HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 10/MUHARRAM/1437h
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
Godiya ta
tabbata ga Allah Mai rahama Mai jin qai; Mai ilimi Mai hikima, Ma'abocin falala
mai girma, Ina yin godiya wa
Ubangina kuma ina yin yabo a gare shi,
Ina kuma tuba zuwa gare shi ina kuma neman gafararSa,
Ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin
tarayya, Ma'abocin al'arshi mai karamci,
Kuma ina
shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu annabi Muhammadu bawanSa ne kuma
manzonsa ne; Ma'abocin halayya masu
girma, Ya Allah ka yi qarin salati da
sallama ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, masu
kira zuwa ga Allah da kuma shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya.
Bayan
haka:
Ku kiyaye
dokokin Allah ta hanyar yin aiki da abubuwan da suke yardar da shi, da kuma
qaurace wa abubuwan da ya haramta;
domin ku rabauta da samun yardarSa da kuma ni'imomin aljannoninSa, sannan ku samu tsira daga fushinSa da
kuma uqobobinSa,
Ya ku
musulmai…
Lallai
Ubangijinmu mabuwayi da xaukaka ya yawaita qofofin alkhairi, da kuma hanyoyin
aiyuka kyawawa, a matsayin falala da
rahama da kuma kyauta daga ma'abocin buwaya da xaukaka; domin musulmi ya shiga kowace qofa ta
alkhairori, ya kuma bi kowace hanya
daga cikin hanyoyin biyayya; sai Allah
ya gyara duniyarSa, ya kuma xaukaka
shi zuwa ga darajoji a lahirarSa;
Sai shi kuma Allah (سبحانه) ya
karrama shi ta hanyar bashi rayuwa daddaxa, da kuma rabauta a cikin
rayuwarsa, daga qarshe sai ya samu
ni'ima tabbatacciya, da kuma yardar Ubangiji, bayan mutuwarsa. Allah (تعالى)
yana cewa:
"Sai ku yi tsere zuwa ga aiyukan
alkhairi. Kuma duk inda kuka kasance Allah zai zo da ku gabaxaya, Lallai Allah
akan komai mai iko ne" [Baqarah: 148].
Kuma Allah (سبحانه)
yana cewa -a dangane da annabawansa; waxanda sune abin koyi ga mutane (Allah yayi
qarin salati da sallama a gare su gabaxaya):
"Lallai su, Sun kasance suna yin
tsere cikin aiyukan alkhairi, Kuma suna yin bauta a gare mu akan kwaxayi da
fargaba, kuma sun kasance a gare mu masu tsoro ne" [Anbiya'i:
90].
Kuma Annabi (صلى الله
عليه وسلم) yace wa sahabinsa Mu'azu (رضي الله عنه):
"Shin ba
zan shiryar da kai zuwa ga qofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, Sadaka kuma
tana shafe kurakurai kamar yadda ruwa ke kashe wuta. haka Sallar mutum a cikin
yankin dare. Sannan sai Annabi ya karanta faxin Allah: (Gefen jikinsu
yana nisantar gurin kwanciyarsu, suna roqon Ubangijinsu cikin fargabar tsoro da
kwaxayi, kuma daga cikin abinda muka azurta su suna ciyarwa. Kuma rai bata san
abinda aka voye a gare ta na sanyin ido ba, sakamakon abinda suka kasance suke
aikatawa). Sa'annan yace: Ba zan ba ka labari dangane da, kan wannan lamarin
ba, da ginshiqansa, da qololuwar tozonsa?
Sai nace: Eh, ka bani labari ya Manzon Allah!
Sai yace: Kan wannan lamarin shine:
Musulunci.
Ginshiqinsa kuwa sallah.
Qololuwar tozonsa kuma shine: Jihadi fiysabillah”.
Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya inganta shi.
KUMA
YANA DAGA CIKIN QOFOFIN ALKHAIRORI, DA HANYOYIN KYAWAWAN AIYUKA DA XA'O'I, KUMA
YANA DAGA CIKIN SABBUBAN SHAFE MUNANAN AIYUKA: NEMAN GAFARA; Saboda
neman gafara sunnar Annabawa da Manzanni ne (عليهم
الصلاة والسلام), Allah (تعالى)
yana cewa a dangane da iyayen 'yan-adam; guda biyu (wato: annabi Adam da
Hauwa'u) Allah ya yi salati mai yawa da rahama da qarin albarka a gare su:
"Suka ce: Ya Ubangijinmu! Mun zalunci
kayukanmu, Idan baka gafarta mana, ka yi rahama a gare mu ba, zamu kasance daga
cikin masu hasara" [A'araf: 23].
Kuma Allah yana cewa a dangane da annabi Nuhu
(عليه السلام)
"Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, da
iyayena guda biyu, da wanda ya shiga gidana yana mumini, da kuma muminai maza
da muminai mata" [Nuh: 28].
Kuma Allah mabuwayi da xaukaka yana faxa
dangane da Ibrahimu alkhalil (عليه السلام):
"Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mini, da
iyayena biyu, da kuma muminai, a ranar da hisabi yake tsayawa" [Ibrahim:
41].
Kuma Allah yana cewa dangane da annabi Musa (عليه السلام):
"Ya Ubangijina! Ka yi gafara a gare
ni, ni da xan'uwana, kuma ka shigar da mu cikin rahamarka; lallai kai ne mafi
rahamar masu rahama" [A'araf: 151].
Kuma Allah (تعالى)
yana cewa:
"Sai annabi Dawuda ya tabbata cewa: Lallai
jarrabarsa muka yi, sai ya nemi gafarar Ubangijinsa, ya kuma faxi yana mai sujjada,
ya kuma mayar da lamari zuwa ga Allah" [Sad: 24].
Allah (تعالى)
yana cewa, a inda yake umurtar annabinSa (صلى الله
عليه وسلم) da cewa:
"Ka sani, Lallai babu wanda ya cancanci
bauta sai Allah, kuma ka nemi gafarar zunubanka, da kuma wa muminai maza da
muminai mata" [Muhammadu: 19].
KUMA
YANA DAGA SHIRIYAR MANZONMU (صلى الله عليه وسلم): YAWAITA
NEMAN GAFARA, tare da cewa Allah ta'alah ya gafarta masa abinda ya gabata
na zunubansa, da abinda ya jinkirta; Ya zo daga Xan Umar (رضي الله عنهما) yace:
"Mun kasance muna qidaya wa
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) a majalisa guda xaya, sau xari: RABBI IGFIR LIY WA
TUB ALAYYA; INNAKA ANTAT TAWWABUR RAHIM.
Ma'ana: Ya Ubangijina! Ka gafarta
mini, ka karvi tuba ta, lallai kai mai yawan karvar tuba ne, Mai rahama".
Abu dawud ya ruwaito shi, da Tirmiziy, kuma yace: Hadisi ne mai kyau
ingantacce.
Kuma an ruwaito daga A'ishah (رضي الله عنها) lallai ta ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance gabanin mutuwansa yana yawaita
faxin: SUBHANALLAHI, WA BI HAMDIHI, ASTAGFIRULLAHA WA ATUBU ILAIHI.
Ma'ana: Tsarki ya tabbata ga
Allah, tare da gode masa, Ina neman gafarar Allah, ina kuma yin tuba zuwa gare
shi. Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) yace:
"Ban ga wani mutumin da yafi
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yawaita faxin ASTAG FIRUL LAHA WA ATUBU ILAIHI".
Ma'ana: Ina neman gafarar Allah, kuma ina tuba zuwa gare shi. Annasa'iy ya
ruwaito shi.
Kuma Annabi |(صلى الله
وسلم) ya kasance bayan yin sallamar fita daga sallah ya kan ce: Astagfirul
laha, Astagfirul laha, Astagfirul laha, har sau uku. Muslim ya
ruwaito shi, daga hadisin Sauban (رضي الله
عنه). Sa'annan daga bisani sai ya faxi zikirorin da aka shar'anta
faxinsu a bayan sallolin farilla.
Kuma lallai NEMAN GAFARA Xabi'ar
salihai ne, kuma aiki ne na mutane masu biyayya, da taqawa, kuma alama ce ta
muminan mutane, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana
zunubanmu, kuma ka kankare mana munanan aiyukanmu, kuma ka xauki rayukanmu tare
da masu yin biyayya" [Ali-imrana: 193].
Kuma Allah (تعالى)
yana cewa:
"Waxanda suke cewa: Ya Ubangijinmu! Lallai
mu mun yi Imani; sai ka gafarta mana zunubanmu, kuma ka katange mu daga azabar
wuta *
Masu haquri, da masu gaskiya, da masu qanqan da kai, da masu ciyarwa, da
masu yin istigfari a lokutan asuba" [Ali-imrana: 16-17].
Alhasan yace: Sun yi ta sallah har zuwa
lokacin sahur, sannan suka fiskanci ibadar neman gafara.
Kuma Allah (تعالى)
yana cewa:
"Sune kuma Waxanda, idan suka aikata
wata alfasha, ko suka zalunci kayukansu su kan tuna Allah; sai su nemi gafarar
zunubansu, Kuma wanene zai gafarta zunubai idan ba Allah ba, kuma basa dogewa
akan abinda suke aikatawa, alhalin suna sane" [Ali-imrana: 135].
Ibnu-rajab yace: ((Shi kuma neman gafara
daga zunubai shine: Neman lulluve su.
kuma lallai bawa yana da matuqar buqata zuwa ga hakan; saboda ko-yaushe ya
kan yi kuskure cikin dare da rana. Kuma lallai ambaton TUBA DA NEMAN GAFARA ya
maimaitu a cikin alqur'ani, da kuma yin umurni da su, da kwaxaitarwa zuwa gare
su)). … Maganarsa ta qare.
Kuma
lallai NEMAN GAFARA DAGA Ubangiji mabuwayi da xaukaka Allah ta'alah yayi
alkawari da cewa zai amsa, kuma zai yi gafara.
Kuma
lallai an shar'anta cewa Bawa ya riqa neman gafara a kan zunubi aiyananne,
sananne; saboda faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
"Lallai bawana ya aikata wani
zunubi, Sannan yace: Ya Ubangijina, lallai ni na aikata wani zunubi; sai ka
gafarta mini shi, Sai Allah yace: Bawana lallai ya san cewa yana da Ubangijin da yake gafarta zunubai, ya kuma tafiyar da shi, to
lallai na gafarta wa Bawana", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi
daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
Kamar
yadda shari'a ta zo da cewa: Bawa ya riqa neman gafara, a sake ba qaidi; sai
yace: Ya Ubangijina! ka gafarta min, kuma kayi mini rahama. Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma ka ce: Ya Ubangijina! Ka yi
gafara kuma ka yi rahama, domin kai ne mafi alherin masu rahama"
[Mu'uminuna: 118].
Kuma lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana sanar da mutumin da ya
musulunta da cewa ya riqa yin addu'a da waxannan kalmomin :
"Ya Allah ka yi gafara a gare ni,
ka yi mini rahama, ka shiryar da ni, ka bani lafiya, ka azurta ni",
Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Xariq xan Ashyam (Allah ya qara yarda a gare
shi).
Kamar
yadda aka shar'anta: Bawa ya riqa nema daga Ubangijinsa cewa ya gafarta masa
zunubansa gabaxayansu; waxanda ya san su da waxanda bai sansu ba; wannan kuma
saboda zunubai dayawa babu wanda ya sansu sai Allah, kuma lallai bawa za a kama
shi akansu; Ya zo daga Abu-Musa
al'ash'ariy (رضي الله عنه)
daga Annabi(صلى الله عليه وسلم) lallai shi ya
kasance yana yin addu'a da wannan addu'ar:
"Ya Allah! Ka gafarta min
kurakuraina da jahilcina, da qetare iyakana cikin lamari, da abinda kai ne ka
fini saninsa. Ya Allah! Ka gafarta mini gaskena da wasana, da kuskurena da
gangancina, kuma dukkan haka, akwai shi a wurina. Ya Allah! Ka gafarta mini
abinda na gabatar da wanda na jinkirta, da abinda na voye da abinda na
bayyanar, da abinda kai ne ka fi ni saninsa, kai ne Mai gabatarwa, kuma kai ne
Mai jinkirtarwa, kuma lallai kai akan kowani abu mai iko ne",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Da kuma saboda faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
"Shirka a cikin wannan al'ummar tafi
vuya fiye da tafiyar tururuwa, Sai Abubakar (رضي الله عنه) yace: To ta yaya za a kuvuta daga gare
ta, ya Manzon Allah? Sai yace: Ka riqa cewa: Ya Allah ina neman ka tsare
ni kan yin shirka a gare ka alhalin ina sane, Ina kuma neman gafararka daga
zunubin da ban sani ba", Ibnu-Hibbana ya ruwaito shi, daga
hadisin Abubakar, Da kuma Ahmad, daga hadisin Abu Musa.
An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai shi ya kasance yana yin addu'a:
"Ya Allah! Ka gafarta min
zunubaina dukkansu; qananansu da manyansu, na kuskurensu dana gangancinsu, na
sirrinsu dana bayyanansu, na farkonsu da na qarshensu", Muslim ya
ruwaito shi, da Abu-dawud.
Idan bawa
ya roqiUbangijinSa gafarar zunubansa; waxanda ya sani daga cikinsu da waxanda
bai sani ba, to lallai an datar da shi; dace mai girma.
Kuma
bawa ya roqi Ubangijinsa gafarar zunubai cikin ikhlasi da naci da roqo mai
tattare da qanqan-da kai yana qunsan TUBA DAGA ZUNUBAN, Shi kuma ROQON A DATAR
DA MUTUM ZUWA GA TUBAN yana qunsan NEMAN GAFARAR; saboda haka, kowanne daga
cikin ISTIGFAAR da TUBA idan aka ambace shi ba tare da xayanba to yana qunsan
ma'anan xayan. Idan kuma ambatonsu ya
haxu a cikin nassoshin Qur'ani ko hadisi to Ma'anan: ISTIGFAARI sai ya zama:
Neman shafe zunubi da gusar da alamarsa ko gurbin da ya bari, tare da bada
kariya kan sharrin da ya gabata na zunubin, da kuma suturce shi. Ita kuma TUBA
sai ma'ananta ya zama: Komawa zuwa ga Allah; ta hanyar barin aikata zunubai, da
kuma kare bawa daga abinda ya ke tsoro; na munanan aiyukansa a rayuwar da yake
fiskanta, tare da yin azama ko niyyar ba zai sake aikata zunubin ba.
Kuma lallai AyarAllah ta ambaci ISTIGFAARI da
TUBA a haxe, a inda Allah yake cewa:
"Kuma ku nemi gafarar Ubangijinku,
sa'annan ku tuba zuwa gare shi, zai jiyar da ku daxi jiyarwa mai kyau, zuwa ga
wani lokaci ambatacce, kuma ya baiwa dukkan ma'abocin girma girmansa, Idan kuma
kuka juya to lallai ni ina tsoron azabar yini mai girma akanku" [Hud:
3].
Da wassu ayoyin waxanda ba wannan ba.
Kuma lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Ya ku mutane! Ku tuba zuwa ga
Ubangijinku, kuma ku nemi gafararSa; saboda Ni na kan tuba zuwa gare shi, ina
kuma neman gafararSa; a kowani yini sau xari",
Annasa'iy ne ya ruwaito shi, daga hadisin Al'agarri Almuzaniy (رضي الله عنه).
Kuma
lallai bawa yana da matsananciyar buqatar YIN ISTIGFAARI, a ko-da-yaushe, musamman kuma a wannan zamanin saboda
yawaitan ZUNUBAI da FITINTINU, wannan
kuma domin Allah ya datar da shi a rayuwarsa, da kuma bayan mutuwarsa, ya kuma
gyara masa sha'aninsa. Saboda yin
istigfaari ya kan buxe qofofin alherori,
ya kuma tunkuxe sharrori da uqubobi.
Kuma
lallai itama al'ummar musulmai tana da matsananciyar buqata zuwa ga dawwama kan
neman gafara; domin Allah ya yaye mata uqubobi da suka sauka a gare ta, ya kuma
tunkuxe mata uqobobin da za su sake sauka a gare ta.
Kuma
babu wanda zai yi sakaci KAN NEMAN GAFARA sai wanda ya jahilci amfanoninsa da
albarkokinsa, saboda falolinsa sun zo
dayawa a cikin ALQUR'ANI da SUNNAH; Allah (تعالى)
yana cewa dangane da annabi Salihu (عليه
السلام):
"Ya ku mutanena! Don me kuke gaggawan
aikata mummuna gabanin kyakkyawa, Da dai kun nemi gafarar Allah; da tsammanin
za a yi rahama a gare ku" [Naml: 46]. Saboda da yin istigfaari ne ake yin rahama
ga al'ummah.
Kuma Allah (تعالى)
yana faxa dangane da annabi Nuhu (عليه
السلام):
"Sai nace: KU NEMI GAFARAR
UBANGIJINKU lallai shi ya kasance mai yawan gafara *
Zai saki ruwan sama akanku; mamako
* kuma ya qarfafe ku da wata dukiya, da 'ya'ya,
kuma ya sanya muku gonakai, kuma ya sanya muku koguna" [Nuh:10-12].
Kuma Allah (تعالى)
yake faxi dangane da annabi Hudu (عليه
السلام):
"Kuma, ya mutanena! Ku nemi gafarar
Ubangijinku, sa'annan ku tuba zuwa gare shi; sai ya saki ruwan sama akanku, ya
kuma qara muku wani qarfi akan qarfinku, Kuma kada ku juya baya kuna masu laifi"
[Hudu: 52].
Allah (تعالى)
yace:
"Allah bai kasance zai azabta su ba
alhalin kana cikinsu, kuma Allah bai kasance mai azabta su ba; matuqar suna
neman gafara" [Anfaal: 33].
Abu-Musa yake cewa (رضي الله عنه):
((Lallai wannan al'ummah a cikinku akwai
abubuwan samun aminci guda biyu; Amma
dangane da wannan annabin –صلى الله عليه وسلم- to
shi kam ya shuxe, Yayin da shi kuma NEMAN GAFARA zai ci gaba da wanzuwa a
cikinku har zuwa tashin kiyama)).
Don
haka; Wannan al'ummar; Idan ta yawaita istigfaari = zai xauke mata musibun da
suka sauka ko suka auku, sannan ya tunkuxe mata waxanda za su sauka a
gaba; saboda bala'i baya sauka sai
idan an yi ZUNUBI, kuma ba a yaye shi
sai da yin TUBA da ISTIGFAARI, An
ruwaito daga Abdullahi xan Abbas (رضي الله
عنهما) yace: Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) yace:
"Duk wanda ya lazimci yin
istigfaari Allah zai sanya masa mafita daga kowani qunci, da kuma yayewa daga
kowani baqin ciki, ya kuma azurta shi ta yadda baya tsammani",
Abu-dawud ya ruwaito shi.
Kuma
lallai KALMOMI DA AKA KIYAYE SU MASU ALBARKA na ISTIGFAARI sun zo daga Annabi (صلى الله عليه وسلم),
kuma lallai cikin faxin waxannan kalmomin akwai lada mai yawa;
Yana
daga cikinsu:
Faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
"Duk wanda ya faxI: ASTAGFIRUL LAHAL
ALZIY LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYAL QAYYUMA, WA ATUBU ILAIHI, Duk wanda ya
faxi haka to an gafarta zunubansa, koda kuwa ya gudu a wurin yaqi". Abu-dawud
da Tirmiziy suka ruwaito shi, da Hakim, kuma yace: hadisi ne ingantacce, akan
sharaxin Bukhariy da Muslim.
An ruwaito daga Abu-Sa'id alkhudriy, daga
Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai yace:
"Duk wanda ya faxa a lokacin da ya
tafo zuwa ga shumfuxinsa: ASTAGFIRUL LAHA ALLAZIY LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYUL
QAYYUMU, WA ATUBU ILAIHI, sau uku, to Allah zai gafarta zunubansa, koda
sun kai kumfan teku", Tirmiziy ne ya ruwaito shi.
An ruwaito daga Ubadah xan As-samit (رضي الله عنه) yace: Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda ya tashi daga barcinsa, a
cikin dare' Sa'annan yace: LA ILAHA ILLAL LAHU, WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL
MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIR, SUBHANAL LAHI, WALHAMDU
LILLAHI, WA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMAG FIR LIY, Sai yayi
addu'a to an amsa masa, idan kuma ya tashi yayi sallah to an karvi sallarsa",
Bukhariy ne ya ruwaito shi.
Ya zo cikin wani hadisin cewa:
"Duk wanda a gabanin ketowar alfijir
xin juma'a yace: ASTAGFIRUL LAHAL ALZIY LA ILAHA ILLA HUWAL HAYYAL QAYYUMA, WA
ATUBU ILAIHI, sau uku, an gafarta zunubansa koda sun kasance misalin
kumfar teku ne".
Kuma an ruwaito daga Shaddad xau Aus (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Jagoran laffuzan neman gafara shine
bawa yace: ALLAHUMMA ANTA RABBIY LA ILAHA ILLA ANTA; KHALAQTANIY, WA ANA
ABDUKA, WA ANA ALA AHDIKA WA WA'ADIKA MASTAXA'ATU, A'UZU BIKA MIN SHARRI MA
SANA'ATU, ABU'U LAKA BI NI'IMATIKA ALAYYA, WA ABU'U BI ZANBIY; FAGFIR LIY; FA
INNAHU LA YAGFIRUZ ZUNUBA ILLA ANTA, Duk wanda ya faxi kalmomin nan cikin yini
yana mai samun yaqini akansu sai ya mutu a wannan yinin nasa, gabanin yayi
yammaci ya shiga aljannah. Wanda kuma ya faxe su cikin dare, alhalin yana da
yaqini akansu sai ya mutu gabanin yayi yammaci to yana cikin 'yan aljannah",
Bukhariy ya ruwaito shi.
An ruwaito daga Anas (رضي الله عنه) yace: Na ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: Allah (تعالى) yana cewa:
"Ya kai xan Adam! Da zunubanka za
su cika sashen sama gabaxaya, sannan sai ka nemi gafarata sai in gafarta maka,
ba zan damu ba!", Tirmiziy ya ruwaito shi, kuma yace: hadisi ne mai
kyau.
Kamar
yadda kuma ake shar'anta neman GAFARAR ALLAH
a lokacin yin wata ibada ko bayan kammala ta; wannan kuma domin ta
magance abinda ya kasance a cikin ibadar na tawaya ko naqasa, tare da nisantar
da mutum daga ji-da kai, ko riya;
Allah (تعالى)
yana cewa:
"Sa'annan ku tafo ta wurin da mutane
suke gangarowa, kuma ku nemi gafarar Allah, lallai Allah Mai gafara ne Mai
rahama" [Baqarah: 199].
Kuma Allah (سبحانه)
yana cewa:
"Kuma ku tsayar da sallah, kuma ku
bada zakka, ku bada rance wa Allah rance mai kyau, kuma duk abinda kuka gabatar ga kayukanku
na alkhairi za ku same shi a wurin Allah, zai kasance mafifici kuma zai fi
girma ga sakamako, Kuma ku roqi Allah gafara; lallai Allah Mai gafara ne Mai
rahama" [Muzammil: 20].
Sai Allah yayi umurnin a nemi gafararSa a
lokacin da ake yin waxannan aiyukan xa'an, da kuma bayan kammala su.
Haka
kuma an shar'anta musulmi ya riqa neman gafara ga 'yan'uwansa muminai; maza da mata,
da musulmai maza da msulmai mata, rayayyu daga cikinsu da waxanda suka
mutu, wannan kuma a matsayin
kyautatawarsa ne a gare su, da bayyanar da soyayya, da lafiyar zuciya, tare da
amfanar da musulmai, da kuma (tsoma baki) don neman cetonsu a wurin Allah; Allah (تعالى)
yana cewa:
"Da kuma waxanda suka zo a bayansu,
suna cewa: Ya Ubangijinmu ka yi mana gafara, tare da 'yan'uwanmu da suka rigaye
mu da Imani, kuma kada ka sanya wani qulli a cikin zukatanmu dangane da waxanda
suka yi imani, Ya Ubangijinmu lallai kai Mai tausayi ne, Mai rahama" [Hahsri:
10].
An ruwaito daga Ubadah xan Assamit (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai shi yace:
"Duk wanda ya nemi gafara ga
muminai maza da muminai mata to lallai Allah zai rubuta masa lada a madadin
kowani mumini namiji da mumina mace", Alhaisamiy yace: Isnadin
wannan hadisin yana da kyau (jayyid).
Wannan kuma kamar nema musu gafara kenan a
lokacin yin sallar janaza a gare su, da kuma nema musu gafara a maqabartai idan
musulmi ya ziyarce su.
Hakan kuma koyi ne da Mala'ikun da suke xauke
da al'arshi, da kuma sauran Mala'iku makusanta, Allah yana cewa:
"Waxanda suke riqe da al'arshi, da
waxanda suke kewayensa suna yin tasbihi da gode wa Ubangijinsu, kuma suna yin imani
da shi, suna kuma neman gafarar Allah ga waxanda suka yi imani (suna cewa) Ya Ubangijinmu!
Lallai ka yalwaci kowani abu da rahama da kuma ilimi; sai ka yi gafara ga
waxanda suka tuba, suka kuma bi hanyarka, kuma ka kare su daga azabar wutar
jahim" [Gafir: 7].
Yin haka kuma yana daga cikin manyan haqqoqin
muminai!
Ya
ku bayin Allah… !
Ku amsawa
umurnin Ubangijinku, Allah yana cewa a
cikin hadisin qudusiy:
"Ya ku bayina ! lallai ku, kuna
yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai gabaxaya; sai ku nemi
gafarata; zan gafarta muku", Muslim ya ruwaito shi daga hadisin Abi-zarrin.
Sai ku fiskanci Ubangijinku da neman
gafararSa, za ku ga karamcinSa da kyautarSa da falalarSa, da albarkokinSa, kuma
za ku sami shafe aiyukanku munana, da xaukaka darajoji, Hadisi y azo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) yace: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Na rantse da wanda raina yake
hannunsa! Da ace bakwa yin zunubi to da Allah ta'alah ya tafiyar da ku, kuma da
ya zo da wassu mutanen waxanda suke yin zunubi; sai suna neman gafarar Allah
ta'alah sai ya gafarta musu", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma saboda kasancewarsa Allah maxaukaki Mai
yalwar gafara ne, mai baiwa da kyauta da karamci, yana son a riqa neman
gafararSa, ana roqonSa Allah (تعالى) yana cewa:
"Kuma duk wanda ya aikata mummunan
aiki, ko ya zalunci kansa, sa'annan sai ya nemi gafarar Allah, to lallai zai
sami Allah Mai yawan gafara Mai rahama" [Nisa'i: 110].
Allah
yayi mini albarka Ni da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da mu da
abinda ke cikinsa na ayoyi da tunatarwa mai hikima, kuma ya amfanar da mu da shiriyar
shugaban manzanni, da kuma maganganunsa miqaqqu, Ina faxar maganata wannan, kuma ina neman
gafarar Allah Mai girma Mai daraja wa Ni da Ku, da kuma sauran musulmai da
muminai, Ku nemi gafararSa; lallai
shi Mai gafara ne Mai rahama.
…
HUXUBA TA BIYU
Godiya
ta tabbata ga Allah, wanda yake gafarta zunubi, Mai karvar tuba, Mai kuma
tsananin uquba, Ma'abocin ni'imomi, Babu abin bautawa da gaskiya sai shi, kuma
zuwa gare shi makoma ta ke. Ina yin godiya wa Ubangijina, ina kuma yaba masa
akan falalarSa mai girma,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,
Masani, Mai qudura.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma
shigabanmu Muhammadu bawan Allah ne kuma Manzonsa ne, mai bushara da gargaxi,
kuma fitila mai haskakawa,
Ya
Allah kayi salati da sallama da qarin albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu,
da iyalansa da sahabbansa gabaxaya.
Bayan haka;;;
Ku kiyaye
dokokin Ubangijinku, kuma kuyi masa ikhlasin dukkan ibadodi, kuma ku nisanci
kamunSa da azabarSa,
Ya
ku musulmai…
Ku
kiyayi fitintinu; saboda suna cutar da addini, da kuma duniya; wato suna
halakar da bawa a lahira, su kuma gurvata yanayin rayuwa a duniya,
Kuma lallai wanda yayi rabo shine wanda aka
nisantar da shi daga fitintinu,
kuma lallai mafi girman fitina wajen muni ita
ce: Wacce gaskiya da varna suka cakuxe wa mutum a cikinta, da kuma shiriya da
vata, da kyakkyawa da mummuna, haka kuma halal da haram.
Kuma tabbas fitintinu masu yawa sun mamaye
garurruka da kuma mutane, waxanda suka fitar da samarin musulmai daga wuraren
tarbiyyarsu masu aminci, da kewayen da suke zaune a cikinsa mai tsari, da
al'ummar da suke rayuwa a cikinta mai tausaya musu = zuwa ga vata, da
vatacciyar aqida, da kuma bi, tare da son khawarijawan wannan zamanin; sai su kuma KHAWRIJAWAN WANNAN ZAMANIN suka
jagorance su zuwa ga/ KAFIRTA
MUSULMAI, da ZUBAR DA JINANEN HARAM
(kisa), harma suka yi musu fatawar SU SHIGA YANAYIN DA ZA SU QONA KANSU DA
KASHE KANSU, (والعياذ بالله),
Shin mutumin da yake (tayar da bomb); ya QONA
KANSA yana zaton wai aikata hakan sababi ne na shiga aljannah???!!!
Shin bai san cewa duk wanda ya KASHE KANSA
yana cikin wuta ba, Shin be ji, ko ya
karanta faxin Allah (تعالى) ba
ne:
"Kuma kada ku kashe kayukanku; lallai
Allah ya kasance mai yin rahama ne a gare ku
* Kuma duk wanda ya aikata
haka, yana mai qetare iyaka, da kuma zalunci, to da sannu zamu shigar da shi
cikin wata wuta, kuma aikata haka, akan Allah mai sauqi ne"
[Nisa'i: 29-30].
Kuma ya zo cikin hadisi cewa "Lallai
wanda ya kashe kansa yana cikin wuta".
Kuma
wanda ya kashe MUSULMI yana zaton cewa kashe shin sababi ne na shiga
aljannah???!!!
Shin bai san cewa KASHE MUSULMI yana dawwamar da ma'abocinsa, a cikin wuta ba?
Shin kuma bai ji, ko ya karanta faxin Allah (تعالى) ba
ne:
"Duk wanda ya kashe wani mumini da
ganganci to sakamakonsa shine jahannama, yana mai dawwama a cikinta, kuma Allah
ya yi fushi da shi, ya kuma yi tattalin azaba mai girma agare shi"
[Nisa'i: 93].
Kuma shin faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم) bai iske su ba ne, a inda yake cewa:
"Duk wanda ya kashe kafirin amana
ba zai ji qamshin aljannah ba".
Shin
waxannan mutanen ba za su xauki darasi daga waxanda suka gabace su; cikin masu
aiki irin nasu ba ne; waxanda suka qetare iyakokin Allah, sai suka yi nidama a
lokacin da nadamar ba ta yi amfani ba a gare su ba! Haka kuma waxanda suka rikitar da su, ko suka
ruxe su, suma basu iya amfanar da su da komai ba;
Duk wanda ya ce maka: ka je ka qona kanka,
to sai ka ce: masa: Saidai shi, ya je ya qona kansa; kuma lallai ba zai
aika hakan ba har abada; saboda yana
son ya jefa ka cikin wuta, ne,
ya kuma yaqi 'yan'uwanka musulmai, da
kai,
ya kuma kawar da amincin da mutane suke
cikinsa, da kai,
ya yaxa rashin nistuwa a cikin jama'a, da
kai,
ya kawo varna ko yaxa ta, da kai,
ya zubar da jinanen haram tare da kashe
musulmai da kai,
Sannan ya sanya ka, ka fice daga cikin jama'ar
musulmai, da kuma yin fito-na-fito da shugabanninsu, alhalin kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Duk Wanda ya fice daga biyayyar
shugaba, ya kuma vangare ga jama'ar musulmai, sai ya mutu to ya mutu irin
mutuwar jahiliyya. Kuma duk wanda ya yi yaqi qarqashin tutar da aka jahilta
yana yin fushi akan qabilanci, ko yana kira zuwa ga a raya qabilanci ko yana
taimakon qabilanci sai aka kashe shi to shima kisansa irin na jahiliyya ne.
kuma duk wanda ya fice daga al'ummata; yana ta dukan nagari da fajirin wannan
al'ummah da takobi, kuma baya nisantar muminanta, baya kuma cika alqawarin
kafiran da aka basu amana, to baya tare da ni, kuma nima bana tare da shi", Muslim
da Abu-dawud suka rawaito shi, daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه).
A wani hadisin "Na hore
ku da zama cikin jama'ar musulmai, Duk
kuma wanda ya fanxare to ya tafi cikin wuta".
Bayin Allah,,,
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati
ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka
yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Manzon Allah kuma (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda yayi mini salati guda
xaya to Allah zai yi masa salati guda goma ".
Sai ku yi salati da sallama ga shugaban
mutanen farko da na qarshe, kuma shugaban manzanni;
Ya Allah! Ka yi salati wa annabi Muhammadu
da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi salati wa annabi Ibrahima da
iyalan annabi Ibrahima, lallai kai a cikin talikai, Abun godiya ne, Mai girma.
Ya Allah! Ka yi albarka wa annabi
Muhammadu da iyalan annabi Muhammadu kamar yadda ka yi albarka wa annabi
Ibrahima da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai a cikin talikai, Abun godiya ne,
Mai girma.
Kuma ka yi musu sallama; tsiratarwa mai yawa.
Ya Allah! Ka yarda da sahabbai
gabaxaya, da kuma khalifofi shiryayyu, kuma shugabanni masu shiryarwa; Abubakar
da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabban annabinka gabaxaya, da waxanda
suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar qarshe,
Ya Allah! Ka yarda da mu tare da su,
da baiwarka, da rahamarka ya mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Ka xaukaka musulunci da
musulmai, ka kuma qasqantar da kafirci da kafirai,
Ya Allah ! ka kashe bidi'oi har zuwa
ranar tashi qiyama;
Ya Allah! Ka dusar da wutar bidi'a;
wacce ta ke cin karo da addininka, kuma take cin karo da shari'arka,
Ya Allah! Ka kashe bidi'oi, har zuwa
tashin qiyama, lallai kai mai iko ne akan komai.
Ya Allah!
Ya Allah!
Ya Allah!
Addu'oi;;;;;;;;;;;;;;;;
;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;
;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;