2019/10/09

AMFANAR DA MUTANE Dr Salah Albudair 12 safar 1441H












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 12/SAFAR/1441H
daidai da 11/OCTOBER/ 2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. SALAH BN MUHAMMADU ALBUDAIR





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
AMFANAR DA MUTANE YANA DAGA MAFI ALHERIN SIFOFI
(نفع البرايا من خير السجايا)
Shehin Malami wato: Abdulmuhsin bn Muhammadu  Alkasim –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: AMFANAR DA MUTANE, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
        Ya ku Musulmai …
Amfanar da Mutane yana cikin mafi alherin sifofi,
MAFIL ALHERIN RANAKUN MUTUM SHINE YININ DA YA AMFANAR
KUMA AIKATA ALKHAIRI SHINE MAFI WANZUWAR ABINDA YA AIKATA
Kuma Mutum mai yawan amfanarwa mai yawaita taimako shine: Wanda ya amfanar da Mutane da dukiyarsa, da kuma matsayinsa, da iliminsa, da dabi'unsa, da kyautatawarsa, kuma wanda alherinsa yake da gwabi, kyautarsa dayawa, mai amfani cikin aikinsa, mai faffadar tukunya, tafin hannunsa kamar girgije ne, yana dawwama akan sada zumunci da kyauta da sadakoki, kuma yana tallafawa gajiyayye, yana falala ga mai nemanta, kuma yana kokarin tsamar da mai neman agajinsa mai neman taimakonsa, kuma yana ilmantar da jahili mai neman shiryawa, kuma yana jin-kan maraya, kuma yana kokarin share hawayen mai bakin ciki, kuma yana hulda da Mutane, cikin so da kauna, da kyautatawa, da tausasawa.
MUTANE SUNA CACIRINDO A KOFAR GIDANSA
AI DADDADAR MASHAYA, YANA DA YAWAN CUNKOSO

TSUNTSU YANA SAUKA A WURIN DA KWAYA TAKE A WATSE
KUMA ANA MAMAYE GIDAJEN MASU KARAMCI DA KYAUTA

Annabin Allah Isah –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Kuma ya sanya ni mai albarka a duk inda na kasance" [Maryam: 31].
Malaman tafsiri suka ce, wato Allah ya sanya ni na zama mai yawan amfanarwa, a duk inda na fiskanta, mai biyan bukatu, mai karantar da alkhairi, mai umurni da kyakkyawa, mai hani ga mummuna, mai albarka da nau'oin albarkoki.
Kuma Mutumin da yafi amfanar da halittu gaba daya shine Annabinmu Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- "Yana masa nauyi abinda yake wahalar da ku, mai kwadayi ne akanku, kuma ga muminai Mai yawan tausasawa ne Mai jin kai" [Maryam: 128].
BAN TABA GANI, KO NA JI LABARIN WANI A CIKIN MUTANE
GABA DAYA, KAMAR ANNABI MUHAMMADU BA

Kuma duk wanda ya kafa kansa domin amfanar da Mutane sai ya rayu a gaba-gaba ana girmama shi, kuma fiska abar mutuntawa,
YABONSA DA DADI A BAKUNAN MUTANE
KUMA YABONSA YANA KASANCEWA A KOWANE WURI
Matsayinsa zai rika daukaka, kuma ambaton zai yi dadi
DA ZAKA RIKA BAYARWA A LOKACIN DA AKE ROKONKA
SAI RANKA TA ZAMA MAI BAYARWA, KUMA KOWANE MASOYI YA KAUNACE KA

Ana cewa, Cikar hankali, da kyakkyawar ambato basu cika haduwa ba.
Wani kuma ya ce: Hana kyauta, munana zato ne ga abin bauta.

DUKIYAR DA TA GADAR WA MA'ABUTARTA SAMUN YABO BATA TOZARTA BA
SAI DAI DUKIYAR MAROWACI ITACE TAKE TOZARTA

Daga cikin Mutane akwai wanda babu abin tatsa ga hantsarsa, kuma ba a kwadayin samun amfanarwarsa,
MUTUM, MATUKAR ZAMANSA DA DAI, BAI YI FA'IDA BA
TO GIRGIJE NE WANDA RANA TA TARE, BAI ZUBO DA RUWA BA, KUMA BAI YI TAFIYA BA

Wasu daga cikin Mutane, namijin dabino ne; basu da abin tsinka, kuma bashi da inuwa, saidai wanda zai yi kansa
Sai ka kasance, ga halittun Allah mai yawan amfanarwa, mai amsa wa mabukata, kuma ka mikar da hannunka domin bada alkhairi, ka mika tafinka.
An ruwaito daga Abu-hurairata –رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Shin ba zan baku labarin mafi alherinku daga mafi sharrinku ba? Sai Wani Mutum ya ce: E, ka bamu labari Ya Ma'aikin Allah, sai ya ce: Mafi alherinku shine wanda ake fatan alherinsa, ake aminta daga sharrinsa, kuma mafi sharrinku shine wanda ba a fatan samun alherinsa, kuma ba a amintuwa daga sharrinsa", Ibnu-Hibbana ya ruwaito.
Kuma an ruwaito daga Abdullahi dan Umar –رضي الله عنهما- daga Annabi –صلى الله عليه وسلم- lallai shi ya ce: "Mafi soyuwan Mutane a wurin Allah shine wanda yafi amfanar da Mutane. Kuma mafi soyuwan ayyuka a wurin Allah Mabuwayi da daukaka shine farin ciki wanda ka shigar da shi zuciyar Musulmi, ko ya yaye masa bakin ciki, ko ya biya masa bashi, ko ka kawar masa da wata yunwa, kuma wallahi na yi tafiya tare da dan'uwana Musulmi cikin bukatarsa, yafi soyuwa a wurina fiye da na yi i'itikafi a wannan masallacin, wato Masallacin Madina- na tsawon wata guda", Dabaraniy ya ruwaito shi a mu'ujamul Ausad ya ruwaito shi
Kuma an ruwaito daga Abu-hurairata -رضي الله عنه- lallai shi ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya kwaranye wa Musulmi wani bakin ciki daga bakin cikin Duniya, Allah zai kwaranye masa bakin ciki daga bakin cikin ranar kiyama. Kuma idan Mutum ya saukaka wa wanda yake cikin wahala, to Allah zai saukaka masa a Duniya da Lahira. Kuma idan Mutum ya rufa asirin Musulmi a Duniya, Allah zai rufa asirinsa a Duniya da Lahira, Allah yana taimakon bawa matukar Bawan yana taimakon dan'uwansa", Muslim ya ruwaito shi.
Nawai ya ce: "A cikin wannan hadisin, akwai falalar biya wa Musulmai bukatu, da amfanar da su da abinda ya saukaka, na ilimi, ko dukiya, ko taimako, ko shawari a cikin wata maslaha, ko nasiha, da makamancin haka".
BIYA BUKATA GWARGWADON IKO,
KUMA KA ZAMA MAI YAYEWA DAN'UWANKA BAKIN CIKI

LALLAI MAFI ALHERIN KWANAKIN MUTUM
SHINE YININ DA YA BIYA WA WASU BUKATU

Ya kai Bawan Allah!!!
Ka bayar da kyauta, kuma ka amsa wa Mutumin da yake cikin yanayi, kuma kada ka raina abin hannunka da zaka yi kyauta da shi, kuma kada ka ga karacin hidimar da zaka gabatar da ita, domin kananan ayyukan sharri, wanda ya aikata su zai same su a halarce dalla-dalla, kuma koda gwargwadon zarra ne na alkhairi, wanda ya aikata su zai same su a cike, a ajiye,
An ruwaito daga Abu Jaryin Alhujaimiy –رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Kada ka raina kyakkyawan abu; ka ki aikata shi, koda ka bada kyautar kulla igiya ne, kuma koda ka diba daga gugarka zuwa ga kwaryar wanda ya nemi shayarwa ne, kuma koda ka hadu da dan'uwanka Musulmi alhalin fiskarka tana shumfude (murmushi) a gare shi, kuma koda ka debe kewa ga wanda yake cikinta ne da kanka, ko kuma ka bayar da kyautar igiyar takalmi", Ahmad da Abu-dawud da nasa'iy suka ruwaito shi.

Kuma an ruwaito daga Jabir dan Abdullahi –رضي الله عنه- ya ce: Wata kunama ta harbi wani daga cikinmu, alhalin muna zaune tare da Annabi –صلى الله عليه وسلم- sai wani Mutum ya ce: Ya Ma'aikin Allah, shin ba zan masa addu'ar rukiyya ba? Sai Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Duk wanda ya samu damar ya amfanar da dan'uwansa to ya aikata", Muslim ya ruwaito shi.
Don haka, kada ka hana gararka, kuma kada ka rike falalarka, kada ka killace alkhairinka, kuma kada ka yi rowa, kuma kada ka nuna kosawa, kada ka nuna takura ga mai rokon da talauci ya bukatar da shi zuwa ga roko, ka bashi koda kadan ne, ko ka mayar da shi da kyakkyawiyar magana, kuma kada ka yi kokarin hada masa zafin talauci da kaskancin dake cikin roko da kausasa harshe da jafa'i.
Kuma alkawarin tallafin mai karamci cika wa ne (ba ajalan ba), Shi kuma alkawarin marowaci jinkiri ne, da lalubo uzuri. Kuma bada uzuri da laffuza masu kyau shi yafi alkhairi fiye da jinkirtarwa mai tsawo. Kuma idan ka yi nufin bada ni'ima to ka kyautata, idan kuma bukatar ba za ta samu ba, to ka fito da bayani a fili.
An ruwaito daga Abdullahi dan Amru –رضي الله عنهما- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai Allah a wurin wasu Mutane, yana da ni'imomin da ya tabbatar da su a wurinsu –ma'ana: ya dawwamar musu da su- matukar dai suna cikin bukatun Musulmai; basu kosa daga gare su ba. To amma idan suka kosa daga biya musu bukatu, sai Allah ya dauke ni'imomin zuwa ga wasunsu"Dabaraniy, a cikin mu'ujamul kabir ya ruwaito shi.
KA KYAUTATA MATUKAR AKWAI DAMA DA IKO
DOMIN DAMAR, BA DOLE TA DAWWAMA GA MUTUM BA
Ina fadar abinda kuke ji, kuma ina neman gafarar Allah, sai ku nemi gafararsa, lallai shi ya kasance ga masu mayar da lamuransu gare shi Mai yawan gafara.

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,


HUDUBA TA BIYU

Ya ku Musulmai…
Mustahabbi ne, yin ceto (shafa'a) a cikin al'amuran alheri (wato sanya baki domin biya ma wani bukata), saboda yin hakan, wani amfani ne da Mutumin da ya aikata hakan zai amfanar da wanda ya nemi ceton dominsa.
Kuma idan Mutum ya yi ceto mai kyau, wanda yake fatan ya amfanar da halittu, da kuma biyan bukatun Mutane, to hakika ya yi kyauta mai gwabi, kuma zai samu yabon Mutane.
An ruwaito daga Abu-Musal Ash'ariy –رضي الله عنه- ya ce: Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ya kasance, idan wani mai bukata ya zo masa, sai ya fiskanci abokan zamansa, sai ya ce: "Ku yi ceto; sai a baku lada, Allah kuma zai hukunta abinda ya so ta harshen ManzonSa" Bukhariy da Muslim suka ruwaito.
KA TAIMAKE SHI KODA DA MATSAYINKA NE, WANDA YA ZO MAKA DA WATA BUKATA
SABODA, KYAUTA DA MATSAYI, YAFI YIN KYAUTAR DUKIYA
Imamus Shafi'iy –رحمه الله تعالى- ya ce: "sanya baki domin yin ceto, shine a madadin zakka a cikin mutunci".
AN FARLANTA MINI FITAR DA ZAKKAR ABINDA HANUNA YA MALLAKA
AMMA BADA ZAKKAR MATSAYINA KUMA SHINE, NA YI TAIMAKO, KUMA NA YI CETO

DON HAKA, IDA KA MALLAKI ABU, TO KA YI KYAUTA,
IDAN KUMA BAKA SAMU IKO BA, TO KA YI IYA KOKARINKA WAJEN GANIN KA AMFANAR
Kuma duk wanda ya yi ceto, domin a kai ga wata da'a, ko don samun sauki cikin abu mai wahala, ko janyo alheri, ko domin tunkude wani sharri, ko domin sulhu tsakanin masu husuma biyu, ko ya yi ceto domin wanda ake nema masa hakkin ya kai zuwa ga wani hakki nasa, duk wanda ya aikata haka, yana da rabo daga alherin ceton da ya yi da kuma ladanta.

Wanda kuma ya yi ceto, domin lalata wani hakki, ko domin tabbatar da wata barna, ko domin tabbatar da zalunci, ko ya yi domin a gabatar da Mutumin da bai cancanta ba, akan wanda ya cancanta, ko kuma domin a baiwa wanda bashi da kwarewa, a kuma dakushe mai kwarewa, ko don bada aiki ga wanda aka nema masa ceto, a kuma haramta wanda ya fishi cancanta, wanda ya aikata hakan, to lallai yana da zunubin wannan ceto, mummuna, na zalunci da ya aikata.
Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Wanda ya yi ceto, mai kyau, zai samu rabo daga gare shi. Wanda kuma ya yi ceto mummuna, to zai samu rabo daga cikinsa" [Nisa'i: 85].

Kuma karbar kyauta, sakamakon amfanar Mutane da matsayinka da kuma saboda ceto, yana tozarta ladan ceton, kuma yana tafiyar da falalarta, don haka, kada ka yi gaggawar karbar ladan cetonka, kuma ka ajiye shi a matsayin guzurin domin lahirarka.

Abdullahi dan Mas'ud –رضي الله عنه– ya ce: "Duk wanda ya yi ceto, domin a dawo da wani hakki, ko domin ya dauke wani zalunci, sai aka masa kyauta, ya karba, to wannan haramun ne".

Kuma an ruwaito daga Abu-Umamah Albahiliy –رضي الله عنه- ya ce: Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya yi wani ceto ga dan'uwansa, sai aka dauko kyauta aka bashi akanta, to lallai hakika ya fada cikin wata kofa daga cikin kofofin riba", Ahmad da Abu-dawud sun ruwaito, saidai akwai magana akan ingancinsa, Amma wasu Maluman sun ce hadisi ne hasan.

SAI KU YI SALATI DA SALLAMA, GA MUHAMMADU MAI SHIRYAR DA HALITTU GABA DAYA
DOMIN IDAN MUTUM YA MASA SALATI GUDA DAYA, ALLAH ZAI NINKA MASA DA WANNAN HAR GUDA GOMA
…

2019/10/03

YARADAR ALLAH TA'ALAH 5 Safar 1441H Dr Abdulmuhsin Alkasim












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 5/SAFAR/1441H
daidai da 4/OCTOBER/ 2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ABDULMUHSIN BN MUHAMMADU ALKASIM





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
YARDAR ALLAH TA'ALAH
(رضا الله)
Shehin Malami wato: Abdulmuhsin bn Muhammadu  Alkasim –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: YARDAR ALLAH, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, to babu mai shiryar da shi.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa.
Salatin Allah su kara tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.

        Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da takawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku yi riko a Musulunci da igiya mai karfi.

        Ya ku Musulmai …
Sunayen Allah sune mafiya kyawu, SifofinSa kuma masu girma. Kuma  a cikin dukkan hakan Allah yana da sifa madaukakiya. Kuma imani da su rukuni ne na Tauhidi. Kuma da hakan aiki yake zama ingantacce.
Kuma YANA DAGA SIFOFIN ALLAH WADANDA SUKA ZO CIKIN ALKUR'ANI DA SUNNAH; SIFAR YARDA (الرضا); Domin Allah Ta'alah yana fushi kuma yana yarda, kuma duka biyun ba kamar na wani daga cikin Halittu ba ne. Kuma akan tabbatar da wannan sifar, Sahabbai da Tabi'ai da magabatan Al'umma suka shude.
Kuma domin neman yardar Allah ne, AnnabawanSa da Waliyyai, da BayinSa; Salihai suka zage damtse (suka yi fadi-tashi), Allah Ta'alah ya ce: "Kuma daga cikin Mutane akwai wanda yake sayar da ransa, domin neman yardar Allah, Kuma Allah Mai tausayi ne ga Bayi" [Bakara: 207].
Kuma annabi Isma'ilu –عليه السلام- Allah ya yabe shi a cikin littafinSa da cewa, ya yi babban rabo da samun yardarSa, ya ce: "Kuma ka ambaci Isma'ila a cikin littafi; lallai shi ya kasance mai gaskiyar alkawari, kuma ya kasance Manzo, Annabi * Kuma ya kasance yana umurtar Iyalansa da salla da zaka, kuma ya kasance yardajje a wurin UbangijinSa" [Maryam: 54-55].
Kuma annabi Musa –عليه السلام- UbangijinSa ya masa alkawarin ganawa a gefen dutsen Dur, sai ya yi gaggawa zuwa gare shi, domin kwadayin samun yardarSa, Allah ya ce: "Kuma menene ya gaggautar da kai ga barin Mutanenka, Ya Musa? * Ya ce: Sune wadancan ga su a bayana (za su iso), kuma na yi gaggawa zuwa gare ka ne, domin ka yarda" [Daha: 83-84].

Kuma annabi Sulaiman –عليه السلام- ya roki UbangijinSa, da cewar ya cusa masa aikata abinda zai yardar da shi, ya ce: "Ya Ubangina! Ka cusa mini in gode wa ni'imarka wanda ka ni'imta ta a gare ni, da kuma ga iyayena biyu, kuma in aikata aiki na kwarai wanda ka yarda da shi" [Naml: 19].
Kuma annabi Zakariyya –عليه الصلام- ya kirayi UbangijinSa, da ya azurta shi da yaro wanda ya yarda da shi, a inda ya ce: "Kuma ka sanya shi yardajje, Ya Ubangiji" [Maryam: 6].
Kuma Allah ya sifanta annabinmu Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- da sahabbansa, da kyautata aiki, suna masu neman yardar Allah, Allah Ta'alah ya ce: "Muhammadu Manzon Allah ne, kuma wadannan da suke tare da shi, masu tsanani ne ga kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, kana ganinsu suna ruku'u da sujjada, suna neman falala daga Allah da yardarSa" [Fat-h: 29].
Kuma domin neman yardar Allah ne, Muhajirawa suka kaura suka bar garinsu, Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Da kuma, ga Matalauta masu hijira, wadanda aka fitar daga gidajensu da dukiyoyinsu, suna neman falala daga Allah, da kuma yarda" [Hashr: 8].
Kuma Mumini yana tawassuli da yardar Allah domin ya tsare shi daga fushinSa, kamar yadda Annabi –عليه الصلاة والسلام- yake neman tsari da hakan a cikin fadinsa: "Ya Allah lallai ni ina neman tsari da yardarka, daga fushinka", Muslim ya ruwaito.
Kuma kyan aiki da karbuwarsa suna rataya akan tsarkake niyya ga Allah, ta hanyar neman yardarSa, Allah Ta'alah ya ce: "Babu alheri cikin yawancin ganawarsu, sai ga wanda ya yi umurni da wata sadaka, ko wani alheri, ko kuwa sulhu a tsakanin Mutane, Kuma idan Mutum ya aikata hakan, yana neman yardar Allah, to lallai za mu bashi lada mai girma" [Nisa'i: 114].
Kuma ciyarwa karbabbiya mai albarka, itace wanda sahibinta ya nemi yardar Allah da ita, Allah ya ce: "Kuma sifar wadanda suke ciyar da dukiyoyinsu domin neman yardar Allah, da tabbatarwa daga kansu, kamar misalin lambu ne a wuri mai jigawa, wanda mamakon ruwa ya samu, sai lambun ya bayar da amfaninsa ninki biyu. To idan ba ruwa mai yawa ne ya same shi ba, sai yayyafi (ya isar masa), Kuma Allah ga abinda kuke aikatawa Mai gani ne" [Bakara: 265].
Kuma Allah ya girmama alfarmar Mahajjata da masu umrah, wadanda suke neman yardarSa, a inda yake fadi: "Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku keta alfarmar wuraren yin bauta wa Allah, da kuma watanni masu alfarma, da hadaya, da ratayar rakumar hadaya, da Masu nufin daki mai alfarma suna neman falala daga Ubangijinsu da yarda" [Ma'ida: 2].
Musulmi yana lazimtar neman yardar Allah a halin tafiye-tafiyensa da zamansa a gida, da halin farin cikin da bakin ciki, da dukkan halinsa gaba daya, domin a halin bulaguro ya kan bude tafiyarsa da rokon Allah, cewa ya saukake masa dukkan abinda zai yardar da shi, sai ya ce: "Ya Allah, lallai muna rokonka a cikin bulaguronmu wannan, ayyukan biyayya da takawa, da kuma aikin da zaka yarda", Muslim ya ruwaito.
Kuma idan musiba ta sauko wa Musulmi, babu abinda zai kasance masa face abinda zai yardar da Allah, Ibrahim; 'Dan Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya rasu, sai Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai ido yana yin hawaye, zuciya kuma tana yin bakin ciki, saidai ba za mu fadi wani abu ba, face abinda Ubangiji zai yarda da shi, Kuma lallai mu dangane da rabuwa da kai –Ya Ibrahim- tabbas masu bakin ciki ne", Bukhariy ya ruwaito.
Yana daga RAHAMAR ALLAH DA KARRAMAWARSA Yadda ya shar'anta wa BayinSa addinin da yarje musu shi, Allah Ta'alah ya ce: "A yau, na kammala muku addininku, kuma na cika muku ni'imata akanku, kuma na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku" [Ma'ida: 3].
Kuma cikin aiki da addinin Musulunci abubuwan da suke hukunta yardar Allah suke; domin imani da Allah shine sababin jin dadin Duniya da Lahira, kuma yana gadar wa Bawa samun yardar MajibincinSa, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne wadanda suka yi imani, kuma suka yi ayyukan kwarai, wadannan sune mafifita alherin halittu * sakamakonsu a wurin Ubangijinsu shine gidajen Aljannar zama, koramu suna gudana daga karkashinta, suna masu dawwama a cikinta har abada. Allah ya yarda da su, suma sun yarda da shi. Wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsoron UbangijinSa" [Bayyinah: 7-8].
Kuma duk wanda ya yi imani kuma ya aikata kyakkyawan aiki, to lallai ya bi hanyar samun yardar Ubangiji, Allah Ta'alah ya ce: "Idan kuka kafirce to lallai Allah wadatacce ne ga barinku, kuma bashi yarda da kafirci ga bayinSa, kuma idan kuka gode yana yarda da godiyar a gare ku" [Zumar: 7].
Tauhidi shine kadaita Allah da bauta, kuma shine mafi girman aiki a wurin Allah, Kuma Allah ya yarje wa BayinSa; cewa: Su bauta masa; kada su hada shi da komai, kuma su yi riko da igiyar Allah gaba daya; kada su rarraba, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai Allah yana yarje muku abu uku, kuma yana kiye muku abu uku; yana yarje muku; ku bauta masa kada ku hada shi da komai, kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya; kada ku rarraba", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma wanda ya tabbatar da Tauhidi sai Allah ya yarda da shi, Allah Ta'alah ya ce: "Wadannan Allah ya rubuta imani a cikin zukatansu, kuma ya karfafa su da wani ruhi daga gare shi, kuma zai shigar da su gidajen Aljannar da koramu suke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu, Allah ya yarda da su, suma sun yarda da shi" [Mujadala: 22].
Kuma idan Mutum ya taimaki addinin Allah, sai Allah ya karfafe shi, kuma ya yarda da shi, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne hakika, Allah ya yarda da Muminan nan, a lokacin da suke maka mubaya'a a karkashin bishiya, domin ya san abinda ke zukatansu, sai ya saukar da natsuwa a kansu, kuma ya saka musu da wani cin nasara makusanci" [Fat-h: 18].
Kuma gaskiya shine tushen imani, kuma shine yake nuna samuwarsa, kuma da gaskiya Bawa yake amfana a Duniyarsa da lahirarsa, Allah Ta'alah ya ce: "Wannan shine yinin da gaskiyar masu gaskiya take amfanarsu, suna da gidajen Aljannar da koramu suke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada, Allah ya yarda da su, kuma sun yarda da shi, Wannan ne rabo mai girma" [Ma'ida: 119].
Godiya ita ce dabaibayi ga ni'imomi, kuma da ita ni'imomin suke karuwa suke dawwama. Kuma yana daga cikin manyan sakayyarta: yadda Allah yake yarda ga Masu godiya, cikin hadisin Mutane uku daga Banu-Isra'ila; wato kuturu da mai kora da makaho, ya ce: "Sai Mala'ika ya zo wurin Makaho, ya ce: Ni Mutum ne, miskini, matafiyin da dabara ta kare masa a tafiyarsa; don haka; bani da guzuri yau, sai a wurin Allah, sannan a wurinka; Ina rokonka da wanda ya dawo maka da ganinka (Allah) ka bani akuya daya, da zan yi guzuri da ita a cikin bulagurona, sai ya ce: Hakika na kasane makaho, sai Allah ya dawo mini da ganina, kuma matalauci, sai ya wadatar da ni; don haka; ka dauki abinda kake so, ina rantsuwa da Allah, ba zan musa maka akan dukiyar da ka dauke ta don Allah ba, a yau. Sai ya ce: Rike dukiyarka, domin jarrabar ku aka yi; kuma lallai hakika Allah ya yarda da kai, kuma ya yi fushi ga abokanka biyu", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Bawa ba zai wadatu ga barin ci da sha ba, Kuma yana daga falalar Allah, yadda Allahn yake ciyar da BawanSa ya shayar da shi, Kuma idan Bawan ya yi godiya ga Ubangiji akan haka, sai Allah ya yarda da shi, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Allah yana yarda ga Bawa; ya ci abin ci, sai ya gode masa akan haka, ko ya sha abin sha, sai ya gode masa akansa", Muslim ya ruwaito.
        Duniya a kewaye take da bala'i da gurbatattun lamura, Kuma Idan Mutum ya yi hakuri akan bala'ointa sai ya rabauta, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai girman sakamako ya kan zama gwargwadon girman bala'i, kuma lallai Allah Ta'alah idan ya so Mutane sai ya jarrabe su; wanda ya yarda yana da yarda, wanda kuma ya yi fushi, yana da fushi", Tirmiziy ya ruwaito shi.
Harshe, mabudin alheri ne da sharri; kuma da fadin kalma mai dadi Mutum zai riski yardar MahaliccinSa, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai Bawa ya kan fadi kalma cikin yardar Allah Ta'alah, bai dauke ta a bakin komai ba, sai Allah ya daga darajojinsa da ita", Bukhariy ya ruwaito.
Kamar yadda Allah yake son tsarkin zuciya, to lallai yana yarda da tsarki na zahiri, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Aswaki tsarki ne ga baki, kuma abin yarda ne ga Ubangiji", Tirmiziy ya ruwaito shi.
Kuma idan kiyama ta tsayu, dukiya ko 'ya'ya ba za su yi amfani ba, sai ga wanda ya je wa Allah da zuciya lafiyayya, kuma babu mai yin ceto, face bayan izinin Allah, da yardarSa ga Mai ceton, Allah Ta'alah ya ce: "A wannan ranar, ceto baya yin amfani, face wanda Allah ya masa izini, kuma ya yarda da zancensa", [Daha: 109].
Kuma ceton ba zai amfanar ba, face wadanda Allah ya yarda da su, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma basu yin ceton, face ga wadanda ya yarda", [Anbiya'i: 28].
Kuma a cikin Aljanna ana yin ni'ima ga Muminai da abinda ido bai taba gani ba, kunne bai taba ji ba, kuma bai taba darsuwa ga zuciyar wani Mutum ba, Kuma yana cikin manyan ni'imomin da suka fi girma, yardar Ubangijinsu a gare su, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma Allah ya yi wa'adi ga Muminai maza da muminai mata, da gidajen Aljannah, wadanda koramu suke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu, da wuraren zama masu dadi a cikin gidajen Aljannar zama, Kuma yarda daga Allah ita ce mafi girma, Wannan shine babban rabo" [Tauba: 72].
Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai Allah zai ce wa ma'abuta Aljannah: Ya Ma'abuta Aljanna! Sai su ce: Mun amsa maka –Ya Ubangijinmu-, kuma dukkan alheri suna hannayenka, Sai ya ce: Shin kun yarda? Sai su ce: Me zai sa ba za mu yarda ba, Ya Ubangiji, alhalin ka bamu abinda baka bayar da shi ga wani daga cikin Halittunka ba? Sai ya ce: Shin ba zan baku abinda yafi muku hakan ba? Sai su ce: Ya Ubangiji: Wane abu ne yafi hakan girma? Sai ya ce: Zan saukar muku da yardata akanku; ba zan yi fushi da ku a bayansa ba har abada" [Bukhariy da Muslim suka ruwaito].

BAYAN HAKA:
YA KU MUSULMAI
Samun rabo gaba dayansa, yana cikin riko da addini, kuma shine yake janyo yardar Allah, kuma idan Mutum ya lazimci abinda yake yardar da Allah, Sai Allah ya yarda da shi, kuma ya yardar da shi. Kuma idan Bawa ya nemi yardar UbangijinSa kuma ya fifita ta akan duk abin da ba ita ba, to lallai Allah zai yarda da shi, kuma ya sa Mutane su yarda da shi.
Kuma wanda ya nemi yardar Mutane da fushin Allah, sai Allah ya yi fushi da shi, kuma ya sanya Mutane su yi fushi da shi.

A'UZU BILLAHI MINAS SHAIDANIR RAJIM
"Shin wanda ya bibiyi yardar Allah, zai zamo kamar wanda ya komo da fushin Allah! Kuma makomarsa Jahannama ce, kuma tir da ita a matsayin makoma" [Ali-imrana: 162].


Allah ya mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, ,,,     
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,


HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa;  Godiya kuma tasa ce bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya; Ina mai girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi dadin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnunkuwa.

Ya ku Musulmai…
Wanda Allah ya yarda da shi, sai ya karrama shi da ni'imomi, a cikin Aljannah, Allah Ta'alah ya ce: "Wadanda suka kyautata, suna da Aljanna da kari" [Yunus: 26].
Karin kuma shine: Dubi zuwa ga fiskar Allah Mai karamci, kamar yadda Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya fassara ayar da hakan, kuma idan Muminai suka yi dubi ga fiskar Ubangijinsu, to hakan yafi soyuwa a wurinsu akan komai, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Idan Ma'abuta Aljannan suka shiga Aljannah, Sai Allah Tabaraka wa Ta'alah ya ce: Kuna son wani abu na kara muku? Sai su ce: Ashe baka haskaka fiskarmu ba? Ashe baka shigar da mu Aljannah, kuma ka tsamar da mu daga fadawa Wuta ba? Sai ya yaye shamaki. Ba a baiwa 'yan Aljanna wani abu da yafi soyuwa a gare su fiye da kallon fiskar Ubangijinsu ba", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma idan Muminai suka yi dubi ga fiskar Allah Mai karamci, sai su kara kyawu da kwar jini, Allah Ta'alah ya ce: "Wasu fiskoki a wannan ranar masu annuri ne * zuwa ga Ubangijinsu masu dubi ne" [Kiyama: 22-23].
Alhasan –رحمه الله– ya ce: "Sun kalli Ubangijinsu, sai suka samu annuri da haskenSa".

Sannan ku sani
Lallai Allah ya umurce ku da yin salati da sallama ga AnnabinSa…


TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...