2015/08/06

MUHIMMANCIN HUDUBAR JUMA'A A MUSULUNCI أهمية خطبة الجمعة في الإسلام








MUHIMMANCIN HUXUBAR JUMA'A A MUSULUNCI
(أهمية خطبة الجمعة في الإسلام)




NA
ASH-SHAIKH ABDULMUHSIN AL-BBAD







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Allah ya yi qarin salati da sallama da albarka ga ManzonSa annabinmu Muhammadu xan Abdullahi da iyalanSa, da sahabbanSa, da duk wanda yabi shi.
Bayan haka;
Lallai sha'anin huxubar juma'a a musulunci yana da girma, kuma tana da muhimmancin gaske, fa'idarta kuma tana da girma, amfaninta kuma abu ne mai gamewa, Kuma muhimmancin nata yana bayyana ta waxannan fiskokin;
Na xaya: Lallai yana daga cikin sharruxan sallar juma'a huxubobi guda biyu su rigaye ta, Saboda yin huxuba a ranar juma'a wajibi ne, zuwa da ita kuma gabanin sallah abu ne na dole.
Na biyu: Lallai yinin juma'a yinin idi ne na sati, ita kuma huxubar; huxubar idin sati ne da take maimaituwa a duk bayan kwanaki guda bakwai (sati),  Kuma yana daga cikin dalilan haka; Faxin Annabi (صلى الله عليه وسلم):
«قَدِ اجْتَمَعَ فِي يَوْمِكُمْ هَذَا عِيدَانِ، فَمَنْ شَاءَ أَجْزَأَهُ مِنَ الْجُمُعَةِ، وَإِنَّا مُجَمِّعُونَ».
Ma'ana: "Lallai idi guda biyu sun haxu a cikin yininku wannan, Duk wanda ya so, to idi ya isar masa ba sai ya je sallar juma'a ba, Amma mu za mu yi juma'a",    [Abu-Dawud ya rawaito shi, lamba: 1073, da isnadi hasan, daga Abu-Hurairah].
Kuma ya zo a cikin [SahihulBukhariy, lamba: 5572] daga Abiy-Ubaid ('yantaccen bawan Ibnu-Azhar) yace:
(شَهِدْتُ العِيدَ مَعَ عُثْمَانَ بْنِ عَفَّانَ، فَكَانَ ذَلِكَ يَوْمَ الجُمُعَةِ، فَصَلَّى قَبْلَ الخُطْبَةِ، ثُمَّ خَطَبَ فَقَالَ: «يَا أَيُّهَا النَّاسُ، إِنَّ هَذَا يَوْمٌ قَدِ اجْتَمَعَ لَكُمْ فِيهِ عِيدَانِ، فَمَنْ أَحَبَّ أَنْ يَنْتَظِرَ الجُمُعَةَ مِنْ أَهْلِ العَوَالِي فَلْيَنْتَظِرْ، وَمَنْ أَحَبَّ أَنْ يَرْجِعَ فَقَدْ أَذِنْتُ لَهُ».
Ma'ana: "Na halarci sallar idi tare da khalifah Usman, hakan kuma ya kasance a ranar juma'a, Sai yayi sallar idin gabanin yayi huxuba, sa'annan ya yi huxuba, yace: Ya ku mutane! Lallai wannan yini ne da idi guda biyu suka haxu muku a cikinsa, Duk wanda ya so, ya jira sallar juma'a daga cikin mutanen unguwar awali to ya jira, Wanda kuma ya so ya koma to nayi masa izini".
Ya zo a cikin [Sunan Ibnu-Majah, lamab: 1098, da isnadi hasan ligairihi] daga Abdullahi xan Abbas, daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
«إِنَّ هَذَا يَوْمُ عِيدٍ، جَعَلَهُ اللَّهُ لِلْمُسْلِمِينَ، فَمَنْ جَاءَ إِلَى الْجُمُعَةِ فَلْيَغْتَسِلْ، وَإِنْ كَانَ طِيبٌ فَلْيَمَسَّ مِنْهُ، وَعَلَيْكُمْ بِالسِّوَاكِ».
Ma'ana: "Lallai wannan ranar idi ne da Allah ya sanya shi, Duk wanda zai zo zuwa ga juma'a to ya yi wanka, idan kuma akwai turare to ya shafa wani abu daga cikinsa, kuam ina horonku da yi aswaki".
            Na uku: Lallai halartar masallaci don yin sallar juma'a da sauraron huxubobi guda biyu gabanin haka wajibi ne, saboda faxin Allah (mabuwayi da xaukaka):
{يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا نُودِيَ لِلصَّلاَةِ مِنْ يَوْمِ الجُمُعَةِ، فَاسْعَوْا إِلَى ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا البَيْعَ، ذَلِكُمْ خَيْرٌ لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ تَعْلَمُونَ} [الجمعة: 9].
Ma'ana: "Ya ku waxanda suka yi imani idan aka yi kiran sallah a ranar juma'a, to sai ku taho zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar kasuwanci, Yin haka shi yafi alkhairi a gare ku in kun kasance kun sani", [Jumu'a; 9].
Ita wannan itace huxubar wani abinda tafiya zuwa gare shi yake wajibi, savanin wassu huxubobin waxanda ba na jumma'a ba, waxanda halartarsu ba wajibi ba ne, haka kuma sauraronsu ba dole ba ne. 
            Na huxu: Lallai halin musulmi a lokacin sauraron huxubar juma'a kamar halinsa ne, a lokacin yin sallah; ba zai riqa magana ko yin magana da wani ko yin wani aiki da zai shagaltar da shi ga barin ji ko sauraron huxubar ba, Yana cikin dalilan haka; Faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
"إِذَا قُلْتَ لِصَاحِبِكَ يَوْمَ الجُمُعَةِ: أَنْصِتْ، وَالإِمَامُ يَخْطُبُ، فَقَدْ لَغَوْتَ".
Ma'ana: "Idan kace wa abokinka a ranar juma'a: Ka yi shiru, alhalin limami yana yin huxuba, to lallai ka yi wargi", [Bukhariy ya ruwaito shi, lamba: 934, da Muslim , lamba: 1965].  Da kuma faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
«مَنْ تَوَضَّأَ فَأَحْسَنَ الْوُضُوءَ، ثُمَّ أَتَى الْجُمُعَةَ، فَاسْتَمَعَ وَأَنْصَتَ، غُفِرَ لَهُ مَا بَيْنَهُ وَبَيْنَ الْجُمُعَةِ، وَزِيَادَةُ ثَلَاثَةِ أَيَّامٍ، وَمَنْ مَسَّ الْحَصَى فَقَدْ لَغَا».
Ma'ana: "Duk wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwalar, sa'annan ya zo juma'a sai ya saurara ya kuma yi tsiru, an gafarta masa abinda ke tsakaninsa da tsakanin juma'a, da qarin kwanaki guda uku. Duk wanda kuma ya tava tsakuwa to lallai ya yi wargi", [Muslim ya rawaito shi, lamba: 1988].
            Amma muhimmancin huxuba dangane da limami mai yinta to ya kasance ne saboda halartarta wajibi ne, haka kuma sauraronta, da kuma saboda aikata hakan yana neman mai huxubar ya bada cikakkiyar himmatuwa, da kula na musamman da huxubarsa, sai hakan ya sanya shi ya yi iya qoqarinsa wajen tanadar huxubar, irin tanadar da zai tava ko-ina na maudu'in huxubar, ba kuma tare da ya tsawaita ba, daxin daxawa kuma ana son mai yin huxuba ya rinqa jin cewa huxuba tana da gamammen amfani, da kuma lada ko sakayya mai girma, wannan kuma saboda faxinsa (صلى الله عليه وسلم):
"مَنْ دَعَا إِلَى هُدًى كَانَ لَهُ مِنَ الْأَجْرِ مِثْلُ أُجُورِ مَنْ تَبِعَهُ، لَا يُنْقِصُ ذَلِكَ مِنْ أُجُورِهِمْ شَيْئًا، وَمَنْ دَعَا إِلَى ضَلَالَةٍ، كَانَ عَلَيْهِ مِنَ الْإِثْمِ مِثْلُ آثَامِ مَنْ تَبِعَهُ، لَا يُنْقِصُ ذَلِكَ مِنْ آثَامِهِمْ شَيْئًا".
Ma'ana: "Duk wanda ya yi kira zuwa ga wata shiriya to lallai yana da lada kwatankwancin ladan waxanda suka bi shi, kuma hakan ba zai tauye komai daga ladansu ba. Kuma duk wanda ya yi kira zuwa ga wata vata to yana da zunubi akansa kwatankwacin zunuban waxanda suka bi shi; kuma hakan ba zai tauye komai daga zunubansu ba", [Muslim ya rawaito shi, lamba: 6804, daga Abu-Hurairah (رضي الله عنه)].
Kuma ya dace huxubar ta zama a rubuce, wannan kuma saboda rubuta ta zai tattara duk abinda yake waste na wannan maudu'in, kuma shi zai haifar da samun nitsuwa wajen cewa huxubar ta samu sifa ta gamewa, tare da kuvuta daga kubcewan wassu daga cikin ma'anoni masu muhimmanci, ko dalilan da a lokacin huxubar za su qi zuwa a kwakwalwarsa; idan har limamin ya yi huxubar daga kansa; ba daga abinda ya rubuta ba.
Kuma yana da muhimmanci sosai, mai yin huxuba ya kula wajen koro dalilai, daga littafin Allah (alqur'ani), da hadisai, da maganganun magabata, tare da komawansa (limami) izuwa ga littatafan da suka haxa ko tattara, maganganun salaf (magabata) da suke magana akan maudu'ai da yawa, musamman littatafan baya-baya, waxanda suke fitar da waxannan maganganun daga littatafa masu girma, kamar littafin siyaru a'alamu annubala'i na Az-zahabiy, da littafin Tarikhu bagdaad na Alkhaxib Albagdadiy, da wassunsu.
            Kuma ita huxubar juma'a tana daidai da darasin sati; wanda halartarsa wajibi ne akan kowani musulmi, kuma musulmi ya kan fahimci addininsa a cikinta; sai ya san aqidarsa, da kuma hukunce-hukncen shari'a mabanbanta. Karantar da mutane hakan kuma shine shiriyar Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) , da kuma aikin sahabbansa, a bayansa (Allah ya qara yarda a gare su).   
Kuma yana daga cikin karantarwar Annabi (صلى الله عليه وسلم) ga mutane, da ta sahabbansa, al'amuran addininsu mabanbanta a cikin huxubobin juma'a, Misalan da suke tafe:
(1)            : Hadisin Abdullahi xan Umar (رضي الله عنهما) yace: Naji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana huxuba akan minbari, yana cewa:
«مَنْ جَاءَ إِلَى الْجُمُعَةِ فَلْيَغْتَسِلْ».
Ma'ana: "Duk wanda zai zo zuwa sallar juma'a to yayi wanka", Bukhariy ya ruwaito shi [lamba: 919], da Muslim [lamba: 1925].
(2)            : Hadisin Zainab 'yar Jahsh (رضي الله عنها) tace: Naji manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) akan minbari yana cewa:
«لاَ يَحِلُّ لِامْرَأَةٍ تؤمن بِالله وَالْيَوْمِ الْآخِرِ، أَنْ تُحِدَّ عَلَى مَيِّتٍ فَوْقَ ثَلاَثِ لَيَالٍ، إِلاَّ عَلَى زَوْجٍ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا».
Ma'ana: "Baya halatta ga matar da tayi imani da Allah da ranar qarshe tayi takaba ga wani mamaci fiye da darare uku, Saidai ga miji; watanni huxu da kwanaki goma", Bukhariy ya ruwaito shi [lamba: 1282], da Muslim [lamba: 3725] .
(3)            : Hadisin farko a cikin littafin sahihul Bukhariy ya ruwaito shi ne daga Alqamah xan Waqqas Allaisiy yace: Naji Umar xan Alkhaxxab (رضي الله عنه) akan minbari yana cewa: Naji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
«إِنَّمَا الْأَعْمَالُ بِالنِّيَّاتِ، وَإِنَّمَا لِكل امْرِئٍ مَا نَوَى».
Ma'ana: "Lallai aiyuka suna inganta ne da niyyoyi, kuma kowani mutum yana samun ladan abinda ya yi niyya"… -Har qarshen hadisin.
(4)            : Hadisin Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما) lallai shi ya ji Umar (رضي الله عنه) yana faxa akan minbari:
«لَا تُطْرُونِي كَمَا أَطْرَتِ النَّصَارَى عِيسَى ابْنَ مَرْيَمَ، فَإِنَّمَا أَنَا عَبْدُهُ فَقُولُوا: عَبْدُ اللَّهِ وَرَسُولُهُ».
Ma'ana: "Kada ku qetare iyaka wajen yabona kamar yadda Nasara suka wuce iyaka wajen yabon Isa xan Maryam; Saboda ni bawan Allah ne, sai ku ce: Bawan Allah kuma ManzonSa", Bukhariy ya ruwaito shi [lamba: 3445], kuma Bukharin ya ruwaito shi a wani wurin cikin hadisi mai tsayi [lamba: 6830], Kuma a cikinsa an tabbatar cewa ya faxe shi ne a cikin huxubar juma'a. Kuma Imam Muslim ya ruwaito shi [lamba: 4418], cikin hadisi mai tsayi, saidai kuma babu lafazin (لا تطروني) a cikinsa.
(5)            : Asar ko hadisin da Imam Malik ya ruwaito shi a cikin littafin muwaxxa'a (1/ 90), da ingantaccen isnadi, daga Abdurrahman xan Abdulqariy lallai shi ya ji Umar xan Alkhaxxab (رضي الله عنه) akan minbari yana koyar da mutane yin "tahiya"; Yana cewa:
قُولُوا: «التَّحِيَّاتُ للهِ... ».
Har qarshen hadisin.
(6)            : Asar ko hadisin da Imam Muslim ya ruwaito shi (lamba: 1345), da isnadinsa zuwa ga Abuzzubairu, yace:
((سَمِعْتُ عَبْدَ اللهِ بْنَ الزُّبَيْرِ، يَخْطُبُ عَلَى هَذَا الْمِنْبَرِ وَهُوَ يَقُولُ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ إِذَا سَلَّمَ فِي دُبُرِ الصَّلَاةِ أَوِ الصَّلَوَاتِ)).
Ma'ana: "Naji Abdullahi xan Azzubair yana huxuba akan wannan minbarin, yana cewa: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya kasance idan yayi sallama a bayan sallah, ko kuma salloli yana cewa:", Sai ya ambaci hadisin zikirorin da ake yi a bayan idar da salloli.
(7)            : Hadisin da yake magana kan haramcin qarin gashi, wanda Imamul Bukhariy ya ruwaito shi (lamba: 3486), da isnadinsa, daga Humaid xan Abdurrahman, lallai shi yaji Mu'awuyah xan AbuSufyan (رضي الله عنهما) a shekarar da yayi hajji, akan minbari yana cewa, bayan ya damqi qunshin gashin da ya kasance a hannayen mai suna Harasiy:
«يَا أَهْلَ المَدِينَةِ، أَيْنَ عُلَمَاؤُكُمْ؟ سَمِعْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَنْهَى  عَنْ مِثْلِ هَذِهِ؟ وَيَقُولُ: إِنَّمَا هَلَكَتْ بَنُو إِسْرَائِيلَ حِينَ اتَّخَذَهَا نِسَاؤُهُمْ».
Ma'ana: "Ya ku mutanen Madina ina malumanku suke? Naji Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana hana irin wannan, yana kuma cewa: Lallai banu-Isra'ila sun halaka ne, a lokacin da matansu suka riqi qarin gashi" .

            IbnulQayyim a cikin littafin zadul ma'ad (1/ 188)  yana cewa:
((Kuma ko-yaushe huxubarsa –صلى الله عليه وسلم- ta kan qunshi/ godiya wa Allah da yaba masa akan ni'imominsa, da sifofin kamalarsa da sauran abubuwan da ya cancanci yabo akansu, tare da karantar da qa'idojin musulunci, da ambaton aljannah da wuta, da makoma, da kuma bayyanar da abubuwan da za su sa Allah yayi fushi, da waxanda za su aukar da yardarsa. Wannan shine abinda huxubobinsa –صلى الله عليه وسلم- suke kai-komo akansu)).

            Kuma "maudu'an" huxubar juma'a ya dace su kasance bayani ne kan aqidar magabatan kirki, wacce aka ciro ta daga littafin Allah da sunnar ManzonSa (صلى الله عليه وسلم), da kuma abinda sahabbai masu karamci suka kasance a kansa, da mutanen bayansu da suka tafi akan tafarkinsu, Wani lokaci kuma su kasance bayani ne kan hukunce-hukuncen shari'a cikin ibadodi da mu'amaloli, Wani lokacin kuma su kasance wa'azi ne da suke motsa zukata sannan su yi tasiri ga rayuka, don su haifar da jin tsoron Allah da kuma fatan samun ladanSa, tare da bada kula ta fiskar huxuba ta qunshi ambato dalilai daga littafin Allah da sunnar ManzonSa, da kuma maganganun magabatan kwarai.

               Kuma yana daga cikin muhimman abubuwan da za a riqa tattaunawa akansu a cikin huxubobin juma'a lokaci bayan lokaci: Irin abinda aka jarrabi wassu samari da shi, a qasar haramai guda biyu na Makkah da Madinah, da wassunsu daga cikin qasashen musulmai; na mummunan fahimta ga hukunce-hukuncen shari'a, sakamakon yadda samarin suka nisanci ma'abota ilimi, suka kuma qi fa'idantuwa da su, ko samun nusarwarsu, ko karvar gyara daga wajensu, ko ilmantar da su gaskiya, Sai huxubovin juma'a su riqa qunsar bayanin gaskiya ga waxannan samarin da wassunsu, da fatan su kuvuta daga aukawa cikin munanan fahimtoci, da kuma aikata aiyukan qyama; sakamakon waxannan fahimtocin, na kashe-kashe da qone-qone da rushe-rushe, da tsoratar da waxanda shari'a ta amintar da su; Duka da da'awar cewa hakan yana cikin jihadi, wanda kuma a haqiqa wannan jihadi ne zuwa ga hanyar shexan, domin da wani hankalin ne, ko da wani addini karkashe musulmai da waxanda aka basu alkawarin amintarwa, da rurrusa abinda aka mallaka yake zama jihadi?!   Saboda da bayanin gaskiya ne da fito da shi a sarari, a cikin huxubobin juma'a ko a waninsu, za a samu fa'ida da izinin Allah, kuma a samu kuvuta daga sharrace-sharrace; waxanda mummunan fahimta ga addini yake haifar da su;  Kuma lallai fa'idar da ta kasance ga wassu mutane waxanda suka yi tunanin shiga cikin ra'ayi irin na khawarijawa = fa'idar da suka samu ta kyautata, a lokacin da suka saurari sahabi mai suna Jabir xan Abdullahi (رضي الله عنهما) alhalin yana karantar da mutane wani hadisi, daga cikin hadisan Annabi (صلى الله عليه وسلم) a masallacinSa, saboda ya zo a cikin littafin Sahihu Muslim, da isnadinsa har zuwa ga Yazid Alfaqiir, Yace:  
 ((كُنْتُ قَدْ شَغَفَنِي رَأْيٌ مِنْ رَأْيِ الْخَوَارِجِ، فَخَرَجْنَا فِي عِصَابَةٍ ذَوِي عَدَدٍ نُرِيدُ أَنْ نَحُجَّ، ثُمَّ نَخْرُجَ عَلَى النَّاسِ، قَالَ: فَمَرَرْنَا عَلَى الْمَدِينَةِ، فَإِذَا جَابِرُ بْنُ عَبْدِ اللهِ يُحَدِّثُ الْقَوْمَ، جَالِسٌ إِلَى سَارِيَةٍ، عَنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: فَإِذَا هُوَ قَدْ ذَكَرَ الْجَهَنَّمِيِّينَ، قَالَ: فَقُلْتُ لَهُ: يَا صَاحِبَ رَسُولِ اللهِ، مَا هَذَا الَّذِي تُحَدِّثُونَ؟ وَاللهُ يَقُولُ: {إِنَّكَ مَنْ تُدْخِلِ النَّارَ فَقَدْ أَخْزَيْتَهُ}، وَ {كُلَّمَا أَرَادُوا أَنْ يَخْرُجُوا مِنْهَا أُعِيدُوا فِيهَا}، فَمَا هَذَا الَّذِي تَقُولُونَ؟ قَالَ: فَقَالَ: «أَتَقْرَأُ الْقُرْآنَ؟» قُلْتُ: نَعَمْ، قَالَ: «فَهَلْ سَمِعْتَ بِمَقَامِ مُحَمَّدٍ عَلَيْهِ السَّلَامُ -يَعْنِي الَّذِي يَبْعَثُهُ اللهُ فِيهِ-» قُلْتُ: نَعَمْ، قَالَ: «فَإِنَّهُ مَقَامُ مُحَمَّدٍ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الْمَحْمُودُ الَّذِي يُخْرِجُ اللهُ بِهِ مَنْ يُخْرِجُ»، قَالَ: ثُمَّ نَعَتَ وَضْعَ الصِّرَاطِ، وَمَرَّ النَّاسِ عَلَيْهِ، -قَالَ: وَأَخَافُ أَنْ لَا أَكُونَ أَحْفَظُ ذَاكَ- قَالَ: غَيْرَ أَنَّهُ قَدْ زَعَمَ أَنَّ قَوْمًا يَخْرُجُونَ مِنَ النَّارِ بَعْدَ أَنْ يَكُونُوا فِيهَا، قَالَ: -يَعْنِي- فَيَخْرُجُونَ كَأَنَّهُمْ عِيدَانُ السَّمَاسِمِ، قَالَ: «فَيَدْخُلُونَ نَهَرًا مِنْ أَنْهَارِ الْجَنَّةِ، فَيَغْتَسِلُونَ فِيهِ، فَيَخْرُجُونَ كَأَنَّهُمُ الْقَرَاطِيسُ»، فَرَجَعْنَا قُلْنَا: وَيْحَكُمْ أَتُرَوْنَ الشَّيْخَ يَكْذِبُ عَلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ؟ فَرَجَعْنَا فَلَا –وَاللهِ- مَا خَرَجَ مِنَّا غَيْرُ رَجُلٍ وَاحِدٍ. أَوْ كَمَا قَالَ: أَبُو نُعَيْم)).
Ma'ana: "Na kasance son wani ra'ayi daga cikin ra'ayoyin khawarijawa ya kama zuciyata, sai muka fita a cikin wata jama'a masu yawa da nufin aikin hajji, daga nan sai mu fita wa mutane (mu kafirta su). Yace: Sai muka bi ta garin Madina, sai ga Jabir xan Abdullahi yana karantar da mutane hadisin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), yana zaune a jikin wata fila. Yace: Sai a cikin haka ya ambaci waxanda ake ce musu 'yan jahannama (wato: musulman da za a babbaka su a wutar jahannama, sa'annan a fitar da su), Yace: Sai nace masa: Ya sahabin Manzon Allah, Menene wannan hadisin da kake bayarwa? Bayan kuma Allah yana cewa: ((Lallai kai, duk wanda ka shigar da shi wuta to lallai ka tozarta shi)), da faxinsa: ((Duk lokacin da suka nufi su fita daga wuta sai a sake mayar da su cikinta)), To menene wannan maganar da kake yi? Yace: Sai Jabir yace: Shin ka haddace alqur'ani? Sai nace: E, Na'am! Sai yace: Shin ka ji  matsayar Annabi Muhammadu; ma'ana: wanda Allah zai tayar da shi akanta? Sai nace: E; Na'am! To shine matsayar Annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) abar yabo; wanda Allah (ta'alah) zai fitar da wanda zai fitar (daga cikin wuta). Sai yace: Daga nan sai Jabir ya siffanta yadda siraxi yake, da yadda mutane za su shige ta kansa, Sai maruwaicin hadisin yace: Saidai ina tsoron ya zama ban haddace abinda ya faxa ba! Yace: Saidai kuma tabbas ya riya cewa lallai wassu mutane za su fita daga cikin wuta, bayan sun riga sun kasance a cikinta. Yace: Ma'ana: sai su fice daga cikinta suna kama da kararen rixi. Yace: Sai a shigar da su cikin kogi daga cikin kogunan aljannah, Sai su yi wanka a cikinsa, sannan su fita daga cikinsa suna kama da fefofin takardu (wajen haske).    Sai muka koma (garinmu), Muka ce: Kaitonku! Shin kuna zaton wannan dattijon zai yi qarya wa Manzon Allah?! Daga nan sai muka dawo daga rakiyar ra'ayin khawarijawa, kuma –wallahi- babu wanda ya yi aiki da ra'ayin khawarij daga cikinmu in banda mutum xaya. Ko kamar yadda Abu-Nu'aim ya faxa". Shi kuma Abu-Nu'aim a cikin wannan hadisin shine mai suna:  Alfadlu xan Dukain, wanda kuma xaya ne daga cikin mazajen da suka ruwaito wannan hadisin.  
Kuma malamin tafsiri mai suna Ibnu-Kasir ya ambaci wannan hadisin na Jabir a cikin littafinsa na tafsiri, a qarqashin faxin Allah ta'alah a cikin suratul Ma'idah,
{يُرِيدُونَ أَنْ يَخْرُجُوا مِنَ النَّارِ وَمَا هُمْ بِخَارِجِينَ مِنْهَا}.
Ma'ana: "Suna nufin su fita daga cikin wuta, amma ba za su samu fita daga cikinta ba ".  ta hanyar Ibnu-AbiyHatim da Ibnu-Mardawaih, da wassunsu.
Kuma wannan hadisin yana yin nuni cewa lallai su waxannan mutanen an jarrabe su, har suka ji ra'ayin khawarijawa da ke kafirta mutumin da ya mutu akan babban laifi (daga cikin kaba'irai, bai tuba ba), da kuma bashi hukuncin dawwama a cikin wuta, wannan ra'ayi  yana burge su, Saidai kuma haxuwansu da sahabi Jabir (رضي الله عنه) da kuma yadda ya musu bayani, sai suka bar abinda suke a kansa na varnar da suka fahimta, suka tafi zuwa ga abinda ya xora su akansa, tare da kauce wa abinda suka niyyaci aikatawa bayan hajji na fita daga xa'ar shugaba ko fito-na-fito da shi, ko kuma ficewa daga al'ummar musulmai.
Wannan kuma yana daga cikin manya-manyan fa'idodin da musulmi zai fa'idanta da su, lokacin da yake komawa zuwa ga ma'abota ilimi.
Kuma haqiqa na rubuta littatafai guda biyu da suke magana akan haka, Na farkonsu da taken:
((بأيِّ عقلٍ ودينٍ يكون التفجير والتدمير جهادًا، ويحكم أفيقوا يا شباب!!)).
Ma'ana "Da wani hankalin ne, da kuma wani addinin qone-qone da rushe-rushe ya ke zama jihadi, Kaitonku! Ku faxaka ya ku samari!", Wanda aka buga shi a shekarar hijira ta 1424h Na biyun kuma da taken:
((بذل النصح والتذكير لبقايا المفتونين بالتكفير والتفجير)).
Ma'ana: "Yin nasiha da tunatarwa ga sauran waxanda suka fitinu da kafirta mutane, da kuma qone-qone ", Shima an buga shi a shekarar hijira ta 1427h. Sannan aka buga su a tare a cikin taron littatafana (6/ daga shafi na 225, zuwa 279), a shekara ta 1428h .

            Kuma yana daga cikin muhimman abubuwan da za a magance su a cikin huxubobin juma'a abinda aka jarrabi wassu mutane da shi, na qoqarin kira zuwa ga kashe kyawawan halayya da xabi'u, da kuma aukawa cikin cututtukan sha'awa,  waxanda da wannan kiran nasu suke son wannan qasar (ta Saudia) ta yi mummunan karkata mai girma, domin samari maza da mata su karkata su bar abinda suka kasance akansa na lazimtar halayya kyawawa, da aiyuka managarta. A nan sai huxubar juma'a ta qunshi jan kunne, daga fitinan maqiya wannan qasa, masu karkashe rayuka da kashe kyawawan halaye, Kuma sananne abu ne, lallai abinda yake aukuwa na jarabtar mutane ta fiskar kashe rayuka, ya auku ne sakamakon abinda aka jarraba su da shi daga farko na kashe halayyan kirki, kamar yadda Allah mabuwayi da xaukaka yake cewa:
{وَمَا أَصَابَكُمْ مِنْ مُصِيبَةٍ فَبِمَا كَسَبَتْ أَيْدِيكُمْ وَيَعْفُو عَنْ كَثِيرٍ}.
Ma'ana: "Kuma duk abinda ya same ku na jarrabawa to saboda abinda hannayenku suka aikata ne, kuma Allah yana afuwa akan abu dayawa". Shehinmu As-sheikh Abdul'aziz Ibnu-Baaz (رحمه الله)  a cikin (majmu'u fatawa nasa, 4/ 127) yana cewa:
((Duk wani abinda yake samun al'umma, ko xaixaikun mutane na fitintinu, ko katangewa daga addinin Allah, ko annoba, ko yaquka, ko wassun haka na nau'ukan bala'i mabanbanta = sababinsu shine abubuwan da bayi suke aikatawa na dangin savawa shari'ar Allah mabanbanta, kamar yadda Allah ta'alah yake cewa:  "Kuma duk abinda ya same ku na jarrabawa to saboda abinda hannayenku suka aikata ne, kuma Allah yana afuwa akan abu dayawa", Kuma haqiqa lallai Allah ta'alah ya bayyana wa mutane irin abubuwan da suka auku ga al'umman da suka shuxe na azabtarwa da hallakawa saboda yadda suka yi ta sava wa shari'arsa, saboda mai hankali ya faxaka, don kuma ya wa'aztu ya xauki izina daga haka)).

            Daga qarshe, Ina roqon Allah mabuwayi da xaukaka ya datar da dukkan masu huxuba, wajen sauke wannan aiki ta fiskar da zata yardar da Allah, ta kuma amfani bayinSa. Sannan ya datar da masu sauraron huxubar wajen amfana da saqon da ta qunsa, da kuma xaukar dukkan abinda akwai tsirarsu a cikinsa, a nan duniya ko a lahira.

            Salatin Allah da sallama da albarka su qara tabbata ga bawanSa kuma manzonSa annabinmu Muhammadu, da iyalanSa da sahabbanSa gabaxaya.   

                        Kammalawa / 15/zulqi'idah/1436h

                        Daidai da 30/08/2015m, a Madinah.   

1 comment:

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...