HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 29/RABIYYUL AWWAL/1440H
daidai da 7/DISEMBA/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH HUSAIN BN ABDUL'AZIZ ALUS-SHEIKH
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
TSARKAKE ZUCIYA
(سلامة الصدر)
Shehin Malami wato: Husain
bn Abdu'aziz AlusSheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TSARKAKE ZUCIYA, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah,
Mai hakuri Masani,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Ubangijin
Al'arshi Mai girma,
Kuma ina shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa wanda aka turo shi da kowace dabi'a Mai
karamci, Ya Allah ka yi salati da sallama da albarka a gare shi da iyalansa da
sahabbansa da wadanda suka bi su, kuma suka yi koyi da riko da addininsa
mikakke.
Ya ku Musulmai
Ina muku wasiyya da ni
kaina da takawar Allah Mabuwayi da daukaka, da kuma yin da'a a gare shi a cikin
tsananin rayuwa da lokacin walwala, domin "Wanda
ya yi da'a ga Allah da Manzonsa hakika ya rabautu da rabo mai girma",
[Ahzab: ].
Ya ku Musulmai
A zamanin da
lamarin son Duniya ya bayyana cikin sifofi da fiskoki masu yawa, Musulmi yana
bukatar tunatarwa kan abinda zai rika zaburar da shi kan son Mutane, da basu
alkhairi da yin kyauta a gare su, da kamewa daga cutar da su, ko yin sharri ga
Musulmai, lallai hakan zai kasance ne, ta hanyar riko da hali ko dabi'ar
TSARKAKE ZUCIYA (سلامة الصدر) wanda Musulmi ke rayuwa da shi, cikin jin dadi, yana abin
yarda.
Lallai tsarkake
zuciya yana cikin managartun dabi'u, da halaye mafi daukaka, wadanda Musulmi
yake riskar lada masu tarin yawa da su, da kuma samun kyakkyawan makoma, Allah
Ta'alah ya ce:
"A ranar da dukiya bata amfani, kuma diya basu yi * face wanda ya je
wa Allah da zuciya mai tsarki" [Shu'ara'i: 87-88].
Kuma yana daga ALAMOMIN
TSARKIN ZUCIYA bayan imani da takawa da tauhidi da yakini, zuciyar ta tsarkaka
daga kulli, hassada da kyashi ga Musulmai, sai Musulmi ya rayu tare da
'yan'uwansa Musulmai cikin tsarkin zuciya da dadin rai, da kyakkyawan nufi, ta
yadda ba zai rike su da kyashi ko kiyayya ba, kuma ba zai boye kulli akansu ko
algus ko makirci ba, A'a, Musulmi ya kan rayu da 'yan'uwansa ne da zuciyar da
take yada alkhairori da kyautatawa, da dabi'u masu kyau, cikin tsaftar zuciya
da tsarkinta, ta yadda shi yana cikin hutu a ransa, sauran Mutane kuma, su samu kubuta daga sharrinsa.
Mutane basu samun bala'i da
sharri daga wurinsa
Kuma basu dandanar cutarwa
da wahala daga gare shi
Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: " 'Dayanku baya
zama Mumini, face ya so wa 'Dan'uwansa abinda yake so ga kansa".
'Yan'uwa, a cikin
Musulunci!!!
Yana daga ni'imomin da ake
gaggautar da bayar da su tun a wannan rayuwar, wanda kuma shine Aljannar
Duniya, kuma da shi rayuwa take yin dadi, Shine Bawa, ya yi kwadayin sifantuwa
da ni'imar tsarkin zuciya, ga dukkan wadanda suke rayuwa da shi, ko suke hulda,
dama sauran Mutane, Allah ya fada a inda yake sifanta 'yan Aljannah: "Kuma muka fitar da
abinda ke cikin kirazansu na kiyayya" [A'araf: 43].
Ibnu-Adiyyah –رحمه الله- ya fada a tafsirin wannan ayar: "Wannan kuma, saboda
wanda ke dauke da kiyayya yana azabtuwa da ita, kuma babu azaba a gidan
Aljannah".
Kuma ya zo cikin muhimman
addu'oin Ma'abuta imani: "Da wadanda suka zo a bayansu, suna cewa: Ya Ubangijinmu ka gafarta
mana, kuma ka yi gafara ga 'yan'uwanmu da suka rigaye mu da imani, kuma kada a
zukatanmu ka sanya kyashi ga wadanda suka yi imani, Ya Ubangijinmu lallai kai
Mai tsananin tausayi ne, Mai jinkai", [Hashr: 10].
'Yan'uwa,
a cikin Musulunci!!!
Yana
daga cikin ayyukan da suka fi falala, Tsarkake zuciya daga dukkan nau'ukan
adawa da kiyayya gaba dayansu, An ce wa Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-
wanene Mutumin da yafi falala? Sai ya ce: "Duk mai tsarkin zuciya, mai yawan
gaskiyar harshe", Sai suka ce: Mai gaskiya a harshe, mun san shi, Wanene
kuma: makhmumul kalb, Sai ya ce: "Shine tsaftatacce, Mai
takawa (النقي التقي), wanda bashi da zunubi, kuma baya zalunci, kuma bashi da
kyashi, kuma baya hassada", Ibnu-Majah ya ruwaito shi, kuma
Almunziriy ya inganta isnadinsa, da Albusiyriy, a cikin littafin Zawa'id, da
Irakiy, kuma Albaniy ya inganta shi.
Kuma
hakika Magabatan wannan al'ummar sun riski wannan lamari, kuma wannan shine Zaid
bn Aslam, yana shiga wurin Abu-Dujanah, alhalin bashi da lafiya, amma sai ga
fiskarsa tana ta sheki, sai ya ce da shi: "Me yasa fiskarka take sheki? Sai ya ce: "Babu aikin da na aikata wanda
nafi aminta da shi, fiye da guda biyu, Amma na farkonsu shi ne lallai na
kasance bana magana sai ga abinda ya shafe ni. Shi kuma na biyun, Zuciyata ta
kasance ga dukkan Musulmai mai tsarki".
Kuma Fudail
bn Iyadh –رحمه الله- ya
ce: "Wanda a cikinmu ya riski falala, bai riske ta saboda yawaita
nafilfilin sallah ko azumi ba, A'a, a wurinmu ya riski hakan ne, saboda fadin rai,
da tsarkin zuciya, da kuma nasiha ga Al'ummah".
'Yan'uwa,
a cikin Musulunci!!!
Daga
cikin SABUBAN DA SUKE TAIMAKO, KAN SAMUN TSARKIN ZUCIYA, akwai Yin ikhlasi ko
tsarkake niyya ga Allah Mabuwayi da daukaka,
da
yarda da kaddara, da kuma dukkan abinda Allah Mabuwayi da daukaka ya rubuta shi
ga Bawa a wannan rayuwar,
da
lazimtar biyayya ga Allah Mabuwayi da daukaka,
da
yawaita tilawar littafinsa Subhanah,
tare da
yin kokari wajen yakar rai daga munanan halaye ko cutuka, kamar algus, da
kulli, da hassada,
tare da
tuna irin abinda munanan halayen suke janyowa ga Mutum na sharri mai tsanani, a
Duniya da Lahira.
Sa'annan
sai Bawa ya yi kokari kan Allah ya azurta shi da zuciya tsarkakakkiya da harshe
mai gaskiya,
Da kuma
aikata dukkan abinda zai janyo kauna da soyayya, ya rika tunkude kyashi da
kiyayya, kamar yada sallama,
da kuma
Mutum ya rika barin abinda bai shafe shi ba, daga lamuran halittu,
da
kokarin bayar da kyauta, saboda tana janyo soyayya, kuma tana tunkude kiyayya,
da kuma
yin addu'a ga Musulmai gaba daya,
da
yafiya ga wanda ya munana,
da lamarin
kyautatawa, da dukkan nau'ukansa,
da
kokarin shigar da farin ciki ga zukatan Musulmai,
da yin
farin ciki a lokacin samuwar abinda ke faranta musu,
da kuma
tarayya da su cikin abinda rarrashi ne, kuma hakurtarwa, a lokacin bacin ransu
da bakin ciki.
Kuma
Bawa ya yaki Shedan, domin yana da aniyar cuccusa dukkan abinda suke tunzura
zukata, suke lalata su, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka ce wa Bayina: su fadi
kalma wanda take mafi kyau, lallai ne Shedan yana sanya barna a tsakaninku,
Lallai ne Shaidan ya kasance ga Mutum, makiyi bayyananne",
[Isra'i: 53].
Kuma ya
zo cikin abinda Muslim ya ruwaito, lallai Annabi صلى الله عليه وسلم ya
ce: "Lallai Shedan ya debe tsammanin cewa Masallata za su bauta masa a
yankin tsibirin Larabawa, saidai zai yi ta sanya husuma a tsakaninsu".
Kuma
lallai yana daga abinda Bawa zai samu tsarkin zuciya da su, Nisantar jayayya da
husuma akan mas'aloli da kuma lamuran da suke aukuwa na yau-da-kullum, saboda
hakan yana tayar da bacin rai da kiyayya, kuma yana rura wutar gaba, kuma yana
haifar da sabani.
Saboda ana
yabon jayayya ko tattaunawa ne kawai idan aka yi ta domin tabbatar da wata
gaskiya ta addini, daga Malami mai tsarkin zuciya da ikhlasi da gaskiya, wanda
ya sifantu da dukkan sharudda da sifofi da ababen lura a lokacin tattaunawar ko
mujadala, kewaye da ladabi mai yawa da halaye managarta. Allah Mabuwayi da
daukaka y ace: "Kuma ku fadi magana mai dadi ga Mutane"
[Bakara: 83].
Ina fadan
wannan maganar, kuma ina neman gafara Allah a ni da ku da sauran Musulmai daga
dukkan zunubai, sai ku nemi gafararSa, lallai shi Mai yawan gafara ne Mai
jin-kai.
,,, ,,,
,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kamar yadda ya dace, da girman
fiskarsa da mulkinsa mai girma,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi
kadai yake bashi da abokin tarayya, ina mai girmama sha'aninsa.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, yana kira zuwa ga
samun yardarsa, Ya Allah ka yi salati da sallama da albarka a gare shi da kuma
iyalansa da sahabbansa.
Bayan haka … !!
Ya ku Musulmai
Lallai tsarkin zuciya kofa
ce mai girma zuwa ga samun tabbatacciyar ni'ima madawwamiya, Wani daga cikin
Magabata ya ce: "Asalin addini shine tsantseni da kamewa, kuma ibadar da ta fi girman
falala ita ce, yin fama cikin dare (salloli), kuma gajeruwar hanyar da take
kaiwa ga Aljannah ita ce, tsarkake zuciya".
Sai ku lazimci ibadar
tsarkake zuciya, da tsaftace rai, da gyaran niyya, kuma saboda haka ne, Annabi
–صلى
الله عليه وسلم- ya ke kwadayin abinda zai tabbatar ko dasa wannan ginshiki (a
cikin rayuwa) ta Mutum, sannan ya tunkude dukkan cutukan da zasu iya bijirowa a
gare shi, a inda Annabin –صلى الله عليه وسلم – ya ce: "Kada ku yi
kiyayya, kada ku yi hassada, kada ku juya baya, kuma ku kasance –Ya ku bayin
Allah- 'yan'uwan juma. Kuma baya halatta Musulmi ya kauracewa dan'uwansa fiye
da kwanaki uku" Muslim ya ruwaito
shi.
Sai ku kasance –Ya
ku bayin Allah- 'yan'uwan juna masu soyayya, kuma akan takawa ku kasance masu nuna
kauna, kuma akan ayyukan da'a masu yin wasici ga juna.
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa
Annabi Muhammadu, ……………………………
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment