2018/09/13

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI 4 Muharram 1440H حسين آل الشيخ









HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 04/MUHARRAM/1440H
daidai da 14/SATUMBA/ 2018M








LIMAMI MAI HUDUBA
SHEHI HUSAINI BN ABDUL'AZIZ AL-ASSHEIKH





TARJAMAR

ABUBAKAR HAMZA ZAKARIYYA

YANA DAGA SUNAYEN ALLAH; AR-RAKIBU
(من أسمائه تعالى الرقيب)
Shehin Malami wato: Husaini bn Abdul'aziz Al-as-sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: DAGA SUNAYEN ALLAH AKWAI AR-RAKIBU, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah, Wanda wani abu a cikin kasa da kuma cikin sama basu buya a gare shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya a Lahira da Duniya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa, annabi zababbe.
Allah yay i Karin salati a gare shi da kuma iyalansa da sahabbansa ma'abuta cike alkawari da takawa.

Ya ku Bayin Allah!
Ina muku wasici da ni kaina da jin tsoron Allah Mabuwayi da daukaka, saboda takawar Allah Mabuwayi da daukaka, a cikinta akwai tsira daga sharrace-sharrace da kuma musibun Duniya da Lahira.

Yak u Bayin Allah!
Yana daga cikin SUNAYEN ALLAH Mabuwayi da daukaka, AR-RAKIBU (MAI TSARON HALITTU), Allah (تعالى) ya ce: "Lallai ne Allah ya kasance a kanku, Mai tsaro ne" [Nisa'i: 1].
Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Kuma Allah ya kasance Mai tsaro ga dukkan komai" [Ahzab: 52].
Don haka, Shi Allah (S.W.T) shine Mai tsaro, wanda ke tsinkayar duk abinda kiraza suka boye, wanda yake tsaye akan kowace rai da abinda ta aikata, kuma Mai kiyayewa wanda babu wani abu da yake buya a gare shi, Wanda ke ganin dukkan halittu, yana ganin halayensu, kuma yana kididdige ayyukansu, Ibnul-kayyim ya ce:

Kuma shine Mai ganin ababen da suke darsuwa, da wadanda sai an lura
Ta, yaya ba zai iya ganin ayyukan da aka aikata da gabbai ba?

Kuma lallai tabbatuwan wannan ma'ana mai girma a cikin zuciyar Bawa zai bashi yakinin dawwamar ilimin Allah, da tsinkayarSa ga zahirin Mutum da badininSa, sai hakan ya haifar masa da tabbataccen ilimi cewa, Allah yana tsaronsa, yana ganinsa, yana jin maganarsa, yana ganin aikinsa, yana tsinkayar aikinsa a kowane lokaci da dakika, da kuma kowane kyaftawar ido;
Saboda Bawa ya san Allah Mai tsaro ne a gare shi, hakan yin bauta ne da sunan Allah AR-RAKIBU (Mai tsaro) ALHAFIZU (Mai kiyayewa) AL-ALIMU (Mai ilimi) ALMUHIDU (Mai kewayewa) ALKHABIRU (Masani Mai labartawa Mai kididdigewa) AL-LADIFU (Masanin abinda ya buya saboda kankantarsa) ALMUHAIMINU (Mai rinjaye) saboda tsinkayarsa ga lamuran da suka buya, da abubuwan da kiraza suka boye. ASH-SHAHIDU (Mai halartar kowane abu) AS-SAMI'U (Mai jin kowane sauti), boyayyunsu da wanda ke bayyane, ALBASIRU (Mai ganin dukkan samammun ababe; kananansu da manyansu, kankanansu da wulakantattunsu), ALKARIBU (Makusanci da ilimkinSa da kowace halitta, ta hanyar saninta da tsaronta da ganinta da gamewar iliminsa);
Don haka,
Duk wanda ya fahimci MA'ANONIN WADANNAN SUNAYEN NA ALLAH KYAWAWA, KUMA YAYI BAUTA A GARE SHI DA ABINDA SUKE HUKUNTAWA, to, ibadar sanin Allah yana tsaron bayi ta gaskiya zata samu a wurinsa, wanda zata kai izuwa/ Zuciyarsa ta rika kulawa da ganin Allah a gare ta, cikin dukkan abinda ke darsuwa a gare ta, da dukkan taku.

Lallai abinda ke wajaba ga Bawa a wannan rayuwar shine/ Zuciyarsa ta kasance cikin kulawa da Allah Mai tsaro madaukakin sha'ani, har ya zama zuciyar ba za ta waiga ba, sai izuwa gare shi, ba za ta ji tsoron kowa ba face shi, sai mutum ya zama mai madawwamin kiyaye umurninSa da haninSa, mai tafiyar da himmarsa ga abubuwan da za su yardar da shi, kuma suke kusantarwa zuwa gare shi سبحانه.
Kuma duk lokacin da Bawa ya san Allah yana tsaronsa (wato, ibadar murakabah) sai hakan ya hukunta masa jin kunyar MahaliccinSa, da girmama wanda ya kage shi, kuma ya hukunta masa tsoron Allah da son Allah, da mayar da lamari ga wanda ya samar da shi, da tawakkali, da kankan-da-kai a gare shi.
Domin gyaruwan gidajen nan biyu (Duniya da Lahira) da samun babban rabo a cikinsu, duka suna rataya ne ga yakinin Bawa, kan UbangijinSa yana tsaronsa, da kirdadon samun yardarSa, da lazimtar Bawa ga bautar Allah, akan sunnar Annabi, tare da lazimtar ikhlasi a gare shi (سبحانه), irin tsarkake niyyar wanda yake da yakinin cewa idan Mutane suna tsaron zahirinsa, to shi kuma Allah yana tsaron zahirinsa ne da badininsa, Allah (سبحانه) ya ce: "Lallai ne Allah, babu wani abin da yake boyuwa a gare shi a cikin kasa, ko a cikin sama" [Ali-imrana: 5].
Kuma Allah Mabuwayin sha'ani ya ce: "Kuma ku sani lallai Allah yana sanin abinda yake cikin zukatanku, saboda haka, ku ji tsoronsa" [Bakara: 235].

Kiyayar Allah (da sanin, Allah yana tsaronka) yana hukunta Bawa ya rika yi ma kansa hisabi, yana mai amsawa ga fadinSa (سبحانه): "Ya ku wadanda suka yi imani, ku bi Allah da takawa, kuma rai ta yi dubin abinda ta gabatar wa kanta domin gobe (kiyama), kuma ku yi takawar Allah, lallai ne Allah Mai bada labari ne ga abinda kuke aikatawa" [Hashr: 18].
Ibnul-kayyim ya ce: "Sai Bawa ya yi dubin abinda ya gabatar domin ranar karshe; shin yana cikin ayyuka ne kyawawa, wadanda za su tseratar da shi, ko kuma daga cikin munanan da za su halakar da shi … manufar dai ita ce, lallai gyaruwan zuciya tana kasancewa ta hanyar yi ma kai hisabi, lalacewanta kuma, idan aka kyale zuciya, aka yi ballagaza da ita".

   Ya ku taron Musulmai!
   Lallai kiyayar Allah na hakika (da sanin cewa, Allah yana tsaron bayinsa), yana sanya Bawa kokarin ayyukan da'a, da ficewa daga dukkan abinda ke cin karo da umurnin Ubangijin kasa da sammai, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne, su, sun kasance suna yin gaggawan ayyukan alkhairi, kuma suna rokonmu akan kwadayi da fargaba, kuma sun kasance masu khushu'i ne a gare mu" [Anbiya'i: 90].

Don haka, Mumini wajibi ne ya kasance a cikin madawwamin kiyayar UbangijinSa, ta hanyar biyayyarsa da tsarkake niyya (ikhlasi) da bin umurni cikin kamala. Dagane da hane-hane kuma, ya tsawatu, ya kame, ya komo daga rakiyarsu, ya tuba; saboda ba a kiyaye dokokin Allah da haramiyarsa, kuma masu isa da wusuli ga Allah basu isa gare shi (سبحانه) face ta hanyar/ TsoronSa, da kiyayarSa, da fatanSa, da kaunarSa.
Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wanda ya ji tsoron tsayawa a gaba ga Ubangijinsa yana da Aljannoni guda biyu" [Arrahman: 46].
Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Amma wanda ya ji tsoron tsayawa a gaba ga UbangijinSa, kuma ya kange kansa daga son rai * to lallai ne Aljannah itace makoma" [Nazi'at: 40].
Ibnul-jauziy ya ce: "Allah Mabuwayi da daukaka, yafi kusa da bawanSa, fiye da jijiyar wuya -har zuwa fadinsa-: Amma zukatan jahilai, su kan ji nisa, don haka suke aukawa cikin sabo, domin da kiyayarsu ga Wanda yake halarce kuma yake ganin bayi ta tabbatu, to da sun kame hannayensu daga fadawa cikin laifuka".
An ce wa wani daga cikin Magabata, cewa: "Menene abinda zai taimake ni wajen runtse idanu? Sai ya ce: Shine saninka cewa, lallai kallon mai kallonka (wato Allah) yana rigayar kallonka ga wanda ka ke kallonta".
Kuma a irin wannan ma'anar ne Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- yake tunatar da mu, Mutanen nan guda bakwai wadanda Allah zai sanya su a karkashin inuwarsa a ranar da babu wata inuwa sai tasa, a inda ya ce: "Jinsi bakwai, Allah zai sanya su karkashin inuwarsa ranar da babu wata inuwa face tasa, Shugaba adali, da saurayin da ya rayu cikin da'ar Allah, da Mutumin da zuciyarsa take rataye da Masallatai, da Mutane biyu da suka yi soyayya domin Allah; suka hadu akan haka, suka rabu akan haka, da Mutumin da wata mata ma'abuciya matsayi da kyawu ta kira shi (domin lalata) sai ya ce, lallai ni ina tsoron Allah, da Mutumin da ya yi wata sadaka sai ya boye ta, har hannunsa na hagu bai san me damansa ta bayar ba, da Mutumin da ya ambaci Allah a kebe, sai idanunsa biyu suka zubar da hawaye", Bukhariy da Muslim.

Sanin Allah yana tsaron bayi (wato, murakaba) yana tsarkake daidaikun Mutane daga fadawa cikin laifuka da ayyukan haramun, kuma yana tsaftace zukata daga abubuwan da suke sanya su cikin dauda, kuma suke lalata su, kuma da aikata hakan ne, za a samu al'umma ta gari, wanda Allah yake nufinta da fadinSa: "Kuma Muminai maza da muminai mata, sashensu majibinta sashe ne, suna umurni da kyakkyawa, suna hani daga abin ki, kuma suna tsayar da sallah, suna bayar da zakka, kuma suna da'a ga Allah da ManzonSa, kuma wadannan lallai Allah zai musu rahama", [Tauba: 71].
Don haka, kiyayar Allah (murakabarsa) tana samar da al'umma tsarkakakku daga dauda, masu wofinta daga aikata miyagun ayyuka, wanda al'ummarsu suke sifantuwa da dukkan abu mai falala, suke yin rayuwa yarjejjiya, masu taimakakkeniya akan ayyukan biyayya da takawa, suna masu riko da igiyar Allah, masu hade kansu akan kalmar Allah, suna watsar da dukkan rabuwar kai da kungiyanci, suna watsar da kowane manhaji ko salo na wuce iyaka da guluwwi, suna yin rayuwa akan ginshikan addininsu, da abinda ya kunsa na adalci da sauki da sassauci da akidar tsakaitawa da taushi da tausasawa da soyayya, Allah Ta'alah yana fada a inda yake sifanta Muminai: "Masu tawali'u ga Muminai, masu izza akan kafirai", [Ma'ida: 54]. 
Suna rayuwa karkashin tsaron Ubangijinsu, cikin istikama da kawo gyara, amintattu, masu samar da zaman lafiya, suna bautar Ubangijinsu, kuma suna gode wa Mahaliccinsu, kuma suna hada kansu cikin soyayyar imani, da kauna irin ta musulunci, tambarinsu shine: "Lallai Muminai 'yan'uwan juna ne", [Hujurat: 10].
Kuma Annabi –sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Kada ku yi hasada, kuma kada ku yi najsh (a cikin kasuwanci), kuma kada ku yi kiyayya, kuma kada sashenku ya yi ciniki akan cinikin sashe, kuma ku kasance –Ya ku bayin Allah- 'yan'uwan juna, saboda Musulmi dan'uwan Musulmi ne, baya zaluntarsa, baya tabar da shi, baya raina shi. Takawa a nan take, sai ya yi nuni ga kirjinsa, har sau uku".
        Don haka, sai ku tsare Allah Mabuwayi da daukaka, wajen bayar da hakkokinSa (سبحانه), da kuma bayar da hakkokin bayinSa, domin ku rabauta ku samu babban rabo.

        Mu da muke magana akan: Tsare Allah Mabuwayi da daukaka, to babu makawa, dole ne sai mun mai da hankali kan wani lamari wanda dole sai mun fadakar akansa, wannan kuma shine:
Lallai wajibi na dole akan masu da'awa da maluma, shine su tsare Allah (سبحانه) cikin abinda suke fitarwa ga Mutane,
kuma dole su sani cewa lallai FATAWA lamarinta yana da hatsari, kuma wajibi ne a tsarkake Allah da ikhlasi a cikinta, da yin gaskiya ma Allah (سبحانه), da tsare shi a cikin sirri da kuma a bayyane.
        Kuma yana wajaba akan kowa, kiyayar yin fatawa ta daidaiku cikin lamuran da suke shafar dukkan al'umma, da sababbin ababen da suke da gamewa ga daukacin al'umma, wadanda baya halattan ayi gaggawa a cikinsu, ko sauri, A'a, babu makawa, sai anyi a taka-tsantsan, tare da komawar gaskiya zuwa ga Allah (سبحانه) kan ya kimsa mana ko ya mana ilhamar bin daidai.
        Kuma babu makawa, sai an lura da abubuwan da lamuran za su haifar, tare da kula da ka'idodin shari'a da manufofinta masu gamewa, da yin nazari mai zurfi akan ka'idar/ Janyo maslaha da kokarin yawaita ta, da tunkude barna, da bin hanyoyin karanta su, tare da yin bakin kokari, kai da fata, wajen hadin kan al'umma da haduwar kansu, da nisantar dukkan abinda zai yi mummunan tasiri akan hakan, koda ta bayan fage ne.
        Kuma babu makawa, a cikin wadannan fatawowin a rika komawa ga Maluma tabbatattu cikin ilimi, kari akan abinda suke da shi na sanin jiya da yau, da zurfin hangen nesa.
        Kuma babu makawa, sai an bada kulawa ga fatawowin da jama'a suke fitarwa; wato wadanda majami'an fikihu na Maluman al'umma suke fitarwa, masu zuwa bayan shawari irin na fikihu, da nazarin wurare, da ingantaccen fahimtar mas'alolin, da nazari mai zurfi ta bangarorin fikihu mai asali da dalili, a cikin sharuddan ijtihadi gaba daya.
        Kuma irin wadannan fatawowin, tabbas za su kai zuwa ra'ayin da yafi maslaha, wanda kuma da shi (da izinin Allah) halaye za su gyaru, lamura kuma su daidaitu.
        Kuma, matukar ba a kula da wadannan dokokin ba, al'umma zata auka cikin yawaitar kace-nace, wanda zai kai ga munanan akibar da Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya tsawatar akansu, a cikin fadinSa: "Har idan be bar wani Malami (na hakika) ba, (duk sun mutu), sai Mutane su riki wasu jagorori jahilai, sai a tambaye su, sai su yi fatawa ba da ilimi ba, sai su bata, su batar".

Muna rokon Allah Mabuwayi da daukaka ya tseratar da mu daga hakan
Kuma muna rokon Allah Mabuwayi da daukaka, ya datar da mu zuwa ga abinda yak e sonsa kuma ya yarda da shi, lallai ne shi akan kowane abu Mai iko ne.

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
   Godiya ta tabbata ga Allah, yabo mai yawa mai dadi mai albarka a cikinsa.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin tarayya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne manzonsa.
Ya Allah ka yi salati da sallama da albarka a gare shi, da iyalansa da kuma sahabbansa.

Bayan haka:
Ya ku Musulmai!
Ku yi takawar Allah Mabuwayi da daukaka, domin itace wasiyyar Allah ga na farko dana karshe.

Ya ku Bayin Allah … !!
Lallai ne, kuna cikin watan Allah ALMUHARRAM, wata mai tarin girma, sai ku nuna wa Allah alkhairan da suke cikin zukatanku, Muslim ya ruwaito daga Abu-hurairah, daga Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama-, ya ce: "Mafificin azumi bayan Ramadhana shine a cikin watan Allah Almuharram".

   Kuma mustahabbi ne yin azumin ranar Ashurah, wanda kuma shine yinin goma, daga watan Allah Almuharram, an ruwaito daga Abu-katadah, ya ce: "An tambayi Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- dangane da azumtar ranar Ashura, sai ya ce: Yana kankare zunubin shekarar da ta shude".
A wata riwaya kuma: "Azumtar yinin Ashura ina tsammanta wa Allah zai kankare zunuban shekarar da take gabaninsa", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma sunna ne, ayi azumin ranar tara (Tasu'ah) tare da Ashurah, saboda fadin Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- cewa: "Idan har na wanzu zuwa shekara ta gaba, to lallai zan yi azumin ranar tara", Muslim ya ruwaito.

Kuma babu abinda ya inganta daga cikin ayyuka na mustahabbi wadanda aka kebance su da ranar Ashura, banda abinda ya zo daga shari'a, wanda kuma shine muka ambata, kamar yadda Maluma ma'abuta tahkiki suka nassanta.

   Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, ……………………………
,,,          ,,,          ,,,


2018/09/07

MA'AIKATA GUDA 4,200 AKA AJIYE DOMIN SAUKAKE FICEWAR MAHAJJATA, 4200 موظف وعامل يسهلون مغادرة الحجاج









MA'AIKATA GUDA 4,200 AKA AJIYE DOMIN SAUKAKE FICEWAN MAHAJJATA,
MINTUNA 40 KUMA, SHINE LOKACIN DA ZA SU CI A KAFOFIN FICEWA DAGA KASAR
(4200 موظف وعامل يسهلون مغادرة الحجاج ...
و40 دقيقة مدة بقائهم في المنافذ)














Tarjamar
Abubakar Hamza Zakariyya


BADA KULAWAR JAGORORIN MASARAUTAR SAUDIA DA HIMMATUWARSU DA BAKIN ALLAH; MAHAJJATA
MA'AIKATA
Labara
SASHEN SADARWA
Fdakar da Mahajjata
MAUDU'I
Cikin kasar Saudia da wajenta
YADAWA
25/ Zul-hijjah/1439h
RANA
>Shugaban majalisar gudanar da ofishin da aka hade na Wukala'u
MASU MAGANA
KULAWA DA BAIWA BAKIN ALLAH; MAHAJJATA MUHIMMANCI
SAKON AIKIN

Sakamakon fadakarwar ministirin hajji da umrah … Shugaban majalisar gudanar da ofishin da aka hade na Wukala'u:
MA'AIKATA GUDA 4,200 AKA AJIYE DOMIN SAUKAKE FICEWAN MAHAJJATA,
MINTUNA 40 KUMA, SHINE LOKACIN DA ZA SU CI A KAFOFIN FICEWA DAGA KASAR

Mai girma Shugaban majalisar gudanar da ofishin da aka hade na Wukala'u; wato, Dr. Faruk bn Yahya Bukhariy ya tabbatar cewa, domin yin aiki da fadakarwar ministirin hajji da umrah, dangane da hajjin shekarar 1439H, to lallai an takaita lokacin jiran Mahajjata a dukkan kafofin ficewarsu daga kasar Saudia na tudu da ruwa da sama, daga awa biyu zuwa minti arba'in (40), kuma minti arba'in lokaci ne wanda hankali zai karba idan aka auna da tarin yawan bakin Allah; Mahajjata.

Kuma Dr. Bukhariy ya ambata cewa lallai tsarin gudanar da hajjin shekarar 1439H, wanda aka mika shi ga Mai girma ministan hajji da umrah, wato Dr.Muhammadu bn Salih Dahir Bintin, ya kwadaitar da mu ma'aikata kan ninka ayyuka, da bunkasa su, tare da gabatar da mafificin hidima ga Mahajjata dakin Allah mai alfarma, domin aiki da umurnin Mai hidimar harami biyu madaukaka; sarki Salman bn Abdul'aziz Alu-Sa'ud, da mai girma yarimansa amintacce –Allah ya kiyaye su-, na cewa: a yi amfani da dukkan damammaki, kuma a hada karfi domin hidmar bakin Allah, domin a basu damar su gabatar da ayyukansu na hajji cikin sauki da walwala, yana mai tsanantawa ko nuna muhimmancin hukuma ta daga darajar iya gabatar da ayyukanta, a karkashin kulawar ministirin hajji da umrah, domin a gabatar da mafificin abinda za a iya na hidimomi ga Mahajjata.
Kuma tsarin aiki na ofishin da aka hade na Wukala'u ya dauki yanayi mai kyau wanda ya banbanta da na shekarun da suka shude, domin samun tabbacin gabatar da jeringiyar cikakkun hidimomi na a gani, a fada, ga Bakin Mai rahama, kari akan bayar da tirenin da kosa-kosen koyar da aiki da sanar da shi ga sababbin ma'aikata, da samun tabbaci iya gabatar da hidimomin kammala hidimomin Mahajjata a lokuta guda biyu na shigowa da fita.
Kuma ya ce: "Kuma sakamakon kulawan hukumar hajji da umrah ta wizara ga akan mu'assasosin mudawwifuna, wanda kuma daga cikinsu akwai: ofishin da aka hade na Wukala'u, to wannan ofishin yana matukar kwadayin tallafawa wannan hukumar, ya karfafe su, ya agaza musu, domin su cimma manufofinsu,  su kuma sauke abinda aka dora musu, ta fiskar da zata yardar, kuma wacce ake nema".
Kuma Mai girma Shugaban majalisar gudanar da ofishin da aka hade na Wukala'u; wato, Dr. Faruk bn Yahya Bukhariy ya yi nuni cewa, lallai su a wannan ofishi, suna yin aiki kan tambari ko taken da hukumar hajji da umrah ta wizara suka runguma "Hidimar Mahajjaci daukaka ne a gare mu", kuma domin kasancewar wannan ofis na wukala'u shi ke sada Mahajjata da Mu'assasosin Mudawwafai da Adilla'u, sai wannan ofishin ya sanya babban sakonsa ya zamto shine, FARO AIKI, SADARWA, da YIN FICE A KODA-YAUSHE, wajen yin hidima da amfanar da Bakin Mai rahama, da kuma sauran bangarori masu alaka, a dukkan mashigan Saudia.

Kuma Ofishin da aka hade na Wukala'u; ya kwadaitu wajen bunkasa aikinsa don samun gamsuwar Mahajjaci a lokacin komawansa kasarsa, ta hanyar gabatar da hidindimu, wadanda suke cike da marabta da girmamawa, kuma ofishin ya tsayu da yin ayyuka masu girma domin bunkasa ayyukansa, da kawo kayan aiki da na'urori na lantarki da injinan dora kaya da jaka, domin saukake wa Mahajjata, wannan kuma saboda aikin jigilar kayan Mahajjata a wuraren shigowa da fitansu yana da muhimmanci na musamman.

Kuma wannan Ofishin (hadadde na Wukala'u) ya tafi da cigaban zamani, ta hanyar amfani da amalanke mai na'ura domin daukar kayan Mahajjata, musamma a lokacin karuwar adadin Mahajjatan da suke shigowa a lokaci ko kwanakin cunkoso, kuma yana karo adadinsa da kimanin dari da ashirin bias dari 120%.
Kamar yadda ofishin ya sanya tsare-tsare wadanda za su bayar da daman fadada aikinsa, domin ya game daukacin matakan jigilar kayan Mahajjata a lokacin zuwansu da komawansu.

Kuma Ofishin da aka hade na Wukala'u yana jibintar hidimar Mahajjata masu komawa gida, ta dukkan hanyoyin ficewa na sararin sama da tudu da teku, wanda adadinsu shine, mafita biyu na jiragen sama, wato airport na sarki Abdul'aziz na kasa-da-kasa da ke garin Jiddah, da airport na Amir Muhammadu bn Abdul'aziz a Madinatul munawwarah, da kuma mafita guda daya ta cikin teku, mai suna Maina'u Jiddah al'islamiy, da hanyoyi tara na kasa (ko mota) wadanda sune, Judaidah, Ar'ar, Ruk'iy, Halah, Ammar, Wadiy'ah, Alab, Khadra'u, Hadiysah, Bad-ha, da Jisr Malik Fahad.

Kuma gwargwadon abinda Shugaban majalisar gudanar da ofishin da aka hade na Wukala'u; ya bayyanar, lallai yawan Mutanen da suke aiki a ofishin hidimar Mahajjata, a dukkan mafitan da muka ambata, sun kai kamar mutum 4,200, wadanda suke yin ayyuka mabanbanta domin saukake lamuran Mahajjata.

WASU DAGA AYYUKAN OFISHIN DA AKA HADE NA WUKALA'U, A LOKUTAN HAJJI
-         Taryo Mahajjata a kafofin shigowa Saudia  da marabtarsu da shiryatarsu izuwa ga gurabensu da aka kebe.
-         Aikin kulawa kan walwalarsu da taimakonsu wajen biyan bukatunsu, a tsawon kwanakin kasancewarsu a Saudia.
-         Jigilar kayan Mahajjata, da samar da ma'aikatan da za su yi hakan, a dukkan mashigai (tashoshi).
-         Aiki tare da Hukumomin hajji na kasashe da kuma mu'assasosin Mudawwafai da Adilla'u, domin shigar da Mahajjatansu ta dukkan mashiga.
-         Tuntubar gamammiyar hukumar kulawa da motoci domin kawo Bus-bus da suke jigilar Mahajjata.
-         Manna rasid da ke nuna an karbi kudin da Mahajjaci ya bayar a jikin passport nasa, domin ya samu hidimar Mudawwifai da masauki da motocin jigila.
-         Kammala dukkan tsare-tsaren ficewar Mahajjata daga Saudia bayan sun gama ayyukansu.
-         Bibiyar halin da Mahajjata ke ciki, a ko-da-yaushe, da taimaka musu wajen kammala mu'amalolinsu na hukuma.
-         Sanar da ofososhin da aka tanadar kan Mahajjatan da suka bace, a kafofin shigowa Saudia da ficewa.  
-         Isar da sako ga mafi kusa daga cikin cibiyoyin lafiya, a lokacin da wani cikin Mahajjata ya kamu da wata cuta, a kafofin shigowa ko ficewa.
-          Sanar wa ressan hukumar hajji da umrah a Jidda, da mu'assar Mudawwafan da abin ya shafa, sunayen wadanda suka mutu, daga Mahajjata.


Domin Karin bayani/ OFISHIN DA AKA HADE NA WUKALA'U, HAJJIN SHEKARA TA 1439h

2018/09/06

DR. SUBAITIY نعمة تنوع العباداتHudubar Masallacin Manzon Allah SAW 27 Zulhijjah 1439H daidai da 7 Satumba 2018M












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 27/zulhijjah/1439H
daidai da 7/Satumba/ 2018M



LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ABDULBARIY BN AWWADH AL-SUBAITIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
NI'IMAR NAU'INTA IBADA
نعمة تنوع العبادات
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Awwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: NI'IMAR NAU'INTA IBADA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan abinda ke tafe, Ya ce:

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Ni'imomin Allah akan bayinSa suna da yawa, Idan Bawa ya ce zai kidanya su, sai kididdige sun ya gagare shi, sai kuma ya kasa sanin iyakansu.
Kuma Musulunci shine mafi girman ni'imomin Allah; ana haifar abin haifuwa a kan fidira ko halittar Musulunci, sai kuma ya taso cikin al'ummar da ake bautar Allah a cikinta, ake daga sauti da kiran sallah, ake karatun Alkur'ani, don haka muna yin godiya ga Allah wanda ya shiryar da mu zuwa ga wannan, bamu kasance zamu shiryatu ba, ba don Allah ya shiryar da mu ba.

Kuma yana daga manyan ababen da suke biye da ni'imar Musulunci, kuma daga cikin ressansa: NI'IMAR NAU'INTA IBADA, DA YAWAITARSU, kuma wannan ni'ima ce da ta kunshi hikimomin Ubangiji.

Hanya zuwa ga Allah guda daya ce, kuma hanyar ta game dukkan abinda Allah yake so, su kuma abubuwan da suke yardar da shi suna dayawa, kuma nau'i-nau'i ne, gwargwadon lokatai da wurare da Mutane da halaye, saboda banbancin shirye-shiryen bayi da yadda za su iya karbar abu, kuma domin a sassauta musu a saukaka musu, da abinda zai dace da ikonsu a halin nashadi ko tilasci.

Cikin nau'antuwan farillai da wajibai na ibadodi akwai jarabawa ga Mumini domin ya iya rinjayar son zuciyarsa, da sanin gaskiyarsa wajen aiki domin neman yardar Allah, saboda Bawa ya taso daga wata ibada zuwa wata, gwargwadon lokacin kowanne daga cikinsu, dalili ne da yake nuna cewa shi Bawa ne ga Allah na hakika, wanda manufarsa –a koyaushe- ita ce bibiyar yardar UbangijinSa Madaukaki.

IBADODI SUNA ZAMA NAU'I-NAU'I LURA DA MANUFOFINSU: Sai kowace ibada daga cikinsu ta tabbatar da wata hikima ta Ubangiji, da wata manufa ta tarbiya, saboda a lamarin SALLAH Allah Ta'alah yana cewa: "Lallai ne sallah tana yin hani daga alfasha da abin kyama" [Ankabut: 45].
A dangane da ZAKKAH kuma, Allah Ta'alah ya ce: "Ka karbi sadaka daga dukiyoyinsu, kana mai tsarkake su, kana mai tabbatar da kirkinsu da ita" [Taubah: 103].
A sha'anin AZUMI kuma Allah Ta'alah ya ce: "Tsammaninku za ku samu takawa", [Bakara: 183].
A dangane da lamarin HAJJI kuma sai Allah Ta'alah ya ce: "Domin su halarci abubuwan amfani a gare su, kuma su ambaci sunan Allah a cikin 'yan kwanuka sanannu" [Hajj: 28].


IBADODI SUNA ZAMA NAU'I-NAU'I LURA DA YADDA KO HANYOYIN DA AKE GUDANAR DA SU: Saboda haka, duk wanda saboda jinya ko bulaguro ko rauni ya gaza aiwatar da wata ibada, to sai ya samu ladansa cikin rangwame, ko wata ibadar ta daban, wannan kuma domin kulawa ne da yanayin Bayi, da kuma dauke kunci a gare su, da saukaka musu, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma Allah yana nufin sauki gare ku, baya nufin tsanani a gare ku" [Bakara: 185].
Musulunci ya bada kulawa ga halin fakiran da suka yi zaton cewa Mawadata sun shige su, saboda abinda suke da shi na rarar dukiyarsu da suke sadaka da ita, saboda Fakirai sun ce: "Ma'abuta dukiya sun tafi da lada! Suna yin salla kamar yadda mu ke yi, suna yin azumi kamar yadda mu ke yi, kuma suna sadaka da abinda ya zama rara daga dukiyoyinsu, Sai Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: Shin Allah bai sanya muku abinda za ku yi sadaka da shi ba ne? Lallai kowane tasbihi sadaka ne, kowane kabbara sadaka ne, kowane hamdala sadaka ne, kowane hailala sadaka ne, kuma umurni da kyakkyawa sadaka ne, hani ga mummuna sadaka ne, kuma cikin saduwar dayanku akwai lada", Muslim ya ruwaito shi.
Musulunci ya dasa mafarin sassautawa ne, domin bada kulawa ga mabanbantan halayen Bayi, saboda wata Mata daga kabilar Khas'am ta zo, sai ta ce: "Ya Ma'aikin Allah, lallai farlantawar hajji da Allah ya yi ga bayinsa ya riski Mahaifina yana tsofo mai yawan shekaru, ba zai iya zama akan abin hawa ba, Shin zan iya yin hajji a gare shi? Sai ya ce: E,", Bukhariy ya ruwaito shi.
Cikin wannan kuma, akwai halaccin wani ya na'ibci wani cikin ibadar hajji.

Kuma yana daga cikin hadisai masu girma wadanda suke nuni kan fadi da yalwar rahamar Allah da falalarSa, da yadda yake kulawa da halin da Bayinsa suke ciki, akwai fadinsa (SAW): "Idan Bawa ya yi rashin lafiya, ko ya yi tafiya, sai a rubuta masa ladan abinda ya saba aikatawa a lokacin yana mai lafiya wanda ba matafiyi ba".

Kuma Musulunci ya bada kulawa ga bayin Allah Mata, a inda suke da gazawa kan tsayuwa da wasu daga cikin ayyukan Maza, sai ya rataya lada mai yawa ga ayyukan Matan, domin girmama matsayinsu, da nuna kimar ayyukansu, saboda Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- yana cewa: "Idan Mace ta yi sallolinta biyar, kuma ta yi azumin watanta, ta kiyaye farjinta, ta yi biyayya ga mijinta, sai a ce mata: Ki shiga Aljannah , ta kowace kofar Aljannah kika so".

IBADODI SUNA ZAMA NAU'I-NAU'I LURA DA FALALOLINSU: Sai kowace ibada ta kara samar da wani shafi na alkhairi a cikin littafin ayyukan Musulmi, da wani tulin sakamako da lada mai girma, saboda a cikinsu akwai ibadun da suke kaiwa ga/ shafe zunubai da kura-kurai, An ruwaito daga Usman –Allah ya kara yarda a gare shi-, daga Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Babu wani mutum Musulmi da sallar farilla zata halarce shi, sai ya kyautata alwalarta, da khushu'inta, da ruku'inta, face ta zama kankarar abinda ya gabace ta na zunubai, matukar bai aikata kaba'ira ba, wannan kuma tsawon rayuwa ne gaba dayansa".

Daga cikinsu kuma akwai/ wanda take kasancewa sababin shiga Aljannah, saboda Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Shi kuma hajji gangariya mabruri bashi da wani sakamako face Aljannah".

Daga cikinsu kuma akwai/ wanda take tseratar da bawa Musulmi daga azabar Wuta: saboda Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Ba zai shiga wuta ba, Mutumin da ya yi kuka domin tsoron Allah Mabuwayi da daukaka, har sai tatsattsen nono ya koma cikin hantsa. Kuma kurar da aka same ta a yaki fisabililLahi ba za ta taba haduwa da hayakin Jahannama ba".

Kuma daga cikin nau'ukan falalan ayyuka akwai/ wanda Mutum Musulmi yake samun daukaka da shi zuwa ga matsayi mai girma, wanda ba a cimma sa, Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- yana cewa: "Lallai mafi soyuwanku a wurina, wanda kuma ya fi ku kusancin wurin zama tare da ni a ranar Kiyama, shine wanda ya fi ku kyawun halaye".

Kuma BANBANCIN LOKUTAN IBADA DA BANBANCIN FALALOLINSU yana ingiza Musulmi kan ya cike rayuwarsa gaba dayanta wajen shigi da fici tsakanin gonakin ibada da lambunansu, saboda lallai shi Allah SWT idan ya so Bawa sai ya aikatar da shi a cikin lokatai masu falala, da ayyuka masu fifikon daraja, idan kuma ya ki wani Bawa, sai ya aikatar da shi da munanan ayyuka, a lokuta na musamman masu falala.
Kuma babu wani lokacin bauta na musamman mai falala, face Allah a cikinsa yana da wani aiki daga cikin ayyukan biyayya a gare shi, wanda ake kusantarsa da shi. kuma a wannan lokacin Allah yana da wata busa daga rahamarsa wanda ya ke shafan wanda ya nufa da ita, da falalarSa da jinkanSa.

CIKIN NAU'INTUWAR IBADA akwai tunkude dabi'ar yin rauni da kosawa, kuma hakan ya kan baiwa rai nashadi, kuma yana sanya Musulmi ya rika jin dadi da zakin ibadar.

Akwai IBADODI NA DAIDAIKU, WADANDA SUKE DA FALALA, KUMA A CIKINSU AKWAI HIKIMOMI, domin suna karfafa alakar Bawa da Allah, kuma suna tarbiyyantar da Mutum akan tsarkake niyya (ikhlasi) da nisantar riya, kuma suna kara tsaftace ruhi, suna kawo debe kewan Bawa da Allah Ubangijinsa, Alhasan Albasariy yana cewa a lokacin da aka tambaye shi:  "Me yasa masu bauta a cikin dare, haske yake kasancewa a fiskokinsu? Sai ya ce: saboda suna kebewa da Ubangijinsu, sai ya tufatar da su daga haskensa S W T".

FISKANTAR ALLAH DA ADDU'A CIKIN KAN-KAN-DA KAI DA TSORO, YANA DAGA CIKIN MAFI KYAN IBADODI NA DAIDAIKU, Allah Ta'alah yana cewa: "Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin ranka da kankan-da kai, da tsoro", [A'araf: 205].

YIN AZUMI DON ALLAH IBADA NE NA DAIDAIKU, kuma dukkan ayyukan dan-adam nasa ne, in banda azumi, shi kam na Allah ne, saboda ya zo cikin hadisin kudusiy, Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: Dukkan ayyukan dan-adam nasa ne, mai kyau akan ninka masa da kwatankwacinsa goma, in banda azumi shi kam nawa ne, kuma nine zan yi sakayya akansa".

YIN SADAKA A BOYE IBADA CE TA DAIDAIKU, Wanda hannun Musulmi na dama take bayar da ita ba tare da hagun dinsa ya san abinda ya bayar ba, saboda ya zo cikin hadisi lallai Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: "Jinsi bakwai, Allah zai inuwantar da su ranar kiyama a karkashin inuwarsa ranar da babu wata inuwa sai tasa", Sai ya ambata daga cikinsu: "Da Mutumin da ya yi sadaka, sai ya boye ta, har hannunsa na hagun bai san abinda damansa ya aikata ba".
.
Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
Bayan haka:
 Kuma kamar yadda ibadodin da Mutum yake yin su shi kadai lamarinsu ya zama mai girma, to lallai ibadodin da Musulmai suke haduwa su taru wajen yinsu kamar salla da hajji da wasunsu suna da manufa wadanda basu boyuwa, Daga cikin hikimomin akwai: samun soyayya da kauna, da kuma Musulmai su san halin da sashensu suke ciki, da bayyanar da buwayar Musulunci, ilmantar da jahili, koyar da al'ummar Musulmai hadin kai da nisantar rabuwar kai, da taimakakkeniya da samar da daidaito, da rushe banbance-banbance na zamantakewa.

Kuma cikin KASANTUWAR IBADA NAU'I-NAU'I NE akwai fagen sukuwa mai girma na yin ayyukan kusanci, saboda akwai daga Mutane wanda ake bude masa kofar yin wani aikin banda wani, kuma kowane Mutum ana saukake masa abinda aka halicce shi domin shi, kuma Mutane suna samun fifiko a wannan kofar,

saboda a cikinsu akwai wanda neman ilimi shine abu mafi sauki a gare shi akan zuhudu da guje wa Duniya,

a cikinsu kuma akwai wanda zuhudun shine yafi sauki a gare shi,

daga cikinsu akwai wanda ibada ce tafi sauki a gare shi akan neman ilimi da zuhudu;

don haka, abinda aka shar'anta wa kowane Mutum shine ya aikata abinda zai iya na alkhairi, kamar yadda Allah Ta'alah ya ce:  "Sai ku bi Allah da takawa gwargwadon abinda kuka samu iko", [Tagabun: 16].

Kuma idan Musulmi ya san ko ya riski girman ni'imar da take cikin NAU'INTUWAR IBADA, TO ya wajaba akansa ya gode wa UbangijinSa akan hakan, kuma godiya ga kowace ni'ima shine yin amfani da ita (ta fiskar da ta dace), saboda an ruwaito daga Anas bn Malik –R.A- ya ce: Manzon Allah –sallal Lahu alaihi wa sallama- yana cewa: "Lallai Allah yana yarda ga Bawa, ya ci abinci sai ya gode masa akan haka, ko ya sha abin sha, sai ya gode masa akansa".


        Ya ku Bayin Allah… !!!
        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu.

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...