2017/11/10

Hudubar 21 Safar!439H Ta Alhuzaifiy kan GODIYAR ALLAH KAN NI'IMOMINSA








HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
صلى الله عليه وسلم
 JUMA'A, 21/SAFAR/1439H
Daidai da 10/NOWAMBA/2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ALIYU XAN ABDURRAHMAN AL-HUZAIFIY







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA





WAJABCIN GODIYA GA MAI NI'IMA (SUBHANAHU) AKAN NI'IMOMINSA
            Shehin Malami wato: Aliyu xan Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: WAJABCIN GODE WA MAI NI'IMA سبحانه AKAN NI'IMARSA, Wanda kuma ya tattauna a cikinta, akan ….
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Dukkan yabo su qara tabbata ga Allah Maxaukaki Mai girma, Masani Mai ikon qudura, Ina yabon Ubangijina, kuma ina yin godiya a gare shi, akan ni'imominSa na zahiri da na voye, kuma ina roqonSa dawwamar godiya akan ni'imominSa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokan tarayya, zuwa gare shi makoma ta ke.  
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu; bawanSa ne kuma manzonSa, kuma masoyinSa badaxi.   
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka annabi Muhammadu Mai albishir da gargaxi, kuma fitila mai haskakawa, da kuma iyalansa da sahabbansa waxanda suka yi jihadi da dukiyoyinsu da kuma rayukansu, domin taimakon addinin Allah, har duniya ta  haskaka da shiriya da kuma hasken (annabta da wahayi) .
Bayan haka:

Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa; domin ku isa ga yardarSa da aljannoninSa, sannan ku tsira daga fushinSa da uqubobinSa.

Ya ku Bayin Allah!
Lallai Ubangijinku Mabuwayi da xaukaka YANA TUNATAR DA KU DA NI'IMOMINSA, waxanda suke da gamewa, da kevantattu, domin ku yi godiya a gare shi, Allah (تعالى) yana cewa: "Ya ku Mutane, ku tuna ni'imomin Allah a kanku, Shin akwai wani Mahalicci wanda ba Allah ba, da yake azurta ku daga sama, da qasa. Babu abin bautawa da gaskiya sai shi, ta yaya ake juya ku" [Faxir: 3].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku, da alkawarinSa wanda ya alkawarta da ku, a lokacin da kuka ce: Mun ji, mun yi xa'a, kuma ku bi dokokin Allah, lallai Allah Masani ne ga abinda ke cikin qiraza" [Ma'ida: 7].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Shin ba ku gani ba ne, cewa lallai Allah ya hore muku abinda ke cikin sammai, da kuma abinda ke cikin qassai, kuma ya kwararo ni'imominSa akanku, a bayyane da kuma a voye" [Luqman: 20 ].
            Kuma Allah Mabuwayi da xaukaka ya bamu labari cewa, lallai ni'imomi gaba xayansu daga wajenSa suke, domin mu tsayu wajen sauke haqqinSa (تبارك وتعالى) na bauta, da godiya. Sannan mu bayyanar da kwaxayinmu zuwa gare shi na neman qarin ni'imomi, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma duk abinda ke tattare da ku, na ni'imomi, to daga Allah ne" [Nahl:  53].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Abinda ya same ka na kyakkyawa daga Allah ne, Wanda kuma ya same ka mummuna to daga ranka ya ke" [Nisa'i: 79]. Saboda su kyawawan ababe, su kan samu mutum da falalar Allah, da rahamarSa, ta kowace fiska. Munana kuma, su kan kasance ne da sababin mutum, Allah kuma shi yake rubuta su, kuma ya qaddara su, Kuma Ubangiji Mabuwayi da xaukaka baya zaluntar wani, ko daidai da kwayar zarra, Allah Ta'alah ya ce: "Saidai Allah shi ne ma'abocin falala ga talikai" [Ali-imrana].

Mutane, kuma sun san dayawa daga cikin ni'imomi, saidai sun jahilci mafi yawan ni'imomi; domin sau dayawa akwai ni'imomin da Allah ya kwararo maka –ya kai wannan mutum- ya kuma jiyar da kai daxi da su, amma kai baka ma ji su ba. Kuma nawa yawan, sharri da musibun da Allah ya ke tunkuxe su daga barinka, alhalin kai baka sani ba, Allah (تعالى) yana cewa, a dangane da kiyaye Mutum: "Yana da Mala'iku masu canjin aiki, a gaba gare shi, da bayansa suna kiyaye mutum, da umarnin Allah" [Ra'ad: 11].
Kuma Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ya hore muku abinda ke cikin sammai da abinda ke cikin qassai, gaba xayansu daga wurinSa, lallai ne cikin haka akwai ayoyi ga mutanen da suke yin tunani" [Jasiya: 13].

            Kuma dayawa daga gavvan jikin Mutum suna yin aikin  da aka samar da su, don aikatawa, domin amfanin jikin da tsayawar rayuwarsa, kuma suna yin aikinsu ba tare da mutum ya yi nufi, ko yayi wani abu a cikin hakan ba, Allah (تعالى) ya ce: "Da kuma cikin rayukanku, Shin ba za ku gani ba" [Zariyaat: 21].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Kuma idan za ku qidaya ni'imomin Allah ba za ku qididdige su ba, Lallai mutum mai yawan zalunci ne mai yawan butulci" [Ibrahim: 34]. Wanda ba zai iya qididdige ni'imomi ba, to lallai ya jahilci mafi yawansu.

            Kuma Allah (تعالى) ya yi baiwa da ni'imomi domin a sanya su cikin xa'a wa Allah, da yin bauta a gare shi, da qoqarin raya qasa da kawo gyara a cikinta, Allah (تعالى) ya ce: "Kamar haka, ya ke cike ni'imominSa akanku, tsammaninku za ku miqa wuya" [Nahl: 81].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Allah shine ya fitar da ku daga cikin uwayenku; alhalin ba ku san komai ba, sai ya sanya muku ji da gani da hankula, tsammaninku za ku yi godiya" [Nahl: 78].

            SHI KUMA GODIYA KAN NI'IMOMI YA KAN KASANCE NE DA HAXUWAR WASU LAMURA;
Da son wanda ya yi ni'imomin Mabuwayi da xaukaka, saboda waxannan ni'imomin da ya bayar.
Da kuma qanqan da kai ga Allah (سبحانه), akan abinda ya kwararo na ni'imomi,
Tare da samun yaqini a cikin zuciya cewa dukkan wata ni'ima da Allah ya yi falala da ita, ko ya kyautata ga bawa da ita, ta kowace fiska shi bawan bashi da cancantarta ga Allah,
Da yin yabo ga Ubangiji, da harshe, akan waxannan ni'imomin,
Da karvar waxannan ni'imomin, da nuna halin buqata da talauci zuwa ga Allah
Da girmama ni'imar,
Da kuma amfani da ni'imomin cikin abinda Allah (تبارك وتعالى) yake so; saboda duk wanda yayi amfani da ni'imomin Allah cikin abinda Allah yake so, kuma ya yarda, sannan ya sanya ni'imomin suka zama taimako a gar shi wajen tsayar da addini, a karan kansa, kuma ya bayar da wajibai na farillar da suke kansa, ta hanyar kyautata wa halittu, da waxannan ni'imomin = to, wanda ya aikata haka, ya yi godiya wa Allah akan ni'imomi.
Wanda kuma yayi amfani da ni'imomin Allah cikin abinda Allah yake qi, ko ya yi hani, ko kuma ya qi  bada haqqoqi na wajibai da suke kansa, a cikin ni'imomin, to lallai ya butulce wa ni'imar.
Sannan kada ni'imomin su sanya bawa girman kai, sai ruxu da ruxi su shige shi, Shexan kuma yayi masa waswasin cewa: Wai yafi waninsa, saboda waxannan ni'imomin, kuma wai ba a kevance shi da waxannan ni'imomin ba, sai saboda fifikon da yake da shi akan wanda ba shi ba.
            Kuma mutum ya sani cewa, lallai Allah yana jarrabar mutane da abubuwan alkhairi, ko sharri, domin ya san Masu godiya da haquri.
Kuma shi imani rabinsa godiya ne, rabinsa kuma haquri, Allah (تعالى) ya ce: "Shin baka ga cewa lallai jirgin ruwa yana gudana a cikin teku da ni'imar Allah, domin ya nuna muku, ayoyinSa ba, lallai cikin haka akwai abin lura ga kowani mai yawan haquri, da yawan godiya" [Luqman: 31].
A'isha (رضي الله عنه) ta rubuta wa Mu'awuya (رضي الله عنه), inda ta ce: "Lallai mafi qarancin abinda ke wajaba na haqqin mai ni'ima, akan wanda yayi masa ni'imar shine kada ya sanya ni'imar da yayi masa ta zama hanyar sava masa".

            Kuma bayan matakin GODIYA GA NI'IMOMI akwai matakin YIN GODIYA (wa Allah) KAN MUSIBU DA SHARRACE-SHARRACE, da yin YABO WA ALLAH AKAN ABABEN QI waxanda suke samun musulmi, waxanda kuma bashi da ikon tunkuxe su.
Ma'abuta wannan matsayin sune farkon waxanda za a kira su domin shiga Aljanna, saboda kasancewar suna godiya (wa Allah) a cikin kowani yanayi.

            Kuma haqiqa Allah Ubangijinmu Mabuwayi da xaukkka ya umarce mu da yin godiya a gare shi, a inda ya ce: "Ku ambace ni sai in ambace ku, kuma ku yi godiya a gare ni, kada ku yi min butulci" [Baqara: 152].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Saidai yana son ya tsarkake ku, kuma ya cika ni'imarSa akanku tsammaninku za ku yi godiya" [Ma'ida: 6].
Kuma Allah ya ce: "Sai ku yi godiya ga ni'imar Allah, idan kun kasance a shi kaxai kuke yin bauta" [Nahl: 114].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Ku so Allah saboda abinda yake ciyar da ku da shi na ni'imominSa", Attirmiziy ya ruwaito shi, kuma ya inganta shi, daga hadisin Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما).

            Mafi girman godiya shine IMANI DA UBANGIJIN TALIKAI, Kuma shine godewa ni'imar turo manzancin annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم) wanda Allah ya turo shi da wannan manzancin, domin ya zama jin qai ga mutane.
            Bayan haka kuma, Sai gode wa (Allah) akan kowace ni'ima, a keve, har kuma mafi qarancin ni'ima, tare da cewa babu qarami a cikin ni'imomin Allah.

            Kuma mafi girma daga cikin BUTULCE WA NI'IMOMI shine: KAFIRCE WA QUR'ANI DA SUNNA, Kuma godiya ga wata ni'ima ba zai yi amfani ga mutum ba, matuqar ya kafirce wa Musulunci, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma duk wanda ya kafirce wa Imani, to lallai aikinsa ya ruguje, kuma shi a lahira yana daga cikin masu hasara" [Ma'ida: 5].

            Kuma lallai haqiqa Allah ya yi alqawari ga masu yin godiya, da cewar zai dawwamar musu da ni'imominsa, kuma zai musu qari, kuma ya sanya musu albarka, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma Ubangijinku ya yi shela cewa, idan kuka gode, to lallai zan yi qari a gare ku, kuma idan kuka butulce lallai azabata mai tsanani ce" [Ibrahim: 7].
            Masu yin godiya sune masu rabauta, da alkhairin duniya da lahira, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma Allah zai yi sakayya wa masu godiya" [Ali-imrana: 144].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Wanda ya nufi samun ladan duniya za mu bashi daga gare ta, Wanda kuma ya nufi samun ladan lahira za mu bashi daga gare ta, kuma za mu yi sakayya ga masu godiya" [Ali-imran: 145].

            Kuma masu godiya sune masu tsira daga uqubobin duniya da sharrace-sharracenta, da kuma baqin cikin lahira, Allah (تعالى) ya ce, dangane da Mutanen annabi Lux (عليه الصلام): "Lallai ne mu mun tura musu iska mai tsanani mai turvaya, in banda iyalan annabi Lux, waxanda muka tseratar da su, a lokacin sahur * Ni'ima ce daga wurinmu, kamar haka make yin sakayya ga wanda ya yi godiya" [Qamar: 34-35].

            Shi godiya matsayi ne na annabawa da manzanni, da kuma bayin Allah muminai, Allah (تعالى) yana cewa dangane da annabi Nuh (عليه الصلاة والسلام): "Lallai ne shi ya kasance bawa mai yawan godiya" [Isra'i: 3].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Lallai ne annabi Ibrahima ya kasance jagora, mai biyayya ga Allah, miqaqqe daga karkata, kuma be kasance daga cikin mushirkai ba * Mai godiya ne ga ni'imominSa, ya zave shi, kuma ya shiryar da shi zuwa ga hanya madaidaiciya" [Nahl: 120-121].
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ya Musa lallai ne ni na zave ka akan mutane, da sakwannina, da kuma maganata, sai ka riqi abinda na baka, kuma ka kasance daga cikin masu godiya" [A'araf: 144].
An ruwaito daga A'isha (رضي الله عنها) ta ce: "Annabi ya kasance yana yin tsayuwar dare (salla), har qafofinsa su kukkumbura, Sai ta ce: Ya Ma'aikin Allah: Kana yin sallar qiyamulLaili har qafofinka suna kumbura? alhalin Allah ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubanka, da abinda ya jinkirta, Sai ya ce: Shin ba zan kasance bawa mai yawan godiya ba", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.

            Kuma masu godiya sune ma'abuta samun ni'imomin Allah, saboda Allah ya kan kevance su da abinda baya bayar da shi ga waninsu, Allah (تعالى) yana cewa: "Kamar haka, muka jarrabi sashensu da sashe, domin su ce: Shin waxannan ne, Allah yayi musu baiwa daga cikinmu? Shin ba Allah ne mafi sanin masu godiya ba?" [An'am: 53].

            Kuma masu godiya sune kevantattun Allah, daga bayinSa, wannan ya sanya suka zamo 'yan kaxan, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma 'yan kaxan ne daga cikin bayina su ke yawaita godiya" [Saba'i: 13].

            Ya kai Mai godiya, ka dawwama akan ibadar godiya, da tsayuwa akan addini, domin duk wanda ya cika alkawari wa Allah to Allah zai cika masa, Allah (تعالى) yana cewa: "Kuma ku cika alqawarina zan cika alqawarinku, kuma nine kaxai za ku ji tsoro" [Baqara: 40].
            Kuma kada ka bari Shexan ya zamar da qafarka, ya kai Mai godiya! Sai ka kasa kaiwa ga godiya ta wajibi, ko ka canza godiyar zuwa ga kafircewa ni'ima, Sai halaye su caccanza maka; wato daga hali mai kyau zuwa ga mummuna mai sharri, Allah (تعالى) ya ce: "Ka tambayi banu-isra'ila, sau dayawa mun basu aya bayyananniya, kuma duk wanda ya canza ni'imar Allah bayan ta zo masa, to lallai Allah Mai tsananin uquba ne" [Baqara: 211]. Wato, duk wanda bai yi godiya ga ni'imomi ba, sai Allah ya yi masa uqubar horarwa. Wanda kuma ya kasance a halin dawwamar da godiya, sai Allah ya yi masa qari.
Wanda kuma ya juya daga aikata savo, zuwa ga abinda ke yardar da Allah, to sai Allah ya juyar masa da ababen da  yake qinsu ko suke munana masa, zuwa ga ababen da bawa yake so.
Wanda kuma ya dace da Allah cikin ayyukan kusantarSa (na xa'a), da nisantar savo, to sai Allah ya jivinci lamuransa gaba xayansu, An ruwaito daga Anas (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), daga Jibrilu, daga UbangijinSa Mabuwayi da xaukaka, Ya ce:  "Wanda ya walaqanta mini waliyyi, to lallai ne yayi fito-na-fito da ni, na yaqi. Kuma ban yi taraddadin aikata wani aikin da nine mai aikata shi ba, kamar taraddadina wajen karvar rayin bawana mumini da ke qin mutuwa, ni kuma nake qin munanta masa, tare da cewa bashi da makawa daga mutuwa. Kuma lallai akwai daga bayina muminai, wanda ke nufan wata qofa ta bauta, amma sai in toshe masa ita, saboda kar jiji-da-kai ko ruxuwa ya shige shi, sai hakan ya lalata shi. Kuma bawana bai kusance ni da wata ibada ba, fiye da aikata abinda na farlanta akansa, kuma bawana ba zai gushe yana yin nafila ba, face na so shi, Duk kuma wanda na so shi, to sai in zama jinsa da ganinsa da hannunsa, kuma mai qarfafa a gare shi, ta yadda idan ya roqe ni sai in amsa masa, idan kuma ya tambaye ni, sai in bashi, idan kuma ya nemi nasihata sai nayi masa nasiha.
Kuma akwai daga cikin bayina waxanda ba abinda zai gyara imaninsu sai wadaci, kuma da zan mayar da shi faqiri da hakan ya lalata shi.
Kuma akwai daga cikin bayina wanda babu abinda zai gyara imaninsa idan ba talauci ba, da kuma zan yalwata masa sai hakan ya lalata shi.
Akwai daga bayina wanda babu abinda zai gyara imaninsa sai cutuka, da kuma zan bashi lafiya to da hakan ya lalata shi.
Kuma akwai daga bayina wanda babu abinda zai gyara imaninsa sai lafiya, da kuma zan hukunta masa cuta, to da hakan ya lalata shi.
Lallai ne ni ina jujjuya lamarin bayina da sanina ga abinda ke cikin zukatansu, lallai ne ni Masani ne Mai bada labari", Axxabaraniy ya ruwaito shi. Kuma sashen laffuzan hadisin suna da abinda ke musu qarfafarsu daga cikin hadisan Sahihul Bukhariy.
            Sai ka kasance, Ya kai bawan Allah, tare da masu godiya wa Allah, waxanda Allahn ke kwarara musu alkhairi kwararawa.
            Ibnul Qayyim (رحمه الله) ya ambaci wata magana da ake danganta ta ga Allah, cewa Allah ya ce: "Ma'abuta ambatona sune ma'abuta zama da ni. Su kuma ma'abuta gode mini sune ma'abuta samun qarina, Su kuma ma'abuta xa'a a gare ni sune ma'abuta samun karramawata, Su kuma ma'abuta sava mini su kuma ba zan sanya su xebe tsammani daga rahamata ba; idan suka tuba; to nine masoyinsu, idan kuma basu tuba ba to nine likitansu; zan jarrabe su da musibobi domin in tsarkake su daga aibobi ".

            Kuma lallai ne Allah ya umarce ka, da kasancewa tare da waxannan bayin masu rabauta, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma ga Allah shi kaxai za ka yi bauta, kuma ka kasance daga masu godiya" [Zumar: 66].

            Kuma haqiqa Allah (تعالى) ya ambaci wasu ni'imomi kevantattu a cikin littafinSa saboda amfaninsu da tarin albarkarsu, ga al'umma, har zuwa tashin qiyama.
            Kuma yana daga cikin wasiyyoyin Annabinmu (صلى الله عليه وسلم) masu amfani, faxinSa: "Ya kai Mu'azu! Lallai ne ni ina sonka, sai ka riqa faxa bayan kowace sallah:
 (اللهم أعني على ذكرك، وشكرك، وحسن عبادتك)
Ma'ana: Ya Allah! Ka taimake ni akan ambatonka, da yin godiya a gare ka, da kyautata bauta a gare ka", Abu-Dawud ya ruwaito shi da Annasa'iy.
Kuma wannan wasiyar ta dace, da xaukacin al'ummah.

            Kalmar  Alhamdu, da Shukru, ma'anar sashensu yana shigar wa sashe, tare da cewa kowannensu ya kevanta da wasu ma'anoni masu zurfi.

            Kuma lallai Allah Ta'alah –a kowane lokaci- yana da ni'imomi kevantattu, da ni'imomi gamammu (ga xaukacin musulmai). Waxanda suke wajabta musu yin godiya, da tsayuwa akan addini.

            Kamar yadda Ubangiji Mabuwayi da xaukaka, yake da wasu manyan ni'imomin ga wannan qasa (masarautar larabawa ta Saudia), wanda Ubangiji ya yi mana baiwa da su.
Kuma yana daga manyan ni'imomi da baiwawwaki: HAXUWAR KAN MUTANE, Saboda haxin kai, tsirkiya ne wanda haxe maslahohin addini dana duniya a qarqashinsa, sai a iya raya garurruka, kuma da ita ne sharrin ma'abuta sharri ke tunkuxa, addini ya qarfafa da shi, kuma maqiya su takuru, sai kalma ta xaukaka, al'umma ta qara samun girma, a iya umarni da kyakkyawa, ayi hani da mummuna, a riqe hannun azzalumi, a kiyaye ababe masu alfarma, a hana zubar da jini ko lalata kayayyakin da aka mallaka, kuma iyakoki su samu buwaya da tsaro, lamura kuma su gyaru.
Kuma idan aka rasa haxin kai, varna ce mai tarin yawa take shigowa al'umma, ta vangaren addini, da kuma ta vangaren duniya, wanda xaixaikun mutane ko al'ummar ba za su iya gyara su ba.
Tsarki ya tabbata, ga Mai hikima, Masani, wanda ke cewa: "Kuma ku yi riqo da igiyar Allah gaba xaya, kuma kada ku rarraba, kuma ku tuna ni'imar Allah akanku, a lokacin da kuka kasance maqiyan juna, sai ya daidata tsakanin zukatanku, sai kuka wayi gari da ni'imarSa; 'yan'uwa, kuma kun kasance a bakin gavar ramin wuta, sai ya tsamar da ku daga gare ta, kamar haka, Allah ke bayyana muku ayoyinSa, tsammaninku za ku shiryu" [Ali-imrana: 103].
Kuma yana daga cikin baiwawwakin Allah da ni'imarSa ga wannan qasa: YADDA SHARI'AR ALLAH TA MAMAYE WANNAN QASA, Saboda kotunan shari'a a masarautar larabawa ta Saudiyyah, kundin da suke xaukar hukunce-hukuncensu (konsutushin) shine littafin Allah Ta'alah, da kuma sunnar ManzonSa –صلى الله عليه وسلم-.
Kuma shari'ar musulunci itace adalci, kuma shari'a matsaikaciya, wanda take tsayar da adalci a tsakanin mutane, kuma take kiyaye haqqoqin mutum, gaba xayansu ba tare da ta tauye wani abu ba; Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce: Lallai ni Ubangijina ya shiryar da ni zuwa tafarki madaidaici; addini miqaqqe, mai aqidar Ibrahima, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga cikin mushirkai ba" [An'am: 161].
Kuma al'ummar musulmai addininta, tsakaitawa ne a tsakanin al'ummai; babu wuce iyaka, kuma babu sakaci, kuma babu tozarta wajibai ko qarfin halin aikata ababen haramun, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma haka ne, mu ka sanya ku al'umma matsakaiciya, domin ku kasance masu bayar da shada akan mutane, kuma Manzo ya kasance mai shaida akanku" [Baqara: 143].
Kuma abinda ke aukuwa na sakaci daga musulmi, cikin haqqin Allah Ta'alah, ko cikin haqqoqin 'yan'uwansa halittu, to ba shari'ar musulunci ta gaskiya ne sababin wannan ba, sababin hakan kawai shine daga kayukan musulmai, sakamakon jahilci, ko rinjayen son zuciya, Kuma dukkan wanda ya tuba, Allah zai karvi tubanSa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Dukkan 'yan Adam masu kuskure ne, kuma mafi alherin masu kuskure sune masu yawaita tuba", kuma saboda shari'ar daga Allah ta ke.
Kuma yana daga cikin baiwawwakin Allah da ni'imarSa ga wannan qasa: TABBATUWAR AMINCI DA ZAMAN LAFIYA; Wanda lamuran musulunci suke daidaituwa da samuwar tsaro, kuma maslahohin rayuwa suke rataya akansa, kuma arziqi suke sauqaqa a inuwarsa, hanyoyi kuma su zama da aminci, kuma qasashen duniya su riqa canjin ababen amfani da maslahohi a tsakaninsu, rayuwa kuma ta bunqasa a dukkan vangarorinta, kuma da samuwar tsaro ake iya kare zubar da jini, da tava mutuncin mutane da dukiyoyinsu, kuma suma burace-buracen mutane da kasuwanci su kan shunfuxu ne a lokacin aminci.
Zaman lafiyar wannan qasa; ta masarautar Saudiya, amfaninsa na qasar ne, da sauran musulmai gaba xaya, saboda matsayin harami biyu maxaukaka, da kuma 'yan'uwantaka ta musulunci, domin wannan qasar tana da haqqi akan kowane musulmi, Allah Ta'alah ya ce:  "Kuma lallai muminai 'yan'uwan juna ne" [Hujurat: 10].

            Kuma yana daga ni'imomin Allah Mabuwayi da xaukaka ga wannan qasa mai albarka: TSARE-TSARE NA ALKHAIRI MASU AMFANI, WANDA SASHENSU KE ZUWA BAYAN SASHE, WAJEN HIDIMA GA 'YAN QASA, DA XAUKACIN MUSULMAI,  Na farko-farkonsu shine aikin raya harami biyu maxaukaka, da samar da sabbuba da ayyukan kawo walwala ga mahajjata da masu ziyara da masu umrah, wanda suke wajabta mana yin godiya, don haka YABO YA QARA TABBATA GA UBANGIJINMU, DA GODIYA A GARE SHI, a kan ni'imominSa.

            Kuma lallai godiya, amfanoninsa, yana komawa ne ga Mai yin godiyar, kamar yadda sakaci kan godiyar cutarwansa yana komawa ne ga gafalalle, saboda Allah yana cewa: "Kuma wanda ya gode, to lallai yana yin godiyar ne domin kansa, wanda kuma ya butulce, to lallai Allah Mawadaci ne, Godadde" [Luqman: 12].

Allah yayi albarka wa Ni da Ku cikin alqur'ani mai girma! Kuma ya amfanar da Ni da Ku da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, kuma ya amfanar da mu da shiriyar shugaban Manzanni, da maganganunsa miqaqqu.
Ina faxar Magana ta wannan, kuma ina neman gafarar Allah, wa Ni da Ku, da sauran Musulmai; sai kuma ku nemi gafararSa; saboda shi Mai yawan gafara ne, Mai jin qai.


HUXUBA TA BIYU
            Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya datar da wanda ya so zuwa ga alkhairori, kuma ya tavar da wanda ya so da adalcinSa da hikimarSa, sai ya bi sha'awowi, Ina yabon Ubangijina kuma ina yin godiya a gare shi, ina tuba zuwa gare shi, ina kuma neman gafararSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,  Ubangijin qasa da sammai.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa, matattarar girma da karamomi.
            Ya Allah kayi qarin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu,    da iyalansa da sahabbansa ma'abuta yin xa'a.
            Bayan haka!

            Ku kiyaye dokokin Allah ta hanyar tsayuwa wajen gode masa, kuma ku ambace shi yadda ya dace a ambace shi.

            Ya ku Bayin  Allah!
Allah (تعالى) yana cewa: "Idan kuka kafirce to lallai Allah Mawadaci ne ga barinku, baya yarda da kafirci wa bayinsa. Idan kuma kuka yi godiya yana yarje muku, kuma rai bata xaukar zunubin wata rai, Sa'annan izuwa ga Ubangijinku makomarku ta ke, sai ya baku labarin abinda kuka kasance kuke aikatawa, lallai shi Masani ne da abinda ke cikin qiraza" [Zumar: 7].

            Kuma ku sani, Lallai bawa duk yadda ya kai ga biyayya wa UbangijinSa, ya ke kuma kusantarSa da dangogin ibadodi, to ba zai tava iya tsayuwa da godiyar Ubangijinsa, a cikakkiyar fiska ba, Saidai kuma yana isar wa bawa ya tsayu wajen aikata farillai, ya kuma hanu daga laifukan da aka hana, sannan ya sani cewa ba domin rahamar Allah ba da ya kasance cikin masu hasara, Sai kuma ya lazimci neman gafara akan gajartawarsa, tare da yawaita roqon Ubangijinsa cewa ya taimake shi ya datar da shi, kuma ya yawaita ambaton Allah Ta'alah; saboda zikirin Allah ana rigayen samu maxaukakan matsayi da shi; An ruwaito hadisi daga Ibnu-Abbas (رضي الله عنهما) lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana addu'a, cewa: "Ya Ubangijina! Ka sanya ni na zama mai yawan godiya a gare ka, mai yawan ambatonka, mai yawan jin tsoronka, mai yawan yi maka biyayya, mai yawan qanqan da kai a gare ka, mai yin kuka da mayar da al'amari zuwa gare ka.
       Ya Ubangijina! Ka karvi tubata, kuma ka wanke zunubaina, ka amsa addu'a ta, ka tabbatar da hujjojina, kuma ka shiryar da zuciyata, ka daidaita harshena, ka zare dauxar zuciyata", Abu-dawud ya ruwaito shi da Attirmiziy, kuma ya ce: hadisi ne mai kyau ingantacce (hasan sahih).

            Ya ku Bayin Allah!
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan annabin, ya ku waxanda su ka yi imani ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Duk wanda ya yi salati guda xaya a gare ni, to Allah zai salati a gare shi guda goma saboda shi".
            Sai ku yi salati, da sallama ga shugaban na farko da na qarshe, kuma jagoran manzanni.
Ya Allah! Ka yi salati wa annabi Muhammadu…

Ya ku bayin Allah!  
"Lallai ne, Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani kan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku wa'aztu" [Nahli: 90].

Ku riqa ambaton Allah zai riqa ambatonku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, Lallai kuma Allah ya san abinda kuke aikatawa.

hudubar ABDULLAHI ALBU'AIJAN 7 Safar 1439H daga Masallacin Manzon Allah SAW











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 07/Safar/1439H
daidai da 27/Oktoba/ 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar, to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne, ya isar da manzanci, ya kawo amana, ya yi nasiha ga al'umma, kuma ya yi jihadi domin Allah iyakar jihadi, har mutuwa ta zo masa.
Salatin Allah ya qara tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa da wanda suka bi su da kyautatawa; da sallamar amintarwa mai yawa, har zuwa ranar hisabi.

       Bayan haka;
Lallai mafi alherin zance shine maganar Allah, mafi alherin shiriya kuma shiriyar annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم), kuma mafi sharrin lamura sune qirqirarru daga cikinsu, kuma kowace bidi'a vata ce, kowace vata kuma tana cikin wuta.

Ya ku bayin Allah;
Lallai abinda al'umma ta ke shigewa ta cikinsa na fitintinu da bala'oi, da jarrabawa, da tsanani, da fin-qarfin maqiya, lallai jarrabawa ne, kuma xauraya, da matashiya ga wata nasara bayyananna, da buwaya, da tabbatarwa da bada iko, da izinin Allah, Allah Ta'alah ya ce: "Ko kuna zaton ku shiga Aljanna, tun gabanin misalign waxanda suka shige daga gabaninku bai zo muku ba? Wahaloli da cuta sun shafe su, kuma aka jijjiga su, har manzonsu da waxanda suka yi Imani tare da shi, suka ce: Yaushe taimakon Allah zai zo? To! Lallai taimakon Allah yana kusa!" [Baqara: 214].

Ya ku taron musulmai … !!!
Haqiqa waxanda suka kasance a gabaninku, ana kama mutum sai a tona masa rami a cikin qasa, sai a zo da zarto, a xora akan kansa; har a raba shi kashi biyu, hakan ba zai kautar da shi daga addininsa ba, kuma ana taje gashinsa da matajin qarfe tsakanin naman jikinsa da jijiya gabanin qashi, hakan baya kautar da shi daga addininsa ba. Wallahi lallai Allah zai cika wannan al'amari (addini), "Kuma lallai Allah zai taimaki wanda ke taimakonsa, lallai ne Allah Mai qarfi ne Mabuwayi", [Hajj: 40].

Ya ku bayin Allah … !!!
Haqiqa wanda suka kasance farkon waxanda suka bayyanar da musulunci mutane bakwai ne, wato: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- da Abubakar, da Ammar da mahaifiyarsa Sumayyah, da Suhaib, da Bilal, da Almiqdad, Amma shi Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- sai Allah ya bashi kariya da samuwar Baffansa; abu-xalib, Shi kuma Abubakar, sai Allah ya bashi kariya da mutanensa, Su kuma sauran sai mushirkai suka xauke su, suka xanxana musu mummunar azaba, sai dai babu wani daga cikinsu face ya aikata musu abinda suka yi nufi, in banda Bilal; saboda shi kam, bai xauki ransa a bakin komai ba, a lamarin Allah, sai ya zama araha a wurin mutanensa; sai mushirkai suka yi ta cutar da shi, suna azabta shi, wai domin ko zai fita daga addininsa, amma sai ya fiskance su da qara daskarewa, da tabbatuwa, sai suka yi ta azabtar da shi, suna jarabtarsa. Kuma shugaban da ya mallaki Bilal; wato Umayyat bn Khalaf ya kasance yana fitar da Bilal idan zafin ranar azahar ta take, sai ya shumfuxa shi akan bayansa, a kan duwatsun Bax-ha'u ta garin Makkah, sannan sai ya yi umarnin a xora dutse mai girma akan qirjinsa, sa'annan sai y ace masa: Ba za ka gushe ba a cikin wannan baqar wahalar hark a mutu, ko ka kafirce da Muhammadu, Sai kuma ya ce: Wani shu'umcin ne ya jefo mu da kai, ya bawan banza! Idan har baka ambaci Allolinmu da alheri ba, to lallai zan sanya ka, ka zama misalin azaba ga bayi. Sai Bilal –رضي الله عنه- ya masa raddi, alhalin yana tabbatacce akan addinin musulunci, baya canza matsayi, ya ce: Ubanjina shine Allah, Shi kaxai yak e, shi kaxai. Kuma da na san wata kalma, wacce zata fi baqanta muku fiye da wanda na faxan, to da na faxe ta.
Yayin da abinda aka qaddara na azabta Bilal y azo qarshensa, sai buxi y azo, sai Abubakar –رضي الله عنه- ya saye shi, ya kuma 'yanta shi domin neman ganin fiskar Allah Mabuwayi da xaukaka, kuma akan haka ne, faxin Allah Maxaukaki: "Kuma za a nisatar daga wuta, wanda yafi kamalar taqawa * Wanda ya bada dukiyarsa yana neman tsarkaka * Kuma babu wani da ke da wata ni'imar da take jiran sakayya, a wurinsa * sai dai neman ganin fiskar Ubangijinsa Mafi xaukaka * Kuma da sannu zai yarda", [].
Sai kwanaki su shuxe, sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- yayi hijira zuwa garin Madina, Sai shima  Bilal –رضي الله عنه-, kuma sai yi hijira, ya kuma wayi- a matsayin mai kiran sallah, ga musulmai. Sai kuma ya fita tare da Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- zuwa yaqin Badar, su kuma mushirkai daga vangaren Makkah, sai suka fiskanto, tare da jagororinsu, wanda a cjininmu har abadaikinsu, akwai Umayyah bn Khalaf, da Abu-jahl, suna ta vangaren gaba cikin tawagar, cikin qasaita da girman kai, da ruxuwa, runduwarsu kusan bataliya guda; sojoji dubu, kuma a tare da su, akwai bayi mata, suna bugun gangar duffi, kuma suna rera waqar zagin musulmai, suna cewa: Wallahi ba za mu koma Makka ba, har sai mun je garin Badr, mu yi kwanaki uku, mu soke raqumi muci abinci, mu sha giya, kuma mata su mana bushi, larabawa kuma su ji labarinmu, da tafowarmu da haxuwarmu, sai kaga ba za su gushe ba, suna ganin kwar-jininmu har abada.
Shi kuma adadin musulmai xari uku ne da sha wani abi, kuma a cikinu babu mai doki, in banda Almiqdad. Sai yaqin ya kaure; Sai kuma Allah ya yi nufin baiwa ga muminai, akan waxannan da  aka raunatar da su a bayan qasa, kuma ya sanya su zama jagorori, kuma ya sanya su zama magada.
Sai Bilal –رضي الله عنه- ya ga tsohon shugabansa; wato Umayyah bn Khalaf, wanda ya xau dogon zango yana cutar da shi a garin Makkah, sai ya keto tsakiyar sahu, yana magana yana cewa:
Ba zaka kuvuta, idan akwai mai kuvuta. Sai Allah ya bashi damar kama shi, sai y agama da shi; sai labarinsa ya zama kamar jiya da ya shuxe, Sai Abubakar As-Siddiq –رضي الله عنه- ya tsara waqoqi akan lamarin, inda ya ce:
Madalla, Allah Mai jin-qai yam aka qarin buwaya
Lallai haqiqa ka riski xaukar fansarka, Ya kai Bilalu
Amma shi kuma maqiyin Allah; wato Abu-Jahlin, to haqiqa ya fiskanto, cikin girman kai da ruxuwa, yana faxin waqe yana cewa:
Wace fansa yaqi zai xauka daga gare ni,
Alhalin ina da gogewar shekaru biyu, ga qananan shekaru
Domin irin haka ne, uwata ta haife ni
Sai Allah ya xanxana wa Abu-jahl qasqanci, a hannun samari biyu qanana, daga Madina, wanda sune 'ya'yan Afra'u, sai ya riqa cewa, da dai ba manomi ba ne ya kasha ni, da haka nafi so, kuma da yafi xaukaka sha'anina, kuma da bani da wata naqasa cikin haka.
Sai Abdullah ibn Mas'ud –رضي الله عنه- y azo, ya xora qafarsa, akan wuyan Abu-jahl, yana cewa: Allah ya wulaqantaka, Ya kai maqiyin Allah. Sai Abu-jahl gabanin ya mutu ya fara aibanta Abdullah ibn Mas'udin, inda yak e cewa: Haqiqa ya kai qaramin mai kiyo awaki, ka hau wani mataki abin qi, mai wahala.

A lokacin da aka shigar da musulunci Makkah (Fat-hu Makkah), sai Bilal –رضي الله عنه- ya hau Ka'abah, domin ya shelanta Kalmar tauhidi, 'yan taku kaxan da inda ake masa azaba a cikinsa, kuma a lokacin azahar, sai gas hi yana xaga sauti a cikin jama'a, da kalmomin kiran salla: ALLAHU AKBARUL LAHU AKBAR, ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL LAHU, ASH-HADU AN LA ILAHA ILLAL LAHU, ASH-HADU ANNA MUHAMMADAN RASULUL LAHI.
Sai wannan matsayar tasa ta xago fushin maqiyansa, har wani daga cikinsu ya ce: Haqiqa Allah ya karrama Mahaifina; tun da yam utu, bai ji wannan ba, balle ya fusata shi.
Wani kuma ya ce: Kaicona, Da na mutu gabanin jin haka.

Ya ku, taron musulmai…!!
Bilal –رضي الله عنه- bai samu matsayi maxaukaki a cikin musulunci ba, sai bayan an jarrabe shi da bala'oi, ya kuma yi haquri da nuna qoqari, "Yak u waxanda suka yi Imani, ku yi haquri, kuma ku yi dauriya, kuma ku yi tsayuwar dakon ribaxi, kuma ku yi taqawa, domin samun babban rabo", [Ali-imrana: 200].

Ina faxan abinda ku ke ji, …

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, kuma ya azurta mu da bin sunnar AnnabinSa mai karamci, da kuma lazimtar shiriyarsa miqaqqa, ina faxin abinda ku ke ji wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai, sai ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Yabo ya tabbata ga Allah, Mai bayyanar da gaskiya, wanda ke xaukaka shi, wanda ke qasqantar da varna, yake tunkuxe shi.
Ya turo ManzonSa da shiriya, da kuma addinin gaskiya, domin ya xaukaka shi aka addinai gaba xaya, koda kafirai sun qi.
Allah ka qara salati ga annabi Muhammadu, da iyalansa, kamar yadda ka yi salati ga annabi Ibrahima, da iyalan annabi Ibrahima, lallai kai abin godiya ne Mai girma..

Ya ku bayin Allah !! …
Lallai Allah yana yin talala, amma baya kyaliya, kuma yana yin jinkiri ga azzalumi, har idan ya tashi kama shi, ba zai kufce masa ba, "Kuma kada waxannan da suka kafirta su yi zaton cewa jinkirin da muke musu alheri a gare su, lallai kawai muna musu jinkiri ne, domin su qara laifi, kuma suna da azaba mai wulaqantarwa", [Ali-imrana: 178].
Don haka, abinda ya sauka ga musulman da aka raunata su a garin Makkah, a farkon musulunci, na jarrabawa da bala'i, lallai ya kasance ne saboda tanadar sabin tsareku, a kuma basu iko da nasara mai yawa, kuma domin ta zama xauraya da tankaxe da rairaya, domin Allah ya ware masu dauxa.
Don haka, ba a zauna ba, sai na wani lokaci taqaitacce, sai Allah ya yi baiwa ga waxanda ake cin cin zarafinsu ake zaluntarsu waxanda aka raunata su a bayan qasa, "Domin ya sanya su shugabanni, kuma ya sanya su magada * kuma ya basu iko a bayan qasa" [Qasas: 5-6]. Sai ga manyan jagororin shirka da kafirci da zalunci, ana yanka su da makaminsu, a hannun tsofaffin 'yantattun bayinsu, kamar qissar Bilal da Umayya, da kuma qissar Abdullah ibn Mas'ud da Abu-jahl, sai suka warkar da qishinsu, suka xauki fansar cutarwarsu, "Kuma lallai Allah yana bada nasara ga wanda ya taimake shi, lallai ne Allah Mai qarfi ne, Mabuwayi" [Hajj: 40].

Ya ku bayin Allah…!!
Lallai ma'aunan gwada falala a wurin Allah, sune (Imani da) aiki, ba dangantaka, ko matsayi da dukiya da girma ba, saboda mutane daidai suke, kamar haoqan matajin kai, dukkansu daga annabi Adamu ne, shi kuma Adamu daga turvaya, kuma babu wata falala, ga wani balarabe akan ba'ajame, sai da taqawa, "Ya ku mutane, lallai ne Mu mun halitta ku, daga namiji da mace, kuma muka sanya ku dangogi da qabilu, domin ku san juna, lallai mafificinku daraja a wurin Allah, shine wanda yafi ku taqawa" [Hujurat: 13].
Na rantse da Ubangijinka, mutum ba komai ba ne, sai da addininsa
Don haka, kada ka bar aikin taqawa, kana mai dogaro ga nasaba
Saboda muslunci ya xaukaka Salmanul farisiy
Kamar yadda shirka ya qasqantar da mutum mai girman nasaba; Abu-lahab

Kuma sau dayawa, voyayyen mutum mai taqawa, wanda ba a wani damuwa da shi, ana rufe masa qofa, babu wani shamaki tsakaninsa da tsakanin Allah, kuma da zai yi rantsuwa ga Allah (kan sai ya aikata wani abu) to, da ya kuvutar da rantsuwarsa.

Kuma a lokacin da sahabi Abu-zarri ya aibanta Bilal, y ace masa: Ya xan baqar mace, Sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya fusata, ya ce: "Ka aibanta shi da Mahaifiyarsa? Lallai kai mutum ne wanda a tare da kai akwai xabi'ar jahiliyya".

Kuma haqiqa, Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya yi bushara wa Bilal da Aljannah, a inda ya ce: "Ya kai Bilal! Ka bani labarin aikin da ka fi fatansa, daga ayyukan da ka aikata, ga musulunci, saboda lallai na ji qarar takalmarka a gaba gare ni, a cikin Aljannah".

Ya ku taron musulmai,,,
Lallai mushirkai sun ji matuqar qunci, a lokacin da suka ji sautin sahabi Bilal yana tsage kiran sallah, akan Ka'abah.
To, kuma idan kiran sallar Bilal ya kasance yana cutar da mushirkai, to haqiqa ya kasance yana sosa qaiayin zukatan musulmai, sai suyi begen sauraronsa, saboda Bilal ya kasance idan ya yi kiran sallah bayan rasuwar Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- sai ya kasa mallakar kansa, sai ya tayar da vacin ran da ke cikin zuciyarsa, ya kuma tsokano masa da kuka, har ya fita daga hankalinsa, mutane kuma su tsorata, garin Madina ya cika da jururuwar tuna Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-.
Saboda a wani dare Bilal ya kira sallah, a lokacin sahur, bayan rasuwar Annabi –صلى الله عليه وسلم- sai yah au rufin wannan masallacin, ya ce: "Allahu akbar, Allahu akbar ", sai Madina ta girgiza, a yayin da ya ce: "Ash-hadu an la ilaha illal lahu", sai ta qara girgiza. A yayin da ya ce: "Ash-hadu anna Muhammadan Rasulul lahi", sai mutane suka fito, daga gidajensu. Ba a ga mutane maza da mata a wani yini da suka fi yin kuka fiye da wannan yinin.
Kuma a lokacin da Umar –رضي الله عنه- ya zo qasar Sham, ya kuma shigar da musulunci Baitul qudus (fat-hu baitul maqdis), to sai ya umarci Bilal da cewar ya yi kiran sallah, sai ya ce: Ya Amiral mu'uminina! Ban so, na sake kiran sallah ga wani mutum ba, bayan rasuwar Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-, don haka; Zan maka biyayya tun da ka umarce ni, a wannan sallar kawai ita xaya. A yayin da Bilal ya yi kiran salla, sai sahabbai suka ji kiran sallarsa, sai suka yi kuka mai tsanani.
Saboda, Bilal ya tunatar da su masoyinsu, kuma sanyin idanunsu, wanda ya sosa musu matattarar imanin da ke cikin zukata, wanda kuma Manzon shine sababin tsiransu, sai rayuka suka yi bege, zukata kuma suka yi haniniya, sai kuma ambatonsa ya tavo soyayyarsu, ya cakuxa kwaryar zukata da fatarta.
Don haka, ba za zargi sahabbai ba, akan haka, ta yaya kuma za a zarge su, alhalin kututturen dabino ya yi haniniya kuma yayi kuka saboda rabuwa da Annabi. Dutsen Uhud ya girgiza domin ya tarjama soyayyar da yake masa, da girmama shi.
Ya Allah, ka azurta mu da soyayyarsa, ka tayar da mu a cikin tawagarsa, ka mana baiwar samun cetonsa.

Ya ku taron musulmai ,,,
            Haquri shine mabuxin da key aye baqin ciki, kuma Aljannah an kewaye ta da ababen qi, kuma an kewaye wuta da ababen sha'awa.
Kuma nasara tana kusa, kuma lallai Allah zai taimaki addininSa, kamar yadda ya taimaki waxanda ake raunana su a garin Makkah, kuma kamar yadda ya yi ta taimakon waliyyansa majivinta tun gabanin haka, da bayan haka, "Kuma a wannan ranar muminai za su yi farin ciki, da nasarar Allah, wanda ke taimakon wanda ke so, kuma shine Mabuwayi Mai jin-qai * alkawarin Allah, kuma Allah baya sava alkawarinsa, sai dai mafi yawan mutane basu sani ba", [Rum: 4-6].
Ya Allah ka xaukaka musulunci da musulmai….

"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
,,,          ,,,          ,,,

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...