HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 19 /RABI'U AS-SANIY/1437H
Daidai da 29 / 01 / 2016M
LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN ABDURRAHMAN XAN MUHAMMADU
ALQASIM
TARJAMAR
ABUBAKAR
HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne;
muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman
tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da kuma munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar babu
mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai
annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara
tabbata a gare shi, da iyalanSa da sahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.
Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin
Allah -Ya ku bayin Allah- iyakar
kiyayewa, saboda taqawar Allah
haske ne ga basirori, kuma da ita ne zukata da zuciyoyi suke samun rayuwa.
Ya ku musulmai …
Yin bauta wa Allah shi
kaxai itace hikimar samar da halitta, da basu umurni, Kuma don samar da ita aka turo dukkan
Manzanni, aka kuma saukar da littatafai, kuma da ita ne kawai waxannan halittun
za su samu xaukaka, su rabauta, su kuma ci nasara su tsira. Kuma lallai matsayin bayi a wurin Allah zai
kasance ne gwargwadon matsayinsu cikin bauta. Allah (تعالى) yana cewa:
"Lallai wanda yafi
karama daga cikinku a wurin Allah shine wanda ya fi ku aiki da taqawa" [Hujuraat: 13].
Kuma yana daga cikin FALALAR ALLAH da KARRAMAWARSA: Yadda
ya sanya ibadodi suka zama nau'i-nau'i; domin ya sanya jin daxin bayi shima ya
zama nau'i-nau'i, kuma domin ya xaukaka darajojinsu da waxannan ibadodin.
Kuma akwai wata ibada a cikin addini mai girma, wacce –a
koyaushe- take yin rigaye ga dukkan ibadar da ba ita ba, sannan ta inganta
sauran ibadodi (ILIMIN ABINDA AKE YIN
BAUTA DA SHI), Wanda ya rabauta da ita ya ci nasara, Wanda kuma yayi sakaci da
ita zai yi nadama. Allah ya yi yabo ga ma'abutanta. Kuma ya fifita wassu
halittu saboda sun mallake ta. Tana shiryar da Bawa zuwa ga UbangijinSa, kuma
tana haskaka hanyoyin rayuwarsa. Kamalar Mutum da tsirarsa a cikin rayuwarsa da
bayan mutuwarsa yana rataya ne akanta. Kuma ba a bauta wa Ubangiji da wani abu
kwatankwacinta ba; Saboda da wannan ibadar ne ake sanin Allah, kana a bauta
masa, Ariqa yin yabo a gare shi, a riqa ambatonSa, a riqa girmama shi. Kuma ake
sanin haqqoqin Mahalicci da halittu, da kuma banbance tsakanin halal da haram,
da kuma gaskiya da varna, da kuma ingantacce daga lalatacce, da mai amfani daga
mai cutarwa, da mai kyau daga mummuna. Ita ce kuma ke xebe kewa ga wanda ke
cikin kaxaici, kuma take abota da shi idan yana wurin da ya kevanta, ta riqa
tunatar da shi yayin gafala. Nemanta (ibadar ilimi) biyayya ne ga Allah, Bayar
da ita kusanci ne zuwa gare shi. Kuma (ilimi) qawa ne ga ma'abutansa, kuma
kariya ne ga sahibinta, Tana haskaka zukata da basirori, kuma tana qarfafa
kwakwale da zukata. Kuma ma'abutanta a bayan qasa kamar taurari ne ga sama (wajen
haskakawa); saboda da Su ne, a ke samun shiriya. Kuma Su ne, ado ga Halittu,
kuma mafi kyanSu, Kuma Su ne, kariya ga al'umma da kuma garkuwanta. Kuma ba don
Su ba, da alamomin addini sun shafe. Kuma da wannan ibadar al'umma take
gyaruwa, kuma ta xaukaka. Da kuma daidaituwan rayuka da samun tsarkinsu. Da
kuma shiriyar 'yan Adam da samun rabonsu. Kuma itace ke bada kariya ga al'ummai
kuma ta basu salama. Buqatuwa izuwa gare ta yafi dukkan wata buqata. Kuma idan
aka rasa ta duniya zata wargaje kuma ta lalace.
Imam Ahmad (رحمه الله) yace:
"Mutane sun
fi buqatar ilimi fiye da buqatarsu zuwa ga abinci da abin Sha; saboda Abinci da
abin Sha ana buqatarsu ne, a cikin yini sau xaya ko sau biyu. Shi kuma ilimi
ana buqatuwa zuwa gare shi a kowani lokaci".
Kuma farkon ayar da ta
sauka ta kasance tana kwaxaitarwa ne kan wannan ibadar (ta neman ilimi):
"Ka yi karatu da
sunan Ubangijinka wanda yayi halitta" [Alaq: 1].
Kuma al'ummarmu (ta
Musulmai) al'ummar ilimi ce, da rataya ga Allah.
Ibnu-Kasir (رحمه الله) yana cewa:
"Kuma farkon
abinda ya sauka na alqur'ani shi ne: Waxannan ayoyin masu karimci, masu
albarka. Kuma sune farkon rahamar da Allah ya yi ga bayi, kuma farkon ni'imar
da ya yi akansu".
Allah ya sanya wa zatinSa sunan AL-ALIMU (wato: Masani).
Kuma ya siffanta kansa da
siffar ILIMI. Sa'annan Allah ta hanyar ILIMI ne ya sanu a wurin halittunSa, Yana
cewa:
"Wanda ya sanar (da
Mutum) game da alqalami * Ya sanar Mutum abinda bai sani ba" [Alaq: 4-5].
Kuma Manzanci gabaxayansa ILIMI ne da AIKI, Kuma ilimi shine
rabinsa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Shine Wanda ya aiko
manzonSa da shiriya (wato: ILIMI) da kuma addinin gaskiya (wato: AIKI NA
KWARAI)"
[Taubah: 33].
Babu wani abu da yafi daxi ga bawa, kuma yafi kawo gyara
ga zuciyarsa fiye da son Allah, Saidai kuma babu hanyar da za a kai izuwa ga
hakan sai ta hanyar ILIMI.
Kuma ilimi shine HIKIMAR da Allah ke bada ita ga wanda ya
nufa daga cikin bayinSa; Allah (سبحانه) yana cewa:
"Yana bada hikima ga
wanda ya nufa, Kuma duk wanda aka bashi hikima to an bashi alheri mai yawa.
Babu wanda yake wa'aztuwa face ma'abuta hankula" [Baqarah: 269].
Mujahid (رحمه الله) yace hikima cikin ayar itace: "Ilimi da
fiqihu".
Allah yayi baiwa da ILIMI ga Annabi Adamu (عليه السلام) kuma ya bayyanar da falalarSa da ILIMI akan sauran
Mala'iku, "Kuma ya sanar da
Adamu sunaye dukkansu, sa'annan ya bijiro da su ga Mala'iku, Sai yace: Ku gaya
mini sunayen waxannan idan kun kasance masu gaskiya" [Baqarah: 31].
Kuma Allah (سبحانه) ya zavi wanda yaga dama daga cikin AnnabawanSa da ManzanninSa
da duk wanda ya nufa daga cikin halittunSa; Sai Mala'iku su ka yi busharar
samun Is-haqu; yaro MAI ILIMI ga matar Annabi Ibrahima.
Shima annabi Yusufu (عليه السلام) Allah yana faxa akanSa:
"Kuma lokacin da ya
kai cikan qarfinsa sai muka bashi hukunci da ilimi" [Yusuf: 22]. Kuma shi annabi Yusuf ya faxi wannan falalar
ga karan-kansa, a inda yace:
"Lallai ne Ni mai
tsarewa ne, Masani"
[Yusuf: 55].
Kuma shima annabi Musa (عليه السلام) an karrama shi da ILIMI ,Sai ya ce:
" Lokacin da ya kai
cikan qarfinsa, kuma ya daidaita sai muka bashi hukunci da ilimi" [Qasas: 14].
Kuma Allah ya faxa dangane da annabi Dawuda da Sulaimana
(عليهما السلام):
"Kowanne mun bashi
hukunci da ilimi"
[Anbiya'i: 79].
Kuma Allah ya tunatar da annabi Isah (عليه السلام) da ni'imar ILIMI, a inda yake cewa:
"Ka tuna ni'imomina
akanka, da kuma ga mahaifiyarka, a yayin da na qarfafe ka da RUHUL QUDUSI, kana
yin magana wa Mutane a cikin shimfixar jariri, da kuma kana dattijo. Da kuma a
lokacin da na sanar da kai littafi da hikima, da attaura da injila" [Ma'ida: 110].
Kuma shima Alkhadir, annabi
sukutum daga cikin ulul-azmi yayi tafiya zuwa gare shi, saboda abinda yake da
shi na fifikon ilimi; "Sai suka sami wani bawa daga bayinMu, Mun ba shi wata
rahama daga wurinMu, kuma Mun sanar da shi wani ilimi daga gunMu" [Kahf: 65].
Kuma rundunar annabi
Sulaimanu (عليه السلام); Wanda yafi ilimi
daga cikinsu shine wanda yafi qarfi a cikinsu; "Sai wanda yake a
wurinsa akwai wani ilimi daga littafi ya ce: Ni zan zo maka da shi gabanin
kyaftawar ganinka ta koma gare ka" [Naml: 40].
Kuma lallai Allah ya
qididdige ni'imominSa ga ManzonSa (صلى الله عليه وسلم) sai ya sanya ilimi, ya zama ya fi sauran ni'imomin matsayi, a
inda yace:
"Kuma Allah ya
saukar da littafi da hikima a gare ka, kuma ya sanar da kai abinda ba ka
kasance ka sani ba"
[Nisa'i: 113].
Kuma bai nemi annabinSa ya nemi qarin wani abu ba, face
ilimi, Ya ce:
"Kuma ka ce: Ya
Ubangiji ka qara mini ilimi" [Xaha: 114].
Kuma ilimi shine kayan gadon annabawa, kuma wanda suka
gaji iliminsu suna daga mafi alherin Mutane a bayansu, kuma sune mutanen da
suka fi kusanci da su; Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Malamai sune magada annabawa, kuma lallai annabawa ba su gadar da
Dinari ko Dirhami ba, kawai! Sun gadar da ilimi ne, kuma duk wanda ya same shi
to lallai ya samu cikakken rabo". Attirmiziy ya ruwaito shi.
Kuma lallai Allah ya kafa ma'abuta ilimi a matsayin masu
shaida kan Uluhiyyar Allah, a inda ya ce:
"Allah ya shaida
cewa: Lallai babu abin bautawa face shi, Kuma Mala'iku da ma'abuta ilimi sun
shaida"
[Ali-imrana: 18].
Kamar yadda Allah ya kafa ma'abuta ilimi a matsayin masu
shaida kan vacin maganar kafirai, a inda ya ce:
"Kuma waxannan da
aka baiwa ilimi da Imani suka ce: Lallai haqiqa, kun zauna a cikin abinda Allah
ya rubuta, har zuwa ranar tayarwa, to, kuma wannan itace ranar tayarwar, kuma
amma ku kun kasance ba ku sani ba" [Rum: 56].
Kuma da ilimi ne, ake jin tsoron Allah; sannan ayi masa
biyayya, "Kawai, Malamai ke tsoron Allah daga cikin bayinSa" [Faxir: 28].
Az-zuhuriy (رحمه الله) ya ce:
"Ba a bauta wa Allah da wani abu kamar ilimi ba".
Samun ilimi alheri ne, da rabauta; saboda "Duk wanda
Allah ya nufe shi da alheri ya kan fahimtar da shi a cikin addini", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi.
Zavavvu a cikin Mutane sune waxanda suka fi ilimi, Manzon
Allah (صلى الله عليه وسلم):
"Zavavvunsu
a jahiliyya sune zavavvunsu a cikin Musulunci idan suka yi fiqihu", Bukhariy da Muslim suka
ruwaito shi.
Ilimi ma'aunin fifikon aiyuka ne da darajojinsu, Kuma da
ilimin ne, aiyuka ke inganta, ko su tsarkaka. Kuma aqidar Mutum ba za ta zama
garau, ya kuma samar da ikhlasi ga UbangijinSa, tare da yin koyi da annabinSa
ba face ta hanyar ilimi, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Sai ka sani, cewa:
Babu abin bautawa da cancanta face Allah…" [Muhammadu: 19], Sai Allah ya fara
ambaton ilimi –a cikin ayar- gabanin zance da aiki.
Ilimi shine shugaba ga aiki, kuma shine yake masa jagora,
kuma duk wani aikin da babu ilimi a cikinsa to ba zai amfani ma'abucinsa ba,
hasalima cutarwa ne a gare shi. Wanda ya yi bauta wa Allah ba tare da ilimi ba
to varnarsa tafi abinda zai kawo na gyara, yawa. Kuma shirka da bidi'a basu
shigo wa Mutane ba, sai saboda qarancin ilimi da kuma nisantar ma'abutansa. Shi
kuma vata abokin tafiyar jahilci ne; wannan ya sanya Allah ya umurce mu da
neman tsarinsa daga hanyar ma'abuta vata, a cikin kowace raka'a daga cikin
raka'oin sallolinmu.
Kuma, Allah ya kore daidaito tsakanin ma'abuta ilimi da
wassunsu, saboda haka; ba za su daidaita ba saidai idan rayayye zai yi daidai
da matacce, da kuma makaho da mai gani, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ka ce: Shin
waxannan da suke da sani, suna daidaita da waxanda ba su sani?" [Zumar: 9].
Kuma da ilimi ne bayi ke rayuwa, kuma suke samun haskensu,
"Shin, kuma wanda ya kasance matacce, sa'an nan muka rayar da shi,
kuma muka sanya wani haske dominsa, yana tafiya da shi a cikin mutane, zai zama
kamar wanda misalinsa yana cikin duffai, Shi kuma ba mai fita ne daga cikinsu
ba"
[An'am: 122 ].
Lallai Kyakkyawan nitsuwa da samun fahimta a cikin addini suna daga cikin sifofin da muminai
suka kevanta da su, Sai zukatansu suka haskaka da ilimi "A'a, Shi ayoyi ne
bayyanannu a cikin qirazan waxanda aka baiwa ilimi, Kuma babu mai musun ayoyinmu face azzalumai" [Ankabut: 49].
Kuma a cikin alqur'ani mai girma akwai misalai
da aka buga, su guda arba'in da wani abu, kuma da ilimi ne, ake hankalta, kuma
ake riskar ma'anonisu, "Kuma waxancan misalan muna buga su ga
mutane, kuma babu mai hankalta da su, sai masu ilimi" [Ankabut: 43].
Kuma wassu daga cikin magabata sun kasance idan
suka bi ta kan, misalin da basu fahimce shi ba, sai suyi ta kuka, sai kuma ya
ce, "Ni ban kasance daga masu ilimi ba".
Rahama tana lulluve majalisosin ilimi da ma'abutanta,
Nitsuwa kuma tana sassauka akansu, Kuma Mala'iku suna kekkewaye su, kuma suna
fakewa a cikinsu, "Kuma lallai Mala'iku
suna sanya fuka-fukansu, saboda yarda da xalibin ilimi", Attirmiziy ya
ruwaito shi.
Ibnu-Alqayyim (رحمه الله) ya ce: "Idan
babu wata falala ga ilimi, sai kusantar da mutum zuwa ga Allah, Ubangijin
talikai, da kuma riskar halittar
Mala'iku, da yin abota da maxaukakan Mala'iku, to da hakan ya ishe shi falala
da xaukaka. To, yaya kuma, alhalin xaukakar duniya da lahira an rataya ta da
ilimi ne, kuma an sharxanta mata samuwansa".
A majalisosinsu ake samun hikima, kuma su masu ilimi ga
al'umma sune mafi alherin abin koyi. Amfanin masu ilimi yana isa zuwa ga
waninsu bayan amfanar da kansu, Wannan kuma shine dalilin da ya sa kowa yake yin
yabo a gare su, kuma yake musu addu'a, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Lallai Allah da Mala'ikunSa, da ma'abutan sammai, da qassai, har
tururuwa a cikin raminta, da kuma kifi, suna yin addu'a ga wanda yake koyawa
Mutane alkhairi",
Attirmiziy ne ya ruwaito shi.
Yin tafiya don neman ilimi yana daga cikin aiki akan
hanyar Allah (fi-sabili Allah), Abu-Addarda'i (رضي الله عنه) yana cewa:
"Duk wanda
ya ga fita da safe, ko kuma da yamma, zuwa ga ilimi baya cikin jihadi
(fiy-sabili Allah), to lallai ya samu tawaya cikin hankalinsa da ra'ayinsa".
Rigaggeniya a cikin ilimi abin godiya ne, kuma babu
hassada sai cikin abubuwa guda biyu, Mai kyautatawa a cikin iliminsa, da Mai
kyautatawa a cikin dukiyarsa, Waxanda ba su ba, kuma ba a yin (GIBXA) a
cikinsu, saboda qarancin amfaninsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Babu
hassada sai cikin abubuwa guda biyu; Mutumin da Allah ya bashi dukiya, sai kuma
ya rinjayar da shi akan rowarsa, a cikin lamarin gaskiya. Da kuma mutumin da
Allah ya bashi hikima sai yake hukunci da ita, kuma yake karantar da Mutane ita", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi.
Kuma lallai dalilai na shari'a, da abinda aka qaddara sun
nuna cewa: Lallai sakayya ta kan zama daga jinsin aiki, Don haka; Duk wanda ya
bi hanyar ilimi to ya bi hanyar aljannah, kuma lallai ilimi shine hanyar zuwa
aljannah da ta fi sauqi, kuma tafi daxi, "Duk wanda
ya bi wata hanya da yake neman wani ilimi akanta, to Allah zai sauqaqe masa
hanyar aljannah da ita", Muslim ya ruwaito shi.
Ilimin shari'a garkuwa ne daga fitintinu da musibobi,
Imam Malik (رحمه الله) ya ce:
"Lallai
wassu mutane sun nemi ibada sai suka tozarta ilimi, daga qarshe sai suka fice
da takobi ga al'ummar annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم), Saidai da sun nemi
ilimi da ya katange su, daga hakan".
Kuma don girman amfaninsa sai umurni ya zo cewa a isar da
shi, a kuma yaxa shi, a faxin duniya, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Ku isar mini koda da aya xaya", Bukhariy
ya ruwaito shi.
Allah ya yi umurnin a riqa tambayar ma'abutansa, ana
komawa zuwa gare su, "Sai ku tambayi ma'abuta ilimi idan kun kasance ba ku
sani ba"
[Nahl: 43].
Annabi (صلى
الله عليه وسلم) ya yi addu'ar hasken fiska ga ma'abuta ilimi, wanda kuma shine,
walwala da kyan fiska, da farin ciki, da buxawan qirji, a inda yake cewa:
"Allah ya
kyautata fiskan mutumin da ya ji daga gare mu, sai ya isar da shi kamar yadda ya
ji, Dayawa wanda aka isar masa yafi kiyayewa daga wanda ya ji (daga farko)", Attirmiziy ya
ruwaito shi.
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya yi addu'a ga wanda ya ke so, da cewa ya kasance daga cikin
ma'abutan ilimi, sai ya faxa akan Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما), "Ya Allah ka fahimtar da shi
addini",
Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Da ilimi ne ake xaukaka darajoji, a cikin rayuwa, da
bayan mutuwa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Allah yana xaukaka
waxanda suka yi Imani daga cikinku, da waxanda aka baiwa ilimi wassu darajoji
masu yawa"
[Mujadilah: 11].
Ibnu-Alqayyim (رحمه الله) yana cewa:
"Duk wanda
ya yi ilimi sai ya yi aiki, to irin wannan ana kiransa babba, a cikin mulkin
sammai".
Kuma amfanin ilimi yana riskan ma'abucinsa a bayan
mutuwa, matuqar ana amfana da iliminsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Idan Mutum
ya mutu aikinsa ya yanke sai guda uku, Saidai sadaka mai gudana, ko ilimin da
ake amfana da shi, ko xa nagari da yake masa addu'a", muslim ya ruwaito
shi.
Mafificin ilimi da yafi girma, wanda kuma shine abin yabo
a cikin nassoshin Alqur'ani da hadisi, shine ilimin da ya vuvvugo daga cikin
littafin Allah da Sunnah, Wanda kuma yafi qololuwa shine ilimin sanin Allah da
sunayenSa da sifofinSa, kuma wannan ilimin shine (GAYAR) da ta sanya Allah ya
yi halitta, kuma ya bada umurni, "Allah, Wanda ya halitta sammai bakwai, kuma
daga qasa kwatankwacinsu, Umarninsa yana ta sauka a tsakaninsu, domin ku SAN
lallai Allah mai iko ne akan dukkan komai, kuma lallai Allah yana kewaye da
dukkan komai da SANI"
[Xalaq: 12].
Kuma wajibi ne akan kowani Musulmi ya nemi sanin
gwargwado na farilla daga cikin ilimi, wanda kuma da shi ne zai inganta
tauhidinsa, da sallarsa da azuminsa. Kuma ya bada wani zamani daga cikin
lokacinsa don ganin samuwan hakan. Kuma kada ya riqa jin nauyin zuwa halqoqin
ilimi da majalisosinsa, saboda Annabi Musa; wanda Allah ya yi magana da shi (كليم الله), kuma yana daga cikin manzanni na
ulul-azmi, ya yi tafiya kuma ya haxu da gajiya a hanyarsa ta neman ilimi, haka
kuma ya faxi tausasan Magana wa Alkhadir, yana mai cewa:
"Shin ba zan bika,
don ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya?" [Kahf: 66].
Kuma wajibi ne akan mai nemansa ya riqa girmama
matsayinsa tare da roqon Allah akan ya bashi mai amfani daga cikinsa, da kuma
kyautata masa zato, dalazimtar taqawa, saboda kasancewarta mafi alherin abinda
zai taimake ka wajen samun ilimi. Kuma wajibi ne niyyarsa ta kasance an
tsantsance ta ga neman ganin fiskar Allah, kada kuma ya nemi ilimi don ya riqa
alfahari ga wawaye, ko don jayyaya da
malamai, da shi. Kuma lallai duk wanda ya yi aiki da abinda ya sani, sai Allah
ya gadar masa da ilimin abin da bai sani ba.
BAYAN HAKA, YA KU MUSULMAI!
Lallai Allah ya yi alqawari ga wanda ya xau hanyar neman ilimi
da cewa: Zai sauqaqe masa shi, kuma zai bashi abinda bai yi zato daga cikinsa
ba, a inda ya ce:
"Ka yi karatu, kuma
Ubangijnka shi ne Mafi karimci" [Alaq: 3].
Kuma hanyar neman ilimi tana da sauqi, kasancewarta hadda
ne ga littafin Allah Mai girma, da wani abu na hadisan annabi (صلى الله عليه وسلم), da wassu zavavvu daga cikin littatafan
ma'abuta ilimi, tare kuma da fahimtar abinda suka gabata (na ayoyi da hadisai
da littatafai). Kuma da haka ne Mutum zai samu yardar Allah, da maxaukakan
aljannonin ni'imah.
A UZU BILLAHI MINASH
SHAIXANIR RAJIM:
"Kuma baya kasancewa
ga muminai su fita zuwa yaqi gabaxaya, To don menene wata jama'a daga kowane
vangare daga gare su ba ta fita (zuwa neman ilimi ba) domin su nemi ilimi ga
fahimtar addini, kuma domin su yi gargaxi ga mutanensu idan sun koma zuwa gare
su, tsammaninsu za su yi taka-tsan-tsan" [Taubah: 122].
ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI
GIRMA. …
HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah
kan kyautatawarSa; godiya kuma tasa ce
bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya; Ina mai girmama sha'aninSa.
Kuma ina shaidawa lallai
annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi daxin salati a
gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.
Ya ku musulmai…
Malaman wannan al'ummar;
daga cikin waxanda suka yi rigaye, da waxanda suke riskansu: Ba a ambatonsu sai
da kyakkyawan ambato, saboda haqqinsu akan wannan al'ummar yana da girma, ta
fiskar sonsu da girmama su, da darajanta su, da komawa izuwa gare su, da xaukan
ilimi a gare su. Kuma lallai girmama ma'abuta ilimi yana daga girmama addini;
saboda kasancewarsu waxanda suke dauke da shi, kuma waxanda aka basu amanar
kiyaye shi. Kuma dukwanda ya karkace bai yi irin wannan mu'amalar da sub a, to
lallai ya vace; ya bar hanya. Shi kuma qin ma'abuta ilimi da yin adawa da su
tawaya ne cikin hankali, kuma karkacewa ne daga fixira. Wannan yana shelanta
masa yaqin Allah da kuma cewa zai masa uquba, Allah a cikin hadisin Alqudusiy
yana cewa:
"Wanda ya yi
adawa da waliyyina to lallai na shelanta yin yaqi da shi", Bukhariy da Muslim
suka ruwaito shi.
Sannan ku sani; Lallai
Allah ya umurce ku da yin salati da kuma sallama ga Annabinsa
Sai yace, a cikin mafi kyan
abinda aka saukar:
"Lallai Allah da
Mala'ikunSa suna yi salati ga wannan annabin, Yak u waxanda suka yi Imani, ku
yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga
annabinmu Muhammadu,
Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu,
waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci,
Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka haxa
da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
Ya Allah! Ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka
qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya –Ya
Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala, da kuma
sauran qasashen Musulmai.
Ya Allah! Ka gyara halin Musulmai a kowani wuri.
Ya Allah! Ka mayar da su izuwa ga addininka,
mayarwa mai kyau.
Ya Allah! Ka sanya qasashensu su zama garurrukan
aminci da zaman lafiya, Ya Mai qarfi, Ya Mabuwayi!
Ya Allah! Ka tabbatar da rundumarmu, Ya Allah! Ka tabbatar
da dugadugansu, Ya Allah! Ka daidaita jifansu, kuma ka azurta su da yi
don kai (ikhlasi), Ya Ma'abucin girma da Baiwa.
Ya Allah! Ka datar da shugabanmu, kuma ka sanya aikinsa ya
zama cikin yardarka. Kuma ka datar da sauran jagororin Musulmai wajen yin aiki
da littafinka, da hukunta shari'arka, Ya ma'abucin girma da yin baiwa.
"Ya UbangijinMu ka bamu mai kyau a duniya,
ka bamu mai kyau a lahira, kuma ka kare mu daga azabar Wuta" [Baqarah: 201].
Ya Allah! Lallai ne Mu muna roqonka ilimi mai
amfani da kuma aiki mai kyau.
Ya Allah! Lallai kai ne abin bautawa; Babu wani
abin bauta face kai, Kai ne Mawadaci, mu kuma mune Faqirai, Ka saukar mana da
ruwan sama kada ka sanya mu daga cikin masu xebe tsammani, Ya Allah! Ka
bamu ruwan sama!
Ya Allah! Ka bamu ruwan sama!!
Ya Allah! Ka bamu ruwan sama!!!
"Ya Ubangijinmu lallai ne Mu mun zalunci kayukanmu, idan
har baka gafarta mana, ka yi rahama a gare mu ba, za mu kasance daga cikin masu
hasara"
[A'araf: 23].
Bayin Allah!!!
"Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa
makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku
wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai
girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari,
kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke
aikatawa.
,,, ,,, ,,,
,,, ,,, ,,,