2017/03/09

hudubar 11 JUMADAL AKHIRAH 1438 daidai da 10 MARIS 2017 TA الثبيتي MASALLACIN MANZON ALLAH SAW










HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 11 /JUMADAL AKHIRAH/1438H
daidai da 10/ MARIS/ 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULBARIY XAN AWWADH AS-SUBAITIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA



RAYUWARMU TA GABA
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Auwadh As-subaity –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: RAYUWARMU TA GABA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna,

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO

Bayan haka:

Shekarun rayuwar mutum suna ciratuwa ne tsakanin (lokatai uku); lokacin da ya gabata, wanda ya shuxe,
da lokacin da ake ciki, halartacce,
da kuma lokaci mai zuwa, wanda aka alqawarta, Allah yana cewa: "Kuma haqiqa Ya halitta ku, mataki-mataki" [Nuh: 14].
Domin, Allah (تعالى) ya halicci mutum yana JINJIRI, da ke cikin mahaifiyarsa,
sa'annan aka haife shi, yana QARAMIN YARO,
sai kuma ya dawo, SAURAYI QAQQARFA,
sa'annan DATTIJO.
Kuma duk abinda ya kasance abin jira, to, lokacinsa, zai halarto,
duk kuma abinda ake cikinsa, to zai wayi-gari ya wuce,
       Sai dai kuma abinda ke shagaltar da tunani, ko hankalin mutum (a koda-yaushe), ya ke kuma cika masa lokacinsa, shi ne tunani kan abinda gaba za ta zo da su,

       Kuma haqiqa ya tabbatu, cikin aqidar musulmi, lallai lokaci mai zuwa, yana daga ilimin gaibu, wanda kuma babu mai saninsa sai Mahalicci, wanda tsarki ya tabbata a gare shi, Allah (تعالى) yana cewa: "Ka ce: Waxanda ke cikin sammai da qasa, babu wanda ya san gaibu, face Allah" [Naml: 65].
Kuma ababen da za su auku, a gaba, iliminsu yana wurin Allah; domin Allahu (تعالى) yana cewa: "Kuma Rai bata san me za ta aikata gobe ba, kuma babu wata rai da ta san a wace qasar za ta mutu, lallai ne Allah Masani ne, Mai bada labari" [Luqman: 34].
Sai dai kuma NEMAN TSINKAYAR ABINDA  ZAI AUKU A GABA, DA BEGEN SANINSA, DA SON GANO MENENE SHI, na daga halittar Allah; wanda ya halitta mutane akansu, kuma rayuka an xabi'antar da su, ga son hakan.
Kuma jiran me gaba za ta zo da shi, yana daga haqiqanin musulunci, da kuma saqon Annabawa; saboda annabi Yusuf (عليه السلام) ya yi hasashen mai zai kasance a lokaci na-gaba (a fassarar mafarki), kuma da hakan ya kyautata tsarin fiskantar yanayin, kuma da shi Allah (ta'alah) ya tsamar da garurruka, da bayinSa daga mutsalar tattalin arziqi (da yunwa), mai matuqar tsanani.
  Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana hasashen abu mai kyaun da zai zo a gaba, ta mahangar mai kyautata zato (mai fa'al), wanda ya aminta, da zuwan abinda Allah ya alqawarta, sai Annabi ya riqa cewa: "Wallahi!!! Lallai Allah zai cika wannan lamari (na musulunci), har mahayi (matafiyi) ya yi tafiya daga garin San'a'a, zuwa garin HadaraMaut, baya tsoron komai face Allah, ko kuma kyarkeci ga dabbobinsa, Sai dai kuna yin gaggawa ne".
Jiran kyakkyawan gobe, na farkar da rayuka, rayayyu, lafiyayyu, kuma yana kunno himmomi maxaukaka, yana korar xabi'ar; xebe fata, yana kuma yaqar sanyin guiwa, yana tunkuxa mutane zuwa ga tunanin yadda za a amfana da damammakin da ake da su, a yanzu, a hanyar mu ta gina, zamani na-gaba mai haske.
Kyautata fatar me gaba zata zo da shi, baya nufin, tsawaita ko, dogon buri, da jinkirta aikin yau, wanda ke kashe himmomi maxaukaka, kuma ya ke raunata azama, kuma ya ke gadar da kasala, da jinkirta aiyuka. Kuma aiki bai ta tava muni ba, face sababin hakan shi ne tsawaita buri, Allah (تعالى) ya ce: "Bar su (kyale su), su ci, kuma su ji daxi, kuma guri ya shagaltar da su, kuma da sannu za su sani" [Hijir: 3].
Ba a gina lokatai masu zuwa, kuma ba a fatan ganin kyansa, ta hanyar gurace-gurace wanda basa tare da aiyuka a tattare da su, a qasa, kuma hakan, baya canza komai a cikinsu, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma Allah ya buga wani misali, na mutane biyu, xayansu bebe ne baya iya samun damar aikata komai, kuma shi nauyi ne akan wanda ya mallake shi, in da duk ya fuskantar da shi, ba ya zuwa da wani alheri. Shin, zai daidaita, shi da wanda ke umurni da ayi adalci, kuma yana a kan, tafarki madaidaici?" [Nahl: 76].

Sai dai kuma akwai waxanda su ka karkace, daga madaidaiciyar hanya, wajen qoqarin sanin me lokaci na-gaba zai zo da shi, ta hanyar aukawa cikin abinda Allah ya haramta, na bokanci da sihiri da tsubbu (rufa ido), Sai xayansu ya tafi zuwa ga bokaye waxanda su ke magana, da shaci-faxi, kuma su ke aiyukan halarto da shaixanu, ya je wurinsu yana qan-qan da kai ga rubuce-rubucen sihiri, da sihirin karatun tafukan hannu, da kofi, da taurari.
Bokaye hatsarinsu mai girma ne, kuma munkarin aikinsu babba ne, kuma bokaye kafirai ne fajirai, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya je wa mai duba, sai ya tambaye shi kan wani abu, to ba za a karva masa sallar darare arba'in (da yininsu) ba", Kuma ya ce: "Wanda ya je wa mai duba, ko boka, sai ya gaskata shi cikin abinda ya ke faxi, to lallai ya kafirce da abinda aka sauqar wa (annabi) Muhammadu –صلى الله عليه وسلم-".
       Fatan gobe da zo da kyau, hanya ce ta masu hankali, da kwakwale,
Sai dai abinda dole a kiyaye shi ne, kada wannan tunanin ya juye zuwa ga vacin rai, wanda ke dagula ko gurvata wa mutum tunaninsa a makwancinsa, ko ya zama baqin cikin da zai lalata masa rayuwarsa, ko kuma rashin natsuwa, wanda zai dame shi a kai-komonsa, sai ya riqa tsoron kada cuta ta kama shi, ko kuma talauci, ko wani bala'in, ko samun canjin hali, Allah (تعالى) yana cewa: "Shexan yana alqawarta muku talauci, kuma yana umurtar ku da alfasha, Allah kuma yana alqawar muku wata gafara daga wajensa da falala" [Baqara: 268].

Kuma muna da abin koyi mai kyau daga  rayuwar Manzon Allah, saboda halinsa ya caccanza daga qaramin yaro maraya, zuwa ga mai neman mafaka, wanda ake zalunta, zuwa ga shugaban wannan al'ummar gaba xayanta.
Annabi, ya yi ta fafutuka domin tunkuxe bala'oin rayuwa, har ya fito mana da al'ummar (sahabbai) waxanda su ka canza yadda tarihin duniya ke tafiya.

       Aiki domin gina rayuwa ta gaba, yana farawa ne, daga xaukar ibra ko kula, da matsayoya na tarihi, da darrusa waxanda su ka gabata, da qissoshin magabata, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma haqiqa misalai sun shuxe a gabaninku, sai ku yi tafiya a bayan qasa, sa'an nan ku duba, yaya aqibar masu qaryatawa ta kasance" [Ali-imrana: 137].
Kuma ya ce: "Lallai ne, abin kula ya kasance a cikin qissosinsu, ga masu hankali" [Yusuf: 111].
Jiran rayuwa ta gaba mai kyau, ana gina shi ne a kan, lokacin da ake ciki, domin idan mutum ya kyautata aikin lokacin da ya ke ciki, to, sai lokacinsa da ke tafe ya haskaka,
Wanda kuma, ya tozarta zamanin da ake ciki (yau xinsa), to, sai ya gaza kyautata lokacinsa da ke tafe.
Kuma duk wanda ya tozarta gina hankalinsa da tunani, ko aqidarsa da jikinsa, to sai ya girbi talauci, da baxala, da kuma cuta,
Wanda kuma ya tozarta tarbiyyar 'ya'yansa, to sai ya girbi karkacewarsu, da kuma cutarwa.

Jiran rayuwa ta gaba mai kyau, da qoqarin yin tasiri ga lokacin da ke tafe, a kan ginshiqai lafiyayyu, yana hukunta mutum ya yi amfani da rayuwarsa wajen bunqasa hankalinsa, da gina tunaninsa da aqidarsa.
Kuma, lallai Mutum ba zai xebe fata ko tsammani dangane da lokacin da sha'ani ke tsananta ba, a'a, mutum (ana neman) ya yi qoqarin mayar da baqin ciki, farin ciki, yana mai shuka fata, a cikin lamura masu tsanani, kamar yadda lamarin ke hukunta, musulmi ya kasance mai haquri da juriya wajen cimma manufofinsa, mai kuma wadatuwa da abinda Allah ya raba ya bashi, mai imani da abinda Allah ya ke qaddara masa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Idan qiyama ta zo tashi, sai kuma ya kasance, a hannun xayanku akwai abin dashe, sai ya samu damar dasa su gabanin ta tashi, to, sai ya dasa".

Kuma qoqarin samar da rayuwa ta gaba mai kyau na kafuwa ne, har tushenta su yi qarfi, a kan ginshiqin ilimi, wanda ya ke haskaka hanya, kuma ke samar da  rayuwa mai karamci, ya kuma bunqasa al'ummai, ya kuma ciyar da qasashe gaba, ya kare su daga qunci, Imamu Malik –رحمه الله- yana cewa: "Lallai ne, wasu mutane, sun yi bauta, sai su ka tozarta ilimi, sai su ka fice daga al'ummar annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم)".

       Rayuwa ta gaba za ta bada fa'ida ne, kuma tasirinta ya bayyana kuma ya tabbatu, ta hanyar bada tarbiyya, da tsarkake halayya, saboda bayan kowace al'umma mai girma, akwai tarbiyya da gyaran hali, waxanda su ke musu jagora zuwa ga tudun tsira, kuma su ke gina 'ya'ya da jikoki, waxanda za su samar da rayuwarsu ta-gaba.

       Kuma babu shakka, lallai takun musulmi wajen tafiyarsa don samar da zamaninsa na-gaba, takunsa dole su kasance an kewaye su da faxakuwa, a matakan tashin musulmi daga yanayi zuwa wani yanayin, ta hanyar yin hisabi -a ransa-, a kan lamarin rayuwar duniya, kuma ya riqa tsayawa domin yin tunani, a tsawon tafiyarsa ta rayuwa, yana mai bada hukunci ga zuciya da hankali da soyayya a salonsa na gino rayuwar gobe, yana kuma amfani da lokutan ibadodi, waxanda su ke qarin haske da albarka da walwala, ga rayuwar da za ta zo a gaba, da bashi kariya, da datarwa.
Kuma musulmi mai kaifin hankali da hangen nesa, yana sane cewa, lallai zamani mai zuwa zai bunqasa ne, idan musulmi ya zamo ya fi kusantar bautarsa (سبحانه), tare da tuba ta gaskiya, wacce za ta riqa bada kariya ga zamanin, daga sharrin shexan, da rai mai umurni da mummuna, da bin son zuciya, da gafala, ko rafkana.

       Aure mai tarin nasara, wanda ya ginu akan manufofi maxaukaka, shima wani lokaci ne da kowani musulmi ke cikiyar samu, wanda kuma aminci da natsuwa su ke tabbatuwa a cikinsa, da kuma hutu, da ni'ima.
       Kamar yadda ni'imar uwa da uba, suma suna qara wa rayuwarmu ta gaba ado da qawa, su kuma 'ya'ya, su ne ai, ababen dogararmu a gobe, kuma da su ne rayuwa ke zaqi, kuma ake janyo arziqi, kuma rahama tana sauka, ana kuma rivanya lada.

       Rayuwar gaba ta al'ummomi da jama'u, da rabauta a rayuwarmu ta gobe, haqiqa samarinmu na yau sune su ke gina ta, su ke zana yadda za ta zama, don haka; idan al'umma ta yi aikin gina 'ya'ya nagari da jikoki, to lallai rayuwarta ta gaba za ta kasance, cikin xinbin alkhairi. Sai xaukaka ya jira wannan al'ummar, qarfi kuma ya bata kariya, halayya nagari su katange ta,

       Kuma, a nan, (wajibi) mu sani, cewa lallai gina gobenmu yana wajaba ne a kan xaixaiku, kuma yana wajaba akan al'ummai da jama'u,
       Kuma lallai al'umma duk lokacin da ta qara kusantar tsari ko shari'ar musulunci, to sai ta bunqasa, tana mai xaukaka,     Kamar yadda kuma, idan ta nisanci tsarin musulunci, to sai koma-bayanta da rauninta su qaru.

       Kuma mai hankali baya shakka, cewa lallai rayuwarmu ta gaba za ta bunqasa ne, kawai a inuwar AMINCI DA ZAMAN LAFIYA, saboda koma-baya cikin lamuran tsaro yana tauye rayuwa, kuma yana jagorantar mutane zuwa ga rashin tabbas, da kuma zamani na gaba mai tangal-tangal, Allah (تعالى) yana cewa: "Saboda sabon Quraishawa * sabonsu na tafiyar hunturu, da ta bazara * Sai su, bauta wa Ubangijin wannan gida (Ka'aba) * Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Quraish: 1-4].

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Ina faxar abinda ku ke ji wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
           
Bayan haka:
Wasu mutane suna manta maslahohin rayuwarsu ta gaba, sai kuma su dulmuyu cikin rayuwarsu ta yau, sai mutum ya yi nitso cikin ni'ima, ya fifita rayuwar gaggawa (ta duniya) akan rayuwa me nisa (rayuwar lahira), Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ku ribaci abu biyar gabanin guda biyar, samartakarka gabanin tsufarka, da afiyarka gabanin cutarka, da wadacinka gabanin talaucinka, da faragar lokaci gabanin shagaltuwarka, da rayuwarka gabanin mutuwarka".

Mutum, ana sanya masa shamaki daga samun rayuwa ta gaba mai kyau, a lokacin da ke ratayuwa da kwanson rayuwa (ababe marasa muhimmanci), kuma ya ke dubi ga ababen da su ke aukuwa a cikinta, su kaxai (ba tare da ya yi dubi ga wanda ya qage su ba), sai kuma ya ruxu da kyalkyalin rayuwar duniya.

Rayuwar gaba madawwamiya tana jiranmu, gaba xaya, wanda a cikinta akwai farin ciki da walwala, ko kuma raxaxi, ko ni'ima da karramawa, wanda kuma shi ne, lokacin sakayya, da bada lada, a yinin qiyama.
Shi kuma wannan lokacin da mu ke fiskanta yana farawa ne, daga daqiqar da ake rabuwa da iyalai (a mutu) sai a cusa bawa cikin turvaya (qabari), domin a shamakance tsakaninsa da yin aiyuka.

Wannan shi ne abu na gaba, wanda ya wajaba mu sanya shi a gaba gare mu, a fiskarmu, mu riqa tanadi a gare shi,
Kuma yana daga aiyukan da su ke baka aminci ga wannan abu mai zuwa (qiyama), faxin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم): "Abubuwa bakwai ladansu na gudana ga bawa, bayan mutuwarsa, alhalin yana cikin qabarinsa; WANDA YA KARANTAR DA WANI ILIMI, ko YA JANYO KOGI, ko YA TONI WATA RIJIYA, ko YA DASA BISHIYAR DABINO, ko YA GINA MASALLACI, ko YA GADAR DA MUS-HAFIN QUR'ANI, ko YA BAR XA NAGARI YANA NEMA MASA GAFARA a bayan mutuwarsa".
Kuma Qur'ani ya hakaito mana labarin wasu mutane, waxanda rayuwar lahira da su ke jira, ta zo musu kwatsam, alhalin ba su mata tanadi, ko aiki ba, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma a ranar da sa'a za ta tsayu, masu laifi za su yi rantsuwa cewa ba su, zauna (a duniya ko a qabari) ba, face sa'a guda, kamar haka su ka kasance ake karkatar da su" [Rum: 55].
Kuma ya ce: "Kamar, Su, a ranar da su ke ganinta (qiyama), ba su zauna ba, face gwargwadon lokacin maraice ko hantsi" [Nazi'at: 46].

Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, saboda Allah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa: "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].

Ya Allah! Ka yi salati wa Annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi salati wa Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai girma. Kuma ka yi albarka ga annabi Muhammadu da matansa da zurriyarsa, kamar yadda ka yi albarka wa Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai Abin godiya ne Mai girma.      
Ya Allah! Ka yarda da khalifofi guda huxu shiryayyu;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da iyalan annabi da sahabbai masu karamci, ka haxa da mu da baiwarka, da rahamarka, Ya mafificin masu rahama.
            Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
Ya Allah! ka xaukaka musulunci da musulmai,
kuma ka qasqantar da kafirci da kafirai, kuma
Ya Allah! Ka ruguza maqiyanka; maqiyan addini,
Ya Allah! Ka sanya wannan qasar ta zama da aminci, cikin nitsuwa, da sauran qasashen musulmai.
            Ya Allah! Ka kasance wa musulman da ake raunata su a kowani wuri, ka kasance musu, Mai qarfafawa, Mai basu nasara, kuma Mai taimako,
            Ya Allah! Ka kasance wa musulman a garin Halab, da Shaam, da Mausil, da Iraqi, da Filasxinu, da kowani wuri ya Ubangijin talikai, Ya Allah ka kasance musu, Mai qarfafawa, Mai basu nasara, kuma Mai taimako,
Ya Allah! Lallai su, masu jin yunwa ne ka ciyar da su, basu da takalma ka basu, tsirara su ke, ka tufatar da su, kuma an zalunce su, ka taimake su, Ya Allah lallai ne su an zalunce su, ka taimake su, Ya Allah lallai ne su an zalunce su ka taimake su,
Ya Allah! Duk wanda ya nufe su da mummuna to ka sanya kaidinsa a qirjinsa, kuma ka sanya rugujewarsu cikin tsare-tsarensu, Ya Mai amsa addu'a
Ya Allah ka rarraba kan maqiyansu, kuma ka wargaza haxuwarsu, ka sanya mummuna ya juyo akansu, Ya Ubangijin talikai,
Ya Allah Wanda ya saukar da littafi, wandas ke gudanar da gajimare, Mai ruguza qungiyoyi, ka ruguza maqiya musulmai, kuma ka taimake musulmai akansu, Ya Ubangijin talika, Ya Mai tsananin qarfi.
Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka aljanna, kuma muna neman tsarinka daga wuta.
Ya Allah! Ka gyara mana addininmu, wanda shine qashin bayan lamarinmu, kuma ka gyara mana duniyarmu wacce rayuwarmu ta ke cikinta, kuma ka gyara mana lahirarmu wanda zuwa gare ta ake mayar da mu, kuma ka sanya rayuwa ta zamo qari a gare mu daga kowani alkhairi, kuma ka sanya mutuwa ta zama hutu a gare mu daga aikata kowani sharri, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka mabuxan alkhairi da qarshensu, da abinda ya tattara su, da farkonsu da qarshensu, da zahirinsa da baxininsa, kuma muna roqonka darajoji maxaukaka a cikin aljanna, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka taimake mu, kada ka taimaki maqiya akanmu, ka bamu nasara, kada ka basu nasara akanmu, ka qulla mana, kada ka qulla musu akanmu, ka shiryar da mu, kuma ka sauqaqe shiriya a gare mu, ka bamu nasara akan wanda ya zalunce mu,
            Ya Allah! Ka sanya mu mu zama masu ambatonta, masu gode maka, masu tsoro a gare ka, masu yin kuka a gare ka, masu mayar da lamari,
Ya Allah! Ka karvi tubanmu, ka wanke zunubanmu, kuma ka tabbatar da hujjarmu, ka daidaita harsunanmu, kuma ka cire dauxar zukatanmu.
            Ya Allah! Lallai muna neman tsarinka daga gushewar ni'imominka, da canzawar lafiyarka, da zuwan azabarka kwatsam, da kuma dukkan fushinka.
            Ya Allah! Ka yi rahama ga mamatanmu, ka bada waraka ga marasa lafiyanmu, kuma ka jivinci lamuranmu, kuma ka sa mu cika da alheri, Ya Ubangijin talikai.
            Ya Allah! Ka gyara sha'aninmu dukkansa, kuma kada ka dogarar da mu zuwa ga kayukanmu, daidai da kyaftawar ido,
            Ya Allah! Lallai ne mu muna roqonka kyakkyawan cikawa, da kuma afuwa kan abinda ya gabata, ko ya kasance
            Ya Allah! Ka shumfuxa mana daga albarkokinka, da rahamarka, da falalarka, da arziqinka
            Ya Allah! Lallai mu muna roqonka –ya Allah- saboda kai ne Allah, wanda babu abin bauta sai kai, kai ne Mawadaci mu kuma mu ne faqirai, Ya Allah ka saukar mana da ruwan sama, kada ka sanya mu daga cikin masu xebe tsammani, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama, Ya Allah! Ka shayar da mu ruwan sama.
Ya Allah!, shayarwa ta rahama, ba na azaba, ko bala'i, ko rusau, ko nitsewa ba
            Ya Allah! Ka datar da shugabanmu zuwa ga abinda kake so, kuma yarda, Ya Allah! Ka datar da shi zuwa ga shiriyarka, kuma ka sanya aiyukansa cikin yardarka, Ya Ubangijin talikai.
            Ku ka datar da xaukacin jagororin musulmai wajen yin aiki da littafinka da yin hukunci da shari'arka, Ya Ubangijin halittu.
            "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kayukanmu idan baka gafarta mana, ka yi mana rahama ba to zamu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
            "Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana, da 'yan'uwanmuda suka rigaye mu da imani, kuma kada a zukatanmu ka sanya wani qulli ga waxanda su ka yi imani, Ya Ubangijinmu lallai kai Mai tausasawa ne Mai jin qai" [Hashr: 10].
            "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau a duniya, kuma ka bamu mai kyau a lahira, ka kare mu daga azabar wuta" [Baqarah: 201].

"Lallai ne Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanta, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.

,,,          ,,,          ,,,

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...