HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى
الله عليه وسلم)
JUMA'A, 13/SHAWWAL/1438H
daidai da 07/JULAYE/ 2017M
LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
Nm,,
Shehin Malami wato: Aliyu
bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: mn,,, Wanda kuma a cikinta ya
tattauna, akan
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
"Yabo ya tabbata ga
Allah Ubangijin talikai", "kuma yabon nasa ne a ta farko (duniya) da
ta qarshe (lahira), kuma hukunci nasa ne, kuma zuwa gare shi za a mayar da ku" [Qasas: 70],
Ya halitta halittu, ba a
kan wani misali ba da ya gabata, kuma ya qaddara qaddarori da iliminSa da kuma
qudurarSa, kuma sunnarSa ta shuxe, kuma nufinSa ya zartu, kuma kalmarSa ta
xaukaka, Tsarki ya tabbata ga Ubangijina; "Ba a tambayarSa kan
abinda ke aikatawa, su ne ake tambayarsu" [Anbiya'i: 23].
Ina yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa akan
ni'imominSa gaba xaya,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya, sai Allah shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, mulki
nasa ne, kuma yabo nasa ne, kuma ya xaukaka ga barin abinda su ke masa shirka.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Wanda aka tayar da
shi, domin ya zama rahama ga talikai.
Ya Allah! ka yi salati, da
sallama ga bawanka kuma manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa, waxanda
su ka shiryu da shiriyarsa.
Bayan haka:
Ku bi Allah ta'alah
da taqawa; saboda taqawar Allah ita ce dalilin sa'ada a duniya, da samun rabo a
lahira, domin babu wanda zai samu sa'ada idan ba masu taqawa ba, kuma babu
wanda zai yi hasara face bijirarru.
Ya ku, Bayin Allah…
!!!
Mafi alherin abinda mutum ya
samar shi ne, AIKI NA KWARAI, wanda UbangijinSa, zai yarda da mutum saboda aikin,
sai ya samu sa'ida da shi a duniyarsa, ya kuma rabauta da shi a cikin dukkan
halin da ya samu kansa, ya kuma samu daraja maxaukakiya da shi a lahira, sai a xora
shi bisa ga matsayin da Allah ya rubuta masa samunsa.
Kuma idan Allah ya sauqaqe
wa bawa ibada, kuma ya masa baiwar yin ikhlasi a cikin aikin, kuma ya datar da
shi da bin shiriyar Annabi, da riqo da Sunnah, to haqiqa Allah -Mabuwayi da
xaukaka- ya karrama shi da mafi girman abin karramawa, kuma ya masa baiwa da
mafi girman abin nema, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Lallai ne Allah yana bada duniya ga wanda
Allahn ke so, da wanda baya so, sai dai kuma baya bada addini sai ga wanda ya
ke so".
Kuma Allah ta'alah yana
cewa: "Lallai ne Allah yana karvar aiki ne daga masu taqawa" [Ma'ida: 27].
Kuma wajibi ne akan bawa, ya tsayu wajen gode wa
karramawar da Allah ya masa na aikata xa'a, ta hanyar dawwamar da daidaituwa
akan addini, saboda duk wanda ya dawwama akan tsayuwa a bisa addini, shi ne zai
rabauta da alkhairori, kuma ya tsira daga abubuwa masu halakarwa, Allah ta'alah
yana cewa: "Lallai waxannan da su ka ce, Ubangijinmu shi ne Allah, sannan su ka
daidaitu, Mala'iku na sassauka akansu (a lokacin saukar ajalinsu, suna cewa:)
Kada ku ji tsoro, kuma kada ku yi baqin ciki, kuma ku yi bushara da aljannah,
wadda kuka kasance ana muku wa'adi da ita" [Fussilat: 30].
Kuma an karvo daga Sufyan
xan Abdullahi, ya ce: Na ce ya Manzon Allah! Ka gaya mini wani zance a cikin
musulunci, wanda ba zan tambayi wani ba, idan ba kai ba? Ya ce: "Ka ce: Na yi imani
da Allah, sa'annan ka daidaitu". Muslim ya ruwaito shi.
Ayyuka kyawawan da Allah ke karrama wanda ya nufa daga
cikin bayinSa, dole sai an yi aikin KIYAYE SU, ta hanyar nisantar ababen da za
su vata su, na ayyukan savo da zunubai, ko su ke tauye ladansu; na laifuka, da zalunci,
Allah ta'alah yana cewa: "Ya ku waxanda su ka yi imani, ku yi xa'a wa
Allah, da ManzonSa, kuma kada ku vata ayyukanku" [Muhammadu: 33].
Sai ka yi qoqari –Ya kai musulmi- ka kasance a yau, ka fi
alkhairi akan jiyanka, kuma ka kasance a gobenka ka fi alkhairi akan yau xinka.
kuma duk wanda ya yaqi kansa wajen ayyukan xa'oi, ya kuma
yaqi kansa wajen nisantar abubuwa na haram, sai Allah ya taimake shi, ya kuma
shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma waxannan da su
ka yi jihadin neman yardarmu, lallai za mu shiryar da su ga hanyoyinmu, kuma
lallai Allah yana tare da masu kyautatawa" [Ankabut: 69].
Yau (wato a duniya) ake tsere, gobe (kiyama) kuma, yini ne
na raba kyautukan waxanda su ka yi rigaye.
HASARA wacce babu wani abu da ke tsayuwa a matsayin
canjinta, da KARAYAR da bata warkewa, da TAVEWAR da babu sa'ida a tare da ita, ita ce LALACEWAN AYYUKA, bayan kyawunsu, da
KOMAWA BAYA bayan DAIDAITUWA.
Saboda shexan yana jiran mutum a madakata, kuma ya zauna
masa akan kowace turbar alkhairi, domin ya kange shi daga aikata alkhairin,
kuma domin ya vata ayyukansa nagari, da abinda (a kullum) ya ke qawata masa na
shubuhohi da bidi'oi da sha'awowi, Allah ta'alah ya faxa, dangane da adawar
Shexan: "Sa'annan zan je musu daga gaba gare su, da baya gare su, da kuma
daga jihohin bayansu, da jihohin hagunsu, kuma ba za ka sami mafi yawansu suna
masu godiya ba"
[A'araf: 17].
Sai dai kuma qofofin alkhairi suna dayawa, hanyoyin samun
falaloli da gafara suma suna da faxi, kuma rahamar Allah ta dabaibaye halittu,
kuma a cike, kuma babu mai halaka a wurin Allah, face halakakken da babu
alkhairi a tare da shi.
Kuma lallai ibadodi, da ayyukan samun falaloli suna nan a
kowani wata, bal a kowace rana.
Kuma Ubangiji yana gode wa bayinSa akan aikinsu kaxan,
sai ya sakanta musu da sakamako mai tarin yawa, Allah ta'alah yana cewa: "Lallai Allah ba ya
zaluncin gwargwadon nauyin zarra, idan ta kasance alheri ce, sai ya rivanyata,
kuma ya kawo daga wurinsa lada mai yawa" [Nisa'i: 40].
Kuma yana daga cikin QOFOFIN ALKHAIRI MASU GIRMA, da amfani
mai gamammen fa'ida, kuma yana daga cikin qofofin biyayya wanda tasirinsu ke
tsawaita, alkhairinsa ke da faxi: BIYA WA MUTANEN DA AKE BIN
BASHI BASHINSU, DA TAIMAKA MUSU WAJEN SAUKE HAQQOQIN WAJIBIN DA SUKA XORU
AKANSU, kana
mai neman abinda ke wurin Allah na sakamako mai girma, musamman kuma waxanda aka
kurkukunce su, daga cikin mutanen da su ka gaza wajen biyan basukan da ke
wuyansu, waxannan da su ke jiran wanda zai tsamo su, daga cikin ma'abuta
jin-qai, da kyautatawa, saboda sun yi kama da waxanda ruwa ya haxiye wanda su
ka cancanci a kama hannunsu, zuwa gavar tsira, waxanda lokutan idi da lokutan
farin cikin mutane ke shuxe musu alhalin suna cikin kurkuku, saboda basuka,
alhalin sun dulmuya cikin vacin ran tunanin basuka. Abinda kuma ya fi hakan
girma, shi ne tunaninsu ga waxanda ke bayansu, (na 'ya'ya) waxanda su ke tsorace
musu tozarta, ga kuma tarin buqatu.
Ma'abuta musulunci su ne ma'abuta jin-qai da kyautatawa.
Kuma lallai a cikin dukiyar mawadata ta zakka () da
sadakoki, akwai abinda ya xoru akan buqatun mabuqata.
Kuma yana da sauqi, a iya kaiwa ga xaixaikun waxannan
mabuqatan waxanda su ke kulle a kurkuku, saboda basuka, ta hanyar shugabannin
gidajen kurkukun, domin a biya masu basukan bashin da su ke bi, ta hanyar
yaqini, tare da baiwa mutanen da ake bi bashi, abinda za su ciyar da iyalansa,
na tsawon lokacin da zasu fara aiki, a bayansa.
Kuma abu ne mai sauqi, bibiyan mabuqata domin warware
musu buqatunsu, a kowani birni da gari, domin taimaka musu a lokutan
buqatuwansu, Allah kuma yana cewa: "Kuma duk abinda ku ka ciyar daga wani abu,
to shi ne zai musanya shi, kuma shi ne mafificin masu azurtawa" [Saba'i: 39].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Sadaka bata tauye
wata dukiya".
Kuma albishir wanda ya fi duniya da abinda ke cikinta
alkhairi ta tabbata ga wanda aka datar da shi, wajen yin irin wannan aikin, da
kuma mutumin da ya buxe irin wannan qofar ta taimako, kuma ya lazimce ta, albishir,
wanda ya zo a cikin faxin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم): "Wanda ya kwaranye baqin ciki ga mumini, daga cikin
baqin cikin duniya, Allah zai kwaranye masa baqin ciki, daga cikin baqin cikin
lahira, kuma duk wanda ya sauqaqe wa mutumin da ke cikin qunci, Allah zai
sauqaqe masa a duniya da lahira, kuma duk wanda ya rufa asirin musulmi, Allah
zai rufa masa asirinsa a duniya da lahira, Allah yana taimakon bawa, matuqar bawan
yana cikin taimakon xan'uwansa", Muslim ya ruwaito shi.
Kalmar "kurbatun" a cikin hadisin,
tana nufin tsanani mai girma, wanda ke aukar da ma'abucinsa, cikin baqin ciki.
Shi kuma baqin cikin yinin
qiyama, wanda ke kasancewa a gabanin shiga aljannah, dukkansu suna da girma, ga
kuma tarin yawa. Kuma yana daga cikinsu: Abinda Bukhariy da Muslim su ka
ruwaito daga hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه) ya ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mutane za su yi
gumi, a yinin qiyama, har sai guminsu ya tafi a bayan qasa, na tsawon zira'i
saba'in, kuma zai musu linzami, har sai ya kai ga kunnuwansu".
Kuma an ruwaito daga Uqbah
bn Amir (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce: "Kowani mutum yana
qarqashin inuwar sadakarsa ne, har a yi hukunci a tsakanin mutane", Hadisi ne
ingantacce, Ahmad ya rawaito shi.
Allah ta'alah yana cewa: "Kuma ku yi gaggawa
zuwa ga neman gafarar Ubangijinku, da wata aljannah, wadda faxinta daidai da
sammai da qasa ya ke, an yi tattalinta domin masu taqawa * Waxannan da su ke ciyarwa
a cikin sauqi da tsanani, kuma su ke masu haxiyewar fushi, kuma masu yafe wa
mutane, kuma Allah yana son masu kyautatawa" [Ali-imraan: 133-134].
Allah ya yi mini albarka NI
da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI
da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman
gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi,
Ku nemi gafararSa, lallai shi Mai
gafara ne Mai rahama.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, Mai yawan
azurtawa, ma'abucin tsananin qarfi,
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, Mai gaskiya, Amintacce,
Ya Allah ka qara salati da
sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalansa, da
sahabbansa, har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka … !!
Ku yi taqawar Allah, iyakar
taqawa, domin duk wanda ya yi taqawar Allah, sai ya sanya shi cikin
majivintarsa, kuma duk wanda Allah ya jivince su, to sai ya kiyaye su, a
duniyarsu da lahiransu.
Ya ku Bayin Allah …
!!
Ku sani lallai manufar
musulunci ita ce: Mutum ya kyautata wa ransa, da kuma kyautatawa halittu,
Amma KYAUTATA WA RAI to, ta
kan tabbatu ne, ta hanyar TABBATAR DA TAUHIDI GA UBANGIJI Mabuwayi da xaukaka,
da tsayuwan bawa da AIKATA NAU'UKAN IBADODI, cikin son Allah, da qanqan-da-kai
da rusunawa da miqa-wuya, da NISANTAR ABUBUWAN HARAMUN, Allah yaan cewa: "Kuma bayin Mai
rahama su ne waxanda ke yin tafiya akan kasa da sauki, kuma idan jahilai suka
yi musu magana sai su ce salama (a zauna lafiya) * kuma waxanda su ke kwana
suna masu sujjada da tsayi a wurin Ubangijinsu * kuma waxanda su ke cewa ya Ubangijinmu
ka karkatar da azabar jahannama daga gare mu, lallai ne azabarta ta kasance mai
dawwama * lallai ne jahannama ta munana ta zama wurin tabbata da mazauni * kuma
waxanda su ke, idan sun ciyar basu yin varna kuma basu yin kwauro kuma
(ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakanin wancan da tsakaitawa * kuma waxanda basu
kiran wani Ubangiji tare da Allah, kuma basu kashe rai wanda Allah ya haramta
face da haqqi, kuma basu yin zina, kuma wanda ya aikata wancan zai gamu da
laifuffuka * za a rivanya masa azaba ranar qiyama, kuma ya tabbata cikinta yana
wulaqantacce * sai wanda ya tuba, yayi imani, kuma ya aikata aiki na kwarai, to
waxancan Allah yana musanyan miyagun ayyukansu da masu kyau, Allah ya kasance Mai
gafara Mai jin qai"
[Furqan: 63-70]
Amma shi kuma KYAUTATA WA
HALITTU to, ta kan kasance, da NA'UKAN KYAUTATAWA, na ciyarwar wajibi ko ta mustahabbi,
ko karantarwa, ko jurewa da shanyewa da haquri, da kamewa daga cutarwa, da
makamncin haka, Annabi (صلى
الله عليه وسلم) yana cewa: "Halittu iyalan Allah ne, kuma halittar da
ta fi soyuwa a wurin Allah, ita ce, wanda ta fi amfanar da iyalanSa".
Ma'anar "iyali" a
cikin hadisin, shi ne, Allah ke xaukar nauyinsu.
Ya ku Bayin Allah… !!!
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga
wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da
sallama ta aminci"
[Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa
Annabi Muhammadu, ……………………………
,,, ,,, ,,,