2015/05/19

آداب الأكل في الإسلام LADDUBAN CIN ABINCI

LADDUBAN CIN ABINCI A MUSULUNCI:

Lallai addinin musulunci ya zo mana da ladduba masu muhimmanci a lokacin da musulmi ya yi niyyar cin abinci, ko yake tsakiyar ci, ko bayan ya kammala, ga bayaninsu kamar haka:    
1. Faxin "bismillah" a lokacin fara cin abinci: Wannan kuma saboda hadisin Umar xan Abiy-salamah (RA) yace: Na kasance yaro qarqashin kulawar Manzon Allah –r- kuma hannuna ya kasance yana yawo a cikin akwashin abinci, sai yace:
"يَا غُلاَمُ! سَمِّ اللَّهَ، وَكُلْ بِيَمِينِكَ، وَكُلْ مِمَّا يَلِيك. فَمَا زَالَتْ تِلْكَ طِعْمَتِي بَعْد"([1]).
Ma'ana: (Ya kai yaro! Ka ambaci sunan Allah, ka ci da hannunka na dama, ka kuma ci daga abinda ke gabanka. –Jabir yace:- Daga wannan lokacin ban gushe ba; wannan ne irin cin abincina).
2.     Cin abinci da hannun dama: Wannan kuma sunna ne saboda hadisin da ya gabata.
  1. Mutum ya ci gabansa: Shima wannan sunna ne saboda hadisin da ya gabata. Sai dai idan mutum ya san cewa mutumin da suke cin abinci tare ba zai cutu ko kyamaci yawo da hannu a cikin kwaryar abincin ba, to a nan babu laifi idan ya ci daga ko-ina na kwano; saboda hadisin Anas (RA)  a qissar "telan nan da ya gayyaci Manzon Allah (r) i zuwa ga wani abinci" Anas yace:
"فَرَأَيْتُهُ –يعني النبي r- يَتَتَبَّعُ الدُّبَّاءَ مِنْ حَوَالَيِ القَصْعَة"([2]).
Ma'ana: (Sai na ganshi –yana nufin: Annabi r- yana bibiyan kabewa daga geffan kwano).
Ko kuma idan mutum ya kasance yana cin abincin ne shi kaxai; babu wani a tare da shi, ko kuma abincin akwai launukan abubuwan ci da dama; a irin wannan halin ya halatta ya ci abincin da ke gaban waninsa; matuqar dai bai cutar da wani da hakan ba.
  1. Cin abinci akan ledar cin abinci (Sufurah): Wannan kuma saboda hadisin Anas xan Malik (RA) yace:
"مَا أَكَلَ نَبِيُّ الله r عَلَى خِوَانٍ، وَلاَ فِي سُكُرُّجَةٍ، وَلاَ خُبِزَ لَهُ مُرَقَّقٌ. قال: فقُلْتُ لِقَتَادَةَ: فعَلاَمَ كانوا
يَأْكُلُونَ؟ قَالَ: عَلَى هذه السُّفَرِ"([3]).
Ma'ana: (Annabin Allah –r- bai tava cin abinci a kan "khiwaan([4])", ko a kan "Sukurrujah([5])" ba, haka kuma ba a tava yi masa al-khubuz mai laushi ba. Yace, sai nace wa Qatadah: To, a kan me suka kasance suke cin abinci? Sai yace: A kan waxannan "sufurori([6]); -ledodin cin abinci").
  1. Makruhi ne cin abinci a kishingixe: Wannan kuma saboda hadisin A'ishah (RA) tace:
"قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، كُلْ -جَعَلَنِي اللَّهُ فِدَاكَ- مُتَّكِئًا؛ فَإِنَّهُ أَهْوَنُ عَلَيْكَ، فَأَصْغَى بِرَأْسِهِ حَتَّى كَـادَ أَنْ
تُصِيبَ جَبْهَتُهُ الأَرْضَ، قَالَ: لا، بَلْ آكُلُ كَمَا يَأْكُلُ الْعَبْدُ، وَأَجْلِسُ كَمَا يَجْلِسُ الْعَبْد"([7]).
Ma'ana: (Nace: ya ma'aikin Allah! Ka ci abinci –Allah ya sanya ni na zamo fansarka- a halin kishingixa; saboda zai fiye maka sauqi, Sai manzon Allah –r-  ya karkata kansa har sai da goshinsa ya yi kusan tava qasa, sai yace: A'a! zan ci abinci ne kamar yadda bawa ke cin abinci, zan kuma zauna kamar yadda bawa ke zaunawa). Da kuma saboda hadisin Abu-juhaifah (RA) yace: Manzon Allah (r) yace:
"إِنِّي لا آكُلُ مُتَّكِئًا"([8]).
Ma'ana: (Lallai ni bana cin abinci a kishingixe).
  1. Mustahabbi ne hanuwa daga aibata abincin da mutum baya son cinsa: Wannan kuma saboda hadisin Abu-hurairah (RA) yace:
"مَا عَابَ رَسُولُ اللَّهِ r طَعَامًا قَطُّ، إِنِ اشْتَهَاهُ أَكَلَهُ، وَإِلا تَرَكَه"([9]).
Ma'ana: (Manzon Allah –r- bai tava aibanta abinci ba; idan ya yi sha'awarsa sai ya ci, in kuma bai yi ba, sai ya bari).
  1. Mustahabbi ne cin abinci daga geffan masaki, makruhi ne kuma cinsa daga tsakiyar kwarya: Wannan kuma saboda hadisin Ibnu-abbas (RA), daga Annabi (r) lallai shi an zo masa da masaki da aka sanya kwavavviyar gurasa (alkubuz) da nama mai suna (Sarid), Sai yace:
"كُلُوا مِنْ جَوَانِبِهَا، وَلا تَأْكُلُوا مِنْ وَسَطِهَا؛ فَإِنَّ الْبَرَكَةَ تَنْزِلُ فِي وَسَطِهَا"([10]).
Ma'ana: (Ku ci daga geffan masakin, kada ku ci daga tsakiyansa, saboda albarka tana sauka ne a tsakiyarsa).
  1. Mustahabbi ne cin abinci da yatsu guda uku, da kuma suxe yatsun bayan kammalawa: Wannan kuma saboda hadisin Ka'ab xan Malik (RA) yace:
"كَانَ النَّبِيُّ r يَأْكُلُ بِثَلاثَةِ أَصَابِعَ، وَلا يَمْسَحُ يَدَهُ حَتَّى يَلْعَقَهَا"([11]).
Ma'ana: (Annabi –r- ya kasance yana cin abinci da 'yan yatsunsa guda uku, baya kuma goge hannunsa har sai ya suxe su).
  1. Mustahabbi ne cinye abinda ya zuba ana tsakiyan cin abinci, ko wanda ya warwatsu: Wannan kuma saboda faxinsa (r):
"إِذَا سَقَطَتْ لُقْمَةُ أَحَدِكُمْ فَلْيُمِطْ عَنْهَا الأَذَى وَلْيَأْكُلْهَا، وَلا يَدَعْهَا لِلشَّيْطَان"([12]).
Ma'ana: (Idan lomar xayanku ta faxi to sai ya kaxe mata kura, sannan ya cinye ta, kada ya barta ga shexan).
  1. Mustahabbi ne suxe kwaryar da aka ci abinci, da kuma lashe yatsu: Wannan kuma saboda faxin Anas (RA) a cikin hadisin da ya gabata:
"وَأَمَرَنَا –يعني النبي r- أَنْ نَسْلُتَ الْقَصْعَة"([13]).
Ma'ana: (Kuma ya umurce mu –yana nufin Annabi r- da mu katse kwaryar abinci). Ma'ana: mu suxe ta, mu kuma bibiyi abinda ya rage a cikinta na abinci. A wata riwayar kuma aka ce: Annabi –r- ya umurce mu da mu suxe 'yan yatsu da kuma akwashi, yace:
"إِنَّكُمْ لا تَدْرُونَ فِي أَيِّه الْبَرَكَة"([14]).
Ma'ana: (Saboda lallai ku ba ku san a ina ne daga cikin abincinku albarkar ta ke ba!).
  1. Faxin "alhamdu lillah" a qarshen abinci: Saboda hadisin Abu-umamah (RA) yace: Manzon Allah (r) ya kasance idan aka xage akwashin abinci –bayan kammala cinsa- daga gaba-gare shi Sai yace:
"الْحَمْدُ لِلَّهِ حَمْدًا كَثِيرًا طَيِّبًا مُبَارَكًا فِيهِ, غَيْرَ مُوَدَّعٍ, وَلا مُسْتَغْنًى عَنْهُ رَبَّنَا"([15]).
Ma'ana: (Yabo mai yawa daddaxa mai albarka sun tabbata ga Allah, Allah Ubangijinmu ba a barin yi masa xa'a, ko kuma ace an wadata ga barinsa). Da kuma saboda faxinsa (r):
"إِنَّ اللهَ لَيَرْضَى عَنِ الْعَبْدِ أَنْ يَأْكُلَ الأَكْلَةَ فَيَحْمَدَهُ عَلَيْهَا، أَوْ يَشْرَبَ الشَّرْبَةَ فَيَحْمَدَهُ عَلَيْهَا"([16]).
Ma'ana: (Lallai Allah yana yarda da bawa, idan ya ci abinci ya gode masa akanta, ko ya sha abun sha ya gode masa akansa).




([1]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5376), da Muslim (lamba: 2022)
([2]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5379)
([3]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5386)
([4]) "Khiwaan": Teburi ne da ake cin abinci akansa, Kalmar asalinta ba larabci ba ce. Haka kuma ana kiran shunfuxin da ake cin abinci akansa da wannan suna. 
([5]) "Sukurrujah"; Masaki ne qarami da ake sanya miya kaxan don a ci a cikinsa. Itama wannan kalma ce ta "farisanci".
La'alla abinda ya sanya Manzon Allah (r) ya qi ya ci a cikin "khiwaan" saboda kasancewarta daga al'adan "ajamawa", da ke kasancewa a kan wani hali aiyananne.
Kuma la'alla wannan sababin shi ya hana shi ya ci a cikin masakin "sukurrujah".    
([6]) "Sufrah": Kamar leda ne da ake cin abinci akansa
([7]) Albagawiy a cikin littafin "Sharhus sunnah" ya ruwaito shi (11/286-287), da Ahmad a "Zuhdu" (5-6) kuma Shu'aibul Arna'ux ya inganta shi da "wani hadisi mursal da ya ke masa shaida", a cikin (Hashiyar sharhus sunnah)
([8]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5398)
([9]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5409), da Muslim (lamba: 2064)
([10]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5409), da Muslim (lamba: 2064)
([11]) Ahmad ya ruwaito shi (1/270), da At-tirmiziy (lamba: 1805), ya kuma ce: hadisi ne hasan ingantacce. Da Abu-dawud (lamba: 3772), da Ibnu-majah, (lamba: 3277), Albaniy ya inganta shi (Sahihu sunan Ibni-majah, lamba: 2650)
([12]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 2032)
([13]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 2305)
([14]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 2033)
([15]) Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 5459)
([16]) Muslim ya ruwaito shi (lamba: 2734).  

2015/05/11

AIYUKAN SHUGABANNI

MANYAN AIYUKAN SHUGABANNI GUDA GOMA

A littatafanmu na musulunci anyi bayanin aiyukan da suke kan shugaba, da kuma alhakin da ke rataya a wuyansa, Daga cikinsu akwai abinda ya zo cikin littafin "AL-AHKAM AS-SULXANIYYAH na malamin nan da ya rasu kusan shekaru dubu baya; mai suna: Abul hasan Aliyu bn Muhammadu Al-mawardiy (marigayi a shekarar hijira ta 450)" A inda yake cewa:
 "مهام الخليفة ومسئولياته": وَاَلَّذِي يَلْزَمُهُ مِنَ الْأُمُورِ الْعَامَّةِ عَشَرَةُ أَشْيَاءَ:
"AIYUKAN SHUGABA, DA ABUBUWAN DA SUKE RATAYA A WUYANSA: Lallai lamuran da suke wajaba akansa na gamammun aiyuka: Abubuwa ne guda goma", Sai yace: 
أَحَدُهَا: حِفْظُ الدِّينِ عَلَى أُصُولِهِ الْمُسْتَقِرَّةِ، وَمَا أَجْمَعَ عَلَيْهِ سَلَفُ الْأُمَّةِ، فَإِنْ نَجَمَ مُبْتَدِعٌ أَوْ زَاغَ ذُو شُبْهَةٍ عَنْهُ، أَوْضَحَ لَهُ الْحُجَّةَ، وَبَيَّنَ لَهُ الصَّوَابَ، وَأَخَذَهُ بِمَا يَلْزَمُهُ مِنَ الْحُقُوقِ وَالْحُدُودِ؛ لِيَكُونَ الدِّينُ مَحْرُوسًا مِنْ خَلَلٍ، وَالْأُمَّةُ مَمْنُوعَةً مِنْ زَلَلٍ.
Ma'ana: "NA XAYA: Kiyaye addinin mutane, akan ginshiqansa tabbatattu, da kuma abinda magabatan wannan al'ummar suka yi ittifaqi akansa –ijma'i-. Idan wani xan bidi'a ya vullo, ko kuma ma'abocin wata shubuha ya karkata ga barin miqaqqen addini to sai shugaba ya fitar masa da hujja a fili, ya kuma bayyana masa gaskiya. Sa'annan in ta kama sai ya kwato haqqoqin da suke wurinsa, ko ya zartar masa da haddin da ya cancanta, saboda a kiyaye wa mutane addininsu daga tasgaro, al'umma kuma a hane ta, kauce masa". Ya ci gaba da cewa: 
الثَّانِي: تَنْفِيذُ الْأَحْكَامِ بَيْنَ الْمُتَشَاجِرِينَ، وَقَطْعُ الْخِصَامِ بَيْنَ الْمُتَنَازِعِينَ حَتَّى تَعُمَّ النَّصَفَةُ، فَلَا يَتَعَدَّى ظَالِمٌ، وَلَا يَضْعُفُ مَظْلُومٌ.
"NA BIYU: Zartar da hukunce-hukunce tsakanin vangarori biyu da suke faxa, da yanke husumar da ta shiga tasakanin masu jayayya, har adalci ya game kowa-da-kowa, ta yadda mai zalunci ba zai wuce iyaka ba, Wanda kuma aka zalunta ba zai yi rauni (wajen neman haqqoqinsa) ba". Ya ci gaba da cewa:
الثَّالِثُ: حِمَايَةُ الْبَيْضَةِ وَالذَّبُّ عَنِ الْحَرِيمِ؛ لِيَتَصَرَّفَ النَّاسُ فِي الْمَعَايِشِ، وَيَنْتَشِرُوا فِي الْأَسْفَارِ آمِنِينَ مِنْ تَغْرِيرٍ بِنَفْسٍ أَوْ مَالٍ.
"NA UKU: Kiyaye iyaka, da kare abun da aka hana, domin mutane su samu sake cikin rayuwarsu, su kuma watsu cikin tafiye-tafiyensu da aminci, ba tare da an ruxe su cikin rayukansu, ko kuma a cikin dukiya ba". Ya ci gaba da cewa:
وَالرَّابِعُ: إقَامَةُ الْحُدُودِ؛ لِتُصَانَ مَحَارِمُ اللَّهِ تَعَالَى عَن الِانْتِهَاكِ، وَتُحْفَظَ حُقُوقُ عِبَادِهِ مِنْ إتْلَافٍ وَاسْتِهْلَاكٍ.
"NA HUXU: Tsayar da haddodi; domin a kare abubuwan da Allah ta'alah ya haramta daga keta alfarmarsu, a kuma kiyaye haqqoqin bayinsa daga lalata su, ko halaka su". Sannan yace:
وَالْخَامِسُ: تَحْصِينُ الثُّغُورِ بِالْعُدَّةِ الْمَانِعَةِ وَالْقُوَّةِ الدَّافِعَةِ؛ حَتَّى لَا تَظْفَرَ الْأَعْدَاءُ بِغِرَّةٍ يَنْتَهِكُونَ فِيهَا مُحَرَّمًا، أَوْ يَسْفِكُونَ فِيهَا لِمُسْلِمٍ أَوْ مُعَاهَدٍ دَمًا.
"NA BIYAR: Sanya garkuwa a dukkan kafafe ko iyakoki da nau'ukan tsaro da za su hana shigowar maqiya ko su tunkuxe su bayan shigowarsu, Wannan kuma don kada maqiyan a cikin gafalar mutane su samu su kekketa alfarmar abubuwa na haram, ko kuma su zubar da jinin musulmi ko kafirin aman". ya ci gaba da cewa:
وَالسَّادِسُ: جِهَادُ مَنْ عَانَدَ الْإِسْلَامَ بَعْدَ الدَّعْوَةِ حَتَّى يُسْلِمَ أَوْ يَدْخُلَ فِي الذِّمَّةِ؛ لِيُقَامَ بِحَقِّ اللَّهِ تَعَالَى فِي إظْهَارِهِ عَلَى الدِّينِ كُلِّهِ.
"NA SHIDA: Yaqar mutumin da ya yi taurin kai ga musulunci bayan an kira shi zuwa gare shi har sai ya musulunta ko kuma ya shiga cikin kafiran amana, Wannan kuma don a tsayar da haqqin Allah ta'alah, na cewa zai xaukaka musulunci akan addinai gabaxayansu". Ya ci gaba da cewa:
وَالسَّابِعُ: جِبَايَةُ الْفَيْءِ وَالصَّدَقَاتِ عَلَى مَا أَوْجَبَهُ الشَّرْعُ نَصًّا وَاجْتِهَادًا، مِنْ غَيْرِ خَوْفٍ وَلَا عَسْفٍ.
"NA BAKWAI: Tattara ganima da zakka, kamar yadda shari'a ta wajabta, qarara, ko da ijtihadi, ba tare da tsoro ba, ko zalunci". Ya ci gaba da cewa:
وَالثَّامِنُ: تَقْدِيرُ الْعَطَايَا وَمَا يَسْتَحِقُّ فِي بَيْتِ الْمَالِ مِنْ غَيْرِ سَرَفٍ وَلَا تَقْتِيرٍ، وَدَفْعُهُ فِي وَقْتٍ؛ لَا تَقْدِيمَ فِيهِ وَلَا تَأْخِيرَ.
"NA TAKWAS: Yanka gwargwadon kyautuka, da duk abin da aka cancanta na dukiya daga baitul mali, ba tare da wuce iyaka ko mammaqo ba, da bada shi ga waxanda suka cancance shi a cikin lokacinsa; babu gaggawa, kuma babu jinkiri". Ya ci gaba da cewa:
التَّاسِعُ: اسْتِكْفَاءُ الْأُمَنَاءِ وَتَقْلِيدُ النُّصَحَاءِ؛ فِيمَا يُفَوَّضُ إلَيْهِمْ مِنَ الْأَعْمَالِ، وَيَكِلُهُ إلَيْهِمْ مِنَ الْأَمْوَالِ؛ لِتَكُونَ الْأَعْمَالُ بِالْكَفَاءَةِ مَضْبُوطَةً، وَالْأَمْوَالُ بِالْأُمَنَاءِ مَحْفُوظَةً.
"NA TARA: Neman ma'aikatan da suka dace kuma aminai, da rataya aiyuka ga waxanda za su kyautata shi, ga duk aiyukan da zai xora ga wassu, ko ya wakilci da zai bayar na dukiya, Wannan kuma domin aiyuka su zamto an rataya su ga waxanda za su iya aikata su, dukiya kuma ga aminan da za su iya kiyaye su". Ya ci gaba da cewa:
الْعَاشِرُ: أَنْ يُبَاشِرَ بِنَفْسِهِ مُشَارَفَةَ الْأُمُورِ، وَتَصَفُّحَ الْأَحْوَالِ؛ لِيَنْهَضَ بِسِيَاسَةِ الْأُمَّةِ، وَحِرَاسَةِ الْمِلَّةِ، وَلَا يُعَوِّلُ عَلَى التَّفْوِيضِ تَشَاغُلًا بِلَذَّةٍ أَوْ عِبَادَةٍ، فَقَدْ يَخُونُ الْأَمِينُ وَيَغُشُّ النَّاصِحُ"
"NA GOMA: Ya rinqa dubiyar dukkan lamura da kansa, yana bincika halayen da lamura suke ciki, domin ya tsayu da kansa wajen jagorantar al'umma, da kare musu addini. Kada kuma ya yarda da wakiltawa ko-yaushe, saboda neman hutun jin daxi, ko shagaltuwa da wata ibada; saboda ta yiwu wanda aka aminta das hi ya yi ha'inci, ko wanda aka san shi da aiki mai kyau wata rana ya yi algus".
          Daga qarshe muna yin fatan alkhairi ga shugabanni, muna kuma roqon Allah ya taimake su kan sauke dukkan nauyin da yarata akansu, amin!. Salati da sallama su qara tabbata ga manzon Allah annabinmu Muhammadu da da iyalansa da sahabbansa gabaxaya.

INUWAR ALLAH TA'ALAH

WAXANDA ALLAH ZAI SANYA SU A QARQASHIN INUWARSA RANAR DA BABU WATA SAI TASA

Daga Abu-hurairah (Allah ta'alah ya yarda da shi) daga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) cewa:
"سَبْعَةٌ يُظِلُّهُمُ اللهُ فِي ظِلِّهِ يَوْمَ لَا ظِلَّ إِلَّا ظِلُّهُ: الْإِمَامُ الْعَادِلُ، وَشَابٌّ نَشَأَ بِعِبَادَةِ اللهِ، وَرَجُلٌ قَلْبُهُ مُعَلَّقٌ فِي الْمَسَاجِدِ، وَرَجُلَانِ تَحَابَّا فِي اللهِ اجْتَمَعَا عَلَيْهِ وَتَفَرَّقَا عَلَيْهِ، وَرَجُلٌ دَعَتْهُ امْرَأَةٌ ذَاتُ مَنْصِبٍ وَجَمَالٍ، فَقَالَ: إِنِّي أَخَافُ اللهَ، وَرَجُلٌ تَصَدَّقَ بِصَدَقَةٍ فَأَخْفَاهَا حَتَّى لاَ تَعْلَمَ شِمَالُهُ مَا تُنْفِقُ يَمِينُهُ، وَرَجُلٌ ذَكَرَ اللهَ خَالِيًا فَفَاضَتْ عَيْنَاهُ".
Ma'ana: "Vangarori guda bakwai Allah zai sanya su a inuwarsa ranar da babu wata inuwa sai tasa; Shugaba adali, da Saurayin da ya rayu cikin bautar Allah, da Mutumin zuciyarsa a rataye ta ke da masallatai, da Mutane biyu da suka yi soyayya don Allah, suka haxu akan haka, suka kuma rabu akan haka, da Mutumin da mace ma'abociya matsayi da kyau ta kira shi don yin lalata sai yace: Lallai ni ina tsoron Allah, da Mutumin da ya bada wata sadaka; ya voye ta; hatta hagunsa bai san abinda damanya ya bayar ba, da Mutumin da ya ambaci Allah a keve sai idanunsa guda biyu suka yi hawaye". [Littafin sahihul Bukhariy, lamba: 660, da Sahihu Muslim, lamba: 1031].
Allah ta'alah kawai muke roqo da ya sanya mu daga cikin waxanda a ranar tashin alkiyamah zasu rabauta da kasancewa qarqashin inuwarSa, ranar da babu wata inuwa sai tasa. Ya kuma taimake mu wajen aiki da wannan hadisi, ta kowace fiska. Amin!

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...