HUXUBAR
MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 22 /RabiyusSaniy/1438H
daidai da 20/ Janairu/ 2017M
LIMAMI
MAI HUXUBA
DR.
ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY
TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
MAXAUKAKIYAR
HIMMA
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Auwadh As-subaity –Allah ya kiyaye
shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: MAXAUKAKIYAR HIMMA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna,
بسم الله الرحمن
الرحيم
HUXUBAR FARKO
Bayan haka:
Jin zuwa albishir, da fatan samun alkhairi, suna daga qa'idodin musulunci, da
xabi'ar musulmai, a cikin kowani hali, Allah ta'alah yana faxa ta harshen
annabinsa; Ibrahim (عليه السلام):
"Kuma babu mai xebe
qauna daga rahamar Ubangijinsa face vatattu" [Hijr: 54].
Kuma busharar jin cewa alkhairi ne ke tafe, yana haifar da kuzari (qarfin jiki),
kuma yana zaburar da himmomi, yana kuma tunkuxa mutane zuwa ga aiki, kuma yana
samar da rayuwar gaba, mai kyau (ga xaixaiku da al'umma).
Kuma duk lokacin da wani abu, mai vata wa musulmai rai, wutarsa ta
kunnu, a wani wuri a bayan qasa, sai buqatar tuno ko halarto da ababen albishir
ya qara qarfi, Kuma wannan shine shiriyar Manzon al'umma; annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم); domin
sau dayawa, ya juya bala'i da kyakkyawar fatansa, izuwa ga ni'ima, ya kuma
tayar da fatan kyau, daga cikin raxaxi.
Yana daga manyan ababen janyo farin ciki da sabubban albishir a
rayuwar mumini, Yaxuwar addinin
Ubangijin halittu, da shiryiwar waxanda ba musulmai ba zuwa ga musulunci.
Yaxuwa kuma, cikin gaggawa yana daga tabbatattun ababen da
musulunci ya kevanta da su, waxanda su ka fito daga musuluncin, kuma (hakan yak
an kasance) a kowani lokaci da zamani, koda mabiyan musuluncin sun yi qaranci,
ko masu taimakonsa sun yi sakaci, ko maqiyansa sun tsananta.
Saboda musulunci ya fara ne daga Makkah, daga mutane 'yan kaxan
masu rauni (da ake qara raunana su); waxanda su ka sha nau'ukan kamun qeta da
cutarwa, Amma a cikin taqaitattun shekaru, sai musulunci ya shiga ko-ina a
tsibirin larabawa (Jaziyratul Arab). Sai kuma aka samu al'ummar da ta xauki
saqon musulunci tana yaxa shi, a tudu da kwari, da cikin duwatsu da faqo, sai
sautin musulunci ya yaxu, kuma faxaxuwarsa ta yalwata; sai al'ummai su ka shiga
cikinsa, jama'a-jama'a, da saurin da ba a san irinsa, a tarihi ba. Wannan kuma
yana daga manya-manyan mu'ujizozi, kuma gaskatawar alqawarin Allah ne, da ke nuna
cewa, kyakkyawan gobe na addinin musulunci ne.
Msulunci yana yaxuwa ne, saboda shi ne addinin da Allah ta'alah ya
yarda da shi ga mutane gabaxaya, kuma ya xauki alhakin kiyaye shi, da yaxa shi,
Allah (تعالى) yana
cewa: "Shi ne wanda ya turo ManzonSa da shiriya da addinin gaskiya domin ya
rinjayar da shi akan addinai gabaxaya, kuma Allah ya isa Mai shaida" [Alfat'h
28].
Kuma Manzon Allah
(صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai wannan
addinin zai kai wurin da dare da yini su ka kai, kuma Allah ba zai bar gidan
laka ko na tanti ba, face ya shigar da wannan addinin, da buwayar mai buwaya,
ko da qasqancin maqasqanci, wanda zai samu buwaya da buwayar Allah, a cikin
islama, kuma ya qasqantar da shi a cikin kafirci", Alhakim a
cikin almustadrak ya ruwaito shi.
Mutane kuma, sun so musulunci ne; saboda alamominsa a bayyane su ke, kuma (shi,
wato musulunci) gaskiya ne da ta ke a fili, wanda ya dace da fixirar da aka
halicci mutane akanta miqaqqa, da hankula madaidaita, kuma musulunci ya haskaka
duffai, ya sanya rayuka cikin sa'ida, kuma ya yaye qiraza, "Halittar Allah ne
wanda ya halicci mutane akanta, babu canji ga halittar Allah" [Rum: 30].
Musulunci yana yaxuwa ne saboda aqida ne na imani, wacce ta ke cike, ko qosar
da guraben da su ke cikin zukata, kuma ta ke tsarkake ximuwar rayuka, ta cike
filin da ke cikin tunani, kuma ta ke amsa buqatun rayuka, ta basu aminci, ta
qosar da qishinsu.
Mutane suna shiga cikin addinin Allah, jama'a-jama'a ne, saboda shi ne addinin
da ya tabbatar wa mutum karamarsa da darajarsa, kuma ya xaukaka mutum; ta
vangaren ruhi da jiki, da hankali da zuciya, da nufi da soyayya, ya buxe masa
qofofin sama, ya hore masa duniya, bai kuma haramta masa abubuwa masu daxi ba.
Kyakkyawar safiya tana ga wannan addinin, saboda abinda ake
gani na tasirinsa mai girma; wanda ba a iya siffantawa, da aikinsa mai girma
wanda ba a iyakance shi, domin ya ciro mutum daga qasqanci irin na savo, zuwa
buwayar xa'a, haka, ya kan fitar da mutum daga iyakokin duniya zuwa ga yalwar
gidan dawwama (aljanna), yana kuma fitar da shi, daga qaiqashewar zukata, zuwa
ga farfajiya irin ta soyayya, da kuma rahama faffaxa.
Musulunci yana yaxuwa ne; saboda yana daraja ilimi, kuma yana
karrama maluma, kuma yana yin yabo ga hankali da tunani. Kuma duk lokacin da addinin
musulunci ya isa wani gari, daga cikin garurruka, to sai ya qawata shi da
ilimi, ya haskaka shi da sani; Sai wannan al'ummar (musulmai) su ka bada
gudumawa wajen gina ilimi da wayewa ga mutane, kuma sai wayewar musulunci ta
wayi-gari ita ce gadar da ta haifar da dukkan wayewar da su ka yi ta zuwa (a
duniya) a bayan juna.
Mutane sun natsu da musulunci ne, saboda yana tabbatar wa mutane
adalci a cikin zamantakewa, ta dukkan vangarorin rayuwa, kuma shi ne ya qarfafa
igiyar 'yan'uwanta, kuma ya rayar da qa'idodin taimakakkeniya, ya kuma assasa
ma'anoni irin na zamantakewa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kuma xayanku ya
tafi, tare da xan'uwansa; wajen biya masa buqata, shi ya fi falala akan ya yi i'itikafi
a masallacina wannan; na tsawon wata biyu –sai ya yi nuni da yatsarsa-", Alhakim
ya ruwaito shi, a cikin Mustadrak xinsa.
Adalci a musulunci, abun nuninsa mai haske ne, kuma fahimta ce
tabbatatta, wanda ma'aunin wannan fahimtar baya tasirantuwa da matsayi ko
dangantaka, ko daraja ko dukiya,
kuma suna cin
gajiyar adalci, dukkan waxanda su ke zaune a qasar musulunci; Musulmai ne, ko
wasunsu, Allah ta'alah yana cewa: "Ya ku waxanda su ka yi imani, ku kasance
masu tsayin daka domin Allah, masu shaida da adalci, kuma kada qiyayyar wasu
mutane ta xauke ku, a kan ba za ku yi adalci ba, ku yi adalci domin shi ne mafi
kusa da taqawa, kuma ku bi Allah da taqawa, lallai Allah Masani ne ga abinda ku
ke aikatawa" [Ma'ida: 8].
Kuma alhakin yaxa musulunci yana rataya ne ga wuyan musulmai, da
isar da shi ga dukkan saqon duniya, farawa da annabinta (صلى الله عليه وسلم), Allah
ta'alah yana cewa: "Ya kai wannan Manzo, ka isar da abinda aka saukar zuwa
gare ka daga Ubangijinka" [Ma'ida: 67].
Kuma Manzon Allah
(صلى الله عليه وسلم) ya
ce: "Ku iyar mini koda aya xaya ce", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma haqiqa Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya bi dukkan sabuban
faxaxa lko yaxa musulunci, wannan ya sanya a lokacin da Abu-zarri Algifariy (رضي الله عنه) ya
musulunta sai Annabi ya umurce shi da ya zauna a cikin qabilar Xiyan-gifar (بنو غفار), domin ya musu da'awa
zuwa ga musulunci, haka kuma a lokacin da Axxufail bn Amru Ad-dausiy ya
musulunta sai ya umurce shi da ya zauna a cikin qabilarsa; Daus (دوس), domin ya riqa yaxa
musulunci a cikinsu.
Musulmi ana umurtarsa da yin aiki domin yaxa musulunci, sai dai ba
a wajabta masa ya tilasta mutane kan karvar addini da qarfi ba, da kuma tursasa
musu akansa tursasawa, Allah ta'alah ya ce: "Ba komai ba ne
akanka face isarwa" [Shurah: 48].
Kuma Allah
ta'alah ya ce: "Ba akanka shiriyarsu ta ke ba, sai dai Allah shi ke shiryar da wanda
ya ke so" [Baqara: 272].
Kuma alhaki ko nauyin yaxa musulunci ya kan kai, qololuwarsa, a
wajen musulmin da ya rabu da qasarsa; zuwa ga qasashen waxanda ba musulmai ba,
sawa'un ya kasance ambasada ne, ko wanda aka tura karatu, ko attajiri, ko
ma'aikaci.
Aikin yaxa musulunci, yana daga mafi girman falaloli, da martabobi
mafi xaukaka, Allah ta'alah ya ce: "Babu wanda ya fi kyan magana fiye da wanda
ya yi kira zuwa ga Allah, kuma ya aikata aiki na kwarai, kuma ya ce: Lallai ni
ina cikin musulmai" [Fussilat: 33].
Kuma Manzon Allah
(صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Kuma Allah, ya
shiryar da mutum xaya ta hanyarka, ya fi maka alkhairi fiye da jajayen raquma", Bukhariy
ya ruwaito shi, da Muslim.
Kuma za mu iya bada tabbacin cewa, lallai babban abinda ya fi
taimakawa magabata wajen yaxa musulunci shi ne, tarihinsu mai haske, cikin
shigar da musulunci garurruka, da adalcinsu cikin hukunce-hukuncensu, da
xabi'unsu, ta fiskar riqo da addini, da kamun kai, da tsayuwa akan dokokin
addini.
Daga
cikin nagaba-gaba wajen aikata hakan kuma, akwai jagororin buxa garurruka da
shigar musu da musulunci da rundunoninsu, waxanda su ka kasance masu da'awa, ba
mayaqa ba, saboda waxanda su ka yaxa musulunci (a tarihi); Sun siffantu da
tsarkin zukata, da kuma tsarkin rai, da ji soyayya maxaukakiya,
kuma kowani xaya
daga cikinsu, mavuvvuga ne da ke kwararar da alkhairi da rahama, kuma ya ke
tultular da amfanarwa da albarka.
Hanyar da ta fi yawan tasiri wajen isar da musulunci, ita ce isar
da Alqur'ani mai karamci zuwa kunnuwan mutane, kuma cikin ayar da ke tafe,
akwai qarfafa muhimmancin jiyar da mushirkai alqur'ani mai girma, Allah ta'alah
ya ce: "Kuma idan wani daga cikin mushirkai ya nemi makwabtaka da kai, to ka
karvi bakwabtakarsa, har ya ji maganar Allah, sannan ka isar da shi ga wurin
amincewarsa, Wannan kuma saboda su mutane ne da ba su sani ba" [Tauba: 6].
Kuma masu himmatuwa wajen yaxa musulunci sun san muhimmancin
sadarwa ta zamani, da kuma amfani da hanyoyin ci-gaba na kafafen zamani wajen
yaxa da'awa.
Kuma
duk da sakacinmu wajen yaxa musulunci, sai dai Allah ya hore waxannan kafofi ko
minbarorin sadarwa, masu aikin tasiri, in har masu aiki da su sun kyautata
amfani da su, a duniyance, domin isar da rangwamen musulunci da sauqinsa, da
kuma tsayawa a fiskar wanda ke qoqarin munana fiska ko kamar musulunci, wato, masu
sanya masa dabaibayin (da zai hana yaxuwarsa).
Kuma ba abu ne da ke vuya ba, cewa lallai musulunci lokaci bayan
lokaci, yana fiskantar munanta surarsa don ta zama abar qi, da yi masa qarya da
zalunci, da manna masa tuhumar tsanani da ta'addanci, ga shi musuluncin (kansa)
da kuma mabiyansa, ta hanyar hotuna katun, da faya-fayen kafafen sadarwa
mabanbanta, domin tsoratar da mutane daga addinin musulunci, da riya cewa;
musulunci mavuvvugar shakku ne, da koma-baya ko ci-baya, da munanan abubuwa,
Sai dai kuma, dukkan waxannan basa canza komai daga haqiqanin
musulunci, kuma basa sace guiwar 'ya'yansa; musulmai, kuma basa dusashe hasken
musulunci mai haskakawa, ko kuma kyansa mai walqawa, Allah yana cewa: "Kuma suna nufin su
dusashe hasken Allah da bakunansu, Allah kuma yana cika haskensa, koda kuma
kafirai suna qi" [Saff: 8].
Kuma Allah
ta'alah ya ce: "kuma Allah yana qi, face ya cika haskensa, koda kafirai sun qi " [Tauba: 32].
Sun
riya, karkatattun magana da qarya cewa, wai musulunci ya yaxu ne da kaifin
takobi,
sai dai kuma,
musulunci bai tilasta wani ya canza aqidarsa ba, kuma tarihi ya rubuta, da
tawadar gaskiya da adalci, cewa lallai musulunci ya yaxu ne da hujjoji
maxaukaka, da kuma dalilai bayyanannu, da kuma tausasawa, da adalci, Allah
ta'alah ya ce: "Babu tilastawa a cikin addini, haqiqa shiriya ta bayyana daga vata" [Baqara:
256].
Kuma Allah
ta'alah ya ce: "Shin, kai kana tilasta mutane ne, har su kasance masu
imani" [Yunus: 99].
Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya
kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai
hikima, Ina faxar abinda ku ke ji wannan, kuma
ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga
kowani zunubi, Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne
Mai rahama.
,,,
,,, ,,,
,,,
,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Bayan haka:
Lallai sashen musulmai suna aukawa da jahilci, cikin qoqarin munana
kamar musulunci a idon mutane, ta hanyar binsu ga hanyoyi vatattu, da mazhabobi
karkatattu, da manhajojin vata mabanbanta, waxanda su ke kekketa al'ummar
musulmai, kuma su ke kawo rarrabuwa, su ke kuma raunata haxin kansu,
Wannan kuma yana
da mummunan tasiri, da janyo koma-baya wajen aikin yaxa wannan addinin.
Kuma vangaren sadarwa da hanyoyinsa masu yawa, shima yana bada
gudumawa wajen tsayar ko taqaita yaxuwar musulunci, da mummunan tasiri,
ga ingantaccen hoton musulunci a ido, ta hanyar sukar wannan addinin da yin
isgilanci ga wasu daga shugabanninsa, da siffanta su da tsanani da tsanantawa,
da kuma rufewar tunani, ko kuma ta hanyar munana wasu xabi'un (na musulunci).
Kuma ba voyayye ne, ga kwakwale ba, cewa lallai akwai alhaki mai
girma akan musulman qasar masallatan harami biyu; na yaxa wannan addinin, saboda
kasancewar (Makkah) alqiblar musulmai, (Madina) kuma wajen hijiran shugaban
manzanni, (صلى الله عليه وسلم), Allah (تعالى) ya ce: "Kun kasance mafi
alherin al'umma, wadda aka fitar ga mutane, kuna umurni da kyakkyawa, kuma kuna
hani daga abin qi, kuma kuna Imani da Allah" [Ali-imrana: 110].
Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda
Allah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa: "Lallai ne, Allah da
Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku
yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati wa
Annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi salati wa
Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai girma. Kuma
ka yi albarka ga annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi
albarka wa Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai
girma.
Ya Allah! Ka yarda da
khalifofi guda huxu shiryayyu; Abubakar da Umar da Usmanu da
Aliyu, da iyalan annabi da sahabbai masu karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da
rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
kuma ka qasqantar
da kafirci da kafirai, kuma
Ya Allah! Ka ruguza maqiyanka; maqiyan addini,
Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin
nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
Ya Allah! Ka kasance wa musulman da ake raunata
su a kowani wuri, ka kasance musu, Mai qarfafawa, Mai basu nasara, kuma Mai
taimako,
Ya Allah! Ka kasance wa musulman a garin Halab,
da Shaam, da Mausil, da Iraqi, da Filasxinu, da kowani wuri ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka kasance musu, Mai qarfafawa, Mai
basu nasara, kuma Mai taimako,
Ya Allah! Lallai su, masu jin yunwa ne ka
ciyar da su, basu da takalma ka basu, tsirara su ke, ka tufatar da su, kuma an
zalunce su, ka taimake su, Ya Allah lallai ne su an zalunce su, ka taimake su,
Ya Allah lallai ne su an zalunce su ka taimake su,
Ya Allah! Duk wanda ya nufe su da mummuna to
ka sanya kaidinsa a qirjinsa, kuma ka sanya rugujewarsu cikin tsare-tsarensu,
Ya Mai amsa addu'a
Ya Allah ka
rarraba kan maqiyansu, kuma ka wargaza haxuwarsu, ka sanya mummuna ya juyo
akansu, Ya Ubangijin talikai,
Ya Allah Wanda ya
saukar da littafi, wandas ke gudanar da gajimare, Mai ruguza qungiyoyi, ka
ruguza maqiya musulmai, kuma ka taimake musulmai akansu, Ya Ubangijin talika,
Ya Mai tsananin qarfi.
Ya Allah! Lallai ne mu muna
roqonka aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah! Ka gyara mana
addininmu, wanda shine qashin bayan lamarinmu, kuma ka gyara mana duniyarmu
wacce rayuwarmu ta ke cikinta, kuma ka gyara mana lahirarmu wanda zuwa gare ta
ake mayar da mu, kuma ka sanya rayuwa ta zamo qari a gare mu daga kowani
alkhairi, kuma ka sanya mutuwa ta zama hutu a gare mu daga aikata kowani
sharri, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka mabuxan
alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, da
zahirinsa da baxininsa, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna,
Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka taimake mu, kada ka taimaki
maqiya akanmu, ka bamu nasara, kada ka basu nasara akanmu, ka qulla mana, kada
ka qulla musu akanmu, ka shiryar da mu, kuma ka sauqaqe shiriya a gare mu, ka
bamu nasara akan wanda ya zalunce mu,
Ya Allah! Ka sanya mu mu zama masu
ambatonta, masu gode maka, masu tsoro a gare ka, masu yin kuka a gare ka, masu
mayar da lamari,
Ya Allah! Ka karvi tubanmu, ka wanke
zunubanmu, kuma ka tabbatar da hujjarmu, ka daidaita harsunanmu, kuma ka cire
dauxar zukatanmu.
Ya Allah! Lallai muna neman tsarinka daga
gushewar ni'imominka, da canzawar lafiyarka, da zuwan azabarka kwatsam, da kuma
dukkan fushinka.
Ya Allah! Ka yi rahama ga mamatanmu, ka bada
waraka ga marasa lafiyanmu, kuma ka jivinci lamuranmu, kuma ka sa mu cika da
alheri, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah! Ka gyara sha'aninmu dukkansa, kuma
kada ka dogarar da mu zuwa ga kayukanmu, daidai da kyaftawar ido,
Ya Allah! Lallai ne mu muna
roqonka kyakkyawan cikawa, da kuma afuwa kan abinda ya gabata, ko ya kasance
Ya Allah! Ka shumfuxa mana daga
albarkokinka, da rahamarka, da falalarka, da arziqinka
Ya Allah! Lallai mu muna roqonka –ya Allah-
saboda kai ne Allah, wanda babu abin bauta sai kai, kai ne Mawadaci mu kuma mu
ne faqirai, Ya Allah ka saukar mana da ruwan sama, kada ka sanya mu daga cikin
masu xebe tsammani, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama, Ya Allah! Ka shayar
da mu ruwan sama, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama.
Ya Allah!,
shayarwa ta rahama, ba na azaba, ko bala'i, ko rusau, ko nitsewa ba
Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga
abinda kake so, kuma yarda, Ya Allah! Ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma
ka sanya aiyukansa cikin yardarka, Ya Ubangijin talikai.
Ku ka datar da xaukacin jagororin musulmai wajen yin aiki da littafinka da yin
hukunci da shari'arka, Ya Ubangijin halittu.
"Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi
mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf:
23].
"Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana, da 'yan'uwanmuda suka rigaye mu da
imani, kuma kada a zukatanmu ka sanya wani qulli ga waxanda su ka yi imani, Ya
Ubangijinmu lallai kai Mai tausasawa ne Mai jin qai" [Hashr:
10].
"Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a
lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].
"Lallai ne Allah
yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanta, kuma yana yin
hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama
masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku gode masa akan
ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah
ya san abinda kuke aikatawa.
,,,
,,, ,,,