HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 07/Safar/1439H
daidai da 27/Oktoba/ 2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar,
babu mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar, to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne, ya isar da manzanci, ya kawo amana, ya
yi nasiha ga al'umma, kuma ya yi jihadi domin Allah iyakar jihadi, har mutuwa
ta zo masa.
Salatin Allah ya qara tabbata
a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa da wanda suka bi su da kyautatawa; da
sallamar amintarwa mai yawa, har zuwa ranar hisabi.
Bayan haka;
Lallai mafi alherin zance
shine maganar Allah, mafi alherin shiriya kuma shiriyar annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم), kuma mafi sharrin lamura sune qirqirarru
daga cikinsu, kuma kowace bidi'a vata ce, kowace vata kuma tana cikin wuta.
Ya ku bayin Allah;
Lallai abinda al'umma ta ke
shigewa ta cikinsa na fitintinu da bala'oi, da jarrabawa, da tsanani, da
fin-qarfin maqiya, lallai jarrabawa ne, kuma xauraya, da matashiya ga wata
nasara bayyananna, da buwaya, da tabbatarwa da bada iko, da izinin Allah, Allah
Ta'alah ya ce: "Ko kuna zaton ku shiga Aljanna, tun gabanin misalign waxanda suka
shige daga gabaninku bai zo muku ba? Wahaloli da cuta sun shafe su, kuma aka
jijjiga su, har manzonsu da waxanda suka yi Imani tare da shi, suka ce: Yaushe
taimakon Allah zai zo? To! Lallai taimakon Allah yana kusa!" [Baqara: 214].
Ya ku taron musulmai … !!!
Haqiqa waxanda suka kasance
a gabaninku, ana kama mutum sai a tona masa rami a cikin qasa, sai a zo da
zarto, a xora akan kansa; har a raba shi kashi biyu, hakan ba zai kautar da shi
daga addininsa ba, kuma ana taje gashinsa da matajin qarfe tsakanin naman
jikinsa da jijiya gabanin qashi, hakan baya kautar da shi daga addininsa ba.
Wallahi lallai Allah zai cika wannan al'amari (addini), "Kuma lallai Allah
zai taimaki wanda ke taimakonsa, lallai ne Allah Mai qarfi ne Mabuwayi", [Hajj: 40].
Ya ku bayin Allah … !!!
Haqiqa wanda suka kasance
farkon waxanda suka bayyanar da musulunci mutane bakwai ne, wato: Manzon Allah
–صلى الله عليه وسلم- da Abubakar, da
Ammar da mahaifiyarsa Sumayyah, da Suhaib, da Bilal, da Almiqdad, Amma shi
Manzon Allah –صلى
الله عليه وسلم- sai Allah ya bashi kariya da samuwar Baffansa; abu-xalib, Shi
kuma Abubakar, sai Allah ya bashi kariya da mutanensa, Su kuma sauran sai
mushirkai suka xauke su, suka xanxana musu mummunar azaba, sai dai babu wani
daga cikinsu face ya aikata musu abinda suka yi nufi, in banda Bilal; saboda
shi kam, bai xauki ransa a bakin komai ba, a lamarin Allah, sai ya zama araha a
wurin mutanensa; sai mushirkai suka yi ta cutar da shi, suna azabta shi, wai
domin ko zai fita daga addininsa, amma sai ya fiskance su da qara daskarewa, da
tabbatuwa, sai suka yi ta azabtar da shi, suna jarabtarsa. Kuma shugaban da ya
mallaki Bilal; wato Umayyat bn Khalaf ya kasance yana fitar da Bilal idan zafin
ranar azahar ta take, sai ya shumfuxa shi akan bayansa, a kan duwatsun Bax-ha'u
ta garin Makkah, sannan sai ya yi umarnin a xora dutse mai girma akan qirjinsa,
sa'annan sai y ace masa: Ba za ka gushe ba a cikin wannan baqar wahalar hark a
mutu, ko ka kafirce da Muhammadu, Sai kuma ya ce: Wani shu'umcin ne ya jefo mu
da kai, ya bawan banza! Idan har baka ambaci Allolinmu da alheri ba, to lallai
zan sanya ka, ka zama misalin azaba ga bayi. Sai Bilal –رضي الله عنه- ya masa raddi, alhalin yana tabbatacce
akan addinin musulunci, baya canza matsayi, ya ce: Ubanjina shine Allah, Shi
kaxai yak e, shi kaxai. Kuma da na san wata kalma, wacce zata fi baqanta muku
fiye da wanda na faxan, to da na faxe ta.
Yayin da abinda aka qaddara
na azabta Bilal y azo qarshensa, sai buxi y azo, sai Abubakar –رضي الله عنه- ya saye shi, ya kuma 'yanta shi domin neman
ganin fiskar Allah Mabuwayi da xaukaka, kuma akan haka ne, faxin Allah
Maxaukaki: "Kuma za a nisatar daga wuta, wanda yafi kamalar
taqawa * Wanda ya bada dukiyarsa yana neman tsarkaka * Kuma babu wani da ke da
wata ni'imar da take jiran sakayya, a wurinsa * sai dai neman ganin fiskar
Ubangijinsa Mafi xaukaka * Kuma da sannu zai yarda", [].
Sai kwanaki su shuxe, sai
Manzon Allah –صلى
الله عليه وسلم- yayi hijira zuwa garin Madina, Sai shima Bilal –رضي الله عنه-, kuma sai yi hijira, ya kuma wayi- a matsayin mai kiran
sallah, ga musulmai. Sai kuma ya fita tare da Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- zuwa yaqin Badar, su kuma mushirkai daga
vangaren Makkah, sai suka fiskanto, tare da jagororinsu, wanda a cjininmu har
abadaikinsu, akwai Umayyah bn Khalaf, da Abu-jahl, suna ta vangaren gaba cikin
tawagar, cikin qasaita da girman kai, da ruxuwa, runduwarsu kusan bataliya
guda; sojoji dubu, kuma a tare da su, akwai bayi mata, suna bugun gangar duffi,
kuma suna rera waqar zagin musulmai, suna cewa: Wallahi ba za mu koma Makka ba,
har sai mun je garin Badr, mu yi kwanaki uku, mu soke raqumi muci abinci, mu
sha giya, kuma mata su mana bushi, larabawa kuma su ji labarinmu, da tafowarmu
da haxuwarmu, sai kaga ba za su gushe ba, suna ganin kwar-jininmu har abada.
Shi kuma adadin musulmai
xari uku ne da sha wani abi, kuma a cikinu babu mai doki, in banda Almiqdad.
Sai yaqin ya kaure; Sai kuma Allah ya yi nufin baiwa ga muminai, akan waxannan
da aka raunatar da su a bayan qasa, kuma
ya sanya su zama jagorori, kuma ya sanya su zama magada.
Sai Bilal –رضي الله عنه- ya ga tsohon shugabansa; wato Umayyah bn
Khalaf, wanda ya xau dogon zango yana cutar da shi a garin Makkah, sai ya keto
tsakiyar sahu, yana magana yana cewa:
Ba zaka kuvuta, idan akwai
mai kuvuta. Sai Allah ya bashi damar kama shi, sai y agama da shi; sai
labarinsa ya zama kamar jiya da ya shuxe, Sai Abubakar As-Siddiq –رضي الله عنه- ya tsara waqoqi akan lamarin, inda ya ce:
Madalla, Allah Mai jin-qai
yam aka qarin buwaya
Lallai haqiqa ka riski
xaukar fansarka, Ya kai Bilalu
Amma shi kuma maqiyin
Allah; wato Abu-Jahlin, to haqiqa ya fiskanto, cikin girman kai da ruxuwa, yana
faxin waqe yana cewa:
Wace fansa yaqi zai xauka
daga gare ni,
Alhalin ina da gogewar
shekaru biyu, ga qananan shekaru
Domin irin haka ne, uwata
ta haife ni
Sai Allah ya xanxana wa
Abu-jahl qasqanci, a hannun samari biyu qanana, daga Madina, wanda sune 'ya'yan
Afra'u, sai ya riqa cewa, da dai ba manomi ba ne ya kasha ni, da haka nafi so,
kuma da yafi xaukaka sha'anina, kuma da bani da wata naqasa cikin haka.
Sai Abdullah ibn Mas'ud –رضي الله عنه- y azo, ya xora qafarsa, akan wuyan
Abu-jahl, yana cewa: Allah ya wulaqantaka, Ya kai maqiyin Allah. Sai Abu-jahl
gabanin ya mutu ya fara aibanta Abdullah ibn Mas'udin, inda yak e cewa: Haqiqa
ya kai qaramin mai kiyo awaki, ka hau wani mataki abin qi, mai wahala.
A lokacin da aka shigar da
musulunci Makkah (Fat-hu Makkah), sai Bilal –رضي الله عنه- ya hau Ka'abah, domin ya shelanta Kalmar tauhidi, 'yan taku
kaxan da inda ake masa azaba a cikinsa, kuma a lokacin azahar, sai gas hi yana
xaga sauti a cikin jama'a, da kalmomin kiran salla: ALLAHU AKBARUL LAHU AKBAR,
ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL LAHU, ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL LAHU, ASH-HADU ANNA
MUHAMMADAN RASULUL LAHI.
Sai wannan matsayar tasa ta
xago fushin maqiyansa, har wani daga cikinsu ya ce: Haqiqa Allah ya karrama
Mahaifina; tun da yam utu, bai ji wannan ba, balle ya fusata shi.
Wani kuma ya ce: Kaicona,
Da na mutu gabanin jin haka.
Ya ku, taron musulmai…!!
Bilal –رضي الله عنه- bai samu matsayi maxaukaki a cikin
musulunci ba, sai bayan an jarrabe shi da bala'oi, ya kuma yi haquri da nuna
qoqari, "Yak u waxanda suka yi Imani, ku yi haquri, kuma ku yi dauriya, kuma
ku yi tsayuwar dakon ribaxi, kuma ku yi taqawa, domin samun babban rabo", [Ali-imrana: 200].
Ina faxan abinda ku ke ji,
…
Allah ya yi mini albarka NI
da KU, cikin alqur'ani mai girma, kuma ya azurta mu da bin sunnar AnnabinSa mai
karamci, da kuma lazimtar shiriyarsa miqaqqa, ina faxin abinda ku ke ji wannan,
kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai, sai
ku nemi gafararSa, lallai shi Mai
gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah, Mai bayyanar da gaskiya, wanda
ke xaukaka shi, wanda ke qasqantar da varna, yake tunkuxe shi.
Ya turo ManzonSa da
shiriya, da kuma addinin gaskiya, domin ya xaukaka shi aka addinai gaba xaya,
koda kafirai sun qi.
Allah ka qara salati ga
annabi Muhammadu, da iyalansa, kamar yadda ka yi salati ga annabi Ibrahima, da
iyalan annabi Ibrahima, lallai kai abin godiya ne Mai girma..
Ya ku bayin Allah !! …
Lallai Allah yana yin
talala, amma baya kyaliya, kuma yana yin jinkiri ga azzalumi, har idan ya tashi
kama shi, ba zai kufce masa ba, "Kuma kada waxannan da suka kafirta su
yi zaton cewa jinkirin da muke musu alheri a gare su, lallai kawai muna musu
jinkiri ne, domin su qara laifi, kuma suna da azaba mai wulaqantarwa", [Ali-imrana: 178].
Don haka, abinda ya sauka
ga musulman da aka raunata su a garin Makkah, a farkon musulunci, na jarrabawa
da bala'i, lallai ya kasance ne saboda tanadar sabin tsareku, a kuma basu iko
da nasara mai yawa, kuma domin ta zama xauraya da tankaxe da rairaya, domin
Allah ya ware masu dauxa.
Don haka, ba a zauna ba,
sai na wani lokaci taqaitacce, sai Allah ya yi baiwa ga waxanda ake cin cin
zarafinsu ake zaluntarsu waxanda aka raunata su a bayan qasa, "Domin ya sanya su
shugabanni, kuma ya sanya su magada * kuma ya basu iko a bayan qasa" [Qasas: 5-6]. Sai ga
manyan jagororin shirka da kafirci da zalunci, ana yanka su da makaminsu, a
hannun tsofaffin 'yantattun bayinsu, kamar qissar Bilal da Umayya, da kuma
qissar Abdullah ibn Mas'ud da Abu-jahl, sai suka warkar da qishinsu, suka xauki
fansar cutarwarsu, "Kuma lallai Allah yana bada nasara ga wanda ya taimake
shi, lallai ne Allah Mai qarfi ne, Mabuwayi" [Hajj: 40].
Ya ku bayin Allah…!!
Lallai ma'aunan gwada
falala a wurin Allah, sune (Imani da) aiki, ba dangantaka, ko matsayi da dukiya
da girma ba, saboda mutane daidai suke, kamar haoqan matajin kai, dukkansu daga
annabi Adamu ne, shi kuma Adamu daga turvaya, kuma babu wata falala, ga wani
balarabe akan ba'ajame, sai da taqawa, "Ya ku mutane, lallai ne Mu mun
halitta ku, daga namiji da mace, kuma muka sanya ku dangogi da qabilu, domin ku
san juna, lallai mafificinku daraja a wurin Allah, shine wanda yafi ku taqawa" [Hujurat: 13].
Na rantse da Ubangijinka,
mutum ba komai ba ne, sai da addininsa
Don haka, kada ka bar aikin
taqawa, kana mai dogaro ga nasaba
Saboda muslunci ya xaukaka
Salmanul farisiy
Kamar yadda shirka ya
qasqantar da mutum mai girman nasaba; Abu-lahab
Kuma sau dayawa, voyayyen
mutum mai taqawa, wanda ba a wani damuwa da shi, ana rufe masa qofa, babu wani
shamaki tsakaninsa da tsakanin Allah, kuma da zai yi rantsuwa ga Allah (kan sai
ya aikata wani abu) to, da ya kuvutar da rantsuwarsa.
Kuma a lokacin da sahabi
Abu-zarri ya aibanta Bilal, y ace masa: Ya xan baqar mace, Sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya fusata, ya ce: "Ka aibanta shi da
Mahaifiyarsa? Lallai kai mutum ne wanda a tare da kai akwai xabi'ar jahiliyya".
Kuma haqiqa, Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya yi bushara wa Bilal da Aljannah, a
inda ya ce: "Ya kai Bilal! Ka bani labarin aikin da ka fi fatansa, daga ayyukan
da ka aikata, ga musulunci, saboda lallai na ji qarar takalmarka a gaba gare
ni, a cikin Aljannah".
Ya ku taron musulmai,,,
Lallai mushirkai sun ji
matuqar qunci, a lokacin da suka ji sautin sahabi Bilal yana tsage kiran
sallah, akan Ka'abah.
To, kuma idan kiran sallar Bilal
ya kasance yana cutar da mushirkai, to haqiqa ya kasance yana sosa qaiayin
zukatan musulmai, sai suyi begen sauraronsa, saboda Bilal ya kasance idan ya yi
kiran sallah bayan rasuwar Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- sai ya kasa mallakar kansa, sai ya tayar da vacin ran da ke
cikin zuciyarsa, ya kuma tsokano masa da kuka, har ya fita daga hankalinsa,
mutane kuma su tsorata, garin Madina ya cika da jururuwar tuna Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-.
Saboda a wani dare Bilal ya
kira sallah, a lokacin sahur, bayan rasuwar Annabi –صلى الله عليه وسلم- sai yah au rufin wannan masallacin, ya
ce: "Allahu akbar, Allahu akbar ", sai Madina ta girgiza, a yayin da ya ce:
"Ash-hadu an la ilaha illal lahu", sai ta qara girgiza. A yayin da ya
ce: "Ash-hadu anna Muhammadan Rasulul lahi", sai mutane suka
fito, daga gidajensu. Ba a ga mutane maza da mata a wani yini da suka fi yin
kuka fiye da wannan yinin.
Kuma a lokacin da Umar –رضي الله عنه- ya zo qasar Sham, ya kuma shigar da
musulunci Baitul qudus (fat-hu baitul maqdis), to sai ya umarci Bilal da cewar
ya yi kiran sallah, sai ya ce: Ya Amiral mu'uminina! Ban so, na sake kiran
sallah ga wani mutum ba, bayan rasuwar Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-, don haka; Zan maka biyayya tun da ka
umarce ni, a wannan sallar kawai ita xaya. A yayin da Bilal ya yi kiran salla,
sai sahabbai suka ji kiran sallarsa, sai suka yi kuka mai tsanani.
Saboda, Bilal ya tunatar da
su masoyinsu, kuma sanyin idanunsu, wanda ya sosa musu matattarar imanin da ke
cikin zukata, wanda kuma Manzon shine sababin tsiransu, sai rayuka suka yi
bege, zukata kuma suka yi haniniya, sai kuma ambatonsa ya tavo soyayyarsu, ya
cakuxa kwaryar zukata da fatarta.
Don haka, ba za zargi
sahabbai ba, akan haka, ta yaya kuma za a zarge su, alhalin kututturen dabino
ya yi haniniya kuma yayi kuka saboda rabuwa da Annabi. Dutsen Uhud ya girgiza
domin ya tarjama soyayyar da yake masa, da girmama shi.
Ya Allah, ka azurta mu da
soyayyarsa, ka tayar da mu a cikin tawagarsa, ka mana baiwar samun cetonsa.
Ya ku taron musulmai ,,,
Haquri shine mabuxin da key aye baqin ciki, kuma Aljannah
an kewaye ta da ababen qi, kuma an kewaye wuta da ababen sha'awa.
Kuma nasara tana kusa, kuma
lallai Allah zai taimaki addininSa, kamar yadda ya taimaki waxanda ake raunana
su a garin Makkah, kuma kamar yadda ya yi ta taimakon waliyyansa majivinta tun
gabanin haka, da bayan haka, "Kuma a wannan ranar muminai za su yi farin
ciki, da nasarar Allah, wanda ke taimakon wanda ke so, kuma shine Mabuwayi Mai
jin-qai * alkawarin Allah, kuma Allah baya sava alkawarinsa, sai dai mafi yawan
mutane basu sani ba",
[Rum: 4-6].
Ya Allah ka xaukaka
musulunci da musulmai….
"Lallai ne, Allah da
Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku
yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment