2018/05/20

YAYA 'DANKA ZAI HADDACE KUR'ANI (كيف تُحفِّظْ طفلك القرآن؟)








YAYA 'DANKA ZAI HADDACE KUR'ANI
(كيف تُحفِّظْ طفلك القرآن؟)









Tarjamar
Abubakar Hamza


Alkur'ani maganar Allah ne, kuma shine mafi alherin guzurin da Uba zai gabatar da shi ga 'Dansa, saboda kasancewarsa, hanyar SHIRIYA, da DAIDAITUWA AKAN ADDINI,
Allah Ta'alah yana cewa:
((إنّ هذا القرآن يهدي للتي هي أقومُ ويبشّر المؤمنين الذين يعملون الصالحات أنّ لهم أجرًا كبيرًا)) [الإسراء: 9].
Ma'na: "Lallai ne wannan Kur'ani yana shiryatarwa zuwa ga hanyar da tafi daidaita, kuma yana albishir ga muminai wadanda suke aikata kyawawan ayyuka, lallai suna da lada mai girma"

AKwai TUNANI DA HANYOYI wanda suke taimakon Mai tarbiyya, wajen kara kulla alakar kananan Yara da littafin Allah Ta'alah,

DAGA CIKINSU akwai: Yawaita karanta Alkur'ani a gaban idon yara, saboda bada abin koyi (kud-wa), yana daga cikin manyan hanyoyi kuma masu karfi, wajen gyaran halaye.

KARFAFA GUIWA: Ta hanyar karanto tare da sharhin ayoyi da hadisan da suke bayanin falalar karatun Alkur'ani da haddace shi.

YIN RIJISTA GA YARA A TSANGAYOYI KO MASALLATAI DA MAKARANTUN HADDAR KUR'ANI MAI GIRMA: domin wadannan makarantun suna sanya dalibi ya rika kokarin tsere tare da abokan karatunsa, kuma suna taimakonsa wajen inganta karatu da tajweed, kuma suna kara kulla alakarsa da Masallaci, da kuma zama da mutane nagari.

BAIWA YARO KISSOSHIN DA SUKA ZO A CIKIN ALKUR'ANI, ta hanya mai sauki, da jan-rai, saboda hikaya da kissa abun so ne ga Yara, kuma yana bada gudumawa wajen ratayuwar zukatunsu da Kur'ani, kamar yadda hakan ke kara bunkasa wa mutum yawan kalmomin harshe larabci da suka zo a cikin Alkur'ani.

KA BAIWA 'DANKA KYAUTAR ALKUR'ANI, saboda son mallakar abu, dabi'a ce, da za a iya amfana da ita ta fiska mai kyau, wanda hakan zai sanya Yaro ya rika son Kur'aninsa  da ya kebanta da mallakarsa, sai ya rika karanta shi, yana jujjuya shi yana bubbude shi duk lokacin da ya so.

KARFAFA GUIWAR YARO TA HANYAR BASHI KYAUTUKA, DA KUMA KARFAFA SHI KAN SHIGA MUSABAKA, domin yaro zai iya gaza yin hadda shi-kadansa, sai dai iya zama abokin gogayya mai karfi, kuma mai kyakkyawar hadda, idan lamarin ya kasance a cikin jama'a, musamman kuma idan aka tanadi wasu kyautuka.

AMFANI DA HANYOYIN ZAMANI YAYIN HADDA: saboda suna kosar da bukatun Yara na yin amfani da wadannan hanyoyi na ci-gaban zamani, wanda a mafi yawan lokaci ake aiki da su, ta wasu hanyoyin na-daban. Kuma abu ne mai kyau, ya zama suna da na'urorin rakodin din karatu, da sauraronsa, da hanyoyin sanin kura-kuran da suke cikin karatun mutum; Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce:

((مَن قرأ القرآن وتعلمه وعمِل وعمِل به: أُلبِسَ والداه يوم القيامة تاجًا مِن نورٍ، ضوؤه مثل ضوء الشمس، ويُكسى والداه حُلَّتان، لا تقوم لهما الدنيا، فيقولان: بِمَ كسينا هذا؟ فيُقال: بأخذ ولدكما القرآن)). رواه الحاكم، وحسَّنه الألباني في صحيح الترغيب والترهيب [1434].
Ma'ana: "Wanda ya karanta Alkur'ani, ya koye shi, ya yi aiki da shi: to lallai za a sanya wa iyayensa wani kambi na haske a ranar tashin Kiyama, Haskensa kamar hasken rana, kuma za a sanya wa iyayensa biyu tufafin alkebba biyu, wadanda Duniya gaba dayanta bata kai su kima ba. Sai su ce: Ta yaya aka tufatar da mu, wannan? sai ace musu: Saboda 'danku ya haddace Alkur'ani". Hakim ya fitar da shi, kuma Albani yace hadisi ne hasan, a cikin Sahih da da'if na Attargibi wat tarhibi [1434].

2018/05/19

ZIKIRIN YARO MUSULMI (أذكار الطفل المسلم)








ZIKIRIN YARO MUSULMI
(أذكار الطفل المسلم)









Tarjamar
Abubakar Hamza


Abokaina!
Me yafi zikiri (ko ambaton Allah) kyawu! Kuma me yafi tsananin bukatarmu ga zikirin Allah da yawaita shi!!
Saboda zikirin Allah Ta'alah yana da falala mai girma, da fa'idodi masu yawa, domin da zikirin ne, zuciya ke samun natsuwa, kuma ake gafarta zunuban bayi, kuma muke samun lada mai tarin yawa.
Allah Ta'alah ya ce:
"ألا بذكر الله تطمئن القلوب" [الرعد: 28].
Ma'ana: "Lallai da ambaton Allah zukata ke samun natsuwa" [Ra'ad: 28] .

Kuma Allah Ta'alah ya ce:
"والذاكرين الله كثيرًا والذاكرات أعد الله لهم مغفرة وأجرًا عظيمًا" [الأحزاب: 25].
Ma'ana: "Da masu ambaton Allah dayawa maza, da masu ambatonSa Mata, Allah ya yi tanadin wata gafara, da wani sakamako mai girma a gare su" [Ahzab: 25].

Akwai ZIKIRORI NAU'I-NAU'I, WADANDA SUKA DACE A GARE MU –Ya ku abokaina-, mu kiyaye aiwatar da su, a lokutansu,

DAGA CIKINSU akwai: Zikirin lokacin barci, Sai mu rika cewa:
BISMIKA RABBIY WADA'ATU JANBIY, WA BIKA ARFA'UH, IN AMSAKTA NAFSIY FARHAMHA, WA IN ARSALTAHA FAHFAZHA BIMA TAHFAZU BIHI IBADAKAS SALIHINA.

Da kuma a lokacin TASHI, Nan kuma, zamu rika cewa:
ALHAMDU LILLAHIL LAZIY AHYANA BA'ADA MA AMATANA, WA ILAIHIN NUSHUR.

Haka a yayin FITA DAGA GIDA, Sai mu rika cewa:
BISMILLAH, TAWAKKALTU ALAL LAHI, ALLAHUMMA INNAH NA'UZU BIKA MIN AN NAZILLA AU NUZALLA, AU NAZLIMA, AU NUZLAMA, AU NAJHALA, AU YUJHALA ALAINA.

A lokacin shiga cikin gida kuma, za mu rika cewa:
BISMILLAHI WALAJNA, WA BISMILLAHI KHARAJNA, WA ALAL LAHI; RABBINA TAWAKKALNA.

A lokacin shiga bandakai kuma, za mu rika cewa:
ALLAHUMMA INNIY A'UZU BIKA MINAL KHUBUSI WAL KHABA'ISI.

A lokacin fitanmu kuma daga, Bandakai kuma, za mu rika cewa:
GUFRAANAKA.

A lokacin shiga Masallaci kuma, za mu rika cewa;
ALLAHUMMA IFTAH LIY ABWABA RAHMATIKA.

A lokacin fita daga Masallaci kuma. Sai mu rika cewa:
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKA MIN FADLIKA.

A lokacin hawa ababen kai-komo, kamar misalin mota kuma, sai mu rika cewa:

BISMILLAHI, ALHAMDU LILLAHI,
SUBHANAL LAZIY SAKKHARA LANA HAZA, WAMA KUNNA LAHU MUKRININA, WA INNA ILA RABBINA LA MUNKALIBUNA.

Haka yin zikiri, bayan kiran sallah; sai mu rika cewa:
ALLAHUMMA RABBA HAZIHID DA'AWATIT TAAMATI, WASSALTIL KA'IMAH, AATI MUHAMMADANIL WASILATA, WAL FADILAH, WAB AS-HU, MAKAMAN MAHMUDAN ALLAZIY WA'ADTAHU.

Wannan kuma kari akan, ZIKIRORIN SAFIYA DA MARAICE.

Kuma mu sani, ya ku abokaina, Lallai idan har muka tabbatu akan wadancan zikirorin, to lallai za mu kasance cikin kulawar Allah da samun kariyarsa; don haka babu wani abu da zai cutar da mu, da izininSa Madaukaki.

YA ALLAH KA TAIMAKE MU, KAN YAWAITA AMBATONKA, DA YIN GODIYA A GARE KA, DA KYAUTATA YIN BAUTA A GARE KA.

Wassalamu alaikum wa rahmatul Lahi wa barakatuhu.


2018/05/18

KA KARANTA; SAI KA SAMU 'DAUKAKA (اقرأ واصعد)


KA KARANTA; SAI KA SAMU 'DAUKAKA
(اقرأ واصعد)









Tarjamar
Abubakar Hamza


Zai kama hannunka domin ya daukaka ka zuwa ga matsayi mafi daukaka,
Zai tsaya tare da kai domin baka kariya, a lokacin kunci da tarin bakin-ciki,
Lallai wannan shine ALKUR'ANI, saboda ya zo a cikin hadisin da, Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ke cewa:
((يقال لصاحب القرآن إذا دخل الجنة: اقرأ واصعد، فيقرأ ويصعد بكل آية درجة حتى يقرأ آخر شيء معه))، رواه ابن ماجه، وصححه الألباني.
Ma'ana: "Za a gaya wa mahaddacin Alkur'ani, idan ya shiga Aljannah: karanta, domin ka samu daukaka, sai ya karanta, yana hawa daraja daya da kowace ayar da ya karanta ta, har ya kai ga ayoyin karshe da suke tare da shi", Ibnu-Majah ya ruwaito, kuma Albaniy ya inganta shi.

Kuma a lokacin da firgicin yinin kiyama da tsananin cikinsa za su zo, to Kur'ani ba zai gudu ya kyale ma'abuta karanta shi ba; Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم– yana cewa:
((اقرؤوا القرآن فإنه يأتي يوم القيامة شفيعًا لأصحابه))، رواه مسلم [804].
Ma'ana: "Ku rika karanta Alkur'ani; domin Kur'ani zai zo a ranar kiyama, yana neman ceto ga ma'abutansa", Muslim [804].

Kuma Alkur'ani zai amfani ma'abucinsa, da kowane harafin da ke cikinsa, saboda Kur'ani zai rika amfanarka yana daukaka darajarka a Duniya da Lahira, saboda ya zo cikin hadisi; Annabi –صلى الله عليه وسلم- yana cewa:
((مَن قرأ حرفًا من كتاب الله فله به حسنة، والحسنة بعشر أمثالها))، رواه الترمذي، وصححه الألباني.
Ma'ana: "Wanda ya karanta harafi daya daga littafin Allah, to yana da ladan kyakkyawa akansa, shi kuma kyakkyawa ana ninninka shi da kwatankwacinsa", Tirmiziy ya ruwaito shi, Kuma Albaniy ya inganta shi.

Wannan ya sanya ma'abucin Alkur'ani ya shiga cikin wadanda suka cancanci a rika hassadar samun irin abinda yake wurinsu, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce:
((لا حسد إلا في اثنتين؛ رجلٍ آتاه الله القرآن، فهو يقوم به آناء الليل وآناء النهار، ورجلٍ آتاه الله مالا فهو ينفقه آناء الليل وآناء النهار))، رواه مسلم [804].
Ma'ana: "Babu hassada sai cikin abubuwa biyu; Mutumin da Allah ya bashi Alkur'ani, sai yake tsayuwa da shi, cikin dare, da cikin yini. Da kuma Mutumin da Allah ya bashi tarin dukiya; sai yak e ciyar da ita, cikin dare da cikin yini", Muslim ya ruwaito [804].

Don haka, sai ka kasance tare da wannan sahibi mai r8ike amanar abota, kuma ka yi rayuwarka cikin inuwarsa, saboda kana cikin kasuwa ce mai riba, da tijarar da babu asara a cikinta;
((إن الذين يتلون كتاب الله وأقاموا الصلاة وأنفقوا مما رزقناهم سِرًّا وعلانية يرجون تجارة لن تبور)) [فاطر: 29].
Ma'ana: "Lallai ne wadanda ke karatun littafin Allah, kuma suka tsayar da sallah, kuma suka ciyar daga abinda muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, suna fatan samun fatauci ne wand aba ya yin tasgaro", [Fadir: 29].

2018/05/17

SUNA TILAWAR KUR'ANI HAKIKANIN TILAWARSA (يتلونه حق تلاوته)








SUNA TILAWAR KUR'ANI HAKIKANIN TILAWARSA
(يتلونه حق تلاوته)









Tarjamar
Abubakar Hamza


Alkur'ani, taska ne da ya cika da falaloli da alkhairori.

Kuma domin samun fa'idodin wannan taskar babu makawa, sai an yi amfani da mabudansa.

Wanda sune, LADDUBAN TILAWARSA

DAGA CIKIN WADANNAN LADDUBAN akwai: Tsarkake niyya ga Allah Ta'alah, saboda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya bada labarin cewa lallai: daga cikin na-farko-farkon wadanda za a iza wutar sa'ira da su, a ranar Kiyama, akwai makaranci ko mahaddacin Alkur'ani, za a ce masa: Ka haddace Alkur'ani ne, domin a ce: Shi mai hadda ne. Muslim ya ruwaito.

Kuma DAGA CIKINSU: Akwai yin asiwaki da tsarkaka daga karamin kari (hadasi), da fiskantar alkibla.

Kuma a lokacin fara karatun, zai nemi tsarin Allah daga Shedan;
((فإذا قرأت القرآن فاستعذ بالله من الشيطان الرجيم)) [النحل: 98].
Ma'ana: "Kuma idan zaka karanta Alkur'ani, sai ka nemi tsarin Allah daga Shedan jefaffe daga Rahama" [Nahl: 98]. 

Kuma zai yi karatu ko tartilin Alkur'ani ne cikin tsanaki, da kokarin bayyanar da harrufansa, karatun, Abdullahi bn Abbas ya kasance yana cewa:
((لأنْ أقرأ سورة أُرتلها، أحبّ إليَّ مِن أنْ أقرأ القرآن كلَّه))، رواه أبو داود عن ابن عباس.
Ma'ana: "Na karanta sura daya cikin tsanaki da tartili, lallai shi yafi soyuwa a wurina fiye da na karanta Alkur'ani gaba dayansa". Abu-dawud ya ruwaito shi, daga Ibnu-Abbas.

Kuma Mustahabbi ne, a rika kyautata sauti, a yayin karatun Alkur'ani, saboda Annabi –صلى الله عليه وسلم- yana cewa:
((زيِّنوا القرآنَ بأصواتكم))، رواه أبو داود، وصححه الألباني.
Ma'ana: "Ku kawata Kur'ani da sautinku", Abu-dawud ya ruwaito shi, Albaniy ya inganta shi.

Idan kuma ya bi ta kan ayar Rahama, sai ya nemi Allah daga falalarSa, idan kuma ya biyo ta kan ayar azaba, sai ya nemi tsarin Allah, daga wannan azaban.

        Kuma mustahabbi ne, mutane su rika haduwa wajen karatun Alkur'ani, da kai-komo kan ma'anoninsa, da yin darasunsa, saboda fadin Annabi –صلى الله عليه وسلم-:

"ما اجتمع قوم في بيت من بيوت الله يتلون كتاب الله ويتدارسونه بينهم إلا نزلت عليهم السكينة، وغشيتهم الرحمة، وحفَّتهم الملائكة، وذكرهم الله فيمن عنده"، رواه مسلم.
Ma'ana: "Lallai Mutane ba za su hadu a cikin daki daga cikin dakunan Allah, suna tilawar Alkur'ani ba, suna yin darasunsa a tsakaninsu, face natsuwa ta sauka akansu, kuma rahama ta lullube su, kuma Mala'iku sun kewaye su, kuma sai Allah ya ambace su ga wadanda suke wurinsa", Muslim.


2018/05/15

AZUMI AKAN WA YAKE WAJABA?

AZUMI AKAN WA YAKE WAJABA?
10. Azumi yana wajaba ne, akan kowane Musulmi, balagagge, mai hankali, mazaunim gari (ba mai bulaguro ba), mai ikon zartar da shi, wanda ya kubuta da ababen da suke hana azumin, kamar haila da jinin haifuwa.
11. Ana umartar karamin yaro da yin azumi, tun daga shekaru bakwai, idan har zai iya azumin, Kuma wasu ma'abuta ilimi sun ce, za a iya dukansa idan ya kai shekaru goma; sai bai yi azumin ba, kamar lamarin sallah.
12. Idan kafiri ya musulunta, ko karamin yaro ya balaga, ko mahaukaci ya warke, a tsakiyan yinin azumi, to wajibi ne akan wadannan su kame bakunansu daga cin abinci, ga abinda ya rage na wannan yinin. Sai dai ba wajibi ba ne, su yi ramukon kwanakin da suka gabaci haka; na wannan watan.
13Mahaukaci an dauke alkalami akansa. Amma idan ya kasance yana yin haukan ne, cikin wani lokaci, sai kuma ya warke a wasu kwanakin, to wajibi ne akansa ya yi azumin kwanakin da yake da lafiyar hankali, banda kwanakin da yake cikin hauka. Kuma mai farfadiya misalin irin wannan ne cikin hukunci.
14. Wanda ya mutu, a tsakiyan watan azumi, to babu komai akansa, ko ga waliyansa, na azumtar kwanakin da suka rage a karshen wannan watan.
15. Wanda ya jahilci wajabcin azumi a cikin Ramadhana, ko ya jahilci haramcin cin abinci ga mai azumi, ko jima'i, to jamhurin malamai da suka fi yawa sun tafi akan bashi uzuri, idan kamarsa za a iya masa uzuri. Amma wanda ya kasance a tsakiyar al'ummar Musulmai, kuma zai iya yin tambaya ko ya koya, to wannan kam bashi da wani uzuri.

TABBATAN SHIGAN WATAN AZUMI


TABBATAN SHIGAN WATAN AZUMI
9. Shigan watan Ramadhana yana tabbatuwa ne, da ganin jinjirin watansa, ko ta hanyar cike watan Sha'abana kwanaki talatin (30).
Amma yin aiki da lissafe-lissafe wajen shigan wannan watan, to bidi'a ne.


BAI HALATTA A RIGAYI RAMADHANA DA AZUMTAR YINI BIYU KO DAYA A GABANINSA, DON TSANTSENI KO NEMAN FITAR DA KAI DAGA SABANI لا يجوز تقدُّم رمضان بصومٍ للاحتياط

Matashiya kan azumin watan Ramadhana (03)

لا يجوز تقدُّم رمضان بصومٍ للاحتياط

1/ عن أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه،
عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ‏:‏

"لاَ يَتَقَدَّمَنَّ أَحَدُكُمْ رَمَضَانَ بِصَوْمِ يَوْمٍ أَوْ يَوْمَيْنِ، إِلاَّ أَنْ يَكُونَ رَجُلٌ كَانَ يَصُومُ صَوْمَهُ فَلْيَصُمْ ذلِكَ الْيَوْم".

‏‏أخرجه البخاري [‏1914]‏، ومسلم [1082].

BAI HALATTA A RIGAYI RAMADHANA DA AZUMTAR YINI BIYU KO DAYA A GABANINSA, DON TSANTSENI KO NEMAN FITAR DA KAI DAGA SABANI

Fassara:
An ruwaito daga Abu-hurairah -Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce:

Annabi -sallal lahu alaihi wa sallama- ya ce:

"Kada ku rigayi Ramadana da azumtar yini daya, ko biyu, sai dai ga mutumin da ya kasance ya ke yin wani azumi, to ya azumce shi".

Bukhariy [1914] ya rawaito shi, da Muslim [1082].


2/  وعَنْ صِلَةَ بْنِ زُفَرَ رحمه الله قَالَ:

كُنَّا عِنْدَ عَمَّارِ بْنِ يَاسِرٍ فِي الْيَوْمِ الَّذِي يُشَكُّ فِيهِ، فَأُتِيَ بِشَاةٍ مَصْلِيَّةٍ، فَقَالَ: كُلُوا، فَتَنَحَّى بَعْضُ الْقَوْمِ، فَقَالَ: إِنِّي صَائِمٌ،

فَقَالَ عَمَّارٌ: «مَنْ صَامَ الْيَوْمَ الَّذِي يَشُكُّ فِيهِ النَّاسُ، فَقَدْ عَصَى أَبَا الْقَاسِمِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ".

أخرجه أبو داود [2334‏]‏، والترمذي [686]، وقال:
حديث حسن صحيح.

Fassara:
An ruwaito daga Silatu bn Zufar -Allah ya yi masa rahama-, ya ce:

Mun kasance a wurin sahabi; Ammar bn Yasir -Allah ya kara yarda a gare shi- a ranar da ake shakku a kansa, sai aka zo masa da akuyar da aka gasa namanta,
sai Ammar ya ce: ku ci,
sai wani daga cikin mutanen ya matsa can gefe,
Sai Ammar ya ce:

"Wanda ya yi azumin yinin da mutane ke kokwanto a kansa, to hakika ya saba wa Abul-kasimi -sallal lahu alaihi wa sallama".

Abu-dawud [2334] ya ruwaito shi, da Tirmiziy [686],
kuma ya ce: hadisi ne hasan ingantacce.


Tsokaci
Wadannan hadisan suna nuna;

(1) Hani kan rigayar watan Ramadhana da azumin yini daya ko biyu, da nufin idan wannan yinin ya kasance -a hakikanin lamari- daga kwanakin Ramadhana, to, shi dai ya kubuta, idan kuma baya cikinsu, to hakan ya zame masa nafila.
Da kasancewar aikata hakan saba wa Manzon Allah ne, sallal lahu alaihi wa sallama, saboda ya shar'anta mana a tashi da azumi Ramadhana idan aka ga wata, bayan dubiyar wata, da ganinsa, a lokacin da watan Sha'abana ya ke da kwanaki 29.
Idan kuma ba a gani ba, to sai ya yi hani kan azumtar yinin da ke biye, ya kuma umarci halittu da mu cike kidayar Sha'abana kwanaki 30, sa'annan sai mu tashi da azumin Ramadhana bayan hakan.

(2) Azumi a musulunci an gina shi ne akan abu na sarari, wato ganin jinjirin wata, ko cike kidayar Sha'abana kwanaki 30.

(3) Wanda ke da sauran azumin kaffara akansa, ya halatta ya cigaba da yin azumi, koda kuwa a cikin yini daya ko biyu da su ka rigayi Ramadhana ne.
Haka mutumin da ya saba azumin ranakun litinin da alamis, idan su ka kasance a ranar shakku (wato, yinin da ya zo bayan 29/Sha'abana, idan ba a ga watan Ramadhana a daren 29n ba).

Allah Shi ne mafi sani

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...