2019/03/31

FIKIHUN AZUMI (فقهُ الصيام)


FIKIHUN AZUMI
(فقهُ الصيام)

NA
SHEHIN MALAMI
HAISAM BN MUHAMMADU JAMIL SARHAN
Tsohon Malami a Sakandaren Masallacin Annabi -SAW-,
kuma shugaban shafin intanet


TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
Bismillahir RahmanirRahim
AZUMI wato, SIYAAM a harshen larabci, shine: Kamewa.
A shari'akuma, Bauta wa Allah, ta hanyar kamewa daga cin abinci, da abin sha, da sauran ababen da suke karya azumi, daga ketowar alfijir na-gaskiya, zuwa faduwar rana.
RUKUNNAN AZUMI
1-    Niyyah.
2-    Kamewa daga ababen da suke karya azumi.

KARKASUWAR NIYYAR AZUMI
1-    Niyyar azumin farilla: Babu makawa dole ne, sai an kwana da niyyar, ga azumin farillai, tun cikin dare, wato gabanin ketowar alfijir. Kuma yana wadatarwa a kulla niyyar daga shigan watan azumi. Kuma mahallin niyya zuciya ne, furta ta kuma da harshe bidi'a ne.
2-    Niyyar azumin nafila: Kuma niyyar tana inganta idan aka yi ta cikin kowace dakika ko lokaci na yini, matukar bai kusanci abinda suke karya azumin ba. Saidai zai fara samun lada ne, daga lokacin da ya kulla niyyar.
KARKASUWAR AZUMI
1-    Azumi na wajibi: (Ramadana, kaffara, da bakance).
2-    Na nafila.
SHARRUDAN WAJABCIN AZUMIN RAMADANA
1. Musulunci.
2. Hankali.
3. Balaga (Shi kuma Yaron da ya kai shekarun tantancewa, za a rika kwadaitar da shi kan azumi, waliyyinsa ya rika umartarsa).
4. Zaman gari (Saboda azumi baya wajaba akan matafiyi, kuma abinda ya fi a gare shi, shine ya yi azumin, matukar azumin ba zai yi tsanani a gare shi ba; saboda hakan shine aikin Annabi –S.A.W-, kuma saboda hakan shi ya fi saurin sauke nauyin da ya doru a wuyansa, kuma ya fi sauki ga Mutum, kuma domin ya riski falalar yin azumi a cikin wannan watan).
5. Lafiya.
6. Kubuta daga jinin haila da na haihuwa.
JINYA KASHI BIYU NE DANGANE DA AZUMI:
1-      Jinyar da ba a tsammanin gushewarta.
Ana yin kiyasin tsofon da ya gajiya; wanda kwata-kwata ba zai iya azumi ba, da majinyacin da ba zai iya azumin ba; sai azumin ya sauka akansa, sai dai kuma zai ciyar da miskini guda daya a madadin kowane azumi; ko ta hanyar ya hada miskinai gwargwadon yawan kwanakin da bai yi azuminsu ba, sai ya ciyar da su. Ko kuma ya rarraba abinci ga miskinan, na tsawon wadannan kwanakin; ta hanyar baiwa kowane miskini rubu'i wato daya bisa hudun sa'iy irin sa'in Annabi SAW; (1/4), (Ma'ana: ya bayar da gwargwadon awun rabin kilo, da giram goma, na shinkafa ko alkama mai kyau).
Kuma abu ne mai kyau ya hada da abinda zai zama, kamar miya a gare shi, na mai, ko nama.
2-      Jinyar da ake tsammanin za ta gushe; sai dai yin azumi zai tsananta ga mai ita, Wannan kuma ana kiyasin Mace mai haila da jinin biki (haihuwa), da Mai shayarwa, da Matafiyi, da wannan nau'i na jinya, Sai Majinyacin ya biya adadin kwanakin da ya karya azumi a cikinsu; idan har ya warke. In kuma ya rasu gabanin ya samu damar biya, to azumin ya fadi daga wuyansa.

Kuma shigowan watan Ramadana yana tabbatuwa, ta hanyar ganin jinjirin wata, ko kuma watan Sha'abana ya cika kwanaki talatin (30).
ABABEN DA SUKE LALATA AZUMI
(amma ana yin uzuri ga Jahili, da Mai mantuwa, da wanda aka masa tilasci)
1-    Ci, ko sha da ganganci, Amma wanda ya yi da mantuwa to azuminsa ingantacce ne.
2-    Jima'i, Idan har ya auku a cikin yinin Ramadana, alhali yin azumin wajibi ne akansa, To dole ne ya yi kaffara mai tsanani, wanda itace, 'yanta baiwa, idan kuma bai samu ba, sai ya yi azumin watanni biyu a jere, idan kuma ba zai iya ba, sai ya ciyar da miskinai sittin (60).
3-    Fitar maniyyi, ta hanyar runguma, ko sumba, ko hada jiki, ko makamancinsu.
4-    Abinda ke daukar ma'anar ci da sha, Misalin allurar abinci. Ita kuma allurar da ba a sanya mata abinci a cikinta ba, ita kam bata karya azumi.
5-    Fitar da jini ta hanyar kaho. Amma fitar da jini kadan, domin awu, ko makamancin haka, shi kam baya karya azumi.
6-    Yin amai  da ganganci.
7-    Fitar jinin haila da na biki (haihuwa).
MUSTAHABBAN AZUMI
1-     Yin sahur.
2-     Jinkirta yin sahur.
3-     Gaggauta buda-baki.
4-     Yin buda-baki da dabinon da bai bushe ba (rudab). Idan kuma bai samu ba, sai ya yi da busasshen dabino, kuma dabinon su kasance wutiri, Idan kuma bai samu ba, sai ya sha ruwa, Idan kuma bai samu wani abu ba, sai ya yi niyyar karya azumin a zuciyarsa.
5-     Yin addu'a a lokacin buda-baki, da a halin azumi.
6-     Yawaita yin sadaka.
7-     Dagewa wajen yin sallolin dare.
8-     Karatun Alkur'ani.
9-     Yin umrah.
10-  Fadin: Ni mai azumi ne, ga wanda ya zage shi.
11- Kokarin neman Lailatul kadr.
12- I'itikafi a goman karshen watan azumi.
MUKRUHAN AZUMI
1-      Kaiwa makura cikin kurkuran baki.
2-       'Dandana abinci, ba tare da bukatar hakan ba.
YANA HALATTA GA MAI AZUMI
Hadiye yawu, 'dan'dana abinci yayin bukata, yin wankan ibada, Yin asiwaki, shafa turare, da yin wanka domin jin sanyi.
HARAMUN NE GA MAI AZUMI
Hadiye kaki (sai dai baya karya azumi), Da yin sumba, ga wanda yake tsoron lalacewar azuminsa, da fadin zancen zur ko shaidar karya (da aikata kowane haramun), da aikin jahilci (wauta, da rashin hakuri), da yin wucel (ma'ana yin kwanaki biyu bai yi buda-baki ba).
AZUMIN NAFILA
1-      Yin azumin ranaku shida a watan Shawwal, ga wanda ya cika azuminsa na Ramadana. Kuma abinda ya fi, shine, a fara yinsu daga yini na biyu, kuma a jeranta su.
2-       Azumin yinin Arafah, ga wanda ba Mahajjaci ba.
3-      Azumin yinin Ashura, da kuma ranar tara, da ranar goma sha daya (9, 10, 11, na watan Muharram).
4-       Azumin ranar Litinin da Alamis, kuma na ranar litinin sunnarsa tafi karfi.
5-      Azumtar kwanaki uku, a kowane wata, kuma abinda yafi shine azumtarsu ya kasance a kwanakin da wata yake cika haskensa wato, 13, 14, da 15.
6-      Azumtar yini, da shan ruwan yini.
7-      Yin azumi a cikin watan Allah na Muharram.
8-      Azumtar yini tara na farkon watan Zul-hijjah.
9-      Yin azumin watan Sha'aban, amma kada ya kammala shi gaba dayansa.
AZUMI NA MAKRUHI
Yinin Juma'a, da Asabat, da Lahdi, makruhi ne a kebance kowanne da azumi, sai dai idan kebe shin ya zamo sakamakon wani sababi ne, to ba makruhi ba ne, kamar yinin Arafah.
AZUMI NA HARAM
1-      Kebe watan Rajab da azumi.
2-      Azumtar yinin shakku, Amma wanda ya saba da wani azumi, to babu komai akansa.
3-      Azumtar yinin idi guda biyu.
4-      Azumtar kwanaki uku na bayan idin layya (Tashrik), sai ga Mahajjacin da bai mallaki hadaya ba.
5-      Azumtar zamani (kullum-kullum).
Mustahabbi ne, a jeranta azumin ramuko, kuma ya dace, Mutum ya yi gaggawan yinsu, daga bayan idi, kuma bai halatta ya jinkirta ramukon da yake kansa har wani Ramadanan ya sake shigowa ba, Idan kuma ya jinkirta shin, ba tare da wani uzuri ba, to dai wadancan azumin da suka wucen sune zai rama (babu kari), sai dai kuma ya yi zunubi.
ZAKKAR FID-DA-KAI (FIDR)
            Tana wajaba ne ga wanda yinin Ramadana na karshe ta fadi masa alhalin yana Musulmi, sai (aka yi dacen) sa'in abinci guda 'daya ya doru akan abincinsa da na iyalan gidansa da bukatunsa na asali.
            Kuma mustahabbi ne a cire ta ga 'Dan tayi (da yake cikin mahaifa).
HIKIMAR FITAR DA ZAKKAR FID-DA-KAI:
1-    Domin ta tsarkake Mai azumi daga wargi da kwarkwasa.
2-    Domin a wadatar da Miskinai; kada su yi roko a ranar idi (yinin farin ciki).
LOKACIN FITAR DA ZAKATUL FIDR
1-    Lokaci na halacci, shine gabanin ranar idi da yini daya ko biyu.
2-    Lokaci na mustahabbi, shine, gabanin ayi sallar idi, bayan ketowan alfijir.
3-    Lokaci na haramci wannan kuma shine, Bayan yin sallar idi.
GWARGWADON ZAKATUL FIDR
Sa'iy daya ne na dangogin abincin da Mutane suka rika a matsayin abinci, don haka, bata isarwa idan aka fitar da ita daga cikin kudi.
(Gwargwadon sa'iy shine, kilo biyu, da giram arba'in na alkama mai kyau).
SALLAR IDI
Farilla ce akan kowane Mutum.
Kuma ana sallatar ta ne, bayan dagowar rana daidai da kibiya, har zuwa lokacin gotawar rana (zawali).
Kuma ba a yin ramukonta, idan ta wuce.
Sunnah shine a yi ta a sahara ko fili, ba cikin gini ba.
Kuma ya halatta a yi ta a cikin Masallaci.
Mustahabbi ne Mutum ya ci dabino wutiri gabanin sallar idi, kuma ya yi tsafta, ya fesa turare, ya sanya mafi kyan tufafinsa, ya tafi ta wata hanya, ya komo ta wata hanya.
Babu laifi kan gaishe-gaishen idi, ta hanyar fadin: TAKABBAL LAHU MINNAH WA MINKUM (Allah ya karba mana; mu da ku).
Kuma sunnah ne, yin kabbarori mudlakai, a daren idi, da bayan salloli, har zuwa faduwar ranar yinin idi. Kuma SIFAR KABBARAR ITACE:
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILAHA ILLAL LAHU, ALLAHU AKBAR, WALLAHU AKBAR, WA LILLAHIL HAMDU.
Kuma SIFAR SALLAR IDI ita ce Raka'oi biyu gabanin yin huduba, zai yi kabbarori shida a raka'ar farko, bayan kabbarar harama.
A raka'a ta biyu kuma gabanin fara karatu, sai ya yi kabbarori biyar, kari akan kabbarar tasowa.

2019/03/29

22 Rajab 1440 Hudubar dr Aliyu Huzaifiy akan HIKIMA الحكمة











HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 22/Rajab/1440H
daidai da 29/Maris/ 2019M


LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH DR. ALIYU DAN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY



TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
HIKIMA
(الحكمة)
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy–Allah ya tsare shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: HIKIMA,Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Godiya ta tabbata ga Allah Mabuwayi Mai yawan baiwa,  Mai gafarar zunubai, Mai karbar tuba, Mai tsananin ukuba, Ma'abucin ni'imah, Babu abin bautawa face shi, zuwa gare shi makoma take.
Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa akan ni'imominSa, wadanda muka sani, da wadanda bamu sani ba. Godiya tasa ce, da yabo mai kyau, a gare shi nake dogaro kuma zuwa gare shi tuba take.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin tarayya, Mai jin kai Mai yawan tuba.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne ManzonSa, wanda ya zo da hasken sunnah da kuma Alkur'ani.
Ya Allah ka yi dadin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu da iyalansa da sahabbansa, wadanda suka taimaki Musulunci, kuma suka kaskantar da kafirci, har ya kasance a cikin hasara.
Bayan haka
Ku ji tsoron Allah Ta'alah kuma ku yi masa da'a, domin babu wanda zai samu rabo sai ta hanyar yin biyayya a gare shi, kuma babu wanda zai tabe face mai sabon Allah.  Allah Subhanahu ya ce: "Kuma wadanda suka yi da'a ga Allah da Manzonsa, to wadannan suna tare da wadanda Allah ya yi ni'ima a gare su, daga Annabawa da masu yawan gaskatawa, da masu shahada, da salihai, kuma wadannan sun kyautatu ga zama abokan tafiya" [Nisa'i: 69].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, to lallai yana da Jahannama, yana mai dawwama a cikinta har abada" [Jin: 23].

Ya ku Bayin Allah
Kowane Mutum yana son, kuma yana fatan kuma yana kokarin ya kasance a mafi kyan hali, kuma akan mafi girman sifofi, kuma ya kasance da'iman akan hanya mafi mikewa, kuma da'iman ya kasance tabbatacce akan tafarki madaidaici, wanda Allah ya hada masa alkhairin rayuwa, da alkhairin mutuwa.
Kuma kowane Mutum yana kin tabewa da hasara da kaskanci da karanta da munanan sifofi da dabi'u ababen ki, da hanyoyin wulakanci da tabewa da bata, kuma yana kin mummunan karshe cikin dukkan halaye,.
Kuma kowane Mutum yana son ya tunkude wa kansa sharrori da abubuwa masu halakarwa, kuma yana yin kokarin haka, da dukkan abinda yake da iko akansa na sabubba masu tseratarwa.
To, shin akwai hanyar samun wadannan ababen neman madaukaka? Kuma shin rabauta da wadannan alherorin, da tsira daga sharrace-sharracen rayuwa, da fitinoni masu batarwa, da munanan karshe cikin al'amura, shin wannan abu ne mai yiwuwa?
E, abu ne mai yiwuwa, ga wanda Allah ya saukake masa.
Lallai hanyar samun wadancan alkhairorin, da tunkude karshe na sharri, a cikin wannan rayuwar da bayan mutuwa, hanya ce guda daya, kuma hanya ne mikakke, wanda babu na biyunsa, Wannan kuma ita ce, HIKIMA, da ma'anarta faffada mai gamewa, Allah Ta'alah ya ce:  "Yana bayar da hikima ga wanda ya so, kuma duk wanda aka bashi hikima to lallai an bashi alkhairi mai yawa, Amma babu mai wa'azantuwa face ma'abuta hankula" [Bakara: 269].
Amma hanyoyin kaucewa hikima da nisantarta, to lallai suna da yawa, babu mai kididdige iyakarsu in banda Allah Ta'alah, Allah Mabuwayi da daukaka yana cewa: "Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku bi hanyoyin Shedan, domin duk wanda ya bi, hanyoyin Shedan, to lallai yana yin umurni da alfasha da munkari" [Nur: 21].
Kuma hanyoyin Shedan dukansu wauta ne da bata, saboda wanda ya fara binsu shine Iblisu wanda yafi dukkan wawaye wauta, Allah Ta'alah ya fada a cikin suratul jin ya fada: "Kuma lallai wawanmu (Iblisu) ya kasance yana fadar abinda ya ketare haddi ga Allah" [Jin: 4]. Maluman tafsiri suka ce, abinda ake nufi da Wawa a cikin wannan ayar, shine Iblisu.
Kuma Allah ya kira, mabiyansa da suna wawaye, ainda ya ce: "Kuma wawaye daga cikin Mutane za su ce: Menene ya juyar da su daga alkiblarsu wadda suka kasance akanta? Ka ce: Allah ne yake da gabas da yamma, yana shiryar da wanda ya so zuwa ga tafarki madaidaci" [Bakara: 142].
Kuma ya sifanta masu yin shirka ga Allah da dabi'ar wauta, wanda ita ce rashin basira, da karancin hankali, Allah Ta'alah: "Kuma babu mai gudu daga akidar annabi Ibrahimu face wanda ya wautar da kansa, kuma hakika mun zabe shi a cikin duniya, kuma lallai shi a lahira hakika yana daga cikin salihai * A lokacin da Ubangijinsa ya ce masa: Ka sallama, ya ce: Na sallama ga Ubangijin talikai" [Bakara: 130-131].
Don haka, hanyoyin wauta suna da yawa, kuma dukkansu suna komawa zuwa ga nau'ukan kafirci da munafurci da manyan zunubai na kaba'ira da sabo.
Kuma daidaikun hanyoyin wauta suna yin daura da daidaikun hikima.
Kuma maganganun Maluman tafsiri sun kasance nau'i-nau'i, wajen bayanin menene hikima, Imamul Bagawiy ya fada a tafsirin fadin Allah Ta'alah: "Wannan yana daga abinda Ubangijinka ya maka wahayi na" [Isra'i: 39].
Ya ce: "Dukkan abinda Allah ya yi umurni da shi (yinsa), ko ya yi hani akansa (barinsa) hikima ne".
Kuma Bagawin ya ce dangane da fadinsa madaukakin sarki: "Sai Allah ya bashi mulki da hikima" [Bakara:]. Ya ce: Shine ilimi da aiki da shi.
Kuma ya ce, a tafsirin: "Yana bayar da hikima ga wanda ya so" [Bakara]. Mujahid ya ce: "Alkur'ani da ilimi da fikihu",
Ibnu-kasir -Allah ya yi masa rahama- a tafsirinsa na fadin Allah: "Kuma muka bashi hikima" [:] ya ce: Katadah ya ce: "Littafin Allah, da bibiyar abinda yake cikinsa". Mujahid kuma ya ce:  Dacewa da daidai.
Don haka, HIKIMA, ma'anoni masu yawa, sune ILIMIN SHARI'A DA AIKI DA SHI, DA YIN DACE DA DAIDAI A CIKIN ZANTUKA, DA YIN HUKUNCI DA NASSOSIN SHARI'A AKAN AYYUKA, DA AMFANAR DA HALITTU DA DUKKAN NAU'UKAN AMFANIN DA AKE DA IKO AKANSA, cikin gaskiya da tsarkin kirji, da tsarkake niyya ga Allah Ta'alah, domin neman ladansa, da guje wa ukubarsa,.
Kuma mafi girman hikima shine abinda Allah ya yi mana wasici da shi a cikin littatafinsa, kamar yadda ya zo a cikin suratul An'aam, a cikin fadinsa: "Ka ce; ku zo in karanta abinda Ubangijinku ya haramta akanku, (wajibi ne) kada ku yi shirkar komai da shi, kuma ga mahaifa biyu ku kyautata musu kyautatawa, kuma kada ku kashe diyanku saboda talauci, mune muke azurta ku da da su, kuma kada ku kusanci abubuwan alfasha, abinda ya bayyana daga gare ta, da abinda ya boyu kuma kada ku kashe rai wanda Allah ya haramta, face da hakki, Wannan ne Allah ya muku wasiyya da shi, tsammaninku za ku hankalta * Kada ku kusanci dukiyar maraya, face ta hanyar da take itace  mafi kyau, har ya kai ga karfinsa, kuma ku cika mudu da sikeli da adalci, ba mu kallafa wa rai face iyawarta, kuma idan za ku fadi magana to ku yi adalci, koda ya kasance ma'abucin zumunci ne, kuma da alwarin Allah ku cika, Wannan ne ya muku wasiyya da shi, tsammaninku za ku wa'aztu * Kuma lallai wannan ne tafrkina madaidaici, sai ku bi shi, kuma kada ku bi wasu hanyoyi sai su rarraba da ku daga barin hanyata, Wannan ne Allah yake muku wasiyya da shi, tsammaninku za ku yi takawa" [An'am: 151-153]. Wannan ayar, da ayoyi biyu bayanta.
Sa'annan sai wasiyyoyin Annabinmu -صلى الله عليه وسلم- kamar fadinsa, alokacin hajjin bankwana: "Ku bauta wa Ubangijinku, kuma ku yi sallolinku biyar, kuma ku rika yin azumin watanku, kuma ku rika biyayya ga ma'abucin lamarinku (shugaba), sai ku shiga Aljannar Ubangijinku", Ahmad ya ruwaito shi daga hadisin Abu-umamah -رضي الله عنه-.
Sa'annan sai wasiyyoyin ma'abuta hikima Muminai.
Kuma yana daga cikin wasiyyoyin da suka fi tattara alkhairi, wasiyyar Mutum salihi, wato Lukman -عليه السلام-wanda Allah Ta'alah ya bashi hikima, sai yake fada akansa: "Kuma a lokacin da Lukman yace wa dansa, alhalin yana masa wa'azi, Ya karamin dana! Kada ka yi shirka ga Allah, lallai shirka zalunci ne mai girma", [Lukman: 13]. Sai ya yi wasiyya ga Mutumin da yafi so, da yin Tauhidi ga Ubangiji Mabuwayi da daukaka, kuma ya hane shi yin shirka ga Allah a cikin nau'ukan ibada. Wannan kuma shine samun rabo a Duniya, da sababin tsira a Lahira, kuma shine matattarar alheri gabadayansa.
Sai ya kwadaitar da shi kan aikata alheri, koda ya kasance kadan ne. Ya kuma tsawatar wa dansa dangane da aikata sharri, koda kuwa daidai da kwayar zarra ne, domin Allah zai halarto da shi, kuma ya yi sakayya akansa.
Sai ya yi wasici ga dansa da ya rika tsayar da sallah, yana mai cika ta, yana kyautata ta.
Kuma ya masa wasiyya da riko da dabi'ar umurni da kyakkyawa da hani kan mummuna, saboda yin hakan lamari ne mai karfi, kuma farilla ne daga Ubangiji Madaukaki. Kuma sai ya masa wasici da yin hakuri akan wannan, saboda Mutane suna cutar da wanda yake kishiyantarsu cikin hana su abinda suke so, kuma saboda ibadar hakuri tana da mafi girman sakamako.
Kuma sai ya masa wasiyya da kyawawan dabi'u da tawali'u, da kuma ya lazimci natsuwa a cikin tafiyarsa da maganarsa.
Kuma lallai mun sani muna masu tabbaci cewa lallai Lukmanu ya yi wasiyya ga dansa kan biyayyar iyaye, saidai Allah Ta'alah da kansa ya jibinci al'amarin wasici da iyaye biyu, saboda girman lamarin biyayya a gare su, sai Allah ya kawata wasiyyoyin Lukman da wasiyyarsa Mabuwayi da daukaka akan biyayya ga iyaye biyu, a bayan wasiyyar Lukman cewa a kula da hakkin Allah.
Wadannan wasiyyoyin sune hikimar da tafi kyau, kuma yin aiki da su yana tabbatar da hikima a cikin rayuwa.
Kuma yana daga cikin asiran wannan surar mai girma, yadda Allah Mabuwayi da daukaka a farkon surar ya sifanta Alkur'ani da cewa shi Mai hikima ne. Kuma Allah ya sifanta kansa a wannan surar da cewar shi: Mabuwayi ne Mai hikima, da kuma "Lallai ne Allah Mabuwayi ne Mai hikima".
Wadannan wasiyyoyi masu hikima daga Lukman, sun dace da abinda ya zo a farkon suratul Isra'i na umurce-umurce da hani. Kuma ita hikima dukkan nau'ukanta suna komawa ne zuwa ga yin aiki daga umurni da hanuwa da hani.
Allah Mai hikima ne cikin zancensa, Mai hikima ne cikin shari'arsa, Mai hikima cikin hukuncinsa da kaddarawarsa, Mai hikima cikin halittarsa. Kuma hikimar sifarsa ce, kuma mulkinsa ne da yake bai wa wanda  yake so.
Kuma Ma'abuta hikima sune Annabawa -عليهم الصلاة والسلام- da kuma mabiyansu, gwargwadon koyinsu da Annabawa, kuma sune ma'abuta kyautatawa wadanda Allah ya musu tanadin sakamakon da ya dace da baiwarsa Mabuwayi da daukaka, a cikin alkawalinsa na gaskiya, kamar fadinsa: "Lallai wadannan da suka yi imani suka yi aiki na kwarai, lallai ne Mu bamu tozarta ladan wanda ya kyautata aiki * Wadannan suna da gidajen aljannar zama, koramu na gudana daga karkashinsu, ana sanya musu kawa a cikinsu daga mundaye na zinariya, kuma suna sanya wasu tufafi kore, na alhariri sirara da alhariri mai kauri, suna kishingide a acikinsu, akan karagogi, Madalla da sakamakonsu, kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutawa" [Kahf: 30-31].
hikima matsayi ne madaukaki, kuma aiki ne yardadde, kuma alheri ne mai dadi. Bawa yana samun hikima da baiwar Allah da karramawarsa da falalarsa, Sa'annan da sabubban da Bawan yake aikata su, yana mai neman taimakon Allah Ta'alah:
YANA DAGA CIKIN SABUBBAN DA AKE SAMUN HIKIMA DA SU, TAUHIDI GA ALLAH TA'ALAH DA KIN YIN SHIRKA MA ALLAH Mabuwayi da daukaka, Allah Ta'alah yana cewa: "Wadanda suka yi imani, sai basu gauraya imaninsu da wani zalunci ba, wadannan lallai suna da aminci, kuma sune shiryayyu" [An'am: 82]. don haka, tsaftar akida haske ne dake karuwa akan hasken fidira, kuma karin fahimta ne akan fahimtar hankali, kuma karfi ne ga gangar jiki da ruhi, wanda Mutum zai rika riskar abubuwa da shi, a bisa hakikanin yadda suke, Allah Ta'alah ya ce: "Wanda Allah bai sanya masa haske ba, to bashi da wani haske" [Nur: 40].
YANA DAGA CIKIN SABUBBAN SAMUN HIKIMA: GODIYAR ALLAH TA'ALAH AKAN NI'IMOMINSA, da zance da kuma aiki, Allah Ta'alah ya ce, dangane da Annabi Sulaiman -عليه السلام-: "Ya Ubangijina, ka cusa mini in gode wa ni'imarka wadda ka ni'imtata a gare ni, da kuma ga mahaifana biyu" [Naml: 19]. Kuma Annabinmu -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Shin ba zan kasance Bawa mai yawan godiya ba!".
YAN DAGA CIKIN SABUBBAN: KIYAYE GABBAI DAGA BARIN SABO, DA KIYAYE ZUCIYA DAGA MUNANAN ABABEN DA SUKE DARSUWA, DA KUMA BAWA YA BAR DUKKAN ABINDA BAI DAME SHI BA, Maluman Tarihi sun ambata, a cikin labarun wadanda suka shude, lallai wani Mutum ya tsaya akan Lukman sai ya ce: Kai mai kiyon dabbobi ne? Ya ce: E, Ya ce: Kai bakin Mutum ne? Ya ce: Lamarin bakin launina a fili yake, to me yake burge ka daga al'amarina? Sai ya ce: Yadda Mutane dayawa suke zama a shumfudarka, suke cika kofar gidanka, suke yarda da maganarka! Sai ya ce: Ya kai dan' dan'uwana, idan ka karkatu zuwa ga abinda zan gaya maka, kai ma za ka kasance kamar haka. Sai Lukman ya ce: "Runtse idanuna, da kame harshena, da tsarkin abincina (halal), da kiyaye farjina, da yadda nake fadin gaskiya, da cika alkawalina, da girmama wanda ya bakunce ni, da kiyaye hakkin makwabcina, da barin dukkan abinda bai dame ni ba, Wadannan sune suka kai ni zuwa ga abinda kake ga ni".
KUMA YANA DAGA CIKIN SABUBBAN SAMUN HIKIMA: FADIN ZUCIYA DA KYAUTARTA, DA SHUMFUDA HANNUWA, DA AMFANAR DA HALITTU, DA KAMEWA DAGA CUTAR DA SU, DA KUBUTAR ZUCIYA DAGA KYASHI DA HASSADA, saboda wadannan sifofin suna da wani sirri na janyo wa Mutum yin dace.
Kuma wadannan sabubban duka sun tattaru cikin, TSORON ALLAH A ASIRCE DA KUMA A BAYYANE, DA DAWWAMAR DA ADDU'A, wanda kuma shine mafificin ayyuka bayan farillai, tare da yawaita zikirin Allah Ta'alah, Allah -سبحانه- ya ce: "Lallai Ubangijinku ya bayar da shela, cewa: Idan kuka yi godiya tabbas zan kara muku, idan kuma kuka kafirce to lallai azabata mai tsanani ce" [Ibrahim: 7].
Allah ya mini albarka ni da ku cikin Alkur'ani mai girma, ,,,.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
            Godiya ta tabbata ga Allah Ma'abucin girma da karramawa, Majibincin kyautatawa da bada ni'imomi, Ma'abucin buwayar da ba a iya cimmata, da mulkin da ba a iya samunsa. Ina yin yabo ga Ubangijina kuma ina gode masa.
            Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake bashi da abokin tarayya Mai mulki da tsarki.
            Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa.
Ya Allah ka yi dadin salati da sallama da albarka ga bawanka kuma Manzonka Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa masu karamci.
Bayan haka
Ku ji tsoron Allah wanda ya halitta ku, kuma yake ciyar da ku da ni'imomi, kuma ku tuna abinda Allah ya muku baiwa na Alkur'ani da hikima (hadisai), da yadda ya sanya su suka zama hasken da kuke tafiya da shi.
saboda Mumini idan ya dawwama akan hisabi ga ransa, to sai hisabinsa ya yi sauki a Lahira. Kuma dawwamar da hisabinsa ga kansa zai shi zuwa ga yau dinsa yafi alheri fiye da jiyansa, Allah ta'alah ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, kuma Rai ta yi dubi kan abinda ta gabatar domin gobe, kuma ku yi takawar Allah, domin Allah Mai bada labari akan abinda kuke aikatawa" [Hashr: 18].
Kuma rigaggeniya mai amfani, mai wanzuwa kuma mai gadar da samun ni'ima tabbatacciya yana nan ne, cikin kokarin samun HIKIMA CIKAKKIYA MAI GAMEWA, Annabi -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Babu hassada sai cikin abu guda biyu; Mutumin da Allah ya bashi hikima, sai yake hukunci da ita, kuma yake karantar da Mutane ita. Da Mutumin da Allah ya bashi dukiya, sai ya dora shi akan hallaka ta, a al'amuran gaskiya" Bukhariy da Muslim, daga hadisin Abu-hurairah -رضي الله عنه-.
An ruwaito da Suwaid dan Alharis Al'azdiy, ya ce: Na zo wurin Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- daya daga cikin bakwai, yayin da muka shiga wurinsa muka yi magana da shi, sai abinda ya gani na natsuwarmu  da tufafinmu ya burge shi, sai ya ce, Ku su wanene? Sai muka ce: Muminai. Sai Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya yi murmushi, sa'annan ya ce: "Lallai kowane zance yana da hakika, to menene hakikanin zancenku da imaninku?" Sai muka ce: Halaye ne guda goma sha biyar (15); Biyar daga cikinsu Manzanninka suka umurce mu da mu yi imani da su, Biyar kuma suka umurce mu muyi aiki da su, Biyar kuma mun dabi'antu da su tun a jahiliyya, don haka muna kan wadannan dabi'un, saidai idan ka kiye mana wani abu daga cikinsu! Sai Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Menene biyar din da 'yan aikana suka umurce ku da ku yi imani da su?" Sai muka ce: Sun umurce mu da muyi imani da Allah, da Mala'ikunsa, da littatafansa, da Manzanninsa, da tayarwa bayan mutuwa, Sai ya ce: "Menene biyar din da suka umurce ku da ku yi aiki da su?" Sai muka ce: Sun umurce mu da mu tsayar da sallah, mu bada zakkah, mu yi azumin watan Ramadhana, mu yi hajjin dakin Allah, ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi, Sai ya ce: "To, Menene biyar din da kuka dabi'antu da su tun a Jahiliyya?" Sai suka ce: Godiya a yayin wadaci, da hakuri a lokacin bala'i, da yarda da kaddara mai daci, da gaskiya a lokacin gwabzawa, da barin dariyar keta ga makiya, Sai Manzon Allah -صلى الله عليه وسل- ya ce:  "Masu hikima, Maluma, sun yi kusa saboda zurfin fahimtarsu su kasance Annabawa" Sa'annan yace: "Ni kuma zan kara muku abubuwa biyar sai su zama ashirin: Idan kun kasance kamar yadda kuke fadi, to, kada ku tara abinda ba za ku cinye ba, kada ku gina abinda ba za ku zauna ba, kuma kada ku yi tsere akan abinda ku a gobe za ku barshi, kuma ku ji tsoron Allah wanda zuwa gare shi za a mayar da ku, kuma za a bijiro da ku a gare shi, kuma ku yi kwadayin ga abinda zaku tafi gare shi, kuma a dawwamar da ku a cikins" Sai suka tafi daga wurin Manzon Allah -صلى الله عليه وسلم-, kuma suka kiyaye wasiyyarsa, suka yi aiki da ita.
Ibnu-Asakir ya ruwaito shi, da Abu-Sa'id Annaisaburiy.

Ya ku Bayin Allah!
"Lallai ne Allah da Mala'ikunSa suna yin salati ga wannan Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani ku yi salati a gare shi, da sallamar aminci" [Ahzab: 56].


TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...