HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم )
JUMA'A, 06/RABIYUL
AWWAL/1439h
DAIDAI
DA 24/11/2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo ya
tabbata ga Allah Mai rahama Mai jin kai; Mai ilimi Mai hikima, Ma'abucin falala
mai girma, Ina yin yabo ga Ubangina
kuma ina yin godiya a gare shi, Ina tuba zuwa gare shi ina neman gafararSa,
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da
abokin tarayya, Ma'abucin al'arshi mai karamci,
Kuma ina
shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu annabi Muhammadu bawanSa ne manzonsa
ne; Ma'abucin halayya masu girma,
Ya Allah
ka yi karin salati da sallama ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu, da
iyalansa da sahabbansa, masu kira zuwa ga Allah, da shiryatarwa zuwa ga hanya
madaidaiciya.
Bayan
haka:
Ku kiyaye
dokokin Allah ta hanyar yin aiki da abubuwan da suke yardar da shi, da kuma
kaurace wa ababen da ya haramta; domin
ku rabautu da samun yardarSa da kuma ni'imomin aljannoninSa, sannan ku samu tsira daga fushinSa da kuma ukobobinSa,
Ya ku
musulmai…
Lallai
Ubangijinmu mabuwayi da daukaka ya yawaita kofofin alkhairi, da kuma hanyoyin
ayyuka kyawawa, Falala da rahama da kuma kyauta daga ma'abucin buwaya da daukaka;
domin musulmi ya shiga kowace kofa ta alkhairori, ya kuma bi kowace hanya daga cikin hanyoyin
biyayya; sai Allah ya gyara
duniyarSa, ya kuma daukaka shi zuwa ga
darajoji a lahirarSa; Sai Allah (سبحانه) ya
karrama shi ta hanyar bashi rayuwa daddada, da kuma rabauta a cikin rayuwarsa,
daga karshe sai ya samu ni'ima tabbatacciya, da kuma yardar Ubangiji, bayan
mutuwarsa. Allah (تعالى) yana cewa: "Sai ku yi tsere zuwa
ga ayyukan alkhairi. Kuma duk inda kuka kasance Allah zai zo da ku gaba daya,
Lallai Allah akan komai Mai iko ne" [Bakarah: 148].
Kuma Allah (سبحانه)
yana cewa a dangane da annabawansa; wadanda kuma sune abin koyi ga mutane
(Allah yayi dadin salati da sallama a gare su gaba daya): "Lallai ne sun
kasance suna yin tsere cikin ayyukan alkhairi, Kuma suna yin bauta a gare mu
akan kwadayi da fargaba, kuma sun kasance a gare mu masu tsoro ne"
[Anbiya'i: 90].
Kuma Annabi (صلى الله
عليه وسلم) ya ce wa sahabinsa Mu'azu (رضي الله عنه): "Shin ba zan shiryar da kai zuwa
ga kofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, sadaka kuma tana shafe kurakurai kamar
yadda ruwa ke kashe wuta. haka sallar mutum a cikin dare. Sannan sai
ya karanta fadin Allah: (Gefen jikinsu yana nisantar wuraren
kwanciya, suna rokon Ubangijinsu cikin fargabar tsoro da kwadayi, kuma daga
cikin abinda muka azurta su suna ciyarwa. Kuma rai bata san abinda aka boye
mata na sanyin ido ba, sakamakon abinda suka kasance suke aikatawa).
Sa'annan yace: Ba zan ba ka
labari dangane da, kan wannan lamari ba, da ginshikinsa, da kololuwar tozonsa?
Sai na ce: Eh, ka bani labara, ya Manzon
Allah!
Sai ya ce: Kan wannan lamari shine:
Musulunci. Ginshikinsa kuwa sallah. Kololuwar tozonsa shine: Jihadi fiysabillah”. Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya inganta shi.
KUMA
YANA DAGA CIKIN KOFOFIN ALKHAIRORI, DA HANYOYIN KYAWAWAN AYYUKA DA DA'OI, KUMA
YANA DAGA CIKIN SABBUBAN SHAFE MUNANAN AYYUKA: NEMAN GAFARA; Saboda
neman gafara sunnar Annabawa da Manzanni ne (عليهم
الصلاة والسلام), Allah (تعالى)
yana cewa dangane da iyayen 'yan-adam; guda biyu (Adam da Hauwa'u) Allah ya yi
salati mai yawa da rahama da karin albarka a gare su: "Suka ce: Ya
Ubangijinmu lallai mun zalunci kayukanmu, Idan baka gafarta mana, ka yi rahama
a gare mu ba, zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf:
23].
Kuma Allah yana cewa dangane da annabi Nuhu (عليه السلام): "Ya Ubangijina ka gafarta mini, da
iyayena biyu, da wanda ya shiga gidana yana mumini, da kuma muminai maza da
muminai mata" [Nuh: 28].
Kuma Allah mabuwayi da daukaka yana fada dangane
da Ibrahimul khalil (عليه السلام): "Ya Ubangijinmu, ka
gafarta mini, da iyayena biyu, da kuma muminai, a ranar da hisabi ke tsayawa"
[Ibrahim: 41].
Kuma Allah yana cewa dangane da annabi Musa (عليه السلام): "Ya Ubangijina, ka yi gafara a gare
ni, ni da dan'uwana, kuma ka shigar da mu cikin rahamarka; lallai kai ne mafi jin-kan
masu rahama" [A'araf: 151].
Kuma Allah (تعالى)
yana cewa: "Sai annabi Dawud ya tabbata cewa: lallai jarrabarsa muka yi, sai ya
nemi gafarar Ubangijinsa, ya kuma fadi yana mai sujjada, ya kuma mayar da
al'amari ga Allah" [Sad: 24].
Kuma Allah (تعالى), a
inda yake umartar annabinSa (صلى الله عليه وسلم) yana
cewa: "Kuma ka sani, Lallai babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, kuma ka
nemi gafarar zunubanka, da kuma ga muminai maza, da mata"
[Muhammadu: 19].
KUMA
YANA DAGA SHIRIYAR MANZONMU: YAWAITA NEMAN GAFARA, tare da cewa Allah Ta'alah
ya gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa, da abinda ya jinkirta; Ya zo
daga Dan Umar (رضي الله عنهما)
yace: "Mun kasance muna qidaya wa Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) a majalisa daya, sau dari: RABBI IGFIR
LIY WA TUB ALAYYA; INNAKA ANTAT TAWWABUR RAHIM.
Ma'ana: Ya Ubangijina, ka gafarta
mini, ka karbi tubata, lallai kai mai yawan karbar tuba ne, Mai jin-kai".
Abu dawud ya ruwaito shi, da Tirmiziy, kuma ya ce: Hadisi ne mai kyau
ingantacce.
Kuma an ruwaito daga A'ishah (رضي الله عنها) lallai ta ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance gabanin mutuwarsa yana yawaita
fadin: سبحان الله وبحمده، أستغفر الله وأتوب إليه
Ma'ana: Tsarki ya tabbata ga
Allah, tare da gode masa, Ina neman gafarar Allah, ina kuma tuba zuwa gare shi.
Bukhariy
da Muslim suka ruwaito shi.
An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) ya ce: "Ban ga mutumin
da yafi Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yawaita fadin ASTAG FIRUL LAHA WA ATUBU ILAIHI".
Ma'ana: Ina neman gafarar Allah, kuma ina tuba
zuwa gare shi. Annasa'iy ya ruwaito shi.
Kuma Annabi (صلى الله عليه
وسلم) ya kasance bayan yin sallamar fita daga sallah yana cewa: Astagfirul
laha, har sau uku. Muslim ya ruwaito shi, daga hadisin Sauban (رضي الله عنه). Sai kuma daga bisani, ya fadi zikirorin
da aka shar'anta fadinsu a bayan sallolin farilla.
Kuma lallai NEMAN GAFARA Dabi'ar salihan
mutane ne, kuma aiki ne na masu biyayya da takawa, kuma alama ce ta muminan
mutane, Allah (تعالى) yana cewa: "Ya Ubangijinmu ka
gafarta mana zunubanmu, kuma ka kankare mana munanan aiyukanmu, kuma ka dauki
rayukanmu tare da masu biyayya" [Ali-imrana: 193].
Kuma Allah (تعالى)
yana cewa: "Wadanda suke cewa: Ya Ubangijinmu lallai ne, mun yi imani; sai ka
gafarta mana zunubanmu, kuma ka katange mu daga azabar wuta *
Masu hakuri, da masu gaskiya, da masu kankan da kai, da masu ciyarwa, da
masu yin istigfari a lokutan asuba" [Ali-imrana: 16-17].
Kuma Allah (تعالى)
yana cewa: "Kuma sune wadanda, idan suka aikata wata alfasha ko suka zalunci
kayukansu sukan tuna Allah; sai su nemi gafarar zunubansu, Kuma wanene ke
gafarta zunubai idan ba Allah ba, kuma basa dogewa akan abinda suke aikatawa,
alhalin suna sane" [Ali-imrana: 135].
Ibnu-rajab yace: ((Shi neman gafara daga
zunubai shine: neman lullube su, kuma lallai bawa yana da matukar bukatar hakan;
saboda ko-yaushe ya kan yi kuskure cikin dare da rana. Kuma lallai ambaton TUBA
DA NEMAN GAFARA ya maimaitu a cikin alkur'ani, kuma an yi umarni da su, an kwadaitar
akansu)). … Maganarsa ta qare.
Kuma
lallai NEMAN GAFARA DAGA Ubangiji mabuwayi da daukaka, Allah yayi alkawarin
cewa zai amsa, kuma zai yi gafarar.
Kuma
lallai an shar'anta bawa ya nemi gafara akan zunubi ayyananne, sananne; saboda
fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم): "Lallai
bawana ya aikata wani zunubi, Sannan ya ce: Ya Ubangijina, lallai ni na aikata
wani zunubi; sai ka gafarta mini, Sai Allah ya ce: Bawana lallai ya san
cewa yana da Ubangijin da ke gafarta zunubai, ya kuma tafiyar da shi, to
lallai na gafarta wa Bawana", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi
daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
Kamar
yadda shari'a ta zo da cewa: Bawa ya rika neman gafara mudlakan, (a sake ba
tare da ya qayyde wani zunubi ba; kamar ya ce: Ya Ubangijina, ka gafarta min,
kuma kayi mini rahama.
Allah (تعالى)
yana cewa: "Kuma ka ce: Ya Ubangijina, ka yi gafara kuma ka yi rahama, domin kai
ne mafi alherin masu jin-kai" [Mu'uminuna: 118].
Kuma lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana sanar da mutumin da ya
musulunta da cewa ya rika yin addu'a da wadannan kalmomin: "Ya Allah
ka yi gafara a gare ni, ka yi mini rahama, ka shiryar da ni, ka bani lafiya, ka
azurta ni", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Darik dan Ashyam
(Allah ya kara yarda a gare shi).
Kamar
yadda aka shar'anta ga Bawa ya rika nema Ubangijinsa ya gafarta masa zunubansa
gaba dayansu; wadanda ya san su da wadanda bai sansu ba; wannan kuma saboda
zunubai dayawa babu wanda ya sansu sai Allah, kuma lallai za a kama bawa akansu;
saboda ya zo daga Abu-Musa Al'ash'ariy (رضي الله
عنه) daga Annabi(صلى الله عليه وسلم)
lallai shi ya kasance yana yin addu'a da wannan addu'ar: "Ya Allah ka
gafarta min kurakuraina da jahilcina, da ketare iyakana cikin lamari, da abinda
kai ne ka fini saninsa. Ya Allah ka gafarta mini gaskena da wasana, da
kuskurena da gangancina, kuma dukkan hakan akwai shi a wurina. Ya Allah ka
gafarta mini abinda na gabatar da wanda na jinkirta, da abinda na boye da
abinda na bayyanar, da abinda kai ne ka fi ni saninsa, kai ne Mai gabatarwa,
kuma kai ne Mai jinkirtarwa, kuma lallai kai akan kowani abu Mai iko ne",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Da kuma saboda fadin Annabi (صلى الله عليه وسلم): "Shirka a cikin wannan
al'ummar tafi buya fiye da tafiyar tururuwa, Sai
Abubakar (رضي الله عنه) yace: To ta
yaya za a kubuta daga gare ta, ya Manzon Allah? Sai yace: Ka rika
cewa: Ya Allah ina neman ka tsare ni kan yin shirka a gare ka alhalin ina sane,
Ina kuma neman gafararka daga abinda ban sani ba",
Ibnu-Hibbana ya ruwaito shi, daga hadisin Abubakar. Da kuma Ahmad, daga hadisin
Abu Musa.
An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai shi ya kasance yana yin addu'a: "Ya Allah ka
gafarta min zunubaina dukkansu; kananansu da manyansu, na kuskurensu dana
gangancinsu, na sirrinsu dana bayyanansu, na farkonsu da na karshensu", Muslim ya
ruwaito shi, da Abu-dawud.
Idan bawa
ya roki UbangijinSa gafarar zunubansa; wadanda ya sani daga cikinsu da wadanda
bai sani ba, to lallai an datar da shi, dace mai girma.
Kuma
bawa ya roki Ubangijinsa gafarar zunubai cikin ikhlasi da naci da roko mai
tattare da kankan-da kai yana kunsan TUBA DAGA ZUNUBAN, Shi kuma ROKON A DATAR
DA MUTUM ZUWA GA TUBAN yana kunsan NEMAN GAFARAR; domin kowanne daga cikin
ISTIGFAAR da TUBA idan aka ambace shi ba tare da dayan ba, to yana kunsan
ma'anan dayan, Idan kuma ambatonsu ya
hadu a cikin nassoshin Kur'ani ko hadisi to Ma'anan: ISTIGFAARI zai zama:
Neman shafe zunubi da gusar da alamarsa, tare
da bada kariya kan sharrin da ya gabata na zunubin, da kuma suturce shi.
Ita kuma TUBA sai ma'ananta ya kasance: Komawa
zuwa ga Allah ta hanyar barin aikata zunubai, da kuma kare bawa daga abinda ya
ke tsoronsa na munanan ayyukansa a rayuwar da yake fiskanta, tare da yin azama
ko niyyar ba zai sake aikata zunubin ba.
Kuma lallai Ayar Allah ta ambaci ISTIGFAARI da
TUBA a hade, a inda yake cewa: "Kuma ku nemi gafarar Ubangijinku, sannan ku
tuba zuwa gare shi, zai jiyar da ku dadi jiyarwa mai kyau, zuwa ga wani lokaci
ambatacce, kuma ya baiwa dukkan ma'abucin girma girmansa, Idan kuma kuka juya,
to lallai ni ina tsoron azabar yini mai girma akanku"
[Hud: 3].
Da wassu ayoyin wadanda ba wannan ba.
Kuma lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ya ku
mutane! Ku tuba zuwa ga Ubangijinku, kuma ku nemi gafararSa; saboda Ni na kan
tuba zuwa gare shi, tare da neman gafararSa; a kowani yini sau dari",
Annasa'iy ne ya ruwaito shi, daga hadisin Al'agarri Almuzaniy (رضي الله عنه).
Kuma
lallai bawa yana da matsananciyar bukatar YIN ISTIGFAARI, a ko-da-yaushe,
musamman kuma a wannan zamanin; saboda yawaitan zunubai da fitintinu, wannan kuma domin Allah ya datar da shi a
rayuwarsa, da kuma bayan mutuwarsa, ya kuma gyara masa sha'aninsa. Saboda yin istigfaari ya kan bude kofofin
alherori, ya kuma tunkude sharrori da
ukubobi.
Kuma
lallai itama al'ummar musulmai tana da matsananciyar bukata zuwa ga dawwamar da
neman gafarar Allah; domin Allah ya yaye mata ukubobi da suka sauka a gare ta,
ya kuma tunkuxe mata uqobobin da za su sake sauka a gare ta.
Kuma
babu wanda zai yi sakaci KAN NEMAN GAFARA sai wanda ya jahilci amfanoninsa da
albarkokinsa, saboda falolin istigfari
sun zo dayawa a cikin ALQUR'ANI da SUNNA; Allah (تعالى) yana cewa dangane da annabi Salihu (عليه السلام): "Ya ku mutanena Don me kuke gaggawan
aikata mummunan aiki gabanin kyakkyawa, Da dai kun nemi gafarar Allah; don
tsammanin za a yi rahama a gare ku" [Naml: 46]. Saboda da yin istigfaari ne ake yin rahama
ga al'ummah.
Kuma Allah (تعالى)
yana fada dangane da annabi Nuhu (عليه
السلام): "Sai nace: KU NEMI GAFARAR UBANGIJINKU lallai shi ya kasance
mai yawan gafara ne * Zai saki ruwan
sama akanku; mamako * kuma ya karfafe
ku da wata irin dukiya, da 'ya'ya, kuma ya sanya muku gonakai, kuma ya sanya
muku koguna" [Nuh:10-12].
Kuma Allah (تعالى)
yake fadi dangane da annabi Hudu (عليه
السلام): "Kuma, ya mutanena, ku nemi gafarar Ubangijinku,
sa'annan ku tuba zuwa gare shi; sai ya saki ruwan sama akanku, ya kuma kara
muku wani karfi akan karfinku, Kuma kada ku juya baya kuna masu laifi"
[Hudu: 52].
Allah (تعالى)
yace: "Allah bai kasance zai azabta su ba alhalin kana cikinsu, kuma Allah
bai kasance mai azabta su ba; matukar suna neman gafara"
[Anfaal: 33].
Abu-Musa yake cewa: ((Lallai wannan
al'umma a cikinku akwai abubuwan samun aminci biyu; Amma dangane da wannan
annabin –صلى الله عليه وسلم- to shi kam ya shude, yayin da shi kuma NEMAN GAFARA zai ci-gaba da
wanzuwa a cikinku har zuwa tashin kiyama)).
Don
haka; Wannan al'ummar ta yawaita istigfaari = zai dauke mata musibun da suka
sauka ko suka auku, sannan ya tunkude mata ukubobin da za su sauka a gaba; saboda
bala'i baya sauka sai idan an yi ZUNUBI,
kuma ba a yaye shi, sai da yin TUBA da ISTIGFAARI, An ruwaito daga Abdullahi dan Abbas (رضي الله عنهما) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace: "Duk wanda
ya lazimci yin istigfaari Allah zai sanya masa mafita daga kowani qunci, da
kuma yayewa daga kowani baqin ciki, ya kuma azurta shi ta yadda baya tsammani",
Abu-dawud ya ruwaito shi.
Kuma
lallai KALMOMI DA AKA KIYAYE, MASU ALBARKA na ISTIGFAARI sun zo daga Annabi (صلى الله عليه وسلم),
kuma lallai cikin fadin wadannan kalmomin akwai lada mai yawa;
Yana
daga cikinsu:
Fadinsa (صلى الله عليه وسلم):
"Duk wanda ya fadi: ASTAGFIRUL LAHAL ALZIY
LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYAL KAYYUMA, WA ATUBU ILAIHI, Duk wanda ya
fadi haka to an gafarta zunubansa, koda kuwa, ya gudu ne a wurin yaki",
Abu-dawud da Tirmiziy suka ruwaito shi, da Hakim, kuma yace: hadisi ne
ingantacce, akan sharadin Bukhariy da Muslim.
An ruwaito daga Abu-Sa'id alkhudriy, daga
Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai yace: "Duk wanda ya
fada a lokacin da ya tafo zuwa ga shumfudinsa: ASTAGFIRUL LAHA ALLAZIY LA ILAHA
ILLA HUWAL HAYYUL KAYYUMU, WA ATUBU ILAIHI, sau uku, to Allah zai gafarta
zunubansa, koda sun kai kumfan teku", Tirmiziy ne ya ruwaito
shi.
An ruwaito daga Ubadah dan As-samit (رضي الله عنه) yace: Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace: "Duk wanda ya
tashi daga barcinsa, a cikin dare' Sa'annan yace: LA ILAHA ILLAL LAHU, WAHDAHU
LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR,
SUBHANAL LAHI, WALHAMDU LILLAHI, WA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMAG
FIR LIY, Sai yayi addu'a to an amsa masa, idan kuma ya tashi yayi sallah to an
karbi sallarsa", Bukhariy ne ya ruwaito shi.
Ya zo cikin wani hadisin cewa: "Duk wanda a
gabanin ketowan alfijir din juma'a yace: ASTAGFIRUL LAHAL ALZIY LA ILAHA ILLA
HUWAL HAYYAL KAYYUMA, WA ATUBU ILAIHI, sau uku, an gafarta zunubansa koda sun
kasance misalin kumfar teku ne".
Kuma an ruwaito daga Shaddad dau Aus (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace: "Jagoran
laffuzan neman gafara (سيد الاستغفار)
shine bawa yace: ALLAHUMMA ANTA RABBIY LA ILAHA ILLA ANTA; KHALAKTANIY, WA ANA
ABDUKA, WA ANA ALA AHDIKA WA WA'ADIKA MASTAXA'ATU, A'UZU BIKA MIN SHARRI MA
SANA'ATU, ABU'U LAKA BI NI'IMATIKA ALAYYA, WA ABU'U BI ZANBIY; FAGFIR LIY; FA
INNAHU LA YAGFIRUZ ZUNUBA ILLA ANTA, Duk wanda ya faxi kalmomin nan cikin yini
yana mai samun yaqini akansu sai ya mutu a wannan yinin nasa, gabanin yayi yammaci
ya shiga aljannah. Wanda kuma ya faxes u cikin dare, alhalin yana da yaqini
akansu sai ya mutu gabanin yayi yammaci to yana cikin 'yan aljannah",
Bukhariy ya ruwaito shi.
An ruwaito daga Anas (رضي الله عنه) yace: Na ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: Allah (تعالى) yana cewa: "Ya kai dan
Adam da zunubanka za su cika sashen sama gaba daya, sannan sai ka nemi gafarata
sai in gafarta maka, ba zan damu ba!", Tirmiziy ya ruwaito shi,
kuma yace: hadisi ne mai kyau.
Kamar
yadda kuma ake shar'anta neman GAFARAR ALLAH
a lokacin yin wata ibada ko bayan kammala ta; wannan kuma domin ta
magance abinda ya kasance a cikin ibadar na tawaya ko nakasa, tare da nisantar
da mutum daga jiji-da kai, ko riya;
Allah (تعالى)
yana cewa: "Sa'annan ku tafo ta wurin da mutane suke gangarowa, kuma ku nemi
gafarar Allah, lallai Allah Mai gafara ne Mai rahama"
[Baqarah: 199].
Kuma Allah (سبحانه)
yana cewa: "Kuma ku tsayar da sallah, kuma ku bada zakka, ku bada rance wa Allah
rance mai kyau, kuma duk abinda kuka
gabatar ga kayukanku na alkhairi za ku same shi a wurin Allah, zai kasance
mafifici kuma zai fi girma ga sakamako, Kuma ku roqi Allah gafara; lallai Allah
Mai gafara ne Mai jin-kai" [Muzammil: 20].
Haka
kuma an shar'anta musulmi ya riqa neman gafara ga 'yan'uwansa muminai maza da
muminai mata, da musulmai maza da msulmai mata, rayayyu daga cikinsu da waxanda
suka mutu, wannan kuma a matsayin
kyautatawarsa ne a gare su, da bayyanar da soyayya, da lafiyar zuciya, tare da
amfanar da musulmai, da kuma (tsoma baki) don neman cetonsu a wurin Allah; Allah (تعالى)
yana cewa: "Da kuma waxanda suka zo a bayansu, suna cewa: Ya Ubangijinmu ka yi
mana gafara, tare da 'yan'uwanmu da suka rigaye mu da Imani, kuma kada ka sanya
wani qulli a cikin zukatanmu dangane da waxanda suka yi Imani, Ya Ubangijinmu
lallai kai Mai tausayi ne, Mai rahama" [Hahsri: 10].
An ruwaito daga Ubadah xan Assamit (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai shi yace: "Duk wanda
ya nemi gafara ga muminai maza da muminai mata to lallai Allah zai rubuta masa
lada a madadin kowani mumini namiji da mumina mace",
Alhaisamiy yace: Isnadin wannan hadisin yana da kyau (jayyid).
Wannan kuma kamar nema musu gafara Kenan a
lokacin yin sallar janaza, da kuma nema musu gafara a maqabartai idan musulmi
ya ziyarce su.
Hakan kuma koyi ne da Mala'ikun da suke xauke
da al'arshi, da kuma sauran Mala'iku makusanta, Allah (تعالى)
yana cewa: "Wadanda suke rike da al'arshi, da wadanda suke kewayensa suna
yin tasbihi da gode wa Ubangijinsu, kuma suna yin Imani da shi, suna kuma neman
gafarar Allah ga waxanda suka yi Imani (suna cewa) Ya Ubangijinmu! Lallai ka
yalwaci kowani abu da rahama da kuma ilimi; sai ka yi gafara ga waxanda suka
tuba, suka kuma bi hanyarka, kuma ka kare su daga azabar wutar jahim" [Gafir:
7].
Yin haka kuma yana daga cikin manyan haqqoqin
muminai!
Ya
ku bayin Allah… !
Ku amsawa
umurnin Ubangijinku, Allah yana cewa a
cikin hadisin qudusiy: "Ya ku bayina ! lallai ku, kuna
yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai gaba daya; sai ku nemi
gafarata; zan gafarta muku", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin
Abi-zarrin.
Sai ku fiskanci Ubangijinku da neman
gafararSa, za ku ga karamcinSa da kyautarSa da falalarSa, da albarkokinSa, kuma
za ku sami shafe aiyukanku munana, da xaukaka darajoji, Hadisi y azo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace: "Na rantse
da wanda raina ke hannunsa! Da ace bakwa yin zunubi to da Allah ta'alah ya
tafiyar da ku, kuma da ya zo da wassu mutanen waxanda suke yin zunubi; sai suna
neman gafarar Allah ta'alah sai ya gafarta musu",
Muslim ya ruwaito shi.
Kuma saboda kasancewarsa Allah maxaukaki Mai
yalwar gafara ne, mai baiwa da kyauta da karamci, Allah (تعالى)
yana cewa: "Kuma duk wanda ya aikata mummunan aiki, ko ya zalunci kansa,
sa'annan sai ya nemi gafarar Allah, to lallai zai sami Allah Mai yawan gafara
Mai rahama" [Nisa'i: 110].
Allah
yayi mini albarka Ni da KU, cikin alqur'ani mai girma
…
HUXUBA TA BIYU
Yabo
ya tabbata ga Allah, Mai yawan gafara da godiya, Kuma sunaye mafiya kyau na
Ubangajina ne, da kuma sifofi madaukaka. Ina yin yabo ga Ubangijina akan
ni'imominSa masu girma.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya
sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai shugabanmu kuma
annabinmu Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, zababbe,
Ya
Allah ka yi salati da sallama da karin albarka ga bawanka kuma manzonka
Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa masu takawa.
Bayan haka;;;
Ku kiyaye
dokokin Ubangijinku Madaukaki, ta hanyar neman yardarSa, da yin aiki da da'a a
gare shi, da kuma nisantar haramiyarSa,
Kuma lallai Ubangijinku ya baku damar yin aiki
na kwarai, kuma ya sanya wannan duniyar ta zama gidan yin aiki ne, Lahira kuma
gidan sakamako.
Kuma hakika masu yin aiki da ikhlasi da
kyautatawa a wannan gida na duniya sun samu babban rabo, Masu kuma barna da
kautar da kai ga addini sun tabe.
Ku kaddara ga ku, kamar ajalinku ya riga ya zo
shi, burinku shi kuma ya kare.
Kuma lallai kuna da abin daukar izina cikin
lamarin wadanda suka rigaye ku, kuma a cikin labarunsu da tarihinsu akwai abin
wa'aztuwa; domin ma'abuta kabari dayansu yana burin ya dawo duniya, domin ya
sallaci raka'oi guda biyu, ya nemi gafarar Allah dayawa, Saidai faufau ba za a
amsa masa wannan bukatar ba, Allah Ta'alah ya ce: "Har idan
mutuwa ta je wa dayansu, Sai ya ce: Ya Ubangijina, a mayar da ni (duniya) * tsammanina in aikata aiki na kwarai cikin
abinda na bari, Kayya, wannan kalma ce, da shi yake fadanta, a gaba gare shi
akwai rayuwar barzahu, har zuwa lokacin da za a tayar da su" [Mu'uminuna:
99-100].
Don
haka, Kada ka raina aikin alkhairi duk karancinsa, kuma kada ka raina aikin
sharri duk karancinsa, saboda ya zo cikin hadisi cewa: "Ina tsawatar
muku kan raina zunubai saboda karantarsu, domin su kan hadu ga mutum, sais u
halaka shi".
Kuma ya zo cikin wani hadisin cewa: "Kada ka
raina wani abu, daga aikin alkhairi".
Ya ku bayin Allah,,,
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin
salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda
suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Addu'a;;;;;;;;;;;;;;;;