2017/12/08

Hudubar Dr Buaijan 20 Rabiul Awwal 1439 daidai 8 Disemba 2017











HUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى الله عليه وسلم
JUMA'A, 20/RABI'UL AWWAL/1439H
daidai da 8/DISAMBA/ 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
SHIRI GA AZUMIN RAMADHANA
Shehin Malami wato: Abdullahi bn Abdurrahman Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: , Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah; wanda zamani ke juyawa da umarninSa, kuma lokatai ke riskar juna da izininSa, "Yana shigar da dare akan yini, kuma yana shigar da yini akan dare" [zumar: 5], Ya sanya rana ta zama babban haske mai zafi, wata kuma mai haske, kuma ya kaddara shi manziloli, domin ku san kidayar shekaru da lissafi [Yunus: 5].
Ina yin yabo ga Ubangijina, saboda shine ma'abucin yabo da girma, kuma ina yin godiya a gare shi akan ni'imominSa da basu kididdiguwa ko kirguwa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, cikin sha'aninSa,
kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, mai kira ga samun yardarSa, Wanda ya turo shi da shiriya da kuma addinin gaskiya, domin ya daukaka shi akan addinai gaba daya, koda mushirkai sun ki [Tauba: 33].

Allah ka yi karin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da wanda ya shiryu da shiriyarsa, ya kuma bi sunnarsa, har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka:
Lallai mafi gaskiyar zance shine littafin Allah, kuma mafi karfin igiya ita ce, Kalmar takawa (ta LA ILAHA ILLAL LAHU), Kuma mafi alherin addinai shine addinin annabi Ibrahima, kuma mafi kyawun kissosi shine na cikin Kur'ani, kuma mafificiyar shiriya ita ce shiriyar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), kuma mafiya sharrin lamura sune kagaggu daga cikinsu, kuma kowace bidi'a bata ce.
Ina yin wasici a gare ku, da ni; kaina, da tsoron Allah Mabuwayi da daukaka a asirce da kuma a bayyane, saboda takawa ita ce tsira a duniya mai karewa, kuma dalilin samun babban rabo a lahira mai wanzuwa, "Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, kuma ku fadi magana madaidaiciya * Zai kyautata muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku, kuma wanda ya yi da'a ga Allah da ManzonSa, to lallai ya rabauta da babban rabo mai girma" [Ahzab: 70-71].
Ya ku bayin Allah
A wasu yinin, mutane kan nemi kariya daga matsanancin zafin tsakiyar rana, ko kunar lokacin zafi. A wani yinin kuma, sai mutane su shirya domin tunkarar funturun sanyi, sai kuma su nemi wanduna da kayan sanyi. To, lallai cikin hakan akwai babban wa'azin jan-kunne ga ma'abuta basirori; domin tsananin sanyi, da kuma tsananin zafi, numfashi ne guda biyu, na Jahannama; Hadisi ya zo daga Abu-hurairah –رضي الله عنه-, a lokacin da ya ce: "Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: Idan zafi ya tsananta to, ku sanyaya sallah; domin tsananin zafi yana daga numfashin Jahannama, kuma wutar ta kai kukanta zuwa ga Ubangijinta; a inda ta ce: Ya Ubangijina, lallai sashena ya cinye sashe, Sai ya mata izinin ta rika numfashi guda biyu; numfashi daya a lokacin sanyi, numfashi dayan kuma a lokacin zafi. Don haka, Duk abinda kuka samu na sanyin jaura, to yana daga numfashin jahannama, kuma duk abinda kuka samu na yanayin zafi ko zazzafar iska, to daga numfashin Jahannama ne". Bukhariy da Muslim.
To, Menene zatonku –Ya ku bayin Allah- dangane da wutar jahannama?
Lallai ita ce wutar Allah wanda ake furawa, * wanda take lekawa akan zukata" [Humaza: 6-7]. "Lallai ne ita tana yin jifa da tartsatsi kamar benayi, * kamar dai su rakummai ne fatsatse" [Mursalat: 32], "Bata ragewa kuma bata bari * mai nacewa ce ga jiki da kuna * akanta akwai masu tsaro guda goma sha tara" [Mudassir: 28-30], "A aha, lallai ne fa ita ce wutar laza * mai twale fatar goshi * tana kiran wanda ya juya baya (daga addini) kuma ya kauda kai * ya tara dukiya, kuma ya kiyaye ta" [Ma'arij: 15-18], kuma lallai ita ce "wutar hawuya * kuma me ya sanar da kai mecece ita? Wata wuta ce mai zafi" [Alkari'ah: 9-11].
An kunna ta, aka iza, na tsawon shekaru dubu, har ta zama kalar ja, sa'annan aka iza ta, na tsawon shekaru dubu, har ta koma fari, sa'annan aka sake iza ta na tsawon shekaru dubu har ta zama baki, don haka, ita baka ce, kirin. Wacce tartsatsinta baya yin haske, baki-n wutar kuma, baya mutuwa;
"Sai ku ji tsoron wutar da makamacinta sune mutane da duwatsu" [Tahrim: 6],
Hadisi ya zo daga Abu-hurairah, lallai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wutarku wanda 'dan-adam ke furawa, bangare ce guda, daga bangarori saba'in na zafin wutar Jahannama", Sai suka ce: Idan ta kasance kamar ta duniya ita ma ta wadatar? Ya ma'aikin Allah! Sai ya ce: "Lallai an fifita wutar lahira akan ta duniya, da bangare sittin da tara, dukkansu zafinsu kamar nata". Allah ya tsare mu da ku, daga aukawa wuta.

Ya ku taron musulmai
Lallai sunnonin rayuwa suna gudana ne cikin wani tsari mai ban kayatarwa, da hukuncin Allah da lamarinsa abin sallamawa, kuma Allah ya kan ji-kan wanda ya nufa da wadannan sunnonin sai su amfanar da shi. Kuma ya kan yi ibtila'i ga wanda ya so, da su, sai su cutar da shi; saboda haka, an hore wadannan sunnonin da nufin Allah, kuma basu da nufin zartarwa ko ikon juya komai, "Wannan shine Allah Ubangijinku, mulki nasa ne, su kuma wadannan da ku ke roko baicinsa, basu mallakar koda fatar bayan dabino" [Fadir: 13].

Hakika Allah ya taimaki annabi Nuhu, da ruwan Dufana, sai ya halakar da mutanensa ta hanyar nitsarwa a cikin ruwa, Sai kuma ya tsamar da shi, da wadannan da suka yi imani da shi.

Kuma Allah ya bada nasara ga annabi Musa, da teku, ya kuma nitsar da fir'auna a cikinsa, da wadanda suke tare da shi.

Kuma ya taimaki annabi Hudu, sai ya halakar da mutanensa da iska kaikasasshiya, wanda bata barin abinda ta bi ta kansa face, ta sanya shi kamar rududdugagen kashi.

Kuma ya taimaki annabi Salihu, sai ya halakar da mutanensa, da tsawa, alhalin suna gani, kuma basu samu damar tsayawa ba, kuma basu kasance wadanda za a agaza musu ba.

"Kuma kowannensu mun kama shi da laifinsa, kuma daga cikinsu akwai wanda muka aika iskar tsakuwa akansa, kuma daga cikinsu akwai wanda tsawa ta kama, kuma daga cikinsu akwai wanda muka birkice kasa da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda muka nitsar. Kuma baya yiwuwa ga Allah ya zalunce su, amma sun kasance kansu suke zalunta" [Ankabut: 40].
Don haka, ababen da suke aukuwa a cikin duniya, dukkansu a hannun Allah suke, kuma karkashin nufin Allah, bashi da abokin tarayya, a cikin hakan.

A UZU BILLAHI MINAS-SHAIDANIR RAJIM:
"Kuma na Allah ne, mulkin sammai da kasa, kuma zuwa ga Allah makoma take" [Nur: 42].

Allah ya yi albarka ga ku, da ni cikin alkur'ani mai girma, ya kuma mafanar da ni da ku da abinda ke cikinsa na ayoyi da tunatarwa mai hikima, Ina fadan abinda kuke ji, kuma, …

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya halicci sammai da kasa, kuma ya sanya duffai da haske [An'am: 1], mai juya yinnai da watanni, kuma mai karar da shekaru da zamannai, ina yin yabo a gare shi a dukkan lamari.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya.
Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa
Allah ya kara salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa.

Ya ku bayin Allah !! …
Lallai sanyin lokacin funturu yana dauke da wahalar da ta sanya hukunce-hukuncen shari'a basu gafala da shi ba, Sai mai shari'a ya yi rangwame kan ayi shafa akan safa (huffi) domin dauke wahala, a kuma yi taimama idan za a cutu, kamar yadda aka shar'anta yin sallar rokon ruwa, idan aka samu fari a lokacinsa, da kuma yin addu'ar neman sama ta washe (ko tsayawar ruwa), a yayin bukatar hakan; saboda wahala tana janyo sauki, kuma Ubangiji bai sanya muku wani kunci a cikin addini ba. Wannan kuma an shar'anta su ne, ba wai domin kaiwa makura wajen walwala ne ko hutu ba, A'a, saboda Allah ya tayar da ManzonSa da shiriya, da addinin gaskiya, domin ya daukake shi akan addinai gaba daya, koda mushirkai sun ki. Kuma sai ya zabar masa da wannan yankin tsakiya na duniya, wanda ya hada matsanancin zafin kudancin duniya, da kuma funturun sanyin da ke arewacinta, sai ya cancantar da shi (da sauran mazauna wannan yankin) zamowa matsakaitan mutane tsaka-tsaki, wajen iya jure wa dabi'ar yanayi; ta fiskar zafinsa da sanyi, har su iya jure daukar sakon manzanci zuwa ga duniya gaba daya;
Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana dora sahabbansa akan jure wa wahalhalun tsananin zafi da sanyi, a cikin halin yunwa da kishi, yana mai karfafa musu cewa, gwargwadon wahala shine gwargwadon iya cimma buri, kuma ba a iya riskar daukaka ko samunta, sai bayan an ci wahala, kuma aljanna an kewaye ta ne da ababen da rai ke ki, kamar yadda aka kewaye wuta da sha'awoyi, kuma ni'ima ba a riskarta da ni'ima.
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya fita zuwa ga yakin Ahzab, domin ya hadu da makiyansa, alhalin mayaka dubu goma sun yi tarun-tarume akansa, Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya fita shi da sahabbansa a lokacin matsanancin sanyi, da kuma jure wahalwalu da bacin rai da gajiya, tare da hakurin kishi da yunwa, Huzaifah (رضي الله عنه) yana cewa: "Da dai, wani dare bai taba zuwa mana, wanda yafi tsananin dufu, ko yafi tsananin sanyi, ko yafi tsananin tasowar iska, kamar wannan daren ba, saboda sautin iskar da ke tashi a cikin daren kamar misalin sautin tsawa ne, ga matsanancin dufun da ya kai dayanmu baya iya ganin yatsarsa".

Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya fita yakin Tabuka ne cikin mayaka dubu talatin, a yanayin bugun iskar zafi mai tsanani, har munafikai suke fadin maganganun sace guiwa, suna cewa: "Kada ku fita zuwa ga yaki a cikin zafi" [Tauba: 81]. Sai Allah ya mayar musu da martini: "Kace wutar jahannama, tafi tsananin zafi, da sun kasance suna da sani" [Tauba: 81].
Umar (رضي الله عنه) ya ce: "Mun fita zuwa ga yakin Tabuka ne a lokacin matsanancin zafi, sai muka yada zango a wani masaukin da kishi ya kama mu, har sai da muka yi zaton wuyoyinmu zasu yayyanke, kuma har sai da ya zama, mutum yana soke rakuminsa, sai ya matse abinda ya saura a cikin tunbinsa don ya sha, ya kuma sanya abinda ya saura akan hantarsa".
        To, haka Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ilmantar da sahabbai kan sadaukarwa ga wannan addinin, da kuma yin jihadi fi sabilil Lahi, a cikin sauki ko tsanani da cuta da lokacin yaki, ya kuma koya musu rayuwar wahala, da juriya, da yin hakurin aiwatar da aikin da'a.

        Ya ku bayin Allah
Lallai Allah ya mana baiwar ni'imomin da ba a iya kididdige su, kuma ya kwararo mana ni'imominSa na zahiri da na boye, saboda karamcinsa da kyautarSa da falalarSa. Kuma hakika ya halicce mu domin yin bauta a gare shi; don haka wajibi ne akanmu mu forar da kayukanmu don yin biyayya a gare shi, a cikin wahala da sauki, a lokacin nashadi ko ki, a halin lafiya da walwala, ko cuta.
Kuma wajibi ne mu yi amfani da ni'imomin Allah wajen yin biyayya a gare shi, mu yi kwadayin su zama taimako a gare mu, wajen aikata ababen da za su yardar da Shi, kuma sababin shiga aljannoninSa.
Muna kuma neman tsarin kan aiki da ni'imomin da ya yi akanmu, wajen saba masa, ko su kasance sababin fushinSa da azabarSa.

Ya ku bayin Allah
Kyautayi ga halittu yana tunkude mummunan kaddara, kuma mafi girman abinda ake tunkude musibobi da bala'i da su, kuma yake janyo albarka da bunkasar dukiya, shine: Tallafawa fakirai, musamman a lokacin shigan funturu, saboda akwai daga cikin fakirai wanda sanyi ke addabarsa ba tare da tufa ba, daga cikinsu kuma akwai wanda yunwa ke kayar da shi, ba tare da yana da riyal daya ko dinari ba, daga cikinsu kuma akwai wanda ruwan kasa da na sama ke malale musu mahallai, daga cikinsu akwai gajiyayyu da marayu da zawarawa da tsofaffi masu yawan shekaru, kuma daga cikinsu akwai makusanci ta fiskar dangantaka, da bako, da makwabci.
Sai ku yi laluben 'yan'uwanku mabukata, kuna masu farawa da danginku, da ma'abuta zumuncinku, sa'annan sai makwabtanku da garinku, sa'annan sai wanda suka fi kusa da ku; bi da bi, kuma kada mutum ya raina kyakkawan abu, duk karancinsa.
Ku rika yaye musu bakin ciki, ku taimaki wanda aka zalunta, ku tallafawa mutumin da aka masa rauni, "kuma ku ji toron Allah, wa la alla sai a yi muku rahama".

Ya ku taron musulmai
Lallai bada kariya ga kasa, ko garurrukan musulunci, kare asalin musuluncin ne, da abinda musulmai suka mallaka, da mutuncinsu da ababen mallakarsu. Kuma musulmai gaba dayansu gini ne guda daya, kuma al'umma daya, kuma gangan jiki daya, ta yadda idan wata gaba ta koka, sai sauran jikin ya amsa, ta hanyar zazzabi da kasa yin barci.
Kuma duk wani ta'addancin da zai taba tubali daya daga ginin musulmai, da garurrukansu, to lallai ta'addanci ne ga alfarmar dukkan musulmai, To, yaya kuma idan ta'addancin ya kasance ga Kudus ne? Yaya idan ta'addancin ya kasance ga kudus ne? wurin saukar wahayi, wurin da aka tayar da Annabawa da Manzanni, kuma alkiblan annabawa wanda musulmai suka fiskance ta da sallolinsu, a wani zamani na tarihi, wurin da aka yi Isra'i da Annabi (صلى الله عليه وسلم), kuma mihirabinsa wanda a cikinsa ya limanci dukkan annabawa (عليهم الصلاة والسلام) a salla.
"Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi isra'i da bawansa, cikin dare, daga Masallaci Mai Alfarma, zuwa Masallaci Mai Nisa, wanda muka sanya albarka a gefensa, domin mu nuna masa daga ayoyinmu, lallai ne shi, shi ne Mai ji, Mai gani" [Isra'i: 1].
Kuma lallai lokaci ya yi, wanda dukkan duniya zata sani, lallai lokaci ya yi, wanda dukkan duniya za su sani, cewa lallai wurin da aka yi isra'i da Annabinmu Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) wuri ne, na dukkan masu tauhidi, a ko-ina suke a duniya, wuri ne na wadanda suka fadi LA ILAHA ILLAL LAHU, MUHAMMADUR RASULUL LAHI.
Kuma masarautar Larabawa ta Saudiya ta kasance kuma ba za ta gushe ba, tana tsaye, kuma baza ta taba ja-da baya ko ta nisanci manufofinta da halayenta na musulunci da 'dan'adamtaka ba, a kan lamarin Falasdinu, da Kudus wadanda aka mamaye, Kuma za ta ci gaba da ayyukanta da izinin Allah, wajen warware wannan matsalar, da kuma taimaka wa wanda aka zalunta.
Kuma rayukanmu natsattsu ne da alkawarin Allah, domin duk yadda makiya suka yi karfa-karfa, to ita kuma nasara tana tare da muminai masu hakuri. Kuma lallai wannan masallacin yana da Ubangijinsa wanda zai kare shi,
"Kuma hakika mun rubuta a cikin littatafain baicin Lauhul mahfuz, cewa lallai kasa, Bayina salihai suke gadonta" [Anbiya'i: 105].
Ya Allah! Ka kiyaye Kudus madaukaki, kuma ka dawo da shi cikin kulawar musulunci da musulmai, Ya Allah ka daukaka musulunci da musulmai
Bayin Allah
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].

,,,          ,,,          ,,,

No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...