TACE TAUHIDI MAI AMFANI
(تَجريدُ التوحيد الْمُفيدِ)
Na babban Malami/
Ahmad bn Aliyu Almakariiziy Alhanafiy
Fassarar mai neman afuwar Ubangijinsa/
Abubakar Hamza Zakaria
(abusafiyya01@yahoo.co.uk)
Mukaddima
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin
halittu, Yabo da shira su kara tabbata ga fiyeyyen Annabawa da Manzanni;
Annabinmu Muhammadu, da Iyalensa da Sahabbansa gaba daya … Bayan haka;
Saboda
tauhidin Allah mabuwayi da daukaka da kadaita cikin bauta a ka halicci dukkan halitta,
kuma don tabbatar da shi (kadaita Allan) aka shar' anta dukkan bauta (sallah,
azumi, addu'a,da sauransu); don haka: Shi tauhidi shi ne manufa mafi girma,
kuma shi ne target mafi daukaka (da aka so kar mutum ya nufa da duk wani
motsinsa da bautarsa sai shi), kuma abun nufa madaukaki mai girma, Allah
madaukaki ya ce:
ﭽ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭼ [الذاريات: ٥٦].
(Kuma ban halicci aljani da mutum ba sai don su
kadaita ni da bauta).
Kuma hakika
(ayoyin) Alqur'ani da sunnar (Manzon Allah s a w) sun zo kan cewa duk wadda ya TABBATAR
DA TAUHIDI YA SHIGA ALJANNA BA TARE DA HISABI, KUMA BA TARE DA AZABA BA; SHI
YASA MALUMA –ALLAH YA MUSU RAHAMA- SU KA YI TA KOKARIN SU BAYYANA WANNAN
AL'AMARI MAI MUHIMMANCI KUMA SU KUSANTO DA SHI, DA BAYANINSA, A CIKIN WALLAFE
WALLAFE DA LITTATAFA MASU YAWA; DAGA CIKINSU AKWAI WANNAN:
تَجريدُ التوحيد الْمفيد،
(TACE TAUHIDI MAI AMFANI),
''Littafi mai
babban matsayi, Na Imam, mai yawan sani, Takiyyudden, Almakariiziy,
Alhanafiy, -Allah ya masa rahama-.
Shi kuma TACE TAUHIDI (TAJRIDUT TAUHID) na
nufin:
Tabbatar da shi,
da tace
shi,
da kuma karkade masa kurar
shirka mai girma da shirka karama,
da bidi'o'in kuduri, da bidi'o'in
aiyuka,
da kuma barin sabo;
Hakan kuma zai kasance ne ta hanyar;
Cikar Ikhlasi wa Allah a cikin
zantuttuka, da aiyuka da niyyoyi, da kuma kubutuwa daga babban shirka da ke
warware tushen tauhidi (musulunci), da
kuma kubuta daga karamar shirka da ke kore cikarsa (tauhidi), da kuma kubuta
daga bidi'o'I da su ke kawo gibi ga tauhidi, da kuma sabo da ke tauye tauhidi,
kuma ke hana cikarsa, sa'an nan ya ke katange shi daga samun tasirorinsa.
Muna fatan Allah ya amfanar (da bayinsa)
da wannan littafin, sa'an nan ya girmama lada da sakayya ga mawallafinsa, da
wadda ya yada shi, da kuma mai karanta shi.
Allah kuma ya yi dadin tsira ga
shugabanmu kuma annabinmu Muhammadu, da kuma Iyalensa da sahabbansa gaba daya.
(Gabatarwan)
Mai yadawa.
**********
TARIHIN MAI LITTAFIN –Allah ya yi masa rahama-
Shi ne
takiyyuddeen Ahmad bn Aliyu bn Abdilkadir bn Muhammad bn Ibrahim bn Muhammad,
bn Tamim, bn Abdissamad, bn Tamim Almakriiziy, Babban malami Ibnu Hajar –Allah
ya masa rahama- ya masa alkunya da: Abu Muhammad, Yayin da Imam Sakhawiy ya
masa alkunya da: Baban Abbas.
Shi kuma ''almakriiziy''
dangantawa ne zuwa ga unguwar ''makarizat'' a Ba'ala –bakka; wadda
kakansa na sama Ibrahim ya taba sauka a wajen, Sai kuma ya shahara da haka.
***********
An haifi mai wannan littafi ne a ''Alkahirah''
(babban birnin Misra) a shekara ta dari bakwai da sittin da shida (766na
hijira), a Unguwan da ake kiranta: ''Burjuwan'' a da, Unguwan a yanzu (wannan zamanin) na bin
yankin ''jamaliyya'' wajen kal'ar (dutsen) Muhammadu bn Aliyu .
***********
Ya tashi a cikin iyalai (haula) masu addini; sai ya hardace
alqur'ani tun yana karaminsa, da kuma kananan littatafa na fiqhun (Mazhabar)
Hanafiyya.
Amma babansa kuma to an haife shi a Damaskas (damashk), ya
kuma yi karatun (sauraron) hadisi a can, sa'an nan ya yi kaura zuwa ga ''Alkahirah'',
ya yi wassu aiyuka da su ke da alaka da alkalanci.
***********
Mai littafi ya yi
wassu aiyuka da su ked a muhimmanci, yayi wakilcin hukunci, ya zama shi ne mai
sa hannu (signature), ya yi aikin hisba, da huduba a masallacin juma'a na Umar,
ya kuma yi limancin (salloli biyar) a massalacin shugaba, sa'an nan ya karantar
da hadisi a ''mu'ayyidiyyah'' a madadin ALMUHIB BN NASRULLAHI, Ya kuma
tsayu wajen yin wadannan aiyukan mafi alkhairin tsayuwa; aka kuma yaba wa
salonsa da tsarinas. Duk wadannan abubuwan sun kasance a Misra ne. Yayin da
kuma yak aura zuwa damaskas, Sakhawiy ya ce –dangane da shi: ''Haka nan kuma ya
shiga Damaskas sau da dama, kuma ya jagoranci kula da wakafin kalaniysiy, da
Baimaristan Annuriy, da kuma karantarwa a makarantar ''darul hadith
al'ashrafiyyah'' da '' makarantar ikbaliyya'', kuma an bijiro masa
Shaf'iyya a shaam (seria) amma sai ya ki,
Sa'an nan sai marubucin –Allah ya masa rahama- ya kaurace wa
duk wadannan aiyukan; Sakhawiy yana cewa: ''Sa'an nan sai ya kaurace wa hakan,
ya kuma zauna ya lazimci garinsa ya shagalta da tarihi har ambatonsa ya shahara
da shi, kuma sautinsa ya yi nisa a cikinsa, kuma ya zama yana da wallafe
wallafe a cikinsa''.
***********
Marubucin –Allah ya masa rahama- ya yi farkon rayuwarsa ne;
a farkon neman iliminsa tun yana yaro kan
hardatan alqur'ani da kuma wassu kananan littatafan fiqhun Hanafiyya; sai ya tashi
akan mazhabar Abu hanifata
***********
١. المواعظ والاعتبار بذكر الخطط والآثار
Shi ne wadda ya
fi shahara da:
الخطط للمقريزي.
٢. إمتاع الأسماع بما للرسول r من الأبناء والأموال والحفدة والمتاع.
٣. الخبر عن البشر.
٤. درر العقود الفريدة في تراجم الأعيان المفيدة.
٥. الذهب المسبوك في ذكر من حج من الخلفاء والملوك.
٦. السلوك في معرفة دول الملوك.
Da kuma
wassunsu na littatafansa.
***********
Ya rasu –Allah
ya masa rahama- a watan ramadana na shekarar 845 na hijira, bayan ya doshi
shekara tamanin, bayan tsawon rai (rayuwa) da ke cike da ilimi, karantarwa, da
wallafe wallafe.
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin
halittu, kyakkyawar makoma ta tabbata ga masu tsoron Allah, kuma salatin Allah
ya kara tabbata ga annabinmu Muhammadu; cika makon annabawa, da iyalensa da
sahabbansa gaba daya.
Bayan haka:
Wannan littafi ne mai fa'ida da yawa, mai
kuma yaukakan dayaituttun fa'idoji a babinsu, wadda duk wadda ya nufi Allah da
gidan lahira zai amfana da shi' Na sanya masa take:
LITTAFIN TACE TAUHIDI; MAI AMFANI
Allah kawai na ke rokon –da
baiwansa- taimako kan
aiki da shi.
Ka sani Lallai Allah madaukaki shine
ubangijin komai, mamallakinsa, kuma abun bautarsa; Shi kuwa ''RABBU'' tushen
kalma ne na: Ya rena, yana reno, reno; kuma ma'anar fadin (Allah) madaukakin
sarki: ''RABBUL AALAMINA'' shi ne mai renon (mai kula da) dukkan
halittu, Kuma shi rabbu (s w t) shi ne mahalicci da ya samar da bayinsa, kuma
shi ya tsayu da tarbiyyarsu (wajen kula da su) da kuma gyara su, wadda ke gyara
su cikin halittansu, arzikinsu, lafiyansu, dama gyara addininsu da duniyarsu.
Shi kuma ''ILAHIYYA
–Bautantaka-'' shi ne kasancewar bayi suna rikan (Allah) madaukaki abun so,
abun bauta, kuma suna 'dayanta shi wajen so da tsoro, kauna da kan-kan-da-kai,
tuba, bakance, da'a (biyayya), nema da tawakkali, da makamantan wadannan
abubuwa.
Shi kuma TAUHIDI;
HAKIKANINSA: Shi ne Mutum ya rika ganin al'amura dukkansu daga Allah ne
madaukaki; ganin da zai yanke waiwaye zuwa ga sabbuba da tafinta (saboda sababi
ba shi ya ke samar da abu ba, haka tafinta); don haka ba za ka ga alkhairi da
sharri ba face tushensa daga Allah ne madaukaki.
Shi kuwa (imani) da wannan
matsayi na haifar da; TAWAKKALI (saboda duk wadda ya san dukkan abubuwa daga
Allah ne; don me zai dogara ga waninsa!), BARIN KOKA HALITTA (idan da mutum zai
rasa wani abu… don me zai koka wani halitta irinsa ya ce: Shi ya hana shi?), DA KUMA BARIN
ZARGINSU, DA KUMA YARDA DA ALLAH, DA SALLAMA WA (MIKA WUYA) WA ABIN DA YA
HUKUNTA.
Idan ka san wannan; to ka
sani lallai RUBUBIYYA ya kasance daga Allah ne madaukaki zuwa ga bayinsa. Shi
kuma ULUHIYYA (Bautantaka) ya kan
kasance ne daga bayinsa zuwa gare shi, Ita kuma RAHAMA (Tausayi) itace ta hada
tsakaninsu da tsakaninsa mabuwayi da daukaka.
Kuma ka sani lallai mafi
tsadan ayyuka, wadda kuma ya fi su girman matsayi: shi ne KADAITA ALLAH
MADAUKAKI (Tauhidi).
Sai dai kuma shi TAUHIDI yana
da wassu abubuwa guda biyu da suke bayyana shi:
NA DAYA: Shi ne ka ce:
LA'ILAHA ILLAL LAHU (ba wadda ya cancanci bauta sai Allah) da harshenka; Wannan
maganan ana kiransa TAUHIDI; saboda yana karo da ukuntaka da nasara (crister)
suka kudurce shi (yana kuma warware shi).
Sai kuma shi wannan tauhidin
yana iya samuwa daga MUNAFUKIN da sirrinsa ya saba da abin day a bayyana.
ABU NA BIYU: Kada zuciya ya
saba da abin da harshen ya fada, kuma kar ya musanta abin da ake fahimta na
ma'anar abin da aka furta (na waccar kalmar ).
Abin da ya wajaba shi ne: Zuciya ya kunshi kudurce hakan, ya kuma gaskata shi;
Wannan shi ne tauhidin gamagarin mutane.
Amma MADARAR TAUHIDI kuma shi
ne: Ya ga al'amura gaba dayansu daga Allah ne madaukaki; sa'an nan ya yanke
waiwaye ga barin tsanuka, ya kuma bauta wa Allah madaukaki bautar da zai
kadaita shi da ita, ba zai kuma bauta wa waninsa ba.
Abin da ke fitar da Mutum
kuma daga wannan tauhidin shi ne; Bin son zuciya; domin duk wadda ya bi son
zuciyarsa to ya riki abin da zuciyar nasa yak e so a matsayin abun bautarsa;
Allah madaukaki yana cewa:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭪ ﭼ [الجاثية: ٢٣]
Ma'ana:
" Shin baka ga wadda ya riki son zuciyarsa a matsayin abun bautarsa ba! …
".
Idan
–kuma- ka lura za ka ga wadda ya bauta wa gunki a hakikanin gaskiya bai bauta
masa ba; abun sani kawai shi ne ya bauta wa son zuciyarsa; wadda shi ne
karkatuwan zuciyarsa ya zuwa ga addinin iyayensa, sai kuma ya bi wannan
karkatar. Shi kuwa karkatan zuciya ya zuwa ga abubuwan da aka saba da su daya
ne daga cikin abubuwan da ake kiransu SON ZUCIYA.
Abin
da ke fitarwa daga wannan tauhidin shi ne: YIN FUSHI DA HALITTU, DA KUMA
WAIWAYAWA ZUWA GARE SU; domin duk wadda ya ke ganin cewa komai daga Allah ne to
ta yaya zai yi fushi wa waninsa (wai don –misali- ya rasa wani arziki), Ko kuma
ta yaya zai kaunaci waninsa (wata ni'ima; saboda duka daga Allah ne; don haka
sai a nema daga gare shi). Wannan matsayi a cikin tauhidi shi ne matsayin
SIDDIKAN BAYI.
Kuma ba shakka lallai
tauhidin RUBUBIYYA Mushirkai ba su musanta shi ba, hasali ma sun tabbatar da
cewa (Allah) madaukaki shi kadai shi ne MAHALICCINSU, KUMA MAHALICCIN SAMMAI DA
KASSAI, WADDA KE TSAYE KAN DUKKAN ABUBUWAN DA ZA SU GYARA HALITTUNSA GABA
DAYANSU, Abin sani kawai shi ne su Mushirkai sun yi inkarin TAUHIDIN ULUHIYYA
NE (tauhidin bauta) da soyayya, kamar yadda Allah ya hakaito akansu a cikin
fadinsa:
ﭽ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ
ﮇﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍﮎ ﮞ ﭼ [البقرة: ١٦٥ ].
Ma'ana: '' Akwai daga cikin
mutane wadda ya ke rikon wanin Allah a matsayin kishiyoyi; yana sonsu kamar
yadda ya ke son Allah. Wadanda su ka yi imani sun fi tsananin so ga Allah ''.
Yayin da (wadannan) suka
daidaita waninsa da shi a cikin wannan tauhidin; sai su ka zama mushirkai (masu
hada Allah da wani) kamar yadda Allah ya ce:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ
ﭙﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭼ [الأنعام: ١].
Ma'ana: '' Yabo da godiya sun tabbata ga Allah
day a halicci sammai da kassai, kuma ya halicci duffai da haske, sa'an nan
wadanda su ka kafirta sun kasance: Ubangijinsu su ke daidatawa ( da wani).
Madaukaki ya kara cewa:
ﭽ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﭼ [الأنعام: ١٥٠].
Ma'ana:
" ( Su kafirai) sun kasance dangane da ubangijinsu suna daidaita shi (da
waninsa).
Kuma
lallai Allah madaukaki ya ilmantar da bayinsa yadda za su rabu da shirka a
cikin tauhidin ULUHIYYA, kuma Allah madaukaki shi ne ya cancanci kadaita shi a
matsayin abun so, mai hukunci, kuma ubangiji; allah ta'ala yana cewa:
ﭽ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﯙ ﭼ [الأنعام: ١٤].
Ma'ana:
" Ka ce: Yanzu wanin Allah zan rika masoyi!; wadda ya kagi halittan sammai
da kassai ". Ya kuma ce:
ﭽ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮩ ﭼ [الأنعام: ١١٤].
Ma'ana:
" Shin wanin Allah zan nema (zan rika) a matsayin mai hukunci? ". Ya
kuma ce:
ﭽ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫﰇ ﭼ [الأنعام: ١٦٤].
Ma'ana:
" Ka ce: Shin wanin Allah ne zan nema (zan rika) a matsayin ubangiji?
".
Don
haka babu wani masoyi (waliyyi), babu kuma mai hukunci, sa'an nan babu ubangiji
sai Allah; Wadda duk wadda ya daidaita waninsa da shi to ya yi shirka cikin
tauhidin ULUHIYYAH, koda kuwa ya kadaita RUBUBIYYARSA. Shi tauhidin RUBUBIYYA
shi ne wadda dukkan halittu su ka hadu akansa; Mumininsu da kafirinsu. Yayin da
shi kuma TAUHIDIN ULUHIYYA shi ne: mararrabar hanyar muminai da mushirkai; don
haka ne ma KALMAR MUSULUNCI ''La'ilaha illal lahu'' (ma'ana: ba wadda ya
cancanci a bauta masa sai Allah). Kuma da mutum zai ce Babu mahalicci, ba
mamallaki, ko ba mai juya al'amura Sai Allah; To da bai isar masa (ya shiga
musulunci da shi) ba, A wajen maluma ma'abuta tahkiki (masu zurfi cikin ilimi
tare da tacewa). Shi TAUHIDIN ULUHIYYA shi ne abun nema daga dukkan bayi, don
haka ne ma asalin kalmar
الله
shi
ne:
الإلـه
kamar
yadda hakan shi ne fadin Babban Malamin harshen larabci SIBAWAIHI, Kuma shi ne
magana mai inganci, kuma shi ne fadin mafi yawan Maluma daga sahabbansa, sai
dai wanda ya yi shuzuzi (wato ya zo da sabani maganan maluma).
Kuma
da wannan ma'anar dam u ka tabbatar da ma'anar ''AL ILAHU'' cewa shi ne (abun
bauta) kuma abun so; saboda haduwar sifofin kamala (cika da bunkasa) a tattare
da shi YA ZAMA LAFAZIN ''ALLAH'' shi ne sunan day a kunshe duk ma'anonin
sunayen Allah mafiya kyan sunaye, da kuma sifofi madaukaka; kuma wannan shi ne
abin da mushirkai ke inkarinsa (musanta shi).
Shi
kuma ubangiji ya kasance yana kafa musu hujja da kadaita shi da su ke yi cikin
rububiyyarsa (aiyukansa) kan
su kadaita shi cikin uluhiyyarsa (wato aiyukansu da su ke yin a bauta); kamar
yadda Allah madaukaki ya ce:
ﭽ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔﮕ ﮖ ﮗ ﮘﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﭼ [النمل:59-٦٠].
Ma'ana:
" Ka ce: godiya ta tabbata ga Allah (wato: Alhamdu lillahi), kuma aminci
ya tabbata ga bayinsa day a zaba. Shin Allah shi ne ya fi alkhairi akan abin da
su ke tara shi da su! (Amsa lallai Allah shi
ya fi!) *** Ko kuma wanene ya halicci sammai da kassai, ya kuma saukar muku dad
a ruwa daga sama; sa'an nan ya tsirar muku da lambuna masu kayatarwa da shi,
wadda ba ku da ikon (ba don ya muku ba) ku tsirar da bishiyar ta, Shin akwai
wani abun bauta tare da Allah? (Amsa: Babu wani abun bauta na gaskiya tare da
shi), Kai dai kawai naïf yawansu mutane ne da su ke daidaita wanin allah tare
da shi (cikin bautarsu, su kuma karkatar da hakkinsa ya zuwa waninsa). (A wannan
jerin gwanon ayoyin) duk lokacin da Allah madaukaki ya ambaci wani yanki na
ayoyinsa sai ya bi bayanta da fadinsa:
ﭽﮖ ﮗ ﮘﮙﭼ
Ma'ana: " Shin akwai wani abun bauta ne
tare da Allah? ", Sai madaukaki mai tsarki ya bayyana –mana- da hakan
cewa: Su mushirkai sun kasance suna tsayawa wajen tabbatar da tauhidin ULUHIYYA
(basa tabbatar da shi), ba rububiyya ba; Duk da cewa a cikinsu akwai wadda ya
hada Allah da wani har ma a cikin rububiyyar tasa –kamar yadda daga baya hakan
zai zo; in Allah ya yarda-.
A
dunkule dai Shi Allah ya kasance yana kafa hujja ga wadanda su ka musanta
cancantar bautarsa (su ke yenta ga waninsa) yana kafa musu hujja da
tabbatarwansu da tauhidin rububiyya (wato: Tun da kun gamsu allah shi ne
mahalicci, mai juya al'amura to dole ne kuma ku tabbatar cewa wadda ya ke yin
wadancan abubuwan shi daya, shi kadai ya cancanci ku yi masa bauta, ba tare da
kun hada shi da wani ba).
Shi
kuma ''ALMALIKU'' (Mamallaki) shi n eke umurni da hani; wadda ba zai halicci
halitta ba, kamar yadda rububiyyarsa ta hukunta, sa'an nan sai ya bar su kara
zube, sakaka ba tare da an umurce su ba, ko kuma a hana su ba, haka kuma ba za
a musu sakayya ba ko a musu horo ba; domin shi mai mulki (Allah) shi ne mai
umurni da hani, mai bayarwa, mai hanawa, mai cutarwa da amfanarwa, mai kuma
bada sawaba (sakamako kan mai kyau) da horo.
Shi
yasa neman tsari day a zo a cikin SURATUN NASS da SURATUL FALAK ya zama da
sukane masu kyau guda uku (ARRABBU, ALMALIKU,da AL'ILAHU);
Saboda
yayin da ya ce:
ﭽ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﭼ [الناس: ١].
(Kace ina neman tsarin ubangijin
mutane).
Wadda
a cikin wannan akwai tabbatar da cewa shi (Allah) shi ne mahaliccinsu, makagin
halittarsu, Abun day a saura shi ne: A ce: Yayin day a halicce su shin ya
kallafa musu wassu aiyuka kuma ya umurce su, ya kuma hana su? Sai aka ce:
Na'am; Sai fadinsa:
ﭽ ﮅ ﮆ ﮇ ﭼ [الناس: ٢]
(Mamallakin mutane)
Ya
zo, ya tabbatar da halitta da umurni,
ﭽ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡﮢ ﮧ ﭼ [الأعراف: ٥٤].
Ma'ana:
Ku saurara! Halitta d umurni nasa ne (Na Allah ne ubanjin halittu, wadda
albarkansa ta yawaita). Yayin da aka fadi haka, Sai aka ce: Idan ya kasance
ubangiji mai samarwa, kuma mai mulki da ke kallafawa bayinsa (yi da hani) To
shin ana sonsa, kuma ana nuna kwadayi zuwa gare shi; don ya zama fiskantarsa
shi kadai ita ce: MANUFAR YIN HALITTA DA KUMA UMURNI?
Sai
aka ce:
ﭽ ﮈ ﮉ ﮊ ﭼ [الناس: ٣ ].
(Abun bautar mutane).
Ai
abun bautarsu, kuma abun sonsu; wadda bawa halitta, da aka kallafa masa (wassu
aiyuka), kuma mai bauta baya fiskantuwa sai zuwa gare shi; Sai ULUHIYYA ta zo
don ta zama cika makon (sunaye ukun) kuma manufa (da aka yi halittan aljani da
mutum don ita), abun day a zo gabaninta kuma ya zama kamar shumfuda ne a gare
ta, kuma sharer fage.
Su
kuma wadannan surori biyu (Falaki/ Nass) sun e mafi girman magani a cikin
Alqur'ani (ruk'yah). Haka kuma neman tsari da su ya z one lokacin da aka bukaci
hakan; wadda shi ne: lokacin da aka yi wa Manzon Allah (s a w) sihiri; har ma
ake suranta masa –a kwakwalwarsa- cewa ya aikata wani abu alhali bai aikata shi
ba; ya yi kwana arba'in (40) yana kan
haka. Kamar yadda ya zo cikin Sahihul Bukhari da Muslim. Kuma kullin sihirin ya
kasance kulli ne goma sha daya; Sai Allah ya saukar da ayoyi goma sha daya
(11); Sai kowani kulli daya ya warware tare da aya daya.
Sai
kuma neman tsari da ya zo a farkon Alqur'ani ya rataya da sunansa ''AL'ILAHU
–ALLAHU-); wadda shi ne abun bauta shi kadai; saboda haduwar sifofin kamala a
tattare da shi, da kuma ganawar bawa da wannan abu bauta mai kamala (cikakke)
ma'abocin sunaye mafi kyau, da kuma sifofi madaukaka, wadda ake kwadayin ya
tsare bawansa da ke ganawa da shi da maganarsa= daga shedan wadda ya ke sa
shamaki shakaninsa da tsakanin ganawa da ubangijinsa.
Sa'an
nan wannan rataya da sunan ''AL'ILAHU'' (a wuraren neman tsari)ya ci gaba da
kasancewa a duk wuraren da ake cewa:
ﭽ ﮰ ﮱ من الشيطان الرجيم ﭼ
(Ina neman tsarin
Allah daga shedan abun yasarwa); saboda sunan Allah "Allah'' Shi ne taget
(abun nufi) ga sauran sunayen; don haka ne ma kowani sunan –waninsa- baya
sanuwa ya ganu a wajen halittu sai an jingina shi da shi (Allah); Sai mu ce:
Allah shi ne ''ASSALAMU, ALMU'UMINU, ALMUHAIMINU''; don haka suna mai girma
(Allah) shi ya ke yin bayanin waninsa. Waninsa kuma ba ya yin bayaninsa.
Wadanda
kuma su ka yi masa shirka cikin RUBUBIYYARSA; daga cikinsu akwai wadanda su ka
tabbatar da wani abun halittan na daban tare da shi –duk da cewa ba su ce:
wannan mai halittan (wadda ba Allah ba) yana daidai da Allah ba; Wadannan sun e
Mushirkai da kuma wadda ya yi kama da su (cikin masu da'awar musulunci) da ake
kiransu: AL'KADARIYYAT.
Ita
kuwa rububiyyarsa –madaukaki- ga dukkan halittu rubuyya ce: CIKAKKIYA,
SAKAKKIYA, DA TA GAME (dukkan halittansa), kasancewar rububiyyarsa da wannan
sifar ta ruguje dukkan maganganunsu; saboda tana hukunta rububiyyarsa ga dukkan
abin da ke cikinsa (duniya da lahira, mai kyau ko mummuna) na zatoci (jikkai)
da sifofi, da dukkan motsi, da ayyuka.
Shi
kuma hakikanin akidar KADARIYYA MAJUSIYYA shi ne: Lallai (Allah) madaukaki ba
shi ban e UBANGIJIN (mahaliccin) ayyukan halittu, kuma rububiyyarsa –wai- bata
shafe wannan ba; kuma ta yaya rububiyyar tasa za ta shafi abin da ba shi da iko
akansa, bai kuma nufe shi ba, sa'an nan bai halicce shi ba?
Shi
kuma shirkan dukkan al'ummai gaba dayansa nau'i biyu ne: Shirka cikin ULUHIYYA,
da kuma SIRKA CIKIN RUBUBIYYA.
Shi
shirka cikin (tauhidin) Uluhiyya; da ibada shi ne ya fi rinjaye ga ma'abota
shirka, kuma shi ne shirkan masu bautar gumaka, da masu bautar mala'iku, da
masu bautar aljanu, da masu bautar shehunai da salihan bayi; rayayyu da
matattu; wadanda su ka ce: ABIN SANI KAWAI MUNA BAUTA MU SU NE DOMIN SU
KUSANTAR DA MU –WANI- KUSANCI ZUWA GA ALLAH, kuma SU CECE MU A WAJENSA,
Sa'annan saboda kusancinsu zuwa ga Allah, da kuma baiwar da ya yi musu (karrama
su da ya yi) sai kusanci da karama muma ta same mu; kamar yadda abin yak e
sabebbe a nan duniya; cewa akan samu karama da kusanci ga wadda ke hidima ga
mataimakan mai mulki, da makusantansa, da wadanda ya kebanta da su.
Su
kuma littatafan Allah daga farkonsu har zuwa karshensu (sun yi ittifaki) wajen
ruguza wannan mazhabar (shirka cikin bauta) da kuma yi masa raddi, tare da
munana wadanda su ka auka cikinsa, da nassanta cewa su makiya Allah ne
madaukaki. Suma annabawa –wadanda Allah ya aiko amincin Allah ya kara tabbata a
gare su- gaba dayansu sun yi ittifaki akan haka; daga na farkonsu zuwa na
karshensu. Kuma Allah madaukaki bai halaka wadda ya halaka ba daga al'ummai
face sababinsa shi ne wannan shirkan, kuma don shi.
Asalin
wannan shirka shi ne shirka cikin son Allah madaukaki, Allah madaukaki ya
ce:
ﭽ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ
ﮇﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍﮎ ﮞ ﭼ [البقرة: ١٦٥ ].
'' Akwai daga cikin mutane wadda ya ke rikon wanin Allah a
matsayin kishiyoyi; yana sonsu kamar yadda yak e son Allah. Wadanda su ka yi
imani sun fi tsananin son Allah ''. Madaukaki –a cikin wanna ayar- ya bada
labari cewa: Lallai wadda ya so wani abu tare da Allah kamar yadda yak e son
Allah to lallai ya riki wannan abun kishiya wa Allah –wannan kuma shi ne mafi
ingancin fassara biyu da ake yi wa ayar; Cewa lallai su suna sonsu kamar yadda
su ke son allah.
Wannan kuma shi ne daidata
wanin Allah da shi da aka ambata a cikin fadinsa madaukaki:
ﭽ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭼ [الأنعام: ١].
'' Sa'an nan wadanda su ka kafirta sun
kasance: Ubangijinsu su ke daidatawa ( da wani). Ma'ana –ga mafi ingancin zance
biyu- cewa; Lallai su sun kasance suna daidaita waninsa (Allah) da shi cikin
bauta; sai su daidaita tsakaninsa da tsakaninsa cikin so da bauta, haka kuma
fadin mushirkai –al'hali suna cikin wuta- fadinsu ga gumakansu:
ﭽ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﭼ [الشعراء: ٩٨].
Ma'ana:
" Mun rantse da Allah! Mun kasance a cikin bata mabayyaniya*** yayin da mu
ke daidaita ku da ubangijin halittu''.
Kuma
sananne ne –yanke- cewa wannan daidatawa bai kasance tsakaninsu da tsakanin
Allah ba cikin kasancewarsa shi ne ubangijinsu, kuma mahaliccinsu, da kuma cewa
kasa da abin da ke cikinta na Allah ne shi kadai, kuma shi ne ubangijin sammai
bakwai, da kuma ubangijin al'arshi mai girma, kuma lallai shi madaukaki shi ne
mulkin komai ya ke hanunsa, kuma shi ne ke tunkude sharri ga bayinsa, kuma ba
wadda ya isa ya tunkude abin da ya kaddara ga wani bawa; in shi bai kawar masa ba.
Abin
sani kawai wannan daidaitawar ta kasance ne tsakaninsu da shi madaukaki cikin:
SOYAYYA DA IBADA; don haka duk wadda ya so wanin Allah madaukaki, ya kuma ji
tsoronsa, ya yi fatansa, ya kuma kankan da kai a gare shi kamar yadda ya ke son
Allah, ya ke kuma tsoronsa, da kaunarsa to Lallai wannan shi ne shirkar da
Allah ba ya gafarta shi! To kuma yaya ga mutumin da wanin Allah shi ya fi
fifiko a wajensa akansa (Allah), yafi sonsa, ya fi kuma tsoronsa, sa'an nan ya
zama wajen neman yardarsa ya fi tsananin aiki akan neman yardan allah?! To idan
wadda ya daidaita Allah da waninsa cikin abin da ya gabata ya zama ''MUSHIRKI''
to menen zaton da wannan? (Ma'ana: wadda ya fifita waninsa akansa!); Muna neman
tsarin Allah daga tobuwar zuciya da kadaita shi da kuma musulunci; kamar yadda
maciji ya ke fita daga sabarsa, mutum ya tobu daga musulunci al'halin yana
zaton shi musulmi ne mai tauhidi. Wannan shi ne daya daga cikin nau'oin shirka.
Su
kuma dalilai da su ke nuni kan :
(Allah) madaukaki ya wajaba ya zama shi kadai ake bautawa suna ruguza wannan
nau'in na shirka, su kuma warware hujjoji (shubuhohin) ma'abotansa, yawansu
kuma (wadannan dalilan) ba wanda ya isa ya kididdige su sai Allah madaukaki,
KAI! DUK ABIN DA ALLAH MADAUKAKI YA HALITTA DALILI NE DA KE YIN SHAIDA KAN KADAITUWARSA, HAKA
KUMA DUK ABIN DA YA YI UMURNI DA SHI. Don haka duk halittunsa, da umurninsa, da
kuma abin da allah ya kagi halittunsa akansu, da abin da ya kimtsa musu na
kwakwale = dukkansu dalilai ne da su ke shaida cewa ba wadda ya cancanci a yi
masa bauta sai shi kadai, kuma duk abin bauta –waninsa- to barna ne, Shi kuma
Allah shi ne gaskiya mabayyani –Ya tsarkaka kuma ya daukaka-.
وواعجبًا كيف يُعصى الإلـه
|
|
أم كيف يَجحَدُه الجاحدُ
|
ولله في كلّ تَحـريكةٍ
|
|
وتسكيـنةٍ أبدًا شـاهدُ
|
وفي كلّ شيءٍ لـه آيةٌ
|
|
تـدل على أنـه واحدُ
|
Ma'ana:
" Ka yi mamakin yadda ake saba wa (Allah) abun bauta!
Kuma
ka yi mamakin yadda mai musantawa ke musanta Allantakarsa!
Al'hali
Allah na da –a cikin kowani motsi… har abada, da kuma kowani shiru, yana abin
da ke masa shaida kan
cancantarsa ga bauta!
Haka
kuma cikin kowani abu yana da aya (alama) da ta ke nuni kan kadaitakarsa!
Shi
kuma nau'i na biyu na shirka shi ne SHIRKA CIKIN RUBUBIYYA (wato: kudurta akwai
wani mahalicci dare da Allah):
Hada
Allah madaukaki da wani cikin rububiyya; misalinsa kamar wadda ya kudure cewa
akwai wani mahaliccin na dabam; kamar masu bautar wuta (MAJUSAWA) da wassunsu;
wadanda su ke cewa: WANNAN HALITTUN SUNA DA UBANGIJI GUDA BIYU; DAYA daga
cikinsu shi ya halicci dukkan alkhairi; da yaren mutane Iran
(Farisanci) suna kiran wannan Allan: YAZDAN.
'DAYAN
KUMA; Shi ya halicci sharri, (majusawa da harshensu suna kiransa: AHRAMAN.
Kuma
kamar misalin PILOSERPERS DA WADANDA SU KA BI SU; da su ke kudure cewa: Ba abin
da ya samu daga Allah (ya halitta) sai abu guda kwara kadai; wadda kuma tushen
halittu gaba dayansu daga kwakwale ne da rayuka; Shi kuma tushen wannan duniyar
daga wani kwakkwaran hankali ne (da su ke kiransa: AL'AKLUL FA'AAL); Shi kuma
shi ne ubangijin abin da ke karkashinsa, kuma mai jujjuya shi.
Wannan
shirkan ya fi sharri fiye da ma shirkan masu bautar gumaka da majusawa (masu
bautar wuta) da Nasara (crister), kuma shi ne mafi daudar shirka a duniya; ta
yadda ya kunshi kore Allah, da musanta uluhiyyarsa (cancantarsa ga bautan bayi),
da kuma rububiyyarsa, da jingina halittar halittunsa zuwa ga waninsa, da haka
ne ya kunshi abin da ba wani shirkan wata al'umma ta kunshe shi.
(Misali
na gaba) Shirkan KADARIYYA; Shi kuma an tsakuro shi ne daga wannan, sa'an nan
–kamar- kofa ne na shiga wa wancan shirkan (Majusawa); Shi yasa sahabbai –Allah
ya kara musu yarda- su ka kamanta su da majusawa kamar yadda ya tabbata daga
(Abdullahi) dan Umar da (Abdullahi) bn Abbas. Allah ya kara musu yarda. Kuma
ma'abucin sunan (Abu dawud) ya ruwaito haka din yana mai jingina shi zuwa ga
Annabi (s a w) cewa: (Su kadariya) su ne majusawan wannan al'ummar([1]) .
Sau
da yawa shirka biyu (na rububiyya da na uluhiyya) su kan hadu wa bawa, kamar yadda daya daga
cikinsu kuma –a wassu lokutan- ya kan
kebanta wajen siffantuwar wani da shi.
Alqur'ani
mai karamci, dama sauran littatafan (Allah) da aka saukar daga gare shi;
dukkansu su fito karar sun yi raddi ga ma'abota wannan shirkar; misali fadinsa
madaukaki:
ﭽ ﭢ ﭣ ﭦ ﭼ
( A kai kadai mu ke bautawa) Wannan na
kore hada shi da wani cikin soyayya da bauta. Fadinsa kuma:
ﭽ ﭤ ﭥ ﭦ ﭼ [الفاتحة: 5].
(kuma a gare ka kai kadai mu ke neman
taimako) Shi kuma wannan na kore gama Allah da wani cikin halittarsa da
rububiyya.
Wannan
ayar ta kunshi: TACE TAUHIDI ga (Allah) ubangijin halittu cikin bauta, kamar
yadda bai halatta a tara shi da wani ba cikin
ayyuka, ko laffuza, ko cikin niyyoyi;
Misalin
shirka da shi cikin ayyuka shi ne kamar: yin sujjada ga waninsa, da kuma yin
dawafi ba ga daki mai alfarma ba, da kuma aske kai da nufin bauta da kankan da
kai ga waninsa, da kuma sunbantan wassu duwatsu wadda ba ALHAJARUL ASWAD; wadda
daman Allah ne a bayan kasa([2]) = ba, ko kuma
sunbantar kaburbura da shafarsu, da kuma yi musu sujjada.
Kuma
hakika Annabi (s a w) ya la'anci wadda ya riki kaburburan Annabawa da salihai
masallatai da ke yi wa Allah salla a cikinsu, yaya kuma wadda kuma ya rike su
abun bauta da ake bauta musu koma bayan Allah!! Wadda ya aikata haka bai san
ma'anar:
ﭽ ﭢ ﭣ
ﭦ ﭼ
( A kai kadai mu ke bautawa), ba.
Ya
zo cikin Sahihul (Bukhari da Muslim) daga Annabi (s a w) cewa shi ya ce:
" لَعَنَ اللَّهُ الْيَهُودَ اتَّخَذُوا
قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ مَسَاجِدَ "
Ma'ana:
" Allah ya la'anci yahudawa da Nasara; saboda sun riki kaburburan
Annabawansu masallatai ".
A
cikinsa kuma (Bukhari, amma ta'aliki) daga annabi s a w ya ce:
"
إنّ مِن شِرَار النَّاسِ مَن تُدْرِكُهُمْ السَّاعَةُ وهم أَحْيَاء، وَالَّذِينَ يَتَّخِذُونَ
القُبُورَ مَسَاجِدَ "
Ma'ana:
" Lallai ashararan mutane su ne: wadanda kiyama za ta riske su al'halin
suna da rai, da kuma wadanda su ke rikon kabari a matsayin wuraren salla
".
Ya
zo kuma a ciki Sahuhu (muslim) daga Annabi s a w:
"
وَإِنَّ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ كَانُوا يَتَّخِذُونَ قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ وَصَالِحِيهِمْ
مَسَاجِدَ، أَلا فَلَا تَتَّخِذُوا الْقُبُورَ مَسَاجِدَ إِنِّي أَنْهَاكُمْ عَنْ ذَلِكَ ".
Ma'ana:
"Lallai wadanda su ka kasance gabaninku sun kasance suna rikan kaburburan
Annabawansu da salihansu a matsayin
wuraren salla; Ku saurara! Kada ku riki kaburbura wuraren salla, lallai ni ina
hana ku wannan ".
A
cikin Musnad din Imamu ahmad da Sahihu bn Hibban daga Annabi s a w :
"
لَعَنَ رَسُولُ اللَّهِ r زُوارَاتِ الْقُبُورِ، وَالْمُتَّخِذِينَ عَلَيْهَا الْمَسَاجِدَ وَالسُّرُجَ
"
Ma'ana: "
Manzon Allah s a w ya la'anci mata masu yawan ziyartar kaburbura, da kuma masu
rikansu masallatai, da kuma sa musu fitila ". Ya kuma ce:
"
اشْتَدَّ غَضَبُ اللَّهِ عَلَى قَوْمٍ؛ اتَّخَذُوا قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ مَسَاجِدَ
"
Ma'ana: "
Fushin Allah ya yi tsanani ga mutanen da su ka riki kaburburan Annabawansa masallatai
". Ya sake cewa:
"
إنّ مَن كان قبلكم كانوا إِذَا مَاتَ فيهمْ الرَّجُلُ الصَّالِحُ بَنَوْا عَلَى قَبْرِهِ
مَسْجِدًا، وصَوَّرُوا فِيهِ تِلْكَ الصُّورَةَ، أُولَئِكِ شِرَارُ الْخَلْقِ عِنْدَ
اللَّهِ "
Ma'ana: "
Lallai wadanda su ke a gabaninku sun kasance idan mitum na gari ya rasu a
cikinsu; sai su gina masallaci a kabarinsa, su kuma suranta wancan suran
akansa; wadnnan su ne mafi sharrin halitta a wajen Allah ".
MUTANEN DA su
ke ziyartar mamata; Sai su yi musu addu'a, Wannan ita ce ziyara irin ta
shari'a.
MUTANEN DA su
ke ziyartarsu; Sai kuma su roki Allah (bukatunsu) da su; Wadannan su ne
MUSHIRKAI, KO KUMA JAHILAN GAMA GARIN MUTANE, DA KUMA WULAKANTATTU DAGA MASU
WUCE GONA-DA-IRI (kan bayin Allah matattu tare da juyar da hakkin Allah zuwa
gare su).
MUTANEN DA su
ke ziyartarsu sai kuma su roke su (koma bayan Allah s w t); Al'hali Annabi s a
w ya ce:
" اللَّهُمَّ لا تَجْعَلْ قَبْرِي وَثَنًا يُعْبَدُ "
Ma'ana: "
Ya Allah! Kada ka sa kabarina ya zama gunki; da za a bauta masa!! Wadannan su ne wadanda su ke hada Allah da
waninsa (mushirkai) a cikin rububiyya.
Lallai hakika
Annabi s a w ya bada kariya wa tauhidi; mafi girman kariya (ya kuma kiyaye shi;
kiyayenwan da ba wadda ya masa irinsa); saboda ya tabbatar da fadin (Allah):
ﭽ ﭢ ﭣ ﭦ ﭼ
(
A kai kadai mu ke bautawa).
Har ma ya yi
hani kan yin
salla a lokuta biyu; (lokacin fitowar rana, da na faduwarta) don toshe kofar
kamancecceniya da masu bautar rana; wadanda su ke mata sujjada a wadannan
lokutan.
Haka kuma ya
toshe kofa; ta hanyar hani kan
yin sallah bayan la'asar, da kuma bayan sallar asuba; saboda haduwan lokuta
biyun da lokutan da mushirkai su ke yin sujjada wa ranan([4]).
Amma dangane da
sujjada ga wanin Allah kuma sai (Manzon Allah) s a w ya ce:
" لا ينبغي لأحدٍ أنْ يسجد لأحدٍ إلا لله "
(Bai dace ba ga wani ya yi sujjada ga wani in banda
Allah ba)
Fadin (BAI DACE
BA) kuwa a cikin maganan Allah da manzonsa; ana amfani da shi cikin abin da ya
kai makura wajen hani (da muni); kamar fadin Allah:
ﭽ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ
ﯮ ﭼ [مريم: ٩٢]
(Kuma
bai dace ga mai rahama ba ya riki da), Da fadinsa madaukaki:
ﭽ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰﯱ
ﯸ ﭼ [يس: ٦٩].
(Kuma
bamu ilmantar da shi waka ba, kuma ma bai dace da shi ba), Da fadin madaukaki:
ﭽ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭯ ﭼ [الشعراء:210-٢١١].
(Alqur'ani
Sahidanu ba su su ka sassaukar da shi ba *** kuma bai dace musu ba (saukar da
shi qur'anin) …), Da kuma fadin madaukaki:
ﭽ ﮜ ﮝ
ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮯ ﭼ [الفرقان: ١٨].
(Bai dace da mu ba mu riki waninka a
matsayin majibinta -masoya- ).
Kuma
yana daga cikin shirka da Allah madaukaki; wadda ya ke warware fadin (Allah)
madaukaki:
ﭽ ﭢ ﭣ ﭦ ﭼ
(
A kai kadai mu ke bautawa).
Yana
daga cikin haka: HADA ALLAH DA WANINSA CIKIN LAFAZI; kamar rantsuwa da waninsa,
kamar yadda Imam Ahmad da Abu Dawuud su ka ruwaito daga gare shi (s a w) lallai
shi ya ce:
"
مَنْ حَلَفَ بِغَيْرِ اللَّهِ فَقَدْ أَشْرَكَ "
Ma'ana: "
Duk wadda ya rantse da wanin Allah hakika ya yi shirka ". Hakim da Ibnu
Hibban sun inganta shi.
Ibnu Hibban ya
ce: Hassan bn Sufyan ya ba mu labari, yace Abdullahi bn Umar Alju'ufiy ya bamu
labari, ya ce: Abdurrahim bn Sulaiman ya ba mu labari, daga Alhasan bn
Ubaidullah Annakha'iy, daga Sa'ad bn Ubaidata, lallai ya ce: Na kasance a wajen
Ibnu Umar (Allah ya kara yarda da su); Sai wani Mutum ya a wajensa ya rantse da
ka'aba; Sai Ibnu Umar ya ce: Kaitonka! Kada ka aikata!! Lallai ni na ji manzon
Allah s a w yana cewa:
"
مَنْ حَلَفَ بِغَيْرِ اللَّهِ تعالى فَقَدْ أَشْرَكَ "
Ma'ana:
" Duk wadda ya rantse da wanin
Allah madaukaki to hakika ya yi shirka ".
"
أجَعَلْتَنِي لِلَّهِ ندًّا؟ قل: مَا شَاءَ اللَّهُ وَحْدَهُ "
Ma'ana:
" Shin ka sanya wa Allah kishiya?! Ka ce: Allah shi kadai ya ga dama (ya
nufa).
Tare
kuma da cewa; Lallai Allah madaukaki ya tabbatar wa mutum da nufi (ganin dama;
misali cikin fadinsa:
ﭽ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﭼ [التكوير: ٢٨].
Ma'ana:
" Duk wadda ya so daga cikinku ya yi istikama (tsayuwa akan tafarkin
Allah; tare da bin umurni da hani).
(To
idan shari'a ta hana wannan lafazin) to ya ya kuma ga wadda ya ke cewa: NI NA
DOGARA AKNA ALLAH DA KANKA, KO KUMA NI INA CIKIN KULAR ALLAH DA KULARKA, KO
KUMA BANI DA KOWA SAI ALLAH DA KAI, KO KUMA WANNAN YA SAMU NE DAGA ALLAH DA
KAI, KO KUMA WANNAN NA DAGA CIKIN ALBARKOKIN ALLAH DA ALBARKOKINKA, KO KUMA A
SAMA INA DA ALLAH, A KASA KUMA BANI DA KOWA SAI KAI?!
KA
AUNA tsakanin wadannan laffuzan da su ke fitowa daga bakin yawan mutane da kuma
tsakanin abin da aka hana na lafazin: ALLAH NE DA KAI KU KA NUFE NI DA WANNAN
ALKHAIRIN, sa'an nan sai ka duba wanne daga cikinsu ya fi muni?!
Zai
bayyana (bayan aunawan) maka cewa lallai wadda ke fadin wadannan na karshen shi
ya fi cancantar nisa da:
ﭽ ﭢ ﭣ ﭦ ﭼ
(
A kai kadai mu ke bautawa).
Kamar
yadda shi ya fi cancantar amsan Annabi s a w da ta gabata ga wadda ya fadi
waccar karma! (Ka sanya wa Allah kishiya!). Sa'annanidan har wancan ya ya sanya
manzon Allah s a w kishiya wa Allah; To shi kuma wadda ya fadi wadannan ya
sanya wadda bai yi kusa da manzon Allah matsayi ba wa Allah kishiya!
A
dunkule; Ibadar da aka ambata a cikin fadin:
ﭽ ﭢ ﭣ ﭦ ﭼ
(
A kai kadai mu ke bautawa).
(Wannan
ibadar ita ce): Sujjada, da dogaro ga Allah (tawakkali), mayar da al'amari zuwa
gare shi, da takawa, da tsoro, da tuba, da bakance, da rantsuwa, da tasbihi, da
kabbara, da fadin La'ilaha illal lah, da cewa Alhamdu lillah, da neman gafara,
da aske kai kaskantar da kai ga Allah da bauta, da addu'a; dukkan wadannan
tsantsar hankin Allah ne madaukaki (da bai halatta a juyar da shi ya zuwa
waninsa ba!).
Ya
zo cikin musnad din Imamu Ahmad lallai wani mutum an zo da shi wajen Annabi s a
w al'halin ya aikata wani zunubi, yayin da ya tsaya a gaba gare shi sai ya ce:
"
اللَّهُمَّ إِنِّي أَتُوبُ إِلَيْكَ وَلا أَتُوبُ إِلَى مُحَمَّدٍ؛ فَقَالَ النَّبِيُّ
r: عَرَفَ
الْحَقَّ لِأَهْلِهِ ".
Ma'ana:
" Ya Allah lallai ni ina tuba zuwa gare ka, bana tuba zuwa ga Muhammadu,
Sai (Manzon Allah) s a w ya ce: Ya san gaskiya, kuma ya jingina ta zuwa ga
ma'abocinta".
Kuma
Hakim ya fitar da shi daga hadisin Alhasan, daga Al'aswad bn Sari'I, ya kuma
ce: Hadisi ne ingancecce.
Amma hada Allah kuma da wani cikin nufi da
niyyoyi, to wannan kam kogi ne da bashi da iyaka, wadda kuma kadan ke tsira
daga gare shi; saboda duk wadda ya yi nufin wanin fuskar Allah madaukaki da
aikinsa; To bai tsayar hakikanin fadinsa ba:
ﭽ ﭢ ﭣ ﭦ ﭼ
( A kai kadai mu ke bautawa).
Saboda:
ﭽ ﭢ ﭣ ﭦ ﭼ
( A kai kadai mu ke bautawa). Ita ce taceccen addini (addinin da ba shirka)
addinin annabi Ibrahim; wadda Allah ya umurci dukkan bayinsa da shi, Kuma Allah
ba zai karbi wani addini ba waninsa, kuma shi ne hakikanin musulunci;
ﭽ ﭯ ﭰ ﭱ
ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ
ﭷ ﭸ ﭹ
ﭺ ﭻ ﭼ ﭼ [آل عمران: ٨٥].
Ma'ana:
" Duk wadda ya riki (nemi) wanin addinin musulunci a matsayin addini to ba
za a karba masa ba, kuma lallai shi a lahira yana daga cikin masu hasara
".
Don
haka; ka yi riko da wannan tushen mai asali, Sa'annan duk abin da 'yan bidi'a
da mushirkai su ka fito da shi ka yi kokarin mayar da shi ya zuwa gare shi (don
ka gane, girman nisansa da shi wannan asalin); In ka yi haka za ka tabbatar da
ma'anar kalmar
LA'ILAHA ILLAL LAHU; (za ka tsira).
Da
ko za a ce: AI SHI MUSHIRKAI YA NUFI GIRMAMA ALLAH NE MADAUKAKI; KUMA DON MA
GIRMAN NASA NE (ALLAH) BAI DACE A SHIGA MASA BA SAI DA TSANI DA KUMA MASU CETO,
kamar dai halin masu mulki (sai da kamun kafa); KA GA KENAN SHI MUSHIRKI BAI YI
NUFIN WULAKANTA ALLAH BA, HASALI MA YA YI NUFIN GIRMAMA SHI NE! ya kuma ce:
ﭽ ﭢ ﭣ ﭦ ﭼ
( A kai kadai mu ke bautawa). KUMA AI
INA BAUTA WA WADANNAN TAFINTOTIN (WADDA NA KE KAMA KAFANSU) DOMIN SU KUSANTAR
DA NI ZUWA GARE SHI, SA'AN NAN SU SHIGAR DA NI KANSA; DON HAKA (ALLAH) SHI NE
MANUFA, SU KUMA HANYOYI NE ZUWA GA MANUFA;
In
ko haka ne; don me yasa wannan gwargwadon ya ke hukunta fushin Allah, kuma ya
dawwamar (da mai yinsa) a cikin wuta, sa'an nan ya hukunta zubar da jinin
ma'abutansa, ya halatta matansu da dukiyansu (matan mushirkai da dukiyansu, a
lokacin yaki)?
Kuma
shin –a hankalce- ya halatta Allah madaukaki ya shar'anta wa bayinsa su rika
kusantarsa (bauta masa) da masu ceto da kuma tsanoni, Sai ya zama haramcin hakan
kawai an fa'idanta da shi ne da ya zo cikin shari'a (aya, hadisi) kawai? Ko
kuma hakan mummuna ne a shari'ance da kuma hankalce; wadda kwata-kwata ba zai
yiwu ace wata shari'a daga cikin shari'oin (Allah) sun zo da shi ba??
Kuma
menen sirrin da ya sanya shi ba a gafarta shi sabanin sauran zunbai? Kamar
yadda Allah madaukaki ya ce:
ﭽ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ
ﮬ ﮭ ﮮﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﭼ [النساء: ٤٨].
Ma'ana: " Lallai Allah
baya gafarta a hada shi da wani (shirka, matukar an mutu akai ba a tuba ba); Yana kuma gafarta abin da ke kasa da haka ga wadda ya ga
dama (ya nufa), kuma duk wadda ya hada Allah da wani to hakika ya kirkiri laifi
(zunubi) mai girma "???
(Don Amsa wadannan
tambayoyin) Sai mu ce:
Shirka iri biyu ne; Shirka da
rataya da ZATIN ABIN BAUTA, DA SUNAYENSA DA SIFOFINSA, DA KUMA AYYUKANSA.
Da kuma shirka a cikin YI
MASA BAUTA DA MU'AMALANTARSA; koda kuwa ma'abucin wannan yana kudurta cewa
–Allah madaukaki- ba shi da mai tarayya cikin zatinsa, haka kuma cikin
sifofinsa (wato bai fada cikin shirka da take nau'I na farko ba).
Shi shirka na biyun nan shi
ne mu ka gama magana akansa (dazu), kuma muka sa ke nuni zuwa gare shi –a nan-,
kuma –a gaba- za mu kara magana a kansa kuma mu kosar.
Amma shirkar (nau'in) farko
kuma, to shi kam ya kasu kashi biyu:
Na Farkonsu: Shirkan kore samuwan Allah (wadda
malamai su ka masa lakabi da: SHIRKAN TA'ADIL); Wannan kuma shi ne mafi
munin shirka; (misalinsa) kamar shirkar Fir'auna a cikin fadinsa:
ﭽ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭼ [الشعراء: ٢٣].
(Wanene
Ubangijin halittu?), Ya kuma ce wa Hamana:
ﭽ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞﮟ ﮯ ﭼ [غافر:36-٣٧].
(Gina min gini mai tsayi –bene- tsammani na
zan isa kofofin; kofofin sammai; don na tsinkaya zuwa ga Allan Musa (da ya ke
riyawa), Kai ni ina ma zaton karya ya ke yi).
Shi shirka da kore samuwar Allah ko cancantarsa
ga hakkinsa suna lazimtar juna; don haka duk mushirki to ya kore wa Allah
cikarsa da zama wajibi a siffanta shi da ita, ko kuma ya ma kore samuwarsa.
Haka kuma duk wadda ya yi haka (ta'adil) to mushirki ne. Sai dai kuma shirka ba
ya lazimtar tushen ta'adil; saboda ai ana samun mushirkin da ya tabbatar da
samuwan mahalicci madaukaki da kuma sifofinsa; Sai dai kuma ya wofantar da ba
shi hakkinsa na kadaitawa.
Tushen shirka da kuma
ka'idarsa da ke- kai- komo a kanta shi ne: Ta'adil; Shi kuma ya kasu kashi uku:
Na farkonsu: Kore halitta daga
mahaliccinsa: (misalinsa kamar cewa: Duniyan nan bata da mahalicci, ko aikin
bayi ba halittan Allah ba ne, d. sauransu).
Na biyu: Kore wa mahicci kamalarsa (cikarsa da
bunkasarsa) da ya tabbata masa (cikin ayoyi da hadisai).
Na uku: Tozarta mu'alarsa ga barin abin da ya wajaba
masa akan bawa na hakikanin tauhidi (kadaita shi wajen ibada).
Haka; yana daga cikinsa;
Shirkar kafirai da su ke cewa: Halittu (duniya) babu wani lokacin da su ka faru
– a ta baya; saboda tun da can can… akwaisu- kamar yadda kuma ba lokacin da za
su kare (Ka ga wannan sifar Allah ne shi daya). Kuma su ke cewa: Lallai duk abin
da ya faru (halittu) to sun jingina (dogara) ne ya zuwa wassu sabuba da kuma
tsanoni da su ka hukunta samuwarsu; wadanda su ke kiransu: HANKULA DA RAYUKA (AL'UKUL
DA NUFUUS).
Nau'i na biyu: SHIRKAR
MISALTAWA; (wadda ita ce shirkan wanda ya sanya wa Allah kwatankwaci)
misali shirker wadda ya riki wani abin bautan daban tare da Allah madaukaki;
kamar Nasara (creister) dangane da (Annabin Allah) Almasihu, da kuma yahudawa
dangane da uzairu, da kuma masu bautar wuta (majusawa) da su ka kudure jingina
abubuwan alkhairi ya zuwa ga haske, da kuma abubuwan sharri ya zuwa ga duhu.
Shirkan kadariyya -majusawa wannan al'ummar- an tsakure shi
daga wannan.
Wadannan su ne yawa –
yawan mushirkan duniya, Kuma su bangarori ne masu yawa:
* Daga cikinsu akwai
wadda ke bautawa wassu bangarori na sama (rana, taurari ko wata d. sauransu).
* Daga cikinsu kuma
akwai wadda ke bautawa wassu bangare na kasa (kamar gumaka, kaburbura,
waliyyai, da Annabawa da salihai).
* Daga cikin wadannan
akwai wadda ke riya cewa abun bautarsa shi ne mafi girman abun bauta.
* Daga cikinsu akwai
wadda ke riyawa cewa: abun bautarsa daya daga cikin abubuwan bauta.
* Haka kuma daga cikinsu
akwai wadda ke riya cewa: Idan har ya kebe abun bautar dad a bautarsa, da kuma
yankewa ya zuwa gare shi; Sai abin bautar ya fiskance shi ya kuma lura da shi.
* Kamar yadda a cikinsu
akwai mai riya cewa abun bautarsa na kasa zai kusantar da shi ya zuwa ga abun
bautarsa na sama, shi ko na sama ya zuwa ga na sama da shi; har wadannan
abubuwan bautar su kusantar da shi zuwa ga Allah madaukaki mai tsarki; don haka
wani lokaci –sai ka ga- wadannan shamaki su yi yawa, wani lokacin kuma sai su
yi kadan.
Idan har ka san wadannan
kungiyoyi, kuma ka san tsanantawar kama daga
Manzon Allah s a w ga wadda ya hada Allah madaukaki da wani (shirka) cikin
ayyuka da zantuka da kuma niyyoyi –kamar dai yadda ambaton haka ya gabata- To;
(SAI A CE): KOFAR AMSA WADANNAN TAMBAYOYI (DA SU KA GABATA) YA BUDE MAKA; Sai
mu ce:
Ka sani Lalllai
hakikanin shirka shi ne: Kamanta mai halitta (Allah) da kuma halitta (ko
wanene shi; mala'ika ne ko annabi; ballentana waninsu), da kuma kamanta halitta
da mai halitta.
Amman a farkon ; To
lallai mushrki ya kamanta halitta da mai halitta a cikin abubuwan da allah ya
kebanta da su (WADANDA DA LARABCI AKE KITANSU; KHASA'ISUL ILAHIYYA; kuma shi
ne: cikar zati, da kamalar sunaye da sifofi;wadda ke haifar da cancantar
fiskantar da dukkan bauta zuga Allah kamili shi kadai); sun e kuma kadaitaka da
mallakan cutarwa da amfanarwa, da bayarwa da hanawa; don haka duk wadda ya
rataya hakan zuwa ga wani halitta; to lallai ya kamanta shi da mai halitta
madaukaki, ya kuma daidaita turbaya da ubangijin alloli.
To wani irin fajirci ne,
ko kuma wani irin zunubi ne ya fi wannan girma?!
Kuma ka sani lallai na
daga cikin abubuwa da Allah ya kebanta da su; Gama-garin kamala kuma
tumbatsttse ta kowace fuska; wadda ba nakasa a cikinsa ta kowace fuska daag
cikin fuskoki; hakan kuma na wajabta dukkan bauta ta zama nasa ne shi kadai (da
a fuskantar da ita zuwa ga wani sai shi daya); a hankalce, a shari'ance da kuma
a fidirance (wato yadda ya Allah ya kimtsa wa bayinsa lokacin day a halicce
su). Duk kuma wadda ya sanya hakan ga
waninsa (wanin Allah; ya bauta masa) to lallai ya kamanta wannan din da wadda
ba shi da makamanci. Kuma saboda tsananin muninsa (shirka; kamanta wani da
Allah) da kuma yadda hakan ya kunshi kololuwan zalunci; Shi yasa ( Allah) da ya
wajabta wa kansa rahama ya bada labari kan
har abada ba zai gafarta shi ba ( baya kankare shirka).
Sai dai yayin da Shedanu
su ka jirkita (canza) fidirorin yawa-yawan halitta (mutum da aljan) su ka kuma
gusar da su daga kan addininsu, su ka umurce su su hada Allah (da wassunsa;
shirka) wadda Allah bai saukar da dalili ba akan haka, -kamar yadda mafi sanin Allah kuma mafi sanin bayin Allah
(Manzon Allah s a w) ya ruwaito haka
din-; (Su ko mushirkai) sun makanta ga sanin shirka har su ka yi zatonsa a
matsayin abu mai kyau.
Amma a bangaren
kamantuwa To;
Duk wadda ya ya girmama,
ya yi girman kai, sa'an nan ya kirayi mutane ya zuwa ga wuce gona-da-iri, da fatan samun abin da ke
wajensa, da tsoronsa … To lallai hakika ya nemi kamantuwa da Allah, kuma ya yi
jayayya da shi cikin rububiyyarsa (da ma sunayensa da sifofinsa); don haka; ya
cancanci Allah ya wulakanta shi matukar wulakantawa, sa'an nan ya sanya shi ya
zama kamar kwayar zarra (don kaskanci; sabanin abin day a nema na girma dab a
hakkinsa ba ne) karkashin diddigen halittunsa.
Ya zo cikin Sahihu
Muslim da Annabi s a w, lallai shi ya ce:
"يقول اللَّهُ U: الْعَظَمَةُ
إِزَارِي، والْكِبْرِيَاءُ رِدَائِي؛ فَمَنْ نَازَعَنِي وَاحِدًا مِنْهُمَا عذّبتُهُ
"
Ma'ana: " Allah yana cewa: Girma tufa ta ne (da na kadaita da
siffantuwa da ita), girman kai mayafina; Duk wadda ya yi jayayya da ni daya
daga cikinsau (ta hanyar siffantuwa da shi) To zan azabtar da shi ".
Kuma idan mai daukar hoto; da ke daukar daukar hotunan da hanunsa
yana cikin wadanda su ka fi tsananin azaba a ranar tashin kiyama; saboda ya yi
kamancecceniya da Allah a gundarin sana'ntawa; To menene kuma zatonka da wadda
ya ke kamantuwa da Allah cikin rububiyya da uluhiyya? Kamar yadda Annabi s a w ya ce:
" أَشَدُّ النَّاسِ عَذَابًا يَوْمَ
الْقِيَامَةِ الْمُصَوِّرُونَ، يُقَالُ لَهُمْ: أَحْيُوا مَا خَلَقْتُمْ "
Ma'ana: " Lallai mafi tsananin azaba ranar kiyama su ne: masu
dauakr hoto; za a ce musu: ku raya abin da ku ka halitta ". Ya zo kuma
cikin Sahihul Bukhari da Muslim daga
Annabi s a w; lallai shi ya ce:
" يَقُولُ اللَّهُ U: وَمَنْ
أَظْلَمُ مِمَّنْ ذَهَبَ يَخْلُقُ كَخَلْقِي؛ فَلْيَخْلُقُوا ذَرَّةً فليخْلُقُوا شَعِيرَةً
".
Ma'ana:
"Allah yana mabuwayi da daukaka yana cewa: Babu wadda ya fi zalunci fiye da
mutumin da ya tafi yana halitta irin halittata; to su halicci kwayan zarra, su
kuma halicci Sha'ir ". ( A cikin hadisin) Sai Allah ya fadakar (da mutane)
da kamar kayar zarra, sha'ir don ya ya yi nuni kan (rashin iya halittar) abin da ke sama da
su!
Haka kuma mutumin da ya yi kamancecciniya da shi madaukakin sarki
a cikin sunan da baya dacewa sai da shi (shi kadai) kamar; Sarkin sarakuna, Mai
hukuncin masu hukunci, da kuma Alkalin alkalai … da makamantansu; ya tabbata a
cikin Sahihul Bukhari da Muslim daga Annabi s a w; lallai shi ya ce:
"
إنّ أَخْنَعُ الأَسْمَاءِ عِنْدَ اللَّهِ رَجُلٌ تَسَمَّى بشَاهَانْ شَاهْ؛ مَلِكِ
الْملوكِ، لا مالك إلا الله "
Ma'ana: "Lallai yana daga cikin mafi munin sunaye a wajen
Allah; Mutumin da ya sa wa kansa suna: SHAHAN-SHAH; Sarkin sarakuna, babu sarki
(mai mulki) sai Allah".
A cikin wanilafazi:
"
أَغْيَظُ رَجُلٍ عند اللَّهِ رَجُلٌ تسَمَّى مَلِكَ الأَمْلاكِ ".
Ma'ana:
" Mutumin da ya fi bakanta wa Allah rai shi ne: Mutumin da ya sa wa kansa
suna: Sarkin sarakuna … "
A dunkule dai; Kamantawan (wata halitta da
mahaliccinta) da kamantuwa wannan shi ne hakikanin shirka; shi ya sa ma wadda
ya yi zaton cewa: Idan ya nemi kusantuwa da wata ibada zuwa ga wanin Allah, wai
wannan wanin zai kusantar da shi zuwa gare shi madaukaki; to idan ya yi haka ya
yi kuskure; saboda ya kamanta shi da shi, ya kuma yi abin da (ibada) da bai
dace ga wani ba sai ga shi (Allah); sai ya hada wanin Allah da Allan a cikinta;
ya kuma tauye wa madaukaki hakkinsa; Yin haka kuma mummuna ne a hankalce da kuma
shari'ance;
Shi
ya sa ba shar'anta (yin shanin ba), kuma ba a gafarta wa mai aikata shi.
Kuma
ka sani Lallai wadda ya yi zaton cewa: Lallai Ubangiji baya ji, ko baya amsa
(addu'a ko karbar bauta) sai in an yi ta da kamun kafa (tsani); wadda za su
tsinkayar da shi hakan, ko kuma su roki abin da aka roka daga gare shi; To lallai irin wannan mutum ya yi mummunan
zato da Allah;
Saboda
in har ya yi zaton cewa (Allah) baya sanin (abin da aka roke shi), ko kuma ba
ya ji Sai waninsa ya isar masa (ya ilmantar da shi) ko ya jiyar da shi; to
wannan kore wa Allah ne: iliminsa, da jinsa, da kuma cikar riskarsa ga abubuwa,
Hakan kuwa ya ishe ka girman zunubi!
In
kuma har ya yi zaton cewa (Allah) na ji, kuma na gani, sai dai kuma ana bukatan
wadda zai (lallabe shi) ya sa ya ji tausayin bayinsa, kuma ya tattausar da shi
akansu; To ya munana zato kan
falalolin ubangijinsa, da kyautatawarsa, da kuma yalwar kyautarsa.
A dunkule dai: Mafi girman zunubai a wajen
Allah madaukaki shi ne: Munana zato da shi (allah); Shi ya sa ya fadi narkon
azabarsu mai girma a cikin littafinsa (Alqur'ani) akan munana zato da shi,
kamar yadda madaukaki ya ce:
ﭽ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟﮠ ﮡ ﮢ ﮣﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﭼ [الفتح: ٦].
Ma'ana: " (Munafikai
da mushirkai) masu yi mummunan zato ga Allah, mugunyar masifa mai kewayewa ta
tabbata akansu, kuma Allah ya yi fushi da su, ya kuma tsine musu, ya musu
tanadin jahannama; tir da ita (ta kasance) makoma. Madaukaki yana cewa dangane
da masoyinsa (Annabi) Ibrahim a. s:
ﭽ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﭼ [الصافات:86-٨٧].
"
A karya, abubuwan bauta koma bayan Allah ku ke nufa (da bauta) ** To menene
zatonku da ubangijin halittu?
Ma'ana:
Menene zatonku kan abin da zai muku sakayya idan har kuka bauta wa waninsa tare
da shi, Sa'an nan ku ka yi zaton cewa (Allah) na da bukatar wajen tsinkayar
bukatun bayinsa = yana bukatar wadda zai zamo kamar kofa na bukatunsu zuwa gare
shi (shamaki), da makamancin haka?
Wannan
kuma sabanin sarakuna (masu mulki); wajen bukatuwansu bukatuwa ta lalura (dole)
zuwa ga tafintoti; saboda bukatuwansu da gazawansu, da rauninsu, da kuma
gajercin (karancin) iliminsu kan
sanin bukatun masu bukata, lalura (talakawa).
Amma
wadda jin wani wani maganan ba ya shagaltar da shi ga barin jin wani (Alllah
kenan), wadda rahamarsa ta rinjayi fushinsa, ya kuma wajabta wa kansa rahama,
To me tafintoti za su yi a wajensa?! Duk kuwa wadda ya riki tafinta a
tsakaninsa da tsakanin Allah madaukaki to hakika ya zata masa mafi munin zato.
Kuma hakan korerre ne Allah ya shar'anta shi ga bayinsa, kai! Dadin- dadawa, hakan
korerre ne a cikin kwakwale da fidrori.
Kuma ka sani lallai kan-kan-da-kai da bauta
da Bawa ke sanya shi ga wadannan tafintoti mammuna ne shi a karan-kansa –kamar
yadda mu ka zayyana-; musamman ma idan wadda aka yi masa haka (aka yi masa
ibadar): Bawa ne na MAI MULKI, MAI GIRMA, MAI RAHAMA, MAKUSANCI KUMA MAI
AMSAWA; kamar yadda Allah ya ce:
ﭽ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆﮇ
ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘﮙ
ﮟ ﭼ [الروم: ٢٨].
(Allah " Ya buga muku misali daga karan-kanku; Shin kuna
abokin tarayya daga cikin abin da damarku ta mallaka (bayinku) kan abin da mu ka azurta
ku! Da ku ke tsoronsu kamar yadda ku ke tsoronsu kamar tsoronku ga karan kanku
".
Ma'ana:
Idan dayanku na kin a ce bawansa da ya mallaka ya yi tarayya da shi cikin
arzikinsa, to ta yaya za ku sanya mini wassu daga cikin bayina abokan tarayya
cikin abin da ni kadai na kebanta da shi; wadda shi ne cancantar bauta bauta da
na ked a shi, wadda kuma bat a dacewa ga wanina, kuma bata inganta ga wadda ba
nib a; Duk kuwa wadda ya riya haka to bai girmama ni iyaka girmama ta.
A
dunkule; Duk wadda ya bauta wa wanin Allah tare da shi da zaton wai zai isar da
shi zuwa gare shi, (to wannan) bai girmama Allah ba iyaka girmama shi; Allah
yana cewa:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖﭗ ﭘ ﭙ
ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫﭬ ﭭ ﭮ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵﭶ ﭷ
ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ الحج:73-٧٤].
(Ya ku mutane! An buga mu ku misali; ku saurara masa; Lallai
wadanda ku ke roko (bauta) koma bayan Allah ba za su taba iya halittan kuda ba
koda kuwa sun taru masa (saboda rauninsu), kuma idan kuda ya dauke mu su wani
abu ba za su iya tsamo shi ba (kwato shi) daga gare shi, mai nema da abin da
ake neman sun yi rauni (wadda ake bauta masa … ya yi rauni) ** (mushirkai) ba
su girmama Allah ba iyaka girmama shi; lallai Allah mai karfi ne mabuwayi ).
(Allah)
Madaukaki ya ce:
ﭽ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ
ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﭼ [الزمر: ٦٧].
(Kuma basu girmama Allah ba iyaka girmama shi; Kassai gaba daya
damkarsa ne a ranar tashin alkiyama, sammai kuma suna nade a damansa, tsarki ya
tabbata masa kuma ya daukaka ga barin abin da su ke tara
shi da su (shirka).
Don haka; Bai girmama (Allah ) mai karfi
mabuwayi ba wadda ya tara shi (ya yi masa
shirka) da mai rauni makaskanci.
Kuma –ka sani- Idan ka yi lura cikin daukacin
(dukkan) kungiyoyin bata da bidi'a ('yan bidi'a gaba dayansu) za ka samu cewa;
Tushen batansu yana komawa ne zuwa ga abubuwa guda biyu:
Na
farkonsu: Mummunan Zatonsu ga Allah.
Na
biyu: Lallai ba su girmama shi ba iyaka girmamawansa;
Lallai
wadda ya yi zaton cewa Allah bai turo wani manzo ba, kuma bai saukar da wani
littafi ba; kawai dai ya bar halitta
haka siddan (ba umurni ba hani), ya kuma halicce su don wasa, to hakika bai
girmama shi ba iyaka girmamawansa.
Kuma
bai girmama shi ba iyaka girmamawa wadda ya kore masa gamewar ikonsa (ga dukkan
halittu da ayyukansu), da kuma ratayarta da aiyukan bayinsa; da'arsu ne da
sabonsu, ya kuma cire su (aiyukan bayin) daga cikin halittunsa da kuma ikonsa
(Wadannan mutanen su ake kira da KADARIYYA).
Kuma
bai girmama shi ba iyaka girmamawa kishiyoyin wadannan; wadanda su ka ce (su ka
kudurta):Allah yana horo wa bawansa akan abin da bawan bai aikata ba, wai Allah
yana masa horo ne kan
aikinsa shi Allan mai tsarki (Wadannan mutanen su ake kira da JABARIYYA).
Kuma
idan ya koru a kwakwale a ce shugaba ya tilasta wa bawansa kan aikata wani aiki, sa'an nan sai ya masa
horo akansa, To ta yaya wannan zai kasance daga mafi adalcin adilai (Allah),
Zancen wadannan (Jabariyya) ya fi sharri fiye da zancen masu kama
da majusawa; wato kadariyya makaskanta.
Kuma
bai girmama shi ba iyaka girmamawa WADDA ya kore rahamarsa da soyayyarsa, da
yardarsa da fushinsa, da hikimarsa a sake , da hakikanin aikinsa, kuma
bai sanya masa wani aiki ba da zabinsa; kawai dai aiyukansa halittu ne da su ke
daban da shi (masu wadannan kuduri su ne ASHA'IRAH).
Kuma bai girmama shi ba iyaka girmamawa WADDA
ya sanya masa mata da 'da, (KAMAR MUSHIRKAN LARABAWA, DA YAHUDU DA NASARA) ko
kuma ya sanya shi ya zama yana shigewa cikin abubuwan da ya halitta (KAMAR
HULULIYYA), ko kuma ya sanya shi ya zama shi ne zatin wannan duniyar (KAMAR
'YAN WAHDATUL WUJUD).
Kuma
bai girmama shi ba iyaka girmamawa WADDA ya ce: (Allah) ya daukaka makiyan
annabinsa da kuma iyalen gidansa (MASU WANNAN MAGANAR SU NE: RAFIDA; 'YAN
SHI'A) kuma su ka ce; (Allah) ya sanya mulki cikinsu (wato; suna nufin
sahabbai; ta yadda Allah ya bada khalifanci wa Abubakar, Umar, sa'an nan
Uthmanu radiyallahu anhum, kafin bawa Aliyu –r. a-), wai kuma ya kaskantar da
manzonsa da kuma iyalen gidansa (ahlul baiti); Wannan ya kunshi matukar sukar
ubangiji; Allah madaukaki ya daukaka ga barin zancen rafidawa ('yan shi'a).
Wannan kuma ('yan shi'a) sun tsamo shi ne daga fadin Yahudawa da Nasara
(creister) kan ubangijin halittu; cikin cewarsu: (Allah) ya turo wani mai mulki
ne azzalumi sai ya riya cewa shi Annabi ne, ya kuma yi karya wa Allah, ya zauna
wani zamani mai tsayi (Manzon Allah ya yi shekara 23), alhali yana cewa:
(Allah) ya umurce ni da kaza, ya kuma hana ni kaza, (shi wannan mai riya
annabcin, a cewarsu): ya ci gaba da halatta jinanen annabawan Allah da waliyyaensa
(masoyansa); Shi kuma Allah madaukaki yana ta daukaka shi, yana karfafa shi,
sa'annan kuma ya yi ta tsayar da dalilai da mu'ujizozi kan gaskiyarsa, haka
kuma ya yi ta fiskantar da zukatan halittu da jikinsu ya zuwa gare shi (su ka
yi ta imani da shi) yana mai tsayar masa da daularsa; tana ta daukaka da
karuwa, ya kuma kasakntar da makiyansa, fiye da shekara dari takwas (wato har
lokacin da mai littafi ya ke rubuta shi).
Ka
auna tsakanin maganan wadannan (Yahudu da Nasara akan Annabi s a w) da kuma
maganan 'yan uwansu Rafida 'yan shi'a (kan Sahabban Manzon Allah s a w) za ka
samu ceawa maganganu biyu daya ne.
Kuma
bai girmama shi ba iyaka girmamawa WADDA ya riya cewa Allah ba zai rayar da
mamata ba, kuma ba zai tashi wadanda su ke cikin kabari ba, domin ya bayyana wa
bayinsa abin da su ka kasance su ke ta sabani, sa'an nan kafirai su san cewa
sun kasance –a rayuwarsu ta duniya- makaryata.
A dunkule dai;
Wannan (maganar) kofa ne mai fadi, manufa dai shi ne; Lallai duk wadda
ya bauta wa wanin Allah tare da Allah to lallai ya bauta wa Shedan; Allah yana
cewa:
ﭽ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ
ﭻ ﭼﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﭼ [يس: ٦٠].
Ma'ana:
" Shin ban yi alkawari ba ne zuwa gare ku, Ya ku 'yan adam cewa kada ku
bauta wa shedan; domin shi a gare ku makiyi ne mai bayyana adawa! ";
Don
haka; Wani ba zai bauta wa wani ba daga cikin 'yan adam –ko kuma wanene shi-
face bautarsa ta auku ga shedan; Sai mai bautar ya dan ji da'di da abin bautar
nasa wajen samun biyan bukatarsa, Shi kuma wadda aka bauta masan shi ma ya ji
da'di da da wadda ya bauta masan; wajen girmama shi da ya yi, da kuma gama shi
(shirka) da Allah madaukaki, WANNAN KUMA SHI NE KOLOLUWAN ABIN DA SHAIDAN YA
YARDA DA SHI; Shi yasa Allah madaukaki ya ce:
ﭽ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ
ﮎ ﮏ ﮐﮑ ﭼ
" (Ya Muhammad! Ka ambata musu) ranar da Allah zai tattara
su gaba daya, (yana mai ce musu): Ya ku taron Aljanu kun ya waita wa mutane
" Ma'ana: Kun yawaita tabar da su da kuma batar da su, (Allah ya ci gaba
da cewa:
ﭽ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞﮟ ﮠ ﮡ
ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﭼ [الأنعام: ١٢٨].
( Sai majibintansu daga mutane su ce: Ya ubangijinmu; Lallai
sashenmu ya ji dadi da sashe, ya zuwa ajalin da ka yanka mana! Sai ya ce: Wuta
ce makomarku, kuna masu tabbata a cikinta, sai abin da Allah ya nufa; Lallai ubangijinka
mai hikima ne masani".
Lallai abin da ya gabatan nan nune karami kan
dalilin da yasa shirka ya zama shi ne mafi girma a wajen Allah kan kowane
babban laifi (KABA'IR), kuma lallia shirka ba a gafarta shi matukar ba a tuba
ba daga gare shi, haka kuma shi na wajabta dawwama a cikin azaba mai girma.
Kamar kuma yadda haramcinsa da muninsa ba wai kawai ya kasance ba ne saboda
tsurar hani da aka yi a kansa (a cikin Alqur'ani da hadisai) ba ne, A'ah! Yana koruwa ga Allah s w t ya shar'anta (wa bayinsa)
bautar wani abun bauta koma baya gare shi, kamar kuma yadda ya ke korerre ne a
gare shi duk abin da zai warware sifofin kamalarsa da daukakarsa.
*********
[KASUWAN MUTANE KASHI HUDU DANGANE DA
BAUTAR ALLAH MADAUKAKI DA NEMAN TAIMAKONSA]
Sa'an nan ka sani Lallai mutane dangane da
bautar Allah madaukaki da neman taimakonsa sun kasu zuwa kashi hudu:
MAFI
GIRMANSU DA FIFIKONSU SU NE: Ma'abota ibada da kuma neman taimakon Allah akan
haka; (su wadannan mutanen) Bautar Allah ita ce karshen manufarsu, Neman kuma
ya taimake su akanta, ya kuma datar da su wajen tsayuwa da ita shi ne karshen
burinsu; Shi yasa ya zama mafi girman abin da aka roki Ubangiji (Allah) ta'ala
akansa shi ne: NEMAN TAIMAKONSA KAN YARDARSA; Kuma shi ne abin da Annabi s a w
ya koyar da shi wa Mu'azu (bn Jabal r a) ya ce:
" يَا مُعَاذُ! واللهِ إِنِّي لأُحِبُّكَ؛ فَلا
تَدَعْ أَنْ تَقُولَ فِي كُلِّ صَلاةٍ: اللهم أَعِنِّي عَلَى ذِكْرِكَ، وَشُكْرِكَ،
وَحُسْنِ عِبَادَتِكَ "
Ma'ana: "
Ya Mu'azu! Wallahilalallai ni ina sonka; don haka; Kada ka bari fadin –bayan kowace salla-: Ya Allah ka
taimake ni kan
ambatonka, da gode maka, da ku yi maka mafi kyan bauta ".
Don haka; Mafi
amfanin addu'a shi ne: Neman taimako kan abubuwan da Allah
madaukaki ya yarda da su.
WADANDA SU KE KISHIYANTAR WADANNAN KUMA SU
NE; 'Yan kaso na biyu: Masu kawar da kai ga barin bautar Allah da neman
taimakonsa; Su wadannan basu da bauta kuma basu da neman taimako, Kai! –in da
ma- 'dayansu zai roki madaukaki, ya kuma nemi taimakonsa, To zai roke shi ne kan rabonsa da
sha'awowinsa.
Shi kuma Allah
s w t duk wadanda su ke cikin sammai da kassai suna rokonsa; Masoyansa da
makiyansa duk suna rokonsa; Sai kuma ya ba wa wadannan, ya bawa wadannan.
Kuma mafi
kiyuwan halittunsa a wajensa shi ne IBLIS; amma duk da haka; Allah ya amsa masa
addu'arsa, ya kuma biya bukatarsa, ya jiyar da shi dadi da ita, Sai dai kuma
yayin da bai zama taimako kan
biyayya wa Allah ba, sai ya zama karin tabewarsa da nisansa.
To kuma haka
abun ya ke ga duk mutumin da ya roki madaukaki, ya kuma nemi taimakonsa akan
abin da ba mai taimakonsa ba ne kan
biyayya wa Allah, Sai rokonsa ya zama mai kara njisantar da shi daga Allah.
Don haka mai hankali ya yi tunanin wannan,
Sa'an nan ya san cewa: Amsa addu'ar da Allah ya ke yi ga wassu masu rokon, Ba
wai saboda karamarsu ne (matsayinsu ne) a wajensa ba. Kai ai wani lokaci ma bawa ya kan roke shi wata
bukata; Sai kuma ya biya masa ita, alhali a cikinta akwai halakarsa, (a irin
wannan yanayin) hana bawan abin da ya roka shi ne kariyarsa da gyaransa. Kawai
dai kiyayeyye shi ne wadda Allah ya kiyaye, Mutum kuma shi ya fi sanin kansa.
Shi kuma alamar
wannan (abin da aka ambata a baya) Shi ne: Ka kan ga mutumin da Allah ya kare
shi daga haka (abin da halakarsa ke cikinsa) alhali yana mai jahiltar hakikanin
al'amarin; Idan ya ga (Allah) mai tsarki yana biyan bukatun wassunsa sai ya
munana zatonsa da madaukaki, zuciyarsa ta cika da haka (munana zato ga Allah)
alhali bai sani ba. Kuma (wata alamar haka) ita ce: Jin haushin abubuwan da aka
kaddara, da kuma zarginsa –ta cikin zuciyarsa- a gare ta.
Kuma hakika Allah madaukaki ya yaye wannan
ma'anar iyaka yayewa (ya kuma yi bayaninsa dalla-dalla) a cikin fadinsa
madaukaki:
ﭽ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ
ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪﮫ ﮰ ﭼ [الفجر:15-١7].
( Amma mutum idan
ubangijinsa ya jarrabe shi; sai ya karamta shi, ya kuma ni'imta shi, Sai ya ce:
Ubangijina ya karrama ni *** Amma idan ya jarrabe shi; Sai ya kuntata masa
arzikinsa Sai ya ce: Ubangijina ya walakanta ni *** A'a ha, (al'amarin ba haka
ya ke ba!).
Ai; Ma'ana:
Al'amarin ba haka ya ke ba; Saboda ba duk wadda na masa baiwa ba ne, na yi masa
ni'ima, na kuma sakar masa ba ne, wai na karrama shi; sai dai na kan yi haka da
nufin jarabawa daga waje na zuwa gare shi; don na ga shin zai gode min sai na
masa baiwa fiye da yadda na ba shi, ko kuma zai kafirce min (ya butulce) sai na
kwace daga gare shi, na kuma canza shi ya zuwa waninsa!
Haka kuma ba
duk wadda na jarrabe shi ba ne; na kuntata masa arzikinsa; ta yadda na sanya
(arzikin nasa) kan wani gwargwadon da bai fi bukatarsa ba, cewa hakan wai
saboda kaskancinsa ne a wajena; Sai dai kawai (hakan) ya kan zamo jarabawa ne
daga gare ni zuwa gare shi; don na ga shin zai yi hakuri ne; sai na bashi
ninkin ba ninkin abin da ya kufce, ko kuma zai yi ta nuna fushi sai ya zamo
rabonsa shi ne fushin?
A dunkule; Allah madaukaki ya yi bayanin cewa
lallai karramawa da wulakantawa ba sa rataya kan dukiya da kuma yalwar arziki, da kuntata
shi; Saboda Allah mai tsarki yana yalwata wa kafiri, ba don matsayinsa ba
(karamarsa a wajen Allah ba). Haka kuma ya kan kuntata (arziki) ga mumini ba wai don
shi kaskantacce ne a wajensa ba. Kawai dai abin sani (Allah) mai tsarki ya kan karrama (wadda ya
so) daga cikin bayinsa; ya kuma datar da shi zuwa ga SANINSA DA SONSA DA
BAUTARSA TARE DA NEMAN TAIMAKONSA.
Don haka;
Kololuwar tsira ta har abada na kasancewa ne cikin bautar allah da kuma neman
taimakonsa akanta.
KASHI NA UKU:
Su ne wadanda su ke da nau'in bauta ba tare da neman taimako (Allah) ba;
Wadannan nau'I
biyu ne:
Na farko:
Ma'abuta kaddara da su ke cewa (su ka kudure cewa): Lallai (Allah) mai tsarki
ya gama aikata wa bawa duk abin da ya ke da iko na ludufi (maban banta), kuma
ba wani taimako kan wani aiki da ya saura masa; saboda ya riga ya taimake shi
ta hanyar halitta masa gabbai da kuma bashi lafiya a cikinsu, ya kuma nusar da shi
hanyar (tsira), ya turo manzo, sa'an nan ya bashi damar yin aiki; don haka babu
wani taimako da ke da iko kanta wadda (bawan) zai tambaye shi ita.
Wadannan an
tabar da su, kuma an dogarar da su zuwa ga kayukansu, An kuma toshe musu kofar
neman taimako da tauhidi; Ibnu abbas –Allah ya kara musu yarda- ya ce:
"
الإيمان بالقدر نظام التوحيد؛ فمن آمَن بالله، وكذَّب بقدره نقض تكذيبُه توحيدَه
".
Ma'ana: "
Imani da kaddara shi ne wani tsari ne (igiya) da ya rike tauhidi; Don haka duk
wadda ya kadaita Allah, sa'an nan ya karyata kaddara to karyatawarsa ya warware
tauhidinsa ".
Nau'I na biyu: Su ne wadanda su ke da ibada da da wuridin
(zikrori ko karatun alqur'ani ko salla, ko duka), Sai dai kuma rabonsu na
tawakkali (ga Allah) da neman taimakonsa yana da rauni; saboda zukatansu ba su
yi yalwar da za su kulla sabbuba da kuma kaddara ba (shi ya sa su ke ga tun da
su allah ya kaddara musu yi masa bauta to wannan abun ba shi da wassu sabbuba;
wadda hakan sai ya kai su ya zuwa ga rashin neman taimakonsa da dogara da shi),
sa'an nan su sabbuban idan aka tobe su daga abin da Allah ya kaddara (wajen
rashin tasirinsu) kamar mamacin da ba shi da wani tasiri ne, kai kamar babu ne
da bai taba samuwa ba, Shi kuma kaddaran kamar rai ne da ke motsa sabbuban,
sa'an nan kuma ya rataya akan mai motsawa na farko (Allah).
Su wadannan mutanen
basirarsu ba ta wuce ganin sababi ya zuwa ga mai sanya sababin ba (Allah), haka
kuma bata wuce ganin abin da aka yi halitta da shi ba ya zuwa ga wadda ya yi
halittan (wato sun kasa hada tsakanin sababi da kuma Allah da ke sa sababin da
ya halitta ya yi tasiri; domin shi ya halicci sababi, kuma shi ke sa shi ya yi
tasiri); Don haka; Sai rabunsu na neman agaji ya yi karanci.
Wadannan mutanen su na da rabo na tasarrufi
gwargwadon dan neman taimakon da su ka yi da kuma dogararsu (ga Allah), Suna
kuma da rabo na rauni da tabarwa gwargwadon karancin neman taimakonsu da
tawakkalinsu; saboda da bawa zai dogara ga Allah iyaka dogara akansa (dogara na
hakika) wajen gusar da dutse (mai girma) daga gurbinsa da (Allah ya taimake
shi) ya gusar da shi.
Idan da za a ce: Menene hakikanin neman
taimakon a aikace??
Sai mu ce:
(Neman taimako) Shi ne in an fadi lafazin tawakkali ake nui da shi; Shi kuma (neman taimako) wani hali ne a cikin
zuci da ke haifuwa saboda sanin Allah madaukaki, da kuma (sanin) kadaituwarsa
da yin halitta da al'amari da juya al'amari, da cutarwa da amfanarwa, haka kuma
duk abin da ya so shi ya ke kasancewa abin da bai so ba kuma baya kasancewa;
SAI WADANNAN ABUBUWAN SU WAJABTA DOGARA AKANSA, DA FAWWALA ABUBUWA ZUWA GARE
SHI, TARE DA SAMUN AMINTUWA DA SHI.
SAI jinginan
bawa zuwa gare shi madaukaki ya zama kamar jinginuwan 'da ne zuwa ga iyayensa
kan abin da ya sako shi a gaba na abin da ya ke fatan samu (kaunar samu) ko
kuma tsoro; da wani abin da aka hukunta zai dufafo shi na cutuwa zai dufafo
shin to da ba zai fake ba sai zuwa gare su (ubansa da uwarsa); Idan bawa –tar
da wannan dogaran- ya kasance daga cikin masu takawa sai kyakkyawar makoma,
kuma abar yabo ta kasance masa; domin:
ﭽ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ
ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﯚ ﭼ [الطلاق:2-٣].
(
Duk wadda ya ji tsoron Allah; to zai sanya masa mafita *** Ya kuma azurta shi
ta yadda baya tsammani, Duk wadda ya dogara ga Allah, Allah ya isar masa ).
Kaso na hudu: Su ne wadanda su ke da neman
taimako ba tare da bauta ba, Wannan kuma shi ne halin wadda ya shaida wa Allah
da cutarwa da amfanarwa, amma kuma bai san abubuwan da (Allan) ya ke so kuma ya
yarda da su ba; don haka sai ya dogara akansa a cikin rabonsa (na duniya), sai
Allan kuma ya taimake shi ya bashi su.
Irin wannan
mutum bashi da kyakkyawar makoma; kuma daidai ne abin da aka bashin dukiya ne
ko kuma mulki ko matsayi a wajen halitta ko makamancin wannan; saboda abin da
ya samun kawai shi ne rabonsa a duniyarsa da lahirarsa.
[SHARRUDAN
KARBAN AYYUKA GUDA BIYU; IKHLASI TARE DA KOYI DA MANZO]
Kuma ka sani lallai bawa baya kasancewa bawan
Allah na hakika (da ake karbar aikinsa) sai da tabbatar da asaloli guda biyu:
Na farkonsu: Bin manzon Allah s a w.
Na biyu: Tace bauta (da yinta ga Allah shi
kadai; ikhlasi).
[KASUWAN MUTANE KASHI HUDU DANGANE DA WANNAN]
Mutane akan wadannan asaloli guda biyu sun
kasu kashu hudu:
Na farko:
Ma'abota ikhlasi (yi don Allah) da kuma bin Manzon Allah s a w: Wadannan
aiyukansu da zancensu dukkansu suna yinsu ne don Allah, da hanawansu da
bayarwansu, da sonsu da kinsu, dukkan wannan ya kan kasance ga Allah ne madaukaki, ba sa
nufan wani sakamako ko godiya daga bayi. ('Yan wadannan kason) sun dau mutane
kamar wadanda ke cikin kabari; basa mallakan cutarwa ko amfanarwa, haka (basa
mallakan) kashewa, rayarwa, ko tayarwa; saboda ba wadda ke mu'amalantar wani
daga cikin halittu (ya nema daga wajensa; yana mai barin Allah) sai saboda
jahiltarsa ga Allah, da kuma jahiltarsa ga halitta.
Shi kuma ikhlasi shi ne: Aikin da Allah baya
karba wa mai aiki aikinsa da ya dace da sunna (Annabi s a w) ba tare da shi ba
(ikhlasi), kuma shi ne allah ya lazimta wa bayinsa aikata shi har zuwa mutuwa,
(Allah) madaukaki yana cewa:
ﭽ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢﭣ ﭤ
ﭥ ﭦ ﭧ ﭼ [الملك: ٢ ].
(Domin
-Allah- ya jarrabe ku wanene daga cikinku ya fi kyan aiki).
Ya kuma ce:
ﭽ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ
ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ [الكهف: ٧ ].
(Lallai
mun sanya abin da ke kan
kasa ya zama ado a gare ta, domin mu jarrae ku wanene daga cikinku zai fi kyan
aiki ).
KUMA MAFI KYAN
AIKI SHI NE: Wadda ya fi ikhlasi, kuma ya fi dacewa da zama sawaba (daidai da
koyarwar manzon Allah s a w; don haka;
Aiki tacecce
(mai ikhlasi) shi ne: wadda ya aka yi shi don Allah.
Shi kuma wadda
ya dace shi ne: Ya zama daidai da sunnar manzon Allah s a w.
Kuma shi wannan
aiki na kwaren shi ne aka ambata a cikin fadinsa madaukaki:
ﭽ ﰐ ﰑ ﰒ
ﰓ ﰔ ﰕ ﰖ ﰗ ﰝ ﭼ [الكهف: ١١٠ ].
(Duk
wadda ke fatan haduwa da ubangijinsa (lami lafiya) to ya yi aiki aiki na
kwarai).
Kuma shi ne
aiki mai kyau cikin fadin (Allah) madaukaki:
ﭽ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ
ﮖ ﮗ ﮘ ﮢ ﭼ [النساء: ١٢٥].
(Babu
wadda ya fi kyan addini fiye da wadda ya mika fiskarsa ga Allah (tare da
ikhlasi), alhali yana mai kyautata aiki ).
Kuma shi ne Annabi s a w ya yi umurni da shi a
cikin fadinsa:
" كلّ عَمِلٍ لَيْسَ عَلَيْهِ أَمْرُنَا فَهُوَ رَدٌّ"
(Kowani
aikin da babu umurninmu akansa to shi abun mayarwa ne).
Kuma dukkan
aikin da aka yi shi ba koyi (da Manzon Allah s a w) to ba zai kara komai wa mai
aikata shi ba sai nisantarwa daga Allah, saboda Allah madaukaki ana bauta masa
ne da umurninsa, ba da son zuciya ba ko ra'ayoyi ba.
Nau'I na biyu: Su ne wadanda ba su da ikhlasi
kuma ba su da koyi da (Annabi s a w); Wadannan su ne mafi sharrin halittu, Su
ne masu sa rigar ayyukan alkhari, suna riya da su awa mutane.
Wannan nau'in
su kan yi yawa cikin wadanda su ka kauce wa madaidaiciyar hanya na daga masu
nasabta kansu zuwa ga fiqhu da ilimi da talauci da ibada; saboda kasancewar su
kan aikata bidi'o'I da bata da riya da sum'a (yin ibada don mutane su ji da
kunnuwansu, ba don Allah ba), sa'an nan su na son a rika yaba musu da abin da ba
su aikata ba.
Kuma akan irin
wadannan nau'oin nen fadin madaukaki ya sauka:
ﭽ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭭ ﭮ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭼ [آل عمران: ١٨٨ ].
(Kada
ka yi zaton wadanda su ke farin ciki kan
abin da su ka bayar, kuma su ke son a yabe su da abin da ba su aikata ba, kada
ka yi zaton za su tsira daga azaba, kuma suna azaba mai radadi).
Nau'I na uku:
Su ne wadda ya zama yana ikhlasi cikin ayyukansa; sai dai kuma (ayyukan) sun
kasance ba tare da bin umurnin (ma'aiki s a w) ba; misalinsu kamar JAHILAN MASU
YAWAN BAUTA, DA KUMA MASU NASABTA KANSU ZUWA GA GUDUN DUNIYA DA TALAUCI, DA MA DUK
WADDA YA BAUTA WA ALLAH BA AKAN YADDA ALLAH YA NUFA BA.
Saha'anin ba
kawai cikin a bauta wa Allah ba ne kadai, A'a! a bauta masa ne akan yadda Allan
ya nufa (shari'arsa).
Shi yasa; Daga
cikin wadannan nau'in akwai wadda ke zama a wajen da ya ke khalwa (wurin da ya
kebe wa kansa don bauta) yana mai barin zuwa sallar juma'a, kuma yana ga hakan
wai bauta ne, kuma kusantan Allah ne. Haka kuma (irin wadannan) suna ganin
sadar da azumin dare da yini ma karin kusanci ne ga Allah. Haka kuma yin azumin
ranar idi ma wai karin kusanci ne (bayan shari'a ta hana). Da makamantan haka.
Nau'I na hudu:
Wadanda aiyukansu su ka kasance kan bin umurni (shari'ar manzon Allah s a w),
sai dai kuma yana yin su ne ba don allah madaukaki ba; misalin wannan shi ne;
kamar da'ar masu yin riya, da kuma kamar mutumin da ya yi yaki da nufin riya da
sum'a (ya yi suna, a ji shi, da a ganshi), da me yi don kabilanci, ko a ce shi
gwarzo ne, ko ya ke yi don ganima. Ko wadda ya ke yin hajji don a ce ( shi mai
hajji ne, Alhaji; a niyyarsa ya yi don haka, ba don Allah ba). Haka wadda ya ke
yi karatun domin a ce (shi makaranci ne, ba don Allah ba). Da me neman ilimi ko
mai koyar da shi don a fada (ba don Allah ba). Wadannan duk ayyuka ne na gari,
sai dai ba za a karbe su ba; Allah yan cewa:
ﭽ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ
ﮞ ﮟ ﮠ ﮩ ﭼ [البينة: ٥].
(Ba
a umurce su ba sai da su bauta wa Allah suna masu tsarkake masa addini,
karkatattu ga barin shirka zuwa ga tauhidi).
Don haka ba a
umurci mutane ba sai da bauta wa Allah akan bin manzo da kuma tsarkake niyya ga
Allah shi kadai a cikinsu. Wadda kuma ya tsayu akan haka to shi ne ma'abocin:
ﭽ ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭼ [الفاتحة: ٥].
(Kai
kadai mu ke bauta wa, kuma a gare ka –kai kadai- mu ke neman taimako).
************
[IBADAR DA
YA KAMATA MUTUM YA FI FIFITAWA; SABODA FIFIKON AMFANINTA DA FALALARTA]
Sa'annan su ma'abota:
ﭽ ﭢ ﭣ ﭼ .
(Kai
kadai mu ke bauta wa), -dangane da mafificin bauta, kuma mafi amfaninta, wacce
kuma ta fi cancantar a gabatar da ita (a yawaita yi), da kuma kebe ta- dangane
da haka su na da hanyoyi hudu, kuma su sinfi hudu ne::
Kaso na
farko: A wajensu Ibadar da ta fi amfani
kuma ta fi fifiko ita ce: Wacce ta fi wahala ga rayuka, ta kuma fi tsanani.
Su ka ce: (abin
da ya fi wahala) shi ne mafi nisa ga barin son zuciyar bawa, wadda (gudun son
zuciya kuwa shi ne): hakikanin nuna bauta, shi ma lada yana nan gwargwadon
wahala.
(Dalilinsu): Su
ka ruwaito hadisin da ba shi da asali cewa:
" أفضل الأعمال أحمزها "
Wai
mafifcin ayyuka shi ne wadda ya fi tsananin wahala ''.
Wadannan mutanen su ne ma'abutan wahalar da
kai, da zaluntar rayuka, su ka ce: AI ABIN SANI KAWAI, ZUKATA NA SAMUN ISTIKAMA
(TSAYUWA KAN TAFARKIN ALLAH) NE DA HAKA, saboda an 'dabi'antar da rai kan
kasala, da kaskanci (wato kin aikata abin da zai daukaka rai, saboda gudun
wahala), da kuma tabbatuwa zuwa ga neman hutu; don haka rai ba za ta daidaita
ba sai da aikata abubuwa masu wahalwalu, da kuma aikata abubuwa masu tsanani.
Kaso
na biyu: Su ka ce: mafificin ibadu kuma wadanda su ka fi amfani shi ne: Tobuwa
da kuma gudun duniya, da kuma karanta wa daga gare ta gwargwadon iko (iya
iyawa), da kuma watsar da himmatuwa da ita, tare da barin mai da hankali kan duk abubuwanta.
Sa'an
nan su wadannan din kashi biyu ne:
Gama
garinsu; Sun yi zaton cewa hakan wani abu ne da ake nufansa don kansa; don haka
sai su ka zage dantse zuwa gare shi, su ka yi ta yin aiki tukuru don shi, su ka
kuma ce: Ai hakan (gudun duniyan) ya fi falala fiye da darajar neman ilimi da
kuma ibada, sa'an nan su a ganinsu: gudun wannan duniyar shi ne manufar kowace
bauta.
Amma
kebantattunsu kuma; Su suna ganin zuhudu abu ne da aka nufe shi saboda waninsa;
kuma lallai abin da ake nufi da shi shi ne: Killatuwan zuci (lazimtarta) Allah
madaukaki, da kuma dulmuyuwa cikin sonsa, da mayar da al'amari zuwa gare shi,
da kuma dogara akansa, da shagaltuwa da abubuwan da su ke yardar da shi; don
haka sai su ke ganin cewa: MAFIFICIN IBADU SHI NE DAWWAMUWAR AMBATONSA A ZUCI
DA HARSHE.
Sa'an
nan wadannan sun kasu kashi biyu:
Masana
(da ake musu lakabi da: AL'ARIFUNA) daga cikinsu: Su kan kasance idan umurni da hani ya zo, to
sai su yi gaggawa zuwa gare shi; ko da kuwa zai rabe su da taruwar zuciyarsu.
Karkatattun
kuma daga cikinsu sai su ce: Abin da ake nema daga zuciya shi ne; haduwarsa;
don haka idan abin da zai raba shi da wannan haduwar zuciyar ta sa ya zo masa
daga Allah (kaman karantarwa, raka gawa, ko wani umurni alhali yana cikin
khalwarsa ya gama hada zuciyarsa gu guda) to ba zai juya ya zuwa ga wannan
umurnin ba; har ma cewa su ke yi:
يُطالَبُ
بالأوراد مَن هو غافلٌ
|
|
فكيف
بقلبٍ كلُّ أوقاته وردُ
|
Ma'ana:
" Rafkanenne shi ake nema da ya yi wurudi!
To
kuma ta yaya za a nemi zuciyar da dukkan lokutanta wurudi ta ke yi?
Sa'an
nan su wadannaan din ma sun kasu kashi biyu:
Daga
cikinsu akwai wadda ke barin wajibai da farillai wai saboda yana cikin yanayin
da ya hada zuciyarsa.
Daga
cikinsu kuma akwai wadda ke tsayuwa da su (wajibai da farillu) amma sai ya bar
sunnoni da nafiloli, da neman ilimi mai amfani wai saboda hada zuciyarsa.
Gaskiyan
al'amari kuma shi ne; lallai shi hada zuciyan rabon zuci ne, yayin da amsa wa
mai kira zuwa ga Allah kuma rabon Ubangiji ne; don haka duk wadda ya fifita
hakkinsa akan hakkin Ubangijinsa; to ba komai ba ne a cikin bauta!
Kaso na uku: Su wadannan su na ganin cewa
mafificin bauta shi ne wadda a cikinsa akwai amfanarwa da ke tsallake wadda ya
yi bautar ya zuwa ga waninsa; don haka su ke ganin irin wannan nau'in bautan ya
fi matsayi akan wadda ke takaituwa kan wadda ya aikata bautan; Sai su ke ganin
cewa: Hidima wa talakawa, da kuma shagaltuwa da maslahohin mutane, tare da biya
musu bukatunsu, da taimakonsu da matsayi, da dukiya, da kuma amfanarwa shi ya
fi; saboda fadinsa s a w:
"الْخَلْقُ
عِيَالُ اللَّهِ، فَأَحَبُّهم إِلَى اللَّهِ أَنْفَعُهُمْ لِعِيَالِهِ
"
(Halittu iyalai ne na Allah; wadda ya fi su soyuwa zuwa ga Allah
shi ne wadda ya fi amfanar da iyalensa).
Su
ka ce: Shi aikin mai bauta yana takaita akansa, yayin da aikin mai yawan
amfanar da mutane kuma ya ke naso ya zuwa waninsa, to ta yaya za a kwatanta
wannan da wancan? Kai shi fa ya sa falalan malami akan mai bauta ya ke
kasancewa kamar falalan wata ne a daren haske (13-15) akan sauran taurari,
Kuma
ga shi Annabi s a w ya ce wa Aliyu:
"
لأَنْ يَهْدِيَ اللَّهُ بِكَ رَجُلا وَاحِدًا خَيْرٌ لَكَ مِنْ حُمْرِ النَّعَمِ "
(Ai! Allah ya shiryi mutum daya da kai (ta sababinka) ya fi maka
alkhairi fiye da jajayen dabbobi ni'ima (rakuma). Ya kuma ce:
"
مَنْ دَعَا إِلَى هُدًى كَانَ لَهُ مِنْ الْأَجْرِ مِثْلُ أُجُورِ مَنْ تَبِعَهُ غير
أنْ يَنْقُص مِنْ أُجُورِهِمْ شَيْئًا "
(Wadda ya yi kira zuwa ga wata shiriya, ya kasance yana da
kwatankwacin ladan wadda ya bi shi, ba tare da an tauye wani abu ba daga
ladansu). Ya kuma ce:
"
إِنَّ اللَّهَ وَمَلائِكَتَهُ لَيُصَلُّونَ عَلَى مُعَلِّمِي الْخَيْرَ "
(Lallai Allah da Mala'iku suna addu'a ga masu koyar (da mutane)
alkhairi. Ya kuma cewa:
"إِنَّ
العالم لَيَسْتَغْفِرُ مَنْ فِي السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضِ حَتَّى الْحِيتَانُ فِي الْبحر،
والنَّمْلَةَ فِي جُحْرِهَا"
(Lallai malami halittun da su ke cikin sammai da kassai suna
nema masa gafara, har kifaye a cikin teku, har kuma tururuwa a cikin raminta).
Sua
ka ce: Shi ma'abucin bauta idan ya mutu aikinsa ya yanke (da mutuwarsa), yayin
da ma'abocin amfanarwa aikinsa ba zai yanke ba, matukar amfanarwan da ya zama
sababin samuwarsa yana nan.
Kuma
suma annabawa –yabon Allah da tsiransa su kara tabbata a gare su- abin sani
kawai an turo su ne da kyautatawa wa halitta, da shiryad da su, da kuma amfanar
da su a rayuwarsu ta duniya da makomansu, ba a turo su da shiga khalwa ba da
kuma yanke khulda da mutane (kebewa gefe da bauta tare da nisantar cikin
al'umma).
Shi
ya sa ma Annabi s a w ya yi inkari ga wadnnan mutanen da su ka yi niyyar yanke
khulda da mutane, tare da kebewa gefe da bauta.
Su
ka kuma ce: (yana daga cikin abubuwan da amfaninsu ya kan zarta wadda ya tsayu da su ya wuce don
ya yi naso ga waninsa): Neman ilimi da
karantarwa. Da makamantan wadannan al'amura masu falaloli.
Kaso
na hudu: Mafificin ibada shi ne: AIKI
DON NEMAN YARDAN UBANGIJI MAI TSARKI, TARE DA SHAGALTAR DA (CIKA) KOWANE LOKACI
DA ABIN DA SHI NE AIKIN WANNAN LOKACIN KUMA SHI LOKACIN KE HUKUNTA (SAMAR DA
SHI);
Don
haka; Mafificin bauta a lokacin jihadi shi ne: jihadin; koda kuwa al'amarin zai
kai ga barin wurudi na sallan (tsayuwar) dare, da kuma barin azumin yini, kai!
Koda zai kai ga barin cika sallar falilla –a yi ta ba kamar a halin aminci da
rashin yaki ba!
Abin
da kuma ya fi a lokacin da bako ya halarto shi ne: tsayuwa wajen bada hakkinsa,
da kuma shagaltuwa da shi.
Abin
da ya fi kuma a lokutan sahur shi ne: shagaltuwa da salla, qur'ani, zikiri da
addu'a.
Abin
kuma da ya fi a lokacin kiran salla: Shi ne: Barin barin abin da mutum ke
cikinsa na wurododi, da shagaltuwa da amsa wa mai kiran salla.
Amma
a lokutan salloli biyar kuma abin da ya fi shi ne: Kokari da aiki tsayin daka
wajen a ga an aikata su a mafificin (kammalellen) fiska, tare kuma da yin
gaggawa zuwa gare su a farkon lokaci, da fita zuwa masallaci; koda kuwa ya yi
nisa.
A lokacin
lalurar wani mabukaci (shi kuma abin da ya fi a wannan lokacin shi ne): Sauri
wajen taimaka masa da matsayi, da dukiya, da kuma jiki.
Abin
da ya fi a hali na tafiya shi ne: Taimaka wa mabukaci, da abokan tafiya, tare
da fifita hakan akan wurudodi da kebewa.
Abin
da ya fi a lokacin karatun alqur'ani shi ne: tara
zuciya, da himmatuwa kan
tadabburinsa (kai kawo da zuci da nufin fahimtar abin da ake karantawa), tare
da yin azama kan
zartar da umurninsa, (a tara zuciya akan haka)
fiye da tara zuciyar mutumin da littafi (wasika) ya zo masa daga wani sarki.
Abin
da kuma ya fi a lokacin tsayuwar arfa shi ne: Yin kokari wajen kan-kan-da-kai,
da addu'a, da zikiri.
Shi
kuma abin da ya fi a kwanaki goman (10) zul hijja shi ne: Yawaita bauta,
musamman ma kabbarori da hailaloli da godiya (wa Allah), yin haka kuma ya fi
falala fiye da jihadin da wajabcinsa bai aiyana ba akan mutum.
Abin
kuma da ya fi a goman (10) karshen ramadan shi ne: Lazimtar masallatai, da
kebewa a cikinsu, tare da I'itikafi, da kuma kawar da kai ga barin khuldar
mutane da shagaltuwa da su, Yin haka ya fi falala har akan fiskantarsu don
karantar da su ilimi, da kuma ba su karatun alqur'ani a wajen yawa yawan
maluma.
Abin
da ya fi kuma a lokacin rashi lafiyar dan uwanka musulmi ko rasuwarsa shi ne:
Ziyartarsa, da halartar sallarsa tare da raka shi, da gabatar da hakan akan
kebewansa da hada zuciyarsa gu guda.
Abin
da ya fi kuma a lokacin da wassu bala'I su ka sauka (maka), da kuma cutarwan
mutane a gare ka shi ne: Yin abin da Allah ya wajabta na hakuri tare kuma da ci
gaba da khulda da su; saboda muminin da ke cakuduwa da mutane kuma ya ke hakuri
kan cutarwansu shi ya fi falala akan muminin da baya khulda da mutane, kuma
baya hakuri kan cutarwansu.
Kuma
yin khulda da su cikin alkhairi shi ya fi alkhairi akan kaurace musu akan haka.
Kwaurace musu kuma cikin sharri shi ya fi fiye da khulda da su a cikinsa;
Amma
idan mutum ya san cewa idan ya yi khulda da su zai gusar da shi, ko ya karanta
shi (sharrin) to a irin wannan halin yin khulda su din yafi alkhairi fiye da
kaurace musun.
Su
wadannan nau'in su ne ma'abota sakekkiyar bauta (da ake kiranta: ATTA'ABBUDUL
MUDLAK). Su kuma nau'uka (uku) da su ke kafinsu su ne ma'abota nau'in bauta kayyadedde
(ATTA'ABBUDUL MUKAYYAD); don haka; dul lokacin da 'dayansu ya fita daga reshen
da rataya da shi na bauta, sa'an nan ya rabu da shi (in mai sallan dare ne, ya
zama bai yi ba, ko sadaka, ya zama bai samu ikon mikawa ba, haka alqur'ani wani
uzuri ya hana shi karanta abin da ya saba karantawa d. sauransu) sai ya ga
kansa cewa ya samu tawaya, ya kuma sauka daga ibadarsa; saboda shi yana bauta
wa Allah ne ta fiska daya. Yayin da ma'abota sakekkiyar bauta ('yan nau'in
farko) basu da wta manufa akan wata ibada a karan-kanta; da su ke fifita akan
watanta, Kawai dai burinsu shi ne: BIBIYAN ABUBUWAN DA SU KE YARDAR DA ALLAH
MADAUKAKI.; Don haka;
In
har ka ga maluma sai ka ganshi tare da su, haka ya ke cikin masu ambato Allah (zikiri), da
masu sadaka, da wadnda su ke kokarin tar zuciyarsu da lazimtar da ita Allah.
Yin
haka kuwa shi ne: gamemmen abin da zuciyar mai tafiya zuwa ga Allah ta kowane
hanya ke bukata, mai kuma tafiya fatauci zuwa gare shi tare da kungiyar kowani
fatake (masu zikiri ne, masu sadaka ne, maluma masu nusar da al'umma ne d.
sauransu).
A
nan zai yi kyau ka halarto hadisin Abubakar Assidiq –r . a- tare da fadin
Annabi s a w a gaba gare shi:
"
هلْ مِنْكُمْ أحدٌ أَطْعَمَ الْيَوْمَ مِسْكِينًا؟ " قَالَ أَبُو بَكْرٍ:
أَنَا. قَالَ: " هلْ مِنْكُمْ أحدٌ أَصْبَحَ الْيَوْمَ صَائِمًا؟
" قَالَ أَبُو بَكْرٍ: أَنَا. " هلْ مِنْكُمْ أحدٌ عَادَ الْيَوْمَ مَرِيضًا؟
" قَالَ أَبُو بَكْرٍ: أَنَا. " هلْ مِنْكُمْ أحدٌ تَبِعَ الْيَوْمَ جَنَازَةً؟
" قَالَ أَبُو بَكْرٍ: أَنَا. فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ r:
" مَا اجْتَمَعْنَ فِي امْرِئٍ إِلا دَخَلَ الْجَنَّةَ "
(Shin daga cikinku akwai
wadda ya ciyar da miskini a yau? Sai Abubakar ya ce: Ee! Ni na yi. Sai ya ce:
Shin a cikinku akwai wadda ya wayi gari yana mai azumi? Sai Abubakar ya ce: Ee!
Ni ina yi. Sai ya ce: Shin a cikinku akwai wadda ya ziyarci maras lafiya a yau?
Sai Abubakar ya ce: Ee! Ni na yi. Sai ya ce: Shin a cikinku akwai wadda ya raka
gawa a yau? Sai abubakar ya ce: Ee! Ni na raka. Sai Manzon Allah s a w ya ce:
Wadannan abubuwan ba zu taba haduwa ga mutum ba face ya shiga aljanna)([5]).
Kuma
wannan hadisin an ruwaito shi daga hanyar Abdulganiy bn abiy Akiili, ya ce:
Yagnam bn Salim ya bamu labari, daga Anas bn Malik –Allah ya kara yarda da shi-
ya ce:
« كان رسول
الله r جالسًا في جماعة مِن أصحابه فقال: مَن صام اليوم؟ فقال أبو
بكر: أنا. قال: مَن تصدّق اليوم؟ قال أبو بكر: أنا. قال: مَن عاد اليوم
مريضًا؟ قال أبو بكر: أنا. قال: فمَن شهد اليوم جنازة؟ قا أبو بكر:
أنا. قال: وجبت لك –يعني: الجنة- ».
(Manzon Allah s a w ya kasance a cikin masallaci a zaune cikin
jama'ar sahabbansa; Sai y ace: Wenene ya yi azumi yau? Sai Abubakar ya ce: Ni
ne. Sai y ace: Wanene kuma ya yi sadaka a yau? Sai Abubakar ya ce: Ni ne. sai
ya ce: Way a ziyarci maras lafiya yau? Sai Abubakar ya ce: Ni ne. Sai ya ce:
Wanene kuma ya halarci sallan gawa? Sai Abubakar ya ce: Ni ne. Sai ya ce: Shiganta ya wajaba maka –yana nufin aljanna-.
Shi
yagnam bn Salim duk da cewa akwai Magana akansa sai dai Salamatu bn Wardan ya
masa mutaba'a (wato ya ruwaito irin hadisinsa).
Kuma
hadisin yana da asali ingancecce na daga hadisin: Malik daga Muhammadu bn
Shihabin, daga Humaid bn Abdirrahman bn Auf, daga Abu Hurairata –Allah ya kara
masa yarda- Lallai Manzon Allah s a w ya ce:
" مَنْ أَنْفَقَ زَوْجَيْنِ فِي
سَبِيلِ اللَّهِ نُودِيَ فِي الْجَنَّةِ: يَا عَبْدَ اللَّهِ! هَذَا خَيْرٌ؛ فَمَنْ
كَانَ مِنْ أَهْلِ الصَّلاةِ نُودِيَ مِنْ بَابِ الصَّلاةِ، وَمَنْ كَانَ مِنْ أَهْلِ
الْجِهَادِ نُودِيَ مِنْ بَابِ الْجِهَادِ، وَمَنْ كَانَ مِنْ أَهْلِ الصَّدَقَةِ دُعِيَ
مِنْ بَابِ الصَّدَقَةِ، وَمَنْ كَانَ مِنْ أَهْلِ الصِّيَامِ دُعِيَ مِنْ بَابِ الرَّيَّانِ.
فَقَالَ أَبُو بَكْرٍ t: بِأَبِي
–أَنْتَ- وَأُمِّي! يَا رَسُولَ اللَّهِ! مَا عَلَى مَنْ يدعَى مِنْ هذه الأَبْوَابِ
مِنْ ضَرُورَةٍ، فَهَلْ يُدْعَى أَحَدٌ مِنْ تِلْكَ الأَبْوَابِ كُلِّهَا؟ قَالَ: نَعَمْ؛
وَأَرْجُو أَنْ تَكُونَ مِنْهُمْ ".
(Duk
wadda ya ciyar da abu kala biyu a tafarkin Allah to za masa kira da babban
murya daga aljanna (ta kofofin aljanna), an ace masa: Ya kai bawan Allah!
Wannan shi ya fi alkhairi! Duk wadda ya kasance daga cikin ma'abota salla sai a
kira shi daga kofar salla, Wadda kuma ya kasance daga ma'abota jihadi sai a
kira shi ta kofar jihadi. Wadda kuma ya kasance daga ma'abota sadaka sai a kira
shi ta kofar sadaka. Wadda kuma ya zamo daga ma'abota azumi sai a kira shi ta
kofar Rayyan (kofar kasha kishi).
Sai
Abubakar –Allah ya kara masa yarda- ya ce: Ya ma'aikin Allah! Shin akwai wata
cut ace ga wadda aka kira shi ta wadannan kofofin; Kuma shin za a kira wani
kuwa ta dukkan wadannan kofofin? Sai ya ce: Ee! Ina ma fatan ka zama daga
cikinsu.
Haka
nan Yahya bn Yahya, da Ma'an bn Isah, da Abdullahi bnul Mubarak su ka ruwaito
shi daga Malik da sanadinsa zuwa ga Annabi s a w. Amma Yahya bn Bukair da
Abdullahi bn Yusuf sun ruwaito shi daga Malik daga Ibnu Shihab, daga Humaid a
matsayin mursal (wato: hadisin da tabi'I ya ce: Manzon Allah s a w ya ce). A
wajen Alka'anabi kuma hadisin ba MURSALI BA NE KUMA BA MUSNADI BA NE.
Ma'anan:
" مَنْ أَنْفَقَ زَوْجَيْنِ ... "
Shi
ne wadda ya ciyar da abu biyu daga nau'I daya; misalin dirhami biyu, ko dinari
biyu, ko doki biyu, ko riguna biyu. Haka ma wadda ya yi salla raka'a biyu, ko
kuma ya yi tafiya taku biyu a tafarkin Allah madaukaki, ko kuma ya yi azumin
yini biyu. Da makamancin haka.
Allah
shi ne mafi sani; Amma dai la'alla abin da (Annabi s a w) ya nufa da wannan shi
ne: Mafi karancin maimaita abu, da kuma mafi karancin fiskokin dawwama akan
aiki daga cikin ayyukan biyayya; saboda biyu shi ne mafi karancin jam'i.
(Su
'yan nau'I na hudun nan) kamar rowan sama su ke; duk in day a zuba to zai yi
amfani (haka su ma al'amarin ya ke); saboda a wajen mu'amalantar Allah suna
mu'amalantarsa ne ba tare da waiwaya ya zuwa ga halitta ba, suna kuma manta da
kansu in sun zo mu'amalantar halittu (sai su fifita su har akan kansu); Idan ya
kasance tare da Allah to sai ya yi uzula wa dukkan halittu tare da kasancewarsa
yana cikinsu (ba wai ya yi hijira ban e ya koma jeji ko …), sai ya kyale
halittu, Idan kuma ya kasance tare da halittunsa to sai ya tobe kansa daga
cikinsu, ya kyale ran nasa (ya ki kula da ita), KAI IRIN WANNAN BAKO NE A CIKIN
MUTANE! Kuma ka yi mamakin tsananin kadaitakarsa a cikinsu! Sa'an nan ka yi
mamakin debe kewarsa da Allah da farin cikinsa da shi, da nitsuwarsa da
kwanciyar hankalinsa da Allah!
[ Ya
Allah ka sa mu cikin irin wannan kason don zatinka da sifofinka madaukaka].
********
[KARKASUWAN MUTANE DANGANE DA AMFANIN BAUTA DA HIKIMARTA DA
MANUFARTA SUN KASU KASHI HUDU]
Kuma
ka sani mutane ne dangane da amfanin bauta da hikimar da ta sa aka shar'anta
ta, da kuma manufar da ta ke tabbatarwa suna da hanyoyi hudu; don haka sun kasu
kashi hudu:
Kashi na farko: Su ne wadanda su ke kore hikimomi da sababi;
wadanda su ke mayar da umurni zuwa ga tsagoron ganin dama (misali; su a wajensu
da Allah ya yi umrni a yi salla, azumi, zakka, babu wassu sabbuba da su ka sa
ya shar'anta wadannan bautan, sai kawai haka ya ga dama, haka kuma day a hana
shan giya, zina, sata, nan ma ba wassu sabbuba da su ka hukunta hanawan, sai
haka ya ga dama); don haka –a wajen wadannan- tsayuwa da bin umurni da hani bas
u da wassu sababi sai kawai don an yi umurni; ba tare da akwai wani sababi na
tsira a cikin rayuwar duniya ko lahira ba, ko wani sababin tsira; kai dai mutum
yak an tsayu da bin umurni ne saboda an yi umurni, da kuma tsantsan ganin daman
(Allah),
kamar yadda –DANGANE DA HALITTA MA- su ka ce; Allah bai halicci
halitta ba don wata manufa, ko saboda wani sababin day a nufa da su, ko kuma
wata hikima wacce za ta dawo ya zuwa gare shi daga gare su. (Su ka sa ke cewa):
Babu wassu sabbuba a cikin halittu da sun e su ka hukunta halittarsu, kamar
yadda (a fadinsu) babu sababin kuna a cikin wuta, haka ruwa ba shi da karfi na
dulmuyarwa (ga wadda ya shige shi alhali bai iya gudanar da shi ba) ko
sanyintarwa.
To haka ma umurni ya ke a wajensu ba banbanci, kuma (a wajensu) -a
hakikanin al'amari- babu banbanci tsakanin abin da aka yi umurni da shi, da
kuma wadda aka hana (wato kamar zina da aure); kawai dai! Ganin damansa ne
(Allah) ta hukunta ya yi umurni da wannan, ya kuma hana wannan, ba tare da an
samu wata sifa da ta tsayu da abin da aka yi umurni da shi ba, da ta ke hukunta
kyansa, haka kuma wata sifa da tsaya tare da abin da aka hana wacce ta ke
hukunta muninsa.
(WADANNAN MUTANEN SU AKE KIRA JABARIYYA).
Shi dai wannan asalin da su ka kafa yana da (munanan) abubuwan da
su ke biyo bayansa, da kuma ressa da yawa. (Babu dammar ambatonsu a nan).
Su wadannan; mafi yawansu
basa samun zakin ibada ko dadinta, haka kuma bas a ni'imtuwa da ita; shi yasa
ma su ke kiran: salla, azumi, zakka, hajji, tauhidi, da ikhlasi, da sauransu:
(su ke kiransu): Abubuwan da aka kallafa wa (bayi); DA KUWA MAI RIYA SOYAYYAR
WANI SARKI DAGA CIKIN SARAKUNA KO WANINSA ZAI KIRA ABIN DA YA UMURCE SHI DA SU
(NA AYYUKA); KALLAFE – KALLAFE TO DA BAI ZAMA MASOYINSA BA! (Sai Allah ne za a
kira abin da ya umurci masoyinsa, wadda sa'adarsa ta duniya da lahira na cikin
abin day a umurce shin ne kawai, za a kira wadannan umurni: abubuwan da aka
kallafa wa mutum!? ).
Wadda wannan maganan ta fara fitowa daga wajensa shi ne: ALJA'ADU
BN DIRHAM (shugaban masu kore wa Allah sifofin day a tabbatar wa kansa).
Kashi na biyu: Masu kore kaddara (DA AKE KIRANSU: ALKADARIYYATU
ANNUFATU); Wadanda su ke tabbatar da nau'I na hikima da sababi (amma ba
dukkansa ko kuma ta kowace fiska ba), amma (wadda su ke tabbatarwan) ba tsayuwa
da Ubangiji, kuma bay a komawa zuwa gare shi, kawai dai (a wajensu) yana komawa
ne ga tsantsan maslahar bawa da amfaninsa.
Kuma a wajensu su wadannan ibadun an shar'anta sun e don su zama
kudi da bawa ya bayar don sayan abin da bayi ke samu na lada da ni'imomi, wato
su (ibadun) suna nan kamar ace: neman cika hakki ne da wadda ya bada kwadago ke
yi daga wadda ke masa aiki (kafin kuma ya bada sakamako da ke ta bangarensa).
Su ka ce: Shi ya sa Allah mai tsarki ya ke sanya su a matsayin
canji (wato kamar an karbi aikinku an mu ku canji da aljanna, kamar yadda dan
kasuwa ke karban kudinka sai ya baka bukatar ka); kamar fadinsa:
ﭽ ﰂ ﰃ ﰄ ﰅ ﰆ ﰇ ﰈ ﰉ ﰊ ﭼ [الأعراف: ٤٣].
(Sai aka musu kolo cewa ga can aljanna –ku
shiga- an gadar mu ku da ita sakamakon abin da ku ka kasance ku ke aikatawa)
ﭽ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ
ﭩ ﭪ ﭼ [النمل: ٩٠].
(Ba a saka mu ku sakayya sai da abin da ku ka
kasance ku ke aikatawa).
ﭽ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﭼ [النحل: ٣٢].
(Ku shiga aljanna saboda abin da ku ka
kasance ku ke aikatawa).
ﭽ ﰒ ﰓ ﰔ ﰕ ﰖ ﰗ ﰘ ﰙ ﭼ [الزمر: ١٠].
(abun sani kawai; ana cika wa masu hakuri ladansu ne ba tare da
lissafi ba).
Ya kuma zo cikin sahihu (muslim):
" إِنَّمَا هِيَ أَعْمَالُكُمْ أُحْصِيهَا
عليكُمْ ثُمَّ أُوَفِّيكُمْ إِيَّاهَا "
(-Ya ku bayi na!- Ku sani lallai wannan aikin
kun e; na ke kiyaye mu ku, sa'an nan sai in cika mu ku (sakayyansa),
Su ka ce: kuma ga shi (Allah) ya kira su da: sakayya, lada,;
saboda wani abu ne da ke dawowa ya zuwa ga mai aikin na daga aikinsa.
Abin da ke nuni kuma kan
haka (wato, canji) shi ne: aunawa da ake yi; saboda ba don ratayar lada da
ayyukan ba a matsayin canjinsu to da awon ba shi da ma'ana.
(A nan shubuhohinsu su ka kare, saura mayar da martini tare da
bayanin inganceccen ma'anonin ayoyi da hadisan)
Wadannan bangarorin guda biyu suna karo da juna;
Su dai Jabariyya ba su sanya wa aiyuka ba wani kulluwa da sakayya
kwata-kwata; shi ya sa (a kwakwalensu, da akidarsu) su ka halatta Allah ya yi
azaba ga mutumin da ya karar da rayuwansa cikin da'a (wa Allah), ya kuma
ni'imtar da wadda ya karar da rayuwarsa cikin sabonsa; domin dukkansu (wadda ya
mutu a kan da'a da sabo) dangane da shi Allah wadannan daya ne (haka su ka
fada); saboda kowannensu na komawa ne zuwa ga gundarin haka yaga dama!
Su kuma kadariyya sun wajabta ma Allah madaukaki kula da
maslahohi, sa'an nan su ka sanya hakan - gaba dayansa- ya zama na rataye ne da
tsuran aiyuka, kuma wai isar sakamako zuwa ga bawa ba tare da aikinsa ba; cikin
haka akwai nakasawa; wai saboda: akwai yiwuwar a masa gorin sadakar da aka masa
saboda bai bada wani aiki ba a madadin (wannan ladan); don haka; Sai su ka
sanya bada lada da Allah mai tsarki ke yi wa bawansa kamar sadaka ne da bawa ke
yi wa wani bawan (ta yadda –in dai- mai bada sadakar bai ji tsoron Allah ba zai
iya yin gori ga wadda ya karba, to su ka ce; in ba ka yi aikin lada ba sai aka
baka to ai akwai yiwuwar a maka gori; subhanallah). Kuma (su ka ce) bayar da
abin da Allah ke bayarwa bawansa na ladan aikinsa ya fi soyuwa ga bawan fiye da
abin da zai ba shi haka kawai a matsayin falala daga gare shi ba tare da wani
aiki ba. Kuma kwata-kwata ba su sanya wa aiyuka ba wani tasiri cikin sakamako.
Duka wadannan kungiyoyin guda biyu sun bace ga barin madaidaiciyar
hanya, wadda shi ne:
Su dai ayyuka sabbuba ne da su ke kaiwa ya zuwa ga sakayya; su ko
na kwarai daga cikin ayyuka suna daga cikin datarwan Allah madaukaki (ga
bawansa) da falalarsa, amma (ayyuka) ba cuf cuf (dai dai da dai dai) su ke da
sakamakonsa da ladasan ba. Makurarsu –idan aka yi su- akan mafi kamalar fiskoki
shi ne su zamo: GODIYA AKAN DAYA DAGA CIKIN BANGARORI KADAN DAGA NI'IMOMINSA –MAI TSARKI (Allah)-;
Shi yasa da zai azabtar da dukkan halittun sammansa da kassensa to da ya
azabtar da su alhali ba wai yana zaluntar su ba. Da kuma zai musu rahama to da
rahamar ita tafi musu alkhairi fiye da aiyukansu.
Kuma ka yi tunani cikin fadinsa madaukaki:
ﭽ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ
ﯲ ﯳ ﭼ [الزخرف: ٧٢].
( Waccar ita ce aljanna da aka gadar mu ku da
ita saboda abin da ku ka kasance ku ke aikatawa)
(ka yi tunanin wannan ayar) tare da fadin Manzon Allah s a w:
" لَنْ يَدْخُلَ أَحَدٌ الْجَنَّةَ بِعَمَلِهِ
"
Ma'ana: " Ba wani da zai taba shiga aljanna da aikinsa
".
(In ka yi tunanin ) za ka samu cewa ayar tana nuna cewa lallai
shiga aljanna ya kan
kasance ne da ayyuka. Shi kuma hadisin yana kore shigan aljanna da aiyuka, amma
ba cin karo a tsakaninsu;
saboda masaukar kore da tabbatarwan ba a gurbi daya su ke sauka ba,
(balle a yi zaton cin karo);
Wadda aka koren (harafin BA'UN NE) da ke nunin kudi da kima (kamar
mutum ya ce: Na sayi biro da kudi; a wannan yanayin shi kudin kimar biro
ne, aljanna kuma ba haka ta ke dangane da aiyukan bayi).; don haka abin da aka
kore shi ne cancantar aljanna da tsagwaron aiyuka ( ba tare da shigar rahamar
Allah ba), wato raddi kenan (mai da martani) ga kadariyya majusawa; wadanda su
ka riya cewa: haka kawai a ba wa bawa lada ba tare da ya yi aiki ba (kawai dai
falalan Allah) yana kunsan … (nakasa); saboda gori na bata garautakar hakan.
Shi kuma (harafin) BA'UN da aka tabbatar da shi; wadda ya zo cikin
alqur'ani harafi ne da ke nuna sababi; raddi ga jabariyya da su ke cewa: Babu
alaka tsakanin aiyuka da sakayyansu, kuma su (aiyuka) ba sabbubansu (sakamako)
ba ne, Kawai dai makuransu (su aiyuka su zama) alamomi (na sakamako; wato wadda
aiyukansa su ka yi muni; kenan hakan alamar yi masa mummunan sakayya ne, ba
sababin haka ba, haka kuma idan aiyukan su ka yi kyau).
Sunnar Annabi –s a w- na nuna lallai gamewar nufin Allah da ikonsa
(ga komai) ba ya kore kulla sabuban da abubuwan da sabuban ke zama dalilin
samuwarsu, da kuma kulluwansu da su.
Kuma kowace kungiya ta bar wani nau'I na gaskiya To kuma za ta
auka wa wani nau'I na barna saboda shi (ma'ana: barin gaskiyan), Kai! (za ta
auka wa) awssu nau'uka (ba daya ba na barna). Sai Allah da izininsa kuma ya
shiryad da Ahlus sunna zuwa ga gaskiya cikin abin da aka yi sabani akansa.
(walhamdu lillah).
Kashi na uku: Sune wadanda su ke riya cewa: Lallai kawai fa'idan
ibada (da amfaninta) shi ne: Motsa rayuka (kamar yadda ake motsa jiki da wasa)
ta yadda zukatan za su zamo sun shirya wa kwararowar ilimi da wassu sani
mabanbanta akan zukatan. Tare kuma da fitar karfi rai irin na su damusa
(jarumta da ke haifar da zalunci) da kuma na su ayu da sauransu (sha'awa da
kawai nufin biyan bukata); don haka da za a daina bauta to da rayukan sun hadu da rayukan damusosi da
dabbobi, don haka ibada ce ke fitar da rayukan ya zuwa kama da kwakwale
(hankali irin na mala'iku) don haka sai su zama za su iya karbar zanuwar
potunan sani a cikinsu.
Wannan maganar kungiya biyu ne su ke fadansa:
Na farkonsu: Wadanda su ka yi kusa da musulunci da shari'oi na philoserpers
da su ke cewa: (Wai) duniya bata da farko, kuma wai babu mahalicci da ke
halitta cikin zabinsa. (Amma wadannan fa ba musulmai ba ne).
Kungiya ta biyun su ne: Wadda ya koyi phalsafar daga cikin sufayen
da su ke cikin musulunci, sa'an nan su ke kusa da philoserpers To
wadannan na riya cewa: Wai ibadodi motsa rayuka ne don rayuka su zama sun
shirya wa ilimomi da ke kwararowa ga hankula, da kuma saba wa al'adu.
Sa'an nan su wadannan akwai daga cikinsu da baya wajabta yin
bautan sai don samun wannan ma'anar; don haka idan hakan ya samu wa zukatan
nasu (kamar yadda su ke riyawa) to sai su tsaya suna dimautattu; Shin ya kiyaye
abin da ya saba ne na wurudi? (Salla ne, zikiri ne, ko waninsu) Ko kuma ya
shagaltu da abin da ya kwararo masan
ga barin bautan nasa da wurudin da ya saban??
Akwai daga cikinsu wadda ya ke wajabta tsayuwa da wurudin (bautan
da mutum ya saba), da kuma barin sakaci da su.
Su kuma wadannan suma kashi biyu ne:
Na farkonsu: Wadda ya ke ce: wajibi ne a kula da ibadar saboda
kiyaye kanuni, da kuma rike mala'ikan da ya sauko (da ilimin a zuciya; tsoron
kar ya kaura).
Sauran kuma suna cewa: Wajibi ne a ci gaba da bautar har bayan
samun ilimin (da su ke riyawa) saboda kiyaye abin da ya zon, da kuma tsoron kar
ran –a sannu a hankali- bayan barin yin bautar ta koma zuwa ga halinta na farko
na dabbobi.
WANNAN FA (WATO KASO UKU
DA SU KA GABATA) SHI NE KARSHEN KAI KOMON MUTANE WAJEN BAYANIN MENENE HIKIMAR
DA TA SA AKE BAUTA, DA KUMA DALILIN DA YA SA AKA SHAR'ANTA TA, Kuma ba za ka
taba samun wani hanyan ba in banda daya daga wadannan hanyoyi uku ko gaba
dayansu a cikin littatafan WADANDA AKE CE MUSU MUTAKALLIMUNA (wadanda su ka
dauki yawa yawan akidarsu ko salonta daga philoserpers).
Kashi na hudu: Su ne wadanda su ke kudurta hade tsakanin halitta
da umurni, da kaddara da sababi; (wadanda su ka yi aiki da dukkan ayoyi da
hadisai; Ahlus sunna waljama'a); A wajensu: Sirrin bauta da kuma manufarta ya
ginu ne akan sanin hakikanin uluhiyya (bauta wa Allah shi kadai), da kuma
ma'anar kasancewarsa madaukaki shi ne: Abun bauta, sa'an nan ita kuma bauta shi
ne kasancewarsa ILAHU ya ke hukuntawa, haka kuma shi ne athar (alama/ gurbi) na
kasancewarsa ILAHU (domin in kace: yana cikin sifofin Allah: WADDA YA CANCANCI
A YI MASA BAUTA to hakan tun da sifa ce muta'addiyat –kamar yadda maluma ke
bayyanawa- to tana da tasirin a samu masu bauta masan, bayan an ciri suna da
sifa). To kuma ratayuwan samun bauta ga wadda ya cancanci a masa bautar kamar
ratayuwan sifa ne ga wadda ya siffanta da ita, haka kuma kamar ratayuwan abin
da aka sani ne da sanin, da abin da ake da iko akansa da ikon, da kuma
ratayuwan sautuka da ji, da kuma ratayuwan kyautatawa da rahama, da ratayuwan
bayarwa da kyauta (kowanne daga cikin misalan da su ka gabata shi ne tasirin samuwar
sifar da ta rataya da shi).
A wajensu (Ahlus sunna) duk wadda ya tsayu da saninta (wato: sifar
uluhiyya, ko kalmar la'ila illallahu) akan yadda mu ka fassara ta –a harshen
larabci da shari'a, tushenta da yadda ta ke faduwa- (duk wadda haka ya samu masa)
to sanin hikimar ibadodi da manufofinsu (salla, azumi, addu'a da sauransu) zai
inganta masa (kuma ya yi sauki), kuma zai san cewa (samar da kadaiceccen bauta
ga Allah, da barin hada shi da wani, shi ne karshen abin da kowane ibada ke
nufa) don haka a ka halicci bayi, kuma do wannan manufar aka turo manzanni,
kuma aka saukar da littatafa, sa'an nan aka halicci aljanna da wuta.
Kuma hakika (Allah)
madaukaki ya bayyana wannan karara a cikin fadinsa:
ﭽ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭼ [الذاريات: ٥٦].
(Kuma ban halicci aljani da mutum bai sai don
su kadaita ni cikin bauta).
Kai ita kuwa bauta ita ce don ita aka samar da halittu, kamar
yadda madaukaki ya ce:
ﭽ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ
ﭼ [القيامة: ٣٦].
(Shin mutum na tsammanin za a bar shi kara
zube ne (haka siddan), Ai! Kara zube;
Shafi'I –r . l- yana cewa: Ba za a masa umurni da hani ba.
Waninsa kuma ya ce: Ba za a masa sakayya da horo ba.
Dukkan wadannan tafsiri biyun ingantattu ne; saboda bada sakayya
da horo yana rataya ne kan
umurni da hani, su kuwa umurni da hanin su ne neman yin bauta da neman mutane
su nufe ta.
Hakikanin bauta kuwa sh ne: aiki da su (umurni da hani); don haka
(Allah) madaukaki ya ke cewa:
ﭽ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ
ﮥ ﮪ ﭼ [آل عمران: ١٩١].
(Kuma su ke yin tunani cikin halittan sammai
da kassai; Ya ubangijinmu: Baka halicci wannan don barna ba).
Madaukaki ya ce:
ﭽ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬﮭ ﯖ ﭼ [الحجر: ٨٥].
(Bamu halicci sammai da kassai da abin da ke
tsakaninsu ba sai don gaskiya -Allah da bautansa shi ne gaskiya, abin da ake
bautawa koma bayansa kuma shi ne tantagaryan barna- ) .
ﭽ ﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﯹ
ﯺ ﯻ ﯼ ﰀ ﭼ الجاثية: ٢٢
(Kuma Allah ya halicci sammai da kassai da
gaskiya, kuma don a saka wa kowane rai da abin da ya aikata).
Allah madaukaki ya bada labarin cewa lallai shi ya halicci sammai
da kassai da gaskiya; wadda hakan kuma ya kunshi: ya yi umurni, ya hana,
ya yi sakayya, ya yi horo.
To idan sammai da kassai ( da ma abin da ke tsakaninsu) ya zama an
halicce su ne don wannan, wadda kuma shi ne manufar yin halitta daukacinta TA
YAYA ZA A CE: (Allah) ba shi da manufa (na halittansa da ya yi) haka kuma babu
wata hikima da ya nufa?
Ko (a ce) ya halicce su ne don kawai bada kwadago wa ma'aikata
(wato halittu su yi aiki, shi kuma ya bada aljanna ko watanta); (za su yi aiki
don) har kar ladan ya ki yin dadin amfana da shi; saboda gori (in da hka kawai
aka basu ba tare da aiki ba)??
Ko kuma (ace: akan yi ibadu ne) don kawai horas da rayuka don wasu
sani na hankali su kwarara musu, da kuma motsa ran don ya saba wa al'adu???
Idan mai hankali ya yi tunanin banbanci da ke tsakanin wadannan
maganganun, da tsakanin (maganan) da wahayi ya yi nuni zuwa gare shi karara=
Zan san (sani na yakini) cewa: Lallai Allah madaukaki ya halicci halitta ne don
bauta masa; da ya game cikar sonsa, tare da kan-kan-da-kai a gare shi, da kuma
mika wuya ga umurninsa.
Saboda tushen bauta shi ne: Son Allah, kai! Kadaita shi madaukaki
da soyayya, ba a son waninsa –ko wanene shi- tare da shi, kawai dai
(bawa) na son wadda ya ke so saboda shi, da kuma a cikisa kamar yadda ya
ke son Annabawansa da manzanninsa da Mala'ikunsa; saboda sonsu na cikin cikar
sonsa. Amma ba kamar son wadda ya riki kishiyoyi koma bayansa; da ya ke sonsu
kamar sonsa.
To kuma idan son Allah ya zama shi ne hakikanin bauta masa, kuma
sirrin bautar kenan To –ka sani- abin sani kawai soyayyar tasa ta kan tabbatu ne da bin
umurninsa, da hanuwa da haninsa; Kenan a wajen bin umurni da hani hakikanin
bauta da soyayyan ke bayyana.
Don haka ne (Allah) mai
tsarki ya sanya bin manzonsa s a w ya zama alama ne da ke nuna sonsa, kuma (bin
nasa) ya zama mai shaida ne akan son, kamar yadda madaukaki ya ce:
(قل إن كنتم تحبون الله فاتبعوني يحببم الله) [آل عمران: ٣١].
(Ka ce: In kun kasance kuna son Allah; to ku
bi ni, Allah zai so ku).
(A cikin ayar) Sai ya sanya bin manzonsa an shardanta shi kafin
ace ya tabbata suna son Allah madaukaki, sa'an nan (son) kuma shi ne sharadin
Allah ya so su. Shi kuwa samuwan abun da aka shardanta ba tare da tabbatuwan
sharadinsa ba kuwa abu ne da ba zai taba yiwuwa ba.
To daga nan; Sai aka san koruwan soyayyar Allah a lokacin da aka
rasa bin manzo. Kai! Hakan ma bai isa ba har sai Allah da manzonsa su su ka fi
soyuwa a wajensa akan wadanda ba su ba.
Kuma duk lokacin da aka samu wani abu a wajensa ya fi soyuwa a
wajensa fiye da su biyun to wannan shi ne shirkar da Allah madaukaki baya
gafartawa, madaukaki yana cewa:
ﭽ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ
ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖﮗ
ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﭼ [التوبة: ٢٤].
(Ka ce: Idan iyayenku da 'ya'yanku da 'yan
uwanku da matanku da danginku da dukiyar da ku ka gaji wajen tara ta da kuma
kasuwancinku da ku ke tsoron tasgarowanta, da gidajen zama da ku ka yarda da su
(Idan wadannan abubuwan duka, ko sashinsu) ya fi soyuwa a wajenku fiye da Allah
da Manzonsa da jihadi a kan tafarkinsa (in haka ya kasance to ku fasikai ne
azzalumai) to ku jira har sai Allah ya zo da al'amarinsa; kuma lallai Allah
baya shiryar da mutane fasikai ).
Duk kuma wadda wadda ya
gabatar da zancen wanin Allah akan zancen Allah, ko kuma ya yi hukunci da shi,
ko ya kai hukuncinsa zuwa gare shi to baya cikin wadanda su ke sonsa.
Sai dai wani lokaci
al'amarin na rikice wa wadda ya gabatar da maganan wani, ko kuma hukuncinsa, ko
biyayyarsa akan maganansa (Allah); da zaton wannan mutumin ba zai yi umurni, ko
ya yi hukunci, ko ya fadi wani abu sai abin da Manzo s a w ya yi umurni; sai ya
masa biyayya –a irin wannan halin- ya kuma kai hukuncinsa zuwa gare shi, haka
kuma ya rungumi maganansa hanu bibbiyu kamar haka. To irin wannan yana da uzuri
idan ba shi da iko akan wanin haka.
Amma idan ya samu ikon isa ya zuwa ga manzon s a w, ya kuma kuduri
cewa: Wanin wadda ya bi (manzo s a w) ya fi masa wadda ya bi shi a dukkan
hukunce –hukunce, ko a sashin al'amura; kamar wata matsala aiyanenniya
(sananniya); don haka sai ya ki juyawa zuwa ga maganan Manzon s a w, haka kuma
ya karkata ga barin maganan wadda ya fi kusanci da shi (manzon; ta wajen binsa)
To irin wannan ana tsorace masa.
Kuma dukkan abin da
kamawa a matsayin hujja da kuma dalili da hana binsa na:
1- Rashin ilimi.
2- Ko rashin fahimta.
3- Ko kuma rashin bamu ilmukan da za su taimake mu wajen fahimta
cikin addini.
4- Ko kuma kafa hujja da wassu mas'aloli da su ka yi kama da wannan, sai dai kuma a hakika hukuncinsu ya
banbanta.
5- Ko kuma cewa: Wane magabaci (Abu hanifata, Malik, Shafi'i,
Ahmad) ya fi mu sanin manufar Annabi s a w.
Duk wadannan neman dalili ne, da baya amfanarwa (Kawai dai ka bi
Manzon Allah s a w).
Dadin-dadawa tare da ikrarin halarcin yin kuskure ga duk wanda ba
ma'asumi ba (ma'ana: wanda ba Annabi ba);
Saidai idan aka yi jayayya kan wannan ka'idar (cewa: wanin
ma'asumi yana iya yiwuwa ya yi kuskure) idan mutum ya yi jayayya kan wannan
ka'idar to bai ma cancanci a yi magana da shi ba; Don haka in ya kaddamar da
maganansa akan na Annabi s a w sai ya shiga cikin wannan narkon (da ayar ta
rufe da shi).
Idan kuma tare da haka ya halatta aibanta wanda ya saba masa, da
sukan mutuncinsa da addininsa da harshensa, Ko kuma ya ciratu daga haka zuwa yi
masa horo (duka ko kisa) ko kuma kokarin cutar da shi To wannan yana cikin
azzalumai masu wuce gona-da-iri, haka kuma yana cikin na'iban mabarnata.
********
[KAIDOJIN IBADA GUDA HUDU]
Kuma ka sani lallai ibada
tana da ka'idodi guda hudu;
Su ne: Hakikicewa (tabbatarwa) cewa wannan aikin Allah da manzonsa
su na sonsa kuma sun yarda da shi, da kuma tsayuwar hakan a zuci da harshe da
kuma gabbai.
Ita kuma bautantaka: Suna ne da ya game wadannan martabobi guda
hudun. Su kuma ma'abotan ibada ta gaskiya su ne ma'abotan hakan (martabobi
hudun);
Shi FADIN ZUCI SHI NE: kudurce abin da Allah ya bada labari akan
kansa, kuma Manzonsa ya bada labari akan Ubangijinsa na sunayenSa, da
sifofinSa, da aiyukanSa, da Mala'ikunSa, da saduwa da Shi (a kiyama) da
makamantan haka.
SHI KUWA FADIN HARSHE SHI NE: Bada labari dangane da shi (Allan)
da harshen, da kuma yin da'awa zuwa ga Allah (da harshen), da kuma bada kariya
a gare shi, da bayyana batancin bidi'a da su ka saba masa, da tsayuwa da
ambatonsa madaukaki, da kuma isar da al'amarinsa (addininsa).
SHI KUMA AIKIN ZUCI SHI NE: Kamar son Allan, da dogara zuwa gare
shi, da mayar da al'amari zuwa gare shi, da tsoro, da fata, da ikhlasi, da yin
hakuri kan umurce –umurcensa da haninsa da kaddaransa, da kuma yarda da shi, da
yarda don shi, da kuma soyayya don shi, da kiyayya don shi, da kuma
kan-kan-da-kai da mika wuya zuwa gare shi, da natsuwa da shi, da makamantan
wannan na aiyukan zuciya; wadanda farillancin farillensu ya fi karfi kan
farillancin aiyukan gabbai, haka kuma wadanda su ke mustahabbai su kuma sun fi
soyuwa zuwa ga Allah madaukaki fiye da mustahabban aiyukan gabbai.
AMMA AIYUKAN GABBAI KUMA; Misalaensu kamar su salla, jihadi, taku
zuwa masallacin juma'a da jam'o'I (na salloli biyar na yau-da-kullum), da kuma
taimakon gajiyeyye, da kyautatawa ga halittu, da makamantan wadannan.
Don haka; Fadin bawa a cikin sallansa:
ﭽ ﭢ ﭣ ﭼ
(A kai kadai mu ke bauta)
(Fadin hakan) lazimtar hukunce-hukuncen wadannan (martabobi) hudun
ne, da kuma tabbatar da su.
Fadinsa kuma:
ﭽ ﭤ ﭥ ﭦ ﭼ [الفاتحة: ٥].
(Kuma a gare ka –kai daya- mu ke neman
taimako).
(Fadin haka kuma) neman taimakonsa ne akansu, da kuma datar da shi
zuwa gare su (nau'ukan bauta).
Fadinsa kuma:
ﭽ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭼ [الفاتحة: ٦].
(Ka shiryad da mu hanya madaidaiciya);
Ya kunshi abubuwa biyun (bauta da kuma samun taimakon Allah wajen
tsayar da itan), akan bayani dalla-dalla (da ya gabata), tare kuma neman Allah
ya yi wa bawa ilhama wajen tsayuwa da su, da bin turbar masu tafiya zuwa ga
Allah ta'ala (na Manzanni, da Siddikai, da Shuhada'u da Salihai).
Allah shi ne mai datarwa da baiwarsa da kyautarsa.
Kuma godiya ta tabbata ga allah shi kadai.
Yabon Allah ya kara tabbata ga wadda babu annabi bayansa da
iyalensa da sahabbaansa; magadansa kuma rundunansa.
LITTAFIN YA CIKA, DA TAIMAKON ALLAH MAMALLAKI MAI YAWAN BAIWA.
Fassarar: Mai neman afuwar Ubangijinsa/ Abubakar Hamza zakaria,
Ina baran kura-kuraina ta wannan adireshi/
An gama fassara shi ranar 26/ 7/ hijirar Manzon Allah s a w daga
Makka zuwa Madina tana shekarar 1431, a garin Madina –Allah ya kara mata daukaka-,
wanda ya yi daidai da / 8/ 7 /2010 miladiyyar Annabi Isa (a s w),
Shafi
|
|
Abubuwan
da ke cikin littafin
|
|
|
|
|
1
|
|
|
|
2
|
|
|
|
3
|
|
|
|
4
|
|
|
|
5
|
|
|
|
6
|
|
|
|
7
|
|
|
|
8
|
|
|
|
9
|
|
|
|
10
|
|
|
|
11
|
|
|
|
12
|
|
|
|
13
|
|
|
|
14
|
|
|
|
15
|
|
|
|
16
|
|
|
|
17
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|
|