HUDUBAR MASALLACIN ANNABI صلى
الله عليه وسلم
JUMA'A, 4/RABIYUS SANIY/1439H
daidai da 22/DISEMBA/2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
Shehin Malami wato: Aliyu
bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: AURE DA SHIKA A MUSULUNCI, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga AllahN
da Ya halitta jinsin maza da mata, daga abinda kasa ke tsirarwa, da kuma cikin
mutane, har da abinda mutane ba su sani ba.
Kuma Ubangiji Mabuwayi da
daukaka ya yi umarni kan yin gyara da kawo gyara, ya kuma yi hani kan barna, a
cikin fadinsa;
"Kuma ka kawo gyara,
kada ka bi hanyar mabarnata" [A'araf: 142].
Sannan Allah (تبارك وتعالى) ya shar'anta
shari'oi, domin maslahar bayi da amfaninsu, da tunkude barna da kuma dukkan ababen da suke cutar da mutane da aljanu.
Ina yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa, ina tuba zuwa
gare shi, ina neman gafararSa,
Ina kuma shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Mawadacin
da bashi da bukatar talikai.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Mai gaskiya,
Amintacce,
Ya Allah! ka yi salati, da
sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka; Muhammadu, da iyalansa da
sahabbansa gaba daya.
Bayan haka:
Ku bi Allah da
takawa, a asirce da kuma a bayyane, saboda babu mutumin da ke samun rabo a
cikin rayuwarsa, da bayan mutuwarsa, sai da takawa, kuma babu wanda zai tabe,
ya yi hasara, sai ta hanyar bin son zuciya.
Ya ku mutane
Ku rika tuna
mafarin halittarku (daga mutane biyu; Adamu da Hauwa'u), da yadda mazan cikinku
da matanku suka yawaita, alhalin kun samu ne daga rai guda daya; Wanda Allah ya
halitta masa matarsa daga jikinsa, Allah (سبحانه) ya ce: "Ya ku mutane, ku ji
tsoron Ubangijinku wanda ya halitta ku daga rai guda, kuma ya halitta matarsa
daga gare shi, kuma daga gare su, ya watsa maza dayawa, da mata" [Nisa'i: 1].
Kuma Allah Ta'alah ya ce:
"Shi ne wanda ya halitta ku daga rai guda, kuma ya halitta masa
matarsa daga gare shi, domin ya samu natsuwa da ita" [A'araf: 189].
Sa'annan sai sunnar Allah da shari'arsa suka gudana, akan
kulluwar namiji da mace ta hanyar kulla ko daura aure, irin na shari'a,
domin mutane su iya gina gidan auratayya, kuma domin a amsa ga bukatar halitta;
ta irin sha'awar da ke tsakanin mutane, da bin hanyar aure; ba ta hanyar zina
ba, domin hanyar aure ita ce, ke haifar da kamewa, da albarka, da bunkasa, da
tsarkaka, da arziki, da lafiyar zukata, da samun doriyar shekaru; ta hanyar
zurriyar mutum nagari; wato salihai.
Ita kuma hanyar zina tana
da dauda, ga janyo cutukan zuciya, da lalacewar namiji da mace, ga kuma irin kaskancin
da sabo ke janyowa, da matsalolin rayuwa, da tafiyar da albarkar rayuwa, da
samun matsaloli cikin 'ya'ya da jikoki, sannan sai azabar lahira, An ruwaito
daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) cikin abinda ya gani na abubuwan
al'ajabi, a daren da aka yi masa isra'i da mi'iraji, Ya ce: "Sa'annan sai ya je
ga wasu mutane, wadanda ake farfasa kayukansu da dutse, duk lokacin da aka
fasa, sai kan ya koma kamar yadda ya kasance daga farko, kuma baza a dena
aikata musu hakan ba. Sai ya ce: Su wanene wadannan Ya Jibrilu? Sai ya ce:
Wadannan sune kansu ke yin nauyi kan halartar sallolin farilla.
Sa'annan sai ya je
ga wasu mutane, wadanda aka sanya takardu ko fata ta gabansu, da kuma ta
duburarsu, suna kai-komo, kamar yadda rakumi ko dabbobi ke kai-komo, kuma suna
cin kayar rakuma (dari'in), da kuma cin itaciyar danyan wuta (zakkum), da
tsakuwa ko duwatsun da aka dafa su da wuta. Sai ya ce: Su wanene wadannan Ya
Jibrilu? Sai ya ce: Wadannan sune wadanda ba sa bayar da sadakar dukiyarsu
(zakkah), kuma Allah bai zalunce su da komai ba.
Sa'annan sai ya je
ga mutanen da a gaba gare su akwai dafaffen naman da ke cikin tukunya, da kuma
wani naman danye a cikin wata tukunyar mai dauda, amma sai gashi suna cin wannan
danyen mai dauda, suna barin nunannen mai tsafta, Sai ya ce: Su wanene wadannan
Ya Jibrilu? Sai ya ce: Wannan mutum ne daga cikin al'ummarka, zai kasance yana
da mace ta halal, mai tsafta, sai ya je wurin wata mace mai dauda, sai ya kwana
a wurinta, har safiya. Da kuma matar da za ta tashi daga wurin mijinta na halal
mai tsafta, sai ta je wurin wani namji mai dauda; ta kwana da shi, har
safiya". Ibnu-Jarir
ya ruwaito shi a cikin tafsirinsa.
Kuma ya zo cikin hadisin
Sa'ad bn Sinan Alkhudriy (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) akan isra'i da mi'iraji, ya ce: "Sa'annan sai na yi
gaba kadan, sai ga ni a wurin wasu kwanukan da suke dauke da nama a cikinsu a
yayyanke, amma babu wanda ke kusantarsu, sai ga ni a wurin wasu kwanukan da
suke dauke da naman da yake doyi, a wurin kuma akwai mutanen da suke cin wannan
naman. Sai na ce: Ya Jibrilu, su wanene wadannan? Ya ce: Wadannan daga cikin
al'ummarka, suna barin halaliyarsu, sai su je ga haram. Ya ce: Sannan sai ya
matsa gaba kadan, sai ga ni wurin wasu mutanen da cikkinsu kamar gidaje, duk
lokacin da dayansu ya yunkura don ya tashi sai ya fadi, yana cewa: Ya
Ubangijina, kada ka tashi kiyama. Sai ya ce: kuma su suna kan hanya irin ta
iyalan fir'auna. Ya ce: Sai hanyar ta zo, ta rika tattaka su, Sai ya ce: Wadannan
a cikin al'ummarka sune masu cin riba, "Wadanda suke cin riba baza su
tashi ba, sai kamar wanda shedan ke dimautarwa daga shafa ke tashi" Baihakiy ya ruwaito shi a
cikin littafin Dala'ilun nubuwwati.
Gidan aure mafaka ce da ke bada
kulawa ga zurriya, kuma take tausaya musu, take damuwa da su, take ilmantar da
su.
Kuma uwa da uba sune
ke shirya al'umma ('ya'ya da jikoki) domin su iya daukar nauyace-nauyacen
rayuwa, da amfanar da daukacin al'umma, da bunkasa yara cikin kowane sha'ani,
kuma sune suke fadakar da su zuwa ga riko da kowace dabi'a mai kyau, su kuma yi
hani kan aiki da kowace dabi'a abar aibantawa, kuma su rika bada tarbiyya akan
aikin kwarai, domin neman dacewa da gidan lahira, da kuma rayuwa ta har abada,
kuma sai karamin yaro ya yi koyi da abinda yake gani a gida, sai kuma ya
tasirantu da abinda ya ke gani, kuma ya ke ji, tun da bashi da ikon karanta
tarihi, domin daukar izina daga cikinsa, da kuma abin koyi.
Shi kuma daura aure ko
kulla shi, alkawari ne mai girma, kuma igiya ce mai karfi, kuma zumuncin
sadarwa mai tsananin muhimmanci, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma idan kun yi nufin musanya
mace, a gurbin wata macen, kuma kun baiwa dayansu tarin dukiya (kindari), to
kada ku karbi wani abu daga cikinsa, Shin za ku karbe shi da karya da zunubi
bayyananne? * Kuma yaya za ku karbe shi, alhalin, sashenku ya sadu da sashe,
kuma mata sun riki alkawari mai kauri daga gare ku" [Nisa'i:20-21].
Maluman tafsiri suka
fassara alkawari mai kauri da cewa, shine: Daura aure.
Kuma daura aure, yana
kunsar maslahohi da amfani ga miji da mata, da wasu amfani da maslahohin na
'ya'ya, da maslahohi da amfani ga makusantan ma'auratan biyu, da kuma wasu
amfani da maslahohin ga daukacin al'umma, da
wasu maslahohin na duniya da lahira, wadanda ba za a iya kididdige
wadannan amfanonin ba.
Shi kuma warware wannan
alkawarin, da lalata wannan kullin, da tsinke igiyar auratayya, ta hanyar SHIKA,
yana rurrushe wadancan maslahohin da amfanonin gaba dayansu. Sai miji ya
auka cikin fitintinun da za su cutar da shi ga addininsa da duniyarsa da lafiyarsa.
Kuma itama mace, idan
aka sake ta, sai ta auka cikin fitintinun da suka fi tsanani akan wanda mijin
ke aukawa cikinsu, kuma wanda aka sake ba za ta samu ikon mayar da rayuwarta
kamar yadda ta kasance ba, kuma sai ta rayu cikin nadama, musamman a wannan
zamanin wanda a cikinsa mazajen da za su iya dacewa da halinta suka yi karanci,
sai 'ya'yansu su watse, su kuma fiskanci rayuwa mai matukar tsanani, wacce ta
banbanta da wanda suka yi alhalin suna karkashin inuwa ko kulawar iyaye guda
biyu (uwa da uba) a hade, sai kuma su rasa dukkan dadin da zai sanya rayuwarsu
cikin walwala, sai su fiskanci lalacewar halayya da nau'ukansa mabanbanta, da
kuma cutuka iri-iri, sai itama al'umma gaba dayanta, ta cutu, da matsaloli masu
cutarwa, wanda su ke kasancewa bayan aukuwar shika, sai ka ga, yanke zumunta yana
yawaita.
Kuma duk yadda aka kai
makura wajen kididdige matsalolin da suke cikin shikar aure, to lamarin ya fi
haka.
Kuma, domin ka san barnar
da shika ke haifarwa, da yawaitar matsalolinta, kebantattu da masu gamewa, sai
ka yi tunani cikin hadisin Jabir (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai ya ce:
"Lallai Iblisu ya kan dora al'arshinsa ko gadon mulki akan ruwa
(teku), sa'annan ya tura 'yan farautarsa, kuma wanda zai fi su kusancin matsayi
da Iblisu shine wanda yafi tsananin fitina; Sai daya daga cikinsu ya zo, ya ce:
Na aikata kaza, da kaza, Sai ya ce: Ba ka aikata komai ba. Sa'annan sai daya
daga cikinsu ya zo ya ce; Ban bar wane ba, har sai da na raba tsakaninsa da
tsakanin matarsa; Sai Iblisu ya kusantar da shi, yana cewa: Na'am, Kai ne goga,
Sa'annan sai ya rungume shi", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma lallai wasu mutane,
sun yi sako-sako da batun shika, sai suka dauki lamarinsa da sauki, sai
su ka auka cikin lamura masu hatsari, da sharrace-sharrace masu tarin yawa, sannan
su kan aukar da wasunsu cikin abinda suka auka a cikinsu.
Hakika shika saboda sabuba
masu rauni, ya yawaita a wannan zamanin, ko saboda dalilai marasa kan-gado.
Kuma SABBUBAN SHIKA A
WANNAN ZAMANIN suna da yawa,
Yana daga MAFI GIRMANSU:
JAHILTAR HUKUNCE-HUKUNCEN SHIKAN, a cikin shari'a, da rashin aiki da Kur'ani da
sunnah. Saboda shari'ar musulunci ta kewaye kullin aure, da dukkan abinda zai
bashi kariya da kula, kuma ta kare aure da muhimmiyar katanga, domin bashi
kariya; kuma domin kada ya tsattsage, ya rushe, ya girgiza; a lokacin kadawar
guguwar son zuciya.
Kuma domin kasancewar sababin
shika ka iya kasancewa daga miji, ko daga matar, ko daga miji da matar, ko
daga wasu daga cikin makusantansu; Sai shari'a ta magance kowane irin yanayin
da ka iya zama sababin shika;
Sai Allah a cikin
littafinsa ya umarci miji, da ya girmama lamarin aure, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma kada ku rike
mata da cutarwa; har ku kekare iyaka, kuma duk wanda ya aikata hakan, to ya
zalunci kansa, kuma kada ku riki ayoyin Allah da izgili" [Bakara: 231].
Kuma Allah ya ce: "Kuma su mata, suna
da kwatankwacin abinda ke kansu (na hakkoki) da kyautatawa, Kuma su maza suna
da wata daraja akan mata" [Bakara: 228].
Maluman tafsiri suka ce:
Mace akan mijinta, tana da
hakkoki, misalin hakkokin mijin da ke kan matarsa, wajen kyautata zamantakewa,
Sai kuma namiji ya samu fifiko akan mace, ta fiskar kasantuwarsa mai tsayuwa da
lamarinta, .
Don haka wajibi ne, akan
namiji yayi zamantakewa da matarsa cikin abinda aka sani da kuma kyautatawa,
Idan kuma ya kita, to sai ya dau hakuri, la'alla yanayin ya canzu, izuwa ga
wanda yafi kyau, ko la'alla a azurta shi da 'ya'ya salihai tare da ita, sannan
a bashi ladan hakurinsa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma ku yi
zamantakewa da su da kyautatawa, domin idan kun ki su, to, tana yiwuwa ku ki
abu, sai Allah ya sanya alkhairi mai yawa a cikinsa" [Nisa'i: 19].
Kuma wajibi ne ga miji da matarsa, su rika gyara lamuran da
suke janyo sabani, tun suna farko-farkonsu; domin kada kafar sabanin ta fadada.
Kuma wajibi ne ga miji da mace; kowannensu ya san dan'uwansa;
sai kowanne ya rika aikata abinda zai fi yardar da sahibinsa, Ya kuma rika
nisantar abinda dayan baya so, Wannan kuma abu ne mai sauki, da ba a boye ya ke
ba.
YANA DAGA CIKIN SABBUBAN WANZUWAR AURE: Kokarin yin
sulhu a tsakanin ma'auratan, daga ma'abuta alkhairi, masu sulhuntawa, da kawo
gyara, domin kowanne ya iya samun hakkokinsa na wajibi, wanda ke kan sahibinsa,
Allah (تعالى) ya ce: "Kuma idan ku ka ji
tsoron sabani a tsakaninsu, sai ku tayar da mai hukunci daga cikin iyalansa, da
mai hukunci daga iyalanta, idan sun nufi sulhu a tsakaninsu, to lallai Allah
zai daidaita tsakaninsu, Lallai ne Allah ya kasance Masani Mai bada labari" [Nisa'i: 35].
KUMA YANA DAGA SABBUBAN DAWWAMAR AURE DA JIN DADINSA: Hakuri
da yin rangwame, domin dacin da ke cikin hakuri, dan kadan, zaki ne na tsawon
zamani ke biyo bayansa, Kuma ba wani abinda ake fiskantar ababen ki da shi,
wanda ya kai hakuri girma, Allah (تعالى) ya ce: "Kawai, masu hakuri
ana cika ladansu, ba tare da lissafi ba" [Zumar: 10].
Rangwame da yin afuwa, suna kawata rayuwa, kuma suna sanya ma
rayuwa walwala da farin ciki da kyau. Kuma da shi ake warkar da kurjin da zamantakewa
ta haifar. Kuma, Yafiya da yin afuwa dole ne a rayuwa, musamman kuma tsakanin
ma'aurata biyu.
Kuma idan ya kasance cikin
lamura ne na karin kwalliya (ba wajibi ba), Ko kuma cikin lamuran da za a iya
jinkirta su, to lallai yin rangwame a irin wannan, shine mafi alheri ga
ma'aurata. Musamman kuma a irin wannan zamanin, wanda kokarin samar da bukatun
rayuwa, ya wahalar da yawa-yawan mazaje, tare da cewa, wasu ababen ba na lalura
ko dole ba ne.
Kuma lallai neman bada
dukkan hakkoki, da rashin rangwantawa, ko yafe wasu hakkokin, yana gadar da
guje wa juna da kiyayya a tsakanin ma'aurata. Alhalin shi kuma aure ruhinsa
shine, taimakakkeniya, da jin-kan juna, Allah (تعالى) ya ce: "Ya ku wadanda suka
yi imani lallai ne wasu daga matanku da 'ya'yanku makiya ne a gare ku, sai ku
kiyaye su, kuma idan kuka yafe kuma kuka kau da kai, kuma kuka gafarta, to
lallai Allah Mai gafara ne Mai jin kai", [Tagabun: 14].
Gabar da ake nufi a wannan ayar
ita ce, sanyaya guiwar miji ko uba kan aikata alkhairi, ko kuma rashin taimakonsa,
ko kuma hana shi aikata aikhairin.
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ka riki abinda ya
saukaka, kuma ka yi umarni da alheri, kuma ka kau da kai daga jahilai" [A'araf: 199].
KUMA YANA DAGA SABBUBAN
DAWWAMAR AURE: MIJI
ya yi ta kokarin gyara abinda ya karkace na halin matarsa, da abinda shari'a ta
halatta, kuma ta yi izini, Allah (تعالى) ya ce: "Su salihan mata
masu da'a ne, masu tsarewa ga gaibi saboda abinda Allah ya tsare. Su kuma
wadanda ku ke tsoron bijirewarsu, to, ku yi musu gargadi, kuma ku kaurace musu
a wuraren kwanciya, kuma ku doke su, Idan kuma suka muku da'a, to kada ku nemi
wata hanya akansu"
[Nisa'i: 34].
Kuma wajibi ne akan alkalai
su rika yin sulhi tsakanin ma'aurata biyu, cikin abinda ake kaiwa gare su na
kararraki, har a samu ittifaki, a kawar da shika.
Shi kuma HAKKIN MACE AKAN
MIJINTA shi
ne ya yi zamantakewa da ita da kyautatawa, ya kuma bata gidan da ya yi daidai
da irinta, tare da ciyarwa da tufatarwa, da bayar da alkhairi, da kamewa ga
barin cutar da ita.
Kuma lallai SABABIN
SHIKA YANA IYA KASANCEWA DAGA MATAR NE, saboda kaushin harshenta, ko munin
halinta, da jahilcinta, Don haka, wajibi ne akan mace ta rika gyara halinta,
tana mai biyayya ga mijinta, ta yi bakin kokarinta wajen tarbiyyar 'ya'yanta da
ingantacciyar tarbiyya, An ruwaito daga Abdurrahman bn Auf (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Idan mace ta yi
sallolinta biyar, ta yi azuminta na wata, ta kiyaye farjinta, ta yi biyayya ga
mijinta, Sai ace mata: Ki shiga Aljannah, daga dukkar kofar da ki ka so", Ahmad ya ruwaito
shi, kuma hadisi ne hasan.
Kuma wajibi ne ga mace ta
rika hidima ga mijinta, da kyautatawa, tana mai koyi da sahabbai mata –رضي الله عنهن-.
Kuma abu ne mai kyan gaske
ta rika yin tarayya da mijinta cikin farin cikinsa da bacin ransa, kuma ta
kasance mai taimakonsa wajen biyayya ga Allah Ta'alah.
KUMA YANA DAGA SABBUBAN
SAMUWAR SHIKA:
Shisshigin wani daga dangin miji ko mata, ko kuma danginsu gaba daya, Sai su ji
tsoron Allah, kuma su fadi magata ta daidai. Kuma ya zo cikin hadisi, cewa: "Allah ya la'anci mutumin
da ya bata matar wani a gare shi, ko kuma ya bata mijin ga matarsa".
Kuma wajibi ga MACE TA
TSAYU WAJEN BADA HAKKIN MAKUSANTAN MIJINTA, musamman kuma iyayensa biyu.
Kuma shima mijin WAJIBI
NE YA TSAYU WAJEN BAYAR DA HAKKIN MAKUSANTAN MATARSA; saboda sakaci kan
hakkin makusantan ma'aurata, sau dayawa ya kan zama sababin shikan aure.
KUMA YANA DAGA SABBUBAN
SHIKA:
Bibiyar fina-finan da su ke rushe dabi'a, ko shafukan yanan gizo-gizo (internet)
na haram, wadanda suke yada barna.
KUMA YANA DAGA SABBUBAN
SHIKA: Fitan
mace daga gida ba tare da samun izinin mijinta ba , kuma baya halatta a gare
ta, ta fita ba tare da izininsa ba, domin miji shine ke da ma'aunin auna
lamura.
Kuma idan SABBUBAN ZAMAN
AURE SUKA GAGARA To lallai Allah ya halatta yin shika, kuma ya zo cikin
hadisi cewa: "Halal din da Allah ya fi kinsa, shine shika".
Sai miji ya yi shika irin na
shari'a, bayan tsanaki da bi-sannu-sannu, kamar yadda Allah ya yi umarni a
cikin fadinsa: "Ya kai wannan Annabin idan za ku saki mata, sai ku sake su ga
iddarsu, kuma ku kididdige iddar" [Dalak: 1].
Maluman tafsiri suka ce:
Sai ya sake ta a cikin
tsarkin da bai sadu da ita a cikinsa ba, shika daya, Idan ya so, sai ya mata
kome a cikin wannan iddar. Idan kuma ya so, sai ya barta har ta gama iddarta,
sai ta fita daga mulkinsa.
Kuma lallai shika ta irin
wannan hanyar tana bude kofar fatan yin kome, don wanzar da auren, ko a sake
sabon aure, idan har ta yi tsarki, bayan idda.
Sai ka yi dubi, ga yadda
aka karfafa lamarin aure, da yadda shari'ar gaskiya ta kiyaye shi. Kuma ka yi
dubi kan sakacin mutanen wannan zamanin kan lamarin shika, da abinda shikan ke
janyowa; na kayan bacin rai.
Allah (تعالى) yana cewa: "Ya ku wadanda suka
yi imani, kada ku bi, hanyoyin shedan, domin duk wanda ya bi hanyoyin shedan,
to lallai shi yana umarni ne da alfasha, da kuma munkari", [Nur: 21].
Allah ya yi mini albarka NI
da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman
gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi,
Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai
gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Mai rahama Mai
jin-kai, ya shar'anta hukunce-hukunce da iliminsa da hikimarsa da kuma
rahamarsa.
Tsarki ya tabbata a gare
shi; abin bauta Mai girma.
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Masani
Mai hikima.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanka ne kuma manzonka,
Ya Allah ka kara salati da
sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da
sahabbansa, masu riko da shari'arsa mikakkiya.
Bayan haka … !!
Ku ji tsoron Allah, iyakar
tsoronsa, kuma ku yi riko a musulunci da igiya mai karfi.
Ya ku Bayin Allah …
!!
Allah yana cewa: "Kuma ku taimaki juna akan biyayya da
takawar Allah, kada ku taimaki juna akan sabo da ketare iyaka, kuma ku ji
tsoron Allah, lallai ne Allah Mai tsananin ukuba ne" [Ma'ida: 2],
Ya ku Musulmai,
Shika ya zama wani abinda
ke gudana akan harasan wasu samarin ba tare da tsare ko kula da hakkokin 'ya'yansu,
ko wani makusancinsu ba, ko kuma lura da wani ba,
Kuma hakan yana aukuwa, ta
hanyar maimaita shi, a cikin zamani masu nisa da juna, ko maimaita fadinsa a
cikin majalisa daya, sai kuma ya tafi yana ta neman fatawowi, ko ya ce, zai yi
wayo, wani lokacin hanyoyi su kan toshe masa, sai ya yi ta nadamar da ba za ta
masa amfani ba, Alhalin Allah kuma yana cewa: "Duk wanda ya ji
tsoron Allah, to zai sanya masa mafita * kuma ya azurta shi, ta yadda baya
tsammani"
[Dalak: 2-3].
Kuma duk wanda ya ji tsoron
Allah, cikin lamarin shikansa, ta fiskar da shari'a ta yarda, sai Allah ya
sanya masa mafita.
Kuma duk wanda ya dauki
aure da girma, bai yi sako-sako da shi ba, sai Allah ya sanya masa albarka a
cikin aurensa, kuma ya samu kyakkayawar natija.
Kuma wasu daga cikin
na'ukan shika kebantattu, yin shika a cikin wadannan halayen ya kan kasance
laifi ne (sabo), kamar yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce wa Abu-Ayyub: "Lallai sake
Ummu-Ayyub, laifi ne".
Ya ku bayin Allah!
"Lallai ne, Allah da
Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku
yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
……………………………
,,, ,,, ,,,