2018/08/30

TSARIN KULA DA MOTOCIN JIGILAR MAHAJJATA (النقابة العامة للسيارات)









TSARIN KULA DA MOTOCIN JIGILAR MAHAJJATA
(النقابة العامة للسيارات)













Tarjamar
Abubakar Hamza Zakariyya


Ma'aikatar kula da motocin daukan Mahajjata
MA'AIKATA
Rahoro ga jaridu
SASHEN SADARWA
Tsarin yanar gizo da ke dora bus din jigilar daukar Mahajjata hanya/ Bus dubu sha takwas (18,000) domin jigilar Mahajjata zuwa wuraren bauta tsarkaka (Minah, Arfah, da Muzdalifah)
MAUDU'I
Cikin kasar Saudia da wajenta
YADAWA
06/ Zul-hijjah/1439h
RANA
>Shugaban ofishin kulawa da motocin jigilar Mahajjata.
>Daraktan kula da aikin motocin a wuraren aikinsu.
>Bayanan tsarin aikin motocin, na hajjin shekara ta 1439h
MASU MAGANA
Hada hannu domin gabatar da hidima ga Bakin Allah; Mahajjata
SAKON AIKIN

Map a yanar gizo domin bibiya da nusar da bus na daukar Mahajjata
BUS DUBU SHA TAKWAS (18.000) SUNA JIGILAR MAHAJJATA MILIYAN 1.82 ZUWA WURAREN BAUTA MASU TSARKI (MINAH, ARFAH, DA MUZDALIFA)

Shugaban ofishin kula da motocin jigilar Mahajjata; Wato Abdurrahman bn Ma'ayuf Alharbiy ya bayyana cewa bus 18,415 sune za su yi jigilar bakin Allah Mahajjata zuwa wuraren bauta masu tsarki, domin su yi ayyukan hajjinsu na shekara ta 1439H.
            Kuma ofishin kulawa da motoci yana jiran samun karuwan Mahajjata, idan an kula da yadda hajjin baya ya gabata (1438h), Karin da zai iya kaiwa goma cikin dari (10/100) wato kimani Mahajjata (195,965). Kuma shugaban ya ce:
"Lallai kamfanoni masu yin jigilar Mahajjata, wadanda suke yin aiki karkashin inuwar kulawar hukumar kula da motoci, suna burin kawo motocin jigila wadanda suka dace da bakin Allah; Mahajjata, domin jidon su, daga kafafen shigowa kasar Saudia, zuwa inda suka nufa a garin Makkah, ko Madinatul munawwarah, ko tafiya cikin wuraren bauta masu tsarki –Minah, Arfah, Muzdalifa-, domin su yi ibadodinsu".
            Kamar yadda hukumar ta yi doka ga kamfanonin jigilar Mahajjata (wato kamfani 35) cewa lallai shekarun sana'anta motocin jigilar Mahajjata, kada ya fice daga tsakanin 2013 zuwa 2018 (shekaru biyar da suka shude), wannan kuma domin bayin Allah; Mahajjata, su samu cikakken hutu da moriya.

            --------- Tallafin ministirin hajji
Kuma shugaban hukumar kulawa da motocin ya yi nuni cewa, lallai tallafi ne mai girma hukumomin da suke tarayya cikin aikin hidimar Mahajjata daga wannan kasar (ta Saudia), da samun bibiya da umurni daga Mai girma ministan hajji da umrah; wato Dr. Muhammadu Salih bn Dahir Bintin, da Mai girma Na'ibinsa; Dr. Abdulfattah bn Sulaiman Mushad. Yana mai kirga hakan a matsayin sababi mai girma kuma karfafa guiwa domin dorewa wajen bunkasa aiki, da kara kyautata kayan aikin tsare-tsare da na gudanarwa. Da kokarin ficewa daga tsarin da aka masa taken: Khidmar Mahajjaci (خدمة الحاج) zuwa ga tsari mai taken: Shirya garar bako (صناعة الضيافة) tare da gina sarkar hidima Mahajjata mai tasiri, daga hidimomi da tattali domin hajji da umrah, wanda za su ka ga cimma tsarin kawo canji ga kasar mai taken 2020, da manufar bunkasa ta da aka masa lakabi da 2030.
Shugaba Abdurrahman Ma'ayuf Alharbiy ya karfafa cewa lallai hukumar kulawa da motocin jigilar Mahajjata ta tsayu wajen yin jerin ayyuka kuma cikakku, wadanda aka hada karfi domin hidimar Mahajjata, da kauracewa barci domin samun hutunsu, da yin hidimomi a gare su, tun lokacin shigowansu wannan kasa (Saudia), ta dukkan hanyoyin shiganta, domin sauke ayyukansu na hajji, har zuwa lokacin ficewarsu daga kasar ta Saudia.

Tsarin aikin kula da motocin jigilar mahajjata na shekarar 1439h ya yi nunin cewa, lallai jimillar kujerun bus din jigilar hajji, wadanda suke aiki akan tsarin jigilar kai-komo (النقل الترددي) sun kai kujeru 849,019, wanda hakan ke nuna cewa, matsakaicin abinda kowace bus take da sun a wuraren zama shine gurbi 47.

---------- Map na intanet
A karon farko, ofishin kula da motocin jigilar Mahajjata, sun sake wani tsari mai suna "daif" a intanet, domin tsattsara hidimomin jigilar jeka-ka-dawo, a wuraren ibada masu tsarki (Minah, Arfah, Muzdalifah), domin bude hidimar jigilar, ko cike bayanan neman jigilar, da tsara ayyukan gudanar da jigilar motocin, da bin inda suke; ta hanyar map da yake cikin intanet, wanda hakan zai bada damar bin-diddigin fiye da bus dubu goma sha takwas (18), a lokaci guda.

Gwargwadon abinda ya zo cikin maganar Daraktan kula da aikin motoci a wuraren aikinsu; wato injiniya Ahmad Kariy, to lallai wannan matakin ya zo cikin matakan yin amfani da dukkan damammaki, domin hidima ga bakin Allah; Mahajjata, ta hanyar bibiyar yadda bus take tafiya a lokacin tafiyarta, wanda hakan zai samar da kulolon aminci kan motocin jigila da sadarwa".
A nan sai Dr. Kariy ya kara bayani cewa: "Shi tsari mai suna daif, zai baiwa hukumar kula da jigilar motoci damar bibiyar motsawan dukkan bus na jigila mallakin kamfanonin da suka yi tarayya wajen hidimar hajjin wannan shekarar, da yadda motocin nasu suke bin layukan da aka tsara musu, kuma za su samu tabbacin lokatan lodin kai-komo wanda yake cikin tsari ko jadawali, ta hanyar linkin da aka tanadar na intanet". 
Kuma ya kara da cewa: "Lallai map na intanet yana bayyanar da layukan motocin bus, akan wata komfuta, a wani daki ko ofishi na musamman na ma'aikatan kula da wadannan motocin. Kuma wannan tsarin yay i fice ta hanyar bayyanar da gurbin da kowace mota ta ke, kuma yana sane da dukkan motsawanta, ta yadda yake bayyanar da lambar motar, da wuraren da duk ta je, gwargwadon layukansu iyakantattu. Kamar yadda yake bayyanar da kwanan watan duk wani motsi, da lokaci, ta hanyar fadin awoyi da mintoci da sekon din dakikoki, tare da bayanin irin saurin da motar ta ke yi (a dukkan wurare).
Amfani da taknoloji na zamani yana zuwa ne cikin kokarin da baya yankewa na ofishin kula wa da motoci, da nufin su samar da mataki mafi girma aminci da jin amintuwa, ga hanyoyin daukar mutane da sadar da su ga bukatunsu. Da kuma kara kyautata irin hidimar da ake gabatarwa gab akin Allah; Mahajjata.

Kuma ofishin kulawa da motocin hidimar Mahajjata suna da manufofi guda bakwai (07) domin dora motocin bus na jigilar akan hanyar da tafi, daga cikinsu:
1-     Amfani da fasahar map da take cikin intanet.
2-     Shigar da fasahar zamani domin bunkasa ayyukan dora motocin bus na jigilar Mahajjata akan turba.
3-     Bada damar yin hidimomi masu tarin yawa, wadanda suke da alaka da bibiyar motocin jigilar, bayan kulla kowace mota da mai nuna mata hanya, kuma an kasa su kashi-kashi.
4-     Baiwa shugannin kowane kamfani damar gudanar da ko bibiyar dukkan dukkan motocin da mallakinsu ne.
5-     Magance matsalar bacewar motocin jigilar, ko jinkirin dawowansu.
6-     Saurin bada sanarwan bacin motocin da ka iya aukuwa, ta hanyar mai nuna wa Direba hanya.
7-     Gano wurin da motar ta caskare, ta hanyan wannan sabon tsari.
8-     Kari akan, tabbatar wa Mahajjata hutunsu.

An mika lamarin tirenin don iya aiki da tsarin "daif" na intanet, ga ofishin samar da tsare-tsare na kula da motocin jidon Mahajjata, ta yadda su kuma suka sanar da wadanda za su amfana, ko su rika amfani da shi da ma'aikatan a mu'assasosin bayar da hemomi da kula da jigila, tare da nuna wannan tsarin ga masu aikin nuna wa direbobi wurare, da wasu daga cikin direbobin motocin bus wadanda suke jigila ta kai-komo.

·        Adadin Mahajjatan da aka yi jigilarsu da motocin bus, a shekarun da suka gabata:
§  Hajjin 1435H: 1,324,000
§  Hajjin 1436H: 1,364,000     
§  Hajjin 1437H: 1,334,000
§  Hajjin 1438H: 1,644,000
§  Hajjin 1439H: 1,820,000

·        Manufofin aikin bibiyarmotocin jigilar Mahajjata ta tsarin kafar intanet
1)     Amfani da fasahar map da take cikin intanet.
2)     Shigar da fasahar zamani domin bunkasa ayyukan dora motocin bus na jigilar Mahajjata akan turba.
3)     Bada damar yin hidimomi masu tarin yawa, wadanda suke da alaka da bibiyar motocin jigilar, bayan kulla kowace mota da mai nuna mata hanya, kuma an kasa su kashi-kashi.
4)     Baiwa shugannin kowane kamfani damar gudanar da ko bibiyar dukkan dukkan motocin da mallakinsu ne.
5)     Magance matsalar bacewar motocin jigilar, ko jinkirin dawowansu.
6)     Saurin bada sanarwan bacin motocin da ka iya aukuwa, ta hanyar mai nuna wa Direba hanya.
7)     Gano wurin da motar ta caskare, ta hanyan wannan sabon tsari.
8)     Kari akan, tabbatar wa Mahajjata hutunsu.

## Labarin ya kare##  


2018/08/08

hudubar 28 zulkaadah 1439H ta Dr. Alkasim daidai 10 ogas 2018 M











HUDUBAR MASALLACIN ANNABI
 (صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 28/ZUL-KA'ADAH/1439H
Daidai da 10 /OGOSDOS / 2018M




LIMAMI MAI HUDUBA
DR. ABDULMUHSIN DAN MUHAMMADU DAN ABDURRAHMAN ALKASIM





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
HAJJ
تزكية النفوس وإصلاحها
Shehin Malami wato: Abdulmuhsin bn Muhammadu bn Abdurrahman Alkasim –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: AIKIN HAJJ, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan abinda ke tafe, Ya ce:

بسم الله الرحمن الرحيم
HUDUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan ayyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu mai batar da shi, Wanda kuma ya batar, babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su kara tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.

        Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da takawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku kiyaye shi, a asirce, da kuma a bayyane (a lokacin ganawa).

        Ya ku musulmai …
LOKATAN ALKHAIRAI SUNA SABUNTUWA GA BAYI, falala daga Allah da karamci, saboda wata ibada bata shudewa face lokacin yin wata yam aye gurbinta, to yanzu ga Mahajjatan farko-farko sun nufi dakin Allah mai tarihi, suna masu amsa kiran da badin Allah annabi Ibrahim –عليه السلام- ya yi: "Kuma ka yi shelar aikin hajji ga Mutane, za su zo maka da kafa, da kuma akan dawakai, za su zo daga dukkan lungu mai nisa", [].

Nufato dakin Allah da hajji farilla ne, kuma ibada, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ya ku Mutane! lallai ne Allah ya farlanta hajji akanku; sai ku yi hajji", Muslim ya ruwaito shi.
Hajji ibada ce mai girma a Musulunci, domin shine rukuninsa na biyar, kuma yana cikin manyan da'oi, wadanda Allah yafi sonsu, saboda an tambayi Annabi –صلى الله عليه وسلم- cewa: "Wane aiki ne a cikin ayyuka yafi falala? Sai ya ce: Imani da Allah, sai ya ce: sa'annan sai me? Ya ce: sai jihadi fiy sabil Lahi, sai ya ce: sa'annan sai me? Ya ce: sai hajji lafiyayye", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.

Kuma da aikata hajji ake shafe zunubai da kura-kurai, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Kuma hajji yana rushe abinda ya kasance gabaninsa", Muslim ya ruwaito shi.
Don haka, hajji tsarkaka ne ga ma'abutansa kuma dauraya, saboda Annabi –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Wanda yay i hajji bai yi kwarkwasa ba, bai yi fasikci ba, zai koma kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi", Bukhariy da Muslim.

Mahajjata ne kawai Allah ke alfahari da su ga ma'abutan sammanSa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Babu wani yinin da Allah yafi 'yanta bayi a cikinsa daga wuta fiye da ranar Arfah, saboda Allah yak an kusanto, sai ya yi alfahari da su ga Mala'ikunSa, ya ce: Me wadannan suke nema?", Muslim ya ruwaito shi.

Kuma babu wani sakamako ga wanda ya tsarkake niyya cikin hajjinsa face Aljannah, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Umrah zuwa umrah suna kankare abinda ya auku tsakaninsu, shi kuma hajji lafiyayye bashi da wani sakamako face Aljanna", Bukhariy da Muslim.

Hajji shine taron Musulunci mafi girma, wanda ke kulla tsakanin Musulman yau da wadanda suka shude, domin bayi su rayu a matsayin al'umma daya, suna masu riko da addininsu. Kuma babu hanyar tabbatuwan hakan sai sun yi riko da littafin Allah da sunnah, sun kuma tafi akan turbar magabatan al'umma na kwarai.
Kuma a cikin hajji fifikon jinsi da harshe da launi suke tafiya kuma su bace. Sai ma'aunin fifiko dake wanzuwa ya kasance shine takawa, Allah Ta'alah ya ce: "Lallai wanda yafi matsayi a cikinku shine wanda yafi ku takawa", [Hujurat: ].

Kuma mafi alherin guzurin da mahajjata ke tafiya da shi a cikin aikinsu shine takawa, Allah -سبحانه- ya ce: "Kuma ku yi guzuri, kuma lallai mafi alherin guzuri shine tsoron Allah, kuma ku yi takawata ya Ma'abuta hankali", [Bakara: ].

Kuma duk wanda ya nufi dakin Allah, to ya dace da shi ya lazimci tsantsenin da zai kange shi daga aikin sabo, da hakurin da zai hana shi yin fushi, da kyakkyawar mu'amala ga wadanda zai yi abota da su.

Kuma mafi girman abinda bayi suke kusantar Ubangijinsu da shi a cikin hajjinsu shine TAUHIDI, da TSARKAKE AYYUKA GA ALLAH cikin dukkan bautansu, Allah -سبحانه- ya ce: "Kuma ku cika hajji da umrah domin Allah", [Bakara:].

Kuma lallai shelanta kadaitakar Allah a cikin hajji shine tambarin mahajjata, kuma da shi suke samun daukaka "LABBAIKAL LAHUMMA LABBAIK, LABBAIKA LA SHARIKA LAKA LABBAIK, INNAL HAMDA WANNI'IMATA LAKA WALA WAL MULKA LA SHARIKA LAK".

Kuma duk wanda yayi hajji yana mai yakinin haduwa da Ubangijinsa, to ya yi riko da lamarin tauhidin Allah da kadaita shi da ibada har zuwan mutuwansa, Allah -سبحانه- ya ce: "Kuma duk wanda ya kasance yana fatan haduwa da Ubangijinsa, to ya aikata aiki na kwarai, kuma kada yay i shirki da wani cikin ibadar UbangijinSa", [Kahf: ].

Kuma yin KABBARORI GA ALLAH DA GIRMAMA SHI shine ke debe wa Mahajjata kewa a cikin dawafinsu, da sa'ayinsu, da lokacin jifan Shedan da yayin yanka, da cikin darensu da yininsu, domin zukata su wanzu suna rataye da Allah, kuma tsarkakakku daga dukkan wand aba shi ba.

Hajji makaranta ce ta tabbatuwa kan bi da koyi da shugaban halittu –صلى الله عليه وسلم-; saboda babu hajji, haka babu wata ibada da zata cika ta samu kamala, sai irin abinda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya aikata, kuma wanda ta kasance akan shiriyarsa, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Domin ku koyi aikinku na hajji, saboda lallai ni, ban sani ba, la'alla b azan yi hajji ba, bayan wannan hajjin nawa", Muslim ya ruwaito shi.

Kuma koyi da Annabi SAW dalili ne kan gaskiyar imani da kuma sonsa, Allah Ta'alah ya ce: "Ka ce: Idan kun kasance kuna son Allah, sai ku bi ni, Allah zai so ku, kuma ya gafarta zunubanku, domin Allah Mai gafara ne Mai jin kai", [Ali-imrana: ].
Kuma duk ibadar da ta saba wa shiriyar Annabi –صلى الله عليه وسلم- Allah ba zai karbe ta ba, saboda rugujejjiya ce, Annabi –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Wanda ya aikata wani aiki wanda babu umurninmu, to an mayar masa", Muslim ya ruwaito.

Kuma yana daga MANUFOFIN HAJJI MASU GIRMA: Tsayar da ambaton Allah, da yawaita zikirinsa, A'isha –رضي الله عنها- ta ce: "Lallai an shar'anta dawafin dakin Allah ne, da sa'ayi tsakanin Safah da Marwah, da jifan tsakuwa, domin tsayar da ambaton Allah".
Saboda haka, Ambaton Allah Ta'alah yake kasancewa da Mahajjata, duk lokacin da suka taso, ko suka sauka, ko suka gangaro, ko suke hawa, kuma ba zai gushe yana tare da su ba, har lokacin gama aikinsu, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma idan kuka cika aikinku, sai ku yi zikirin Allah, kamar ambaton Ubanninku, ko ambaton da ya fi haka", [Bakara: ].
Kuma Mahajjacin da yafi kusanci da Allah, shine wanda yafi su yawaita ambaton Allah.

Hajji aikin da'a ne, wanda ayyukan da'a suke tattare da shi, a cike yake da tarin amfani da guraben daukar izina da ayoyi. Kuma a cikinsa akwai tsarkake zuciya ga Allah Ta'alah, da sallama rai a gare shi da nuna cikar bauta, Shekhul Islam –رحمه الله- ya ce: "Hajji yana ginuwa ne akan mika wuya da Kankan-da-kai ga Allah, shi ya sa ya kebanta da sunan: NUSUK".

A hajji Musulmai ke samun haduwar zukata, sai igiyoyin soyayya su kara karfi a tsakaninsu. Sai girman Musulunci da falalarsa ta bayyana ga halitta, Allah Ta'alah ya ce: "Kuma ya daidaita tsakanin zukatanku, da zaka ciyar da abinda ke bayan kasa gaba daya, gaba daya, da ba za ka iya daidaita tsakanin zukatansu ba, Saidai Allah shine ya daidaita tsakaninsu", [Anfal: ].
Kuma cikin haduwar Mahajjata a bagire daya akwai nuna ko tunatarwa kan falalar wannan al'ummar, da daukakar sha'aninta.

Kuma mafi alherin Mahajjata shine wanda ya fi su kyan hali, kuma da haka bawa ke koyan sifofi da halaye ababen yabo, Allah Ta'alah ya ce: "Duk wanda ya niyyaci hajji a cikinsu, to babu kwarkwasa, kuma babu fasikci, kuma babu jayayya a cikin hajji", [Bakara: ].
Kuma cikinsa akwai horas da rai kan juriya da hakuri, A'ishah –رضي الله عنها- ta ce: "Muna ganin yin jihadi shine aikin da yafi fifiko, shin mata ba za mu je jihadi ba? Sai Annabi SAW ya ce: A'a! ku kuna da jihadin da yafi falala; shine yin hajji gangariya", Bukhariy ya ruwaito shi.

Musulmi yana jin daukaka da addininsa, kuma yana nisatar da kansa daga ayyukan jahiliyya da halayensu. Kuma a cikin hajji akwai karfafa hakan gaya, Ibnul-kayyim –رحمه الله- ya ce: "Shari'a ta tabbatu wajen nufin saba wa mushirkai, musamman a cikin ayyukan hajji".

Kuma duk lokaci a cikin rayuwar bawa idan bai kusantar da shi ga Ubangijinsa ba, to sai ya nisantar da shi. Kuma lallai bayi suna cikin tafiya ne mai sauri zuwa ga Allah, kuma hakan yana fitowa fili ga Mutum a cikin ibadodin hajji da ayyukansa, idan y agama wata ibadar sai ya yi gaggawar fara wata, to haka sha'anin yake a cikin dukkan rayuwarsa, Allah Ta'alah ya ce: "Idan ka gama ibada, sai ka kafu wurin addu'a * kuma zuwa ga Ubangijinka, ka nuna kwadayi", [: ].

Aikin biyayya yana kara wa ma'abucinsa bukatuwa ga UbangijinSa, da Kankan-da-kai, sai bawa ya shaidi falalar Allah akansa da ya bashi damar aiwatar da ita, sai kuma ya rika neman gafararSa akan sakaci da gajartawa a cikin ibadar, "Sannan ku gangaro ta wurin da Mutane ke gangarowa, kuma ku nemi gafarar Allah, lallai Allah Mai gafara ne Mai jin kai", [Bakara: ].

Kuma duk wanda ya kange kansa daga aukawa cikin Mahzuraat a hajjinsa, to lallai ya dace ya hana kansa aikata sabo, a kowani zamani da kowane wuri.

        BAYAN HAKA, YA KU MUSULMAI!
        Fa'idar hajji shine gyaran rai da tsarkake ta, da rabauta da yardarm Allah Ta'alah, da tsira da Aljannonin ni'ima.
Wanda aka masa katarin samun haka, shine wanda yay i hajjinsa da niyya tagari tsarkakakkiya, cikin ilimi da basira, da guzuri mai dadi na halal, sai ya raya zuciyarsa da harshensa da ambaton Allah. Kuma ya cike ibadarsa da kyautatawa halittu da amfanar da su.

Kuma wanda ya kyautata hajjinsa, ya nisanci abinda suke masa miki, to sai ya koma bayan hajjinsa da mafi kyan hali, kuma ya samu daddadan makoma.
Kuma alamar karbuwar aiki ita ce yin kyakkyawan aiki bayanta, da barin alfahari da girman kai da ibada.

A UZU BILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM:
"Kuma Allah ya wajabta wa Mutane ziyartar dakinsa, ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi, kuma wanda ya butulce, to lallai Allah ya wadatu ga barin Talikai", [Ali-imrana: ].

        ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALKUR'ANI MAI GIRMA. Kuma ya amfanar da ni da ku da abinda ke cikinsa na ayoyi da tunatarwa mai hikima. Ina fadan abinda ku ke ji, kuma ina neman gafarar Allah wa ni da ku da sauran Musulmai daga kowane zunubi, sai ku nemi gafararSa, lallai shi Mai yawan gafara ne, Mai jin kai
         

HUDUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa, kuma godiya tasa ce, akan datarwarSa da ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kadai ya ke bashi da abokin tarayya; ina mai girmama sha'aninSa,
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa,
Ya Allah, ka yi dadin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da sallamar amintarwa mai ninninkuwa

Ya ku Musulmai…
        Fifikon da ke tsakanin darare da yini yana kira don ribatar alherin da ke cikinsu.
        Kuma kusa-kusa mafi falalan yini a wurin Allah za su sauko a cikinmu, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Mafi falalan kwanakin Duniya sune kwanaki goman farkon watan hajji", Ibnu-Hibbana ya ruwaito shi.
        Kuma ranar LAYYAH  a cikinsu shine ranar ayyukan hajji da yafi girma, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Lallai mafi girman kwanaki a wurin Allah Tabaraka Wa Ta'alah shine ranar soke layyah", Abu-dawud ya ruwaito shi.
        Wadannan kwanakin goma Allah yay i rantsuwa da dararensu a inda ya ce: "Ina rantsuwa da Alfijir * da kuma darare guda goma" [Fajr: 1-2].
        Kuma kowane aiki nagari idan aka yi shi a cikin wadannan kwanakin yafi soyuwa a wurin Allah, fiye da a yi shi a cikin kwanakin da ba su ba, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce "Babu wasu yini wanda aiki nagari yafi soyuwa a cikinsu a wurin Allah, fiye da wadannan yinin guda goma. Sai suka ce: Ya Ma'aikin Allah! Koda jihadi ne fiysabilil Lahi?! Sai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: koda jihadi ne fiysabillahi, sai ga mutumin da ya fita da ransa da dukiyarsa, sai bai koma da komai ba", Abu-dawud ya ruwaito shi, Amma tushen hadisin yana wurin Imam Albukhariy.

        Don haka, sai ku yawaita ambaton Allah a cikinsu, da tilawar littafinSa mai girma, Allah Ta'alah ya ce: "Sais u ambaci sunan Allah a cikin kwanaki sanannu", [Hajji: ].
        Kuma yana daga cikin ayyuka na mustahabbi a cikin kwanakin nan guda goma: Yin azumin yini tara na farko daga cikinsu, kuma a cikinsu an kebance yinin Arfah, ga wand aba Mahajjaci ba, da Karin falala, saboda azuminsa yana kankare shekarar da ta shude da wanda ake ciki.

        Kuma yana daga cikin ayyuka na kwarai da suke cikin kwanakin nan goma: Karin biyayya da kyautata wa iyaye biyu, da sadar da zumunci, da sadaka, da yawaita nafilfilin ibadodi.
        Mai rabo shine wanda ya ribaci lokutan alherori gabanin wucewansu, kuma yay i rige wajen aikata kyawawan ayyuka, kuma ya yi rigaggeniya da masu gaggawan aikin kwarai a cikinsu.
        Kuma rayuwa ganima ce ga masu takawar Allah.
Wanda kuma yay i dace, shine wanda aka kidanya shi daga cikin bayin Allah muhsinai.

Wanda ya yi nufin YIN LAYYAH, to kada ya aske wani abu na gashinsa ko yanke farce ko cire fata, har sai ya yi layyah.
Amma wanda aka bashi wakilcin layya, ko wanda za a musu layya, idan suka kasance rayayyu, to wannan hukuncin bai hau kansu ba.

>>> 
        Sannan ku sani, lallai Allah ya umarce ku da yin salati da sallama ga annabinSa, a cikin mafi kyan littafinSa, inda ya ce: "Lallai ne Allah da Mala'ikunSa, suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku waxanda su ka imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa", [Ahzab: 56].
        Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga annabinmu Muhammadu,
       

        Bayin Allah!!!
          "Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.



2018/08/06

HAJJI … RUKUNNANSA DA WAJIBANSA الحج .. أركان وواجبات









HAJJI … RUKUNNANSA DA WAJIBANSA
(الحج .. أركان وواجبات)













Tarjamar
Abubakar Hamza


Shin ka yi azamar hajji a wannan shekarar?
Shin kana son hajjinka ya zama mabrur?
To, sai ka koyi hukunce-hukuncen hajjinka, sai ka yi aiki da su da-kyau, kuma tsarkake Allah da ikhlasi cikin hajjinka.

Hajji yana da RUKUNNAI guda hudu.
Da ayyukan WAJIBI guda bakwai.
Kuma banbanci tsakaninsu shine lallai WAJIBI idan ya kubuce, ana cike gibinsa da yanka dabba. Amma shi kuma RUKUNI to lallai hajjin baya inganta sai in aikata shi.

RUKUNNAN HAJJI sune:
1.   YIN HARAMA: Kuma shine niyyar shiga cikin aikin.
2.   TSAYUWA GA ARFAH.
3.   DAWAFUL IFADHA: Kuma shine ake aikata shi ranar idi ko bayansa.
4.   YIN SA'AYI tsakanin Safah da Marwah.

Su kuma WAJIBAN HAJJI: Sune:
1.   YIN HARAMA daga Mikati.
2.   WANZUWA A FILIN ARFAH, har zuwa faduwar rana, ga wanda yay i tsayuwarsa da rana.
3.   KWANA A MUZDALIFA.
4.   KWANA A MINAH.
5.   JEFA JAKWANKWANI.
6.   ASKE GASHIN KAI GABA DAYA, KO RAGE SHI, Saidai askewan shine yafi falala.
7.   DAWAFIN BANKWANA ga wand aba mai haila ko jinin biki ba.
Duk kuma abin da ba wadannan ba, sunnoni ne abin so, kamar kwana a Minah a dare tara.

Sai ka yi kokarin hajjinka ya cika, ta hanyar aiki da RUKUNNANSA DA WAJIBANSA DA SUNNONINSA, domin ya kasance hajji gangariya karbabbe. Kuma ka sani! Lallai sakamakon haka shine Aljannah, saboda ya zo cikin hadisi cewa:
"والحج المبرور ليس له جزاء إلا الجنة"، متفق عليه.
Ma'ana: "Kuma hajji gangariya bashi da wani sakamako face Aljannah", Bukhariy da Muslim.

ARFAH SHINE WANNAN YININ DA AKE HALARTA عرفة ذلك اليوم المشهود









ARFAH SHINE WANNAN YININ DA AKE HALARTA
(عرفة ذلك اليوم المشهود)













Tarjamar
Abubakar Hamza


Idan rana ta fudo a yini na tara (9) a watan ZUL-HIJJAH, Mahajjata su kan nufi filin Arfah, domin sauke babban rukunin hajji, a cikin wani yini daga cikin jerin yinin da ake halarta, kamar yadda Allah Ta'alah ya ce:
"واليوم الموعود * وشاهد ومشهود".
Ma'ana: "Kuma ina rantsuwa da yinin da aka yialkawarin zuwansa * da yini mai shaidu, da yini da ake halartan Arfa a cikinsa".
Kuma abinda ake nufi da yini mash-hud shine yinin Arfah, kamar yadda hakan ya tabbata daga Annabi –Sallal Lahu alaihi wa sallama-.

Kuma yana daga falalar wannan yinin akan sauran kawanaki, lallai shine yinin da Allah ya dauki alkawari da 'yan-adam. Kuma shine yinin da Allah ya cika addini a cikinsa, kuma ya cika ni'imarsa ga Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama-, da Al'ummarSa. Kuma rana ne na gafarta zunubai, da 'yanta bayi daga fadawa wuta. Kuma ranar idi ne ga wadanda suka tsayu a filin Arfah.

Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya shar'anta azumtar wannan yinin ga wanda ba Mahajjaci ba, a cikin fadinSa:
"صيام يوم عرفة أحتسب على الله أن يكفر السنة التي قبله والسنة التي بعده"، مسلم.
"Azumin yinin Arfah ina fatan Allah zai kankare shekarar da ta gab ace shi da shekarar da take bayansa", Muslim.   

Kuma a farfajiyar Arfah Mahajjata ke tsayawa, suna masu ambaton Allah Ta'alah, suna masu fiskantarsa da addu'oi, suna masu tsoro masu Kankan-da-kai, har zuwa faduwar rana.

Allah yana alfahari da su ga Mala'ikunsa a wannan yammacin wannan yinin, sai ya ce:
"انظروا إلى عبادي أتوني شعثًا غبرًا، من كل فجّ عميق، أُشهدكم أني قد غفرت لهم".
"Ku yi dubi ga bayina, sun zo min da gizo da kura, daga kowani lungu mai nisa, Ina shaida muku lallai ni na gafarta musu".

Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce:
"خير الدعاء دعاء يوم عرفة، وخير ما قلت أنا والنبيون من قبلي: لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير"
"Mafi alherin addu'a shine addu'ar yinin Arfah, kuma mafi alherin abinda na fada Ni da annabawan da suka zo gabanina shine: LA ILAHA ILLAL LAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KADIR".

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...