2017/06/09

hudubar 14 RAMADANA 1438 daidai 9 June 2017 ta AsSubaitiy daga MASALLACIN ANNABI







HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 14/Ramadhana/1438H
Daidai da 09/Yuniyo/2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ABDULBARIY XAN AUWADH AS-SUBAITIY






TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
SIFOFIN BAYIN MAI RAHAMA
     Shehin Malami wato: Abdulbariy xan Auwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'ah, 14/ Ramadhana, 1438H, mai taken: SIFOFIN BAYIN MAI RAHAMA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna akan.

HUXUBAR FARKO
Bayan haka:
A cikin kwanaki da dararen da mu ke ciki (na ramadhana), muna ganin yadda bauta ke bayyana a cikin mafi qayatarwar surarta da ma'anoninta, (ta fiskar) daxin azumi, da zaqin qur'ani, da kyan tsayuwa cikin sallolin dare, da sadaka da ciyarwa, ga kuma harasa, suna furta zikiri ko ambaton Mai rahama,
Gavvai, da soyayya, da zukata, sun rusuna ga Allah, cikin ibadar da ake yi ba da tilasci ba, wacce ginshiqinta shi ne soyayyar zuciya, wanda kuma za ta kai ga samun rabauta, a duniya da lahira.
Ibada bata rabuwa da musulmi, a duk inda ya sauka, a kuma dukkan lokutan da ya kasance a cikinsu, na matakan rayuwarsa, har ajalin da aka yanke masa ya same shi, alhalin yana cikin hali mai kyau, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma, ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka" [Hijr:  99].
Zuciya tana rausayawa, rayuwa kuma, tana xaukaka, a lokacin da kunnuwa ke jin yadda Allah ke siffanta halittunSa da kalmar YA KU BAYINA!
Kuma duk wanda ya faxa qarqashin wannan kira, ya kuma rabauta da xaukakar da ke cikin kalmar YA KU BAYINA! to lallai, ya samu babban rabo, mai girma.
Kalmar YA KU BAYINA! tana tultulo da natsuwa cikin zukata, kuma tana amintarwa daga tsoro, kuma alamar samun yardar Ubangiji ne, da falalarSa da ni'imarSa, Allah ta'alah yana cewa: "YA KU BAYINA! a yau, babu tsoro a kanku, kuma ku, ba masu yin baqin ciki ba ne * Waxanda su ka yi imani da ayoyinmu, kuma su ka kasance masu miqa wuya * Ku shiga aljanna, ku da matayenku, ana girmama ku" [Zukhruf: 68-70].
Rai natsattasiya, wacce imani ya tabbatu a cikinta, kuma ta natsu da tsantsance bautarta; na ikhlasi, kuma ta yi tawakkali ga Mahaliccinta, Ubangijinta lallai ya xaukaka ta da bushararSa mai girma; wanda ta zo a cikin faxinSa: "Ya ke Rai mai natsuwa * Ki koma zuwa ga Ubangijinki, alhali kina mai yarda, abar yardarwa * Sai ki shiga cikin BAYINA! * kuma ki shiga aljannata" [Fajr: 27-30].

Allah yana siffanta halittarSa ne da YA KU BAYINA! domin ya xebe musu kewa, kuma ya musu albishir da cewa, Shi (Allah) a kusa ya ke, kuma domin mutum ya iya shumfuxa buqatunsa, ya kuma watso damuwowinsa, yana mai xaga kokensa ga UbangijinSa; Mai jivintar lamarinsa, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma idan BAYINA! su ka tambaye ka, a kaina, to, lallai Ni Makusanci ne, Ina amsa kiran mai kira idan ya roqe Ni, sai su nemi amsawata, kuma su yi imani da Ni, tsammaninsu su shiryu" [Baqara: 186].


Kalmar YA KU BAYINA! tana yaye qiraza, kuma tana waigo da dubin mutane, zuwa ga rahamar Allah, wanda ta rigayi fushinsa, da tausasawarSa ga bayinSa, da jinqanSa, Allah ta'alah yana cewa: "Ka baiwa BAYINA! labari lallai ne, Ni Mai gafara ne Mai jin qai * Kuma lallai azaba ta, ita ce azaba mai raxaxi"[Hijr: 49-50 ].
A cikin ayar, yayin da Allah Mabuwayi ya ambaci rahama da gafara, sai ya kai maqura wajen qarfafa lamarinsu, da lafuza guda uku, wanda su ne, "ANNIY" da "ANA", da "ALIF DA LAAMUN" na nuna gamewa, ya ce:
(أنّي أنا الغفور الرحيم)
A lokacin da ya ambaci azaba kuma, bai ce: "LALLAI NE, NI NE MAI YIN AZABA", kuma bai siffanta kansa da hakan ba, kawai abinda ya ce, shi ne: "Kuma lallai azabata, ita ce azaba mai raxaxi".
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai Allah Maxaukaki ya halicci jin qai a ranar da ya halicce ta, rahama guda xari (100), sai ya riqe rahama casa'in da tara (99) a wurinsa, ya kuma saki guda xaya a cikin halittunSa gaba xaya, don haka; Da kafiri, ya san dukkan abinda ke wurin Allah na rahama, to da bai xebe tsammani daga samun rahama ba, Da kuma mumini yana sane da dukkan abinda ke wurin Allah ta'alah na azaba, to da bai aminta daga faxawa wuta ba".
Saboda haka,
Duk wanda ya kyautata bauta, zai kyautata zatonsa ga UbangijinSa, ya kuma amintu da yalwar rahamarSa, kuma sai ya ji cewa, lallai ababen da Allah ke qaddara wa mutane alkhairi ne, a haqiqanin lamarinsu, koda kuwa a zahirinsu musibu ne ababen qi, masu ciyo, Allah ta'alah yana cewa –kamar yadda Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya bada labari: "Ni ina wurin da BAWANA ya yi zatona".

Allah ta'alah yana kiran muminai ne da faxinsa: YA KU BAYINA! domin su shiga inuwar bauta a gare shi, akan kowace qasa, a kuma inuwar kowace sama, Allah ta'alah yana cewa: " YA KU BAYINA! waxanda su ka yi imani, lallai fa qasata mai yalwar faxi ce, saboda haka, ku bauta mini; ni kaxai" [Ankabut: 56].

"YA KU BAYINA" kalma ce mai taushi, wacce ta ke zaburarwa, kan yin aiki, kuma da wannan kalmar ce Mahalicci, ya kirayi bayinSa muminai, domin ya ilmantar da su ibadarsa da ta fi girma, wanda kuma ita ce tushen ibadodi (wato, sallah), da kuma xa'oin da su ka fi girma, su ka fi falala, domin su ribaci damar da ke cikin rayuwa, "Ka ce wa BAYINA! waxanda su ka yi imani: Su riqa tsayar da sallah, kuma su ciyar daga abinda mu ka azurta su, a asirce, da kuma a bayyane, gabanin yinin da babu ciniki a cikinsa ya zo, kuma babu abotaka" [Ibrahim: 31].

Don haka, Musulmi yana bautar UbangijinSa a kowani lokaci, kuma a cikin kowani hali; kamar cikin cinsa da shansa, da lokacin barcinsa da farkawarsa, a safiyarsa da maraicensa, Allah ta'alah yana cewa: "(sune) waxanda su ke ambatar Allah a tsaye, da a zaune, da kuma akan kuivinsu" [Ali-imraana: 191].

            Allah ya kira muminai ne, da faxinsa: YA KU BAYINA! domin ya zana musu hanyar samun taqawarsa, ya kuma faxakar da su yadda za su yi aiki da ita, a cikin faxinSa: "YA KU BAYINA! Ku bi ni da taqawa" [Zumar: 16].
Sai kuma Allah ya yaba musu akan aiki da taqawar, yabon da bashi da makamanci, a cikin faxinSa: "Kuma ya lazimta musu, kalmar taqawa, sai su ka kasance mafi dacewa da ita, kuma ma'abutanta" [Fat-h: 26].
Saboda babu wata qima a rayuwa wacce ta fi girma akan samun taqawa, "Lallai mafificnku daraja a wurin Allah shi ne mafificinku a cikin taqawa" [Hujuraat: 13].
            Shi kuma samar da taqawa, shi ne BABBAR ALAMAR WATAN AZUMI, Allah ta'alah yana cewa: "Ya ku waxanda su ka yi imani an wajabta azumi a kanku, kamar yadda aka wajabta shi ga waxanda su ka zo gabaninku, tsammaninku za ku samu taqawa" [Baqara: 183].
            Taqawa a watan ramadhana, tana haifar da tsarkake  rai da tarbiyyantar da ita, daga munanan halaye, ta kuma sabar mata da yin aiki da halaye masu kyau, kuma taqawar za ta koyar da bawa sanin ransa, da buqatuwar ran, da rauninta da buqatarta ga Ubangijinta (SWT), kuma ta riqa tuna mata girman ni'imomin Allah a kanta, da talauci ko buqatar 'yan'uwansa faqirai, sai ya lazimta mata godiyar godiyar Allah (SWT), da kuma yin amfani da ni'imominSa wajen yin xa'a a gare shi, da taimakon 'yan'uwansa faqirai, da kyautata musu.

            Lokacin da mumini ke jin yadda Allah ya siffanta halittunSa, da YA KU BAYINA! zai ji a jika, cewa lallai shi ya fake ga qaqqarfar madogara, da garkuwa mai bada kariya, da kuma kariya a gare shi daga dukkan shexani mai tsaurin kai, Allah ta'alah yana cewa:   "Lallai su BAYINA baka da wani qarfi akansu, Kuma Ubangijinka ya isa ya zama wakili" [Isra'i: 65].
Don haka; zuciyar da ta sadu da Allah; wato wanda rayuwarta ya cika da bauta da son Allah, shexan bashi da qarfin iko akan wannan zuciyar da ta ke haxe da Allah, kuma irin wannan zuciyar ta cancanci ta samu kariyar Allah, kuma a jikin wannan kariyar ne, kaidin shexanu dukkansa ke lalacewa.

            Allah yana siffanta salihan halittarSa da YA KU BAYINA! sai -a zukatansu- ya tayar musu da qarfin fatan samun mayewa da mallakar duniya, da hasken fatan nasara, kuma Allah ya isa ya zama Mataimaki, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma haqiqa mun rubuta a cikin littatafai, baicin lauhul mahfuz, lallai qasa, BAYINA salihai ne za su gaje ta" [Anbiya'i: 105].
Don haka, mallakar qasa, baiwa ce daga Allah, kuma alqawari ne, wanda manufarsa shi ne tabbatar da bauta ga Allah.

            "YA KU BAYINA!" kalma ce mai taushi, kuma salon magana ne tattausa, wacce ma'anarta ta ke gamewa har da masu laifi, da waxanda su ka gajarta ayyuka, matuqar sun tuba, sun kuma mayar da lamari zuwa ga Allah, Allah ta'alah yana cewa: "Ka ce: YA KU BAYINA, waxanda su ka yi varna a kan kayukansu, kada ku yanke qauna daga rahamar Allah, Lallai ne Allah yana gafarta zunubai gaba xaya, lallai shi, shi ne Mai gafara Mai jin qai" [Zumar: 53].
Bukhariy da Muslim da wasunsu sun rawaito daga Abdullahi ibn Abbas –Allah ya qara yarda a gare su- cewa, lallai wasu mutane, daga cikin ma'abuta shirka sun kasance sun yi kisa sun yawaita, sun kuma yi zina sun yawaita, sai su ka zo ga annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- su ka ce: "Lallai abinda ka ke faxa, kuma ka ke yin kira gare shi abu ne mai kyau, da za ka bamu labarin cewa: lallai akwai kaffara ga abinda mu ka aikata (na shirka da kisa da zina), sai faxin Allah ya sauqa: (Kuma su ne waxanda ba su kiran wani Ubangiji tare da Allah, kuma ba su kashe ran da Allah ya haramta kashe ta face da haqqi, kuma ba su yin zina" [Furqan: 68], sai kuma aka saukar: "Ka ce: YA KU BAYINA, waxanda su ka yi varna a kan kayukansu, kada ku yanke qauna daga rahamar Allah".
            Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Allah tabaraka wa ta'alah yana cewa: Ya kai xiyan Adamu, Lallai ne kai, matuqar za ka roqe ni, ka yi fatana, to zan gafarta maka, abinda ya kasance daga gare ka, ba zan damu ba, Ya kai xiyan Adamu, lallai ne kai, da zaka zo da kamar cikin qasa, ko abinda ya yi kusa da cikinta, na kura-kurai, sa'annan ka sadu da ni baka haxa ni da komai, to zan zo maka da gafarar da ta kai cikin qasa".

            Allah ya kyautata wa halittunSa, a inda ya siffatanta su, da YA KU BAYINA domin ya kira su zuwa ga kyautata zance, ko yin maganar da ta fi tsarki, da kuma kyautatawa cikin dukkan ayyuka, da kuma dukkan zance, da kuma dukkan sha'anonin rayuwa, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma ka ce wa: BAYINA, su riqa faxin kalmar da ta ke mafi kyau" [Isra'i: 53].
            Allah yayi mini albarka ni da ku, cikin alqur'ani mai karamci, ya kuma amfanar da mu da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Ina faxar maganata wannan, ina kuma neman gafarar Allah, wa NI da KU, da kuma sauran musulmai, ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.

HUXUBA TA BIYU
Waxancan, wanda Ubangijinsu ya kira su da faxinSa: YA KU BAYINA yana daga sifofinsu: KWAXAITUWARSU GA SALLOLIN DARE, DA QOQARINSU CIKIN HAKA, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma bayin Mai rahama su ne waxanda ke yin tafiya a kan qasa da sauqi, kuma idan jahilai su ka yi musu magana, sai su ce: salama (a zauna lafiya) * Su ne waxanda su ke kwana ga Ubangijinsu suna masu sujada da tsayi" [Furqan: 63-64].
Kuma yana daga cikinmafificin ayyuka a cikin wannan wata (na ramadhana) mai karamci, salloli ko tsayuwan dare, saboda ya zo cikin sahihan littafi biyu, lallai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya tsayu a ramadhana da sallar dare cikin imani da neman lada, an gafarta abinda ya gabata na zunubansa".
Kuma haqiqa tsayuwa don sallar dare ya kasance al'adar Annabi ne –صلى الله عليه وسلم- da sahabbansa.

Kuma yana daga sifofin bayin Mai rahama: TAUSHIN GEFE, DA KAWAR DA KAI DAGA JAYAYYA DA JAHILAI, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma bayin Mai rahama su ne waxanda ke yin tafiya a kan qasa da sauqi, kuma idan jahilai su ka yi musu magana, sai su ce: salama (a zauna lafiya)" [Furqan: 63].

Kuma yana daga sifofin bayin Mai rahama: TSAKAITAWA WAJEN CIYARWA, saboda babu varnatarwa, kuma babu kwauro (ko mammaqo), Allah ta'alah yana cewa: "Kuma sune waxanda idan za su ciyar, basu varnatarwa, kuma ba su yin kwauro, kuma ciyarwarsu ta kan kasance a tsakanin wancan, tsakaitawa" [Furqan: 67].
Kuma varnatar da dukiya a cikin watan azumi da wanin wannan watan, abu ne da aka yi hani akansa, domin kashe dukiya wajen sayan waxannan ni'imomin, sa'annan a tuntsurar da su (ba tare da sun amfanar ba), lamari ne da shari'a ta yi inkarinsa, kuma ta haramta shi, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma ku ci, kuma ku sha, kuma kada ku varnatar; lallai ne shi (Allah) baya son mavarnata" [A'araf: 31].
            Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, sabodaAllah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Yaku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].
,,,          ,,,          ,,,

,,,          ,,,          ,,,

2017/06/01

hudubar 07 Ramadan 1438h daidai da 02 Yuni 2017M daga Dr Husain AlusSheikh Masallacin Annabi SAW











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 07/RAMADHANA/1438H
daidai da 02/YUNI/2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH HUSAIN BN ABDUL'AZIZ ALUS-SHEIKH





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
TTT
Shehin Malami wato: Husain bn Abdul'aziz Alus -Sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TTT, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO

Bayan haka:
Ya ku Bayin Allah… !!
Lallai abin neman da ya fi xaukaka, kuma buqatar da ta fi girma, ita ce: BAWA YA YI GAGGAGWAR AIKATA ALKHAIRORI, YA KUMA RIBACI LOKUTAN ALKHAIRI; TA HANYAR SAMAR DA KYAWAWAN AYYUKA, "Da waxanda su ka yi rigaye. Su waxanda su ka yi rigaye * Waxannan su ne waxanda aka kusantar …" [Waqi'ah: 10-11].
Kuma a cikin watan ramadhana akwai, damammakin yin guzuri, na kyawawan ayyuka, da kusantar Allah da dangogin xa'oi, kuma ya zo cikin hadisi, cewa: "Wanda ya azumci watan ramadhana cikin imani da neman lada, an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa. Wanda kuma ya yi tsayuwar ramadhana (wato, sallar dararen watan) cikin imani da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa" An yi ittifaqi kan ingancinsa.

Ya ku Taron musulmai … !!!
Wanda aka masa taufiqin dace, shi ne wanda ke kiyaye gavvansa, daga aikata ababen da aka hana, da kuma laifuka masu halakarwa,
Kuma lallai yana daga cikin hasara, da tavewa ko halaka, Musulmi ya yi aikin tara ko samun lada, tare da gaggawar aikata xa'oi, sai kuma ya sake gaggawa wajen warware abinda ya qulla, da rushe abinda ya gina, saboda talauci na haqiqa (a lahira), shi ne, wani ya bayar da kyawawan ayyukansa, ga waninsa, sakamakon sakaci ga lamarin haqqoqin halittun Allah, da zaluntarsu da kala-kalan nau'in zalunci, da cutar da su, da dangogin cutarwa, ko yin ta'addanci akansu da na'uka mabanbanta na ta'addanci, wanda Ubangijin halittu ya haramta, kuma annabinmu Muhammdu –صلى الله عليه وسلم- ya tsawatar,   "Shin kun san wanene fallasasshe?
Sai su ka ce: Fallasasshe a cikinmu shi ne wanda bashi da dirhami ko kaya. Ya ce: Sai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: Lallai fallasasshe daga cikin al'ummata, shi ne wanda zai zo a ranar qiyama, da salloli, da azumi, da zakka, sai ya zo alhalin ya zagi wannan, ya yi qazafi ga wannan, ya ci dukiyar wannan, ya zubar da jinin wannan, ya doki wannan, sai a baiwa wannan daga kyawawansa, wannan daga kyawawansa, idan kyawawan nasa su ka qare, gabanin a gama biyan abinda ke kansa, sai a xauko daga zunubansu, a lafta akansa, sai a jefa shi cikin wuta" Muslim ya rawaito shi.
Nawawiy ya faxa –a inda ke sharhin wannan hadisin-: "Haqiqanin fallasasshe shi ne wanda zai halaka cikakkiyar halaka, kuma shi ne aka rasa, rashin da babu samuwa a bayansa, ta hanyar xaukar ayyukansa kyawawa ga masu binsa bashi, idan kuma kyawawan nasa su ka qare, to sai a kwaso munanan ayyukansu, a lafta masa, sai kuma a wurga shi cikin wuta, a nan ne kuma; Sai hasararsa da halakarsa da talaucinsa su gama cika".

Don haka; ka ji tsoron Allah –Ya kai musulmi-, kana mai kiyaye ranka, daga dukkan laifuka, kuma ka nisantar da ita, daga sabbuban halaka, da kuma dalilan yin hasara.

'Yan'uwana musulmai … !!!
Tsira, tana nan a cikin kiyaye gavvai, samun sa'ada kuma a cikin lazimtar xa'oi, da kiyaye su daga dukkan abinda zai gurvata su, ko kuma ya vata tasirinsu, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda a wurinsa akwai zaluncin da ya yi wa xan'uwansa; cikin mutunci ne, ko dukiya, to ya nemi warwarewa daga gare shi, gabanin ya zo a qiyama, a inda babu dinari ko dirhami, kawai za a xauka ne daga kyawawan ayyukansa, idan kuma babu; to sai a xauki munanan sahibinsa, sai a qara su akan munanansa, sai kuma a yi wurgi da shi cikin wuta", Bukhariy ya rawaito shi.
A cikin riwayar waninsa kuma, Ibnu-Hubairah ya ce: "Xaukar fansar qisasi, yana shiga cikin kowane kyakkyawa, har ya zama babu wani abu daga cikinsa da zai saura".
            Sai ka kiyaye –Ya kai Musulmi- daga faxawa cikin halaka, kana mai cikakken kiyayewa, dangane da haqqoqin halittu, Annabi –صلى الله عليه وسلم- kuma, yana cewa: "Lallai za a bada haqqoqi ga ma'abutansu, a ranar qiyamah, har sai an xau fansa ga akuyar da bata da qaho, daga akuya mai qaho". Muslim ya rawaito shi.
            Ma'anar hadisin shi ne, lallai Allah zai xau fansa ga wanda aka zalunta, daga wanda ya zalunce shi, kamar yadda hadisan da su ka gabata su ka bayyanar.

            Daga wannan ne kuma, (za mu ce:)
            Shi mai azumi yana cikin lokaci muhimmi; wanda a cikinsa xa'oin muminai su ke yawaita, sai ya zama wajibi, musulmi ya riqa tuna cewa, lallai haqiqanin azumi tarbiyya ne, kan samar da taqawa, "Ya ku waxanda su ka yi imani an wajabta azumi a kanku, kamar yadda aka wajabta shi ga waxanda su ka zo gabaninku, tsammaninku za ku samu taqawa" [Baqara: 183].
            Kuma cikin faxakarwar Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- tabbatattu, akwai mafi girman tsawatarwa, kuma mafi girman wa'azi, saboda Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Kuma idan ranar azumin xayanku ta zo, to kada ya yi kwarkwasa, kuma kada ya yi Shewa (ihu), idan kuma wani ya zage shi, ko ya aibanta shi, sai ya ce: Ni mai azumi ne…".

            Sai ka kiyaye kyawawan ayyukanka –Ya kai musulmi-, kuma ka kasance a kan, bada kariya ga labulan ayyukan xa'arka, kana mai bayyanar da matsanancin kwaxayi a kan hakan, kuma mafi girmansa, saboda Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Wanda bai bar faxin zancen qarya, ko aiki da shi ba, da kuma jahilci, to lallai Allah bashi da buqatar ya bar abincinsa da abin shansa".

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Ya ku waxanda su ka mallaki kafafen sadarwa!!!, Ya waxanda aka jarabbe su, da rubutu a kafafen sadarwa, da na'ukansu dayawa!!!,
Ku ji tsoron Allah mabuwayi da xaukaka, kuma ku kiyayi yaxa dukkan abinda ya sava wa wannan addini da falalolinsa, ko ya ke yin suka kan tabbacin wannan addinin, ko kuma yaxa abinda zai kai ga aukawa ga bolar ababen kyama, kuma munana, Saboda ya zo cikin qa'idodin shari'a, cewa, duk wanda ya zama sababin faxawar halittu cikin savo, to lallai yana da kwatankwacin zunubinsu, Allah ta'alah yana cewa: Kuma lallai za su xauki kayan nauyinsu (na zunubi), da waxansu nauyayan zunubai, tare da kayan nauyinsu" [Ankabut: 13].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Wanda ya sunnata mummunan sunna a cikin musulunci, yana da zunubinta, da zunubin mutumin da ya yi aiki da ita, ba tare da an tauye komai daga zunubansa ba".
Kuma Allah ya yi rahama ga Shaxibiy, a inda ke faxar maganarsa mai muhimmanci, cewa: "Madalla da mutumin da ya mutu, sai zunubansa su ka mutu tare da shi, Bone kuma ya tabbata ga wanda ya mutu, sai zunubansa su ka cigaba da wanzuwa, shekaru xari, ko shekaru xari biyu, ana masa azaba da su a cikin qabarinsa, ana kuma tambayarsa, har zuwa lokacin qarewarsu".


,,,          ,,,          ,,,

2017/05/19

hudubar 23 SHA'ABAN 1438h ta Dr Abdullahi Albu'aijan daidai da 19 Mayu 2017M MASALLACIN ANNABI s a w











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 23/Sha'aban/1438H
daidai da 19/Mayu/ 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH ABDULLAHI BN ABDURRAHMAN ALBU'AIJAN





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
SHIRI GA AZUMIN RAMADHANA
Shehin Malami wato: Abdullahi bn Abdurrahman Albu'aijan –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: SHIRI GA AZUMIN RAMADHANA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah; wanda ya saukar da Qur'ani a watan azumi, yana mai shiriya ga mutane, da hujjoji bayyanannu, daga shiriya, da kuma rarrabewa, kuma Ya fifita ramalana akan sauran watanni, da zamani.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, shaidawa irin ta gaskiya da imani,
kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, jagora ga qabilar Adnan, kuma mai ceton talikai, a yinin da yara a cikinsa ke fitar da furfura,
Allah ka yi qarin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da waxanda su ka bi su, da kyautatawa.

Bayan haka:
Ya ku bayin Allah;
Lallai ne Allah yana da kyautuka da baiwa, da kuma lokutan alkhairi da xa'oi, wanda a cikinsu rahamomi ke sauka, albarkoki kuma su ke gamewa,
Kuma yana daga cikin waxannan lokutan, tsarkaka masu daxi; WATAN DA A CIKINSA AKE RURRUFE QOFOFIN WUTA, SAI KUMA A BUXE QOFOFIN ALJANNONI,
Kuma haqiqa, ajalin wannan lokacin ya kusanto, zamaninsa kuma ya qarato, saboda babu abinda ya rage a tsakaninku da shi, face wasu yini qididdigaggu,
Sai ku zaburo, a cikinsa da aikata xa'oi, da kuma ninninka kyawawan aiyuka, tare da rabauta da samun kankare munanan ayyuka,
Kuna masu qara zage-damtse, kuma ahir xinku da jinkirin alkhairi, ko samun rauni, domin watan ramalana kwanaki ne qidayayyu, kuma awowi, qididdigaggu, wanda kuma babu fagen wargi a cikinsu ko wasa, kuma babu fagen nuna kasala, kuma ramalana ba fage ne na aikata savo ko munana ayyuka ba, saboda ayyuka, a cikin watan ana ninninka su, "Kuma wanda ya yi rowa, to haqiqa yana yin rowa ne a kansa" [Muhammadu: 38].
"Kuma duk wanda ya kafirce, to kafircinsa zai koma kansa" [Faxir: 39].
"Kuma wanda ya yi tsirfar zunubi, to yana tsirfarsa ne, kawai a kan kansa" [Nisa'i: 111].
"Kuma wanda ya warware, to lallai yana warwarewan ne, kawai akan kansa" [Fat-h: 10].
Don haka; ku nuna wa Allah alkhairin da ke cikin rayukanku, saboda shaqiyyi, shi ne wanda a cikin watan ramalana aka haramta masa samun rahamar Allah.

Tilas, ku yi tanadi da shiri, kuma ku tuba, kuna masu bin dokoki da taqawa, saboda tsoron Allah shi ne mafificin guzuri, "Ya ku waxanda su ka yi imani, an wajabta muku azumi, kamar yadda aka wajabta shi ga waxanda su ka zo gabaninku, tsammaninku za ku samu taqawa" [Baqara: 183].

Ya ku Bayin Allah … !!!
Allah ya shar'anta yin azumin ramalana, kuma Ya farlanta muku shi ne, ba domin yunwa da qishi ba, ba kuma domin qishi da gajiyarwa ba, sai domin ku samu taqawa, saboda taqawa manufa ce abar nema, kuma "dayawa daga masu azumi, basu da komai daga azuminsu, face yunwa, da qishi", haka kuma masu sallar dare dayawa, basu da komai daga tsayuwansa, face hana kai barci, da gajiya.
"Kuma duk wanda bai bar maganar qarya ba, da yin aiki da ita, to Allah bashi da wata buqata; kan ya bar abin cinsa, da abin shansa".
"Kuma azumi garkuwa ne, don haka; idan yinin azumin xayanku ya zo, to kada ya yi 'rafasu' (wato, batsa cikin zance da iyali ko jima'i), kada kuma ya yi ihu, Idan wani ya zage shi, ko ya nemi yin faxa da shi, sai ya ce: Ni Mutum ne mai azumi".
Don haka; ba zai yiwu a kusanci Allah ta'alah a halin azumi da barin ababen da mutum ke sha'awa na halal ba, sai bayan an kusance shi, ta hanyar nisantar abinda Allah ya haramta, a cikin kowani hali, kamar qarya da zalunci, da yin ta'addanci ga mutane, cikin jinanensu da dukiyoyinsu da mutuncinsu.
Sai ku azumci watan ramalana, kuma ku kiyaye shi, kuma ku sani lallai ku masu haxuwa ne da Ubangijinku.

Ya ku bayin Allah … !!!
Ramalana, wata ne na gafara, wanda ake 'yanta mutane a cikinsa, sai ku kusanci rahamar Allah, kuna masu aiki da sababi, saboda shi Allah, Mai baiwa ne, Mai karamci, Mai yawan kyauta, An ruwaito daga Anas –Allah ya qara yarda a gare shi- yana cewa: "Annabi ya hau matakalan farko na minbari, sai ya ce: AMIN!
Sai kuma ya sake hawa matakala na biyu, sai ya ce: AMIN!!
Sa'annan ya hau matakala na ukun, sai kuma ya ce: AMIN!!!
Sannan, ya daidaita; ya zauna, Sai sahabbansa su ka ce: Akan me ka ce, AMIN?
Sai ya ce: Mala'ika Jibrilu ne ya zo mini, sai ya ce: Allah ya turbuxa hancin mutumin da aka ambace ka a wurinsa, sai bai maka salati ba, Sai na ce: Amin.
Sai ya sake cewa: Allah ya turbuxa hancin mutumin da ya riski iyayensa biyu, sai ba a gafarta masa ba, Sai na ce: Amin.
Sai ya ce: Allah ya turbuxa hancin wanda ya riski watan azumi, sai ba a gafarta masa ba. Sai na ce: Amin".
Ina neman tsarin Allah daga hanin aikata alkhairi da tavewa, da kuma mummunan qaddara, da riskar tavewa.

Kuma hadisi ya zo daga Abu-hurairah  -Allah ya qara yarda a gare shi-, ya ce: daga Annabi (SAW) yana cewa: "Wanda ya yi azumin ramadana yana mai imani, da neman lada: an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa.
Wanda kuma ya yi tsayuwar dare yana mai imani da neman lada an gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa.
Wanda kuma ya yi tsayuwar lailatul-kadri, yana mai Imani, da kuma neman lada to an gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa".

Ya ku, bayin Allah…!!
Azumi yana cikin manyan ibadodi da ake kusantar Allah, da kuma xa'oi, waxanda su ka fi girma, da aiyuka mafiya girman lada, kuma lallai shi azumi ibada ne na masu haquri, kuma guzuri ne ga masu taqawa, kuma tanadin masu neman samun rabo, ladansa kuma, yana da girma, kuma alherinsa yana da yawa, kuma amfaninsa bashi da makamanci, saboda azumi waraka ne ga cutuka, kuma yana bada lafiya da qarfi da kuzari da magani, ga rayuka da jiki, kuma yana tarbiyya, kuma yana bada hutu ga jiki, sama da haka kuma gaba xaya, azumi ya kasance xa'a ne ga Ubangiji, kuma gafara, ga zunubai,

Kuma ya ishi azumi falala, kasancewar Allah ta'alah, da ya raba ayyukan 'yan'adam kashi biyu, Ya sanya azumi ya kasance kaso xaya mai cin gashin kansa, kuma ya jingina shi ga kansa, sannan kuma, ya sanya sauran ayyukan 'yan'adam (gaba xayansu) a matsayin xaya kason,  An ruwaito daga Abu-Hurairah –Allah ya qara yarda a gare shi- yana cewa: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Dukkan  ayyukan xan adam ana ninninka masa, kyakkyawa da kwatankwacinsa goma, har zuwa ninki xari bakwai. Allah ta'alah ya ce: Sai dai kawai AZUMI, lallai shi kam nawa ne, kuma nine zan yi sakayya akansa, yana barin sha'awarsa da abincinsa domin Ni.
Mai azumi yana da farin cikin iri biyu, da zai yi su, farin cikin farko, a lokacin buxa-bakinsa, sai kuma wani farin ciki, a lokacin ganawa da Ubangijinsa.
Kuma lallai warin bakin mai azumi, ya fi daxi, a wurin Allah, fiye da turaren almiski".
            Kuma haqiqa Allah ya keve wa masu azumi shiga ta wata qofa daga cikin qofofin aljannah, wanda ba za a musu cinkoso ba ta wannan qofar, kamar yadda ya keve musu wata liyafa wanda ba za a yi tarayya da su cikin amfani da ita ba, An ruwaito daga Sahal bn Sa'ad –Allah ya qara yarda a gare shi- ya ce: Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Lallai a aljanna akwai wata qofa, wanda ake ce mata: AR-RAYYANU, Wanda masu azumi ke shiga ta cikinta ranar qiyama, babu wani wanda ba su ba, da zai shiga tare da su, za a ce: Ina masu azumi? Sai su shiga ta wannan qofar, Idan na qarshensu su ka shiga, sai a rufe ta, kuma babu wani da zai shiga ta wannan qofar, kuma duk wanda ya shiga zai sha ruwa, kuma duk wanda ya shiga ba zai ji qishi ba, har abada".

            Allah ya sanya ni da ku, daga cikin masu riskar azumi, waxanda za su samu karvuwa.

Ina faxan abinda ku ke ji, …

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, kuma ya azurta mu da bin sunnar AnnabinSa mai karamci, da kuma lazimtar shiriyarsa miqaqqa, ina faxin abinda ku ke ji wannan, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai, sai ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ke karvar tuba daga bayinSa, kuma ya ke yafe laifuka, kuma yana sane da abinda ku ke aikatawa.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya, rahamarSa ta game kowani abu, kuma ni'imarSa ta game komai.
Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa, kuma zavavve daga cikin halittarSa, kuma badaxinSa, kuma Shi ne ya fi jivintar muminai fiye da kansu, kuma matansa Uwayensu ne, kuma cetonsa shi ne tsiransu, addu'oinsa kuma shi ne rabautarsu,

Allah ya qara salati da sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da wanda ya shiryatu da shiriyarsa, kuma ya yi addu'ar neman yarda ga sahabbansa.

Ya ku bayin Allah !! …
Musiba a cikin addini ita ce, mafi girman musiba, (Malam) As-Saffariniy yana cewa: "Musibu; wata ta fi wata, sai dai kuma wanda ta fi su girma, ita ce musibar da ta kasance a cikin addini –Muna neman tsarin Allah daga hakan-, saboda ta fi kowace musiba, kuma mutumin da aka wawashe, shi ne wanda aka xauke masa addininsa;
Saboda,
dukkan karaya, ana fatar Allah zai yi xorin ta
Sai dai babu xori ga karayar da ta kasance, a addini
Don haka,
idan ka ga wani mutum, baya damuwa da abinda ya same shi ta vangaren addininsa, kamar ta fiskar aikata zunubai da laifuka, ko barin juma'a da sallar jam'i, da sakaci da lokutan xa'a, ko aukawa cikin haramun, kamar keta alfarmar shari'a, da qetare iyakokin Allah, da tsallake su, to ka san, lallai wannan mutumin an jarrabe shi, alal haqiqa, sannan ka qara sani cewa, lallai wannan ya mutu; shi yasa ba ya jin raxaxin wannan musibar".
Musibarsa ta yi girma, kuma ta fanqama, kuma abin a masa taziya ya yi girma, nadamarsa kuma za ta yi tsayi, Wa? Mutumin da ya tozarta damarsa ta yin azumin ramadana, har lokacin hakan ya wuce.

Haqiqa an gafarta zunubai, kuma an suturce aibuka, an kankare laifuka, kuma an yi afuwa ga kura-kurai, an xaukaka darajoji, an ninnika kyawawa, shi kuma, dolon an haramta masa (waxannan gaba xaya), kuma ya halaka kansa, kuma bai yi rahama ga raunin ransa ba, kuma bai xora karayar ransa ba, ya kuma wuce iyakar shari'a akan haka, muguntarsa ta  halaka shi, kuma walaqancinsa ya tavar da shi, baqin ciki kuma, ya dabaibaye shi.
Ya mai neman aikata alkhairi, ka fiskanto!
Ya mai neman aikata sharri –kaitonka- ka taqaita!

Ya kai mutumin da ya yi sakaci a ramadanan da ya gabata, ya tozarta watan, ya bar shi ya wuce, Sai kuma Ubangijinsa ya masa baiwar qarin lokaci a rayuwa, har ya sake riskar wani ramadanan na daban, To ka gode wa Allah, a kan wannan ni'imar (riskar ramadana), kuma ka fiskanci Ubangijinka, gabanin mutuwa ta zo kwatsam, ko rayuwarka ta qare cikin tavewa, ko qarfinka ya yi rauni, furfura kuma ta yi qarfi,
A lokacin, (babu abinda zai rage) sai, YA HASARATA! YA KAITONA!! YA BAQIN CIKINA!!!
"Ya Ubangijina! Don me ba ka yi mini jiinkiri ba zuwa ga wani ajali makusanci, domin in gaskata, kuma in kasance daga salihai" [Tagabun: 10].
"Ya Ubangijina! Ku mayar da ni (duniya) * tsammanina in aikata aiki na kwarai, cikin abinda na bari, Kayya, lallai ne ita kalma ce da ya ke faxinta, alhali a baya gare su, akwai wani shamaki, har ranar da za a tayar da su" [Mu'uminuna: 99-100].
"Kuma Allah ba zai jinkirta wa rai ba idan ajalinta ya zo" [Munafiquna: 11].
KAITONSA!!! Kuma sannan KAITONSA!!!

Ya ku bayin Allah…!!
Lallai wahalar da ke cikin aikin xa'a tana tafiya, sai daxinta ya wanzu a cikin wannan rayuwar, Ladanta kuma a lahira, taska ce da aka tanada,
Kuma daxin da ke cikin savo yana tafiya; ya qare, sai tavewa ta wanzu na tsawon zamani, wahalar cikinta kuma na tsawon rayuwa, A lahira kuma uquba, da hasara.
Daxi na qarewa daga mutumin da ya samu madararta
Daga haramun, sai zunubi da aibi su wanzu,,,

Aqibar mummunan abu yana wanzuwa a qarshensa
Babu alheri, ga daxin da wuta ce a bayansa,,,

Daga qarshe,
Ya ku bayin Allah…!!
            Lallai Allah ya kwararo mana ni'imomi, kuma ya karrama mu da aminci da zaman lafiya, ya kuma nisantar da mu fitintinun da mu ke ganin suna sauka ga wasunmu a wannan zamanin, har su halaka shuki da 'ya'ya, sannan su rarraba haxin kan mutane.

            Don, haka, Ya wajaba akanmu mu yi ta godiya a kowani lokaci, kuma GODIYA TA TABBATA GA ALLAH a kan ni'imar zaman lafiya da imani, kuma godiya ta qara tabbata ga Allah, wanda mu ke roqon ya kai mu watan ramadana.
            Kuma wajibi akanmu, mu tsayu sahu xaya, a fiskar wanda ransa ta ke saqa masa, ya kawo mana barazana ga zaman lafiyarmu, ko kuma ya shuka fitina a cikin tafiyarmu da haxin kanmu, ko domin ya raunata qarfinmu.
            Saboda abinda ake nufin a lalata mana –Ya ku taron 'yan'uwa- shine aqidarmu da addininmu,

Kuma duk lokacin da musulmai su ke shirin shiga wani lokaci na musamman, daga cikin lokutan addininsu, sai a qulla musu makirci, domin a hana su amfana da shi, a kuma kikkitsa musu qulle-qullen fitina.
Kuma lokutan zartar da rukunnan musulunci, masu shaida akan haka; lokutan ramadana suma sun shaidi hakan, lokutan aikin hajji da umrah suma sun shaidi hakan,

Sai dai kuma imaninmu da Allah, da amintuwar da mu ka yi da jagororinmu shiryayyu, da aqidarmu tabbatacciya, za su sanya masu ha'intarmu yin hasara, rabonsu kuma ya zama tavewa, kaidin da su ka qulla kuma, ya koma ga qirazansu, saboda "makircin cuta baya faxawa, sai ga mutanensa" [Faxir: 43].
Kuma daularmu ba za ta canza daga aqidarta, ko haxin kanta ba.
Kuma da sannu Allah zai kiyaye amincinmu, da kuma addininmu, "Sai su bauta wa Ubangijin wannan xakin * Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Quraish: 3-4].

            Ya Allah! Ka kiyaye wannan qasar da kiyayewanka,
 Ya Allah! Ka dawwamar mata da amincinta da zaman lafiyanta, da haxin kanta,
Ya Allah! Ka kiyaye ta daga fitintinu; wanda su ka bayyana daga cikinsu da waxanda su ka vuya,
Ya Allah! Wanda ya nufi qasar nan da mummuna, ka shagaltar da shi da kansa, kuma ka mayar da kaidinsa zuwa ga qirjinsa

Bayin Allah
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
Ya Allah! Ka yi salati da sallama wa Annabi Muhammadu, kuma ka yarda da khalifofinsa shiryayyu masu shirayarwa;    Abubakar da Umar da Usmanu da Aliyu, da sauran sahabbai gabaxaya, ka haxa da mu, da baiwarka, ya mafi baiwar masu kyauta.

,,,          ,,,          ,,,



TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...