2017/02/23

HUDUBAR 27 JUMADAL ULA 1438 daidai da 24 fabarairu 2017 ta HUZAIFIY daga MASALLACIN ANNABI











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 27/JUMADAL ULA/1438H
daidai da 24/FABARAIRU/ 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
HAQQOQI NA WAJIBI
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: HAQQOQI NA WAJIBI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO

Yabo ya tabbata ga Allah; wanda ya yi falala ga bayinsa; sai ya yi bayanin HAQQOQIN da su ke kansu DA WAJIBAI, kuma ya yarje musu aiyuka masu kyau, ya kuma sanya musu qin munanan aiyuka, ya yi alqawarin alkhairori ga salihan bayi,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Mai amsa addu'oi,
kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa, Wanda aka qarfafe shi da mu'ujizozi.
Allah ka yi daxin salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, masu taimakon addinin Allah, da jihadi da kuma hujjoji bayyanannu,

Bayan haka:
Ku bi Allah da taqawa; kada ku tozarta farillanSa, kuma kada ku qetare dokokinSa, kuma lallai wanda ya yi taqawa, ya samu babban rabo, wanda kuma ya bi son zuciya ya tave,

Ya ku, Bayin Allah… !!!
Ku sani
Lallai aiyukan bayi, sakamakonsu nasu ne, uqubar aiyukan kuma akansu ne, saboda biyayyar bawa bata amfanar da Allah, kuma aikata savo baya cutar da Allah, Allah (تعالى) ya ce: "Wanda ya aikata aikin kwarai, to, domin kansa ne,  wanda kuma ya munana, to, a kansa. Sa'annan zuwa ga Ubangijinku za a mayar da ku" [Jasiya: 15].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Wanda ya aikata mummuna aiki, ba za a sakanta masa ba, face da kwatankwacinsa, wanda kuma ya aikata aiki na kwarai, daga namiji ko mace, alhali kuwa yana mumini, to waxannan za su shiga aljanna, ana ciyar da su a cikinta, ba da lissafi ba" [Gafir: 40].
Kuma Allah Mabuwayi da xaukaka a cikin hadisin qudusi ya ce: "Lallai ku, ba za ku kai ga cutar da ni ba, balle ku cutar da ni, kuma ba za ku kai ga amfanar da ni ba, balle ku amfanar da ni, Ya ku bayina! Lallai waxannan aiyukanku ne, na ke qididdige muku su, sa'annan sai in cika muku sakamakonsu, saboda haka; Wanda ya samu alheri to ya gode wa Allah, wanda kuma ya samu akasin haka, to kada ya zargi kowa, face kansa", Muslim ya ruwaito shi, daga hadisin Abu-zarrin |(رضي الله عنه).

Lallai sauke HAQQOQIN DA SUKA WAJABA AKAN BAWA, Amfaninsu –a qarshen lamari- na komawa ne ga bawa mukallafi (mai hankali balagagge), ta hanyar bashi sakamakonsa a duniya da lahira, kamar yadda Allah (تعالى) ya ke cewa: "Kuma duk wanda ya aikata, aiyukan kwarai, alhalin yana mumini, to babu musu ga aikinsa, kuma Mu a gare shi, masu rubutawa ne" [Anbiya'i: 94].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Lallai waxanda su ka yi imani, kuma suka aikata aiyukan kwarai, lallai ne Mu, ba Mu tozartar da ladan wanda ya kyautata aiki ba" [Kahf: 30].

            Kuma lallai sakaci, wajen sauke sashin HAQQOQIN DA SU KA WAJABTA GA BAWA (mai hankali, balagagge), ko tozarta haqqoqin gabaxaya da barin sauke su, cutar da ke cikin hakan da uqubarsa, yana komawa ne ga mutumin da ya tozarta irin haqqoqin da addini ya shar'anta;
saboda idan mutum ya tozarta HAQQOQIN UBANGIJIN TALIKAI, to, bai cutar da kowa ba, face kansa, a duniya da lahira, domin Allah, Mawadaci ne daga barin talikai, Allah (تعالى) ya ce: "Idan ku ka kafirta, to lallai Allah Wadatacce ne ga barinku, kuma bashi yarda da kafirci (butulci) ga bayinSa, idan kuma ku ka yi godiya zai yarda da godiyar, a gare ku" [Zumar: 7].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ya ku, mutane! Ku ne masu buqata zuwa ga Allah, shi kuma Allah shi ne Mawadaci Abin godiya" [Faxir: 15].
Kuma Allah Mabuwayi da xaukaka ya ce: "Ga ku, Ya ku waxannan! Ana kiranku, domin ku ciyar ga tafarkin Allah, amma daga cikinku akwai mai yin rowa, kuma wanda ya yi rowa, to haqiqa yana yin rowar ne ga kansa" [Muhammadu: 38].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma wanda ya aikata zunubi, to lallai yana tsirfarsa ne a kan kansa, kuma Allah ya kasance Masani Mai hikima" [Nisa'i: 111].

            Haqqin Ubangiji, wanda ya wajaba a kiyaye shi, shine TAUHIDI, Kuma haqiqa Allah ya yi mafi girman alqawari akansa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma an kusantar da aljanna ga masu taqawa, ba da nisa ba * Wannan shi ne abinda ake yi muku wa'adi da shi, ga dukkan mai yawan komawa ga Allah, mai kiyaye (umurninsa)" [Qaf: 31-32].

Kuma duk wanda ya tozarta HAQQIN ALLAH Mabuwayi da xaukaka, ta hanyar SHIRKA  a gare shi, da riqon wasu koma bayan Allah a tsakani, yana yin bauta a gare su, ko yana roqonsu, neman yaye cuta, da baqin ciki, ko biyan buqata, kuma yana tawakkali a gare su, to lallai ya tave, kuma ya yi hasara, kuma aikinsa ya ruguje, kuma Allah ba zai karva masa farilla ba, ko fansa, kuma za a ce masa, ka shiga wuta tare da masu shiga, Sai dai idan ya tuba daga aikata shirka, saboda ya zo cikin hadisi, cewa: Za a faxawa mutum, daga cikin 'yan wuta, cewa: "Da abinda ke cikin duniya naka ne, shin za ka fanshi kanka da shi, daga shiga wuta? Sai ya ce: E, sai a ce masa: Ai an umurce ka da abinda ya fi hakan sauqi, cewa kada ka yi shirka wa Allah", Bukhariy ya ruwaito shi.

            Idan kuma mutum mukallafi (mai hankali balagagge) ya tozarta HAQQOQI, ya kuma qi bada haqqoqin bayin Allah na wajibi akansa, to haqiqa ya haramtawa kansa lada, a duniya da lahira. Idan kuma ya yi sakaci wajen bada sashensu, to lallai za a haramta masa alherori ne, gwargwadon sakacin da ya yi, wajen bada haqqoqin halittun Allah.
            Kuma rayuwa tafiya ta ke yi, da abinda mutum ke samu na tsanani ko wadaci, da hanawa ko baiwa, kuma rayuwar ba za ta tava tsayawa ba, akan yadda xan'adam ke samun haqqoqinsa na wajibi, da ke wajen mutane ba, Sai dai kuma a wurin Allah ne masu husuma za su haxu, sai Ya baiwa wanda aka zalunta haqqinsa, daga mutumin da ya zalunce shi, ya kuma tozarta haqqinsa, Ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Lallai, za ku bada haqqoqi ga ma'abutansu, a ranar qiyama, har sai an xauki fansa ga akuyar da bata da qafo, daga akuya mai qaho", Muslim ya ruwaito shi.

            Kuma mafi garman HAQQOQI        bayan haqqin Allah, da ManzonSa, su ne HAQQOQIN IYAYE BIYU,
Kuma saboda girman haqqinsu ne, Allah ya gwama ambaton haqqoqinsu da haqqinSa, a inda ya ce: "Kuma Ubangijinka ya hukunta kada ku bauta wa kowa face Shi, kuma mahaifa biyu ku kyautata musu kyautatawa, ko da xayansu zai kai ga tsufa a wurinka, ko dukkansu biyun, to, kada ka tsawace su, kuma ka faxa musu magana mai karimci * Kuma ka sassauta musu fikafikan tausasawa na rahama, kuma ka ce: Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda su ka yi renone ina qarami" [Isra'i: 23-24].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma mun yi wasiyya ga mutum, game da mahaifansa biyu; Uwarsa ta xauke shi, a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yayensa a cikin shekaru biyu, (mu ka ce masa:) Ka gode mini da kuma mahaifanka biyu, Makoma zuwa gare Ni ne ta ke" [Luqman: 14].
            Kuma Allah ya girmama haqqin iyaye biyu ne, saboda Allah ya samar da kai ne; ya halitta ka ta hanyarsu; su biyu.
            Ita kuma Uwa ta samu mafi tsananin wahala, a matakan renon ciki, kuma ta yi kusan halaka a lokacin haihuwa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma mun yi wasiyya ga mutum, game da mahaifansa biyu; da kyautatawa, uwarsa ta yi cikinsa da wahala, kuma ta haife shi da wahala" [Ahqaf: 15].
Kuma shayar da mutum, aya ce daga cikin ayoyin Allah.
            Shi kuma Uba yana kulawa, yana tarbiyya, kuma yana yin aiki domin kawo abinci ga xansa.
            Kuma iyaye biyu suna neman magani ga cutukan 'ya'ya,
Kuma suna tashi cikin dare (su hana idanunsu barci) domin xansu ya yi barci,
Suna gajiyar da kansu domin xansu ya samu hutu,
Suna kuma wahalar ko takura wa kayukansu, domin su yalwata wa xansu,
Kuma suna jure wa qazantar yaro, domin ya ji daxi,
Kuma suna ilmantar da xansu, domin ya zama kamili, madaidaicin mutum,
Kuma suna so xansu ya zamto ya fi su, ta kowace fiska

            Don haka;
Kada ka yi mamaki –ya kai yaro- yawaitar wasiyyar da Allah (تعالى) ya yi, dangane da iyaye biyu,
kuma kada ka yi mamakin yawan narkon azabar da aka tanadar, ga mutumin da ya qi yin biyayya ga iyayensa,
            Kuma "xa" ba zai kai ga cikakken biyayya ga mahaifi ba, duk yadda ya yi qoqarin ya kwatanta, sai a hali xaya tak, Hadisi ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai ya ce: "Xa ba zai iya sakanta wa mahaifi ba, sai dai idan ya same shi a matsayin bawan da aka mallaka, sai ya saye shi, sannan ya 'yanta shi", Muslim ya ruwaito shi, da Abu-dawud da Tirmiziy.

Kuma iyaye biyu, qoqfofi ne biyu daga cikin qofofin aljanna; wanda ya musu biyayya, zai shiga aljanna, saboda ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce: "Hancinsa ya turbuxi qasa! Hancinsa ya bugi turvaya!! Hancinsa ya turbuxi qasa!!! Sai aka ce wanene, ya Manzon Allah! Sai ya ce: Wanda ya riski iyayensa biyu da rai, a halin tsufa, ko xaya daga cikinsu, sai kuma bai shiga aljanna ba", Muslim ya ruwaito shi.

Ya kai Musulmi>>> !!!
Idan har iyayenka biyu, su ka yarda da kai, to lallai Ubangijinka ya yarda da kai, Ya zo daga Abdullahi bn Amr (رضي الله عنهما), daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Yardar Allah tana cikin yardar mahaifi, Fushin Allah kuma, yana cikin fushin mahaifi", Hadisi ne ingantacce, Tirmiziy ya ruwaito shi, da Alhakim, a cikin Almustadrak, kuma ya ce: hadisi ne ingantacce.

Kuma biyayya wa iyaye biyu, shi ne:
Yin xa'a a gare su, a cikin umurnin da babu savon Allah a cikinsa,
Da zartar da umurnin da iyayen biyu su ka bayar, da yin aiki da wasiyyar su,
Da tausasa musu,
Da shigar da farin ciki a zukatansu,
da yalwata musu ga ciyarwa,
da bada dukiya a gare su,
da jin qansu, da tausaya musu,
da shiga vacin rai, saboda vacin ransu,
da janyo abinda zai xebe kewa a gare su,
da xa'a ko biyayya ga abokan iyaye biyu,
da sada zumuntar masoyansu,
da sada zumuncinsu,
da kamewa daga dukkan nau'ukan cutarwa a gare su,
da barin aikata dukkan abinda su ka yi hani a kansa,
da son tsawon rayuwarsu,
da neman gafara a gare su a cikin rayuwarsu da bayan mutuwarsu

Shi kuma BIJERA WA IYAYE KO RASHIN BIYAYYA a gare su (wato, Uquq) shi ne abin da ke kishiyantar hakan gabaxayansa,
            Shi kuma yawaitar bijire wa iyaye (Uquq) yana daga alamomin qiyama, saboda ya zo cikin hadisi: "Lallai yana daga alamomin qiyama, ruwan sama ya yawaita, Xa kuma ya zama fushi (ga iyaye), ashararun mutane kuma su yi mungun yaxuwa, su kuma mutanen kirki su qaranta mummunan qaranci".

Yana daga manyan misalan bijire wa iyaye, Kai iyaye; su biyun, ko kuma xaya daga cikinsu, gidan bada kulawa ga masu shekaru dayawa (tsofi), da fitar da su daga kulawar Xansu,  WAL IYAZU BILLAHI,
Kuma yana daga manyan misalan bijire wa iyaye, Yin girman kai a gare su, da ta'addanci akansu ta hanyar dukansu, ko yin wulaqanci a gare su, da zaginsu, da hana su buqatar duniya, Hadisi ya zo daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم): "Lallai aljanna, ana samun qamshinta daga tafiyar shekaru xari biyar, kuma mai cutar (ko bijire) wa iyaye ba zai samu qamshinta ba", Xabaraniy ya ruwaito shi.
Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ku bauta wa Allah, kuma kada ku haxa wani da Shi, kuma ga mahaifa biyu ku kyautata musu, kuma ku kyautata ga ma'abucin zumunta, da marayu, da miskinai, da makwabci ma'abucin kusanta, da makwabci manisanci, da aboki a gefe, da xan hanya (matafiyi), da abinda hannunku na dama su ka mallaka, Lallai ne Allah ba ya son wanda ya kasance mai taqama mai yawan alfahari" [Nisa'i: 36].


Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Mai tsananin qarfi,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Mai gaskiya, Amintacce,

Ya Allah ka qara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da sahabbansa gaba xaya.

Bayan haka … !!
Sai ku yi taqawar Allah, iyakar taqawa, kuma ku yi riqo, a musulunci da igiya mai qarfi,

Ya ku Bayin Allah … !!
Lallai haqqoqin iyaye biyu –tare da abinda ke cikin tsayuwar xansu wajen sauke su, na tarin lada mai girma, da kuma albarka- to kuma, bada su yana daga manyan halayyar musulunci, yana kuma nuna karamcin xabi'u, waxanda mutumin da zuciyarsa ta yi kyau ke tsayuwa wajen bada su, kuma asalinsa ya kyautata, xabi'unsa su ka tsarkaka,
Ku lallai sakamakon kyautatawa shi ne kyautatawa,
Kyakkyawan abu kuma, duk wanda ya maka shi, to, haqqinsa shi ne a kula da shi, a yi masa sakayya,
Kuma abu mai kyau ana fiskantarsa ne da mai kyau irinsa,
Kuma babu mai bijire ga kyakkyawan abu, face mai yasassun halayya, maras mutunci, mai mummunar zuciya, Allah (تعالى) ya ce:
"Kuma kada ku manta da falalar da ta ke a tsakaninku, Lallai ne Allah ga abinda ku ke aikatawa Mai gani ne" [Baqara: 237].

            Kuma Allah (تعالى) yana cewa dangane da annabi Isah (عليه السلام): "Kuma Ni mai biyayya ne ga Uwata, kuma bai sanya ni mai kaushin zuciya, marashin alheri ba" [Maryam: 32].
            Kuma ya faxa, dangane da annabi Yahya (عليه السلام): "Kuma mai biyayya ga mahaifansa biyu, kuma bai kasance mai girman kai, mai savo ba" [Maryam: 14].
            Kuma Allah ya ce, dangane da shaqiyyi marashin alkhairi: "Kuma wanda ya ce ga mahaifansa biyu, Tir gare ku, Shin kuna tsoratar da ni cewa za a fitar da ni daga qabari ne, alhali kuwa qarnonan mutane dayawa sun shusshuxe, a gabanina (basu komo ba), Kuma su (mahaifan) suna neman taimakon Allah, suna ce masa: Kaitonka! ka yi imani, domin alqawarin Allah gaskiya ne, ,,," [Ahqaf: 17].
            Kuma an ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه),

daga Annabi (صلى الله عليه وسلم)

Lallai wani Mutum ya zo wurin Annabi (صلى الله عليه وسلم) sai ya ce: Ya Manzon Allah! WANENE A CIKIN MUTANE YAFI CANCANTAR KYAUTATA MU'AMALATA?
Sai ya ce: "Mahaifiyarka, sai mahaifiyarka, sai mahaifiyarka, sa'annan sai Mahaifinka, sa'annan sai wanda ke kusa da kai, sai wanda ke kusa da kai", Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.

            Ya ku Bayin Allah… !!!
            "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, ……………………………
,,,          ,,,          ,,,



No comments:

Post a Comment

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...