HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
صلى الله عليه وسلم
JUMA'A, 21/SAFAR/1439H
Daidai da 10/NOWAMBA/2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
WAJABCIN GODIYA GA MAI NI'IMA
(SUBHANAHU) AKAN NI'IMOMINSA
Shehin Malami wato: Aliyu xan Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya
yi hudubar juma'a mai taken: WAJABCIN GODE WA MAI NI'IMA سبحانه AKAN NI'IMARSA, Wanda kuma ya tattauna a
cikinta, akan ….
بسم
الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Dukkan yabo su qara tabbata
ga Allah Maxaukaki Mai girma, Masani Mai ikon qudura, Ina yabon Ubangijina,
kuma ina yin godiya a gare shi, akan ni'imominSa na zahiri da na voye, kuma ina
roqonSa dawwamar godiya akan ni'imominSa.
Ina shaidawa babu abin bautawa
da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokan tarayya, zuwa gare shi
makoma ta ke.
Ina kuma shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu; bawanSa ne kuma manzonSa, kuma masoyinSa
badaxi.
Ya Allah ka yi daxin salati
da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu Mai albishir da
gargaxi, kuma fitila mai haskakawa, da kuma iyalansa da sahabbansa waxanda suka
yi jihadi da dukiyoyinsu da kuma rayukansu, domin taimakon addinin Allah, har
duniya ta haskaka da shiriya da kuma
hasken (annabta da wahayi) .
Bayan haka:
Ku kiyaye dokokin Allah da
taqawa; domin ku isa ga yardarSa da aljannoninSa, sannan ku tsira daga fushinSa
da uqubobinSa.
Ya ku Bayin Allah!
Lallai Ubangijinku Mabuwayi
da xaukaka YANA
TUNATAR DA KU DA NI'IMOMINSA, waxanda suke da gamewa, da kevantattu, domin ku
yi godiya a gare shi, Allah (تعالى) yana cewa: "Ya ku Mutane, ku
tuna ni'imomin Allah a kanku, Shin akwai wani Mahalicci wanda ba Allah ba, da
yake azurta ku daga sama, da qasa. Babu abin bautawa da gaskiya sai shi, ta
yaya ake juya ku"
[Faxir: 3].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma ku tuna ni'imar
Allah akanku, da alkawarinSa wanda ya alkawarta da ku, a lokacin da kuka ce:
Mun ji, mun yi xa'a, kuma ku bi dokokin Allah, lallai Allah Masani ne ga abinda
ke cikin qiraza"
[Ma'ida: 7].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Shin ba ku gani ba
ne, cewa lallai Allah ya hore muku abinda ke cikin sammai, da kuma abinda ke
cikin qassai, kuma ya kwararo ni'imominSa akanku, a bayyane da kuma a voye" [Luqman: 20 ].
Kuma Allah Mabuwayi da xaukaka ya bamu labari cewa,
lallai ni'imomi gaba xayansu daga wajenSa suke, domin mu tsayu wajen sauke
haqqinSa (تبارك وتعالى) na bauta, da
godiya. Sannan mu bayyanar da kwaxayinmu zuwa gare shi na neman qarin ni'imomi,
Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma duk abinda ke
tattare da ku, na ni'imomi, to daga Allah ne" [Nahl: 53].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Abinda ya same ka
na kyakkyawa daga Allah ne, Wanda kuma ya same ka mummuna to daga ranka ya ke" [Nisa'i: 79]. Saboda
su kyawawan ababe, su kan samu mutum da falalar Allah, da rahamarSa, ta kowace
fiska. Munana kuma, su kan kasance ne da sababin mutum, Allah kuma shi yake
rubuta su, kuma ya qaddara su, Kuma Ubangiji Mabuwayi da xaukaka baya zaluntar
wani, ko daidai da kwayar zarra, Allah Ta'alah ya ce: "Saidai Allah shi ne
ma'abocin falala ga talikai" [Ali-imrana].
Mutane, kuma sun san dayawa
daga cikin ni'imomi, saidai sun jahilci mafi yawan ni'imomi; domin sau dayawa
akwai ni'imomin da Allah ya kwararo maka –ya kai wannan mutum- ya kuma jiyar da
kai daxi da su, amma kai baka ma ji su ba. Kuma nawa yawan, sharri da musibun
da Allah ya ke tunkuxe su daga barinka, alhalin kai baka sani ba, Allah (تعالى) yana cewa, a dangane da kiyaye Mutum:
"Yana da Mala'iku masu canjin aiki, a gaba gare shi, da bayansa suna
kiyaye mutum, da umarnin Allah" [Ra'ad: 11].
Kuma Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ya hore muku
abinda ke cikin sammai da abinda ke cikin qassai, gaba xayansu daga wurinSa,
lallai ne cikin haka akwai ayoyi ga mutanen da suke yin tunani" [Jasiya: 13].
Kuma dayawa daga gavvan jikin Mutum suna yin aikin da aka samar da su, don aikatawa, domin
amfanin jikin da tsayawar rayuwarsa, kuma suna yin aikinsu ba tare da mutum ya
yi nufi, ko yayi wani abu a cikin hakan ba, Allah (تعالى) ya ce: "Da kuma cikin rayukanku,
Shin ba za ku gani ba"
[Zariyaat: 21].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma idan za ku
qidaya ni'imomin Allah ba za ku qididdige su ba, Lallai mutum mai yawan zalunci
ne mai yawan butulci"
[Ibrahim: 34]. Wanda ba zai iya qididdige ni'imomi ba, to lallai ya jahilci
mafi yawansu.
Kuma Allah (تعالى) ya yi baiwa da ni'imomi domin a sanya su cikin xa'a wa Allah,
da yin bauta a gare shi, da qoqarin raya qasa da kawo gyara a cikinta, Allah (تعالى) ya ce: "Kamar haka, ya ke
cike ni'imominSa akanku, tsammaninku za ku miqa wuya" [Nahl: 81].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Allah shine ya
fitar da ku daga cikin uwayenku; alhalin ba ku san komai ba, sai ya sanya muku
ji da gani da hankula, tsammaninku za ku yi godiya" [Nahl: 78].
SHI
KUMA GODIYA KAN NI'IMOMI YA KAN KASANCE NE DA HAXUWAR WASU LAMURA;
Da son wanda ya yi
ni'imomin Mabuwayi da xaukaka, saboda waxannan ni'imomin da ya bayar.
Da kuma qanqan da kai ga
Allah (سبحانه), akan abinda ya
kwararo na ni'imomi,
Tare da samun yaqini a
cikin zuciya cewa dukkan wata ni'ima da Allah ya yi falala da ita, ko ya
kyautata ga bawa da ita, ta kowace fiska shi bawan bashi da cancantarta ga
Allah,
Da yin yabo ga Ubangiji, da
harshe, akan waxannan ni'imomin,
Da karvar waxannan
ni'imomin, da nuna halin buqata da talauci zuwa ga Allah
Da girmama ni'imar,
Da kuma amfani da ni'imomin
cikin abinda Allah (تبارك
وتعالى)
yake so; saboda duk wanda yayi amfani da ni'imomin Allah cikin abinda Allah
yake so, kuma ya yarda, sannan ya sanya ni'imomin suka zama taimako a gar shi wajen
tsayar da addini, a karan kansa, kuma ya bayar da wajibai na farillar da suke
kansa, ta hanyar kyautata wa halittu, da waxannan ni'imomin = to, wanda ya
aikata haka, ya yi godiya wa Allah akan ni'imomi.
Wanda kuma yayi amfani da
ni'imomin Allah cikin abinda Allah yake qi, ko ya yi hani, ko kuma ya qi bada haqqoqi na wajibai da suke kansa, a
cikin ni'imomin, to lallai ya butulce wa ni'imar.
Sannan kada ni'imomin su
sanya bawa girman kai, sai ruxu da ruxi su shige shi, Shexan kuma yayi masa
waswasin cewa: Wai yafi waninsa, saboda waxannan ni'imomin, kuma wai ba a
kevance shi da waxannan ni'imomin ba, sai saboda fifikon da yake da shi akan
wanda ba shi ba.
Kuma mutum ya sani cewa, lallai Allah yana jarrabar
mutane da abubuwan alkhairi, ko sharri, domin ya san Masu godiya da haquri.
Kuma shi imani rabinsa
godiya ne, rabinsa kuma haquri, Allah (تعالى) ya ce: "Shin baka ga cewa lallai jirgin ruwa yana
gudana a cikin teku da ni'imar Allah, domin ya nuna muku, ayoyinSa ba, lallai
cikin haka akwai abin lura ga kowani mai yawan haquri, da yawan godiya" [Luqman: 31].
A'isha (رضي الله عنه) ta rubuta wa Mu'awuya (رضي الله عنه), inda ta ce: "Lallai mafi
qarancin abinda ke wajaba na haqqin mai ni'ima, akan wanda yayi masa ni'imar
shine kada ya sanya ni'imar da yayi masa ta zama hanyar sava masa".
Kuma bayan matakin GODIYA GA NI'IMOMI akwai matakin YIN GODIYA (wa
Allah) KAN MUSIBU DA SHARRACE-SHARRACE, da yin YABO WA ALLAH AKAN ABABEN QI
waxanda suke samun musulmi, waxanda kuma bashi da ikon tunkuxe su.
Ma'abuta wannan matsayin
sune farkon waxanda za a kira su domin shiga Aljanna, saboda kasancewar suna
godiya (wa Allah) a cikin kowani yanayi.
Kuma haqiqa Allah Ubangijinmu Mabuwayi da xaukkka ya umarce
mu da yin godiya a gare shi, a inda ya ce: "Ku ambace ni sai in
ambace ku, kuma ku yi godiya a gare ni, kada ku yi min butulci" [Baqara: 152].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Saidai yana son ya
tsarkake ku, kuma ya cika ni'imarSa akanku tsammaninku za ku yi godiya" [Ma'ida: 6].
Kuma Allah ya ce: "Sai ku yi godiya ga
ni'imar Allah, idan kun kasance a shi kaxai kuke yin bauta" [Nahl: 114].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ku so Allah
saboda abinda yake ciyar da ku da shi na ni'imominSa", Attirmiziy ya
ruwaito shi, kuma ya inganta shi, daga hadisin Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما).
Mafi girman godiya shine IMANI DA UBANGIJIN
TALIKAI,
Kuma shine godewa ni'imar turo manzancin annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) wanda Allah ya turo shi da wannan manzancin,
domin ya zama jin qai ga mutane.
Bayan haka kuma, Sai gode wa (Allah) akan kowace ni'ima,
a keve, har kuma mafi qarancin ni'ima, tare da cewa babu qarami a cikin
ni'imomin Allah.
Kuma mafi girma daga cikin BUTULCE WA NI'IMOMI
shine: KAFIRCE WA QUR'ANI DA SUNNA, Kuma godiya ga wata ni'ima ba zai yi amfani ga
mutum ba, matuqar ya kafirce wa Musulunci, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma duk wanda ya
kafirce wa Imani, to lallai aikinsa ya ruguje, kuma shi a lahira yana daga
cikin masu hasara"
[Ma'ida: 5].
Kuma lallai haqiqa Allah ya yi alqawari ga masu yin
godiya, da cewar zai dawwamar musu da ni'imominsa, kuma zai musu qari, kuma ya
sanya musu albarka, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma Ubangijinku ya
yi shela cewa, idan kuka gode, to lallai zan yi qari a gare ku, kuma idan kuka
butulce lallai azabata mai tsanani ce" [Ibrahim: 7].
Masu yin godiya sune masu rabauta, da alkhairin duniya da
lahira, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma Allah zai yi
sakayya wa masu godiya" [Ali-imrana: 144].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Wanda ya nufi samun
ladan duniya za mu bashi daga gare ta, Wanda kuma ya nufi samun ladan lahira za
mu bashi daga gare ta, kuma za mu yi sakayya ga masu godiya" [Ali-imran: 145].
Kuma masu godiya sune masu tsira daga uqubobin duniya da
sharrace-sharracenta, da kuma baqin cikin lahira, Allah (تعالى) ya ce, dangane da Mutanen annabi Lux (عليه الصلام): "Lallai ne mu mun tura musu iska mai
tsanani mai turvaya, in banda iyalan annabi Lux, waxanda muka tseratar da su, a
lokacin sahur * Ni'ima ce daga wurinmu, kamar haka make yin sakayya ga wanda ya
yi godiya"
[Qamar: 34-35].
Shi godiya matsayi ne na annabawa da manzanni, da kuma
bayin Allah muminai, Allah (تعالى) yana cewa dangane
da annabi Nuh (عليه
الصلاة والسلام): "Lallai ne shi ya kasance bawa mai yawan godiya" [Isra'i: 3].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Lallai ne annabi
Ibrahima ya kasance jagora, mai biyayya ga Allah, miqaqqe daga karkata, kuma be
kasance daga cikin mushirkai ba * Mai godiya ne ga ni'imominSa, ya zave shi, kuma
ya shiryar da shi zuwa ga hanya madaidaiciya" [Nahl: 120-121].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ya Musa lallai ne
ni na zave ka akan mutane, da sakwannina, da kuma maganata, sai ka riqi abinda
na baka, kuma ka kasance daga cikin masu godiya" [A'araf: 144].
An ruwaito daga A'isha (رضي الله عنها) ta ce: "Annabi ya
kasance yana yin tsayuwar dare (salla), har qafofinsa su kukkumbura, Sai ta ce:
Ya Ma'aikin Allah: Kana yin sallar qiyamulLaili har qafofinka suna kumbura? alhalin
Allah ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubanka, da abinda ya jinkirta,
Sai ya ce: Shin ba zan kasance bawa mai yawan godiya ba", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi.
Kuma masu godiya sune ma'abuta samun ni'imomin Allah,
saboda Allah ya kan kevance su da abinda baya bayar da shi ga waninsu, Allah (تعالى) yana cewa: "Kamar haka, muka
jarrabi sashensu da sashe, domin su ce: Shin waxannan ne, Allah yayi musu baiwa
daga cikinmu? Shin ba Allah ne mafi sanin masu godiya ba?" [An'am: 53].
Kuma masu godiya sune kevantattun Allah, daga bayinSa,
wannan ya sanya suka zamo 'yan kaxan, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma 'yan kaxan ne daga cikin bayina su ke
yawaita godiya"
[Saba'i: 13].
Ya kai Mai godiya, ka dawwama akan ibadar godiya, da
tsayuwa akan addini, domin duk wanda ya cika alkawari wa Allah to Allah zai
cika masa, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ku cika
alqawarina zan cika alqawarinku, kuma nine kaxai za ku ji tsoro" [Baqara: 40].
Kuma kada ka bari Shexan ya zamar da qafarka, ya kai Mai
godiya! Sai ka kasa kaiwa ga godiya ta wajibi, ko ka canza godiyar zuwa ga
kafircewa ni'ima, Sai halaye su caccanza maka; wato daga hali mai kyau zuwa ga
mummuna mai sharri, Allah (تعالى) ya ce: "Ka tambayi
banu-isra'ila, sau dayawa mun basu aya bayyananniya, kuma duk wanda ya canza ni'imar
Allah bayan ta zo masa, to lallai Allah Mai tsananin uquba ne" [Baqara: 211]. Wato,
duk wanda bai yi godiya ga ni'imomi ba, sai Allah ya yi masa uqubar horarwa.
Wanda kuma ya kasance a halin dawwamar da godiya, sai Allah ya yi masa qari.
Wanda kuma ya juya daga
aikata savo, zuwa ga abinda ke yardar da Allah, to sai Allah ya juyar masa da
ababen da yake qinsu ko suke munana masa,
zuwa ga ababen da bawa yake so.
Wanda kuma ya dace da Allah
cikin ayyukan kusantarSa (na xa'a), da nisantar savo, to sai Allah ya jivinci
lamuransa gaba xayansu, An ruwaito daga Anas (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى
الله عليه وسلم), daga Jibrilu, daga UbangijinSa Mabuwayi da xaukaka, Ya
ce: "Wanda ya
walaqanta mini waliyyi, to lallai ne yayi fito-na-fito da ni, na yaqi. Kuma ban
yi taraddadin aikata wani aikin da nine mai aikata shi ba, kamar taraddadina
wajen karvar rayin bawana mumini da ke qin mutuwa, ni kuma nake qin munanta
masa, tare da cewa bashi da makawa daga mutuwa. Kuma lallai akwai daga bayina
muminai, wanda ke nufan wata qofa ta bauta, amma sai in toshe masa ita, saboda
kar jiji-da-kai ko ruxuwa ya shige shi, sai hakan ya lalata shi. Kuma bawana
bai kusance ni da wata ibada ba, fiye da aikata abinda na farlanta akansa, kuma
bawana ba zai gushe yana yin nafila ba, face na so shi, Duk kuma wanda na so
shi, to sai in zama jinsa da ganinsa da hannunsa, kuma mai qarfafa a gare shi,
ta yadda idan ya roqe ni sai in amsa masa, idan kuma ya tambaye ni, sai in
bashi, idan kuma ya nemi nasihata sai nayi masa nasiha.
Kuma akwai daga
cikin bayina waxanda ba abinda zai gyara imaninsu sai wadaci, kuma da zan mayar
da shi faqiri da hakan ya lalata shi.
Kuma akwai daga
cikin bayina wanda babu abinda zai gyara imaninsa idan ba talauci ba, da kuma
zan yalwata masa sai hakan ya lalata shi.
Akwai daga
bayina wanda babu abinda zai gyara imaninsa sai cutuka, da kuma zan bashi
lafiya to da hakan ya lalata shi.
Kuma akwai daga
bayina wanda babu abinda zai gyara imaninsa sai lafiya, da kuma zan hukunta
masa cuta, to da hakan ya lalata shi.
Lallai ne ni
ina jujjuya lamarin bayina da sanina ga abinda ke cikin zukatansu, lallai ne ni
Masani ne Mai bada labari", Axxabaraniy ya ruwaito shi. Kuma sashen laffuzan hadisin
suna da abinda ke musu qarfafarsu daga cikin hadisan Sahihul Bukhariy.
Sai ka kasance, Ya kai bawan Allah, tare da masu godiya
wa Allah, waxanda Allahn ke kwarara musu alkhairi kwararawa.
Ibnul Qayyim (رحمه الله) ya ambaci wata magana da ake danganta ta ga Allah, cewa Allah
ya ce: "Ma'abuta ambatona sune ma'abuta
zama da ni. Su kuma ma'abuta gode mini sune ma'abuta samun qarina, Su kuma
ma'abuta xa'a a gare ni sune ma'abuta samun karramawata, Su kuma ma'abuta sava
mini su kuma ba zan sanya su xebe tsammani daga rahamata ba; idan suka tuba; to
nine masoyinsu, idan kuma basu tuba ba to nine likitansu; zan jarrabe su da
musibobi domin in tsarkake su daga aibobi ".
Kuma lallai ne Allah ya umarce ka, da kasancewa tare da
waxannan bayin masu rabauta, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma ga Allah shi kaxai za ka yi bauta,
kuma ka kasance daga masu godiya" [Zumar: 66].
Kuma haqiqa Allah (تعالى) ya ambaci wasu ni'imomi kevantattu a cikin littafinSa saboda
amfaninsu da tarin albarkarsu, ga al'umma, har zuwa tashin qiyama.
Kuma yana daga cikin wasiyyoyin Annabinmu (صلى الله عليه وسلم) masu amfani, faxinSa: "Ya kai
Mu'azu! Lallai ne ni ina sonka, sai ka riqa faxa bayan kowace sallah:
(اللهم أعني على ذكرك، وشكرك، وحسن عبادتك)
Ma'ana: Ya
Allah! Ka taimake ni akan ambatonka, da yin godiya a gare ka, da kyautata bauta
a gare ka",
Abu-Dawud ya ruwaito shi da Annasa'iy.
Kuma wannan wasiyar ta dace,
da xaukacin al'ummah.
Kalmar Alhamdu, da Shukru, ma'anar sashensu yana
shigar wa sashe, tare da cewa kowannensu ya kevanta da wasu ma'anoni masu
zurfi.
Kuma lallai Allah Ta'alah –a kowane lokaci- yana da
ni'imomi kevantattu, da ni'imomi gamammu (ga xaukacin musulmai). Waxanda suke
wajabta musu yin godiya, da tsayuwa akan addini.
Kamar yadda Ubangiji Mabuwayi da xaukaka, yake da wasu
manyan ni'imomin ga wannan qasa (masarautar larabawa ta Saudia), wanda Ubangiji
ya yi mana baiwa da su.
Kuma yana daga manyan
ni'imomi da baiwawwaki: HAXUWAR KAN MUTANE, Saboda haxin kai, tsirkiya ne wanda haxe maslahohin
addini dana duniya a qarqashinsa, sai a iya raya garurruka, kuma da ita ne sharrin
ma'abuta sharri ke tunkuxa, addini ya qarfafa da shi, kuma maqiya su takuru, sai
kalma ta xaukaka, al'umma ta qara samun girma, a iya umarni da kyakkyawa, ayi
hani da mummuna, a riqe hannun azzalumi, a kiyaye ababe masu alfarma, a hana
zubar da jini ko lalata kayayyakin da aka mallaka, kuma iyakoki su samu buwaya
da tsaro, lamura kuma su gyaru.
Kuma idan aka rasa haxin
kai, varna ce mai tarin yawa take shigowa al'umma, ta vangaren addini, da kuma ta
vangaren duniya, wanda xaixaikun mutane ko al'ummar ba za su iya gyara su ba.
Tsarki ya tabbata, ga Mai
hikima, Masani, wanda ke cewa: "Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gaba xaya,
kuma kada ku rarraba, kuma ku tuna ni'imar Allah akanku, a lokacin da kuka
kasance maqiyan juna, sai ya daidata tsakanin zukatanku, sai kuka wayi gari da
ni'imarSa; 'yan'uwa, kuma kun kasance a bakin gavar ramin wuta, sai ya tsamar
da ku daga gare ta, kamar haka, Allah ke bayyana muku ayoyinSa, tsammaninku za
ku shiryu"
[Ali-imrana: 103].
Kuma yana daga cikin baiwawwakin
Allah da ni'imarSa ga wannan qasa: YADDA SHARI'AR ALLAH TA MAMAYE WANNAN QASA, Saboda kotunan shari'a a
masarautar larabawa ta Saudiyyah, kundin da suke xaukar hukunce-hukuncensu (konsutushin)
shine littafin Allah Ta'alah, da kuma sunnar ManzonSa –صلى الله عليه وسلم-.
Kuma shari'ar musulunci itace
adalci, kuma shari'a matsaikaciya, wanda take tsayar da adalci a tsakanin
mutane, kuma take kiyaye haqqoqin mutum, gaba xayansu ba tare da ta tauye wani abu
ba; Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce: Lallai ni Ubangijina ya shiryar da
ni zuwa tafarki madaidaici; addini miqaqqe, mai aqidar Ibrahima, mai karkata
zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga cikin mushirkai ba" [An'am: 161].
Kuma al'ummar musulmai
addininta, tsakaitawa ne a tsakanin al'ummai; babu wuce iyaka, kuma babu
sakaci, kuma babu tozarta wajibai ko qarfin halin aikata ababen haramun, Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma haka ne, mu ka sanya ku al'umma matsakaiciya, domin ku kasance
masu bayar da shada akan mutane, kuma Manzo ya kasance mai shaida akanku" [Baqara: 143].
Kuma abinda ke aukuwa na
sakaci daga musulmi, cikin haqqin Allah Ta'alah, ko cikin haqqoqin 'yan'uwansa halittu,
to ba shari'ar musulunci ta gaskiya ne sababin wannan ba, sababin hakan kawai
shine daga kayukan musulmai, sakamakon jahilci, ko rinjayen son zuciya, Kuma
dukkan wanda ya tuba, Allah zai karvi tubanSa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Dukkan 'yan
Adam masu kuskure ne, kuma mafi alherin masu kuskure sune masu yawaita tuba", kuma saboda shari'ar
daga Allah ta ke.
Kuma yana daga cikin
baiwawwakin Allah da ni'imarSa ga wannan qasa: TABBATUWAR AMINCI DA ZAMAN
LAFIYA; Wanda
lamuran musulunci suke daidaituwa da samuwar tsaro, kuma maslahohin rayuwa suke
rataya akansa, kuma arziqi suke sauqaqa a inuwarsa, hanyoyi kuma su zama da
aminci, kuma qasashen duniya su riqa canjin ababen amfani da maslahohi a
tsakaninsu, rayuwa kuma ta bunqasa a dukkan vangarorinta, kuma da samuwar tsaro
ake iya kare zubar da jini, da tava mutuncin mutane da dukiyoyinsu, kuma suma burace-buracen
mutane da kasuwanci su kan shunfuxu ne a lokacin aminci.
Zaman lafiyar wannan qasa;
ta masarautar Saudiya, amfaninsa na qasar ne, da sauran musulmai gaba xaya,
saboda matsayin harami biyu maxaukaka, da kuma 'yan'uwantaka ta musulunci, domin
wannan qasar tana da haqqi akan kowane musulmi, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma lallai muminai 'yan'uwan juna ne" [Hujurat: 10].
Kuma yana daga ni'imomin Allah Mabuwayi da xaukaka ga
wannan qasa mai albarka: TSARE-TSARE NA ALKHAIRI MASU AMFANI, WANDA SASHENSU KE ZUWA BAYAN
SASHE, WAJEN HIDIMA GA 'YAN QASA, DA XAUKACIN MUSULMAI, Na farko-farkonsu shine aikin raya harami biyu maxaukaka, da samar
da sabbuba da ayyukan kawo walwala ga mahajjata da masu ziyara da masu umrah,
wanda suke wajabta mana yin godiya, don haka YABO YA QARA TABBATA GA
UBANGIJINMU, DA GODIYA A GARE SHI, a kan ni'imominSa.
Kuma lallai godiya, amfanoninsa, yana komawa ne ga Mai
yin godiyar, kamar yadda sakaci kan godiyar cutarwansa yana komawa ne ga
gafalalle, saboda Allah yana cewa: "Kuma wanda ya gode, to lallai yana
yin godiyar ne domin kansa, wanda kuma ya butulce, to lallai Allah Mawadaci ne,
Godadde"
[Luqman: 12].
Allah yayi albarka wa Ni da
Ku cikin alqur'ani mai girma! Kuma ya amfanar da Ni da Ku da abinda ke cikinsa
na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, kuma ya amfanar da mu da shiriyar shugaban
Manzanni, da maganganunsa miqaqqu.
Ina faxar Magana ta wannan,
kuma ina neman gafarar Allah, wa Ni da Ku, da sauran Musulmai; sai kuma ku nemi
gafararSa; saboda shi Mai yawan gafara ne, Mai jin qai.
HUXUBA
TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya datar da wanda ya so
zuwa ga alkhairori, kuma ya tavar da wanda ya so da adalcinSa da hikimarSa, sai
ya bi sha'awowi, Ina yabon Ubangijina kuma ina yin godiya a gare shi, ina tuba
zuwa gare shi, ina kuma neman gafararSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa
da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, Ubangijin qasa da sammai.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, matattarar girma
da karamomi.
Ya Allah kayi qarin salati da sallama da albarka ga
bawanka kuma manzonka Muhammadu, da
iyalansa da sahabbansa ma'abuta yin xa'a.
Bayan haka!
Ku kiyaye dokokin Allah ta hanyar tsayuwa wajen gode
masa, kuma ku ambace shi yadda ya dace a ambace shi.
Ya ku Bayin Allah!
Allah (تعالى) yana cewa: "Idan kuka kafirce
to lallai Allah Mawadaci ne ga barinku, baya yarda da kafirci wa bayinsa. Idan
kuma kuka yi godiya yana yarje muku, kuma rai bata xaukar zunubin wata rai,
Sa'annan izuwa ga Ubangijinku makomarku ta ke, sai ya baku labarin abinda kuka
kasance kuke aikatawa, lallai shi Masani ne da abinda ke cikin qiraza" [Zumar: 7].
Kuma ku sani, Lallai bawa duk yadda ya kai ga biyayya wa
UbangijinSa, ya ke kuma kusantarSa da dangogin ibadodi, to ba zai tava iya
tsayuwa da godiyar Ubangijinsa, a cikakkiyar fiska ba, Saidai kuma yana isar wa
bawa ya tsayu wajen aikata farillai, ya kuma hanu daga laifukan da aka hana,
sannan ya sani cewa ba domin rahamar Allah ba da ya kasance cikin masu hasara,
Sai kuma ya lazimci neman gafara akan gajartawarsa, tare da yawaita roqon
Ubangijinsa cewa ya taimake shi ya datar da shi, kuma ya yawaita ambaton Allah Ta'alah;
saboda zikirin Allah ana rigayen samu maxaukakan matsayi da shi; An ruwaito hadisi
daga Ibnu-Abbas (رضي
الله عنهما) lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana addu'a, cewa: "Ya Ubangijina!
Ka sanya ni na zama mai yawan godiya a gare ka, mai yawan ambatonka, mai yawan
jin tsoronka, mai yawan yi maka biyayya, mai yawan qanqan da kai a gare ka, mai
yin kuka da mayar da al'amari zuwa gare ka.
Ya Ubangijina! Ka karvi tubata, kuma ka
wanke zunubaina, ka amsa addu'a ta, ka tabbatar da hujjojina, kuma ka shiryar
da zuciyata, ka daidaita harshena, ka zare dauxar zuciyata", Abu-dawud ya
ruwaito shi da Attirmiziy, kuma ya ce: hadisi ne mai kyau ingantacce (hasan
sahih).
Ya ku Bayin Allah!
"Lallai Allah
da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, ya ku waxanda su ka yi imani
ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Duk wanda ya
yi salati guda xaya a gare ni, to Allah zai salati a gare shi guda goma saboda
shi".
Sai ku yi salati, da sallama ga shugaban na farko da na
qarshe, kuma jagoran manzanni.
Ya Allah! Ka yi salati wa annabi
Muhammadu…
Ya ku bayin Allah!
"Lallai ne, Allah yana yin
umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani kan
alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku wa'aztu" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai
riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah
shine mafi girma, Lallai kuma Allah ya san abinda kuke aikatawa.
No comments:
Post a Comment