2019/02/15

NI'IMAR SAMUN BASIRA A CIKIN ADDINI نعمة البصيرة في الدين DR. Salah Albudair 26 5 1440












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 26/JUMADAL ULAH/1440H
daidai da 01/FABARAIRU/2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. SALAH DAN MUHAMMADU ALBUDAIR





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
NI'IMAR SAMUN BASIRA A CIKIN ADDINI
(نعمة البصيرة في الدين)
Shehin Malami wato: Salah bn Muhammadu Al-Albudair –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken:NI'IMAR SAMUN BASIRA A CIKIN ADDINI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO

Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya daga martabar ma'abuta BASIRA A CIKIN ADDINI, kuma ya sanya su tsayayyu ga lamarin addini, masu riko da kyawawan ayyuka.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma wanda ya yi shirka da Allah zai gamu da laifuka, kuma a dawwamar da shi a wutar Jahannama yana wulakantacce.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa, kuma ya rabauta, wanda Annabin ya kasance abin koyi a gare shi kuma jagora.
Ya Allah ka yi salati da sallama a gare shi da iyalansa da sahabbansa salati mai dawwama, da aminci wanda yake biye da aminci.

Bayan haka:
Ya ku Musulmai

Ku ji tsoron Allah, saboda mai takawa ya rabauta, kuma mabarnaci shakiyyi ya yi asara, "Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, iyakar tsoronsa, kuma kada ku mutu face kuna Musulmai" [Ali-imrana: 102].

Ya ku Musulmai
Yana cikin jigajigan ni'imomi, da gwalagwalan baiwawwaki, NI'IMAR SAMUN BASIRA A CIKIN ADDINI,
Kuma BASIRAH Ita ce Tauhidi da yin watsi da shirka, da kuma barin da'a ga kowace halitta cikin saba wa Allah Ta'alah.
Kuma BASIRAH Ita ce, Hujja, da samun yakini da tabbatuwa a cikin addini, Allah Ta'alah yana cewa: "Ka ce: Wannan ce hanyata, ina kira zuwa ga Allah akan basira, ni da wadanda suka bi ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah, ni ban kasance daga masu shirka ba" [Yusuf: 108].
Kuma BASIRAH Ita ce: Wayo (hankali).
Ana cewa:      
KUMA HASKEN IDANU YANA DUSASHEWA, ALHALIN RA'AYI YANA DA TSANANIN HASKE.
KumaBASIRAH haske ne wanda Allah yake jefa shi a cikin zuciya, sai Mutum ya rika banbance gaskiya da barna da basirarsa, da kuma alheri da sharri, da halin kirki da na banza.

Ya ku Musulmai
MAKANCEWAR BASIRAH yafi tsananin muni da girmar musiba, fiye da MAKANTAR GANI, saboda makancewar basira shine makanta ta hakika. Allah Mabuwayi da daukakaya ce:"Shin ba za su yi tafiya a cikin kasa ba, domin samun zukatan da za su rika hankalta da su, ko kunnuwan da za su yi saurare da su, domin idanun ba su makanta, amma zukata wadanda suke a cikin kiraza suke makanta" [Haj: 46].
KANA GANIN DUBBAN MASU IDO BABU SHIRIYA
KAI KA CE, A SAMAN IDANUNSU AKWAI SHAMAKI

Makaho na hakika ba shine Mutumin da baya gani da idanunsa biyu ba, saidai makaho, shine wanda ya jahilci hakkin Allah akansa,
Babban Malami a cikin al'ummar Musulmai; wato Abdullahi dan Abbas –رضي الله عنهما- ganinsa ya tafi, a karshen rayuwarsa, Sai ya yi wannan wakar:

IDAN ALLAH YA DAUKE HASKEN IDANUNA GUDA BIYU
TO, A CIKIN HARSHENA DA ZUCIYATA, AKWAI HASKE

ZUCIYATA MAI KWAZO CE, HANKALINA KUMA LAFIYA YAKE
A BAKINA KUMA, AKWAI TAKOBI (HARSHE) MAI YANKA, MAI HADISI

BASIRAH Ita ce, Alkur'ani da sunnah, Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Hakika basirori sun zo muku daga Ubangijinku, kuma wanda ya yi basira to ya yi wa kansa, wanda kuma ya makance to ya makance wa kansa" [An'am: 104].
Ma'ana: Hakika dalilai da hujjoji sun je muku wadanda Alkur'ani ya kunsa, da wadanda sunnar Annabi -صلى الله عليه وسلم- ta kunsa, kuma sune hasken da suke cikin zukatanku, mai matsayin hasken da idanunku suke gani, sai ku samu daukaka da basirorin Alkur'ani da sunnah, kuma kada ku gangara cikin ramukan zato da zunubai.
Kuma ta yaya za ku auka cikin daudar sabo, alhalin a tare da ku akwai cikakken haske na zahiri mai ban kaye, wanda shine littafin Allah da sunnar Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم-,
Sai ku nemi mafi daukakar haske daga cikinsu, a lamarin duffai kuma kada ku raina mafi karancinsu!
An ruwaito daga Abdullahi dan Amru dan Ass -رضي الله عنهما- lallai wannan ayar da take cikin Alkur'ani, wato: "Ya wannan Annabin, lallai ne mun turo ka, mai shaida, kuma mai albishir, kuma mai gargadi" [Ahzab: 45].
A cikin Attaurah kuma, "Ya kai wannan Annabin, lallai ne mun turo ka, mai shaida, kuma mai albishir, kuma mai gargadi, kuma garkuwa ga Larabawa, Kai Bawana ne kuma manzona, na sanya maka suna Mai tawakkali (dogaro ga Allah). kuma shi ba mai mummunan hali, da kaushin harshe, kuma ba mai shewa a kasuwa ba ne, kuma baya tunkude mummuna da mummuna, sai dai ya kan yi afuwa ya yafe. Kuma Allah ba zai karbi rayuwarsa ba, face ya mikar da karkataccen addini da shi, ta hanyar su ce, LA ILAHA ILLAL LAHU; sai ya bude idanu makafi da wannan kalmar, da kunnuwa masu kurumci, da zukata rufaffu", Bukariy ya ruwaito shi.
Ma'ana sai ya bude da kalmar tauhidi (ta LA ILAHA ILLAL LAHU) idanu makafi dagaganin gaskiya, ba makantar idanu ba, sai ya kore shirka kuma ya tabbatar da tauhidi. Ita kuma "الملة العوجاءkarkataccen addini" shi ne addinin kafirci. Kuma abinda ake nufi da tsayarwa da ita kalmar, shine ya fitar da ma'abutanta daga kafirci zuwa imani.
Wanda ya ji wa'azozin Allah, da ayoyin littafinSa, da hadisan AnnabinSa -صلى الله عليه وسلم- sai ya kurumtar da kunnuwansa daga gaskiya, ya kuma rufe idonunsa biyu da abin rufewan barna, to wannan shine hakikanin makaho dimautacce a cikin duffan jahilci da bata, 
Ma'abuta kafirci da fasikci da bata, kurame ne ga barin gaskiya; basu jinta, makafi ne ga barin shiriya; basu ganinta, saboda basu ji irin jin wanda ke amfana, kuma basu gani irin na mai shiryatuwa, Allah Ta'alah ya ce: "Ba su kasance suna iya ji ba, kuma ba su kasance suna gani ba" [Hud: 20].
Kuma Ubangijinmu Mabuwayi da daukaka yake fada akansu, a sha'anin lahira da kiyama: "A'a, Lallai sun kasance cikin shakka ne a lamarinta, a'a, sun dangane da ita makafi ne" [Naml: 66].
Amma Muminai to su kam wayayyu ne ma'abuta basira, kuma mumini shine mai ingantaccen nazari, mai karfin basira, mai kyakkyawan gurbi da aiki. Allah Mabuwayi da daukaka ya fada: "Kuma makaho ba zai yi daidai da mai gani ba *** da kuma duffai da haske" [Fadir: 19-20].
"Makaho ba zai yi daidai" wato wanda ya makance daga addinin Allah, da ya turo AnnabinSa Muhammadu -صلى الله عليه وسلم- da shi ba, Ba zai yi daidai "da mai gani ba" wato, wanda ya ga shiriyarsa a cikin addinin, sai ya bi annabi Muhammadu ya gaskata shi, kuma ya karbi abinda Allah ya turo annabin da shi.
Abdullahi dan Abbas -رضي الله عنهما- ya ce: Ayar "Makaho baya zama daidai..." har karshenta: Misali ne da Allah ya buga shi, akan lamarin ma'abuta da'arsa da ma'abuta saba masa.

Ana cewa:
Kowane Mutum yana da idanu guda hudu, Guda biyu sune a jikin kayinsa, domin sanin duniyarsa, Da kuma idanu biyu a cikin zuciyarsa domin lahirarsa, idan idanun kayinsa suka makance, sai idanun zuciyarsa suka zauna da basira, to makancewar idanunsa ba zai cutar da shi komai ba. Idan kuma idanunsa kayinsa suka kasance suna gani, amma sai idanun zuciyarsa suka makance, to lallai ganin idanunsa ba zai amfanar da shi da komai ba.
Kuma meye amfanin ji da gani, idan Mutum ba ya iya jin gaskiya da kunnuwansa, baya ganin shiriya da idanunsa biyu!
Meye amfanin ido a wurin Mutum
Idan haske da duhu suka daidaita a wurinsa!

Allah ya sanya ni da ku, daga cikin wadanda suke ganin gaskiya da zukatansu, sai ta zama jagora a rayuwarsu, kuma haske a gare su, a cikin kabarinsu.
Ina fadan abinda kuke ji, kuma ina gafarar Allah, sai ku nemi gafararSa, lallai shi ya kasance ga masu komawa gare shi, Mai yawan gafara ne.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah wanda a cikin tausasawarSa yake bada mafaka ga mai neman mafakarsa,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, wanda cikin ni'imarSa yake bada waraka ga wanda ya debe tsammanin waraka daga cutukansa,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonSa, wanda ya bi shi ya samu shiriya, wanda kuma ya saba masa ya bace hanya,
Allah ka yi dadin salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa, salatin da ke wanzuwa, da sallama mai ninkuwa.

Ya ku Musulmai
Yana daga sifofin Ma'abuta imani, kasancewarsu masu fadakakken zukata, masu hankali mai fahimta, suna kiyaye wa Allah umurninSa da haninSa, da alwalinSa da narkonSa, Idan aka karanta musu ayoyinsa, sai su karkata gare su, suna masu ji, masu kiyayewa, masu kula, da kunnuwan da suke jin ayoyin, da kuma zukatan da suke kiyaye su, ba su gafala daga wa'azinsa, kuma ba su girman kai kan ibadarSa, kamar yadda yasassun Mutane suke yi, masu nuna girman kai, kurame wadanda ba su jin gaskiya, makafi wadanda ba su ganin gaskiya, Ubangijinmu ya ce:   "Sune wadanda idan aka tunatar da su ayoyin Ubangijinsu, basu faduwa akansu kuramai, makafi" [Furkan: ].
 Alhasan Albasariy ya ce: "Sau nawa, Mutum yake karanta aya, sai kuma ya fadi akanta kurma kuma makaho".

Ya ku Musulmai
Lallai samun girma da daukaka, da matsayi da fifiko da mukami yana nan, cikin SAMUN BASIRA A CIKIN ADDINI
Ya Allah ka sanya mu daga cikin ma'abuta basira a cikin addini, masu yin sujjada domin kai, masu yin tasbihi da gode maka, masu kankan da kai ga umurninka, masu girmama shari'arka! Ya Ubangijin Talikai
Sai ku yi salati da sallama ga Ahmad, Mai shiryatarwa, mai ceton Mutane gaba daya
Domin idan Mutum ya masa salati guda daya, Allah Ta'alah zai masa guda goma da shi
            Ya Allah! Ka yi salati da sallama ga bawanka kuma manzonka Muhammadu,
            Kuma –Ya Allah- ka yarda da iyalansa da sahabbai, ka hada da mu tare da su, Ya Mai karimci ya Mai baiwa!
            Ya Allah! Ka daukaka Musulunci da Musulmai, kuma ka kaskantar da shirka da mushirkai, ka ruguza makiya addini,
Kuma ka game kasashen Musulmai da aminci da wadaci, kuma ka kiyaye kasar harami biyu madaukaka, daga kaidin masu kaidi, da makircin masu masu makirci, da hassadar masu hassada, da kyashin masu kyashi, Ya Ubangijin Talikai!
            Ya Allah ka datar da shugabanmu majibincin lamarinmu mai hidimar harami biyu ga abinda kake so, ka yarda da shi, kuma ka rike makyamkyamarsa da ayyukan da'a da takawa. Ya Allah ka datar da shi da na'ibinsa ga abinda akwai daukakar Musulunci a cikinsa, Ya Ubangijin talikai!
            Ya Allah ka taimaki rundunoninmu masu kiyaye iaykokinmu, Ya Allah ka kiyaye jami'an tsaronmu, kuma ka saka musu da mafi alherin sakamako, Ya Ubangijin Talikai!
            Ya Allah ka gafarta mana kuskurenmu da gangancinmu, da warginmu da kuma gaskenmu, kuma dukkan hakan akwai shi a wurinmu.
            Ya Allah lallai ne muna neman tsarinka daga mummuniyar rana, da mummunan dare, da lokaci mummuna,
            Ya Allah, lallai muna neman tsarinka daga annoba, da zuwan bala'i Ya Ubangijin Talikai
            Ya Allah ka warkar da marasa lafiyanmu, kuma ka bada lafiya wadanda aka jarrabe su daga cikinmu, ka yi rahama ga mamatanmu, ka taimake mu akan mai gaba da mu, Ya Ubangijin Talikai!
            Ya Allah! Ka sanya addu'armu ta zama abar ji, ka daga kiraye-kirayenmu, Ya Mai karramawa, Ya Mai girma, Ya Mai jin kai.


2019/01/18

Husain AlusSheikh 12 Jumadal Ula 1440 daidai 18 Janairu 2019 daga Minbarin Annabi SAW












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 12/JUMADAL ULAH/1440H
daidai da 18/JANAIRU/2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. HUSAIN DAN ABDUL'AZIZ AL-ASHEIKH





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
DA'AWA ZUWA GA KYAUTATAWA
(الدعوة إلى الإحسان)
Shehin Malami wato: Husain bn Abdul'aziz Al-Sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: KIRA ZUWA GA KYAUTATAWA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO


Bayan haka:
Ya ku Musulmai
Yana daga KYAWAWAN LAMURA MASU GIRMA A CIKIN ADDININ MUSULUNCI, TABBATATTU A CIKIN DALILANSU NA YANKAN SHAKKU: DA'AWA ZUWA GA LAMARIN KYAUTATAWA (الدعوة إلى الإحسان), da dukkan surori da misalansa mabanbanta, Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Lallai Allah, Yana umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa ma'abucin zumunta" [Nahl: 90].
Kuma Allah (سبحانه) ya ce: "Kuma ku fadi magana mai kyau zuwa ga Mutane" [Bakara: 83].
Kuma an ruwaito cikin hadisi daga Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) lalllai shi ya ce: "Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da kuma ranar karshe, to ya kyautatawa makwabcinsa, kuma wanda ya yi imani da Allah da kuma ranar karshe, to ya karrama bakonsa", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana fada, a inda yake tabbatar ko yin wasiyya kan riko da wannan dabi'a mai girma, da yin aiki da wannan ka'ida ko manufa abar karramawa: "Lallai Allah ya wajabta lamarin kyautatawa ga kowane abu" [Muslim]. Malamai masu sharhi suka ce: "abin nufi shine a kyautata wa kowane abu". Don haka, ana nufin, a game komai, kuma a mamaye komai da kyautatawa.

Ya ku taron Musulmai...
Lallai mabudin rahama shine kyautatawa, cikin bautar Mahalicci, da yin aiki cikin amfanar da BayinSa, Allah (سبحانه): "Lallai ne rahamar Allah a kusa take da masu kyautatawa" [A'araf: 56].
Kuma Musulmi, ya dace ya lazimci lamarin kyautatawa, cikin aiki da zance, cikin mu'amalolinsa, da kuma cikin rayuwarsa, don ya rabauta da alfano masu girma, da kuma fa'idodi manya, domin Ma'abucin kyautatawa yana cikin tarayya da Allah kebantacciya (المعية الخاصة), wanda take hukunta, samun kiyayewarSa, da karfafawa, da taufiki, da dacewa, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne Allah yana tare da wadanda suka yi takawa, da wadanda suke su masu kyautatawa ne" [Nahl: 128].
Kuma Allah Mabuwayi da daukaka yana cewa: "Kuma lallai Allah yana tare da masu kyautatawa" [Ankabut: 69].
Kuma lallai Mai kyautatawa zai rabautu da samun mafi girman abin nema, wanda shine, Soyayyar Allah Ta'alah ga BawanSa mai kyautatawa (محبة الله), to a wannan lokacin ne, zai rabauta ba; ba zai tabe ba har abada, a Duniya da Lahira, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ku kyautata, domin Allah yana son masu kyautatawa" [Bakara: 195].

'Yan uwa a cikin imani ...
Da lamarin kyautatawa ne, ake faranta zukata, kiraza suke yalwata, ake janyo ni'imomi, ake tunkude azabobi.
Kuma kyautatawa baya yaduwa a cikin wata al'umma, face gininta ya yi karfi, kuma an kare ta (wato al'ummar) daga aukawa cikin matsaloli, kuma sun kasance wayayyu madaukaka, wanda suka wofinta daga gurbatar rayuka da cutukan zuciya. Kuma da haka za su kubuta daga wutan fitintinu, da sabubban fadace-fadace da musibu. Domin haka ne, umurnin Ubangiji ga BayinSa ya zo akan lamarin kyautatawa cikin dukkan motsawansu, da yin rayuwa tare da shi, cikin mu'amalolinsu.
Allah Ta'alah ya ce: "Ka tunkude cuta da abinda yake mafi kyawu, sai wanda akwai kiyayya a tsakaninka da tsakaninsa ya kasance kamar Majibinci ne masoyi" [Fussilat: 34]. 
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka fada wa Bayina su rika fadar kalma wadda take mafi kyau, lallai ne Shedan yana rura gaba a tsakaninsu" [Isra'i: 53].

Ya ku taron Musulmai...
Lamarin kyautatawa ta hanyar bada kyautayi da baza hannu, lamarinsa yana kara karfi ga hakkin ma'abuta matsayi da mukamai, da dukiyoyi da wadaci, Sai ka yi kwadayin aiki da wannan Ya wanda Allah ya kyautata maka, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah ya kyautata maka" [Kasas: 77].
Ibnu-Kayyim –رحمه الله- ya ce: "Ba a janyo ni'imomin Allah, kuma a tunkude azabobinsa, da abinda yafi yin da'a a gare shi, da kyautatawa halittunSa".

'Yan uwa a cikin imani ...
Kyautatawar da shari'a ta kwadaitar akansa yana kunsar  dukkan amfani da kowane nau'i, ga kowane halitta, Mutum ne ko dabba, saidai ladansa yana banbanta, kuma falalarsa tana kara girma, gwargwadon wadanda aka gabatar da kyautatawar a gare su, da girman hakkinsu da matsayinsu, kuma mafi kololuwan wanda ya wajaba a kyautata musu sune iyaye biyu, sa'annan sai makusanta, sa'annan sai sauran halitta.
Kalmar ihsani (wato kyautatawa) tana dauke da ma'ana mai kyau, wanda take hukunta maka -Ya kai Musulmi- ka mu'amalanci waninka da dukkan aiki kyakkyawa, da kuma dadadan maganganu.
Kuma daga cikin kyautatawa akwai, kyautar da zaka gabatar, da dukiyar da zaka bayar, da wani amfanin da zaka gabatar, da kalma daddada, da lafazi mai kyau, tare da haduwa mai kyau, cikin walwala da sakin fiska, da kuma yin sallama.
An tambayi Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) wane lamarin Musulunci yafi alkhairi? Sai ya ce: "Ka ciyar da abinci, ka karanta sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma ya inganta daga gare shi (صلى الله عليه وسلم) lallai ya ce: "Murmushinka a fiskar dan'uwanka sadaka ne a gare ka".
Kyautatawa bayarwa ne wanda baya yankewa, da fadada karbar bakunci, ko agazawa na gaskiya, ko taimako a lokacin bukata.
Ya zo cikin littafin Sahihul Jami'i, daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mutumin da Allah yafi so, shine wanda yafi amfanar da Mutane, kuma mafi soyuwan ayyuka a wurin Allah Mabuwayi da daukaka shine, farin cikin da ka sanya ga Musulmi, ko ka yaye masa wani bakin ciki, ko ka biya masa wani bashi, ko ka kore masa wata yunwa, Kuma nayi tafiya da 'Dan'uwana cikin wata bukata, lallai shine yafi soyuwa a gare ni fiye da nayi ibadar i'itikafi a wannan Masallacin -yana nufin Masallacin Madina- na tsawon wata guda", har karshen hadisin.
Kuma Muslim ya ruwaito cewa, Lallai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Wanda ya kwaranye wani bakin cikin daga ababen bakin cikin Duniya ga wani Mumini, Allah zai kwaranye masa baki ciki daga bakin Lahira, Kuma wanda ya saukaka wa Mutumin da yake cikin kunci, Allah zai saukaka masa a Duniya da Lahira, Wanda ya suturce Musulmi, Allah zai suturce shi a Duniya da Lahira, Allah yana cikin taimakon Bawa matukar Bawan yana taimakon 'Dan'uwansa".

Ya ku Bayin Allah! ...
Kyautatawa shine shigar da farin ciki ga Musulmi, da bayar da mai kyau, da baiko ga wanda bashi da shi, da taimakon wanda aka zalunta, da tsamar da Mutum daga bakin ciki, da taimakon wanda ya fada bala'i, da ziyartar maras lafiya, da ciyar da mai jin yunwa, da sauran dukkan ababen da za su sanya Mutane cikin farin ciki, da walwala da jin dadi.
Allah Ta'alah ya ce: "Kuma suna ciyar da abinci, akan sonsa ga Matalauci da Maraya da Bawa * (Suna cewa:) Muna ciyar da ku ne, domin Allah, bamu nufin wani sakamako daga wurinku, kuma bamu nufin godiya" [Insan: 8].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma suna fifita wdansu akan kawunansu, koda a tare da su akwai lalura (talauci)" [Hashr: 9].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Mai tafiya cikin lamarin bazaura da miskini, kamar mai jihadi ne domin daukaka kalmar Allah, ko kuma kamar mai tsayuwan dare, mai azumin yini", Bukhariy ya ruwaito shi.
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Kuma hakika naga wani Mutum yana jujjuyawa a gidan Aljannah, sakamakon wata bishiyar da ya yanke daga kan hanya, ta kasance tana cutar da Mutane", Muslim ya ruwaito shi.

Sai ku kyautata, domin Allah ya kyautata muku, kuma ya ninninka sakamakonsa a gare ku, "Wadanda suka kyautata, suna da abu mai kyawu, da kuma kari" [Yunus: 26].

Ina fadar abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah; sai ku nemi gafararSa, lallai ne shi ya kasance ga masu  komawa gare shi, Mai yawan gafara.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,


HUDUBA TA BIYU
        Bayan haka
Ya ku Musulmai
Lamarin kyautatawa a Musulunci, baya takaituwa kawai ga Mutane, a'a lamarin a kyautata yana game wadanda basu magana; na dabbobi, saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Wata rana Wani Mutum yana tafiya akan wata hanya, kishin ruwa ya tsananta a gare shi, sai ya samu wata rijiya, sai ya shiga cikinta ya sha ruwa, sa'annan ya fita, sai ga wani kare yana lallagi yana cin kasa saboda kishi, Sai Mutumin ya ce: Lallai wannan karen kishi ya tsananta a gare shi, kwatankwacin yadda ya tsananta a gare ni! Sai ya shiga rijiyar, ya ciko huffinsa da ruwa, sa'annan ya rike shi da bakinsa, sai ya shayar da karen, Sai Allah ya gode masa, kuma ya gafarta masa, Sai suka ce:  Ya Ma'aikin Allah! Shin muna da wani lada akan dabbobi? Sai ya ce: Lallai cikin dukkan abu mai rai akwai lada", Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
Sai ku yi salati da sallama ga

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...