2017/12/21

خطبة الحذيفي 4 ربيع الثاني 1439ه KAN AURE DA SHIKA A MUSULUNCE











HUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى الله عليه وسلم
JUMA'A, 4/RABIYUS SANIY/1439H
daidai da 22/DISEMBA/2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: AURE DA SHIKA A MUSULUNCI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga AllahN da Ya halitta jinsin maza da mata, daga abinda kasa ke tsirarwa, da kuma cikin mutane, har da abinda mutane ba su sani ba.
Kuma Ubangiji Mabuwayi da daukaka ya yi umarni kan yin gyara da kawo gyara, ya kuma yi hani kan barna, a cikin fadinsa;
"Kuma ka kawo gyara, kada ka bi hanyar mabarnata" [A'araf: 142].
Sannan Allah (تبارك وتعالى) ya shar'anta shari'oi, domin maslahar bayi da amfaninsu, da tunkude barna da kuma dukkan ababen  da suke cutar da mutane da aljanu.
        Ina yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa, ina tuba zuwa gare shi, ina neman gafararSa,
Ina kuma shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Mawadacin da bashi da bukatar talikai.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Mai gaskiya, Amintacce,
Ya Allah! ka yi salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gaba daya.

Bayan haka:
Ku bi Allah da takawa, a asirce da kuma a bayyane, saboda babu mutumin da ke samun rabo a cikin rayuwarsa, da bayan mutuwarsa, sai da takawa, kuma babu wanda zai tabe, ya yi hasara, sai ta hanyar bin son zuciya.

Ya ku mutane
Ku rika tuna mafarin halittarku (daga mutane biyu; Adamu da Hauwa'u), da yadda mazan cikinku da matanku suka yawaita, alhalin kun samu ne daga rai guda daya; Wanda Allah ya halitta masa matarsa daga jikinsa, Allah (سبحانه) ya ce: "Ya ku mutane, ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halitta ku daga rai guda, kuma ya halitta matarsa daga gare shi, kuma daga gare su, ya watsa maza dayawa, da mata" [Nisa'i: 1].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Shi ne wanda ya halitta ku daga rai guda, kuma ya halitta masa matarsa daga gare shi, domin ya samu natsuwa da ita" [A'araf: 189].
        Sa'annan sai sunnar Allah da shari'arsa suka gudana, akan kulluwar namiji da mace ta hanyar kulla ko daura aure, irin na shari'a, domin mutane su iya gina gidan auratayya, kuma domin a amsa ga bukatar halitta; ta irin sha'awar da ke tsakanin mutane, da bin hanyar aure; ba ta hanyar zina ba, domin hanyar aure ita ce, ke haifar da kamewa, da albarka, da bunkasa, da tsarkaka, da arziki, da lafiyar zukata, da samun doriyar shekaru; ta hanyar zurriyar mutum nagari; wato salihai.
Ita kuma hanyar zina tana da dauda, ga janyo cutukan zuciya, da lalacewar namiji da mace, ga kuma irin kaskancin da sabo ke janyowa, da matsalolin rayuwa, da tafiyar da albarkar rayuwa, da samun matsaloli cikin 'ya'ya da jikoki, sannan sai azabar lahira, An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) cikin abinda ya gani na abubuwan al'ajabi, a daren da aka yi masa isra'i da mi'iraji, Ya ce: "Sa'annan sai ya je ga wasu mutane, wadanda ake farfasa kayukansu da dutse, duk lokacin da aka fasa, sai kan ya koma kamar yadda ya kasance daga farko, kuma baza a dena aikata musu hakan ba. Sai ya ce: Su wanene wadannan Ya Jibrilu? Sai ya ce: Wadannan sune kansu ke yin nauyi kan halartar sallolin farilla.
Sa'annan sai ya je ga wasu mutane, wadanda aka sanya takardu ko fata ta gabansu, da kuma ta duburarsu, suna kai-komo, kamar yadda rakumi ko dabbobi ke kai-komo, kuma suna cin kayar rakuma (dari'in), da kuma cin itaciyar danyan wuta (zakkum), da tsakuwa ko duwatsun da aka dafa su da wuta. Sai ya ce: Su wanene wadannan Ya Jibrilu? Sai ya ce: Wadannan sune wadanda ba sa bayar da sadakar dukiyarsu (zakkah), kuma Allah bai zalunce su da komai ba.
Sa'annan sai ya je ga mutanen da a gaba gare su akwai dafaffen naman da ke cikin tukunya, da kuma wani naman danye a cikin wata tukunyar mai dauda, amma sai gashi suna cin wannan danyen mai dauda, suna barin nunannen mai tsafta, Sai ya ce: Su wanene wadannan Ya Jibrilu? Sai ya ce: Wannan mutum ne daga cikin al'ummarka, zai kasance yana da mace ta halal, mai tsafta, sai ya je wurin wata mace mai dauda, sai ya kwana a wurinta, har safiya. Da kuma matar da za ta tashi daga wurin mijinta na halal mai tsafta, sai ta je wurin wani namji mai dauda; ta kwana da shi, har safiya". Ibnu-Jarir ya ruwaito shi a cikin tafsirinsa.
Kuma ya zo cikin hadisin Sa'ad bn Sinan Alkhudriy (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) akan isra'i da mi'iraji, ya ce: "Sa'annan sai na yi gaba kadan, sai ga ni a wurin wasu kwanukan da suke dauke da nama a cikinsu a yayyanke, amma babu wanda ke kusantarsu, sai ga ni a wurin wasu kwanukan da suke dauke da naman da yake doyi, a wurin kuma akwai mutanen da suke cin wannan naman. Sai na ce: Ya Jibrilu, su wanene wadannan? Ya ce: Wadannan daga cikin al'ummarka, suna barin halaliyarsu, sai su je ga haram. Ya ce: Sannan sai ya matsa gaba kadan, sai ga ni wurin wasu mutanen da cikkinsu kamar gidaje, duk lokacin da dayansu ya yunkura don ya tashi sai ya fadi, yana cewa: Ya Ubangijina, kada ka tashi kiyama. Sai ya ce: kuma su suna kan hanya irin ta iyalan fir'auna. Ya ce: Sai hanyar ta zo, ta rika tattaka su, Sai ya ce: Wadannan a cikin al'ummarka sune masu cin riba, "Wadanda suke cin riba baza su tashi ba, sai kamar wanda shedan ke dimautarwa daga shafa ke tashi" Baihakiy ya ruwaito shi a cikin littafin Dala'ilun nubuwwati.

Gidan aure mafaka ce da ke bada kulawa ga zurriya, kuma take tausaya musu, take damuwa da su, take ilmantar da su.
Kuma uwa da uba sune ke shirya al'umma ('ya'ya da jikoki) domin su iya daukar nauyace-nauyacen rayuwa, da amfanar da daukacin al'umma, da bunkasa yara cikin kowane sha'ani, kuma sune suke fadakar da su zuwa ga riko da kowace dabi'a mai kyau, su kuma yi hani kan aiki da kowace dabi'a abar aibantawa, kuma su rika bada tarbiyya akan aikin kwarai, domin neman dacewa da gidan lahira, da kuma rayuwa ta har abada, kuma sai karamin yaro ya yi koyi da abinda yake gani a gida, sai kuma ya tasirantu da abinda ya ke gani, kuma ya ke ji, tun da bashi da ikon karanta tarihi, domin daukar izina daga cikinsa, da kuma abin koyi.

Shi kuma daura aure ko kulla shi, alkawari ne mai girma, kuma igiya ce mai karfi, kuma zumuncin sadarwa mai tsananin muhimmanci, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma idan kun yi nufin musanya mace, a gurbin wata macen, kuma kun baiwa dayansu tarin dukiya (kindari), to kada ku karbi wani abu daga cikinsa, Shin za ku karbe shi da karya da zunubi bayyananne? * Kuma yaya za ku karbe shi, alhalin, sashenku ya sadu da sashe, kuma mata sun riki alkawari mai kauri daga gare ku" [Nisa'i:20-21].
Maluman tafsiri suka fassara alkawari mai kauri da cewa, shine: Daura aure.

Kuma daura aure, yana kunsar maslahohi da amfani ga miji da mata, da wasu amfani da maslahohin na 'ya'ya, da maslahohi da amfani ga makusantan ma'auratan biyu, da kuma wasu amfani da maslahohin ga daukacin al'umma, da  wasu maslahohin na duniya da lahira, wadanda ba za a iya kididdige wadannan amfanonin ba.

Shi kuma warware wannan alkawarin, da lalata wannan kullin, da tsinke igiyar auratayya, ta hanyar SHIKA, yana rurrushe wadancan maslahohin da amfanonin gaba dayansu. Sai miji ya auka cikin fitintinun da za su cutar da shi ga addininsa da duniyarsa da lafiyarsa.
Kuma itama mace, idan aka sake ta, sai ta auka cikin fitintinun da suka fi tsanani akan wanda mijin ke aukawa cikinsu, kuma wanda aka sake ba za ta samu ikon mayar da rayuwarta kamar yadda ta kasance ba, kuma sai ta rayu cikin nadama, musamman a wannan zamanin wanda a cikinsa mazajen da za su iya dacewa da halinta suka yi karanci, sai 'ya'yansu su watse, su kuma fiskanci rayuwa mai matukar tsanani, wacce ta banbanta da wanda suka yi alhalin suna karkashin inuwa ko kulawar iyaye guda biyu (uwa da uba) a hade, sai kuma su rasa dukkan dadin da zai sanya rayuwarsu cikin walwala, sai su fiskanci lalacewar halayya da nau'ukansa mabanbanta, da kuma cutuka iri-iri, sai itama al'umma gaba dayanta, ta cutu, da matsaloli masu cutarwa, wanda su ke kasancewa bayan aukuwar shika, sai ka ga, yanke zumunta yana yawaita.
Kuma duk yadda aka kai makura wajen kididdige matsalolin da suke cikin shikar aure, to lamarin ya fi haka.
Kuma, domin ka san barnar da shika ke haifarwa, da yawaitar matsalolinta, kebantattu da masu gamewa, sai ka yi tunani cikin hadisin Jabir (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai ya ce: "Lallai Iblisu ya kan dora al'arshinsa ko gadon mulki akan ruwa (teku), sa'annan ya tura 'yan farautarsa, kuma wanda zai fi su kusancin matsayi da Iblisu shine wanda yafi tsananin fitina; Sai daya daga cikinsu ya zo, ya ce: Na aikata kaza, da kaza, Sai ya ce: Ba ka aikata komai ba. Sa'annan sai daya daga cikinsu ya zo ya ce; Ban bar wane ba, har sai da na raba tsakaninsa da tsakanin matarsa; Sai Iblisu ya kusantar da shi, yana cewa: Na'am, Kai ne goga, Sa'annan sai ya rungume shi", Muslim ya ruwaito shi.

Kuma lallai wasu mutane, sun yi sako-sako da batun shika, sai suka dauki lamarinsa da sauki, sai su ka auka cikin lamura masu hatsari, da sharrace-sharrace masu tarin yawa, sannan su kan aukar da wasunsu cikin abinda suka auka a cikinsu.
Hakika shika saboda sabuba masu rauni, ya yawaita a wannan zamanin, ko saboda dalilai marasa kan-gado.
Kuma SABBUBAN SHIKA A WANNAN ZAMANIN suna da yawa,
Yana daga MAFI GIRMANSU: JAHILTAR HUKUNCE-HUKUNCEN SHIKAN, a cikin shari'a, da rashin aiki da Kur'ani da sunnah. Saboda shari'ar musulunci ta kewaye kullin aure, da dukkan abinda zai bashi kariya da kula, kuma ta kare aure da muhimmiyar katanga, domin bashi kariya; kuma domin kada ya tsattsage, ya rushe, ya girgiza; a lokacin kadawar guguwar son zuciya.
Kuma domin kasancewar sababin shika ka iya kasancewa daga miji, ko daga matar, ko daga miji da matar, ko daga wasu daga cikin makusantansu; Sai shari'a ta magance kowane irin yanayin da ka iya zama sababin shika;
Sai Allah a cikin littafinsa ya umarci miji, da ya girmama lamarin aure, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma kada ku rike mata da cutarwa; har ku kekare iyaka, kuma duk wanda ya aikata hakan, to ya zalunci kansa, kuma kada ku riki ayoyin Allah da izgili" [Bakara: 231].
Kuma Allah ya ce: "Kuma su mata, suna da kwatankwacin abinda ke kansu (na hakkoki) da kyautatawa, Kuma su maza suna da wata daraja akan mata" [Bakara: 228].
        Maluman tafsiri suka ce:
Mace akan mijinta, tana da hakkoki, misalin hakkokin mijin da ke kan matarsa, wajen kyautata zamantakewa, Sai kuma namiji ya samu fifiko akan mace, ta fiskar kasantuwarsa mai tsayuwa da lamarinta, .
Don haka wajibi ne, akan namiji yayi zamantakewa da matarsa cikin abinda aka sani da kuma kyautatawa, Idan kuma ya kita, to sai ya dau hakuri, la'alla yanayin ya canzu, izuwa ga wanda yafi kyau, ko la'alla a azurta shi da 'ya'ya salihai tare da ita, sannan a bashi ladan hakurinsa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma ku yi zamantakewa da su da kyautatawa, domin idan kun ki su, to, tana yiwuwa ku ki abu, sai Allah ya sanya alkhairi mai yawa a cikinsa" [Nisa'i: 19].
        Kuma wajibi ne ga miji da matarsa, su rika gyara lamuran da suke janyo sabani, tun suna farko-farkonsu; domin kada kafar sabanin ta fadada.
        Kuma wajibi ne ga miji da mace; kowannensu ya san dan'uwansa; sai kowanne ya rika aikata abinda zai fi yardar da sahibinsa, Ya kuma rika nisantar abinda dayan baya so, Wannan kuma abu ne mai sauki, da ba a boye ya ke ba.
       
        YANA DAGA CIKIN SABBUBAN WANZUWAR AURE: Kokarin yin sulhu a tsakanin ma'auratan, daga ma'abuta alkhairi, masu sulhuntawa, da kawo gyara, domin kowanne ya iya samun hakkokinsa na wajibi, wanda ke kan sahibinsa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma idan ku ka ji tsoron sabani a tsakaninsu, sai ku tayar da mai hukunci daga cikin iyalansa, da mai hukunci daga iyalanta, idan sun nufi sulhu a tsakaninsu, to lallai Allah zai daidaita tsakaninsu, Lallai ne Allah ya kasance Masani Mai bada labari" [Nisa'i: 35].

        KUMA YANA DAGA SABBUBAN DAWWAMAR AURE DA JIN DADINSA: Hakuri da yin rangwame, domin dacin da ke cikin hakuri, dan kadan, zaki ne na tsawon zamani ke biyo bayansa, Kuma ba wani abinda ake fiskantar ababen ki da shi, wanda ya kai hakuri girma, Allah (تعالى) ya ce: "Kawai, masu hakuri ana cika ladansu, ba tare da lissafi ba" [Zumar: 10].
        Rangwame da yin afuwa, suna kawata rayuwa, kuma suna sanya ma rayuwa walwala da farin ciki da kyau. Kuma da shi ake warkar da kurjin da zamantakewa ta haifar. Kuma, Yafiya da yin afuwa dole ne a rayuwa, musamman kuma tsakanin ma'aurata biyu.
Kuma idan ya kasance cikin lamura ne na karin kwalliya (ba wajibi ba), Ko kuma cikin lamuran da za a iya jinkirta su, to lallai yin rangwame a irin wannan, shine mafi alheri ga ma'aurata. Musamman kuma a irin wannan zamanin, wanda kokarin samar da bukatun rayuwa, ya wahalar da yawa-yawan mazaje, tare da cewa, wasu ababen ba na lalura ko dole ba ne.
Kuma lallai neman bada dukkan hakkoki, da rashin rangwantawa, ko yafe wasu hakkokin, yana gadar da guje wa juna da kiyayya a tsakanin ma'aurata. Alhalin shi kuma aure ruhinsa shine, taimakakkeniya, da jin-kan juna, Allah (تعالى) ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani lallai ne wasu daga matanku da 'ya'yanku makiya ne a gare ku, sai ku kiyaye su, kuma idan kuka yafe kuma kuka kau da kai, kuma kuka gafarta, to lallai Allah Mai gafara ne Mai jin kai", [Tagabun: 14].
Gabar da ake nufi a wannan ayar ita ce, sanyaya guiwar miji ko uba kan aikata alkhairi, ko kuma rashin taimakonsa, ko kuma hana shi aikata aikhairin.
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ka riki abinda ya saukaka, kuma ka yi umarni da alheri, kuma ka kau da kai daga jahilai" [A'araf: 199].

KUMA YANA DAGA SABBUBAN DAWWAMAR AURE: MIJI ya yi ta kokarin gyara abinda ya karkace na halin matarsa, da abinda shari'a ta halatta, kuma ta yi izini, Allah (تعالى) ya ce: "Su salihan mata masu da'a ne, masu tsarewa ga gaibi saboda abinda Allah ya tsare. Su kuma wadanda ku ke tsoron bijirewarsu, to, ku yi musu gargadi, kuma ku kaurace musu a wuraren kwanciya, kuma ku doke su, Idan kuma suka muku da'a, to kada ku nemi wata hanya akansu" [Nisa'i: 34].

Kuma wajibi ne akan alkalai su rika yin sulhi tsakanin ma'aurata biyu, cikin abinda ake kaiwa gare su na kararraki, har a samu ittifaki, a kawar da shika.

Shi kuma HAKKIN MACE AKAN MIJINTA shi ne ya yi zamantakewa da ita da kyautatawa, ya kuma bata gidan da ya yi daidai da irinta, tare da ciyarwa da tufatarwa, da bayar da alkhairi, da kamewa ga barin cutar da ita.

Kuma lallai SABABIN SHIKA YANA IYA KASANCEWA DAGA MATAR NE, saboda kaushin harshenta, ko munin halinta, da jahilcinta, Don haka, wajibi ne akan mace ta rika gyara halinta, tana mai biyayya ga mijinta, ta yi bakin kokarinta wajen tarbiyyar 'ya'yanta da ingantacciyar tarbiyya, An ruwaito daga Abdurrahman bn Auf (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Idan mace ta yi sallolinta biyar, ta yi azuminta na wata, ta kiyaye farjinta, ta yi biyayya ga mijinta, Sai ace mata: Ki shiga Aljannah, daga dukkar kofar da ki ka so", Ahmad ya ruwaito shi, kuma hadisi ne hasan.

Kuma wajibi ne ga mace ta rika hidima ga mijinta, da kyautatawa, tana mai koyi da sahabbai mata –رضي الله عنهن-.
Kuma abu ne mai kyan gaske ta rika yin tarayya da mijinta cikin farin cikinsa da bacin ransa, kuma ta kasance mai taimakonsa wajen biyayya ga Allah Ta'alah.

KUMA YANA DAGA SABBUBAN SAMUWAR SHIKA: Shisshigin wani daga dangin miji ko mata, ko kuma danginsu gaba daya, Sai su ji tsoron Allah, kuma su fadi magata ta daidai. Kuma ya zo cikin hadisi, cewa: "Allah ya la'anci mutumin da ya bata matar wani a gare shi, ko kuma ya bata mijin ga matarsa".

Kuma wajibi ga MACE TA TSAYU WAJEN BADA HAKKIN MAKUSANTAN MIJINTA, musamman kuma iyayensa biyu.
Kuma shima mijin WAJIBI NE YA TSAYU WAJEN BAYAR DA HAKKIN MAKUSANTAN MATARSA; saboda sakaci kan hakkin makusantan ma'aurata, sau dayawa ya kan zama sababin shikan aure.

KUMA YANA DAGA SABBUBAN SHIKA: Bibiyar fina-finan da su ke rushe dabi'a, ko shafukan yanan gizo-gizo (internet) na haram, wadanda suke yada barna.

KUMA YANA DAGA SABBUBAN SHIKA: Fitan mace daga gida ba tare da samun izinin mijinta ba , kuma baya halatta a gare ta, ta fita ba tare da izininsa ba, domin miji shine ke da ma'aunin auna lamura.

Kuma idan SABBUBAN ZAMAN AURE SUKA GAGARA To lallai Allah ya halatta yin shika, kuma ya zo cikin hadisi cewa: "Halal din da Allah ya fi kinsa, shine shika".

Sai miji ya yi shika irin na shari'a, bayan tsanaki da bi-sannu-sannu, kamar yadda Allah ya yi umarni a cikin fadinsa: "Ya kai wannan Annabin idan za ku saki mata, sai ku sake su ga iddarsu, kuma ku kididdige iddar" [Dalak: 1].
Maluman tafsiri suka ce:
Sai ya sake ta a cikin tsarkin da bai sadu da ita a cikinsa ba, shika daya, Idan ya so, sai ya mata kome a cikin wannan iddar. Idan kuma ya so, sai ya barta har ta gama iddarta, sai ta fita daga mulkinsa.
Kuma lallai shika ta irin wannan hanyar tana bude kofar fatan yin kome, don wanzar da auren, ko a sake sabon aure, idan har ta yi tsarki, bayan idda.

Sai ka yi dubi, ga yadda aka karfafa lamarin aure, da yadda shari'ar gaskiya ta kiyaye shi. Kuma ka yi dubi kan sakacin mutanen wannan zamanin kan lamarin shika, da abinda shikan ke janyowa; na kayan bacin rai.
Allah (تعالى) yana cewa: "Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku bi, hanyoyin shedan, domin duk wanda ya bi hanyoyin shedan, to lallai shi yana umarni ne da alfasha, da kuma munkari", [Nur: 21].

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Mai rahama Mai jin-kai, ya shar'anta hukunce-hukunce da iliminsa da hikimarsa da kuma rahamarsa.
Tsarki ya tabbata a gare shi; abin bauta Mai girma.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Masani Mai hikima.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanka ne kuma manzonka,

Ya Allah ka kara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa, masu riko da shari'arsa mikakkiya.

Bayan haka … !!
Ku ji tsoron Allah, iyakar tsoronsa, kuma ku yi riko a musulunci da igiya mai karfi.

Ya ku Bayin Allah … !!
Allah yana cewa:  "Kuma ku taimaki juna akan biyayya da takawar Allah, kada ku taimaki juna akan sabo da ketare iyaka, kuma ku ji tsoron Allah, lallai ne Allah Mai tsananin ukuba ne" [Ma'ida: 2],

Ya ku Musulmai,
Shika ya zama wani abinda ke gudana akan harasan wasu samarin ba tare da tsare ko kula da hakkokin 'ya'yansu, ko wani makusancinsu ba, ko kuma lura da wani ba,
Kuma hakan yana aukuwa, ta hanyar maimaita shi, a cikin zamani masu nisa da juna, ko maimaita fadinsa a cikin majalisa daya, sai kuma ya tafi yana ta neman fatawowi, ko ya ce, zai yi wayo, wani lokacin hanyoyi su kan toshe masa, sai ya yi ta nadamar da ba za ta masa amfani ba, Alhalin Allah kuma yana cewa: "Duk wanda ya ji tsoron Allah, to zai sanya masa mafita * kuma ya azurta shi, ta yadda baya tsammani" [Dalak: 2-3].
Kuma duk wanda ya ji tsoron Allah, cikin lamarin shikansa, ta fiskar da shari'a ta yarda, sai Allah ya sanya masa mafita.
Kuma duk wanda ya dauki aure da girma, bai yi sako-sako da shi ba, sai Allah ya sanya masa albarka a cikin aurensa, kuma ya samu kyakkayawar natija.

Kuma wasu daga cikin na'ukan shika kebantattu, yin shika a cikin wadannan halayen ya kan kasance laifi ne (sabo), kamar yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce wa Abu-Ayyub: "Lallai sake Ummu-Ayyub, laifi ne".

Ya ku bayin Allah!
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
 ……………………………
,,,          ,,,          ,,,


No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...