2019/10/02

رضا الله تعالى Hudubar Abdulmuhsin Alkasim 5 Safar 1441H












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 5/SAFAR/1441H
daidai da 4/OCTOBER/ 2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ABDULMUHSIN BN MUHAMMADU ALKASIM





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
YARDAR ALLAH TA'ALAH
(رضا الله)
Shehin Malami wato: Abdulmuhsin bn Muhammadu  Alkasim –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: YARDAR ALLAH, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO


Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, to babu mai shiryar da shi.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa.
Salatin Allah su kara tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.

        Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da takawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku yi riko a Musulunci da igiya mai karfi.

        Ya ku Musulmai …
Sunayen Allah sune mafiya kyau, SifofinSa kuma madaukaka ne. Kuma  Allah a cikin dukkan hakan yana da sifa madaukakiya. Kuma imani da su rukuni ne na Tauhidi. Kuma da haka aiki yake zama ingantacce.
Kuma YANA DAGA SIFOFIN ALLAH WANDA ALKUR'ANI DA SUNNA SUKA AMBATA; SIFAR YARDA (الرضا); Domin Allah Ta'alah yana yin fushi kuma yana yarda, ba kuma kamar na wani daga cikin halittu ba. Kuma akan tabbatar da wannan sifar, Sahabbai da Tabi'ai suka shude, da kuma sauran jagororin Musulmai.
Kuma domin neman yardar Allah ne, AnnabawanSa da WaliyyanSa da Bayin Allah; Salihai suka zage damtse (suke ta fadi-tashi), Allah Ta'alah ya ce: "Kuma daga cikin Mutane akwai wanda yake sayar da ransa, domin neman yardar Allah, Kuma Allah Mai tausayi ne ga Bayi" [Bakara: 207].
Kuma annabi Isma'ilu –عليه السلام- Allah ya yabe shi a cikin littafinSa da cewa, ya samu rabauta da yardarSa, a inda ya ce: "Kuma ka ambaci Isma'ila a cikin littafi; lallai shi ya kasance mai gaskiyar alkawari, kuma ya kasance Manzo, Annabi * Kuma ya kasance yana umurtar Iyalansa da salla da zaka, kuma ya kasance yardajje a wurin UbangijinSa" [Maryam: 54-55].
Kuma annabi Musa –عليه السلام- UbangijinSa ya masa alkawarin ganawa a gefen dutsen Dur, sai ya yi gaggawa zuwa gare shi, domin kwadayin samun yardarsa, Allah ya ce: "Kuma menene ya gaggautar da kai ga barin Mutanenka, Ya Musa? * Ya ce: Sune wadannan ga su a bayana (za su iso), kuma na yi gaggawa zuwa gare ka ne, domin ka yarda" [Daha: 83-84].

Kuma annabi Sulaiman –عليه السلام- ya roki UbangijinSa, ya masa ilhamar aikata abinda zai yardar da shi, a inda ya ce: "Ya Ubangina! Ka cusa mini inj gode wa ni'imarka wanda ka ni'imta ta a gare ni, da kuma ga iyayena biyu, kuma in aikata aiki na kwarai wanda kake yarda da shi" [Naml: 19].
Kuma annabi Zakariyya –عليه الصلام- ya kira UbangijinSa, da ya azurta shi da yaro wanda ya yarda da shi, a inda ya ce: "Kuma ka sanya shi yardajje, Ya Ubangiji" [Maryam: 6].
Kuma Allah ya sifanta annabinmu Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- da sahabbansa, da kyautata aiki, suna masu neman yardar Allah, Allah Ta'alah ya ce: "Muhammadu Manzon Allah ne, kuma wadannan da suke tare da shi, masu tsanani ne ga kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, kana ganinsu suna ruku'u suna sujjada, suna neman falala daga Allah da yardarSa" [Fat-h: 29].
Kuma domin neman yardar Allah ne, Muhajirawa suka kaura suka bar garinsu, Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Da kuma, ga Matalauta masu hijira, wadanda aka fitar daga gidajensu da dukiyoyinsu, suna neman falala daga Allah da kuma yarda" [Hashr: 8].
Mumini yana neman tsari da yardar Allah daga fushinsa, kamar yadda Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya nemi hakan a cikin fadinsa: "Ya Allah lallai ni ina tsari da yardarka daga fushinka", Muslim ya ruwaito.
Kuma kyan aiki da karbuwarsa ya rataya ne akan tsarkake niyya ga Allah, ta hanyar neman yardarSa, Allah Ta'alah ya ce: "Babu alheri cikin yawa-yawan ganawansu, sai ga wanda ya yi umurni da wata sadaka, ko wani alheri, ko kuwa sulhu a tsakanin Mutane, Kuma wanda ya aikata haka, yana mai neman yardar Allah, to lallai za mu bashi lada mai girma" [Nisa'i: 114].
Kuma ciyarwa karbabbiya mai albarka, itace wanda sahibinta ya nemi yardar Allah, Allah ya ce: "Kuma sifar wadanda suke ciyar da dukiyoyinsu domin neman yardar Allah, da tabbatuwa daga kansu, kamar misalin lambu ne a jigawa, wanda wabilin hadiri ya samu, sai ya bayar da amfaninsasa ninki biyu. To idan kuma wabili bai same ta ba, sai yayyafi (ya isar mata), Kuma Allah ga abinda kuke aikatawa Mai gani ne" [Bakara: 265].
Kuma Allah ya girmama alfarmar Mahajjata da masu umrah, wadanda suke neman yardarSa, a cikin fadinSa: "Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku keta alfarmar wuraren bautar Allah, da kuma wata mai alfarma, da hadaya, da ratayar rakumar hadaya, da Masu nifin daki mai alfarma suna neman falala daga Ubangijinsu da yarda" [Ma'ida: 2].
Musulmi yana lazimtar neman yardar Allah a halin tafiye-tafiyensa da zamansa na gida, da farin cikinsa da bakin cikinsa, da dukkan halinsa, domin a halin tafiya ya kan bude bulaguronsa ne da rokon Allah ya saukake masa dukkan abinda zai yardar da shi, sai ya ce: "Ya Allah, lallai muna rokonka a cikin bulaguronmu wannan, biyayyarka da takawa, da kuma irin aikin da zaka yarda", Muslim ya ruwaito.
Kuma idan musiba ta sauko masa, to babu abinda ya ke kasancewa ga Musulmi, sai abinda zai yardar da Allah, Ibrahim; Dan Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya rasu, sai Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai ido yana yin hawaye, zuciya kuma tana yin bakin ciki, saidai ba za mu fadi komai ba, face abinda Ubangijinmu zai yarda, Kuma lallai mu dangane da rabuwa da kai –Ya Ibrahim- tabbas masu bakin ciki ne", Bukhariy ya ruwaito.
Yana daga RAHAMAR ALLAH DA KARRAMAWARSA Yadda ya shar'anta wa BayinSa addinin da yarje musu shi, Allah Ta'alah ya ce: "A yau, na kammala muku addininku, kuma na cika muku ni'imata akanku, kuma na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku" [Ma'ida: 3].
Kuma cikin aiki da addinin Musulunci ake samun abinda yake hukunta yardar Allah; domin imani da Allah shine sababin sa'idar Duniya da Lahira, kuma yana gadar wa Bawa samun yardar MajibincinSa, Allah ta'alah ya ce: "Lallai ne wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukn kwarai, wadannan sune mafifita alherin halittu * sakamakonsu a wurin Ubangijinsu shine gidajen Aljannar zama, koramu suna gudana daga karkashinta, suna masu dawwama a cikinta har abada. Allah ya yarda da su, suma sun yarda da shi. Wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsoron UbangijinSa" [Bayyinah: 7-8].
Kuma duk wanda ya yi imani kuma ya aikata kakkawan aiki, to lallai ya bi hanyar godiya, da samun yarda, Allah Ta'alah ya ce: "Idan kuka butulce to lallai Allah wadatacce ne ga barinku, kuma bashi yarda da kafirci ga bayinSa, kuma idan kun gode zai yarda da godiyar a gare ku" [Zumar: 7].
Kuma Tauhidi shine kadaita Allah da bauta, Kuma Allah ya yarje wa Bayinsa da su rika bauta masa; ba tare da sun hada shi da komai ba, kuma su yi riko da igiyar Allah gaba dayansu; kada su rarraba, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai Allah ya yarje muku abu uku, kuma yana kiye muku abu uku; yana yarje muku ku bauta masa kada ku hada shi da komai, kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya; kada ku rarraba", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma inanin Bawa baya daidaita, sai da son muminai da kin kafirai, kuma duk wanda ya yi haka, sai Allah ya saka masa, kuma ya yarda da shi, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ba za ka samu Mutanen da suka yi imani da Allah da ranar karshe, suna soyayya da wanda ya saba wa Allah da manzonSa ba, koda sun kasance Iyayensu ne, ko 'ya'yansu, ko yan'uwansu, ko danginsu, Wadannan Allah ya rubuta imani a cikin zukatansu, kuma ya karfafa su da wani ruhi daga gare shi, kuma zai shigar da su gidajen Aljannar da koramu suke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu, Allah ya yarda da su, kuma suma sun yarda da shi" [Mujadala: 22].
Kuma duk wanda ya taimaki addinin Allah, Allah sai ya karfafe shi, kuma ya yarda da shi, Allah Ta'alah: "Lallai ne hakika, Allah ya yarda da Muminan nan, a lokacin da suke maka mubaya'a a karkashin bishiya, domin ya san abinda ke zukatansu, sai ya saukar da natsuwa a kansu, kuma ya saka musu da wani cin nasara makusanci" [Fat-h: 18].
Kuma gaskiya shine tushen imani, kuma shine yake nuna samuwarsa, kuma da shi Bawa yake amfana a Duniyarsa da lahirarsa, Allah Ta'alah ya ce: "Wannan shine yinin da gaskiyar masu gaskiya take amfanarsu, suna da gidajen Aljannar da koramu suke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada, Allah ya yarda da su, kuma sun yarda da shi, Wannan ne rabo mai girma" [Ma'ida: 119].
Kuma cikin zikirin Allah akwai gyaruwar zukata, da samun yardar Masanin abinda yake fake, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Shin ba zan baku labarin mafi alherin ayyukanku, kuma wanda Mamallakinku yafi yarda da shi, kuma wanda yafi daga muku darajarku, kuma yafi alheri a gare ku fiye da bayar da zinari da azurfa, da kuma jihadi; wato ku hadu da makiyanku, ku sare wuyansu suma su sare wuyanku? Sai suka ce: Menene haka Ya Ma'aikin Allah? Sai ya ce: Ambaton Allah", Ibnu-Majah ya ruwaito.
Godiya ita ce dabaibayi ga ni'imomi, kuma da ita ni'imomin suke karuwa suke dawwama. Kuma yana daga cikin manyan sakayyar godiya: yardar Allah ga Ma'abutansa, cikin hadisin Mutane uku daga Banu-Isra'ila; wato kuturu da mai kora da makaho, ya ce: "Sai Mala'ika ya zo wurin Makaho, ya ce: Ni mutum ne, miskini, matafiyin da dabara ta kare masa a tafiyarsa; don haka bani da guzuri yau, sai a wurin Allah, sannan a wurinka; Ina rokonka da wanda ya dawo maka da ganinka (Allah) ka bani akuya daya, da zany i guzuri da ita a cikin bulagurona, sai ya ce: Hakika na kasane makaho, sai Allah ya dawo mini da ganina, kuma matalauci, sai ya wadatar da ni; don haka; ka dauki abinda kake so, ina rantsuwa da Allah, ba zan musa maka akan wani abin da ka dauke shi don Allah ba a yau. Sai ya ce: Rike dukiyarka, domin jarrabar ku aka yi; kuma lallai hakika Allah ya yarda da kai, kuma yay i fushi ga abokanka biyu", Bukhariy da Muslim.
Yana daga falalar Allah, yadda Allahn yake ciyar da BawanSa ya shayar da shi, Kuma idan Bawa ya yi godiya ga Ubangiji akan haka, Allah sai ya yarda da shi, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce:       "Allah yana yarda ga Bawa; ya ci abin ci, sai ya gode masa akan haka, ko ya sha abin sha, sai ya gode masa akansa", Muslim ya ruwaito.
        Kuma Duniya a kewaye take da bala'i da gurbatattun lamura, Wanda ya yi hakuri akan bala'ointa sai ya rabauta, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai girman sakamako ya kan zama gwargwadon girman bala'i, kuma lallai Allah Ta'alah idan ya so Mutane sai ya jarrabe su; wanda ya yarda yana da yarda, wanda kuma ya yi fushi to yana da fushi", Tirmiziy ya ruwaito shi.
Harshe mabudin alheri ne da sharri; kuma da kalma mai dadi Mutum zai riski yardar MahaliccinSa, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Lallai Bawa ya kan fadi kalma cikin yardar Allah Ta'alah, bai dauke ta da girma ba, sai Allah ya daga darajojinsa da ita", Bukhariy ya ruwaito.
Mutanen da suka fi cancantar kyautata musu da biyayya sune iyaye biyu, kuma a cikin yardarsu ake samun yardar Allah, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Yardar Ubangiji tana cikin yardar mahaifi, kuma fushin Ubangiji yana cikin mahaifi", Tirmiziy ya ruwaito.
Kamar yadda Allah yake son tsarkin zuciya, to lallai yana son tsarki na zahiri, Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Aswaki tsarki ne ga baki, kuma abin yarda ne ga Ubangiji", Tirmiziy ya ruwaito shi.
Kuma idan kiyama ta tsayu, dukiya ko 'ya'ya ba za su wani amfani ba, sai ga wanda ya je wa Allah da zuciya lafiyayya, kuma babu mai yin ceto, face da izinin Allah, da yardarSa ga wanda zai yi ceton, Allah Ta'alah ya ce: "A wannan ranar, ceto baya yin amfani, face wanda Allah ya masa izini, kuma ya yarda da zancensa", [Daha: 109].
Kuma baya amfani, face ga wadanda Allah ya yarda da su, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma basu yin ceto, face ga wanda ya yarda", [Anbiya'i: 28].
Kuma a cikin Aljanna ana yin ni'ima ga muminai da abinda idanu basu gani ba, kunne bai ji ba, kuma bait aba darsuwa ga zuciyar wani mutum ba, Kuma yana cikin madaukakan ni'imomi da suka fi girma, yardar Ubangijinsu a gare su, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma Allah yay i wa'adi ga muminai maza da muminai mata, da gidajen Aljannah, wadanda koramu suke gudana a karkashinsu, suna masu dawwama a cikinsu, da wuraren zama masu dadi a cikin gidajen Aljannar zama, Kuma yarda daga Allah ita ce mafi girma, Wannan shine babban rabo" [Tauba: 72].
Annabi –عليه الصلاة والسلام- y ace: "Lallai Allah zai ce wa ma'abuta Aljannah: Ya Ma'abuta Aljanna! Sai su ce: Mun amsa maka –Ya Ubangijinmu-, kuma dukkan alheri suna hannayenka, Sai ya ce: Shin kun yarda? Sai su ce: Me yasa ba za mu yarda ba, Ya Ubangiji, alhalin ka bamu abinda baka bayar da wani daga cikin halittunka ba? Sai ya ce: Shin ba zan baku abinda yafi muku hakan ba? Sai su ce: Ya Ubangiji: Wane abu ne yafi hakan falala? Sai ya ce: Zan saukar muku da yardata akanku; ba zan yi fushi da ku a bayansa ba har abada" [Bukhariy da Muslim].

BAYAN HAKA:
YA KU MUSULMAI
Samun rabo gaba dayansa, yana cikin riko da addini, kuma duk wanda ya lazimci abinda yake yardar da Allah, Allah sai ya yarda da shi kuma ya yardar da shi. Kuma idan Bawa ya nemi yardar UbangijinSa kuma ya fifita shi akan dukkan abinda ba shi ba, to lallai Allah zai yarda da shi, kuma ya sa Mutane su yarda da shi.
Kuma wanda ya nemi yardar Mutane da fusata Allah, sai Allah yay i fushi da shi, kuma ya sanya Mutane su yi fushi da shi.
A UZU BILLAHI MINAS SHAIDANIR RAJIM
"Shin wanda ya bibiyi yardar Allah, yana zama kamar wanda ya komo da fushin Allah! Kuma makomarsa jahannama ce, kuma tir da ita a matsayin makoma" [Ali-imrana: 162].


Allah ya mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,     
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU

Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa;  Godiya kuma tasa ce bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya; Ina mai girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi dadin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnunkuwa.

Ya ku Musulmai…

Wanda Allah ya yarda da shi, to sai ya karrama shi da mafifiyar ni'ima, a cikin Aljannah, Allah Ta'alah ya ce: "Wasu fiskoki a wannan ranar masu annuri ne * zuwa ga Ubangijinsu masu kallo ne" [Kiyama: 22-23].
Alhasan –رحمه الله– ya ce: "Sun kalli Ubangijinsu, sai suka haskaka da haskensa".
Kuma dubi zuwa ga fiskar Allah mai karamci, shine karin da Allah ya yi alkawari ga BayinSa; masu kyautatawa, Allah ya ce: "Wadanda suka kyautata suna da Aljanna da kari" [Yunus: 26].
Annabi –عليه الصلاة والسلام- ya ce: "Idan Ma'abuta Aljannan suka shiga Aljannah, Sai Allah Tabaraka wa Ta'alah ya ce: Kuna son wani abu na kara muku? Sai su ce: Ashe baka haskaka fiskarmu ba? Ashe baka shigar da mu Aljannah, kuma ka tsamar da mu daga wuta ba? Sai ya yaye shamaki. Ba a baiwa 'yan Aljanna wani abu da yafi soyuwa a gare su fiye da kallon fiskar Ubangijinsu ba", Muslim ya ruwaito shi.

Sannan ku sani
Lallai Allah ya umurce ku da yin salati da sallama ga AnnabinSa…


2019/09/20

HARE HARE A KARAMAR HUKUMAR BAKIK DA KHARIS Hudubar 21 Muharram 1441 Dr Abdulbariy dan Awwadh












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 21/MUHARRAM/1441H
daidai da 20/SEPTEMBER/ 2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ABDULBARIY BN AWWADH AS-SUBAITIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
HARE-HARE A KARAMAR HUKUMAR BAKIK DA KHARIS
(الأحداث في البقيق والخريص)
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Awwadh  AsSubaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: HARE-HARE A KARAMAR HUKUMAR BAKIK DA KHARIS, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO


Musulunci ya sanya dukkan abinda Allah ya ajiye a bayan kasa ne, na manyan albarkatunta, da hanyoyin shigowar dukiya masu yawa, a karkashin kulawar Mutane, domin tabbatar da ma'anar kwanciyar hankali, Allah Ta'alah ya ce: "(Allah) Shine wanda ya sanya muku kasa horarriya, sai ku tafi cikin sasaninta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare shi tayar da ku yake" [Mulk: 15].
Kuma dukkan umurni da hani, da manufofin shari'a, da lalurorinta biyar, sun zo ne domin tabbatar da ginshikan kwanciyar hankali a rayuwar Mutane, wannan kuma domin umurni da hani a shari'a  suna komawa ne ga/ Kiyaye manufofin shari'ar, a cikin halittu. Kuma wadannan manufofin dole babu makawa, sai an basu kulawa, gabanin tsayuwar maslahohin Duniya da Addini, ta yadda idan aka rasa su, to maslahohin Duniya ba za su tabbatu ba.
Musulunci ya rataya mafi tsananin azaba, akan kawo barna a ban kasa; kuma duk wanda ya yi barna a bayan kasa kuma ya yi kokarin rushe ma'anonin kwanciyar hankali, to wannan mabarnaci ne.
Matsala zata iya samun Mutane saboda makircin makirai, kuma za su iya cutuwa saboda kaidin masu kaidi, wannan kuma domin Allah ya jarrabi Muminai, kuma domin ya yaye al'amarin munafikai da karyar allunan da suke dagawa (na cewar su masu son gyara ne).
A cikin rayuwar al'ummomi akwai tashoshi da wasu ibtila'oi da suke bayyanar da kimar al'ummomin, da kyan asalin tushensu.  Kuma hakikanin al'ummomi yana bayyana ne a lokacin ibtila'oi da tsanani, ta fiskar karfin ginuwarsu da zurfin fahimtarsu da ilimi. Domin ibtila'oi da tsanani suna girgiza wasu al'ummun sai su fadi su ruguje, wasu al'ummun kuma (bayan ibtila'i) sai su yi karfi, damtsensu ya kara kwari, saiwarsu ta kara kafuwa, himmominsu su daukaka. Saboda tsanani basa raunana azamar mazaje, kuma basa karya lakar kasashe, kuma basa tsayar da tafiya ko gudanar rayuwa, a'a al'ummomi suna rungumar musibun, kuma suna wuce su, suna daukaka akansu.
Lallai hare-hare masu radadi da suka auku a kwanakin nan, a karamar hukumar Bakik da Hijrah da Kharis, kuma suka yi mummunan tasiri ga albarkatun kasa na wannan al'ummar, aiki ne abin kyama, Kuma lallai ba za su cimma manufofinsu kaskantattu ba, kuma ba za su samu muradinsu na barna ba, kuma da falalar Allah, sannan da fadakar shugabannin wannan kasa, da azamar jami'an tsaronta da masu gadin iyakoki, hare-haren za su koma da asara mabayyaniya.
Kuma idan masu barna da 'yan rushe-rushe suka ketare iyakoki,suka yi dagawa suka yi zalunci suka yi ta'addanci, to sai a mu'amalance su da abinda zai taka musu birki, domin amincin kasa ya tabbatu, kuma aikin gina kasar da bunkasata ya cigaba.

Duk da wadannan hare-haren kan al'umma yana kara haduwa, kuma ana daidaita sahu, 'yan kasa suna kara basira, kan al'amarin kiyaye iyakoki, da kawo kwanciyar hankula, da karfafa aminci da zaman lafiya.

Lallai wannan kasa, tana fama da kalu-bala masu girma, bala'oi suna kai-komo a cikinta, da fitintinu masu sarkakiya, kuma lallai ana nufinta da sharri, domin neman a tunbuke ta daga saiwarta, a sare ta daga tasowarta tun a farkon fari, ana mata haka domin ita ce cibiyar Musulunci, kuma mafaka ga imani.
Saidai makiya -masu aikin wofi- su sani, lallai ba za su iya rushe tsaron wannan kasar ba, ba za su iya wargaza ta ba, kuma ba za su cimma makircinsu ba, domin kasar ta ki jinin zalunci, kuma tana tsananin yakar ta'addanci; kuma saboda alakokin 'ya'yanta na cikin gida suna da karfi, kuma ita saboda kiyayewar Allah ganuwa ce mai karfi, kuma Allah zai cigaba da kiyaye ta cikin kiyayewarsa, sakamakon daga tutar littafin Allah da sunnar manzo, wanda sune ginshikin hukuncinta, mabubbuga ga shari'arta, salo kuma ga rayuwarta, matabbatan samun iko a cikinta, tushen samun rabo da tsira. Wannan kuma shi zai sanya al'amarin tsaro a kasarmu ya tabbatu, muna zuzuta karfinsa, kuma Mutane suna fatan ganin bunkasarsa.

Danganta kai ga kasarka al'amari ne wanda a al'adance aka dasa shi a jikin Mutane, kuma kauna ce da aka halitta Mutum akanta, ana ciro ta daga danganta kai ga addini, sai su tafi a tare, Kuma yaya Mutum ba zai kaunaci kasar da yake rayuwa akanta ba, ya taso a kan turbayarta, alakarsa ta kullu da Mutanenta, da tarihinta? Kuma yaya ba zai ji radadin abinda zai cutar da ita ba, ya kuma yi fushi da abin da zai munana mata? Kuma yaya ba zai yi aiki domin dakatar da masu ta'addanci a gare ta ba?
Karfin dangantuwar Mutane ga kasarsu yana karfafa al'amarin tsaronsu da dukkan nau'ukansa, sai ya karfafa dangatakar 'yan kasar ta cikin gida, wanda kuma hakan shine zai kare su, daga wanda yake son kunno fitintinu da tashin-tashina a cikin kasarsu.

Lallai hadin kai da daidaita sahu da gujewa rarrabar zukata, shine hanyar samun nasara, da daukaka, kuma shine sinadarin samun karfi, da natsuwa da zaman lafiya. kamar yadda sifantuwa da hakuri da takawa suke raunata kulle-kullen makirci, suke dauke abu mai cutarwa.

Kuma lallai amincin wannan kasar; wato kasar harami biyu madaukaka, ta Saudiya, shine ginshikin amincin al'ummar Musulmai, saboda Saudiya ita ce zuciya mai bugawa na al'ummar, kuma guzurin al'umma mai tunkuda. Kuma lallai munana wa kasar nan munanawa ne ga zaman lafiyar daukacin Musulmai. Kuma gangar jikin al'umma ba zai gushe yana cikin alheri ba, matukar zuciyarta tana bugawa, domin alherin wannan kasar mai gamewa ne, ayyukanta masu amfani basu yankewa. Kuma hada hannu da yin aiki domin kwanciyar hankalin wannan kasar, da kare ta daga makircin makiya da kaidin masu kaidi, abu ne da shari'a take nema, kuma wajibi ne na addini. Kuma masu hankali suna fahimtar hakan, kuma suna bada gudumowa da wayewarsu wajen rushe kulle-kullen masu dakonta da sharri, kuma suna yin aiki domin kiyaye amincin wannan kasar, da amincin harami guda biyu.
Kuma wanda ya yi kokarin cutar da amincin wannan kasar, to lallai yana hidima ne ga makiyan Musulunci, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma idan kuka yi hakuri, ku ka yi takawa, kaidinsu ba zai cutar da ku komai ba" [Ali-imrana: 120].
Kuma gaskiya madaukakiya ce abar taimako. Kuma duk yadda kiraye-kiraye barna ya daukaka, kururuwa zuwa gare ta ya yawaita, to lallai barna gininsa mai girgiza ne, bangarorinsa masu rauni ne, kuma mai saurin halaka ne, "Kuma muna jifa da gaskiya akan karya, sai ta darkake ta, sai ga ta halakakka" [Anbiya'i: 18].

Kuma duk yadda bala'oi suka tsananta, fitintinu suka dabaibaye, kuma duk yadda masu kaidi suke kaidi, kuma ma'abuta sharri da zalunci suka yi makirci, masu jiran ganin sharri suke zaman dako, kuma suka saka kulle-kulle, to lallai wannan kasar mai kariya ga harami biyu, gininta yana nan da karfinsa, madaukaki, wanda zai gagari makiya, Mai neman ya taba girman kasar zai kaskanta, mai adawa da ita zai fadi ya wulakanta, wannan kuma babu makawa akansa, saboda Musulunci shine shamakinta mai karfi, imani kuma sulkenta, kuma lallai daukakarta yana karkashin bin addininta, Umar dan Khaddab –Allah ya kara yarda a gare shi- ya ce: "Mun kasance mutanen da suka fi kaskanci, sai Allah ya daukaka mu da Musulunci".

Zarata akan iyakokinmu suna yin zaman dako (ribadi), suna kiyaye addini da kasa, suna gwabzawa da makiyansu suna lankwame su, kuma basu girgiza, cikin kudurinsu, suna masu karfi da azamarsu da zukatansu, domin yanke (katse) karshen masu ta'addanci, da kakkabe ko buge makamansu na barna.
A nan, Muna jinjina ga gudumowa mai girma wanda zaratan jami'an tsaro suke bayarwa, wadanda suke ribadi kan kiyaye tsaro da kare iyakoki, wajen yakar ta'addanci, da gano mafakar masu neman rusa kasarmu, da wargaza tsare-tsarensu tun a farkon fari. Allah ya kiyaye kasarmu da kasashen Musulmai daga dukkan mummuna da abin ki, Allah Ta'alah ya ce: "Sai su yi bauta ga Ubangijin wannan dakin * Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Kuraish: 3-4].

Allah ya mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,     
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU

Mumini a lokacin tsanani da fitintinu, alakarsa da UbangijinSa tana kara karfi, sai zuciyarsa ta ratayu da MajibincinSa, yana neman fakewa a mafakarSa, "Kuma ka sanya mini, daga wajenka wani karfi mai taimako" [Isra'i: 80].
Fakewa ga Allah, da nuna masa matsanancin bukata, da neman ya yaye bakin ciki, ya dauke fitintinu, da yin gaskiya a gare shi, shine halin Musulmi a cikin farin ciki da cuta.
Kuma idan Musulmii ya bayyana bukatarSa ga MajibincinSa, to ya hada bukatarsa da aiki da kuma lazimtar addu'a, kuma lallai Allah ya yi alkawarin amsa addu'ar wanda ya roke shi, kuma Musulmi zai yi addu'a ne alhalin yana da tabbacin MahaliccinSa zai amsa masa, "Kuma Ubangijinku ya ce: Ku roke ni zan amsa muku" [Gafir: 60].
Kuma Allah shine Mai kiyayewan da yake kiyaye wanda ya so, daga sharri da cutuwa da bala'i.
Kuma yana daga addu'oin da Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya koyar da mu: "Ya Allah ka suturta al'aurata, ka amintar da tsorona, ka kiyaye ni ta gaba gare ni da bayana, da ta damana da haguna, da ta samana, kuma ina neman tsarinka kada a halaka ni ta kasana".
Wanda ya nemi karfinsa daga Allah, to ba zai san wata ma'ana ta rauni ba, kuma dabi'ar debe tsammani ba za ta samu gurbi ba a zuciyarsa, domin Allah shine Mai taimako Mai tilastawa, kuma zuwa gare shi lamura suke tafiya.

Kuma Al'ummar Musulmai za su hada tsakanin riko da sababi da kuma dogaro ga Allah –Subhanahu-, kuma duk wanda ya jingina al'amarinsa ga Allah kuma ya fawwala masa, to UbangijinSa ya isar masa, kuma zai kiyaye shi ya bashi kariya.
Kuma Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana hasashen zuwa lokaci na gaba (mai kyau) da idon mai kyautata fata, wanda ya amintu cewar Allah zai cika alkawarinsa, Allah Ta'alah ya ce:  "Kuma wanda ya dogara ga Allah, to shine Mai isar masa, Lallai Allah mai kaiwa ga lamarinSa ne, Hakika Allah ya sanya kaddara ga dukkan komai" [Dalak: 3].

2019/09/18

د ثبيتي 21 المحرم 1441 إن الله لا يصلح عمل المفسدين Hudubar












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 21/MUHARRAM/1441H
daidai da 20/SEPTEMBER/ 2019M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ABDULBARIY BN AWWADH AS-SUBAITIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
I
(إن الله لا يصلح عمل المفسدين)
Shehin Malami wato: Abdulbariy bn Awwadh  AsSubaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: K, wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO


Bayan haka:
Musulunci ya sanya dukkan abinda Allah ya ajiye su a bayan kasa, na manyan albarkatunta, da hanyoyin shigowan dukiya masu yawa, a karkashin kulawan Mutane domin tabbatar da ma'anar kwanciyar hankali, Allah Ta'alah ya ce: "(Allah) Shine wanda ya sanya muku kasa horarriya, sai ku tafi cikin sasaninta, kuma ku ci daga arzikinSa, kuma zuwa gare shi tayar da ku yake" [Mulk: 15].

Kuma dukkan umurni da hani, da manufofin shari'a, da lalurorinta biyar, sun zo ne domin su tabbatar ginshikan kwanciyar hankali a rayuwar Mutane, wannan kuma saboda kallafe-kallafen shari'a (umurni da hani)  suna komawa ne zuwa ga kiyaye manufofinta a cikin halittu. Wadannan manufofin kuma babu makawa sai an kula da su gabanin tsayuwar maslahohin Duniya da Addini, ta yadda idan aka rasa su maslahohin Duniya ba za su tsayu ba.
Musulunci ya rataya mafi tsananin narkon azaba, akan kawo barna a bayan kasa; kuma duk wanda ya kawo barna a bayan kasa kuma ya yi kokarin rushe ma'anonin kwanciyar hankali, to wannan mabarnaci ne.
Matsala zata iya samun Mutane saboda makircin masu makirci, kuma za su iya cutuwa saboda kaidin masu kaidi, wannan kuma domin Allah ya jarrabi bayinsa Muminai, kuma domin ya yaye al'amarin munafikai da karyar allunan da suke dagawa (na cewarsu su masu son gyara ne).
A cikin rayuwar al'ummomi akwai tashoshi da wasu ibtila'oi da suke bayyanar da kimar al'ummomin, da kyan asalin tushensu.  Kuma hakikanin al'ummomi yana bayyana a lokacin ibtila'oi da tsanani, ta fiskar karfin ginuwarsu da zurfin fahimtarsu da ilimi. Domin ibtila'oi da tsanani suna girgiza wasu al'ummun sai su fadi su ruguje, wasu al'ummun kuma sai su yi karfi, damtsensu ya kara kwari, saiwarsu ta kara kafuwa, himmominsu su daukaka. Saboda tsanani basa raunana azamar mazaje, kuma basa karya lakar kasashe, kuma basa tsayar da tafiyar tayu na rayuwa, a'a al'ummomi suna rungumar musibun, kuma suna wuce su, suna daukaka akansu.
Lallai musiba mai radadi wanda ya auku a kwanakin nan, a karamar hukumar Bakik da Hijratu Kharidh, kuma ya yi mummunan tasiri ga albarkatun kasa da wannan al'ummar, aiki ne abin kyama, ya nuna wauta da jahilci da rashin hankalin wanda ya sanya ha'inci ya zama mazhabarsa, cin amana kuma dabi'arsa, makirci da yaudara kuma suka zama al'amarinsa. Kuma lallai ba za su cimma manufofinsu kaskantattu ba, kuma ba za su samu muradinsu na barn aba, kuma da falalar Allah za su koma da asara mabayyaniya, haka kuma da fadakar jagororin al'amarin wannan kasa, da azamar jami'an tsaro da masu gadi iyakoki.
Kuma idan masu barna da 'yan rusau suka ketare iyakoki,suka yi dagawa suka yi zalunci suka yi ta'addanci akan mallakin al'umma, to sai a mu'amalance su da abinda zai taka musu birki, domin sanya iyaka ga wawayen hankula da makirce-makirce masu munanan manufofi da tottoshe kafofin masu makiya, da gyara abinda abinda ya karkace, sai amincin kasa ya tabbatu, kuma aikin gina kasa da bunkasata ya cigaba.

Duk da wadannan musibun kan al'umma yana kara haduwa, kuma ana daidaita sahu, 'yan kasa suna kara basira, kan al'amarin kiyaye iyakoki, da kawo kwanciyar hankula, da karfafa aminci da zaman lafiya.

Lallai wannan kasa, tana fama da kalu-bala masu girma, bala'oi suna kai-komo a cikinta, da fitintinu masu sarkakiya, kuma lallai ana nufinta da sharri, domin a tunbuke ta daga saiwarta, a sare ta daga tasowarta, domin itace cibiyar Musulunci, kuma mafaka ga imani.
Saidai makiya masu aikin kawai su sani, lallai su ba za su iya rushe tsaron wannan kasa ba, ba za su iya wargaza ta ba, kuma ba za su cimma makircinsu ba, domin wannan kasar ta ki jinin zalunci, kuma tana da tsananin fada da ta'addanci; domin alakokinta na cikin gida suna da karfi, kuma ita saboda kiyayewar Allah ganuwa ne mai karfi, kuma Allah zai cigaba da kiyaye ta cikin kiyayewarsa, saboda tana daga tutar littafin Allah da sunnar manzo, wanda sune ginshikin hukuncinta, kuma mabubbugar shari'arta, kuma salon rayuwarta, kuma matabbata ga samun gindin zama, tushen samun rabo da tsira. Wannan kuma shine zai sanya tsaro a kasarmu ya tabbatu, muna zuzuta al'amarin karfinsa, kuma rayuka suna fatan ganin bunkasarsa.

Danganta kai ga kasarka al'amari ne da aka dasa shi a jikin Mutane a al'adance, kuma kauna ce da aka halitta Mutum akanta, ana ciro shi daga danganta kai ga addini, sai ya tafi tare da shi, Kuma yaya Mutum ba zai so kasar da yake rayuwa akantaba, ya taso aka turbayarta, alakarsa ta kullu da Mutanenta, da tarihinta? Kuma yaya Mutum ba zai ji radadin abinda zai cutar da ita ba, ya kuma yi fushi da abin da zai munana mata? Kuma yaya ba zai yi aiki don hana masu ta'addanci a gare ta ba?

Karfin dangantuwar Mutane ga kasarsu yana karfafa lamarin tsaron kasar da dukkan nau'ukansa, sai ya samar kuma karfafa dangatakar 'yan kasan na cikin gida, wanda zai kare ta, daga wanda yake son kunno fitintinu da tashin-tashina a cikin kasar. Kuma yana daga abinda hakan yake hukuntawa:
Son kasarsa, da aiki tukuru dominta, da kada dan kasa ya zama kafa ga masu nufinta da sharri, ko duk wanda yake nufinta cutar da ita. Sannan ya yi kokari wajen duk wata maganar da zata kashe wata fitina, ko ta haifar kyakkyawan fata, ta kiyaye tsaro ta karfafa zaman lafiya, ta toshe kofar bala'i da tashin-tashina, ta rinjayar da maslahar kasa, ta karfafa alakokin al'umma. Wannan kuma yana hukunta kada ka amsa wa masu tsegumi da ma'abuta tutotin karya, wadanda nufinsu shine sace guiwa, da kawar da hadin kan jama'a da rushe abinda kasa ta samar kuma al'umma take girmamawa.

Lallai hadin kai da daidaita sahu da gujewa rarrabar zukata shine hanyar samun nasara, da daukaka, kuma shine ginshikin samun karfi, tare da natsuwa da zaman lafiya, kamar yadda sifantuwa da hakuri da takawar Allah yake raunata kulle-kullen makirci, yake dauke abu mai cutarwa.

Kuma lallai amincin wannan kasar; wato kasar harami biyu madaukaka, wato masarautar larabawa ta Saudiya, shine ginshikin amincin wannan al'umma (Musulmai), saboda Saudiya ita ce zuciyarta mai bugawa, kuma guzurinta mai tunkuda. Kuma lallai munana mata munana wa zaman lafiyar Musulmai ne (gaba daya). Kuma gangar jikin al'umma ba zai gushe ba yana cikin alheri matukar zuciyar tana bugawa, don haka, alherin wannan kasar mai gamewa ne, ayyukanta masu amfani kuma basu yankewa. Kuma hada hannu da yin aiki domin kwanciyar hankalin wannan kasa da kare ta daga makircin makiya da kaidin masu kaidi abu ne da shari'a take nema, kuma wajibi ne na addini. Kuma masu hankali suna fahimtar hakan, kuma suna bada gudumawa da wayewarsu wajen rushe kulle-kullen masu dakonta da sharri, kuma suna yin aiki domin kiyaye amincin wannan kasar, da amincin harami guda biyu.
Kuma duk wanda ya yi kokarin cutar da amincin wannan kasar, to lallai yana hidima ne ga makiyan addinin Musulunci, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma idan kuka yi hakuri, ku ka yi takawa, kaidinsu ba zai cutar da ku komai ba" [Ali-imrana: 120].
Kuma gaskiya madaukakiya ce abar taimako,Kuma duk yadda kiraye-kiraye barna ya daukaka, kururuwa zuwa gare shi ya yawaita, to lallai barna gininsa mai girgiza ne, bangarorinsa masu rauni ne, kuma mai saurin halaka ne, "Kuma muna jifa da gaskiya akan karya, sai ta darkake ta, sai ga ta halakakka" [Anbiya'i: 18].

Kuma duk yadda bala'oi suka tsananta, fitintinu suka dabaibaye, kuma duk yadda masu kaidi suka kullo kaidi, kuma ma'abuta sharri da zalunci suka yi makirci, masu dakon ganin sharri suke zaman dako, kuma suka saka kulle-kulle, to lallai wanna kasar mai bada kariya ga harami biyu, tana nan da karfinta, madaukakiya, gagararriya, wanda ya nemi ya taba girmanta sai ya kaskanta, wanda ya yi adawa da ita zai fadi ya kaskanta, wannan kuma babu wata ruduwa a cikin haka, saboda Musulunci shine shamakinta mai karfi, imani kuma sulkenta mai karfi, kuma daukakanta yana karkashin bin addini, Umar dan Khaddab –Allah ya kara yarda a gare shi ya ce-: "Mu mun kasance mutanen da suka fi kaskanci, sai Allah ya daukaka mu da Musulunci".

Da zaman dako (ribadin) zarata akan iyakoki, masu kiyaye addini da kasa, suna gwabzawa da makiya suna lankwame shi, kuma su basu girgiza, cikin kudurinsu, masu karfi da zamarsu da zukatansu, domin katse karshen masu ta'addanci, da bugu ga makaman barna.
Kuma muna yin jinjina kan gudumowa mai girma wanda zaratan jami'an tsaro suke bayarwa, wadanda suke ribadi kan kiyaye tsaro da kare iyakoki, wajen yakar ta'addanci, da gano mafakar masu neman rusa kasa, da wargaza tsare-tsarensu tun suna farko. Allah ya kiyaye kasarmu da kasashen Musulmai daga dukkan mummuna da abin ki, Allah Ta'alah ya ce: "Sais u yi bauta ga Ubangijin wannan dakin * Wanda ya ciyar da su daga yunwa, kuma ya amintar da su daga tsoro" [Kuraish: 3-4].

Allah ya mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,     
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU

Mumini a lokacin tsanani da fitintinu alakarsa da Ubangiji tana kara karfi, sai zuciyarsa ta ratayu da Majibincinsa, ya nemi fakewa a mafakarSa, "Kuma ka sanya mini, daga wajenka wani karfi mai taimako" [Isra'i: 80].
Fakewa zuwa ga Allah, da nuna masa matsanancin bukata, da neman ya yaye bakin ciki, ya dauke fitintinu, da yin gaskiya a gare shi, shine halin Musulmi a cikin farin ciki da cuta. Kuma idan Musulunci ya bayyana bukatarSa ga Majibincinsa, to sai ya hada bukatarsa da aiki da kuma lazimtar addu'a, kuma lallai Allah yay i alkawarin amsawa duk wanda ya roke shi, kuma Musulmi zai yi addu'a ne alhalin yana da tabbacin MahaliccinSa zai amsa masa, "Kuma Ubangijinku ya ce: Ku roke ni zan amsa muku" [Gafir: 60].
Kuma Allah shine Mai kiyayewan da yake kiyaye wanda ya so, daga sharri da cutuwa da bala'i.
Kuma yana daga addu'oin da Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya koyar da mu: "Ya Allah ka suturta al'aurata, ka amintar da tsorona, ka kiyaye ni ta gaba gare ni da bayana, da ta damana da haguna, da ta samana, kuma ina neman tsarinka kada a halaka ni ta kasana".
Wanda ya nemi karfinsa daga Allah to ba zai san wata ma'ana ta rauni ba, kuma dabi'ar debe tsammani ba za ta samu gindin zama a zuciyarsa ba, domin Allah shine Mai taimako Mai tilastawa, kuma zuwa gare shi ake mayar da lamura.

Kuma Al'ummar Musulmai za su hada tsakanin riko da sababi da kuma dogaro ga Allah –Subhanahu-, kuma duk wanda ya jingina al'amarinsa ga Allah kuma ya fawwala masa, to UbangijinSa ya isar masa, kuma zai kiyaye shi ya bashi kariya.
Kuma Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya kasance yana has ashen zuwa lokaci nag aba (mai kyau) da idon mai kyautata fata, wanda ya amintu da cika alkawarin Allah, Allah Ta'alah ya ce:   "Kuma wanda ya dogara ga Allah, to shine Mai isar masa, Lallai Allah mai kaiwa ga lamarinSa ne, Hakika Allah ya sanya ma'auni ga dukkan komai" [Dalak: 3].


Ya ku Bayin Allah… !!!
        "Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].

,,,          ,,,          ,,,




2019/09/06

tsakurowa daga hudubar Dr Abdullahi Albuaijan ta Haramin Madina 7Muharram 1441H


KWADAITARWA KAN RIBATAR LOKATAI
1-   Lallai cikin juyawar yini da dare, da saurin zamani da canzuwan halaye, da zuwan sabin shekaru, da yadda ajali ke kokarin riskar ma'abutansa, dukansu dalili ne akan al'amarin gushewa da makoma, kuma abin lura ne, ga wanda ya ratayu da buri: "Allah yana juyar da dare da yini, lallai ne a cikin wannan akwai abin kulawa ga ma'abuta basirori" [Nur: 44].
2-   Mafi alherinku shine wanda rayuwarsa ta yi tsawo, sai aikinsa ya yi kyau. Mafi sharri kuma shine wanda rayuwarsa tayi tsawo, sai aikinsa ya yi muni. Kuma daga cikinku kowa za a tambaye shi akan rayuwarsa; yaya ya karar da ita, da samartakarsa ta yaya ya tafiyar da ita?
Ya nadamarmu kan tozarta mafi tsadar lokatai
Ya takaicinmu kan sakaci, da mafi girman lokatai!
3-   Ku sani, lallai Allah ya zabi zababbu daga halittunSa, sai ya zabi manzanni 'yan aika daga cikin Mala'iku, suma Mutane ya zabi manzanni daga cikinsu, daga cikin magana kuma ya zabi ambatonsa, a doron kasa kuma ya zabi masallatai, daga cikin watanni kuma ya zabi watan Ramadhana da watanni masu alfarma, daga cikin kwanaki kuma yinin juma'a, daga cikin darare kuma ya zabi lailatul kadari; sai ku rika girmama abinda Allah ya girmama!
4-   Ku saurara! Lallai ga ku a farkon watan Muharram, kuma farkon shekarar hijira, kuma lallai wannan watan yana cikin watanni masu alfarma (hudu) wadanda Allah ya girmama su, ya ce: "Lallai ne kidayar watanni a wurin Allah watanni ne guda goma sha biyu, a cikin littafin Allah, a ranar da ya halicci sammai da kassai, daga cikinsu akwai hudu masu alfarma, wannan ne addini madaidaici, saboda haka, kada ku zalunci  kanku a cikinsu" [Taubah: 36].
5-   Hakika Musulmai tun zamanin khilafancin Umar –رضي الله عنه- sun yi riko da al'amarin hijirar Annabi -SAW- daga garin Makkah zuwa Madinah; sai suke kulle abin tarihi da shekarar hijira, saboda Allah ya rarrabe tsakanin gaskiya da barna da al'amarin hijira. Kuma sahabbai sun fari kidayar shekarar da watan Allah Muharram, sai lamarin ya tabbatu akan haka, kuma sai al'umma gabadayanta ta rungumi hakan.
6-   An ruwaito daga Ibnu-Abbas –رضي الله عنهما- ya ce: "Ban ga Annabi –SAW– yana kirdadon yinin da ya fifita shi akan waninsa ba, fiye da wannan yinin –wato, ranar Ashurah, da kuma wannan watan, yana nufin watan Ramadhana", Bukhari da Muslim.

HUDUBAR MADINA A TAKAICE DR ABDULLAHI ALBUAIJAN KAN Kwadaitawa kan ribatar lokatai 7Muharram 1441H


1-   Ku ribaci damar shekaru da rayuwa, kuma ku gabatar da ayyukan da suka fi tsarki domin kanku, kada ku rika jinkirta aiki, domin cikin hakan akwai hana rai aikin kwarai, sai ku ribaci rayuwarku gabanin mutuwa, da faragarku gabanin shagaltuwa da ayyuka, da wadacinku gabanin talauci, da samartaka gabanin tsufa, da lafiya gabanin cuta.
2-   Shekara ta kare, an rufe ayyukanta, an nade takardunta, madalla da Mutumin da ya ribaci damarsa, ya mori lokacinsa, ya gyara ayyukansa.
3-   Lokatan rayuwa dama ne na yin aiki, kuma ni'ima ne da suke hukunta godiya, "Idan za ku nemi kididdige ni'imomin Allah ba za ku iya lissafa su ba" [Ibrahim: 34]. Kuma lokaci yana wucewa, rayuwar kadan ce, ayyukan wajibai wani akan wani, hakkoki kuma suna dayawa, don haka; babu damar wargi da wasa, kuma babu lokacin hutawa da sakaci.
4-   Ku ji tsoron Allah Ta'alah, kuma ku rigayi shekarunku da ayyukanku, kuma ku tabbatar da zantukanku da ayyukanku; domin hakikanin rayuwar Mutum ita ce abinda ya tafiyar da ita a cikin biyayyar Allah, kuma "Mai hankali shine wanda ya yi ma kansa hisabi, kuma ya yi aiki domin abinda ke tafe bayan mutuwa. Gajiyayye kuma shine wanda ya bi son ransa, sai kuma yake kwallafa wa Allah buri".
5-   Lallai zalunci –Ya ku Musulmai- haramun ne a dukkan watanni, saidai Allah ya girmama alfarmar watanni hudu masu alfarma, sai ya sanya aikata zunubi a cikinsu yafi girma, kuma aiki na kwarai da lada a cikin watannin shima yafi girma.
6-    A cikin Sahihu Muslim, lallai Annabi –SAW- ya ce: "Azumtar yinin Arafah, ina zata wa Allah cewa zai kankare shekarar da take gabaninsa da wanda take a bayansa. Azumtar yinin Ashurah kuma, ina zata wa Allah cewa zai kankare shekarar da take a gabaninsa".

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...