Abubakar, saboda ban taba wuce shi ba. Sai na dauko rabin dukiyata
na tafo, sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
ya ce, Me ka bari ga iyalanka? Sai na ce, Kwatankwacinsa. Ya ce: Sai Abubakar
ya zo da dukkan abinda ya mallaka, sai Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) ya ce da shi: Me ka bari ga iyalanka? Sai ya ce: Na bar musu
Allah, da ManzonSa",
Abu-dawud ya ruwaito shi.
KHADIJAH ita ce shugaban matan duniya, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya zo mata, farkon
lokacin da wahayi ya fara sauka masa, sai ya ce: "Lallai na ji tsoro
ma kaina, Sai Khadijah ta ke cewa, A'a, wallahi Allah ba zai tozarta ka ba; har
abada, saboda kasancewarka kana sadar da zumunci, kana daukan nauyin gajiyayye,
kana baiwa wanda bashi da shi, kuma kana bada abin tarbar bako, kuma kana
taimakawa akan bala'oi na gaskiya", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma akan kyautata zato ga
Allah ne, Ma'abuta ilimi da salihai suka tafi, Sufyan As-Sauri -رحمه الله- ya ce: "Bana son a baiwa
hisabina ga iyayena biyu, Ubangina yafi alkhairi akan iyayena biyu".
Kuma ya kasance daga cikin
addu'oin Sa'id bn Jubair –رحمه الله- yana cewa: "Ya Allah! Lallai ne ni ina rokonka, ka bani
gaskiyar tawakkali akanka, da kyakkyawan zato a gare ka".
A cikin aljanu akwai
salihai, wadanda zatonsu masu kyau ne, suna da yakini kan karfin Allah, da
yalwar iliminsa, sai ya kasance daga cikin zancensu akwai "Kuma lallai ne mu,
mun samu tabbacin ba zamu gagari Allah, a bayan kasa ba, kuma ba za mu buwaye
shi da gudu ba",
[Jinn: 13].
Kuma a cikin bayin Allah,
akwai wanda inda zai yi rantsuwa ga Allah, da Allah ya kubutar da shi, ba wai
saboda jin ya isa ba, a'a saboda tsantsar kyautata zato a gare shi (تعالى).
Shi kuma Mumini, yana daga
sha'aninsa koyaushe, kuma a cikin kowane hali, kyautata zato ga Ubangijinsa, Kuma
lokacin da yafi cancantar ya kasance kamar hakan, shine lokacin da ya roki
Allah, ya gana da shi; ta hanyar bauta a gare shi, yana mai samun yakinin
kusancinsa, da cewa yana amsa wa mutumin da ya roke shi, kuma baya hana wanda
ya yi tunanin samun fatansa.
Kuma yana daga cikin
SABUBBAN KARBAR TUBA; Kyautata zaton mai yinta ga UbangijinSa, Annabi (صلى الله عليه وسلم) daga cikin abin da
ke ruwaitowa daga Ubangijinsa yana cewa: "Lallai Bawana ya
aikata zunubi, sai ya samu yakinin cewa yana da Ubangijin da ke gafarta zunubi,
sannan ya share shi, ka aikata abinda ka so, lallai hakika na yafe maka", Muslim ya ruwaito
shi.
Kuma a lokacin tsanani da
fitintinu, ake sana'anta kyawawan zato ga Allah, a kuma kwaranye munanan zato a
gare shi, saboda a yakin Uhudu; sha'anin masu imani ya kasance tabbatuwa, su
kuma wadanda ba muminai ba "Suna zaton abinda ba shine gaskiya ba, a
game da Alllah"
[Ali-imrana: 154].
A lokacin yakin Ahzabi,
zace-zace nau'i-nau'i sun yi yawa dangane da Allah, sai Allah ya ke fada
dangane da wasu bangare "A lokacin da munafikai ke cewa, da kuma
wadanda a cikin zukatansu akwai cuta, ba komai Allah da Manzonsa suka alkawarta
a gare mu ba, face rudi" [Ahzabi: 12]. Amma su kuma sahabbai, sai suka samu
yakini cewar, wadannan fitintinun jarabawa ce daga Allah, wanda nasara da
kwaranyewa ke biyo bayansu, Allah ya ce: " kuma a yayin da
muminai suka ga kungiyoyin kafirai, sai suka ce, wannan shine abinda Allah da
ManzonSa suka mana, wa'adi, Allah da ManzonSa sun yi gaskiya, kuma wannan bai
kara musu komai ba, face imani da sallamawa", [Ahzabi: 22].
Saboda samun mafita, a
lokacin kunci, yana nan ne cikin kyautata zato ga Allah, domin mutane ukun da aka
jinkirta karbar tubansu, ba a kwaranye musu abinda ya sauka a gare su na bakin
ciki ba, sai a lokacin da suka kyautata zato ga Allah shi kadai, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma Allah ya karbi
tuban mutane ukun da aka jinkirtar, har kasa da yalwarta ta yi kunci akansu,
kuma su ka yi zaton babu wata mafaka daga Allah, face komawa zuwa gare shi,
sa'annan sai Allah ya karbi tubansu, domin su tabbatu akan tuba, Lallai Allah
shine Mai karbar tuba, Mai jin kai", [Tauba: 119].
Duk wanda rayuwarsa ta yi
kunci, to cikin kyautata zatonsa akwai yalwa da kwaranye matsalolinsa, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda talauci ya
sauka masa, sai ya sauke shi ga mutane, to ba za a toshe talaucinsa ba, Wanda
kuma talauci ya sauka a gare shi, sai ya sauke ta ga Allah, to yayi kusa Allah
ya kawo masa arziki cikin gaggawa, ko kuma a can", Tirmiziy ya ruwaito
shi.
Zubairu bn Al-awwam –رضي الله عنه- ya ce ga 'diyansa
Abdullahi: "Ya kai diyana, idan ka gagara biyan wani abu daga cikin bashin da
ake bina, ka nemi taimako Majibincina; shugabana akan haka, Abdullahi ya ce: Wallahi
ban gane abinda yayi nufi ba, sai da na ce: Wanene kuma shugabanka? Ya
Mahaifina, Ya ce: Allah. Abdullahu ya ce: Ina rantsuwa da Allah, Ban auka cikin
wani bakin ciki ba akan wani abu na bashinsa, face nace: Ya Majibincin Zubairu,
ka biya masa bashinsa, sai ya biya masa", Bukhariy ya ruwaito shi.
Allah shine Mai karfi, Mai
iko, kuma idan ya tashi bada nasara ga bayinsa, babu mai cin galaba akansu.
Kuma yana daga cikin yakini, kyautata wa Allah zato akan hakan, Allah (تعالى) ya ce: "Idan Allah ya baku
nasa, to babu mai rinjayarku, kuma idan ya kyale ku, to wanene zai taimake ku a
bayansa?"
[Ali-imrana: 160].
Kuma shi Allah Mai jin kai
ne Mai rahama, ga wanda ya yi imani da shi (سبحانه) ya kuma aikata aiki na kwarai, kuma idan
ya yi fatan samun rahamar Allah zai same ta, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Yayin da Allah ya
halitta halittu, sai ya rubuta a cikin wani littafi, wanda ke wurinsa, a saman
al'arshi; cewa: Lallai rahamata ta rinjayi fushina", Bukhariy da Muslim.
Kuma shi Allah (سبحانه) Mai yalwar gafara
da kyauta ne, Duk wanda ya kyautata zatonsa da shi, cikin wadacinSa da
karamcinSa, da gafararSa, sai ya bashi abinda ya roka; domin ya kan sauka
"zuwa saman Duniya, sai ya ce: Wa zai roke ni, in amsa masa?" kuma "Hannayensa suna
cike; ciyarwa bata tauye su, yana yin baiwa cikin dare da yini".
Allah Mai yawan karbar tuba
ne, yana farin ciki da tuban bayinSa, kuma yana shumfuda hannunsa da dare,
domin wanda ya munana aiki da rana ya tuba, kuma yana shumfuda hannunsa da
rana, domin wanda ya munana aiki da dare ya tuba. Kuma yana daga cikin
kamalarSa; baya korar wanda ya fiskanto shi.
Kuma lokacin da bawa yafi
tsananin bukatar ibadar kyautata zato ga ubangijinsa, shine idan ajalinsa ya
kusanto shi, kuma yake bankwana da duniya, yake fiskantar UbangijinSa, Manzon
Allah (صلى
الله عليه وسلم) "Kada 'dayanku ya mutu, face yana mai kyautata zatonsa
ga Allah (عز وجل)", Muslim ya ruwaito
Cikin kyautata zato ga
Allah, akwai bin umarninSa, da tabbatar da bautarSa.
Kuma bawa a wurin
Ubangijinsa zai samu irin abinda ya yi zato ne, Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace: "…Ni, ina yadda
bawana ya yi zatona, kuma ina tare da shi, idan ya ambace ni", Bukhariy da Muslim.
Abdullahi bn Mas'ud (رضي الله عنه) ya ce: "Ina rantsewa da
wanda babu wani abin bauta face shi, Bawa ba zai kyautata zatonsa ga Allah
Mabuwayi da daukaka ba, face Allahu (عز وجل) ya bashi abinda ke zato
a wurinsa",
Wannan kuma saboda alkhairi dukkansa yana hannunsa.
Kuma idan kyautata zato,
kofarsa ta budu ga bawa, sai Allah ya bude masa kofar alkhairi mai girma a
cikin addini, Abdullahi bn Mas'ud (رضي الله عنه) yana cewa: "Ina rantsuwa da
Allah, wanda babu abin bautawa da cancanta, face shi, Ba a baiwa bawa mumini
wani abinda yafi alkhairi fiye da kyautata zato ga Allah (عز وجل)".
AYYUKAN MUTANE SUNA
KASANCEWA NE gwargwadon yadda suke zaton Ubangijinsu, Saboda shi MUMINI ya
kyautata zatonsa ga Allah, sai ya kyautata aiki, Shi kuma KAFIRI Ya munana
zatonsa, sai kuma ya munana aiki.
Kuma cikin ibadar kyautata
zato, akwai kyan musulunci, da kamalar imani, kuma wannan ibadar hanya ce ta
zuwa Aljannah, ga ma'abucinta.
Ibadar tana gadar da
Tawakkali ga Allah, da amintuwa da shi, Ibnul-kayyim –رحمه الله- yace: "Kuma gwargwadon
kyautata zatonka ga Ubangijinka, da fatanka ga Ubangiji, gwargwadon haka,
tawakkalinka a gare shi zai kasance, wannan ya sanya wasu maluman suka fassara
tawakkali, da kyautata zato ga Allah. Sai dai maganar gaskiya itace, lallai
kyautata zato a gare shi, yana janyo dogaro a gare shi (tawakkali); saboda a
hankalce ba a iya fahimtar, mutum ya dogara ga wanda ya munana zato akansa, ko
kuma ka yi tawakkali ga wanda baka fatan samun abinda ke hannunsa".
Kuma yana daga cikin FA'IDODIN
kyautata zato ga Allah, samun natsuwar zuci, da fiskantar Allah, da tuba
zuwa gare shi, saboda babu abinda yafi yaye matsalolin kirji, ko ya fadada
zuciyar bawa, bayan imani, fiye da amintuwa da Allah, da fatan Allah, da
kyautata masa zato.
Kuma a cikin kyautata zato,
akwai abinda ke sanya ma'abutansa ga "Fa'al; kyakkyawar fata", Annabi
(صلى
الله عليه وسلم) ya ce: "Cuta bata rabuwa da-kanta, kuma canfi baya
tasiri, Kyautata zato (na Fa'alu mai kyau) yana burge ni; wanda kuma shi ne,
fadin kalma mai kyau",
Bukhariy da Muslim.
Alhaliymiy –رحمه الله- ya ce, "Canfi munana zato
ne ga Allah, shi kuma Fa'alu; kyautata zato ne ga Allah Ta'alah".
Kyautata zato, yana
taimakon ma'abucinsa kan bada kyauta, da gwarzantaka, kuma yana haifar masa da
samun karfi, Abu-Abdullahi As-Sajiy –رحمه الله- ya ce: "Wanda ya aminta da
Allah, to lallai ya taskance karfinsa".
Kuma kyautata zato, shine
mafi alherin guzuri, kuma madalla da shi ga abinda aka tattala, An ce wa
Salamah bn Diynaar –رحمه الله- Ya Aba-Hazim, Me ya same ka? Sai ya ce,"Amintuwa ne da
Allah, da debe zato kan abinda ke hannun mutane".
Kuma wanda ya kyautata
zatonsa ga Ubangijinsa, sai ransa ta zama mai kyauta, ya rika rabar da
dukiyarsa, yana mai samun yakini kan fadin Allah "Kuma duk abinda
kuka ciyar, to Allah zai bada mayewarsa" [Saba'i: 39], Sulaimanud Daraniy ya ce:
"Wanda ya aminta da Allah cikin lamarin arzikinsa, sai dabi'unsa su
kara kyau, sai kuma ya gadar masa da hakuri, ransa ta yi ta kyauta tana
ciyarwa, waswasinsa su yi karanci cikin sallarsa".
Kyautata zato, jagora ne
zuwa ga kyakkyawan fata, ga samun abinda ke wurin Allah, da kuma amintuwar
samun abinda ya yi wa'adi da shi, da aikata alkhairi; cikin fatan samun
falalarsa, kamar yadda ya ke cewa: "Kuma duk abinda suka aikata na alkhairi, to ba za a yi musu musunsa ba" [Ali-imrana: 115].
Allah yana mu'amalantar
bayinsa ne, gwargwadon yadda suke zatonsa, kuma sakayya ta kan zama daga jinsin
aiki; don haka Duk wanda ya yi zaton samun alkhairi, to yana da hakan.
Wanda kuma ya yi zaton kishiyar
haka, to kada ya zargi wani sai kansa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Allah Mabuwayi da
daukaka ya ce: Ni ina yadda bawana ya yi zatona; sai bawana ya yi zatona kamar
yadda ya ga dama; domin idan ya yi zaton alkhairi zai samu, idan kuma ya yi zaton
sharri, shima zai samu", Ahmad ya ruwaito shi.
Kuma duk lokacin da bawa ya
zama mai kyautata zato ga Allah, to lallai Allah baya kunyata ma'abuta kyautata
zatonsu a gare shi; kwata-kwata.
Saboda cikakken karramawa
na kasancewa ne a ranar kiyama, kuma a can ne, wanda ya kyautata zatonsa ga
Ubangijinsa zai ce: "Ku karba ku karanta littafina * lallai ne ni na tabbata
cewa ni mai haduwa ne da hisabina * saboda haka shi yana cikin wata rayuwa
yardadda, a cikin aljanna madaukakiya" [Alhakkah: 19-22].
BAYAN HAKA;
Ya ku Musulmai;;;
Allah Mai girma ne Mai
Karfi da Buwaya, idan ya nufi abu, sai yace, ya kasance, sai kuma ya kasancen,
ya yi alkawarin kiyaye littafinsa, kuma ya sanya kyakkyawan karshe –a
ko-yaushe- ga masu takawa, kuma yana azurta wanda ya so ba tare da lissafi ba,
kuma yana kwaranye bakin cikin mutumin da ya sanya mafakarsa zuwa ga Allah.
Kuma duk wanda iliminsa da
Allah ya karu, sai yakininsa ga Allah ya karu, kuma duk wanda ya munana zato ga
Allah, to hakan ya haifu ne sakamakon jahiltar kamalar sunayen Allah da
sifofinsa, kuma hakan yana daga cikin sifofin mutanen jahiliyya, Allah (سبحانه) ya ce: "Suna zaton abinda
ba shine gaskiya ba, a game da Allah; irin zaton jahiliyya" [Ali-imrana: 154].
Kuma yana daga FA'IDODIN
IMANI DA SUNAYEN ALLAH DA SIFOFINSA, Kyautata zato a gare shi, da dogaro
akansa, da fawwala lamura zuwa gare shi.
A UZU BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIM:
"Duk wanda ya ke
fatan haduwa da Ubangijinsa; to sai ya yi aiki na kwarai, kuma kada ya hada
kowa, ga bauta wa Ubangijinsa" [Kahf: 110].
ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALKUR'ANI MAI GIRMA. …
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah
kan kyautatawarSa; Godiya kuma tasa ce
bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya; Ina mai
girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa.
Ya Allah, ka yi dadin
salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.
Ya ku musulmai…
Hakikanin kyautata zato ga Allah yana kasancewa ne cikin
kyautata aiki, kuma kyautata zato zai yi amfani ne idan ya kasance tare da
"ihsani (bautar Allah da kyau; kamar mutum yana ganinsa).
Kuma wanda yafi dukkan
mutane kyautata zato ga UbangijinSa shine wanda yafi su yin da'a a gare shi.
Kuma duk lokacin da zaton
bawa ga UbangijinSa ya kyautatu, sai aikinsa babu makawa, ya yi kyau.
Wanda kuma aikinsa ya yi
muni, sai zace-zacensa ga Allah, su yi muni.
Kuma ta yaya wanda ya
abauce ga Allah, ta hanyar aukawa cikin ababen da suke fusata shi, yake kinsu
zai iya kyautata zatonsa ga Ubangijinsa.
Wanda kuma ya riya kyautata
zato ga Allah, sai ya zama baya tsoronsa, to wannan yana yaudarar kansa; saboda
duk lokacin da kyautata zato ya hada hanya da aikata zunubai, to mai aikata shi
yana amintuwa ne daga makircin Allah.
Kuma kyautata zato, idan ya
kwashi mai shi, izuwa ga biyayyar Allah, to wannan shine mai amfani, Idan kuma
ya kai shi ga aikin badala, da dulmuya cikin sabo, to wannan rudi ne.
>>>
Sannan ku sani, lallai Allah ya umarce ku da yin salati da
sallama ga AnnabinSa, a cikin mafi kyan littafinSa, inda ya ce: "Lallai ne Allah da
Mala'ikunSa, suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku waxanda su ka imani, ku
yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa", [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga
annabinmu Muhammadu,
Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu,
waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci,
Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka hada
da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da Musulmai, ka
qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya
–Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala,
da kuma sauran kasashen Musulmai.
Bayin Allah!!!
"Lallai Allah yana
yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani
akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu
tunawa"
[Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai
girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari,
kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke
aikatawa.
No comments:
Post a Comment