2019/06/07

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI saw 4Shawwal 1440 الحذيفي











HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 4/Shawwal /1440H
daidai da 7/June/ 2019M


LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ALIYU DAN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY



TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
YI MA KAI HISABI KAN YIN KWAZO CIKIN XA'OI
(محاسبة النفس والاجتهاد في الطاعات)
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy–Allah ya tsare shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: YI,Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah Mabuwayi Mai yawan gafara,  Mai haquri abin godiya, "Ya san yaudarar idanu, da abinda qiraza ke voyewa" [Gafir: 19].
Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa waxanda babu wanda yake qididdige su idan ba shi ba, daga cikin waxanda muka sansu, da waxanda bamu sani ba na bayar alkhairori, da tunkuxe ababen qi da sharrori
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake, bashi da abokin tarayya, zuwa gare shi ake mayar da al'amurori.
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa, wanda aka turo shi domin rahama ga Talikai, wanda Allah ya turo shi da shiriya da haske.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da IyalanSa da SahabbanSa masu gaggawar aikata aikin kwarai lafiyayye.

Bayan haka;
Sai ku kiyaye taqawar Allah Ta'alah ta hanyar aikata abinda ya yi umurni, da nisantar abinda ya yi hani akansa ya yi tsawa, saboda babu mai samun rabo sai masu taqawa. Kuma babu mai yin hasara face saboda bijire wa Allah da bin son zuciya, Allah سبحانه  ya ce: "Amma wanda ya yi girman kai * Kuma ya zavi rayuwa ta kusa (Duniya) * To lallai ne, wutar Jahimu ita ce makoma * Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa a gaba ga UbangijinSa, kuma ya kange kansa daga son rai * To, lallai ne Aljannah ita ce makoma" [Nazi'at: 37-41].

Ya ku Bayin Allah …
Ku sani lallai samun rabon Mutum da tsirarsa da jin daxinsa a cikin rayuwarsa da bayan mutuwarsa, basu kasancewa, sai ta hanyar xa'a ga Ubangijin Talikai.
Ita kuma xa'a bata tabbatuwa sai da bin umurnin Allah Ta'alah, da kuma barin abinda Allah ya yi hani akansa.
Su kuma waxanda suke yin aiki da umurnin Ubangiji Mabuwayi da xaukaka, kuma suke qaurace wa hane-hanenSa, to lallai waxannan suna tare da "waxanda Allah ya musu ni'ima, daga Annabawa da siddiqai (masu yawan gaskatawa) da shahidai, da salihai. Kuma waxannan sun kyautatu ga zama abokan tafiya * Wannan kuma falala ce daga Allah, kuma Allah ya isa ya zama Masani" [Nisa'i: 69-70].
Amma wanda ya yi aiki da xa'ar da aka yi umurni da ita, sai ya ke haye aikin savo, to lallai ya yi biyayya wa Allah a cikin wani hali, ya kuma sava wa Allah a cikin wani hali. Kuma lallai savon da ya yi wa Ubangijinsa Maxaukaki tana cutar da aikinsa na xa'a, ta hanyar rage ladanta, kamar yadda zata iya lalata ladan aikinsa mai kyau; idan ta kasance daga cikin masu ruguza aiki.
Don haka, babu makawa ga wanda yake son yin xa'a ga Allah Ta'alah, cikakkiyar biyayya, ya haxa tsakanin aikata nau'ukan xa'oi, ya  kuma nisanci ayyukan haramun, kamar yadda Allah Mabuwayi da xaukaka yake cewa: "Ya ku waxanda suka yi imani ku yi xa'a wa Allah, kuma ku yi xa'a wa Manzo, kuma kada ku lalata ayyukanku" [Muhammadu: 33]. Ma'ana: kada ku vata ayyukanku na xa'a da aikata savo.
Kuma Allah سبحانه ya ce: "Ka ce: Lallai ni an umurce ni da na bauta wa Allah, ina mai tsarkake addini a gare shi * kuma an umurce ni da na kasance farkon Musulmai * Kuma ka ce:  Lallai ni ina tsoron idan na sava wa Ubangijina azabar rana mai girma * Ka ce: Allah nake bauta ina mai tsarkake masa addinina" [Zumar: 11-14].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma kada ku kasance, kamar wadda ta warware zarenta filla-filla bayan tukkarsa" [Nahl: 92]. Wannan kuma ya dace da kowace biyayya wanda savo da zai cutar da shi ya biyo bayansa.
Kuma Malamai suka faxa dangane da faxinsa سبحانه: "Shin xayanku yana son cewa wani lambu daga dabino da inabobo ta kasance masa, wanda qoramu suke gudana daga qarqashinsu, a cikinsa yana da kowane 'ya'yan itace, sai tsufa ya same shi, alhali kuwa yana da zurriya masu rauni, sai guguwar da take da wuta a cikinta ta same shi, sai ta qone? Kamar haka Allah yake bayyanar da ayoyi a gare ku, tsammanin za ku yi tunani" [Baqara: 266]. Suka ce: Wannan misali ne wanda Allah ya buga shi ga ayyukan xa'a wanda zunubai suke tafiyar da su, suke lalata su. A'uzu billahi Allah ya tsare.
An ruwaito daga Sauban -رضي الله عنه- daga Annabi -صلى الله عليه وسلم- lallai shi ya ce: "Tabbas, na san wasu Mutane daga al'ummata, waxanda za su zo ranar qiyama da ayyuka kwatankwacin duwatsun Tihama farare, sai Allah ya sanya su kasance qura abar watsewa. Sauban ya ce: Ya Ma'aikin Allah, ka sifanta mana su, ka fito da lamarinsu fili, domin kada mu kasance daga cikinsu! Sai ya ce:  Lallai su 'yan'uwanku, kuma daga irin fatunku, kuma yin ibada a cikin dare kamar yadda kuke yi, sai dai su Mutane ne waxanda idan suka keve da abubuwan da Allah ya haramta, sai su keta musu alfarma", Ibnu-Majah ya ruwaito shi, kuma hadisi ingantacce.
Kuma wannan hadisin a cikinsa akwai tsawatarwa mai tsanani da tsoratarwa, ga Mutumin da tsoronsa ga Allah bai hana shi aukawa cikin abinda ya haramta ba, kuma akwai tsoratarwa ga Mutumin da yake biyar da munanan ayyuka a bayan kyawawa.

Ya ku Musulmai…
Lallai Allah Mabuwayi da xaukaka ya muku baiwar taimako daga wurinsa da kuma dacewa, wajen aikata xa'oi da ayyukan kusanci a cikin watan alkhairori da albarkoki, kuma Allah ya kiyaye ku a cikinsa daga laifuka masu halakarwa, kuma ya tsare muku Shaixan, wanda yake kira zuwa ga aikata ayyukan haramun da nau'ukan vata; sai lokuta a cikin watan Ramadhana suka zama masu tsarki a gare ku, kuma sai awowinsa suka zama masu daxi a gare ku, har kuka ji daxin tilawa da sauraron Ayoyi, kuma sai zukatanku suka tsarkaka da yin xa'a ga Mai rahama, kuma kuka wulaqanta Shexan, kuma kuka kasance dangane da kyawawan ayyuka ana taimakonku. Kuma lallai maqiyin Allah Shexan abin zargi korarre yana son ya xauki fansarsa bayan an kunce xaurinsa (daga ficewar watan azumi), domin ya sanya ayyukanku kamar qura abar watsewa, kuma yana son ya sanya fajirci a gurbin taqawa, alkhairori kuma sharrace-sharrace, kuma ya vatar da wanda ya samu iko; domin su kasance tare da shi a cikin wutar Jahannama, tir da ita a makoma, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai Shexan maqiyinku ne, sai ku riqe shi maqiyi; kuma lallai yana qiran rundunarsa ne domin su kasance cikin ma'abuta wutar Sa'ira" [Faxir: 6]. Kuma riqon Shexan maqiyi yana yiwuwa ne da tabbatuwa akan xa'oi, da kuma qauracewa ayyukan haram; don haka; Madalla, kuma lale da Mutumin da ya biyar da kyawawan ayyuka a bayan kyawawa, Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya biyar da kyawawa ayyuka a bayan munana, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ka tsai da salla a gefe guda biyu na yini, da wani yanki daga dare, lallai ne ayyukan qwarai suna tafiyar da munanan ayyuka. Wannan tunatarwa ne ga masu tunawa" [Hud: 114]. Don haka; Mumini yana kyautata aikinsa, kuma yana roqon Allah koyaushe da ya azurta shi kyakkyawan qarshe.
Kuma ba a tunkuxe Shexan face da roqon Allah kyakkyawan qarshe.

Kuma bone ya tabbata ga wanda ya biyar da munanan ayyuka a bayan munana, har mutuwarsa ta zo masa, alhalin yana cikin mayen sha'awowi, to a wannan lokacin za a sanya shamaki tsakaninsa da tsakanin Duniya, kuma abinda aka jiyar da shi daxi na daxaxan abin Duniya ba zai amfanar da shi ba, sai kuma nadama ta sauko masa, sai kuma raxaxin azaba ya dawwama, Allah Ta'alah ya: "Shin ba ka gani ba ne, idan mu ka jiyar da su daxi na tsawon shekaru * sa'annan sai abinda ake musu alqawali ya zo musu * Abinda suka kasance ake jiyar da su daxin, ba zai tunkuxe azaba daga gare su ba" [Shu'ara'i: 205-207 ].
Kuma Allah ya ce: "Sai a shamakance tsakaninsu da tsakanin abinda suke marmari kamar yadda aka aikata da irin qungiyoyinsu a gabaninsu, lallai sun kasance a cikin shakka mai sanya kokonto" [Saba'i: 54].
Kuma rayuwa tana bada shaida kan makomar vangarun nan guda biyu. Kuma mai hankali shine yake xaukar darasi. Tavavve kuma shine wanda ya bijire wa shiriya, ya qi wa'azantuwa.

Ya kai Mutum>>>
Lallai kai ba za ka je ga Ubangijinka da tarin dukiya ba, kuma lallai kai ba za ka je wa Ubangijinka da iyalanka ba ko abokanka ba, kuma ba za je masa da wani abinda zai amintar da kai daga faxawa cikin azaba ba. Kawai zaka je wa Ubangijinka ne da aiki; idan ya kasance aiki ne na kwarai, to sai a shiryar da kai zuwa ga bayar da amsa ga tambayar mala'ika Munkaru da Nakiru, sai kuma a maka albishir da samun ni'ima tabbatacciya. Idan kuma aikin ya kasance ba na kwarai ba ne, sai amsarka ta vace, sai kuma a maka albishir da azaba mai raxaxi, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma dukiyoyinku, haka suma xiyarku basu zamo abinda yake kusantar da ku a wurinmu komai ba, face wanda ya yi imani kuma ya aikata aikin kwarai, to waxannan suna da sakamakon ninkawa, saboda abinda suka aikata. Kuma su amintattu ne a cikin benaye" [Saba'i: 37].
Abin tijararka shine yin biyayya ga Ubangijin Talikai, kuma dalilin samun tsirarka shine biyayya , kuma dalilin samun sa'adarka shine biyayya, xaukakarka shine biyayya. Kuma aikin xa'a zai yi amfani ne idan ya tattara wasu lamurra a cikinsa;
Al'amari na farko: Tsarkake niyya da yin ikhlasi a cikin ayyukan, ta yadda za ka nufin ganin fiskar Allah, babu riya ko yi domin a ji.
Al'amari na biyu: Xa'oin su kasance akan shiriyar Annabi Muhammadu -صلى الله عليه وسلم-, da sunnarsa.
Al'amari na uku: Shine ayyukan su tsira daga abubuwan da suke vata su.
Al'amari na huxu: Dawwama akan aikin biyayya, kamar yadda Allah -سبحانه- ya ce: "Kuma ka bauta wa Ubangijinka har mutuwa ta zo maka" [Hijir: 99].
Malaman tafsiri suka ce: Yaqini shine mutuwa, saboda abu ne da ake da tabbaci akansa, kuma saboda faxin Annabi -صلى الله عليه وسلم-: "Amma Usmanu xan Maz'un to haqiqa yaqini ya zo masa", wato mutuwa.
Kuma duk wanda ya ce: Bawa idan ya kai ga samun darajar yaqini a cikin imani, to ayyuka ibadodi za su sauka akansa, to wannan Shexan ne mai tsaurin kai vatacce mai vatarwa, bashi da komai daga Musulunci koda gwargwadon kwayar zarra, koda kuwa ya ce ya shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, saboda wannan zancen ko aqidar yana lalata kalmomin shahada biyu. Kuma mai wannan aqidar da makamancinsa yana cikin waliyyan Shexan ba waliyyan Allah Mai rahama ba, kuma koda wasu abubuwan mamaki sun bayyana a hannunsu, to hakan daga ayyukan Shexanu ne domin su vatar da Mutane. Saboda waliyyan Allah suna tsaida salla da sauran rukunnan Musulunci da wasunsu, kuma suna tabbatar da tauhidi ta hanyar tsarkake bauta da ikhlasin addu'a da yanka da bakance da neman taimakon Allah, masu tabbatar wa Allah Ta'alah da sunayensa da sifofinsa da ayyukansa, ba tare da tawili da korewa ba, kamar yadda sahabbai suka kasance da tabi'ai da waxanda suka biyo su da kyautatawa.
Kuma shin ayyuka sun sauka wa Annabi -صلى الله عليه وسلم- da sahabbansa?
Kuma shin Manzon Allah SAW ya voye haqiqar ne, su kuma waxannan (shehunan xariqar) vatattu  jahilai suka sani?
Lallai babu abinda ya kai wannan qaryar da suka yi wa Allah Mabuwayi da xaukaka, da kuma ManzonSa -صلى الله عليه وسلم- girma, inda suke cewa: Shari'a tana da zahiri da baxini. Ko faxinsu: Musulunci shari'a ne da haqiqa, kuma wai sune suka san baxinin da haqiqar?
Waxannan maqiyan addini ne, kai maqiyan dukkan Mutane ne, saboda suna kangewa daga shiga hanyar Allah, suna vata Alqur'ani da sunnoni, kuma suna adawa da Allah.
Kuma Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya yi gaskiya a inda yake cewa: "Malami guda xaya, yafi tsanani ga Shexan fiye da masu bauta guda dubu".

Sai ka bauta wa Ubangijinka -Ya kai Musulmi- matuqar ranka yana cikin jikinka, kuma ka nisanci bidi'oi, waxanda suke kishiyantar abinda Annabin shiriya; shugabanmu Muhammadu -صلى الله عليه وسلم- ya zo da shi, Allah Ta'alah ya ce: "Sai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kai da waxanda suka tuba tare da kai, kuma kada ku qetare iyaka, Lallai ne shi  Mai gani ne ga abinda kuke aikatawa" [Hud: 112].

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alkur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
            Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai, Mai mulki Mai gaskiya Mabayyani. Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa na zahiri da baxini, waxanda muka sani da waxanda bamu sani ba.
            Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya; shaidar gaskiya da yaqini.
            Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa Mai gaskiyar alqawari amintacce.
Ya Allah ka yi daxin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gaba xaya.
Bayan haka
Ku ji tsoron Allah Ta'alah a asirce da kuma a bayyane, saboda Ubangijinku shine ya cancanta a masa taqawa, kuma shine ya cancanta ga ya yi gafara.

Ya ku Bayin Allah
Haqiqa watan bauta da qari ya shuxe, Kuma Allah ya buxe wa wannan al'ummar qofofin alhairori da kyawawan ayyuka, bayan ficewar watan Ramadhana; saboda ayyukan farillai suna nan, kuma ladansu ana ninka su, kuma dukkan aikin kwarai da kuke yi a cikin watan azumi, haqiqa an shar'anta kwatankwacinsa a wajen watan Ramadhana, a matsayin wajibi ko mustahabbi.
Kuma Ubangijinku Mai rahama ne Mai jin-qai, kuma daga cikin rahamarSa akwai ya dawwamar wa Bayinsa abinda zai dawwamar da rahamarSa a gare su, da kuma kada ya yanke musu falalarSa da kyautatawarSa.
Kuma Ubangijinmu shine abin bauta a cikin sammai da qassai, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma shine abin bauta a cikin sammai, kuma abin bauta a qassai, kuma shine Mai hikima Masani" [Zukhruf: 84].
Kuma Allah shine abin bautawa a kowane zamani. Kuma shine Wadatacce da kansa, su kuma halittu dukkansu suna da buqata; ba za su tsayu ba, sai da rahamar Allah da iliminSa da ikonSa.
Kuma Allah shine wanda yafi cancantar bauta, yafi cancantar zikiri, an ce wa: Albishir Alhafiy: "Lallai wasu Mutane suna yi qoqarin bauta a cikin watan azumi, Amma idan Ramadhana ya tafi sai su bari? Sai ya ce:  Tir da waxannan Mutanen basu sanin Allah, sai a cikin watan Ramadhana".
Kuma yana daga cikin ibadodin da suke da sauqi, Yin addu'a da ambaton Allah (zikiri); sai ku yawaita addu'a da zikiri.
Kuma ku quntata wa maqiyinku Shexan da dawwama akan ayyukan kusanci, da barin ayyukan haram. Kuma haqiqa tsinannen ya sani, cewa: Lallai rahamar Allah ta game kowane abu, kuma hanyoyin biyayya suna da sauqi kuma suna da yawa.
Kuma haqiqa Annabinmu -صلى الله عليه وسلم- ya kwaxaitar da mu yin azumi guda shida a watan Shawwal, kuma ya bayyana cewa, idan suka haxu da na watan Ramadhana, to kamar azumtar shekara ne.

Ya ku Bayin Allah!
"Lallai ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi, da sallamar aminci" [Ahzab: 56].

2019/06/04

خطبة عيد الفطر 1440 د صلاح البدير HUDUBAR IDUL FIDR, 1 Shawwal 1440H










HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
IDUL FIXR, 1/Shawwal/1440H
daidai da /Yuniyo/2019M



LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. SALAH DAN MUHAMMADU ALBUDAIR

TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
TABBATAR DA XABI'U
(تمكين للقيم)
Shehin Malami wato: Salah bn Muhammadu Al-Albudair –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TABBATAR DA XABI'U, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR KABIRAN, WALHAMDU LILLAHI KASIRAN, WA SUBHANAL LAHI BUKRATAN WA ASILAN
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya saukar da mu ga bazarar falalarSa mai tarin yabanya, kuma ya ajiye mu a tsaunin karamcinSa mai faxi, kuma ya karrama mu da samun rayuwa mai yalwa mai ni'ima mai taushi, kuma ya sanya zuwan idi abu mai riba ga Bawa mai yawan tuba, mai mayar da al'amari gare shi, mai komawa gare shi,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, zuwa gare shi nake da'awa, kuma a gare shi na wakkala,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa ma'abucin usuli a dangantaka da nasaba, da babban matsayi
Ya Allah ka yi salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa salatin da zamu samu lada mai gwavi da ita, da mafi girman rabo.

Bayan haka:
Ya ku Musulmai

Ku ji tsoron Allah, lallai jiya abin misali ne, yau kuma lokacin aiki, gobe kuma buri ne, "Kuma abinda kuka gabatar domin kanku na alheri, za ku same shi a wurin Allah, yana mafifici (daga wanda kuka ajiye), kuma yana mafi girma ga sakamako" [Muzammil: 20].

Ya ku Musulmai
Haqiqa idi mai walwala ya sauka a cikinku, wanda haskensa ya walqa a samanku, ga nan idin alhalin ya yaryaxa qamshinsa mai tashi a cikinku, kuma ya watsa haskensa mai qarfi, sai sanyin safiya ya cakuxa da haskensa, To lale da wannan idin, mai qawa da furanni, mai xauke da jin daxi da farin ciki, kuma ya haskaka da iskokin natsuwa da kwanciyar hankali. Idin da zamaninsa ya sauqa, matsayinsa da mahallin aiwatar da shi suka xaukaka, kuma sunansa da takensa suka yi zaqi.
Jin daxi ya tabbata a gare ku a ranar idinku mai walwalwa, Jin daxi ya qara tabbata a gare ku a ranar idil fixr mai girma.

JIN DAXI YA TABBATA A GARE KA A IDIN DA KAI NE IDINSA
KUMA LALLAI KAI ZAKA QARA MASA KYAU DA HASKE

CIKIN XA'A KA YI AZUMI, KUMA KA KWANA TSAWON WATA GUDA KANA AZUMI
KUMA DA SUNNAR ALLAH ABAR YARDA ZAKA YI BUXA BAKI

KA NI'IMTU DA IDIL FIXR, A MATSAYIN IDI, LALLAI SHI
YINI NE MAI HASKE A CIKIN ZAMANI, KUMA SHAHARRE

YA MAI AZUMIN DA YA BAR CIN ABINCI, YANA MAI KAMEWA** WANDA YA YI YININSA YANA ABOTAR YUNWA DA WAHALA
ALBISHIRINKA, DA SAMUN FARIN CIKI (IDI) A QIYAMA, DA ** KUMA RAHAMAR DA AKA KEWAYE TA DA KYAUTA, DA KAYAN GARA

ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD

YA KU MUSULMAI
Madalla abin farin cikinku, a lokacin da kuka kammala qidayan watanku (na azumi), kuma kuka fitar da zakkar fid-da-kanku, kuma kuka xaga sauti da girmama Ubangijinku, saboda faxin Allahu akbar shine lafazin da ya kai maqura wajen girmama Allah.
Kuma duk wanda ya san UbangijinSa sai zuciyarsa ta cika da kwarjininsa da girmama shi; sai ku girmama Mahaliccinku yadda ya kamata a girmama shi, kuma ku ji tsoron kamunsa da azabarsa, kuma kada ku gafala daga godiyar falalarSa da ni'imarSa, kuma ku riqa bin umurninSa da hanuwa da haninSa. Kuma kada ku yi karan-tsaye ga umurninsa da hani, saboda sakacin 'yan sakaci, ko wuce-iyakar mai guluwwi, ko dalilin wani sababin da zai raunata gaskiyar binsa.  Kuma kada ku ji tsoron wani sai shi, kuma kada ku yi kwaxayi sai daga wurinsa, domin babu mai kusantar da bayi gare shi face shi, kuma ba a samun yardarSa face ta hanyarSa, kuma ku girmama shi, kuna masu tsarkake shi daga abinda Masu bautar gumaka da mushirkai suke faxa kuma suke aikatawa.
Kuma kada ku sanya wa takardun ayyukanku da bidi'oi da qirqirarrun lamura.
Kuma kada ku lalata addininku ta hanyar tafiya ga masu sihiri da bokaye da maqaryata (dujjal) da 'yan rufa-ido da canfi,  waxanda suke riya sanin abinda yake fake na gaibu, da yaye abinda aka voye.
Kuma kada ku yi miki ga imaninku, da rataya igiyoyi da daga, da layoyi da guru, da sauran ababen ratayawa, waxanda basu janyo dukiya, kuma basu tunkuxe fitina, basu bada kariya ga iyalai.
Kuma kada ku ruguza ayyukanku da bautar qasusuwa rududdugaggu, kuma kada ku yi xawafin qabari, kada ku yi yanka a wurin qabari, kada ku nemi agaji daga qabari, kamar yadda masu bautar qabari da gumaka suke yi. Kuma duk wanda ya kiyaye aqidarsa da tauhidin UbangijinSa, to lallai ya ji girman ma'anar kabbara, kuma ya tsayu da wajibin girmamawa ga Ubangiji Mai girma.

ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
YA KU MUSULMAI,,
Idan ranar yinin idi ta fudo, sai fiskokin Mutane suyi ta farin ciki, suna haske suna bushara, suna annashuwa da annuri.
Kuma farin cikin idi sunna ne na Musulmai, kuma alama ce daga cikin alamomin addini.
A lokacin idi an shar'anta bayyanar da jin daxi da farin ciki, ba wai bayyana baqin ciki da kururuwa da kuka ba, ko tuna cutuka da fama raunuka ba.
BA BAQIN CIKI DA VACIN RAI WANDA ZAI  RINJAYI FARIN CIKIN DA AKA SHAR'ANTA ** A RANAR IDI, DOMIN RANAR IDI NA FARIN CIKI NE

Sai ku bayyanar  da farin ciki, ku yaxa su, kuma ku yaxa sa'ida ku game Mutane da ita, kuma ku wargaza  gajimaren baqin ciki, kuma ku futar da jiki, ku shigar da farin ciki ga iyalai da makusanta da makwabta, ku warwatsa kuxi watsawa, ku shumfuxa hannayenku biyu da kyauta, kuma ku yalwata wa iyalai, ku sanya qananan yara sa'ida, ku yi kyautar murmushi da shumfuxa fiska.  
An ruwaito daga Umar xan Alkhaxxab -رضي الله عنه- ya ce: An tambayi Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- "Wane aiki yafi falala? Sai ya ce: Shigar da farin ciki ga Mumini; ka qosar da yunwarsa, ko ka tufatar da tsiraicinsa, ko ka biya masa buqatarsa", Xabaraniy ya ruwaito shi a cikin littafin Al'ausax.

Farin ciki ya tabbata ga dukkan mai baiwa mai yaxa alheri, da dukkan mai tausayi mai jin-qai, wanda yake tallafawa faqirai da miskinai, kuma yake shigar da farin ciki a zukatan marayu da marasa, da waxanda musiba ta ritsa da su, kuma yake tausayin zawarawa da waxanda mazansu suka mutu, da waxanda dukiyarsu ta yanke, kuma yake tausayin masu rauni da waxanda musiba ta shafa, kuma ya tallafa wa mutanen da aka raunata da 'yan gudun hijira.
Kuma shigar da farin ciki ga iyaye biyu, da yin biyayya a gare su, da tunkuxe dukkan abinda zai baqanta musu, shine yafi zama lazimi kuma wajibi.

ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
YA KU MUSULMAI,,
Idi ya sake komowa domin tafkunan soyayya da gulabensu su dawo, kuma magudanan qauna da qoramunsu su cigaba da gudana, sai a tsarkake zukata daga dauxar kyashi da qiyayya, kuma su wanke zukatan daga cutukan qiyayya da gaba.
Idin ya sake komowa domin farin cikinsa ya tsamar da kowane mai baqin ciki, kuma farin cikinsa ya xebe kewar kowane mai matsala, walwalarsa ta faranta wa kowane mai baqin ciki da vacin rai.
Idin yana zuwa ne domin ya wanke wasu fiskoki wanda baqin ciki ya zanu a jikin fatotinsu, har zuka zama sun xebe tsammanin nasara, tare da cewa, alhini baya dawo da abinda aka rasa, kamar yadda nuna an yi asara baya dawo da matacce.

BAN KASANCE ZAN RISKI ABINDA NA RASA BA, ** DA XANKWARA RAI, KO DA YIN DA-NASANI, KO DA FAXIN: DA DAI NI...
Sai ku yi amfani da wannan idin ta mafi kyan amfani, domin bayar da magani ga zukatan da suke karye, da bada magani ga rayukan da suke cikin hasara, kuma ku ziyarci marasa lafiya da waxanda matsaloli suka zaunar da su, kuma ku dawo da murmushi ga wanda ya rasata, haka farin ciki, shima ga wanda ya salwantar da shi.


ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
YA KU MUSULMAI,,
Yin gaisuwar idi tana qara soyayya, kuma tana gwavava qauna. Shi kuma musabahar haxa hannaye tana buxe gadar sanayya da haxin kai, sai ku sanya haxa hannaye ya zama mabuxi ga tsarkin zukata, kuma ku yi rangwame ga wanda ya yi laifi, ya yi kuskure, kuma ku yi afuwa ga wanda ya yi zalunci ya munana, kuma ku yi kyautar raba qauna, ku furta kalmar soyayya, kuma a cikin idinku ku yaryaxa qamshin afuwa mai daxi, ku shelanta afuwa, har qamshinsa ya yi ta tashi, cikin wani yanayi mai daxi,
Kuma "Baya halatta, Musulmi ya qaurace wa xan'uwansa fiye da kwanaki uku, sai su haxu; wannan ya kau da kai, wannan ya kau da kai, kuma mafi alherin biyun shine wanda yake fara yin sallama".
Kuma wane idi ne, ga zukatan da suka qaurace wa juna, kuma ina walwala ga rayukan da suke faxa, kuma ina farin ciki yake, ga qarfi biyu masu husuma.
Idi, wani fage ne na aminci da xinke varaka. Idi ne da ake samun haxin kai a cikinsa, kuma ake haxe kalma a cikinsa, ake toshe varaka a cikinsa, ake kunyata Shexan a cikinsa, a cikin wata al'umma mai qaunar juna, da tsarkin hali mai jagora, a cikin wani taron da yake maimaituwa yake sake komowa.
Kuma babu wani idi ko farin ciki ga zukatan da girman kai, da ruxi, da zalunci suke jagorantsarsu.
Haka babu farin ciki (idi) ga jikin da suka yi wanka irin na idi, saidai basu wanku daga dauxar gaba da qiyayya da adawowi. Haka babu shi ga suka sanya tufafin idi, a jikin dauxar qiyayya.

ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
YA KU MUSULMAI,,
Iyali sune suke bayar da tarbiyya ga zuciya, kuma suke magance raunuka, Shi kuma idi lokaci ne na haxuwan iyalai da iyayensu da kakanni, sai vangarorin iyalai na nesa su tattaru, sai 'ya'ya da jikoki a cikinsa su haxu, sai samarinsu su haxu da dattawansu; A nan, sai ku tsayu da wajibin sadar da zumunci da kyautatawa, kuma ku yi dashe a cikin zukatan 'ya'yanku maza da mata, aqidar so ko jivintar addini da aqida da tauhidi. Da kuma aqidar jivintar wannan qasa mai girma, da kulawa da amincinta da zaman lafiyarta da haxin kanta, da kulawa da 'yan qasan, da wajabcin lazimta jama'a, da watsi da rarrabuwar kai da savani. Kuma ku xora 'ya'yanku akan manhajin tsakaitawa, ku kare su daga faxawa hanyoyin ketare iyaka da guluwwi da irhabi. Kuma ku riqa qarfafarsu domin su kasance masu taimakon jami'an tsaro, wajen kiyaye amincin qasar da tsare-tsarenta. Kuma ku kwashe su zuwa ga wuraren samun ilimi, da sani, da cin nasara da gogewa. Kuma ku tarbiyantar da su akan kyawawan halaye da xabi'u, da qoqarin samun tsarkin hali masu falala, da kamewa a cikin zance, da abinci, da cakuxa. Kuma ku tarbiyantar da su akan haquri da adalci da tawali'u, da sadar da zumunci, da girmama qarami da babba, da mutunta ma'abuta falala da ilimi
FALALA ITACE, LADABI YA KASANCE A CIKIN IYAYE DA KAKANNI ** TABBATACCE, HAKKA KUMA YA DASU A CIKIN 'YA'YA DA JIKA

SUN QAWATA TSHOHONSU, DA KYAWUN NA YANZUNSU **  DA KUMA KYAWAWAN HALAYE,  DA MANAGARTAN SIFOFI

MADALLA DA MUTANEN DA KAI RESHEN ASALIMSU NE? ** KUMA MADALLA DA KAI, TUNDA KAI DAGA TUSHENSU KA ZAMA RESHE                                
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
YA KU MUSULMAI,,
Shari'a ta yi umurnin a riqa cika alqawalin da Mutane suke qullawa a tsakaninsu na saye da sayarwa, da haya, da auratayya da shika, da muzara'a da sulhu da mallakawa, da wanin waxannan daga cikin abinda Mutane suke qullawa, sai a samu jayayya da inkari da makirci a tsakanin masu qullawan, ko a samu ha'inci da gisshu da bugun hanci, da yin qarya a tsakanin wakilai da masu haya da ma'aikata da wanda ake mu su aikin. Kuma wasu ma'aikatan su kan qulla ciniki kan wasu sana'oin da basu iya su ba, da ayyukan da basu kware a cikinsu, koma basun iya su ba. Saboda kowa yana son tara kuxi ne, wa lau ta hanyar haram, kuma waxannan burinsu shine su yi makirci ga 'yan'uwansu, sai dai wanda Allah ya kare shi da taqawa. Kuma Allah zai yi hukunci a tsakanin Bayi a ranar hukunci da rarrabewa. An ruwaito daga A'isha -رضي الله عنها- lallai wani Mutum ya zauna a gaban Annabi -صلى الله عليه وسلم-sai ya ce:
Ya Manzon Allah! Lallai ina da Bayi guda biyu, suna sharara mini qarya, kuma suna ha'intata, kuma suna sava umurnina, Ni kuma zaginsu, ina dukansu, To yaya lamarina yake dangane da su? Ya ce: "Za a qididdige abinda suka yi na ha'intarka da sava maka da qaryar da suka yi maka, da uqubar da ka musu; idan har uqubar da ka musu ya zama daidai da zunubinsu to shi kenan; baka da zunubi kuma baka da wani abu akansu. Idan kuma uqubar da ka musu bata kai zunubansu ba to wannan falalarka ce. Idan kuma uqubar da ka musu ta wuce gwargwadon zunubansu, to sai a kwato musu abinda ya xoru. Ya ce: Sai Mutumin ya koma gefe yana kuka yana kururuwa, Sai Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: Shin baka iya karatun littafin Allah ba ne, faxinsa: (Kuma za mu sanya ma'aunan adalci, ga ranar Qiyama, saboda haka, ba a zaluntar rai da komai, kuma da zai kasance daidai da kwaya daga komayya za mu zo da shi. Kuma mun isa mu zamo masu hisabi" [Anbiya'i: 47] Sai Mutumin ya ce: Wallahi! Ya rasulul lahi! Babu wani abu da naga yafi alheri ga ni da su fiye da na rabu da su, Ina shaida maka cewa, allai su 'yantattu ne gaba xayansu. Ahmad ya ruwaito shi da Tirmiziy.
Sai ku ji tsoron Allah -Ya ku Musulmai- kuma ku yi adalci da gaskiya a cikin mu'amala. Kuma duk wanda ya kasance wajen bayar da abinda yake wuyansa, kamar yadda yake kiyaye abinda nasa ne, to lallai ya yi adalci cikin hukunci, kuma ya yi daidai a hukunci.
Musulunci yana umurni da cika alqawulan da aka qulla, da yin gaskiya cikin mu'amala. Kuma yana hani akan cinye amana da ha'inci da zalunci.
Kuma duk wanda ya shiga daga cikinmu; -Musulmai- yqasar waxanda ba Musulmai ba, da alqawali da amana daga wurinsu -wato, bizar izinin shiga da suka bashi, domin ya iya shiga qasarsu, to haramun ne ya ha'ince su, ko ya musu sata, ko ya yi ta'addanci ga amincinsu da rayukansu da mutuncinsu da abubuwan da suka mallaka. Kuma duk wanda ya sace musu wani abu, to wajibi ne ya mayar da shi ga ma'abutansa, saboda dukiya ce, tsararriya.

 ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
YA KU MUSULMAI,,
Kwanaki suna juyawa, mutuwa kuma tana halartowa, Mutane kuma ko dai matafiyi ko wanda ake bankwana da shi, da wanda ake wawashewa ake masa gaggawa, ko wanda ake masa jinkiri. Kuma dukkan halittu zasu tafi ga qarewa, kuma dukkan mulki to zai qare, kuma babu abinda zai dawwama sai mulkin Allah, tsarki ya tabbata a gare shi; Mi mulki Mai rinjaye, wanda ya kaxaitu da buwaya da wanzuwa, duk kuma abinda ba shi ba, to zai qare;
Domin DUKKANMU MUTANE NE ** QADDARA TANA NAXE MU
KUMA MU MUNA CIKIN TAFIYA NE **MUNA TAFIYA ZUWA QABARI

MUTUWA ZATA NAXE MU ** SANNAN ZA A MANA MATATTARA
Kuma don me kake jinkirta tuba, alhali baka da wani uzuri, kuma har yaushe ba za ka dena laifi ka hanu ba

HAR YAUSHE JINKA BAYA KARKATA GA MAI TUNATARWA ** KUMA KWARYAR ZUCIYARKA BATA YIN TAUSHI GA MAI NUSARWA

INA GANIN KANA RUXUWA DA RAYUWA ** KUMA BAKA YIN GAGGAWAR KOMAWA GA ALLAH
KUMA KANA KWAXAYIN WANZUWA, AMMA TA YAYA ZAKA TABBATA? ** ALHALIN DUNIYA BA WURIN ZAMA BA CE, GA MAZAUNINTA

Sai ku nisanci aikata savo, da tasowa a cikinsa, da rungumarsa, da sakaci wajen keta ladduba, da ta'addanci ga iyakokin shari'a da addini.
Kuma ku nisanci aikata haramun, ku kiyayi kusantarsu da aikata su, kuma kada ku cakuxa da sabubbansu da abinda suke kai mutane ga aikata su, kuna masu godiya ga Allah, akan kyautatawansa masu gamewa, da baiwanmasu girma.
Kuma ku kyautata makwabtakar ni'imomi, sai ku kiyaye ni'imomin da suke hannu, kuma ku janyo ni'imomin da babu su, kuma sai kyautar Allah ta tabbata akanku da karamcinsa da kyautarsa. Saboda ni'ima bata juyawa bayan ta fiskanto, kuma ba a xauke baiwa bayan ta sauka, kuma ba a cire wata karama bayan an bayar da ita, sai saboda wasu kyautan da ba ayi godiya akansu ba, ko saboda kura-kuran da suka bayyana a cikin Mutane suka shahara. Kuma ni'imomi idan aka yi godiya akansu sai su tabbatu, idan kuma aka kafirce aka butulce musu sai su gudu.  
Kuma ku kusanci qofar tuba da mayar da al'amari ga Allah, kuma ku yanke igiyar (tuba) sai gaba, ,,, sai gaba, ,,, kuma ku goge abinda ya gabata na savo, da abinda zai riske shi na kyautatawa. Kuma ku kiyaye salloli biyar na farilla, a lokacin da ake kiransu, kuma kada ku qi halartar jam'i sai idan da uzuri. Kuma ku bayar da zakkar dukiyoyinku. Ku yi gaggawan hajji matuqar kuna da iko. Kuma ku sada zumuncin wanda ya yanke muku. Ku baiwa Mutumin da ya hana muku. Ku yi afuwa ga wanda ya zalunce ku. Kuma mai sada zumunci bashi ne mai ramuko ba, a'a cikakken mai sada zumunci shine idan aka yanke zumuncinsa sai ya sadar da ita. Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da varna. Kuma kada ku yi mu'amala da kasuwancin riba mai hasara, da qarin da yake cikinsa na zalunci, da ninke-ninkensa mai muni. Kuma ku nisanci musa haqqoqi, da yin wasa da farashin kayan sayarwa, da gisshu, da najashu, da zaftare sikeli da ma'aunai. Kuma ku nisanci dukiyar marayu, da awaqafai da wasiyoyi; kada ku cinye su da zalunci da ta'addanci. Kuma ku kyautata wa matanku da 'ya'yanku maza da mata, kuma ku tsayu wajen ciyarwa ta shari'a ta dole, kuma ku mu'amalance su da tausasawa da tausasawa da soyayya da jin-qai da rahama.
Kuma ku kiyaye harsunanku, kuma ku kiyaye farjojinku, kuma ku tsarkake zukatanku daga qyashi da qulli da hassada da qiyayya da gaba, kuma ahir xinku kan zama a majalisar fasiqci da fajirci.
Kuma ku nisanci husumomi da faxace-faxace, kuma ku riqa karvar uzuri, kuna yafiyar tuntuve. Kuma kada ku yanke zumunci, kada ku juya baya, kada ku yi qiyayya, kada ku yi hassadar juna, ku kasance -Ya ku bayin Allah- 'yan'uwan juna.

YA KU MUSULMAI,,,
Wannan yini ne na yafiya, da gaisuwa, da sulhu, sai ku yi rahama ga juna, ku haxa kanku, ku yi rangwame, ku gaggaisa, ku yi sulhu, domin farin cikinku xaya ya ninninku, idinku ya yawaita.

ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD

Ina faxan abinda kuke ji, kuma ina gafarar Allah ga ni da ku da sauran Musulmai daga dukkan zunubai da kura-kurai, sai ku nemi gafararSa, lallai shi ya kasance Mai yawan gafara Mai jin-qai.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMDU
Godiya ta tabbata ga akan ni'imominSa waxanda suka shuxe suka gabata,  Ina gode masa godiyar da ta kai maqura, tafi cika da kamala, da gamewa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai yake bashi da abokin tarayya,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne manzonsa zavavve daga cikin halittunsa da ya qaga,
Ya Allah ka yi salati a gare shi da iyalansa da sahabbansa salati mai ninkuwa mai dawwama, har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka:
Ya ku Musulmai

Ku ji tsoron Allah wanda babu abinda yake vuya a gare shi na manufofi da niyyoyi, kuma babu wani abu da aka voye a cikin zukata da yake vuya masa, saboda voyayyun abubuwa na sirri a wurinsa a bayyane suke, kuma sirri a wurinsa a fili yake, kuma yana tare da ku a duk inda kuke, kuma Allah dangane da abinda kuke aikatawa Mai gani ne.

Ya ku Musulmai
Zaman lafiya yana da farashinsa, Qasa kuma tana da rundunoninta, Hukunci kuma yana da mazajensa.
Kalmar godiya da yabo da jinjina muke gabatarwa ga jami'an tsaronmu masu zaman dako, a wuraren xaukaka, waxanda basu xauki rayukansu a bakin komai ba, kuma suka xauki makamai, suka fiskanci mutuwa domin su kare alfarma da tsarkaka wurare.
Ya ku zaratan mazaje, dakarun sojoji, Ya waxanda kuka shayar da turvayar wannan qasar da jinanenku, kuma kuka bayar da rayukanku domin ku kare ta, Ya waxanda kuka tsaya, kuka toshe ta'addanci mai muni, Ya masu bada kariya ga harami guda biyu, Ya tanadin gida, kuma buwaya ga qasa, kuma garkuwansa, kuma sulken kare shi: Babu kalmar da zata iya biyanku, kuma babu yabon da zai saka muku, kuma babu godiyar da zata saka muku. Ku ne idin; wato masu tsaronsa kuma garkuwansa, kuma sulken kare shi.
Masu yin bauta sun yi bauta, masu ruku'i sun yi ruku'i, masu azumi sun yi azumi, a cikin zaman lafiya da aminci, wanda jihadinku ya samar da shi, kuma fansar da kuka bayar ya kiyaye shi.
Idinku mai albarka ne, (wannan) kalma ce da zata kewaya kafafen aikinku da benayenku. Kuma kowace shekara ku kasance cikin alheri, jihadinku abin taimako, maqiyanku qasqantattu, qasarku abar kiyayewa, nasararku ta zo a kusa.
Godiya  a gare ku, Ya masu gadin qasa, masu kiyaye aqida da addini, godiyar da bata kai ga matsayinku ba!
KA BANI ARON HARSHE -YA KAI WAQA- DOMIN NAYI GODIYA ** IDAN KA GAGARI GODIYA, TO BAKA KASANCE WAQA BA

ZAN RIQA AMBATONKU IRIN AMBATON MASOYI GA MASOYANSA ** KUMA ZAN GODE MUKU IRIN GODIYA MAI FARI GA RUWAN SAMA
Addu'armu ta gaskiya a wannan yini na idi, daga saman minbarin Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- mai daraja, itace: Allah ya rubuta muku nasara cikin gaggawa, kuma ya mayar da maqiyanmu cikin tavewa, da hasara.
AMIN, AMIN, BA ZAN YARDA DA FAXIN GUDA XAYA BA ** SAI NA KAI SU ZUWA GA AMIN DUBU BIYU

Kuma za mu ce ga dukkan maqiyinmu ga amincin qasarmu da zaman lafiyarmu da bunqasarta:
SAMUN NASARA A QASARMU YA MAKA NISA ** ABUN NEMANMU SHINE KA TAFI QASARKA KA YI WALKIYA A CAN DA TSAWA
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
YA KU TARON MATA,,
Lallai ne Allah ya xaukaka ku, ya darajanta ku, kuma ya xaukaka matsayinku, ya kiyaye haqqoqinku, sai ku yi godiyar ni'ima, ku riqa tuna wannan baiwar, ku runtse sashe na ganinku, ku kiyaye farjojinku, kuna yin sadaka, kuma ku yawaita neman gafara, kuma kada ku yawaita tsinuwa, kuma kada ku butulce wa abokin zama, kada ku yi tabarruji, kada ku yi fita na tsiraici.

Kuma mace maxaukakiya kamammiya, ba za ta yarda ta zama tushen tayar da sha'awa ko fitina ga idanu mafarauta, da gani na ha'inci na banza, da rayukan qasqantattu, da maganansu na wulaqantattu, yasassu.

ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
YA KU MUSULMAI,,
Lallai baqonku ya qaura, Ramadhan ya tafi, saidai kyawawan ayyuka basu qarewa; don haka kada ku rufe Alqur'ani, kada ku hana sadakar biredi, kuma kada ku hana mabuqaci, kada ku yanke ayyukan kyautatawa, kada ku qauracewa yin azumi, kada ku bar sallolin dare; domin kyautatawa ya kan yi kyau idan kyautatawa ya biyo bayansa, kamar yadda munanawa yake da matuqar muni idan ya zo a bayan kyautatawa.
Kuma wanda ya azumci Ramadhana, sannan ya biyar da guda shidda a watan shawwal, to kamar ya yi azumin shekara ne.
Kuma wanda bai fitar da zakkar fidda-kai ba, to ya yi gaggawan fitar da ita.
Wanda ya zo ta wata hanya, to ya koma ta wata hanyar ta daban, idan ya samu damar aikata hakan, yana mai koyi da Annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu -صلى الله عليه وسلم-.

ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD
Albishirinku:
Ya waxanda kuka yi sallolin dare, kuka yi azumi ... Albishirinku, Ya waxanda kuka yi sadaka, kuka yi qoqari, haqiqa wahalar ta tafi, kuma gajiyar ta gushe, ladan kuma ya tabbata da izinin Allah Ta'alah.
Allah ya karvi azuminku da sallolinku, kuma ya maimaita muku waxannan ranaku (na Ramadhana) masu albarka na shekaru dayawa, da zamani masu tsawo, alhalin muna cikin lafiya da rayuwa mai daxi.
Ya Allah ka karvi ayyukanmu, kuma ka tsarkake su, kuma ka xaukaka darajarmu.
Ya Allah ka bamu daga cikin gurace-gurace na qololuwansu, alherori kuma qarshensu.
Ya Allah ka karvi azuminmu da sallolinmu, da addu'oinmu ya Mafi jin-qan masu jin qai.
Ya Allah ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka qasqantar da shirka da mushirkai, ka ruguza maqiya wannan addinin, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka dawwamar wa qasar harami biyu maxaukaka, amincinta da wadacinta da buwayarta, da zaman lafiyanta, da sauran qasashen Musulmai.
Ya Allah ka datar da shugabanmu majivincin lamuranmu; mai hidimar harami biyu maxaukaka; Bawanka Salman xan Abdul'aziz zuwa ga abinda kake so, ka yarda da shi, kuma ka riqi makyamkyamarsazuwa ga aikin xa'a da taqawa, kuma ka gyara masa abokan shawarinsa, ka azurata shi da lafiya, kuma ka kiyaye shi daga dukkan sharri da abin qi.
Ya Allah ka datar da na'ibinsa da 'yan'uwamsa da 'ya'yansa da ministotinsa da masu taimakonsa, zuwa ga abinda xaukakar Musulunci da gyaruwan Musulmai yake cikinsa, Ya Ubangijin talikai.
Ya Allah ka taimaki addininka da su, ka xaukaka kalmarka da su, kuma ka sanya mu da su mu zama shiryayyu masu shiryarwa, da rahamarka ya mafi jin qan masu jin qai.
Ya Allah ka datar da xaukacin shugabannin Musulmai, su yi hukunci da shari'arka, su bi sunnar annabinka Muhammadu -صلى الله عليه وسلم-.
Ya Allah ka yaye baqin cikin masu baqin ciki,kuma ka kwaranye musibar masu musiba, kuma ka biya bashin masu bashi, kuma ka warkar da marasa lafiyanmu da marasa lafiyan Musulmai, kuma ka yi rahama ga mamatanmu da mamatan Musulmai.
Ka gafarta wa iyayenmu maza da mata, da matanmu da zuriyyarmu da 'yan'uwanmu da makusantanmu da malumanmu, da jagoran lamuranmu, Ya mafi jin qan masu jin-qai.
SUBHANA RABBIKA RABBIL IZZATI AMMA YASIFUNA, WA SALAMUN ALAL MURSALINA WAL HAMDU LILLAHI RABBIL ALAMINA.

  ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, WAL LAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMD.

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...