HUƊUBAR
MASALLACIN ANNABI SAW
JUMA'A
16/ZULƘI'IDAH/1440H
Daidai
da 19/Yuliyo/2019M
LIMAMI
MAI HUƊUBA
Shehun
Malami Dr. Salah ɗan Muhammadu Albudair
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Ya ku
Musulmai
Waɗannan
fa Matafiyan mahajjata ne suka kusanto, suna keta sahara mai halakarwa, suna
kutso falalen ƙasa da kilomitoci
Sun jigata a cikin
tafiyarsu, sannan sun zo bi-da-bi
Tawaga
tana biye da tawaga a cikin sahara
Ya
fatana! shin zan tashi na wayi gari
Sai na
sunsuni ciyawar izkhiri ta Makkah da karan shukinta (na jalil)
Sai kuma
na kunce jakata a kasar Annabi
Domin na
kwana a harami maɗaukaki ina baƙo
Sau
dayawa, yawale mai yawo da tafiye-tafiye, yanki-yanki, ƙasa-ƙasa, birni-birni,
mai yawaita kai-komo da bulaguro, wanda yake ƙarar da taronsa da sisi akan
hakan, Sai ka samu, ya yi nawa da sakaci kan tafiyar sauke ibadar hajji, ba
tare da uzuri ba, na tsawon shekaru, har ya tsufa.
Baya
burge zuciyata, sautin ƙaramin tsuntsu mai rera waƙa
Haka
kuma murmushin fikar ƙaramin yaro a lokacin bulaguro
???
Saboda
ba kowane bulaguro ke ƙayatar da Ni ba,
???
Saidai
bulaguro zuwa ga hajji wanda za a saka mana da Aljannah
Wannan
kuma baiwa ce daga kyautar Allah Makaɗaici
YA KU
MUSULMAI!!!
Makkah
da Madinah gari biyu masu haske da tsarkaka, sune wuri biyu da suka fi sauran
garurruka daraja, muɗlaƙan, kuma sune suka fi kowane bagire a doron ƙasa girman
matsayi da ijma'in Maluma (ba tare da saɓani ba);
Saboda
Makkah nan ne wurin da wahayi ya fara sauka, maɓuɓɓugar addini, gari amintacce,
alƙiblar Musulmai, makarkata ga zukatan Muminai, uwar alƙaryoyi, wanda bata da
makamanci a cikin birane, kuma bata da tsara a cikin kasashe.
Ita kuma
Madina, ita ce gari abin so ga Masoyinmu SAW, ita ce gidansa matabbatarsa, kuma
garin da ya yi hijirarsa ta farko, garin sunnah, mafakar imani kuma ganuwar
imani mai bashi kariya, kuma mafakar Musulunci da Musulmai.
Wahayi
bai sauka ba, face a ƙasar Makkah da Madinah, kuma fitilar Manzanci bata haska
ba sai akan ƙasarsu, kuma Annabi SAW bai rayu ba face akan turɓayansu.
An
ruwaito daga Abdullahi ɗan Abbas -Allah ya ƙara yarda a gare su- ya ce:
Manzon
Allah -sallal Lahu alaihi wa sallama- a ranar da aka je yaƙin buɗe garin
Makkah, ya faɗa cewa:
"Lallai Allah ya
haramta wannan gari (Makkah), a ranar da ya halicci sammai da ƙasa, don haka;
Makkah harami ne da haramtawar Allah, har zuwa ranar ƙiyama. Kuma lallai yaƙi a
cikinsa bai halatta ga wani Mutum a gabanina ba, kuma nima bai halatta a gare
ni ba, sai a cikin wani zangon lokaci na yini, kuma lallai Makkah harami ne da
haramtawar Allah, har zuwa tashin ƙiyama; ba a yanke ƙayar harami, ba a korar
abin farautar harami, ba a ɗaukar abin tsuntuwar harami, sai ga wanda zai bada
cikiyarsa, ba a cirar ciyawar da ta tsira a cikinsa",
Sai
Abbas ya ce: Saidai ciyawar izkhir, saboda amfanin maƙeransu, da bukkokinsu?
Annabi
ya ce: "Sai dai ciyawar izkhir". Bukhariy [1834, 3189], da Muslim
[1353], suka ruwaito shi.
Kuma
Manzon Allah SAW ya mayar da Madina harami, kamar yadda annabi Ibrahima ya
mayar da Makkah harami, kuma ya karkata zuwa ga Madina sai ya ce: Lallai
Madinah harami ne amintacce.
Don
haka, idan ganyen bishiyar harami da abin farautar harami su ka kasance masu
alfarma ababen girmamawa, to yaya alfarmar Musulmi, da alfarmar hajji, da kuma
alfarmar Mahajjata, da amincinsu da ayyukansu na hajji!; don haka baya halatta
Musulmi ya haifar da abinda zai kawo tasgaro ga amincin gari mai alfarma, ko
tasgaro ga tsarin garin, da natsuwarsa, da walwalar waɗanda suka nufo Makkah da
mazauna cikinsa, kuma bai halatta Musulmi ya cutar da Musulmai da zancensa ko
aikinsa ba.
Allah
Ta'alah ya ce: "Kuma wanda ya yi nufin ilhadi (karkatar da gaskiya) a
cikinsa da zalunci, za mu ɗanɗana masa wata azaba mai radadi" [Hajji:
25].
Don
haka, idan niyyatar zalunci da yin ƙudurin ilhadi ko karkatar da gaskiya yana
hukunta uƙuba mai raɗaɗi, to yaya kuma ga Mutumin da ya yi ta'addancin aikata
laifi mai haddi, ko ya aikata mummunan zunubi, ko ya zubar da jini (kisa), ko
ya firgitar da amintattu, ko ya cutar da mai rauni, ko ya zalunci miskini, ko
ya cuci Mahajjaci; ta hanyar gurɓata aƙidarsa, ko ha'intar alkawalinsa, ko cin
amanarsa, To menene zai kasance sakamako da ukubarsa a wurin Allah, alhalin
kuma ya keta alfarmar lokaci, da wuri, da Mutum!
Ɗana!
Kada ka yi zalunci a Makkah; ƙanƙani ko babba
Ka
kiyaye alfarmominta –Ya kai Ɗana- kada mai ruɗi ya ruɗe ka
Ɗana,
lallai wanda ya yi zalunci a Makkah zai haɗu da sharrori
Domin za
a bugi fiskarsa, kuma za a tuntsura shi wutar sa'ira akan kumatunsa
Ɗana,
lallai ni na jarraba hakan, sai na samu mai yin zalunci a Makkah yana yin
hasara
Allah ne
ya mata baiwar aminci, da abinda aka gina a cikinta na benaye
Kuma
Allah ya amintar da tsuntsayen cikinta, domin tsuntsu ba su da tsoro a Makkah
Giwaye,
an halakar da rundunarsu ana jifansu a garin da duwatsu
Sai ka
ji, idan ana baka labari, kuma ka fahimci yaya ƙarshen al'amura suke kasancewa
Yana
shiga ma'anar zalunci da ilhadi a Masallacin harami: Aikata laifukan haram a
Makkah, ko neman halatta su, kamar bayyanar da shirka da bidi'oi, da aukawa
cikin zina da shan giya, da sace-sace, da cinye dukiyoyi, da makirci da wayo,
da ɗaga tutoci domin raya bangaranci, da bidi'oi, da alamomin shirka, da shuka
fitina da rura wutar saɓani da haifar da banbance-banbance a tsakanin
Mahajjata, da ɗaukar taron hajji a matsayin wurin yaɗa jita-jita na ƙarya, da
lalatattun aƙidu, ko yaɗa sabubban ƙiyayya da adawa, saboda wasu manufofi na
siyasa, ko ƙabilanci ko ɓangaranci ko aƙida ko mazhaba.
Kuma
hajji da waɗannan wuraren masu tsarki, lallai suna da girma da tsarkin da yafi
ƙarfin a mayar da su wuraren yaɗa waɗannan ayyukan masu muni. Kuma al'amarin
hajji da amincinsa yana ga hannaye masu ƙarfi, masu ginawa, masu bada kariya,
masu tausayi, wanda ba za su bar miyagun Mutanen da suke nufin gurɓata lafiyar
hajji, ko siyasantar da shi ba, domin shugabannin za su hana miyagun cimma
manufarsu ko kaiwa ga samun burinsu.
YA KU
MUSULMAI!!!
Wajibi
ne akan 'yan Makkah da Madina da Masu zama a cikinsu, da sauran Mahajjata da masu
umrah da ziyara, su riƙa girmama waɗannan wuraren masu tsarki, suna kiyaye su
suna basu kariya, suna tsarkake su daga ayyukan saɓo da munanan laifuka ababen
ƙi masu halakarwa.
Mummunan
aikin da aka yi a harami ba a ninka shi ta fiskar adadi, saidai ya fi girman
laifi, kuma ya fi tsananin zunubi, akan laifin da aka yi a wurin da ba harami
ba.
Ibnul-ƙayyim
–Allah Ta'alah ya yi masa rahama- ya ce: "Yin mummunan laifi a harami da
kasar harami (Makkah), da kuma akan shumfuɗar Allah (Masallaci) yafi girman
muni, akan aikata laifin, a wani ɓangare na Duniya".
Kuma ya
ce, a cikin littafin Maɗalibi ulin nuha: "Kuma ana ninka kyawawan ayyuka
da munana idan aka yi su a wuri mai daraja, kamar Makkah da Madinah da Baitul
Maƙdis, da kuma a cikin Masallatai, haka kuma idan aka yi su a wani zamani mai
falala, kamar ranar Juma'a, da watanni huɗu masu alfarma, da kuma a kwanakin
watan azumi".
Shehun
Malami Mar'iy bn Yusuf Alkarmiy ya ce: "Lallai an sani daga shari'a mai
haske da addini miƙaƙƙe, cewa zunubi yana ninkuwa a wurare masu daraja da
halaye maɗaukaka, to haka lamarin yake a wurare masu daraja. Sa'annan ya ce:
Kowane wuri, ko zamani wanda yafi daraja, to saɓon Allah a cikinsa yafi muni,
domin baƙar tawada tafi bayyana ga farin abu".
Nawawiy
–Allah Ta'alah ya masa rahama- ya ce: "Zaɓaɓɓiyar magana itace, lallai yin
makwabtaka da ɗakin Allah da kuma Masallacin Manzon Allah (jiwaar) a Makkah da
Madina mustahabbi ne, sai ga wanda zato ya rinjaya masa cewa, zai auka cikin
lamurra abin zargi, ko sashensu. Kuma haƙiƙa halittun da ba za a ƙididdige su
ba, daga magabatan al'umma da wanda suke a bayansu, daga cikin waɗanda ake koyi
da su, sun aikata mujawaran (a Makkah da Madinah)".
Kuma
Ƙurɗubiy –Allah Ta'alah ya masa rahama- ya ce: "Haka kuma, shari'a a
wurare dayawa ta bayyana cewa, lallai duk lokacin da alfarma ta ninku, sai aka
keta su, to uƙubar itama sai ta ninku".
Kuma
Shekhul Islam Ibnu-Taimiyyah –Allah Ta'alah ya masa rahama- ya ce: "Yin
saɓo a kwanakin da ake girmamawa da wuraren da ake girmamawa, zunubinsu da
uƙubarsu yana yin kauri, gwargwadon falalar zamanin, da wurin".
Kuma
Ƙurɗubiy –Allah Ta'alah ya masa rahama- ya ce: "Kuma idan Allah Subhanahu
ya girmama abu, ta ɓangare guda, to sai ya zama yana da alfarma guda ɗaya, idan
kuma ya girmama shi ta ɓangarori biyu, ko ɓangarori dayawa, sai alfarmarsa ta
kasance mai yawa, to sai a ninninka uƙuba akansa idan aka yi mummunan aiki,
kamar yadda ake ninka lada idan aka yi aiki kyakkyawa; domin wanda ya yi
biyayya ga Allah a cikin wata mai alfarma, a kuma gari mai alfarma, to ladansa
ba kamar na Mutumin da ya yi masa biyayya a watannin da basu da wata alfarma,
ko a garin da ba harami ba. Haka wanda ya masa biyayya a watan da bashi da
alfarma, amma a gari mai alfarma, baya zama daidai da wanda ya masa biyayya a
watan da bashi da alfarma, a kuma garin da bashi da alfarma".
YA KU
MUSULMAI!!!
Ku
girmama ababen da Allah ya basu alfarma a cikin halin haramarku da wajensa,
kada kuma ku ƙetare iyakokinSa, kada ku halatta wurare masu alfarma, Allah Ta'alah
ya ce: "Wannan kuma, saboda wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah حرمات الله, to shine mafifici a gare shi a wurin
UbangijinSa"
[Hajji: 30].
Alfarmomin
kuma sune: Girmama mash'arul harami (wuraren hajji), da ɗaki mai alfarma, da
Masallaci mai alfarma, da gari mai alfarma, waɗannan sune alfarmomin.
Kuma ku
girmama abinda Allah ya umurce ku da girmama su, kuma ku gabatar da abinda
Allah ya umurce ku da gabatar da su, kuma ku nisanci abinda Allah ya hukunta
haramcinsa, don ku samu falalarSa da ladanSa da ni'imarSa.
Ina
faɗan abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah, sai ku nemi gafararSa,
lallai shi ya kasance ga masu mayar da lamuransu gare shi Mai yawan gafara ne.
HUƊUBA
TA BIYU
YA KU
MUSULMAI!!!
Sunnah
ta tabbata kan ninka ladan sallah a Masallaci mai alfarma da Masallacin Annabi
SAW, wato ninkawa ta fiskar adadi, ga farilla da nafila, ga maganar da tafi
inganci daga cikin maganganun Maluma biyu.
An
ruwaito daga Jabir -Allah ya ƙara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah -sallal
Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Yin sallah a Masallacina wannan yafi
salloli dubu a waninsa falala; in banda Masallaci Mai alfarma. Sallah kuma a
Masallaci Mai alfarma yafi salloli dubu
ɗari, a Masallacin da ba shi ba". Ahmad ya ruwaito shi, [14694،
15271],
da Ibnu-majah.
Saidai
babu wani dalili ingantacce da ya nuna cewa, kyakkyawan aikin da aka aiwatar a
garin Makkah ana ninka ladansa zuwa lada dubu ɗari. Ko yake cewa ana ninka
ladan azumin Ramadhana idan aka yi shi a garin Makkah, ko a Madinah zuwa ladan
azumin watanni dubu ɗari, ko a bada ladan Ramadhana guda saba'in. Dukkan wannan
babu sunnar da ta tabbatar da shi, kuma babu wani dalili akan hakan. Kuma
hadisan da suke ɗauke da wannan ma'anar ko dai da'ifai ne, ko yasassun hadisai
na ƙarya.
Magana
ingantacciya itace, lallai kyawawan ayyukan da aka yi a lokaci mai daraja, da
wuri mai daraja, ana ninka ladansu, ninkawa ta fiskar girma, ba ta fiskar adadi
ba, sai abinda dalili (ingantacce) ya yi nuni akansa.
Kuma
suma munanan ayyukan da aka zartar da su a wurare ko lokatai masu daraja
zunubinsu yana bunƙasa ta fiskar girma, ba ninkuwa ta fiskar adadi ba.
YA KU
MAHAJJATA DA MASU UMRAH DA ZIYARA!!!
Ku
ribaci lokacin zamanku a garin Makkah da Madinah, ta hanyar kwazo wajen aikata
kyawawan ayyuka, da yawaita aikata su, kuma ku yawaita tuba da neman gafara,
kuma ku bayyanar da rusunawarku da ƙan-ƙan-da kai da nadama, da nuna
buƙatuwarku ga Ubangijnku, da bayyanar da lalura; domin kuna wurin saukowar
rahama, kuma wuraren karɓar ayyuka, da fagagen da ake zaton amsa addu'oi da
gafara, da 'yanta Bayi daga faɗawa Wuta.
Ku riƙa
tuna girman wuraren, da falalar lokatan.
Allah ya
haɗa addu'oinku da amsawa, neman gafararku kuma da yarda, ayyukan da kuke yi
kuma ya karɓa.
Addu'a
….
……………….