2018/10/25

Huduba kan LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAHI حسين آل الشيخ 17 Safar 1440H 26oktoba2018M









HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 17/SAFAR/1440H
daidai da 26/OKTOBA/ 2018M








LIMAMI MAI HUDUBA
SHEHI HUSAINI BN ABDUL'AZIZ AL-ASSHEIKH





TARJAMAR

ABUBAKAR HAMZA ZAKARIYYA

INA MAFITA?
(فأين المخرج؟)
Shehin Malami wato: Husaini bn Abdul'aziz Al-as-sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: INA MAFITA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga Allah Majibincin Masu takawa, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai yake bashi da abokin tarayya, abin bautar halittu gabadaya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu shine mafificin halittu kuma shugaban annabawa da manzanni.
Ya Allah ka yi salati da sallama a gare shi, da albarka, da kuma iyalansa da sahabbansa gaba daya.
Bayan haka
Ya ku Musulmai
Ina muku wasiyya da ni kaina da irin abinda Allah Mabuwayi da dauka ya mana wasiyya da shi, a cikin fadinSa:
"Ya ku wadanda suka yi imani, ku bi Allah da takawa, kuma ku yi imani da ManzonSa, zai baku ninki biyu na rahamarSa, kuma ya sanya muku wani haske da kuke tafiya da shi, kuma ya gafarta muku, Lallai Allah Mai gafara ne Mai rahama" [Hadid: 28].

A irin wannan zamani wanda yake cike da fitintinu musibu kuma suka yawaita,  kuma makiya suka yi karfafar mulki ga al'umar Musulmai, wanda hakan yake haifar da nau'ukan radadi, da tarin kayan bakin ciki mai yawa, To lallai bukata tana tsananta, kan tunatar da Musulmai game da tabbatattun mafita na yakini; daga dukkan kowane bakin ciki, da fadakar da su game da sabuba na hakika wanda za'a kubuta daga dukkan bacin rai da wahalhalu.

Ya ku Musulmai!
Wannan rayuwa mai karewa cike take da musibu da ababen wahala, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai ne,  Mun halitta mutum cikin wahala" [Balad: 4].
Lallai tushe mai girma na fita daga wadannan musibun da suke cikin wannan rayuwar, da kuma kubuta daga damuwowinta yana kasancewa ne cikin tabbatar da tsoro ko takawar Allah a boye da kuma bayyane, da komawa  ga Allah da dawowa zuwa ga kusancinsa dare da wuni , da bada lokaci na gabadaya don girmansa, da kankan-da-kai a gare shi cikin sauki da tsanani,  Allah Ta'alah ya ce: "Kuma wanda  ya bi Allah da takawa, Allah zai sanya masa mafita *.Kuma ya azurta shi daga inda ba ya zato, kuma wanda ya dogara ga Allah to Allah ya isar masa" [Dalak: 2-3]. Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya ce: "Kuma wanda ya bi Allah da takawa,  zai sanya masa sauki cikin lamuransa" [Dalak: 4].

Kuma yana daga cikin nau'i na wannan rusunawar da Kankan-da-kai da mika wuya ga Allah Mabuwayi da daukaka, Abinda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya shiryatar da wasu sahabbai kuma ya musu wasiya da shi; ciki da waje, cikin fadi da aiki, da hali da dabi'a; domin ya shiryar da Abu Musa -Allah ya yarda da shi- da fadinsa a gare shi:  (Ka ce: La haula wala kuwwata illa billahi, domin ita taska ce daga cikin taskokin Aljannah), Bukhari da Muslim suka  rawaito.
Abu-zarrin -Allah ya yarda da shi- ya ce: (Masoyina -tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi- ya min wasiya kan na yawaita fadin: La haula wala kuwwata illah billahi).
Lallai fadin لا حول ولا قوة إلا بالله wasiyya ce madaukakiya kan yin zikiri mai girma, domin kalmominta takaitattu ne, amma ma'anoninta suna da girma.
Zikiri wanda harshe zai furta shi, zuciya kuma ta sakankance da shi; wato ta ji cewa: Babu mai taimako game da tabbatar da maslahohin duniya da lahira face Allah Mabuwayi da daukaka, domin wanda Allah ya taimaka shine wanda aka taimaka, Wanda kuma ya tabar shine tababbe.
Zikiri ne wanda Bawa zai sakankance; cewa bashi da dabara shi ko waninsa na ya fita daga wani hali zuwa wani halin, kuma bashi da wani karfi bisa ga wani sha'ani daga cikin sha'anoninsa, ko tabbatar da wata manufa daga cikin manufofinsa face ta hanyar tsoron ALLah mai karfi Madaukaki Mai girma.
Zikiri ne da Bawa zai bayyana hakikanin talaucinsa da Kankan-da-kai ga UbangijinSa. kuma ya nuna cewa yana cikin larura da matsanacin bukatuwa zuwa ga MahaliccinSa Mabuwayi Mai rinjaye.
Zikiri ne wanda ke fitowa daga harshen Bawan da zuciyarsa take kadaita Makadaici Mai girman sha'ani. Wanda kuma daga wurinsa yake neman nasara da galaba da yayewa da mafita; Allah Mai tsarki da daukaka ya ce: "Allah zai sanya sauki a bayan tsanani" [Dalak: 7].
Zikiri ne wanda da shi ake samun rabauta da nasara da mafita da kubuta, Allah Madaukakin sarki ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani idan kuka hadu da wata kungiyar yaki, to ku tabbata, kuma ku ambaci Allah dayawa, domin tabbas ku samu cin nasara" [Anfal: 45].
Lallai wanna zikiri ne wanda ya dace kowane Musulmi ya rika furta shi da harshen maganarsa da a cikin halinsa, saboda kasancewarsa sirrin tauhidi, wanda yake hukunta rusuna wa Mahalicci, da nuna tarewa gare shi, da kubutar da kai daga jin tana da wata dabara ko karfi, face ta dogara ga Allah Mabuwayi da daukaka.
Ibnul-kayyim -Allah ya yi masa rahama- ya ce; ((Wannan kalmar tana da tasiri na ban mamaki, wurin tafiyar da abubuwa masu tsanani, da dauke wahala da shiga ga wadanda ake tsoro, da dauke manyan wahalhalu).

Ya ku bayin Allah:
ku saurara ga wannan kissa mai girma wanda hujja ce mai haske wanda take nuna cewa lallai karfin tauhidin bawa yakan warware bakin ciki, duk yadda ya kai ga girmama, kuma matsaloli suna warwarewa duk yadda suka kai ga tsananta.
Wato, kissa ce wanda dayawa daga cikin Malaman tafsiri suka ambace ta, kuma ta zo ta fiskoki daban–daban, wanda kuma mafi karancin darajarta a ilimin hadisi ta zama hadisi hasan, Ita ce, lallai Auf dan Malik Al-ashja'i yana da da wanda ake kiransa Salim, kuma lallai mushirikai sun kama shi cikin fursunonin yaki, sai ya zo wurin Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce da shi: Ya Manzon Allah: lallai abokan gaba sun kama dana (cikin kamammun yaki), sannan ya koka masa talauci, sai Manzon Allah -tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi- ya ce: "Ba abinda ya wuni a wurin iyalan Muhammadu sai mudu daya; Sai ka ji tsoron Allah ka yi hakuri, amma ka yawaita fadin: La haula wala kuwwata illa billahi), A wata ruwaya kuma  ya zo cewa Annabi ya umarce shi, sannan ya umarci uwar 'dan, da su rika fadin hakan, Sai mutumin ya akaita hakan, ana cikin haka, yayin da yake cikin gidansa, sai ga dansa ya zo masa, alhali makiyan sun gafala daga gare shi, sai gashi ya samo rakuma; kuma ya zo da su ga Babansa, dama baban matalauci ne, Sai baban ya je wurin Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ba shi labarin Auf da labarin rakuman, sai Manzon Allah ya ce da shi: "ka aikata abinda ka so da rakuman, ka yi abinda kaga dama da wadannan rakumar). Sai ayar ta sauka wato Fadin Allah: (("Kuma wanda  ya bi Allah da takawa, Allah zai sanya masa mafita *.Kuma ya azurta shi daga inda ba ya zato, kuma wanda ya dogara ga Allah to Allah ya isar masa" [Dalak: 2-3]
To, Daga nan ne Sahabbai suka tafi akan wannan wasiyyar, cikin fadinsu da aiki.
Ibnu-Abiddunyah ya ruwaito cewa lallai Abu-Ubaidah makiya sun katange shi (bashi da mafita) sai  Umar ya rubuta takarda zuwa gare shi: duk abinda ya sauka ga  Mutum na tsanani, to Allah zai kawo yayewa bayan haka,  kuma lallai tsanani daya ba zai ci galaba akan sauki biyu ba, kuma Allah yana cewa: (ku yi hakuri kuma ku yi dauriya  kuma ku yi zaman  dako, kuma ku yi takawa , domin ku kai ga cin nasara) [Ali-imrana: 200].
Lallai wannan ratayuwa ne ga Allah  da dogaro a gare shi, da ambaton Allah a harshe,  wanda yake yake tafiyar da bakin ciki, duk yadda ya kai ga tsananta, sai makomansa ya zama yayewa da samun mafita.
Fudail ya ce: Wallahi da Mutum zai debe tsammani daga halittu ka ji ba ka bukatar komai daga gare su, to da Majibincin ya baka dukkan abinda kake so.

Ya ku taron Musulmai
Lallai yana daga SABBUBAN KWARANYE BAKIN CIKI, da gusar da bacin-rai, lallai dan Adam a duk lokacin da  yayewar ta yi jinkiri har ya fara yanke tsammani daga gare shi bayan kuma ya yawaita rokon samun hakan, da kuma Kankan-da-kai, amma sai bai ga wani alama na amsa addu'ar ba a tare da shi, to wajibi ne ya koma ya rika zargin kansa, ya sake wani sabon tuba, ta gaskiya, ya dukufa zuwa ga Allah yana mai tsarkake niyya, yana mai rusunawa ga Majibinci, tare da yin ikirarin cewa, lallai shi ya cancanci bala'i ya sauka a gare shi,  kuma baya cikin wadanda suke ahalin amsar adu'arsu, ko a kwaranye bakin cikinsu, saidai yana fatan samun rahamar UbangijinSa   kuma yana neman afuwarSa,  to a nan ne lamarin amsar adu'arsa zata zo, da yayewar bakin cikinsa; saboda Allah Ta'alah yana tare da wadanda zukatansu suka  rusuna zuwa gare shi, domin shi. kamar yadda Malaman  magabata suka tabbatar.

Ya ku Musulmai!
Ku kiyaye irin wannan zikiri mai girma (na LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAHI) a kowani lokaci da yanayi, domin alherorinsa nau'uka ne daban daban, falalolinsa kuma suna dayawa, Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ba wani Mutum a doron kasa da zai ce: LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR, WA SUBHANAL LAHI, WA LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAHI, face an kankare masa kusakuransa, ko da sun fi kumfan teku yawa", Ahmad ya rawaito, Tirmizi ya ce Hasan ne, Hakim kuma ya inganta shi kuma Zahabi ya mar muwafaka.
An karbo daga Ubadah dan As-samit -Allah ya yarda da da shi- ya ce: "Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce : "Wanda ya tashi cikin dare sai yace : LA ILAHA ILLALAHU WAHDAHU LA SHARKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR, ALHAMDU LILLAHI, WA SUBHANAL LAHI, WA LA ILAHA ILLAL LAHU, WALLAHU AKBAR, WALA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAHI, sai yace: Ya Allah ka gafarta mini, ko ya yi adu'a za'a amsa masa,  kuma in ya yi alwala ya yi sallah za a karbi sallarsa", BuKhari ya rawaito shi.
Lallai adu'a ne na alheri ga Bawa, kuma kariya ne garkuwa ga maslahohinsa, saboda Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya ce- idan ya zo fita daga gidansa- Bismillah, TAWAKKALTU ALAL LAHI, LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAHI, wato: Na dogara ga Allah, babu dabara ko karfi sai gare shi, za a ce da shi: An isar maka, an baka kariya, kuma Shaidan zai yi nesa da shi). Abu Dauda da Tirmizi ne suka rawaito.
Saboda wannan zikiri ne da yake hukunta mika wuya ga Allah da mai da lamura zuwa gare shi, da yarda da rusuna wa gare shi, tsarki ya tabbata a gare shi, kuma yake nuna cewa babu mai iya tunkude lamarinSa, da kuma cewa, lallai Bawa bai mallaki komai daga cikin lamura ba, domin ragamar al'amuran suna hannun Allah ne Madaukaki, al'amuran bayi dukansu suna kulle ne da hukuncinSa da kaddararSa, babu mai tunkude al'amarin Allah, ko bin kadun hukuncinSa.
Sai kasance ya kai Musulmi,  mai natsuwar zuciya, mai kwanciyan hankali, mai sakankancewa da zuwan yayewan bakin ciki da samun mafita, domin dukkan abinda ke cikin Duniya yana karkashin iko ne na Allah.
Dukkan abinda suke cikin wannan Duniyar ko yaya karfinsu ya kai, ko suka kai ga tsanani, to hakika suna karkashin karfin Allah ne da umarninSa, da hukuncinSa da kaddararSa, saboda dukkan wani mai karfi mai rauni ne a wurin Allah Jalla wa alah.
Don haka, Ya kai Bawan Allah! ka shagaltar da kanka da aikata nau'ukan ayyukan da'a da duk nau'uka na alheri, kuma ka lazimci ambaton Allah da nau'ukan zikiri daban-daban, a yanayi na sauki da cuta, da kuma tsanani da yalwa. Saboda ya zo cikin abinda ya inganta daga Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم-: "Duk wanda yake son Allah ya amsa masa adu'a yayin tsanani da bakin ciki, to ya yawaita adu'a lokacin yalwa".
Ka kuma rika aikata aiki na alheri mai yawa, da falala mai girma, saboda Duniya ba za ta yi dadi ba sai da ambaton Allah, kamar yadda Lahira kuma ba za ta yi dadi ba sai da afuwarSa, Aljanna kuma ba za ta yi dadi ba sai da ganinSa.
Ka kasance mai yawan ambaton la haula wala kuwwata illa billahi domin tana taimakawa wajen dauke abubuwa masu nauyi, kuma tana  tunkude abubuwa na ban tsoro da tsanani, da ita ake samun daukaka a dukkan  yanayi. 
Allah ne wanda ake neman taimako a gare shi, kuma a gare shi ake dogaro, babu dabara ko karfi sai ga Allah Mai girma .

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUDUBA TA BIYU
Godiya ta tabbata ga Allah.
Kuma tsarki ya tabbata ga Allah.
Kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.
Kuma Allah shine mafi girma.
Kuma babu dabara babu karfi, face mun koma ga Allah.
Ya Allah ka yi salati, da sallama, da albarka ga annabinmu kuma manzonmu annabi Muhammadu, da kuma iyalansa da sahabbansa gabadaya.

Ya ku Musulmai
Mumini mai kadaita  Allah,  mai kiyaye dokokin Allah, mai lazimtar biyayyarSa da kuma biyayyar ManzonSa –صلى الله عليه وسلم- Allah yana tare da irin wannan bawan da kiyayewanSa na musamman, Allah Madaukakin sarki yana cewa: "Allah yana tare da wadanda suka yi takawa  da kuma wadanda suke su masu kyautatawa ne", [Nahli: 128].
Wanda kuma Allah ya kasance yana tare da shi to lallai yana tare da bangaren da ba a yin galaba akansu, da mai kiyayewa wanda   ba ya yin barci, da mai shiryarwan da ba ya bacewa, kamar yadda Katadah ya fada.
Wannan tarayya ne da Allah, wanda take hukuta bada taimakonSa, da karfafawarSa, da kiyayewa, da agazawa, da fitar bawa daga zaurukan bakin ciki da wahalhalu masu tsanani.
Kuma duk wanda ya kiyaye Allah, kuma ya rika kulawa da bayar da hakkokin Allah, to  zai sami Allah a gaba gare shi  a duk halin da yake ciki. 
Wanda kuma ya tuna Allah a lokacin yalwa to Allah zai kawo masa dauki a lokacin tsanani,  sai ya tseratar da shi daga tsanani, ya kubutar da shi daga musibu.
Wanda ya mu'amalanci Allah  da takawa da biyayya, cikin neman yardarSa, sai Allah ya masa mu'amala da tausasawa  da kuma taimako  a yayin fadawarsa cikin  tsanani; domin  ya zo a Hadisil kudusi: "Bawana ba zai gushe ba  yana kusanta ta da nafilfilu har na so shi,  idan na so shi sai  na kasance  jinsa da yake ji da shi,  da kuma ganinsa wada yake gani da shi, da hanunsa wanda yake damka da shi,  da kafarsa wanda yake tafiya da ita,  kuma  idan ya roke ni zan ba shi, kuma idan ya nemi tsarina tabbas zantsare shi Buhari ne ya rawaito.

Sannan ku sani mafi tsarkin abin da rayuwarmu za ta mike  da shi shagaltuwa da salati da aminci ga Annabi mai girma,  ya Allah  ka yi dadin tsira da aminci da albarka ga bawanka  kuma manzon ka Annabinmu Muhammad ,  ya Allah ka yarda da Al-kulafa'ur rashidun
Abubakar daUmar da Usman da Aliyu ya Allah ka  gyara halayenmu da halayen musulmai, ya Allah ka yaye bakin ciki  ka gusar da bacin rai , ya Allah ka tsiratar da bayin ka musulmai daga dukkan wata jarabawa da fitina , ya Allah ka yi maganin makiya musulmai domin su ba za su gagare ka ba   ya mai girma , ya Allah   ka kiyaye 'yan uwan mu musulmai a ko ina ya Allah ka kasan ce mai taimakon su da ba su nasara  ya  mabuwayi ya mai karfi,  ya Allah ka datar da kadimul haramaini  ash-sharifaini  cikin abin da ka ke so kuma ka yarda da shi ya Allah ka taimaki addini da shi ka daukaka kalmar musulmai da shi,  ya Allah ka gafartawa musulmai maza da musulmai mata rayayyu daga cikin su da matattu ya Allah ka bamu kyakkyawa anan duniya da kyakkyawa a lahira  kuma ka kare mu daga azabar wuta .  

,,,          ,,,          ,,,



2018/10/12

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI 3 SAFAR 1440H Dr Huzaifiy daidai 12 Oktoba2018












HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 3/SAFAR/1440H
daidai da 12/OKTOBA/ 2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
SHEIKH ALIYU BN ABDURRAHMAN ALHUZAIFIY





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
AURE DA SHIKA A ISLAM
Shehin Malami wato: Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: AURE DA SHIKA A MUSULUNCI, Wanda kuma a cikinta ya tattauna abubuwa da dama ya ce:

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Yabo ya tabbata ga AllahN da Ya halitta jinsin maza da mata, daga abinda kasa ke tsirarwa, da kuma cikin Mutane, har da abinda mutane ba su sani ba. Kuma Allah Mabuwayi da daukaka ya yi umarni kan yin gyara da kawo gyara, ya kuma yi hani kan barna, a cikin fadinsa; "Kuma ka kawo gyara, kada ka bi hanyar mabarnata" [A'araf: 142].
Sannan Allah (تبارك وتعالى) ya shar'anta shari'oi, domin maslahar bayi da amfani a gare su, kuma domin tunkude barna da dukkan ababen  da suke cutar da Mutane da Aljanu.
        Ina yabo ga Ubangijina, kuma ina gode masa, ina tuba zuwa gare shi, ina neman gafararSa,
Ina kuma shaidawa babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Mawadacin da bashi da bukatar talikai.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne manzonSa, Mai gaskiya, Amintacce,
Ya Allah! ka yi salati, da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka; Muhammadu, da iyalansa da sahabbansa gabadaya.

Bayan haka:
Ku bi Allah da takawa, a asirce da kuma a bayyane, saboda babu mai samun rabo a cikin rayuwarsa, da bayan mutuwarsa, sai da takawa, kuma Mutum ba zai tabe ba, ya yi hasara, sai ta hanyar bin son zuciya.

Ya ku Mutane
Ku rika tuna mafarin halittarku; (daga Adamu da Hauwa'u), da yadda mazan cikinku da matanku suka yawaita, alhalin kun samu ne daga rai guda daya; Wanda Allah ya halitta masa matarsa daga jikinsa, Allah (سبحانه) ya ce: "Ya ku Mutane, ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halitta ku daga rai guda daya, kuma ya halitta matarsa daga gare shi, kuma daga gare su, ya watsa maza dayawa, da mata" [Nisa'i: 1].
Kuma Allah Ta'alah ya ce: "Shine wanda ya halitta ku daga rai guda, kuma ya halitta masa matarsa daga gare shi, domin ya samu natsuwa da ita" [A'araf: 189].
        Sa'annan sai sunnar Allah da shari'arsa suka gudana, akan kulluwar namiji da mace ta hanyar daurin aure, irin na shari'a, domin Mutane su iya gina gidan auratayya, kuma domin amsawa ga bukata irin ta halitta; ta irin sha'awar da take tsakanin Mutane, da bin hanyar aure; ba ta hanyar zina ba, domin hanyar aure itace, ke haifar da kamewa, da albarka, da bunkasa, da tsarkaka, da arziki, da lafiyar zukata, da samun doriyar shekaru; ta hanyar zurriyar Mutum nagari; wato salihai.
Ita kuma hanyar zina tana da dauda, ga janyo cutukan zuciya, da lalacewar namiji da mace, ga kuma irin kaskancin da sabo ke janyowa, da matsalolin rayuwa, da tafiyar da albarkar rayuwa, da samun matsaloli cikin 'ya'ya da jikoki, sannan sai azabar lahira, An ruwaito daga Abu-hurairah (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) cikin abinda ya gani na abubuwan al'ajabi, a daren da aka yi isra'i da mi'iraji da shi, Ya ce: "Sa'annan sai ya je ga wasu Mutane, wadanda ake farfasa kayukansu da dutse, duk lokacin da aka fasa, sai kan ya koma kamar yadda ya ke daga farko, kuma baza a dena aikata musu hakan ba. Sai ya ce: Su wanene wadannan Ya Jibrilu? Sai ya ce: Wadannan sune kayukansu suke yin nauyi akan halartar sallolin farillai.
Sa'annan sai ya je ga wasu Mutane, wadanda aka sanya takardu ko fata ta gabansu, da kuma ta duburarsu, suna kai-komo, kamar yadda rakumi ko dabbobi ke kai-komo, kuma suna cin kayar rakuma (dari'in), da kuma itaciyar danyan wuta (wato, zakkumin), da tsakuwa ko duwatsun da aka dafa su da wuta. Sai ya ce: Su wanene wadannan Ya Jibrilu? Sai ya ce: Wadannan sune wadanda ba su bayar da sadakar dukiyarsu (zakkah), kuma Allah bai zalunce su da komai ba.
Sa'annan sai ya je ga Mutanen da a gaba gare su akwai dafaffen naman da yake cikin tukunya, da kuma wani naman danye a cikin wata tukunyar mai dauda, amma sai gashi suna cin wannan danyen mai dauda, suna barin nunannen mai tsafta, Sai ya ce: Su wanene wadannan Ya Jibrilu? Sai ya ce: Wannan Mutum ne daga cikin al'ummarka, zai kasance yana da mace ta halal, mai tsafta, sai ya je wurin wata mace mai dauda, sai ya kwana a wurinta, har safiya. Da kuma matar da za ta tashi daga wurin mijinta na halal mai tsafta, sai ta je wurin wani namiji mai dauda; ta kwana da shi, har safiya". Ibnu-Jarir ya ruwaito shi a cikin tafsirinsa.

Gidan aure mafaka ce da take bada kulawa ga zurriya, kuma take tausaya musu, take damuwa da su, take ilmantar da su.
Kuma uwa da uba sune suke shirya al'umma ('ya'ya da jikoki) domin su iya daukar nauyin da ke cikin rayuwa, da amfanar da daukacin al'umma, da bunkasa yara cikin kowane sha'ani, kuma sune suke fadakar da su zuwa ga riko da kowace dabi'a mai kyau, su kuma yi hani kan aiki da kowace dabi'a abar aibantawa, kuma su rika bada tarbiyya akan aikin kwarai, domin neman dacewa da gidan lahira, da kuma rayuwa ta har abada, kuma sai karamin yaro ya yi ta koyi da irin abinda yake gani a gida, sai kuma ya tasirantu da abinda ya ke gani, kuma ya ke ji, tun da bashi da ikon karanta tarihi, domin daukar izina daga cikinsa, da aiki da abin koyi.

Shi kuma daura aure ko kulla shi, alkawari ne mai girma, kuma igiya ce mai karfi, kuma zumuncin sadarwa mai tsananin muhimmanci, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma idan kun yi nufin musanya mace, a gurbin wata macen, kuma kun baiwa dayansu tarin dukiya (na kindari), to kada ku karbi wani abu daga cikinsa, Shin za ku karbe shi da karya da zunubi bayyananne? * Kuma yaya za ku karbe shi, alhalin, sashenku ya sadu da sashe, kuma mata sun riki alkawari mai kauri daga gare ku" [Nisa'i:20-21].
Maluman tafsiri sun fassara alkawari mai kauri da cewa, shine: Daurin aure.

Daura aure, yana kunsar maslahohi da amfani ga miji da mata, da wasu amfani da maslahohin na 'ya'ya, da maslahohi da amfani ga makusantan ma'auratan biyu, da kuma wasu amfani da maslahohin ga daukacin al'umma, da  wasu maslahohin na duniya da lahira, wadanda ba za a iya kididdige wadannan amfanonin ba.

Shi kuma warware wannan alkawarin, da lalata wannan kullin, da tsinke igiyar auratayya, ta hanyar SHIKA, yana rurrushe wadancan maslahohin da amfanonin gabadayansu. Sai miji ya auka cikin fitintinun da za su cutar da shi ga addininsa da duniyarsa da lafiyarsa.
Kuma itama Mace, idan aka sake ta, sai ta auka cikin fitintinun da suka fi tsanani akan wanda mijin ke aukawa cikinsu, kuma matar da aka sake ba za ta samu ikon mayar da rayuwarta kamar yadda ta kasance ba, kuma sai ta rayu cikin nadama, musamman a wannan zamanin wanda a cikinsa mazajen da za su iya dacewa da halinta suka yi karanci, sai 'ya'yansu su watse, su kuma fiskanci rayuwa mai matukar tsanani, wacce ta banbanta da wanda suka yi alhalin suna karkashin inuwa ko kulawar iyaye guda biyu (uwa da uba) a hade, sai kuma su rasa dukkan dadin da zai sanya rayuwarsu cikin walwala, sai su fiskanci lalacewar halayya da nau'ukansa mabanbanta, da kuma cutuka iri-iri, sai itama al'umma gabadayanta, ta cutu, da matsaloli masu cutarwa, wanda suke kasancewa bayan aukuwar shika, sai ka ga, yanke zumunta ya yawaita.
Kuma duk yadda aka kai makura wajen kididdige matsalolin da suke cikin shikar aure, to lamarin ya fi haka.
Kuma, domin ka san barnar da shika take haifarwa, da yawaitar matsalolinta, kebantattu da masu gamewa, sai ka yi tunani cikin hadisin Jabir (رضي الله عنه)  daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), lallai ya ce: "Lallai Iblisu ya kan dora al'arshinsa ko gadon mulki akan ruwa (teku), sa'annan ya tura 'yan farautarsa, kuma wanda zai fi su kusancin matsayi da Iblisu shine wanda yafi tsananin fitina; Sai daya daga cikinsu ya zo, ya ce: Na aikata kaza, da kaza, Sai ya ce: Ba ka aikata komai ba. Sa'annan sai daya daga cikinsu ya zo ya ce; Ban bar wane ba, har sai da na raba tsakaninsa da tsakanin matarsa; Sai Iblisu ya kusantar da shi, yana cewa: Na'am, Kai ne gogan, Sa'annan kuma ya rungume shi", Muslim ya ruwaito.

Kuma lallai wasu mutane, sun yi sako-sako da batun shika, sai suka dauki lamarinsa da sauki, sai suka auka cikin lamura masu hatsari, da sharrace-sharrace masu tarin yawa, sannan su kan aukar da wasunsu cikin abinda suka auka a cikinsu.
Hakika shika saboda sabuba masu rauni, ya yawaita a wannan zamanin, ko saboda dalilai marasa kan-gado.
Kuma SABBUBAN SHIKA A WANNAN ZAMANIN suna da yawa;
Yana daga MAFI GIRMANSU: JAHILTAR HUKUNCE-HUKUNCEN SHIKAN, a cikin shari'a, da rashin aiki da Kur'ani da sunnah. Saboda shari'ar Musulunci ta kewaye kullin aure, da dukkan abinda zai bashi kariya da kulawa, kuma ta kare aure da muhimmiyar katanga, domin bashi kariya; kuma domin kada ya tsattsage, ya rushe, ya girgiza; a lokacin kadawar guguwar son zuciya.
Kuma domin kasancewar sababin shika yana iya kasancewa daga miji, ko daga matar, ko daga miji da matar, ko daga wasu daga cikin makusantansu; Sai shari'a ta magance kowane irin yanayin da ka iya zama sababin shika;
Sai Allah a cikin littafinsa ya umarci miji, da ya girmama lamarin aure, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma kada ku rike mata da cutarwa; har ku kekare iyaka, kuma duk wanda ya aikata hakan, to ya zalunci kansa, kuma kada ku riki ayoyin Allah da izgili" [Bakara: 231].
Kuma Allah ya ce: "Kuma su Mata, suna da kwatankwacin abinda ke kansu (na hakkoki) da kyautatawa, Kuma su Maza suna da wata daraja akan mata" [Bakara: 228].
        Maluman tafsiri suka ce:
Mace akan Mijinta, tana da hakkoki, misalin hakkokin mijin da suke kan matarsa, wajen kyautata zamantakewa, Sai kuma namiji ya samu fifiko akan mace, ta fiskar kasantuwarsa mai tsayuwa da lamarinta;
Don haka; Wajibi ne, akan namiji yayi zamantakewa da matarsa cikin abinda aka sani da kuma kyautatawa, Idan kuma ya kita, to sai ya dau hakuri, la'alla yanayin ya canzu, izuwa ga wanda yafi kyau, ko la'alla a azurta shi da 'ya'ya salihai tare da ita, sannan a bashi ladan hakurinsa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma ku yi zamantakewa da su da kyautatawa, domin idan kun ki su, to, tana yiwuwa ku ki abu, sai Allah ya sanya alkhairi mai yawa a cikinsa" [Nisa'i: 19].
        Kuma wajibi ne ga miji da matarsa, su rika gyara lamuran da suke janyo sabani, tun suna farko-farkonsu; domin kada kafar sabanin ta fadada.
        Kuma wajibi ne ga miji da mace; kowannensu ya san dan'uwansa; sai kowanne ya rika aikata abinda zai fi yardar da sahibinsa, Ya kuma rika nisantar dukkan abinda dayan baya so, Wannan kuma abu ne mai sauki, da ba a boye ya ke ba.
      
        YANA DAGA CIKIN SABBUBAN WANZUWAR AURE: Kokarin yin sulhu a tsakanin ma'auratan, daga ma'abuta alkhairi, masu sulhuntawa, da kawo gyara, domin kowanne ya iya samun hakkokinsa na wajibi, wanda ke kan sahibinsa, Allah (تعالى) ya ce: "Kuma idan ku ka ji tsoron sabani a tsakaninsu, sai ku tayar da mai hukunci daga cikin iyalansa, da mai hukunci daga iyalanta, idan sun nufi yin sulhu a tsakaninsu, to hakika Allah zai daidaita tsakaninsu, Lallai ne Allah ya kasance Masani Mai bada labari" [Nisa'i: 35].

        KUMA YANA DAGA SABBUBAN DAWWAMAR AURE DA JIN DADINSA: Hakuri da yin rangwame, domin dacin da ke cikin hakuri, dan kadan, zaki ne na tsawon zamani ke biyo bayansa, Kuma ba wani abinda ake fiskantar ababen ki da shi, wanda ya kai hakuri girma, Allah (تعالى) ya ce: "Kawai, masu hakuri ana cika ladansu, ba tare da lissafi ba" [Zumar: 10].
        Rangwame da yin afuwa, suna kawata rayuwa, kuma suna sanya ma rayuwa walwala da farin ciki da kyau. Kuma da shi ake warkar da kurjin da zamantakewa ta haifar. Kuma asali, Yafiya da yin afuwa dole ne a rayuwa, musamman a tsakanin ma'aurata biyu.
Kuma idan ya kasance cikin lamura ne na karin kwalliya (ba wajibi ba), Ko kuma cikin lamuran da za a iya jinkirta su, to lallai yin rangwame a irin wannan, shine mafi alheri ga ma'aurata. Musamman kuma a irin wannan zamanin, wanda kokarin samar da bukatun rayuwa, ya wahalar da yawa-yawan mazaje, tare da cewa, wasu ababen ba na lalura ko dole ba ne.
Kuma lallai neman bada dukkan hakkoki, da rashin rangwantawa, ko yafe wasu hakkokin, yana gadar da guje wa juna da kiyayya a tsakanin ma'aurata. alhalin shi kuma aure ruhinsa shine, taimakakkeniya, da jin-kan juna, Allah (تعالى) ya ce: "Ya ku wadanda suka yi imani lallai ne wasu daga matanku da 'ya'yanku makiya ne a gare ku, sai ku kiyaye su, kuma idan kuka yafe kuma kuka kau da kai, kuma kuka gafarta, to lallai Allah Mai gafara ne Mai jin kai", [Tagabun: 14].
Gaba ko kiyayyar da ake nufi a wannan ayar ita ce, sanyaya guiwar miji ko uba kan aikata alkhairi, ko kuma rashin taimakonsa, ko kuma hana shi aikata aikhairin.
Kuma Allah (تعالى) ya ce: "Ka riki abinda ya saukaka, kuma ka yi umarni da alheri, kuma ka kau da kai daga jahilai" [A'araf: 199].

KUMA YANA DAGA SABBUBAN DAWWAMAR AURE: MIJI ya yi ta kokarin gyara abinda ya karkace na halin matarsa, da abinda shari'a ta halatta, kuma ta yi izini, Allah (تعالى) ya ce: "Su salihan mata masu da'a ne, masu tsarewa ga gaibi saboda abinda Allah ya tsare. Su kuma wadanda ku ke tsoron bijirewarsu, to, ku yi musu gargadi, kuma ku kaurace musu a wuraren kwanciya, kuma ku doke su, Idan kuma suka muku da'a, to kada ku nemi wata hanya akansu" [Nisa'i: 34].

Kuma wajibi ne akan alkalai su rika yin sulhi tsakanin ma'aurata biyu, cikin abinda ake kaiwa gare su na kararraki, har a samu ittifaki, a kawar da shika.

Shi kuma HAKKIN MACE AKAN MIJINTA shi ne ya yi zamantakewa da ita da kyautatawa, ya kuma bata gidan da ya yi daidai da irinta, tare da ciyarwa da tufatarwa, da bayar da alkhairi, da kamewa ga barin cutar da ita.
Kuma lallai SABABIN SHIKA YANA IYA KASANCEWA DAGA MATAR NE, saboda kaushin harshenta, ko munin halinta, da jahilcinta, Don haka, wajibi ne akan mace ta rika gyara halinta, tana mai biyayya ga mijinta, ta yi bakin kokarinta wajen tarbiyyar 'ya'yanta da ingantacciyar tarbiyya, An ruwaito daga Abdurrahman bn Auf (رضي الله عنه) daga Annabi (صلى الله عليه وسلم), ya ce: "Idan Mace ta yi sallolinta biyar, ta yi azuminta na wata, ta kiyaye farjinta, ta yi biyayya ga mijinta, Sai ace mata: Ki shiga Aljannah, daga dukkar kofar da ki ka so", Ahmad ya ruwaito shi, kuma hadisi ne hasan.

Kuma wajibi ne ga mace ta rika hidima ga mijinta, da kyautatawa, tana mai koyi da sahabbai mata –رضي الله عنهن-.
Kuma abu ne mai kyan gaske ta rika yin tarayya da mijinta cikin farin cikinsa da bacin ransa, kuma ta kasance mai taimakonsa wajen biyayya ga Allah Ta'alah.

KUMA YANA DAGA SABBUBAN SAMUWAR SHIKA: Shisshigin wani daga dangin miji ko mata, ko kuma danginsu gaba daya, Sai su ji tsoron Allah, kuma su fadi magata ta daidai. Kuma ya zo cikin hadisi, cewa: "Allah ya la'anci Mutumin da ya bata matar wani a gare shi, ko kuma ya bata mijin ga matarsa".

Kuma wajibi ga MACE TA TSAYU WAJEN BADA HAKKIN MAKUSANTAN MIJINTA, musamman kuma iyayensa biyu.
Kuma shima mijin WAJIBI NE YA TSAYU WAJEN BAYAR DA HAKKIN MAKUSANTAN MATARSA; saboda sakaci kan hakkin makusantan ma'aurata, sau dayawa ya kan zama sababin shikan aure.

KUMA YANA DAGA SABBUBAN SHIKA: Bibiyar fina-finan da su ke rushe dabi'a, ko shafukan yanan gizo-gizo (internet) na haram, wadanda suke yada barna.

KUMA YANA DAGA SABBUBAN SHIKA: Fitan mace daga gida ba tare da samun izinin mijinta ba, kuma baya halatta a gare ta, ta fita ba tare da izininsa ba, domin miji shine ke da ma'aunin auna lamura.

Kuma idan SABBUBAN ZAMAN AURE SUKA GAGARA To lallai Allah ya halatta yin shika, tare dacewa yana kin shikan, saboda ya zo cikin hadisi cewa: "Halal din da Allah ya fi kinsa, shine shika".
Sai miji ya yi shika irin na shari'a, bayan tsanaki da bi-sannu-sannu, kamar yadda Allah ya yi umarni a cikin fadinsa: "Ya kai wannan Annabin idan za ku saki mata, sai ku sake su ga iddarsu, kuma ku kididdige iddar" [Dalak: 1].
Maluman tafsiri suka ce:
Sai ya sake ta a cikin tsarkin da bai sadu da ita a cikinsa ba, shika daya, Idan ya so, sai ya mata kome a cikin wannan iddar. Idan kuma ya so, sai ya barta har ta gama iddarta, sai ta fita daga mulkinsa.
Kuma lallai shika ta irin wannan hanyar tana bude kofar fatan yin kome, don wanzar da auren, ko a sake sabon aure, idan har ta yi tsarki, bayan idda.

Sai ka yi dubi, ga yadda aka karfafa lamarin aure, da yadda shari'ar gaskiya ta kiyaye shi.
Kuma ka yi dubi kan sakacin mutanen wannan zamanin kan lamarin shika, da abinda shikan yake janyowa; na kayan bacin rai.
Allah (تعالى) yana cewa: "Ya ku wadanda suka yi imani, kada ku bi, hanyoyin shedan, domin duk wanda ya bi hanyoyin shedan, to lallai shi yana umarni ne da alfasha, da kuma munkari", [Nur: 21].

Allah ya yi mini albarka NI da KU, cikin alqur'ani mai girma, ya kuma amfanar da NI da KU da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima,      Na faxi abinda ku ka ji, kuma ina neman gafarar Allah mai girma ga Ni da KU da kuma sauran Musulmai daga kowani zunubi, Ku nemi gafararSa,    lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,


HUDUBA TA BIYU
        Yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Mai rahama Mai jin-kai, ya shar'anta hukunce-hukunce da iliminSa da hikimarSa da kuma rahamarSa.
Tsarki ya tabbata a gare shi; abin bauta Mai girma.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya, Masani Mai hikima.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa,
Ya Allah ka kara salati da sallama da albarka ga bawanka kuma manzonka Muhammadu, da iyalanSa, da sahabbanSa, masu riko da shari'arsa mikakkiya.

Bayan haka … !!
Ku ji tsoron Allah, iyakar tsoronsa, kuma ku yi riko a Musulunci da igiya mai karfi.

Ya ku Bayin Allah … !!
Allah yana cewa:  "Kuma ku taimaki juna akan biyayya da takawar Allah, kada ku taimaki juna akan sabo da ketare iyaka, kuma ku ji tsoron Allah, lallai ne Allah Mai tsananin ukuba ne" [Ma'ida: 2].

Ya ku Musulmai,
Shika ya zama wani abinda yake gudana akan harasan wasu samarin ba tare da tsare ko kula da hakkokin 'ya'yansu, ko wani makusancinsu ba, ko kuma lura da wani ba,
Kuma hakan yana aukuwa, ta hanyar maimaita shi, a cikin zamani masu nisa da juna, ko maimaita fadin lafazin shika a majalisa daya, sai kuma Mutum ya tafi yana ta neman fatawowi, ko ya ce, zai yi wayo, wani lokacin hanyoyi su kan toshe masa, sai ya yi ta nadamar da ba za ta masa amfani ba, alhalin Allah kuma yana cewa: "Duk wanda ya ji tsoron Allah, to zai sanya masa mafita * kuma ya azurta shi, ta yadda baya tsammani" [Dalak: 2-3].
Kuma duk wanda ya ji tsoron Allah, cikin lamarin shikansa, ta fiskar da shari'a ta yarda, sai Allah ya sanya masa mafita.
Kuma duk wanda ya dauki aure da girma, bai yi sako-sako da shi ba, sai Allah ya sanya masa albarka a cikin aurensa, kuma ya samu kyakkayawar natija.

Kuma wasu daga cikin na'ukan shika kebantattu, yin shika a cikin wadannan halayen ya kan kasance laifi ne (sabo), kamar yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم)  ya ce wa Abu-Ayyub: "Lallai sake Ummu-Ayyub, laifi ne".

Ya ku bayin Allah!
"Lallai ne, Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Ya ku wadanda suka yi imani, ku yi salati a gare shi, da sallama ta aminci" [Ahzab: 56].
……………………………

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...