HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 08/Rabiyus Saniy/1438H
daidai da 06/Janairu/ 2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ABDULLAHI ALBU'AIJAN
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
TAYAR DA KYAKKYAWAR FATA A
ZUKATA
Shehin Malami wato: Abdullahi
Albu'aijan –Allah
ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TAYAR DA FATAN, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah
Ubangijin talikai, majivincin muminai, mai bada nasara ga masu taqawa, Mai
rinjaye akan bayinSa, Mai hikima, Mai bada labari.
Muna yin yabo a gare shi,
cikin yanayin farin ciki da cuta, da tsanani da wadaci, da lafiya da bala'i,
Yabo nasa ne a duniya da lahira, kuma hukunci nasa ne, kuma zuwa gare shi za a
mayar da ku.
Ina shaidawababu abin
bautawa da gaskiya, sai Allah shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya,
kuma ina shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, ya turo shi da shiriya, da kuma addinin
gaskiya domin ya xaukaka shi akan addinai gabaxayansu koda mushirkai sun qi.
Allah ka yi daxin salati a
gare shi da iyalansa da sahabbansa, da waxanda su ka bi su da kyautatawa har
zuwa ranar sakamako, da sallamar aminci masu yawa.
Bayan haka:
Ku bi dokokin Allah –ya ku
bayin Allah- da taqawa, kuma ku yi masa xa'a, kuma ina hana ku yanke tsammani
daga rahamar Allah (S.W.T), saboda babu mai xebe tsammani daga rahamar Allah
face mutane kafirai.
Ya ku taron musulmai !! …
Lallai jarabtar mutane sunna
ce daga sunnonin Allah a wannan duniyar, domin (Allah) shi ne wanda ya halicci
mutuwa da rayuwa, domin ya jarrabe ku,
kuma jarrabawa abu ne da
hikimar Allah ke hukuntawa, Mabuwayi da xaukaka, cikin gwabzawa tsakanin
gaskiya da varna, domin rabe tsakanin masu gaskiya da maqaryata "Ashe, mutane zato
su ke yi, su ce: "Mun yi imani" alhali ba za a fitine su ba? Kuma
haqiqa mun jarrabi waxanda ke a gabaninsu, domin Allah ya san waxanda su ka yi
gaskiya, kuma ya san maqaryata" [Ankabut: 2-3].
Kuma jarrabawa xauraya ce domin
jarraba gwargwadon qarfin imani da tabbatuwa, da kuma sanin qarfin yaqini, kuma
da shi ake gusar da waxanda aka cusa, a cikin sahun muminai, "Allah bai kasance
zai bar muminai, akan abin da ku ka kasance a kansa ba, face ya rarrabe mummuna
daga mai kyau"
[Ali-imrani: 179].
Kuma jarabawa salo ne na
tarbiyya, wanda Allah ke tsamar da mutumin da ya rubuta masa rabo irin na
shiriya, ta hanyar jarraba, sai ya tashi daga barcin gafalarsa, ya qara
fiskantar Ubangijinsa, ya kuma koma ga
addinin Allah.
Ya ku, bayin Allah !! …
Cikin tarin jarabawar
rayuwa masu yawa, da fitintinu, haqiqa abin qi na qara girma, kayan vacin rai
na qara tsanani, yayewar bala'i na qara jinkiri, har zaton xabe tsammani ya
tabbatu a zukata, to "Ko kuna zaton ku shiga aljanna, tun gabanin misalin
waxanda su ka shuxe gabaninku bai zo muku ba? Wahaloli da cuta sun shafe su,
kuma aka girgiza su, har manzonsu da waxanda su ka yi imani tare da shi, su ce:
Yaushe nasarar Allah za ta zo?" [Baqara: 214].
To, a irin wannan yanayi,
wajibi ne a nemi mafaka daga Allah, kuma a kyautata masa zato, saboda a wurin
Allah akwai mafita daga kowani kunci, da yayewa daga kowani baqin ciki, kuma
Allah yana wurin kyakkyawan zaton bayinsa muminai, domin Allah baya tavar da
zaton wanda ya kyautata masa zato.
Ya ku taron musulmai !! …
Lallai watsa natsuwa da
albishir, da tayar da fata a cikin zukata, a lokacin tashin hankali da tsoro,
manhaji ne na qur'ani, kuma shiriya ce ta Manzon Allah (S.A.W),
Allah (تعالى) ya ce wa Musa da Haruna (عليهما السلام) domin su fiskanci qetare iyakar Fir'auna :
"Kada ku ji tsoro, lallai Ni ina tare da ku, ina ji, ina gani" [Xaha: 46].
Kuma annabi Yusuf (عليه السلام) ya ce wa xan'uwansa, bayan abinda ya auka
musu na bala'i: "Lallai ni xan'uwanka ne kada ka yi baqin ciki dangane da abin da su
ka kasance su ke aikatawa" [Yusuf: 69 ].
Kuma annabi Shu'aibu ya ce
wa Musa (عليه السلام), bayan an yi zaman mitin
don ganin an kashe annabi Musa, bayan kuma ya fita daga garin Fir'auna a ankare
(yana jiran me zai faru da shi): "Kada ka ji tsoro, ka tsira daga mutane
azzalumai"
[Qasas: 25].
Kuma annabinmu Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) ya ce wa sahibinsa Abubakar (رضي الله عنه) alhalin suna cikin kogo: "Ya
Ababakrin! Menene zatonka ga mutane biyu, wanda Allah shi ne na ukunsu, Kada ka yi baqin
ciki, lallai Allah yana tare da mu" [Tauba: 40].
A yaqin Badar yawan rundunar musulmai sun kasance mutane
xari uku ne da goma sha wani abu, adadin mushirkai kuma ninkin musulmai har uku,
kuma rashin kwanciyar hankali ya dabaibaye rundunar musulmai wanda bata yi
shiri ko tanadin yaqi ba, kuma adadinsu bai cika ba, haka tanadinsu, a lokacin
da su ke jiran bataliyar (mushirkai) mai qarfi, wanda ta ninninka su, bayan kuma
adadinsu ya cika, da tanadinsu. To a cikin wannan yanayin ne, sai ayoyin
qur'ani waxanda su ke sanya natsuwa, kuma su ke tayar da fata, a cikin rayukan
musulmai, kuma su ke zaburar da su, su ke qarfafa zukatansu, kuma su ke jansu
zuwa ga fito-na-fito, su ka sassauka, Ku saurari faxin Allah (تعالى) lokacin da ke magana da ManzonSa: "Kuma a lokacin da
Allah ke nuna maka su, a cikin barcinka (mafarki), suna kaxan, kuma da ya nuna
maka su, suna dayawa, lallai da kun ji tsoro, kuma lallai da kun yi jayayya a
cikin lamarin, sai Allah ya tsare ku, lallai shi masani ne na abinda ke cikin qiraza
* kuma a lokacin da ya ke nuna muku su, a lokacin da kuka haxu (a fagen daga),
a cikin idanunku suna kaxan, kuma ya qarantar da ku a cikin idanunsu, domin
Allah ya hukunta al'amarin da ya kasance abin aikatawa, kuma izuwa ga Allah ake
mayar da al'amura"
[Anfal: 43-44].
Abdullahi bn Mas'ud (رضي الله عنه) ya ce: "Haqiqa an
qarantar da adadinsu a cikin idanunmu, har na ke ce wa wani mutumin da ke gefena,
kana ganin sun kai saba'in? Sai ya ce: Ina ganin sun kai xari. Ya ce: sai mu ka
kama wani fursuna daga cikinsu, sai mu ka ce masa: Nawa ne yawanku? Sai ya ce:
mu dubu ne".
Kuma mun samu, alqur'ani yana tabbatar da irin wannan
salo, ta wani yanayin na daban, a qissar wannan yaqin, domin alqur'ani ya tayar
da kyakkyawar fata a cikin rayukan musulmai, kuma ya tabbatar musu da samun
nasara, yana kuma alqawarta musu cewa zai gadar musu da qasa, a inda Allah (تعالى) ya ke cewa: "Kuma a lokacin da
Allah ke muku alqawarin (bada nasara akan) xayan qungiyoyi biyu, cewa lallai
ita, ta ku ce, kuma kuna burin lallai qungiyar da bata da qaya (ko makamai) ta
kasance gare ku, kuma Allah yana nufin ya tabbatar da gaskiya, da kalmominSa,
kuma ya katse qarshen kafirai * domin ya tabbatar da gaskiya, kuma ya vata
qarya, koda kuwa masu laifin (kafirci) sun qi" [Anfal: 7-8].
Ya ku bayin Allah !! …
Haqiqa
tarbiyyar Manzon Allah (صلى
الله عليه وسلم) (ga mutane) ta kasance daidai, ko akan wannan manhaji, saboda Annabi
ya kasance idan vacin rai ko baqin ciki ya dami musulmai, ko kuma ya tsorace wa
zukatansu wani tsoro ko rashin kwanciyar hankali, da xebe tsammani, to sai ya
kunno ruhin fata, ya watsa natsuwa, da aqidar amintuwa da Allah a cikin zukatan
mutane,
Wannan ya sanya, lokacin da
rundunoni suka taru a yaqin ahzab, domin su yaqi Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), kuma su ka gayyato sojoji guda dubu goma
(10,000), kuma musulmai yanayinsu ya kasance a cikin hali na qunci, ga kuma
yanayin tsoron da ya dabaibaye rayukansu, har ya kasance xaya daga cikinsu baya
iya fita domin ya biya buqatarsa, kuma yunwa ya tsananta a gare su, har su kan
xaure dutse ga cikinsu, kuma kwanaki masu yawa su kan shige, ba tare da sun samu
abincin da za su ci ba, ko sauran abin xanxanawa. Kuma sanyin funturu ya
fiskance su a lokacin motsawarsa da tsananinsa.
Yaudara kuma da ha'inci da
munafurci sun samu damar shiga cikin sahun musulmai kamar yadda hakan it ace al'adarsu,
domin su kekketa qarfin musulmai, ,,, Kuma haqiqa alqur'ani ya siffanta halinsu
a inda ya ke cewa: "A lokacin da su ka zo muku ta sama da ku, da ta qasa
daga gare ku, kuma a lokacin da gani su ka karkata, kuma zukata su ka kai ga
maqosai, kuma ku ka yi zaton zace-zace (munana) game da Allah * a can aka
jarrabi muminai, kuma aka girgiza su girgizawa mai tsanani" [Ahzab: 10-11].
A irin wannan yanayin ne
kuma
Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya fara tayar da fatan alkhairi a cikin
rayukan sahabbansa, kuma ya rayar da aqidar jin amintuwa da natsuwa a cikin
zukatansu, yana mai alqawarta musu samun
nasara, da cewa za su gaje duniya, kuma yana musu busharar samun nasara
mabayyaniya, sai ya musu alqawarin samun mabuxan taskokin Rumawa da Farisa da
San'a'a, ,,,
An ruwaito daga Albara'a bn
Azib (رضي الله عنه) ya ce: "Yayin da
Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya umurce mu da tonon gwalalo (wato:
khandaq) sai wani dutse ya bijiro mana daga cikin wannan ramin, wanda ya qi
karvar bugun gaturra, sai mu ka kai kuka ga Annabi –صلى الله عليه وسلم-,
sai ya zo ya xauki gatari, ya ce: Bismillahi, sai ya yi duka guda, sai ya karya
xaya bisa ukunsa 1/3, sannan ya ce: Allahu akbar, an bani
mabuxan qasar Shaam, wallahi! a yanzu na ga benayensu jajaye. Sannan ya yi duka
na biyu, sai ya karya xaya bisa ukun 1/3,, sai kuma ya
ce: Allahu akbar, an bani mabuxan qasar Farisa, wallahi! lallai ne ni na ga
benen garin Mada'ina farare. Sai kuma ya yi duka na uku, kuma ya ce:
Bismillahi, sai ya sare sauran dutsen, sannan ya ce: Allahu akbar, an bani
mabuxan qasar Yaman, wallahi! lallai ni ina ganin qofofin garin San'a'a daga
wurina wannan, a wannan lokacin".
Kuma mala'ika Jibrilu ya
bani labari cewa lallai al'ummata za ta samu xaukaka akansu, ina muku albishir.
Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya yi albishir a gare su, da abinda zai
kasance na shigar da musulunci a waxannan garurrukan, alhalin sahabbai (a
lokacin) an hana su shigi-da-fici a jikin gololon khandaq, ga sanyi yana
dukansu, da kuma yunwa (mai tsanani).
Su kuma munafikai (a lokacin), haqiqa halinsu ya siffantu
da tsoro (matsananci), da tsegumi, tare da qin taimakon muminai, sai su ka yi
izgilanci daga wannan albishir (na Manzon Allah S.A.W), har su ke cewa: YANA MANA ALQAWARIN SAMUN
TASKOKIN SARKIN KISRA DA QAISARA, ALHALIN XAYANMU BAYA IYA FITA DOMIN KASHI, "Allah da Manzonsa
basu mana alqawarin komai ba face ruxi" [Ahzab: 12].
Amma su kuma musulmai (masu
gaskata Allah da Manzonsa) sai su ka natsu, kuma su ka ce: "Wannan ne abinda
Allah da Manzonsa su ka yi mana alqawari, kuma Allah da Manzonsa sun yi
gaskiya, kuma wannan bai qara musu komai ba face imani da sallamawa" [Ahzab: 22].
Allah ya yi mini albarka NI
da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman
gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi,
Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai
gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Yabo na Allah ne shi kaxai;
ya cika alqawarinsa,
ya taimaki bawansa,
ya kuma ruguza qungiyoyin
kafirai shi kaxai xinsa.
Salati da sallama su qara
tabbata ga wanda babu wani annabi a bayansa.
Ya ku taron
musulmai !! …
Ku sani! Lallai ne Allah ya
rubuta rinjaye, ga wannan addinin, da ma'abutansa,
kuma ya yi alqawarin bada
nasararsa ga musulmai, a inda ya ce: "Allah ya rubuta cewa: Lallai zan yi
rinjaye Ni da Manzannina, Lallai Allah Mai qarfi ne Mabuwayi" [Mujadala: 21].
Kuma ya ce: "Ya ku waxanda su ka
yi imani, idan ku ka taimaki Allah, zai taimake ku, kuma ya tabbatar da
dugaduganku"[Muhammadu:
7].
Kuma ya ce: "Kuma lallai Allah
zai taimaki wanda ya taimake shi, lallai ne Allah Mai qarfi ne Mabuwayi" [Haj: 40].
Kuma koda musulmai sun qi taimakon addininsu, to lallai
Allah zai taimaki addininSa, kuma zai zo da wasu mutanen da za su tsaya (su
rungumi lamarin) addini, Allah (تعالى) ya ce: "Ya ku waxanda su ka yi imani duk wanda ya
yi ridda daga addininsa, to, Allah zai zo da wasu mutane, yana sonsu, kuma suna
sonsa, masu tawali'u ga muminai, masu izza ga kafirai, suna yin jihadi a cikin
hanyar Allah, kuma ba su tsoron zargin wani mai zargi" [Ma'ida: 54].
Kuma ya ce: "Kuma idan kuka juya
baya, zai musanya waxansu mutane wanda ba ku ba, sa'annan ba za su kasance
kwatankwacinku ba"
[Muhammadu: 38].
Kuma duk yadda sabuban su ka jujjuya, halayen su ka
caccanza, to lallai musulmai suna cikin alkhairi madawwami, "Kuma kyakkyawar
makoma ta masu taqawa ce" [Qasas: 83].
Kuma ya tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai shi ya ce: "Mamakin lamarin
mumini, lallai lamarinsa dukansa alheri ne, kuma babu hakan ga wani face
mumini, Idan abin farin ciki ya same shi sai ya yi godiya, sai hakan ya zama alheri
a gare shi, Idan kuma cuta ce ta same shi sai ya yi haquri sai hakan ya kasance
alkhairi a gare shi"
.
Sai ku yi taqawar Allah a cikin rayukanku, kuma ku kiyaye
xebe tsammani, da xabi'ar tsegumi a lamarin al'ummarku, saboda hakan makamin
yaqi ne, sannan kaidin maqiyanku su ke qoqarin cuso shi a cikin sahunku.
Kuma ku yi bushara, ku yi kyakkyawar fata, ku amintu da
Allah, sai ku zama waxanda su ka fi xaukaka, "Lallai kalmarmu ta
yi rigaye ga bayinmu manzanni, lallai su, sune masu samun nasara, kuma lallai
rundunarmu, su ne masu yin galaba"' [safat: 83].
Kuma kada rinjayen qarfin varna ya ruxe ku, domin Allah,
mai rinjayar lamarinsa ne, koda kafirai sun
qi.
Ya Allah! Ka
xaukaka musulunci da musulmai, kuma ka qasqantar da shirka da mushirkai, ka
bada nasara ga bayinka masu tauhidi,
kuma –ya Allah- ka sanya wannan qasar ta
zama cikin aminci da zama lafiya da sauran qasashen musulmai.
Ya Allah! Ka bamu aminci a cikin qasashenmu,
kuma ka gyara shugabanninmu masu jivintar lamuranmu.
Ya Allah! Ka datar da majivincin
lamuranmu da datarwarka, ka qarfafe shi da qarfafawarka, kuma ka bada buwaya wa
addininka da shi, Ya Allah! Ka
datar da shi, da masu na'ibtarsa zuwa ga abinda a cikinsa alkhairin musulunci
da musulmai ya ke, kuma zuwa ga abinda gyaruwar qasa da bayi su ke, Ya
Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka bada nasara ga
rundunoninmu da su ke ribaxi, akan iyakoki, Ya Allahn ka daidaita jifansu, kuma
qarfafa niyyoyinsu, ka taimake su da taimakonka, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka karvi shahidansu, kuma ka
warkar da marasa lafiyansu, kuma ka warkar da karyayye daga cikinsu.
Ya Allah! Ka kare su cikin iyalansu da
dukiyoyinsu da zurriyarsu, ya Mafi rahamar masu rahama.
Ya Allah! Ka gyara halayen musulmai a
kowani wuri, Ya Allah ka kasance (mai taimakon) 'yan'uwanmu a qasar Sham.
Ya Allah! Ka yaye baqin cikinsu, ka
xauke cutarsu, ka jivinci lamuransu, kuma ka gaggauta yayewar matsalolinsu,
kuma ka haxa kansu ya Ubangijin talikai.
Bayin Allah
"Lallai ne, Allah da
Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku
yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa
Annabi Muhammadu, kuma ka yarda da khalifofinsa shiryayyu masu shirayarwa; Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran
sahabbai gabaxaya, ka haxa da mu, da baiwarka, ya mafi baiwar masu kyauta.
,,, ,,, ,,,
No comments:
Post a Comment