HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 10 /Rabiyul Auwal/1438H
daidai da 09/ Disemba/ 2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
SAMUN CANJE-CANJE SUNNAR
RAYUWAR DUNIYA NE
Shehin Malami wato:
Abdulbariy bn Auwadh As-subaity –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai
taken:
SAMUN
CANJE-CANJE SUNNAR RAYUWAR DUNIYA NE, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Samun canje-canje alama ce ta rayuwar (duniya) wanda babu
wani abu da zai tabbata a cikinta, lafiya da cuta, yin sama da qasa, buwaya ta
xaukaka da qasqanci, yunwa da qoshi, talauci da wadaci, aure da shika, aminci
da tsoro, baqin cikin da farin ciki, da kuma samun sauye-sauye cikin lamuran
tattalain arziqi; Waxannan canje-canjen sunna ne na rayuwa; da ba a iya guduwa
musu ba, kuma muna karanta su a cikin ababen da su ke aukuwa a tarihin kowani
zamani.
Kuma a duk lokacin da rayuwa ta juya zuwa ga yanayi maras
daxi, sai Rai mai rauni ta yi ta qaqalo baqin ciki da nuna jin zogi, har ma da
canfe-canfe, waxanda za su raunata himmarta, sai su hana wannan mutumin tafiya
ko cigaba da rayuwa cikin qoqari da nashaxi.
YANA
DAGA, GINSHIQAN AQIDAR MUSULMI: Yin imani da hukunci da qaddara; na alkhairinsa da
sharrinsa, da samun yaqini ko sakankancewa; cewa lallai dukkan al'amari, da
juya lamura na Allah ne, kuma lallai canje-canje na rayuwa sha'ani ne na
Ubangiji, wanda ya fi qarfin ilimin mutane.
Imani da qaddara shi ne mafi qarfin sababin da ke tunkuxa
mutum domin ya iya qetare bala'oi da tsanani, ya kuma sanya shi ya sake
fiskantar aiyuka cikin azama da amincin zuci, da neman arziqi. Kuma shi ke bada
kariya ga rayuwar da ta cika da aiki daga wofantuwa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ka sani! Da
al'umma za su haxu akan su amfanar da kai da wani abu, to ba za su amfanar da
kai da komai ba, sai da abinda Allah ya rubuta maka. Da kuma za su haxu akan su
cutar da kai da wani abu, to ba za su cutar da kai da komai ba, sai da abinda
Allah ya rubuta maka. An xage alqaluma, kuma takardu sun bushe", Tirmiziy ya ruwaito
shi da isnadi ingantacce.
Wannan wasiyyar tana sanya rayukan mutane ratayuwa da
Allah shi kaxai; a cikin lamuran rayuwarsu, da lahirarsu, ta yadda ba za su
roqi kowa ba sai Allah, kuma ba za su nuna kwaxayinsu ba sai ga falalarsa. kuma
kamar yadda musulmai da harasansu ba za su roki kowa ba sai Allah, to haka
zukatansu ma; ba za su rataya su ga komai ba, sai ga Allah shi kaxai. Kuma da
haka ne kawai, za su sami buwaya da xaukaka, a yayin da wajen rataya zukatan ga
halittun Allah, su ke samun qasqanci da faxuwa; Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Duk wanda
talauci ya sauka akansa, sai ya saukar da shi ga mutane, to ba za a toshe
talaucinsa ba, wanda kuma ya saukar da shi ga Allah, to kusa ya ke, Allah ya
tafiyar masa da shi; ko dai da mutuwar gaggawa, ko wadacin gaggawa", Abu-dawud ya
ruwaito shi da Tirmiziy.
Kuma ana son bawa yana KYAUTATA ZATONSA GA UBANGIJINSA, yana mai qudurta cewa
lallai hukuncin Allah da qaddararSa sun ginu ne akan hikimar Ubangiji, da cikar
adalcinSa, da cikakkiyar rahamarSa; wanda ke talautar da wanda ya ke so, kuma
ya ke wadatar da wanda yake so, ya ke xaukaka wanda ya ke so, kuma ya ke
qasqantar da wanda ya ke so.
Mumini yana rayuwa ne akan yarda, a kowani hali, kuma
idan ya samu yarda da ransa, da UbangijinSa, to sai ya samu nitsuwa akan lamarin
yau xinsa da abinda ke halarce da shi, Idan kuma ya sha aqidar samun yaqini da
Allah, to sai ya nitsu da lamarin gobensa da abinda zai zo, a gaba cikin
rayuwarsa.
Kuma imani da hukuncin Allah da qaddararSa baya nufin
mutum ya sallama wa abinda ya masa dabaibayi na yanayi, ko karkata ga yanayi
guda xaya na rayuwa, ko yarda da xabi'ar xebe tsammani, ko sace guiwa ko azama.
A a hasali ma, imani da hukuncin Allah da qaddararSa yana hukunta, a tunkuxe
qaddarar da ta auku da wata qaddarar (kamar yunwa da qosi), tare da yin aiki da
sabbuba, cikin haquri da sabatin zuciya, da yin aiki domin canza halin da ake
ciki zuwa ga yanayin da ya fi shi kyau. Saboda;; ;; ;;
sau nawa Allah ya juya
halin faqiri zuwa ga wadaci!
Kuma sau nawa, wanda ke
cikin baqin ciki, sai Allah ya sanya vacin ransa farin ciki!!
Kuma sau nawa, wanda ke
cikin damuwa Allah ya mayar da damuwarsa farin ciki!!!
Kuma sau nawa, maras lafiya
Allah ya tufatar da shi da tufar waraka da lafiya!!!!
Kuma sau nawa wanda aka
zalunta ya gane ma idonsa yadda Allah ya xaukar masa fansa daga mutumin da ya
zalunce shi!!!!!
Mutum ana jarabtarsa da haxama idan canjin rayuwa na
kwatsam ya same shi, in banda masallatan da su ke akan sallarsu masu dawwama
ne, Allah ta'alah yana cewa: "Lallai ne, mutum an halitta shi, mai ciyon
kwaxayi * Idan sharri ya shafe shi, sai ya yi gajen haquri * Idan kuma alheri
ya shafe shi, sai ya yi rowa * Sai dai masallata" [ma'arij: 19-22].
Wani lokaci mutum na gafala daga qoqarin kawo gyara ga
halinsa izuwa ga yanayin da yafi kyau, saboda yadda ya bada himma (da vata
lokaci cikin) kukkutsawa ga neman sanin yadda abubuwa suka auku (analises), da qoqarin
binciken yadda abubuwa suka faru, da rayuwa cikin qawalwalniyar gurace-gurace,
sai a hakan, ya tozarta zamaninsa, ya vata lokacinsa, da kukkutsawa cikin
abinda bai dame shi ba, kuma ba zai amfanar da shi komai ba, alhalin Manzonmu
mai karimci (صلى
الله عليه وسلم) yana cewa: "Ka yi kwaxayin abinda zai amfanar
da kai",
Muslim ya ruwaito shi.
Shi kuma kaiwan koke, da riqon fushi da qoqarin sabawa da
shi, da yin hukunci da cewa zamani ya lalace, da qoqarin tona ko tayar da ruhin
munanan abubuwa a cikin al'umma, su waxannan suna karkashe kyawawan
gurace-gurace ne, kuma suna sace azamomi da niyyoyi, kuma suna lalata lamuran aikin
kawo bunqasa.
Mumini ya kan bar zartar ko yanke hukunci ga sababbin ababen
da su ke aukuwa, ta hanyar komawa ko lazimtar ra'ayinsa na haqiqa, domin sau
dayawa, jarabawar rayuwa, a cikinta, ta kan qunshi wasu damammaki, kuma sau
dayawa, wani bala'in, a bayan gushewarsa wata ko wasu ni'imomin su ke bayyana.
Mumini yana riskar cewa, lallai samun canje-canje a
rayuwa ni'ima ce mai girma, wacce ta ke buxe masa qofofi na bushara, ko zaton
kyautatuwar hali, ta kuma bubbuxe masa kafofin buri, kuma a cikinta ana samun
damammakin nasarori da xaukaka da sake gino rayuwa, Kuma duk lokacin bala'i da
bacin rai su ka yawaita su ka qara tsanani, lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana yin albishir, kuma yana mai
tayar da fatan alkhairi, a cikin zukata, da kalmomin da su ke nuna imani ko
gamsuwa zuwan abin da Allah ya alkawarta, da kuma nasararsa; Hadisi y azo daga
Adiyyu bn Hatim, ya ce:
Wata rana
ina wurin Annabi (صلى الله عليه وسلم) sai wani mutum ya zo ya koka masa
talauci, sai kuma wani ya zo yana mai koka masa yankewar hanya (wato: 'yan
fashi), Sai ya ce:
"Ya
kai Adiyyu! Shin ka tava ganin garin Hirah?" Sai na ce: Ban tava gani
ba, sai dai an bani labarinta, to sai ya ce: "Lallai idan ka yi tsawon
rai, za ka ga mace tana tahowa daga garin Hirah, har ta zo ta yi xawafin
ka'abah, bata tsoron kowa face Allah!",
Adiyyu ya
ce: Sai na ke faxa a cikin raina, to ina fasikan qabilar xai'in mavarnata ('yan
fashi) waxanda suka kunno wutar fitina a garurruka?
Sai kuma ya
ce: "Kuma idan ka yi tsawon rai, za a bubbuxe taskokin sarki; Kisrah (na
farisa)",
Sai na ce:
Kisrah xan Hurmuz?
Sai ya ce:
"E, Kisrah xan Hurmuz. Kuma idan ka yi tsawon rai, za ka ga mutum yana
fita da zinari da azurfa cikin tafin hannanusa, yana neman wanda zai karva
masa, saidai ba zai samu wani mutum da zai karvi sadakarsa ba"
Bukhariy ya ruwaito shi.
Musulmi ana umartarsa da sana'ar samar da
canje-canje a ransa, da xabi'unsa da rayuwarsa, zuwa ga yanayin da yafi dacewa, ta hanyar zavin hanyar shiriya da
alkhairi, da tunkuxe ko kawar da munanan sauye-sauye, yana mai koyi da shiriyar
Annabi (صلى الله عليه وسلم) cikin yadda ya
gyara ko ya kawo canje-canje a dayawa daga
sha'anonin rayuwarsa da rayuwar sahabbansa, ta zance da ta aiki, domin "ya canja
sunan wani wai shi: yaqi (harb) izuwa ga zaman lafiya (silm), hanyar vata kuma (shi'ib
addhlalah) ya sanya masa hanyar shiriya (shi'ib alhuda), qabila mai suna
'ya'yan mai vatarwa kuma (banuw mugwiyah), ya kira su da 'ya'yan mai shiryarwa
(wato: banu rishdah)",
Abu-dawud ya ruwaito shi, da isnadi mai inganci.
Kuma Manzon Allah ya
kasance yana kyamar wuraren da su ke da munanan sunaye, wannan ya sanya a
lokacin da Annabi (صلى
الله عليه وسلم) ya iso garin Madina, alhalin sunanta yana (Yasriba –wato: abar
aibantawa-) sai ya canza mata suna zuwa ga (Xaibah –wato: Mai daxi-).
Kuma ya
caccanza fahimtoci na kuskure, daga cikin haka: lokacin da Manzon Allah (صلى الله
عليه وسلم) ya ce: "Wa nene a
cikinku ku ke xaukarsa RAQUB?", Sai su ka
ce: Wanda ba a haihuwa masa, ko kuma wanda 'ya'yansa basa rayuwa, Sai ya ce:
"Wannan ba shi ne Raqubu (a mahangar shari'a) ba, lallai
Raqub shi ne: wani bai bunne wani daga cikin 'ya'yansa (ya yi haqurin rashin
su) ba.
Wanene kuma
jarumi a cikinku?"
ya ce: Sai mu ka ce: shi ne wanda mazaje basa kayar da shi (a kokawa, ko
a faxa),
Sai ya ce: "Ba wannan ba ne jarumi, jarumi shi ne wanda ke
iya mallakar ransa a lokacin fushi", Muslim ya
ruwaito shi.
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم)
ya ce: "Shin kun san wanene fallasasshe?" Sai su ka ce: fallasasshe a cikinmu shi ne wanda bashi da
dirhami, ko wani kaya?
Sai ya ce: "Lallai fallasasshe a cikin al'ummata zai zo
ranar qiyama, da tarin salloli da azumi da zakka, sai ya zo alhalin ya zagi
wannan, ya yi qazafi ga wannan, ya ci dukiyar wannan, ya zubar da jinin wannan,
ya doki wannan, Sai a baiwa wannan wasu daga ladan aiyukansa kyawawa, wannan
shima daga ladansa kyawawa, idan ladansa su ka qare gabanin a biyan abinda ke
wuyansa, sai a xauka daga laifukansu, sai a xora masa, sa'annan a jefa shi
cikin wuta" Muslim ya ruwaito shi.
A wasu lokuta jin wasu
gamsuwa munana suna yin dabaibayi ga zuciyar Musulmi, sai su ke sanya shi ya
riqa tunanin shi gajiyayye ne; ba zai iya canza kansa izuwa yanayin da ya fi dacewa
akan wanda ya ke ciki ba,
Sai dai kuma wannan tunani ne, da ya ke hana ruwa gudu, wanda irinsu su
kan ja xaixaikun mutane zuwa ga ci-baya, kuma dole sai an canza su, da wasu
gamsuwa kyawawa masu amfani, waxanda za su tabbatar wa mutum a cikin zuciyarsa
da hankalinsa cewa, lallai wannan rayuwar ta cancanci ayi mata aiki, kuma
lallai kowace mushkila (wato, matsala) tana da magani, duk yadda ta kai, wajen
girma.
Wannan ne kuma, ya sanya mutane masu azama su ke kawo canje-canje masu
amfani, a cikin sha'anonin rayuwarsu, har su iya canza faxace-faxace da gaba,
ko adawa, zuwa ga: soyayya, da 'yan'uwantaka, da abota, kuma su iya canza
munanan abokai da abokai nagari, kuma su yi rinjaye akan munanan al'adu da
ta'adodin da su ka sava wa addini, kuma basu shiga cikin da'irar musulunci ba.
MUHIMMAN MATAKAN KAWO CANJE-CANJE A RAYUWAR MUTUM; shi ne mutum ya canza kansa da ransa, kuma wannan ita ce gavar farko wajen sauye-sauye
ga halin al'umma, wacce ta ke koka samun koma baya, da talauci, da rashin
ci-gaba.
Sai batun kama makamin ilimi, wanda shi ne madogara
wajen gina wayewa da bunqasa, kuma da shi al'umma ta ke xaukaka a kowani
zamani. Allah ta'alah yana cewa: "Lallai ne Allah ba ya canza abinda ya ke ga
mutane, sai sun canza abinda ya ke ga rayukansu" [Ra'ad: 11].
Kuma yana daga ABINDA CANJIN ALKHAIRI ke
hukuntawa: Gyara zukata da niyya, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma wancan zato
naku, da ku ka yi wa Ubangijinku, ya halakar da ku, sai ku ka wayi gari a cikin
masu hasara"
[Fussilat: 23].
Ya zo kuma a cikin hadisi: Allah y ace: "Ni ina
wurin da bawana ya yi zatona, kuma ni ina tare da shi a lokacin da ya ke
ambatona",
Bukhariy da Muslim su ka ruwaito shi.
Allah ya yi mini albarka NI
da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke
cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,
Ina faxar abinda ku ke ji wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma
ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Bayan
haka:
Yana daga abinda ya ke,
tabbatacce a cikin kwakwaleLallai musulunci ya yi hani, daga dukkan canjin da mutum zai
samar, wanda zai kai ga lalata rayuwar mutam da shi, ya raunata addininsa, ya
kuma keta alfarmar shari'oinsa.
Yana daga cikin haka; Yin ta'addanci ga dukiya
da rayuka, da kawo rashin zaman lafiya da aminci, da cinye dukiyar mutane da
varna, da rashawa, da lalata shugabanci, da yaxa alfasha, da tayar da
fitintinu.
Musulmi kuma ga abinda ya
ke, a sarari ba zai yarda ya karvi duk wani canjin da zai kai ziuwa ga sharri
ba, kuma musulmi ba zai bada gudummawa da halinsa ko da maganarsa ga canjin da
zai kai izuwa ga gushewar ni'imomi ba, Allah ta'alah yana cewa: "Shin ba ka lura da
waxanda su ka musanya ni'imar Allah da kafirci, kuma su ka saukar da mutanensu
a gidan halaka?"
[Ibrahim: 28].
Kuma muna da abin koyi mai
kyau, daga rayuwar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم); saboda ya kasance yana neman mafaka daga Allah, yana neman
taimakonsa, daga dukkan cinjin da akwai mummunan abu da bala'i a cikinsa; yana
neman tsarinsa daga talauci, da qasqanci, da tsoro, da gajiyawa, da kasala, da
gallabar bashi, da fin qarfi daga wasu mutane, da munanan cutuka. Kuma yana
roqon Allah lafiya, da zaman lafiya a duniya da lahira. Kuma yana roqonsa ya
nisantar da musulmai daga fitintinu, ya kuma tsamar da su daga bala'oi.
Kuma, ba za mu wadatu -koda
daidai da kyaftawar ido- daga neman Allah ya bamu sabati da tabbatuwa a cikin
lamarin addini ba, saboda idan bai tabbatar da mu ba, sai samman imaninmu da
qassansa su goce daga gurbinsu, Allah ta'alah yana cewa: "Allah yana tabbatar
da waxanda su ka yi Imani da Magana tabbatacciya a cikin rayuwar duniya, da
cikin lahira"
[Ibrahim: 27].
Sai ku yi salati, -Ya ku
bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Allah ya umurce ku da aikata haka, a
cikin littafinsa; a inda yake cewa: "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna
yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare
shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].
"Lallai ne Allah
yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanta, kuma yana yin
hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama
masu tunawa"
[Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai
riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah
shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment