HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 14/RABIYYUS SANIY/1440H
daidai da 21/DISEMBA/ 2018M
LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. SALAH DAN MUHMMADU ALBUDAIR
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
KYAUTATA LADABI
(حسن الأدب)
Shehin Malami wato: Salah bn Muhammadu Albudi–Allah ya
kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken:LADABI,Wanda kuma
a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya
tabbata ga Allah wanda ya tarbiyantar da mu da Alkur'ani da Sunnah da mafi kyan
ladabi, kuma ya saukar da mu ga bazarar falalarSa mai yabanya, kuma ya ajiye mu
cikin yalwar falalarSa mai fadi.
Kuma ina
shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin
tarayya, zuwa gare shi nake kira, kuma a gare shi nake mayar da lamura.
Kuma ina
shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa,
an turo shi domin ya cika kyawawan halayya, kuma sune matsayi mai girma.
Allah, ya yi
dadin salati da sallama a gare shi da iyalansa da sahabbansa, salatin da zamu
samu cikakken lada da shi, da mafi girman rabo.
Bayan
haka:
Ya
ku Musulmai
Ku
ji tsoron Allah; domin mai takawa ya kan samu babban rabo, kuma mabarnaci
shakiyyi ya yi hasara, "Ya
ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah iyakar tsoronsa, kuma kada ku mutu
face kuna Musulmai" [Ali-imraana: 102].
Ya
ku Musulmai
Samun
daukakar Musulmi shine ladabinsa, kuma ladabi madaukaki yana wadatarwa daga
matsayi madaukaki da danganta madaukaki,
saboda samun daukaka yana cikin himmomi madaukaka, ba daga dangantaka ko kasussuwan
(iyaye da kakanni) da suka rududduge ba.
BAI
CUTAR DA WANDA YA TATTALI LADABI DA HANKALI BA,
KASANTUWAR
BAI FITO DAGA KABILAR ABDU-MANAFI BA
Falala
cikakkiya itace ladabi ya kasance tabbatacce a cikin iyaye, sai kuma ya samu
gindin zama a cikin 'ya'yansu da jikoki;
SUN
KAWATA TSOFONSU DA KYAKKYAWAN NA ZAMANINSU,
DA
KUMA HALAYEN GIRMA, DA KYAWAWAN DABI'U
MADALLA
DA MUTANEN DA KAI NE RESHEN TUSHENSU,
KUMA
MADALLA DA KAI, DOMIN DAGA ASALINSU RESHENKA YA SAMU
LADABI
shine yin abin yabo; cikin zance da aiki.
Kuma
Ladabi shine, aikata ababe masu falala, da barin masu muni.
Kuma
shine, girmama na sama da kai, da tausasawa na kasa.
Kuma
Ladabi shine, riko da kyawawan dabi'u, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma
lallai kai kana kan wasu halaye masu girma" [Kalam: 4].
Adiyyatul
Aufiy ya ce: "Wato, lallai kai kana kan ladabi mai girma".
Ladabi
shine takawar Allah Ta'alah, da yin da'a a gare shi, da nisantar saba masa.
NA YI TARBIYYA
GA KAINA, SAIDAI BAN SAMA MATA
LADABI BA,
IDAN BA A CIKIN TAKAWAR ALLAH BA.
Mujahid
–Allah ya yi rahama a gare shi- ya ce, alhalin yana tafsirin: "Ku
kare kanku da iyalanku daga wata wuta" [Tahrim: 6], wato: "Ku
yi wasiyya ga kanku da iyalanku da takawar Allah, kuma ku ladabtar da su".
YIN
TARBIYYA A SANNU-SANNU, HAKIKA YANA AMFANAR KANANAN YARA
SAIDAI A BAYAN
GIRMA, YIN TARBIYYA (A GALIBI) BAYA WANI AMFANI
SABODA RESSAN
DANYEN BISHIYA IDAN KA NEMI DAIDAITA SU, SUKAN MIKE
AMMA BASU
YIN TAUSHI IDAN KA NEMI DAIDAITA SU BAYAN SUN ZAMA ITACE (BUSASSHE)
KYAU BA
SHINE, TUFAFIN DA SUKE KAWATA MU BA,
LALLAI
KYAU (NA HAKIKA) SHINE KYAN ILIMI DA LADABI
Kuma an yi
wa ladabi sunan ladabi ne, saboda yana ladabtar da Mutane ya dora su akan
abubuwan yabo, ya kuma hana su aikata munanan ayyuka.
Ladabi
shine, kyautata magana, da kyan zance, da dadinsa, da kyautata shirya zance, da
kwarewa cikin mu'amala, da kula da kyan yanayi (na tufafi), da gyaran zuciya da
gangar jiki.
Ladabi (wato
أدب) ba kawai shine
fasaha da balaga da hardace ilmuka da wakokun Labarawa ba, Saidai hakikanin
ladabi shine sifantuwa da kyakkyawan halaye.
Da yin
farin ciki da abinda Allah ya yi ga wani na ni'ima, da nisantar hassada, da
kubuta daga dabi'ar kyashi.
Duk wanda
hankalinsa ya cika, ladabinsa da tarbiyyansa suka zama kawa a gare shi, sai
maganarsa tayi karanci, sai shirunsa ya yawaita, lafazinsa ya yi kyau,
hakurinsa ya bayyana.
SAI KA
KASANCE MAI KARAMCI, MAI HAKURI, MAI HANKALI, FADAKAKKE,
MAI
TSAFTAR HALAYE, DAGA WAUTA, DA FUSHI
KA KIYAYE
HARSHENKA, DAGA ZAMBO, DA WAUTA,
DA KUMA
ABOTAR SAKARKARU, KA NISANCI KARYA.
Ana cewa:
Dabi'u guda uku, Mutum a tare da su baya zama bako: Nisantar wadanda ake zargi,
da kyakkyawan ladabi (tarbiyya), da nisantar cutarwa.
YANA
KAWATA BAKO A YAYIN BAKUNCINSA
DABI'U
GUDA UKU; DAGA CIKINSU AKWAI KYAUTATA LADABI
NA
BIYUNSU: SHINE KYAUTATA DABI'ARSA,
NA UKUNSU
KUMA, NISANTAR WURAREN ZARGI
IbnulKayyim
–رحمه الله- ya ce: "Ladabin Mutum shine
tambarin samun sa'idarsa da nasararsa, Shi kuma karancin ladabinsa shine
tambarin tabewarsa da halakarsa, domin ba a iya janyo alherin Duniya da lahira
da sai da ladabi. Kuma ba a janyo talaucin Duniya da lahira sai da dabi'ar
karanta ladabi. Ka duba lamarin ladabi ga iyaye biyu;
yadda ya tseratar da Ma'abucinsa daga zaman kogo a lokacin da dutse ya sauko
akansu, kuma ka yi dubi ga ladabin Abubakar siddik -Allah ya yarda da shi- ga
Annabi -sallal Lahu alaihi wa sallama- a lamarin sallah, wato lokacin da ya ki
ya shiga gabansa, kuma ya ce: BAI DACE GA IBNU-ABIY KUHAFAT, YA SHIGA GABAN
MANZON ALLAH -SAW-, yadda hakan ya gadar masa da samun matsayinsa da jagorantar
al'umma a bayansa". Maganarsa ta kare.
LALLAI NE NI,
DABI'U MASU KARAMCI SUNA FARANTA MIN,
IRIN FARIN
CIKIN BAKO A LOKACIN DA YA KOMO, YA SADU DA MASOYANSA
KUMA YIN
TUNANI KAN MUTUNTAKA DA KYAUTA A CIKIN JERIN KYAWAWAN HALI
YANA
JIJJIGA NI, JIJJIGAWAR MUTUMIN DA KE CIKE DA SHAUKI
IDAN AKA
AZURTAKA DA DABI'A ABAR YABO,
HAKIKA MAI
RABIYAR ARZIKI, SHINE YA ZABE KA
MUTANE,
WANNAN RABONSA DUKIYA, WANNAN KUMA
ILIMI, WANNAN
KUMA KYAWAWAN DABI'U
SHI ILIMI,
IDAN DABI'UN DA ZASU DAUKAKA SHI BASU DABAIBAYE SHI BA,
SAI YA
KASANCE ABIN HAWAN ZILLEWA,
KADA KA YI
ZATON ILIMI ZAI YI AMFANI, SHI KADAI
MATUKAR
MA'ABUCINSA BAI YI KAWA DA DABI'U BA
SAU NAWA
MAI ILIMI YA SHUMFUDA IGIYOYIN ILIMI
DOMIN CIN
MUTUNCIN MUTANE, DA YANKE ZUMUNTA, DA RARRABA KAI!
SHI KUMA
MALAMIN WASU MUTANE YA RIKA KAFA FIKIHUNSA
DOMIN
MAKIRCI, KO YA ZAMA MAI NEMAN HALATTA SHIKA!
UWA KUMA,
MAKARANTA CE, IDAN KA TATTALE TA,
TO, KA YI
TATTALIN AL'UMMA, MAI KYAWUN HALAYE!
UWA
DAUSAYI CE, IDAN AKA BITA DA BAYIN RUWA,
SAI
DAUSAYIN YA BADA YABANYA DA CIKAKKEN GANYE
UWA ITACE
MALAMAR MALAMAN DA FALALARSU
TA CIKE
SARARIN SAMANIYAR DUNIYA
KU YI
TARBIYYA TAGARI GA 'YA'YANKU MATA
DOMIN
NAGARTA SHINE MAFI ALHERIN ABIN RIKEWA
YANA WAJABA 'YA'YANKU MATA SUSAN
HASKEN
SHIRIYA, KUMA SU SAN KUNYA
Kuma
hakika, littatafan sihah da sunan da musannafaat, sun bada kulawa wajen tattaro
hadisai, kuma babu wani littafi daga cikin wadannan littatafan masu girma
wadanda ake daukansu a matsayin madogarar ma'abuta Musulunci, face mawallafinsa
ya ware littafin ladabi, ko babi-babi akan ladibi, Duba littafin ladabi a cikin
sahihul Bukhariy, da littafin ladabi a cikin sahihu Muslim, da littafin ladabi a
cikin sunan na Abu-dawuda, da littafin ladabi a cikin sunan na Tirmiziy, domin
ka yi mamakin girman ladabi a cikin addinin Musulunci, da matsayinsa a cikin
sunna da shari'a.
Kuma yana
daga manyan sunnoni a babin ladduba da halayya: Abinda aka ruwaito daga
Abu-Umamah Albahiliy -رضي الله عنه-, ya
ce: Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai ni na lamunce
da bayar da gida a gabar Aljannah ga wanda ya bar jayayya, koda yana da
gaskiya. Da wani gidan a tsakiyar Aljannah ga wanda ya bar karya koda a cikin
wasa ne. Da wani gidan a kololuwar Aljannah ga wanda ya kyautata halayensa",
Abu-dawud ya ruwaito shi.
Abdullahi
bn Almubarak ya ce: "Mu, lallai mun fi bukatar
kadan daga ladabi fiye da ilimi mai yawa".
Imamu Maliku ya ce: "Mahaifiyata
ta kasance tana daura min rawani, sai ta ce: Ka tafi ga malam Rabiy'ah, ka koyi
ladabinsa gabanin koyan iliminsa".
Abdullahi dan Wahaf ya ce: "Abinda
muka koya na ladabin Maliku yafi abinda muka koya na iliminsa".
Isma'il dan Ulayyah ya ce: "Lallai
a majalisar Imamu Ahmad Mutane dubu biyar suna taruwa, ko hakan da doriya, kuma
kamar dari biyar, suna rubuta iliminsa, sauran kuma suna koyan kyakkyawan
ladabinsa, da halayya".
Kuma Alkhadib Albagdadiy -رحمه الله- ya ce: "Wajibi
shine daliban hadisi su kasance sun fi sauran Mutane cikar ladabi, da tsananin
tawali'u, kuma su fi su tsantseni da riko da addini, kuma sufi karancin wauta
da fushi, wannan kuma saboda hadisan da suka kunshi kyawawan halayyar Manzon
Allah -صلى الله عليه وسلم- ko-yaushe sukan kwankwasa
kunnuwansa, da batun laddubansa, da tarihin magabatan kwarai, daga iyalan
gidansa da sahabbansa, da hanyoyin Maluman hadisi, da labarun falalar Mutanen
baya, sai dalibin hadisi ya yi aiki da abinda yafi kyau yafi dacewa, ya kuma
kauce wa munanan hanyoyi da ayyuka".
Ina
fadar abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah; sai ku nemi gafararSa,
lallai ne shi ya kasance ga masu komawa
gare shi, Mai yawan gafara.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUDUBA
TA BIYU
Yabo
ya tabbata ga Allah wanda ya bada mafaka ga wanda ya nemi fakewa ga
tausasawarSa,
Kuma
ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ya bada lafiya cikin
ni'imtarwarsa, ga wanda ya debe tsammanin samun waraka daga cutukansa.
Kuma
na shaida lallai shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, wanda
ya bi shi ya shiryatu ya dau hanya, wanda kuma ya saba masa ya bata ya bar
turba,
Allah ya yi dadin salati a gare shi
da iyalansa da sahabbansa, salati mai
ninkuwa, da sallama mai wanzuwa,
Bayan
haka
Ya
ku Musulmai
Ku ji
tsoron Allah kuma ku kiyaye shi, kuma ku yi da'a a gare shi kada ku saba masa,
"Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah kuma ku
kasance tare da masu hakuri" [Tauba: ].
Ya
ku Musulmai
Ku yi godiyar
ni'imar Allah akanku, Lallai ya turo muku da iska masu albishir, da girgije
masu nauyi, masu barin ruwan sama, girgije bayan girgije, da suka sassauka a cikin
kwari masu jin kishi, da saharori masu wahalar samun ruwa, da kuramen duwatsu
daskararru, wanda tuni rashin ruwan ya jigata su, ,,, sai suka jijjika da ruwan
sama, sai gashi kasarku -da falalar
Allah- tayi ciyawa, sai dausayinku ya zama abin kaye da saukan wannan ruwan,
duwatsunku suka yi kore da rahamar Allah, a cikin shekararku da ta cika da
yabanya, da wani yanayi mai kyau mai kayatarwa, wanda yake nuni kan ikon Allah
da hikimarSa da rahamarSa da yalwar falalarSa, da arzikinSa da kyautatawarSa.
HAR
LOKACIN DA DAUSAYI YA RUNGUME KASA
SAI
CIYAWAR FARKO-FARKO MASU KARFAFAR JUNA SUKA FUFFUDO
AKAN KASA
DAYA, SAI SUKA ZAMTO KAMARSU DAYA TA FISKAR KYAWU
YAYIN DA
TA FISKAR LAUNUKA BASU ZAMTO ABU DAYA BA
IDANUNKA
NA NUNA MAKA IDANIYAR RUWA
MASU KYAU
DA DADI, WANDA SUKA FI IDANIYAR YANKIN JA'AZIRI
BA ABINDA
YAFI KYAN GANI, IN KA ZIYARCE SU,
KO KA GA
HAKIKANINSU, NA KYAN DAUSAYI KORE
IDAN KA JE
MUSU, SAI SU BAKA GANI MAFI KYAWU, IDAN KUMA BAKA JE BA,
SAI YA
ZIYARCE KA CIKIN DADDADAR ISKAR DA TAKE ZUWA DA SAFIYA
Sai ku
buda idanuwanku cikin kyawun halittar Allah Ta'alah, tare da kula da ladduban
fita yawon buda ido, kuma kada ku bata, ko ku sanya najasa a wuraren da Mutane
suka rike su a matsayin inuwowin zama, da kailula, haka wuri mai dausayi da
ciyawoyi, ko karkashin bishiya mai 'ya'ya, ko wurin diban ruwa, ko hanyar da
ake binta da kafa, ko da dabbobi, ko da motoci. saboda an ruwaito daga
Abu-hurairah -رضي الله عنه-,
lallai Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ku kiyayi wuraren tsinuwa guda biyu, Sai suka ce: wadanne
ne wurare biyu na la'ana Ya Ma'aikin Allah! Sai ya ce: Wanda yake biyan bukata
akan hanyar Mutane ko inuwarsu",
Muslim ya ruwaito.
Kuma an ruwaito daga gare shi, رضي الله عنه ya ce: lallai Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda
ya yi kashi a hanyar da ba matacciya ba, daga cikin hanyoyin Musulmai, to
tsinuwar Allah ta tabbata a kansa, da ta Mala'iku, da ta Mutane gaba daya",
Baihakiy ya ruwaito.
Sai ku yi salati da sallama ga …………………………