HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 20/JUMADAL ULA/1438H
daidai da 17/FABARAIRU/ 2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ABDULLAHI ALBU'AIJAN
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
TSORON ALLAH A VOYE DA A
BAYYANE
Shehin Malami wato: Abdullahi
Albu'aijan –Allah
ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TSORON ALLAH A VOYE DA A
BAYYANE,
Wanda
kuma a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah; (ALMUJIBU)
Mai ji da amsawa,
(AR-RAQIBU) Mai tsinkayar
abinda aka voye,
(ALHASIBU) Mai qididdiga da
hisabi da kiyayewa,
wanda iliminsa ke tsinkaya
ga abinda ke cikin zukata, Masanin ababen da aka asirce, yana sane da abinda ke
cikin qiraza, kuma izuwa gare shi kawai ake mayar da lamura,
ya qididdige wa bayi
aiyukansu,
kuma ya qaddara musu
ajalinsu.
Ina yabon Ubangijina kuma
ina gode masa, akan falalolinsa da ni'imominsa da ba a qididdige su,
Tsarki ya tabbata ga wanda
ya xaukaka ga barin abokan tarayya da kishiyoyi,
kuma masu girma da
shugabanni su kan qanqan-da-kai ga qarfin mulkinsa,
kuma hanta da zuciya su kan
tsattsage saboda girmansa,
kuramen duwatsu daskararru,
kuma su kan faffashe saboda tsoronsa.
Tsarki ya tabbata ga Allah,
gwargwadon yawan halittunsa, da iya yardar ransa, da nauyin al'arshinsa, da
tawadar rubuta kalmominsa,
Tsarki ya tabbata a gare ka;
Ubangijinmu, mamakin irin girmanka !
Tsarki ya tabbata a gare
ka, saboda girman jin-kanka da rahamarka !!
Tsarki ya tabbata a gare
ka, sunanka albarsa ta yawaita, kuma matsayinka ya xaukaka, babu kuma abin
bautawa koma-bayanka !!!
Ina shaidawababu abin
bautawa da gaskiya, sai Allah shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, ka
xaukaka daga barin kishiyoyi da kini da 'ya'ya.
kuma ina shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanka ne manzonka, ya isar da manzanci, kuma ya sauke amana,
ya kuma yi nasiha ga bayi.
Allah ka yi daxin salati a
gare shi da iyalansa da sahabbansa, da waxanda su ka bi su da kyautatawa, har
zuwa ranar komawa (ga Allah, wato: qiyama).
Bayan haka:
Ya ku Bayin Allah…
!!
Ina yin wasiyya a gare ku,
da ni kaina da bin dokokin Allah Mabuwayi da xaukaka, a asirce da kuma a cikin
ganawa, saboda ita ce wasiyyar Allah ga na farko da na qarshe, "Kuma haqiqa mun yi
wasiyya ga waxanda ke gabaninku, da ku kanku, da cewa: ku ji tsoron Allah" [Nisa'i: 131].
Ya ku Mutane … !!
Ashe bai fi dacewa a gare
mu (musulmai), mu riqa tuna Allah ba, muna yin tunatarwa ga kayukanmu,
muna masu sabunta alqawari da
shi; ta hanyar tuba, da kuma horas da rayukanmu akan savawa bin son zukata, da
lazimtar taqawa,
muna kuma jin cewa; Allah yana
ganin bayi, da jin girmansa,
muna masu tuna hisabin
Allah, da uqubarsa,
sai kuma mu yi tanadi,
domin lokacin barin duniya, da kuma haxuwar wahalhalun barin duniya, da na
farkon shiga lahira,
mu kuma yi guzuri domin
shirin bijiro da mu ga Allah, "a ranar da mutum ke guje wa xan'uwansa, da
kuma uwarsa da ubansa, da matarsa da 'ya'yansa, ga kowani mutum, a wannan yinin
akwai sha'anin da ya wadace shi" [Abasa: 33-37].
Ya ku
Bayin Allah … !!!
Tare da fantsamar ilimi, da
cigaba ta fiskar sadarwa, da buxewar duniya, da qara zurfafa lamarin yaqar
kwakwale (da addinai), da yawaita ko nau'antuwar hanyoyin sadarwa na al'umma,
waxanda su ka yi kutse cikin gidaje, su ka wayi-gari a hannun qananan yara da
manya, da maza da mata, = To, lallai musulmi yana buqatuwa, a karan-kansa, da
tarbiyyar iyalan gidansa; wajen samun garkuwa da yin riqo DA TSORON ALLAH
ta'alah, a zuciya, da jin cewa Allah yana ganinsa, domin tsoron Allah
shi ne ke sanya shamaki tsakanin mutum, da aikata savo, kuma da tsoron Allah
ne mutum zai cire kansa daga abubuwa na haram, ya kuma fiskanci aiyuka na
biyayya, kuma tsoron Allah shi ne ginshiqin samun kowani matsayi,
kuma sababi na aikata kowani aiki na xa'a, kuma tsoron Allah shi
ke tabbatar da girman Allah a cikin zuciya.
Tsoron Allah a voye, matsayi ne daga cikin
maxaukakan matsayi, kuma sifa ne daga cikin sifofi masu darajoji mafi girma,
kuma da tsoron Allah ake samun ibadar taka-tan-tan (الورع), kuma tsoron Allah, bin dokokin Allah a
jikinsa ke rataya, kuma shi ne hujjar da ta ke nuna imani, kuma
shine abinda tauhidi da ikhlasi, su ke haifarwa, kuma tsoron Allah
shi ne mavuvvugar kyawawan halayya, Mutum yana da buqatuwar samun tsoron Allah
a aikace, domin ya iya rayuwa a matsayin mutum miqaqqe.
Tsoron Allah a voye
shi ne abinda martabar IHSAN ta ke hukuntawa, wato, martabar ka bauta wa Allah
kamar kana ganinsa, domin idan kai ba ka ganinsa, ai shi yana ganinka.
Yana daga ababen da tsoron
Allah ke lazimtawa, JIN CEWA ALLAH YANA GANINKA, da samun ilimi ko jin cewa
Allah yana gani kuma yana kula da zukatun bayinsa da aiyukansu, ya san idanu maha'inta,
da abinda qiraza ke voyewa, kuma lallai Allah yana tare da bayinsa a duk inda
su ka kasance, "Babu abinda ke kasancewa na ganawar mutane uku face shi ne na
huxunsu, ko kuma biyar face shi ne na shidansu, ko kuma qasa da haka, ko fiye,
face ya kasance tare da su, a duk inda su ka kasance" [Mujadila 7].
Saboda, duk wanda ya san
cewa Allah yana ganinsa a duk inda ya kasance, kuma lallai iliminsa yana
tsinkaya ga baxinin mutum da zahirinsa, da sirrinsa da abinda ya bayyanar, mutum
ya kuma riqa halarto da hakan a lokacin da ya ke keve, to lallai hakan zai
wajabta masa nisantar savo, a asirce.
Ya ku
Bayin Allah … !!!
Tsoron Allah a voye shine mabuxan qofofin
gafara, kuma a cikinsa akwai alkhairi mai yawa, da lada mai girma, "Lallai waxanda su
ke tsoron Ubangijinsu a voye, suna da wata gafara, da kuma lada mai girma" [Mulk: 12].
Tsoron Allah a voye sababi ne na sauke yardarm
Allah ga bawa, da kuma shiga cikin aljannoninsa, "Wanda ya ji tsoron
Mai rahama a voye, kuma ya zo da zuciya mai tuba * ku shiga aljanna da salama,
wannan yini ne na dawwama" [Qaf: 33-34].
"Lallai waxanda su
ka yi imani, kuma su ka aikata aiki nagari, waxannan su ne mafi alherin halittu
* sakamakonsu a wurin Ubangijinsu shi ne aljannonin zama, wanda qoramu su ke
gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada, Allah ya yarda da
su, suma sun yarda da shi, wannnan sakamako ne, ga wanda ya ji tsoron
Ubangijinsa"
[Bayyinah: 7-8].
Tsoron
Allah a voye
sifa ce daga cikin sifofin masu taqawa, "Kuma haqiqa mun baiwa Musa da Haruna
littafi mai rarrabewa, da haske, da tunatarwa ga masu taqawa * waxanda su ke
tsoron Ubangijinsu a voye, kuma su, dangane da lokacin qiyama masu tsoro ne" [Anbiya'i 48-49].
Tsoron
Allah a voye
yana daga abubuwa masu warware tavewa, kuma yana shiryar da zukata zuwa ga aikata
alkhairi, da karvar tunatarwa da nasiha, Allah ta'alah ya ce: "Lallai kana yin
gargaxi ne ga waxanda su ke jin tsoron Ubangijinsu a voye" [Faxir: 18].
Kuma Allah ya ce: "Lallai wanda ke
amfana da gargaxi shi ne wanda ya bi littafin tunatarwa, kuma ya ji tsoron Mai
rahama a voye
" [Yasin: 11].
Kuma Allah ya ce: "Da sannu, zai
wa'aztu, Wanda ya ke tsoron Allah, * kuma zai nisanci tunatarwa, mutum shaqiyyi" [A'alah: 10-11].
Tsoron
Allah ta'alah a voye
tana sanya wa'azi da tunatarwa da nasiha su zama suna da tasiri ga zukata da
kuma jiki, "Allah shi ne wanda ya saukar da mafi kyan zance; littafi mai
kamantacceniya (cikin kyansa da hukunce-hukuncensa), wanda ake maimaita shi
(hujjojinsa da qissosinsa da hukunce-hukuncensa, kuma ake maimaita tilawarsa ba
tare da qosawa ba), fatu ko tsikar jikin waxanda su ke tsoro Ubangijinsu suna
kaxawa (saboda tasiri), sa'annan sai fatunsu da zukatansu su yi taushi zuwa ga
ambaton Allah"
[Zumar: 23].
Kuma haqiqa Allah ya jarrabi imanin masu harama (da hajji
ko umra) dangane da jin
tsoronsa a voye,
a inda ya ce: "Ya ku waxanda su ka yi imani lallai ne Allah zai jarraba ku da wani
abu; na abin farauta (r tudu), wanda hannunku da mashinku za su same su (a kusa
da ku), domin Allah ya san wanda ke tsoronsa a voye (sai tsoron Allah ya sanya
shi kamewa daga yin farautarsa)" [Ma'ida: 94].
Ya
ku bayin Allah … !!1
Lallai duwatsu, alhalin
basa jin magana, kuma suna daskare, suna yin sujjada, kuma suna tsattsagewa,
suna faxowa, saboda tsoron Allah, kuma kasancewarsu daskararru ko basu da
hankali,
ko don kasancewar su ba
mukallafai (da aka basu umurni da hani ba)
bai hana su ji, ko tasirantuwa da tsoron Allah ba,
kuma qarfi da sandarewa bai
amfanar da su wajen fito-na-fito da wannan yanayi na tasirantuwa ba, "Kuma akwai daga
cikin duwatsu, wanda qoramu su ke vuvvuga daga gare su, kuma daga cikinsu akwai
wanda ke tsattsagewa; domin ruwa ya fita daga cikinsu, kuma akwai daga cikinsu,
wanda ke gangarowa ya faxo domin tsoron Allah" [baqara: 74].
To, yaya su kuma mutane?
Kuma ina zukatansu su ke,
idan an kwatanta da waxannan halittun?
Ina kuma hankulansu?
A UZU BILLAHI MINAS SHAIXANIR
RAJIM:
"Da za mu saukar da
wannan alqur'anin ga dutse, da ka gan shi, cikin kushu'i yana tsattsagewa
saboda tsoron Allah, kuma waxannan misalai ne, waxanda mu ke buga su ga mutane,
la'alla ko za su yi tunani" [Hashr: 21].
Allah ya yi mini albarka NI
da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman
gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi,
Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai
gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah wanda ya shayar da zukata da
addininsa da kuma tsoronsa,
Kuma zukata su kan
qan-qan-da kai, domin fatan Ubangijinsu da tsoronsa,
Kuma, Ya shiryar da mu, da
falalarsa da rahamarsa,
Salati da sallama su qara
tabbata ga cikamakon manzanninsa da annabawansa
Ya ku bayin Allah …
!!
Ku cika alkawari,
kuma ku yi tanadi domin
gobe, saboda lahira ta fiskanto, duniya kuma ta juya baya, ajali kuma yana karatowa,
tafiyar kuma tana da nisa, guzurin kuma ya yi kaxan, hatsarin kuma yana da
girma,
Kuma ku sani, lallai a
kanku akwai masu bada shaida, waxanda ba ababen tuhuma ba ne, su ne; gavovinku,
sai ku kula da su, kuma ku bi dokokin Allah a asirce, da kuma a bayyane, saboda
babu wani voyayyen da ke voyuwa ga Allah, kuma sirri a wurin Allah, a fili ya
ke,
Ya ku taron
musulmai… !!
Lallai tsoron Allah ta'alah a voye na yanyo daddaxar rayuwa ko
sa'ida da natsuwa, da kuma hutu da kwanciyar hankali, kuma garkuwa ne daga
fitintinu.
Kuma daxin hakan, a cikin
zuciya, babu wanda ya san shi, sai wanda ya xanxane shi, sai mu yi azama, mu
dage, mu kuma yi kwaxayin sabar wa rai jin tsoron Allah, a voye, da kuma hana
rai aikata aibi, tare da horas da rai akan hakan, gabanin zuwan furfura, saboda
zuciyar mutum, idan har ta cika da tsoro da girmama Allah mabuwayi da xaukaka,
to sai gavvai su kame ga barin aikata savo.
Ya tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) cikin abinda ya ke ruwaito shi daga
Ubangijinsa mabuwayi da xaukaka, cewa: "Na rantse da buwayata, Ba zan
haxa wa bawana tsoro biyu da aminci biyu ba; idan bawana ya ji tsorona a
duniya, sai in amintar da shi ranar qiyama, idan kuma ya aminta da ni a duniya,
sai in tsoratar da shi ranar qiyama".
Kuma ya inganta daga gare
shi (SAW): "Abu guda uku suna tseratarwa; adalci a cikin halin fushi ko yarda, da
tsakaita ciyarwa a halin talauci da wadaci, da kuma tsoron Allah a asirce da a
bayyane".
Kuma ku sani –Ya ku bayin Allah- lallai tsarkake zuciya,
da samun tsoron Allah, sun rataya ne da gyaruwar zukata, domin "a cikin jiki
akwai wata tsoka, idan ta gyaru, to dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ta vaci
dukkan jikin ya vaci, ita ce zuciya".
Sai ku nemi taimako akan samun haka, ta hanyar addu'a,
kuma jagoranku abun koyi akan haka shine Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم).
Ya Allah! Ka
bamu kaso daga tsoronka, wanda za ka shamakance tsakaninmu da tsakanin yin savo
a gare ka, daga xa'arka kuma, irin abinda za ka isar da mu ga aljannarka, daga
yaqinin kuma, abinda z aka sauqaqe mana musibun duniya da shi, kuma ka jiyar da
mu daxi da jinmu da ganinmu da qarfinmu, har abada matuqar muna raye, kuma ka
sanya su, su zamto masu wanzuwa daga gare mu, kuma ka sanya fansarmu ga wanda
ya zalunce mu, kuma ka bamu nasara akan wanda ya yi adawa da mu, kuma kada ka
sanya duniya ta kasance mafi girman burinmu, ko kuma qarshen iliminmu, kuma
kada ka qaqaba mana –saboda zunubanmu- shugabannin da basa tsoronka, kuma basa
jin qanmu, Ya mafi jin qan masu rahama!
Ya Allah! Lallai ne mu, muna roqonka,
tsoronka a voye da a bayyanae, da kalmar adalci da gaskiya, a cikin yanayin
fushi da kuma yarda, kuma ina roqonka tsagaita ciyarwa a cikin talauci da
wadaci, kuma muna roqonka ni'imar da bata qarewa, da sanyin ido, wanda baya
yankewa, kuma muna roqonka yarda da qaddara, kuma muna roqonka rayuwa mai sanyi
bayan mutuwa, kuma muna roqonka jin daxin kallon fiskarka, kuma muna roqonka
shauqin saduwa da kai, ba a cikin cuta mai cutarwa ba, ko kuma wata fitina mai
vatarwa. Ya Allah! Ka qawata mu da qawar imani, kuma ka sanya mu, mu zama
shiryayyu masu shiryarwa.
…
…
…
Bayin Allah
"Lallai ne, Allah da
Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku
yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa
Annabi Muhammadu, kuma ka yarda da khalifofinsa shiryayyu masu shirayarwa; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da
sauran sahabbai gabaxaya, ka haxa da mu, da baiwarka, ya mafi baiwar masu
kyauta.
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment