2017/06/16

21 ramadan 1438 hudubar juma'a daidai da 16 june 2017 DR. ABDULMUHSIN ALKASIM










HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
 (صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 21/RAMADHANA/1438H
Daidai da 15 /YULI / 2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN MUHAMMADU XAN ABDURRAHMAN ALQASIM







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar, babu mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar, to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara tabbata a gare shi, da IyalanSa da SahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.

       Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah da taqawa -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa, kuma ku kiyaye shi, a asirce, da kuma a bayyane (a lokacin ganawa).

       Ya ku musulmai …
            Ubangijinmu (S.W.T) Mai karmici ne, Mai baiwa, TaskokinSa suna cike, Mulkin komai kuma, a hannunSa ya ke,
Ya zuba ni'imominSa ga bayinSa, kuma ya biyar da kyauta da falaloli, xaya bayan xaya a kansu,
Babu mai hana abinda ya bayar, kamar yadda babu mai bayar da abinda ya hana,
Kyautukan Allah basu da iyaka ta fiskar yalwa da yawa,
Yana yin kyautar alkhairori da karamomi,
Kuma kyautarSa tana ci-gaba bata yankewa, ta kuma game dukkanin halittunSa; sai alkhairorinSa su ka dawwama, falalolinSa da ni'imominSa su ka riqa saduwa,
Yana farar bayi da kyautar ni'imomi gabanin su roqe shi, kuma yana musu baiwar fiye da abinda ke xarsuwa a tunaninsu,
Babu wani a cikin sama da qasa, wanda baya cikin baiwar Allah,
Don haka, Allah shi ne wanda ya fi cancantar samun yabo da zikiri ko ambato akan ni'imominSa, ta hanyar tsantsanta soyayya, da bauta a gare shi, da kuma jingina ni'imomin zuwa gare shi, da yin amfani da ni'imomin cikin xa'a a gare shi.

Yana daga cikin BAIWOWINSA MAXAUKAKI afuwarSa ga wanda ya nufa daga cikin bayinSa, Allah (ta'alah) yana cewa: "Lallai ne Allah Mai afuwa ne, Mai gafara" [Haj: 60].
            Kuma Allah bai gushe ba yana afuwa ga zunuban bayinSa, ta hanyar barin yin uquba, ga dayawa daga cikinsu, matuqar basu masa shirka, ko su ka sanya masa kishiyoyi ba, Allah (ta'alah) yana cewa: "Kuma shi ne, wanda ke karvar tuban bayinSa, ya ke afuwa akan munana, kuma ya ke sane da abinda ku ke aikatawa" [Shura: 25].
            Mai afuwa ne, yana son afuwa, kuma yana son halittunSa su riqa aiki tuquru, domin samar da sabbuban afuwarSa, ta hanyar istigfari, da tuba, da imani, da ayyuka nagari.

            A cikin watan ramadhana kyautukan Allah da afuwarSa suna qara bayyana, watan falaloli da gafara, wanda a cikinsa ake ninninka ayyuka, ake kankare kura-kurai da zunubai, kuma a cikinsa ake bubbuxe qofofin rahama da aljannoni, ake sanya shexanu cikin qullin sarka, ake rurrufe qofofin wuta, watan azumi da karatun alqur'ani, da biyayya da kyautatawa, kasuwanci a cikinsa tare da Allah, ana ninninka shi, Ibnul-Jauziy –رحمه الله- ya ce: "Ladan aiki yana qaruwa, saboda darajar lokaci, kamar yadda ke qaruwa idan aka halarto da zuciya, ko aka tsantsance niyya".

            Sallar dare, ita ce mafificin nafiloli bayan sallolin farilla, kuma Allah ya yi yabo ga bayinSa masu taqawa a cikin faxinSa: "Sun kasance a lokaci kaxan na dare su ke yin barci" [Zariyaat: 17].
            Kuma ya zo cikin hadisi cewa: "Wanda ya yi tsayuwar ramadhana (wato, sallar dararen watan) cikin imani da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa", Bukhariy da Muslim.
Kuma "Duk wanda ya yi sallolin dare tare da liman, har ya idar, to an rubuta masa ladan tsayuwan daren", Tirmiziy ya rawaito shi.
            Kuma duk wanda ya lazimci sallolin dare to ya cancanci shiga aljanna cikin aminci, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Ya ku mutane! Ku riqa yaxa sallama, ku ciyar da abinci, kuma ku sadar da zumunci, ku riqa sallah cikin dare, a lokacin da mutane ke barci, sai ku shiga aljanna da salama", Ahmad ya rawaito shi.

            Ita kuma SADAKA hujja ce kan imanin ma'abucinta, kuma kowani mutum yana qarqashin inuwar sadakarsa, a yinin qiyama, kuma mai ciyarwa an masa alqawarin samun xaukaka da gafara, Allah (سبحانه) yana cewa: "Kuma duk abinda kuka ciyar na kayan ciyarwa, ko, wani bakancen da ku ka yi, to lallai Allah yana saninsa" [Baqara: 270].
            Kuma ladan sadaka yana qara girma, idan aka gudanar da ita, a kwanaki masu falala. Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya kasance "shi ne, ya fi mutane kyauta, sai dai ya fi yawaita kyautar a cikin watan ramadhana", Bukhariy da Muslim.
            Kuma "yin UMRAH a watan azumi yana daidai da yin hajji", Bukhariy da Muslim.
            ADDU'A abu ne mai riba, wanda bashi da wata wahala, kuma addu'a shi ne bauta, kuma shi ne qashin bayan bauta, kuma da addu'a ake janyo wadaci, ake tunkuxe bala'oi, kuma mai azumi idan ya yi addu'a ba a mayarwa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Mutane uku ba a mayar da addu'arsu; Mai azumi har zuwa lokacin buxa-baki, da shugaba adali, da addu'an wanda aka zalunta; Allah yana xaga ta saman girgije, kuma yana buxe mata qofofin sama, kuma Ubangiji yana cewa: Na rantse da buwayata! Zan taimake ki, koda bayan wani lokaci ne", Tirmiziy ya rawaito shi.

            ALQUR'ANI hujja ne, mai ceto, kuma shiriya da waraka, ma'abutansa; masu aiki da shi, su ne zavavvun halittu, kuma mafiya alheri, kuma su ne mutanen Allah, waxanda ya kevance, Allah ya yi musu alkawarin samun sakamako, da kuma qari daga falalarSa, a inda yake cewa: "Lallai waxanda ke karatun littafin Allah, kuma su ka tsayar da salla, kuma su ka ciyar daga abinda muka azurta su da shi, a asirce da a bayyane, to lallai suna fatan fatauci wanda bata tasgaro * domin Allah ya cika musu sakamakonsu, kuma ya musu qari daga falalarSa, Lallai shi Mai gafara ne Abin godiya" [Faxir: 29-30].

            LOKUTAN RAMADHANA fili ne mai faxi ga masu tsere a cikinsa, ayyukan biyayya da sadar da zumunci suna yawaita a cikinsa, kuma rayuka suna tsaftatuwa, halaye kuma suna tsarkaka, Halittu a tsakanin junansu suna kusantar juna, kuma sashinsu yana tausaya wa sashe.
            Lokaci ne mai albarka wanda musulmai su ke zage damtse a cikinsa, kuma ake xaga darajoji a cikinsa,
            Sai dai kash, ga kwanakin watan na ku (na ramadahana), suna shelanta, qarewa, kuma mai hankali shi ne wanda ya ribaci gomansa (na qarshe), sai ya rayar da su, da ayyukan kusanci, da xa'oi, ya kuma canza munanan ayyuka da kyawawa, sai ya kiyaye yininsa, ya rayar da darensa, kuma ya sanya Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya zama abin koyinsa, jagora, domin ya kasance, "yana qara qoqarin bauta a goman qarshe, irin qoqarin da baya yi a sauran dararen", Muslim ya rawaito shi.
Kuma "Idan waxannan goman su ka shigo, ya kasance yana raya dare, yana kuma tayar da iyalansa, sai kuma ya daxa qoqari, ya qara zage damtse", Bukhariy da Muslim.
            A cikin waxannan dararen masu albarka, mustahabbi ne yawaita zikirin Allah, da karatun alqur'ani, Ibnu-Rajabin –رحمه الله- yana cewa: "Amma, lokuta masu falala, kamar watan azumi, musamman a dararen da ake neman lailatul qadari a cikinsu, to lallai mustahabbi ne a yawaita karatun alqur'ani, domin ribatar wannan zamanin".

            Kuma ya dace, Musulmi a cikin waxannan kwanakin ya yi kwaxayin aiki da ADDU'AR DA TA FI AMFANI, kuma ta fi gamewa, A'isha –رضي الله عنها- ta ce: Ya Ma'aikin Allah, idan na yi dacen lailatul qadari, me zan riqa faxa a cikinta? Sai ya ce:  "Ki ce, ALLAHUMMA INNAKA AFUWWUN TUHIBBUL AFWA FA'AFU ANNI, Ma'ana: Ya Allah, lallai ne kai, mai afuwa ne, kana son afuwa, ka min afuwa". Ahmad ya rawaito shi.
            I'ITIKAFIN waxannan goman sunnah ce da ta zo a sharia'a, saboda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya yi i'itikafinsu, sa'annan sai matansa su ka cigaba da i'itikafinsu,
Ibnu-shihabin –Allah yayi masa rahama- yace: "Mamakin lamarin musulmai, sun bar yin i'itikaafi, alhalin Annabi (صلى الله عليه وسلم) bai bar yinsa ba tun da ya shiga garin Madina, kowace shekara, a cikin kwanaki goma na qarshen ramadhana, har Allah ya karvi ransa".
            Kuma ya dace, Mai i'itikafi, ya tsayu domin yin bauta, ya kuma shagaltu da manufar shar'anta i'itikafin, wanda ta fi girma, yana mai nisantar yawaita hulxoxi, da magana, ko yawaita ci, da barci.
Kuma ba zai fita daga masallacin ba, sai ga buqatar da babu makawa daga gare ta, Ibnul-qayyim –رحمه الله- ya ce: "Kuma manufar i'itikafi da ruhinsa, shi ne killace zuciya ga Allah, da tattara ta, a gare shi, da kevantuwa da shi, da yanke ko barin shagaltuwa da halittu, da shagaltuwansa da Allah; shi kaxai (S.W.T), ta yadda ambaton Allah (zikirinsa) da qaunarsa, da fiskantarsa, za su zama a gurbin tunani-tunanin zuciyarsa, da ababen da su ke xarsuwa a gare shi".

            Kuma a cikin DARAREN NAN GOMA NE, Musulmai ke neman dacewa da lailatul qadari, Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ku nemi lailatul qadari a darare goman qarshe, na watan ramadhana", Bukhariy da Muslim.
            Kuma an fi fatan samunta, a cikin dararen mara daga cikinsu, Manzo Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ku kirdadi lailatul qadari a cikin mara ko wutirin darare goman qarshe, na watan ramadhana", Bukhariy ya rawaito shi.
            Kuma acikin darare bakwai na qarshe, an fi fatan samun nata, saboda Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Ku neme ta -yana nufin: lailatul qadari- a cikin goman qarshe, idan xayanku ya yi rauni ko ya gaza, to kada a rinjaye shi akan darare bakwai masu wanzuwa –na qarshe-", Muslim ya rawaito.
            Shekhul Ismlami Ibnu-taimiyyah –رحمه الله- yana cewa: "Sai dai wuturin zai kasance ne, tare da kula da abinda ya gabata; sai a nemi daren ashirin da xaya (21), da daren ashirin da uku (23), da kuma daren ashirin da biyar (25), da daren ashirin da bakwai (27), da daren ashirin da tara (29), ko kuma ya kasance tare da lura da dararen da su ka rage (daga watan), kamar yadda Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: (a neme ta), ga darare tara wanda za su rage, ko ga bakwai waxanda za su rage, ko ga biyar waxanda za su rage, ko ga uku waxanda za su rage. A kan wannan, idan watan ya kasance kwanaki talatin ne (30), sai hakan ya kasance a cikin kwanaki na shafa'i, Sai ashirin da biyu (22), ya kasance, shi ne darare taran da su ka rage, sai kuma daren ashirin da huxu (24) ya kasance shi bakwai da za su rage, kuma da haka Abu-Said –رضي الله عنه- ya fassara shi, a cikin hadisi ingantacce. Kuma haka Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya tsayu a lamarin wata. Idan kuma lamarin ya kasance kamar haka, to lallai ya dace, Mumini ya yi kirdadon dacewa da lailatul qadari a cikin darare goman qarshen gab xayansu".

Daren LAILATUL QASARI dare ne mai girma; ma'abucin matsayi da daraja, kuma Allah ya saukar da sura sukutum akansa domin girmama sha'anin daren, da muhimmantar da lamarinsa, da xaukaka sha'aninsa, a inda ya ce: "To, me ya sanar da kai abinda ake cewa: Lailatul qadari?" [Qadr: 2].
Allah ya sanya ta mai albarka, mai yawan alheri, sai ya ce: "Lallai mu ne muka sauqar da shi a cikin wani dare mai albarka" [Dukhan: 3].
Kuma yada daga albarkar wannan daren, sauqar alqur'ani a cikinsa, Allah ta'alah yana cewa: "Lallai mu ne muka sauqar da shi (Alqur'ani) a daren qaddara" [Qadr: 1].
            Kuma a cikin daren Mala'iku ke sauka zuwa ga duniya, "Mala'iku da Ruhi suna sauka a cikinsa, da izinin Ubangijinsu, da kowani lamari" [Qadr: 4].
Ibnu-kasir –رحمه الله- ya ce: "Saukar Mala'iku yana yawaita, a cikin wannan daren ne, sabodab yawan albarkarta, kuma Mala'iku suna sauka ne tare da saukar albarka, da rahama, kamar yadda su ke sauka a lokacin tilawar qur'ani, kuma su ke kewaye halqoqin zikiri, kuma su ke shumfuxa fuka-fukansu ga xalibin ilimi na gaskiya, domin girmama shi".
            Dare ne na salama da aminci da natsuwa, Allah -تعالى- yana cewa: "Salama ne wannan daren, har fitar alfijir" [Qadr: 5].
Wato, dare ne da ya kuvuta daga sharrori.
            Raya wannan daren da ibadodi riba ne mai girma, Allah -تعالى- ya ce: ''Lailatul qaradi ya fi yawan alkhairi fiye da watanni dubu" [Qadr: 3].
An-Nakha'iy –رحمه الله- ya ce: "Yin aiki a cikin wannan daren, ya fi alkhairi akan yin aiki a cikin watanni dubu".
            Wanda ya rabauta da wannan daren, shi ne wanda ya tsayu a cikinta, yana mai gaskata alqawarin Allah, yana kuma neman lada, ba wata manufar ta daban ba; kamar riya, da makamancinta, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya yi tsayuwar lailatul qadari cikin imani da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa".
            Kuma a cikin wannan daren ake qaddara dukkan qaddarar da za ta samu halittu gaba xaya, na xaukacin shekara, sai ya a yanko shi daga jikin lauhul mahfuz, zuwa ga Mala'iku marubuta, sai abin da zai kasance ya bayyana musu, sai kuma Allah ya umarce su da aikata abinda aikinsu ne, kamar yadda Allah -تعالى- ya ke cewa: "A cikin daren, ake rarrabe kowani lamari da ake hukuntawa * Lamari ko umarni ne daga wajenmu, lallai mun kasance masu aikewa" [Dukhan: 4-5].

          BAYAN HAKA, YA KU MUSULMAI!
            Ayyuka ana lura da abinda aka gama su ne, kuma lallai abin luran shi ne kamalar qarshen ayyuka, ba tawayar farkonsu ba; don haka; duk mutumin da a farkon watansa ya kasance ya mayar da lamari ga Allah, aikinsa kuma ya yi dacen Sunnah, to sai ya qara kyautata gininsa, ya kuma yi godiya wa Allah, kan ni'imomi, kuma kada ya kasance kamar wadda ta warware zaren saqarta, bayan tukka ta yi qarfi, ya zama warwararru.
            Wanda kuma ya munana a cikin kwanakin da su ka shuxe, to sai ya tuba cikin abinda ya rage; saboda qofar tuba a buxe ta ke, kuma baiwar Allah abar bayarwa ce.
Kuma "Kuma wanda ya bi Allah da taqawa, Allah zai sanya masa mafita" [Xalaq: 2].

A UZU BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIM:
"Yak u waxanda su ka yi imani, idan ku ka bi Allah da taqawa, zaisanya muku ma'aunin rarrabewa (na ilimi)" [Anfal: 29].

            ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA. …
             



HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa;  Godiya kuma tasa ce bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke bashi da abokin tarayya; Ina mai girmama sha'aninSa.
Ina kuma shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa.
Ya Allah, ka yi daxin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.

Ya ku musulmai…
            Duniya awowi ne da kwanaki, kuma tana da shekarun da aka xibar mata, shekarun mutum a cikinta kuma, sune wanda ya yi aiki a cikinsu.
Lallai Mai rabo, shi ne wanda ya dawwamar da ambaton duniya, da mafi kyan ayyuka, kamar yadda Wanda ya ci nasara  shi ne, ya ribaci daqiqoqin lokacinsa, kuma bai yi sakaci cikin wani abu na zamaninsa ba.
            Wanda ya faxi babu nauyi, kuma shi ne mutumin da lamuransa su ka sakwarkwace masa, zuciyarsa ta gafala, ya kuma bi son zuciyarsa.
Marashin rabo, shi ne wanda aka hana shi aikin alheri a cikin watan azumi, tavavve kuma shi ne wanda ya yi hasarar lakuta masu falala, Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Turvaya ta bugi hancin mutumin da, watan Ramadhana ya shigo, har ya fita, sai ba a gafarta masa ba",  Tirmiziy ya rawaito shi.
>>> 

            Sannan ku sani, lallai Allah ya umarce ku da yin salati da sallama ga annabinSa, a cikin mafi kyan littafinSa, inda ya ce: "Lallai ne Allah da Mala'ikunSa, suna yin salati ga wannan Annabin, Ya ku waxanda su ka imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa", [Ahzab: 56].

            Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga annabinmu Muhammadu,
            Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu, waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka haxa da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
            Ya Allah! Ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya –Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala, da kuma sauran qasashen Musulmai.


                Bayin Allah!!!
                "Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.


2017/06/09

hudubar 14 RAMADANA 1438 daidai 9 June 2017 ta AsSubaitiy daga MASALLACIN ANNABI







HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 14/Ramadhana/1438H
Daidai da 09/Yuniyo/2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHIN MALAMI ABDULBARIY XAN AUWADH AS-SUBAITIY






TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
SIFOFIN BAYIN MAI RAHAMA
     Shehin Malami wato: Abdulbariy xan Auwadh Al-Subaitiy –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'ah, 14/ Ramadhana, 1438H, mai taken: SIFOFIN BAYIN MAI RAHAMA, Wanda kuma a cikinta ya tattauna akan.

HUXUBAR FARKO
Bayan haka:
A cikin kwanaki da dararen da mu ke ciki (na ramadhana), muna ganin yadda bauta ke bayyana a cikin mafi qayatarwar surarta da ma'anoninta, (ta fiskar) daxin azumi, da zaqin qur'ani, da kyan tsayuwa cikin sallolin dare, da sadaka da ciyarwa, ga kuma harasa, suna furta zikiri ko ambaton Mai rahama,
Gavvai, da soyayya, da zukata, sun rusuna ga Allah, cikin ibadar da ake yi ba da tilasci ba, wacce ginshiqinta shi ne soyayyar zuciya, wanda kuma za ta kai ga samun rabauta, a duniya da lahira.
Ibada bata rabuwa da musulmi, a duk inda ya sauka, a kuma dukkan lokutan da ya kasance a cikinsu, na matakan rayuwarsa, har ajalin da aka yanke masa ya same shi, alhalin yana cikin hali mai kyau, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma, ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka" [Hijr:  99].
Zuciya tana rausayawa, rayuwa kuma, tana xaukaka, a lokacin da kunnuwa ke jin yadda Allah ke siffanta halittunSa da kalmar YA KU BAYINA!
Kuma duk wanda ya faxa qarqashin wannan kira, ya kuma rabauta da xaukakar da ke cikin kalmar YA KU BAYINA! to lallai, ya samu babban rabo, mai girma.
Kalmar YA KU BAYINA! tana tultulo da natsuwa cikin zukata, kuma tana amintarwa daga tsoro, kuma alamar samun yardar Ubangiji ne, da falalarSa da ni'imarSa, Allah ta'alah yana cewa: "YA KU BAYINA! a yau, babu tsoro a kanku, kuma ku, ba masu yin baqin ciki ba ne * Waxanda su ka yi imani da ayoyinmu, kuma su ka kasance masu miqa wuya * Ku shiga aljanna, ku da matayenku, ana girmama ku" [Zukhruf: 68-70].
Rai natsattasiya, wacce imani ya tabbatu a cikinta, kuma ta natsu da tsantsance bautarta; na ikhlasi, kuma ta yi tawakkali ga Mahaliccinta, Ubangijinta lallai ya xaukaka ta da bushararSa mai girma; wanda ta zo a cikin faxinSa: "Ya ke Rai mai natsuwa * Ki koma zuwa ga Ubangijinki, alhali kina mai yarda, abar yardarwa * Sai ki shiga cikin BAYINA! * kuma ki shiga aljannata" [Fajr: 27-30].

Allah yana siffanta halittarSa ne da YA KU BAYINA! domin ya xebe musu kewa, kuma ya musu albishir da cewa, Shi (Allah) a kusa ya ke, kuma domin mutum ya iya shumfuxa buqatunsa, ya kuma watso damuwowinsa, yana mai xaga kokensa ga UbangijinSa; Mai jivintar lamarinsa, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma idan BAYINA! su ka tambaye ka, a kaina, to, lallai Ni Makusanci ne, Ina amsa kiran mai kira idan ya roqe Ni, sai su nemi amsawata, kuma su yi imani da Ni, tsammaninsu su shiryu" [Baqara: 186].


Kalmar YA KU BAYINA! tana yaye qiraza, kuma tana waigo da dubin mutane, zuwa ga rahamar Allah, wanda ta rigayi fushinsa, da tausasawarSa ga bayinSa, da jinqanSa, Allah ta'alah yana cewa: "Ka baiwa BAYINA! labari lallai ne, Ni Mai gafara ne Mai jin qai * Kuma lallai azaba ta, ita ce azaba mai raxaxi"[Hijr: 49-50 ].
A cikin ayar, yayin da Allah Mabuwayi ya ambaci rahama da gafara, sai ya kai maqura wajen qarfafa lamarinsu, da lafuza guda uku, wanda su ne, "ANNIY" da "ANA", da "ALIF DA LAAMUN" na nuna gamewa, ya ce:
(أنّي أنا الغفور الرحيم)
A lokacin da ya ambaci azaba kuma, bai ce: "LALLAI NE, NI NE MAI YIN AZABA", kuma bai siffanta kansa da hakan ba, kawai abinda ya ce, shi ne: "Kuma lallai azabata, ita ce azaba mai raxaxi".
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce: "Lallai Allah Maxaukaki ya halicci jin qai a ranar da ya halicce ta, rahama guda xari (100), sai ya riqe rahama casa'in da tara (99) a wurinsa, ya kuma saki guda xaya a cikin halittunSa gaba xaya, don haka; Da kafiri, ya san dukkan abinda ke wurin Allah na rahama, to da bai xebe tsammani daga samun rahama ba, Da kuma mumini yana sane da dukkan abinda ke wurin Allah ta'alah na azaba, to da bai aminta daga faxawa wuta ba".
Saboda haka,
Duk wanda ya kyautata bauta, zai kyautata zatonsa ga UbangijinSa, ya kuma amintu da yalwar rahamarSa, kuma sai ya ji cewa, lallai ababen da Allah ke qaddara wa mutane alkhairi ne, a haqiqanin lamarinsu, koda kuwa a zahirinsu musibu ne ababen qi, masu ciyo, Allah ta'alah yana cewa –kamar yadda Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- ya bada labari: "Ni ina wurin da BAWANA ya yi zatona".

Allah ta'alah yana kiran muminai ne da faxinsa: YA KU BAYINA! domin su shiga inuwar bauta a gare shi, akan kowace qasa, a kuma inuwar kowace sama, Allah ta'alah yana cewa: " YA KU BAYINA! waxanda su ka yi imani, lallai fa qasata mai yalwar faxi ce, saboda haka, ku bauta mini; ni kaxai" [Ankabut: 56].

"YA KU BAYINA" kalma ce mai taushi, wacce ta ke zaburarwa, kan yin aiki, kuma da wannan kalmar ce Mahalicci, ya kirayi bayinSa muminai, domin ya ilmantar da su ibadarsa da ta fi girma, wanda kuma ita ce tushen ibadodi (wato, sallah), da kuma xa'oin da su ka fi girma, su ka fi falala, domin su ribaci damar da ke cikin rayuwa, "Ka ce wa BAYINA! waxanda su ka yi imani: Su riqa tsayar da sallah, kuma su ciyar daga abinda mu ka azurta su, a asirce, da kuma a bayyane, gabanin yinin da babu ciniki a cikinsa ya zo, kuma babu abotaka" [Ibrahim: 31].

Don haka, Musulmi yana bautar UbangijinSa a kowani lokaci, kuma a cikin kowani hali; kamar cikin cinsa da shansa, da lokacin barcinsa da farkawarsa, a safiyarsa da maraicensa, Allah ta'alah yana cewa: "(sune) waxanda su ke ambatar Allah a tsaye, da a zaune, da kuma akan kuivinsu" [Ali-imraana: 191].

            Allah ya kira muminai ne, da faxinsa: YA KU BAYINA! domin ya zana musu hanyar samun taqawarsa, ya kuma faxakar da su yadda za su yi aiki da ita, a cikin faxinSa: "YA KU BAYINA! Ku bi ni da taqawa" [Zumar: 16].
Sai kuma Allah ya yaba musu akan aiki da taqawar, yabon da bashi da makamanci, a cikin faxinSa: "Kuma ya lazimta musu, kalmar taqawa, sai su ka kasance mafi dacewa da ita, kuma ma'abutanta" [Fat-h: 26].
Saboda babu wata qima a rayuwa wacce ta fi girma akan samun taqawa, "Lallai mafificnku daraja a wurin Allah shi ne mafificinku a cikin taqawa" [Hujuraat: 13].
            Shi kuma samar da taqawa, shi ne BABBAR ALAMAR WATAN AZUMI, Allah ta'alah yana cewa: "Ya ku waxanda su ka yi imani an wajabta azumi a kanku, kamar yadda aka wajabta shi ga waxanda su ka zo gabaninku, tsammaninku za ku samu taqawa" [Baqara: 183].
            Taqawa a watan ramadhana, tana haifar da tsarkake  rai da tarbiyyantar da ita, daga munanan halaye, ta kuma sabar mata da yin aiki da halaye masu kyau, kuma taqawar za ta koyar da bawa sanin ransa, da buqatuwar ran, da rauninta da buqatarta ga Ubangijinta (SWT), kuma ta riqa tuna mata girman ni'imomin Allah a kanta, da talauci ko buqatar 'yan'uwansa faqirai, sai ya lazimta mata godiyar godiyar Allah (SWT), da kuma yin amfani da ni'imominSa wajen yin xa'a a gare shi, da taimakon 'yan'uwansa faqirai, da kyautata musu.

            Lokacin da mumini ke jin yadda Allah ya siffanta halittunSa, da YA KU BAYINA! zai ji a jika, cewa lallai shi ya fake ga qaqqarfar madogara, da garkuwa mai bada kariya, da kuma kariya a gare shi daga dukkan shexani mai tsaurin kai, Allah ta'alah yana cewa:   "Lallai su BAYINA baka da wani qarfi akansu, Kuma Ubangijinka ya isa ya zama wakili" [Isra'i: 65].
Don haka; zuciyar da ta sadu da Allah; wato wanda rayuwarta ya cika da bauta da son Allah, shexan bashi da qarfin iko akan wannan zuciyar da ta ke haxe da Allah, kuma irin wannan zuciyar ta cancanci ta samu kariyar Allah, kuma a jikin wannan kariyar ne, kaidin shexanu dukkansa ke lalacewa.

            Allah yana siffanta salihan halittarSa da YA KU BAYINA! sai -a zukatansu- ya tayar musu da qarfin fatan samun mayewa da mallakar duniya, da hasken fatan nasara, kuma Allah ya isa ya zama Mataimaki, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma haqiqa mun rubuta a cikin littatafai, baicin lauhul mahfuz, lallai qasa, BAYINA salihai ne za su gaje ta" [Anbiya'i: 105].
Don haka, mallakar qasa, baiwa ce daga Allah, kuma alqawari ne, wanda manufarsa shi ne tabbatar da bauta ga Allah.

            "YA KU BAYINA!" kalma ce mai taushi, kuma salon magana ne tattausa, wacce ma'anarta ta ke gamewa har da masu laifi, da waxanda su ka gajarta ayyuka, matuqar sun tuba, sun kuma mayar da lamari zuwa ga Allah, Allah ta'alah yana cewa: "Ka ce: YA KU BAYINA, waxanda su ka yi varna a kan kayukansu, kada ku yanke qauna daga rahamar Allah, Lallai ne Allah yana gafarta zunubai gaba xaya, lallai shi, shi ne Mai gafara Mai jin qai" [Zumar: 53].
Bukhariy da Muslim da wasunsu sun rawaito daga Abdullahi ibn Abbas –Allah ya qara yarda a gare su- cewa, lallai wasu mutane, daga cikin ma'abuta shirka sun kasance sun yi kisa sun yawaita, sun kuma yi zina sun yawaita, sai su ka zo ga annabi Muhammadu –صلى الله عليه وسلم- su ka ce: "Lallai abinda ka ke faxa, kuma ka ke yin kira gare shi abu ne mai kyau, da za ka bamu labarin cewa: lallai akwai kaffara ga abinda mu ka aikata (na shirka da kisa da zina), sai faxin Allah ya sauqa: (Kuma su ne waxanda ba su kiran wani Ubangiji tare da Allah, kuma ba su kashe ran da Allah ya haramta kashe ta face da haqqi, kuma ba su yin zina" [Furqan: 68], sai kuma aka saukar: "Ka ce: YA KU BAYINA, waxanda su ka yi varna a kan kayukansu, kada ku yanke qauna daga rahamar Allah".
            Kuma Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Allah tabaraka wa ta'alah yana cewa: Ya kai xiyan Adamu, Lallai ne kai, matuqar za ka roqe ni, ka yi fatana, to zan gafarta maka, abinda ya kasance daga gare ka, ba zan damu ba, Ya kai xiyan Adamu, lallai ne kai, da zaka zo da kamar cikin qasa, ko abinda ya yi kusa da cikinta, na kura-kurai, sa'annan ka sadu da ni baka haxa ni da komai, to zan zo maka da gafarar da ta kai cikin qasa".

            Allah ya kyautata wa halittunSa, a inda ya siffatanta su, da YA KU BAYINA domin ya kira su zuwa ga kyautata zance, ko yin maganar da ta fi tsarki, da kuma kyautatawa cikin dukkan ayyuka, da kuma dukkan zance, da kuma dukkan sha'anonin rayuwa, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma ka ce wa: BAYINA, su riqa faxin kalmar da ta ke mafi kyau" [Isra'i: 53].
            Allah yayi mini albarka ni da ku, cikin alqur'ani mai karamci, ya kuma amfanar da mu da abinda ke cikinsa na ayoyi, da tunatarwa mai hikima, Ina faxar maganata wannan, ina kuma neman gafarar Allah, wa NI da KU, da kuma sauran musulmai, ku nemi gafararSa, lallai shi Mai gafara ne Mai rahama.
…

HUXUBA TA BIYU
Waxancan, wanda Ubangijinsu ya kira su da faxinSa: YA KU BAYINA yana daga sifofinsu: KWAXAITUWARSU GA SALLOLIN DARE, DA QOQARINSU CIKIN HAKA, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma bayin Mai rahama su ne waxanda ke yin tafiya a kan qasa da sauqi, kuma idan jahilai su ka yi musu magana, sai su ce: salama (a zauna lafiya) * Su ne waxanda su ke kwana ga Ubangijinsu suna masu sujada da tsayi" [Furqan: 63-64].
Kuma yana daga cikinmafificin ayyuka a cikin wannan wata (na ramadhana) mai karamci, salloli ko tsayuwan dare, saboda ya zo cikin sahihan littafi biyu, lallai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda ya tsayu a ramadhana da sallar dare cikin imani da neman lada, an gafarta abinda ya gabata na zunubansa".
Kuma haqiqa tsayuwa don sallar dare ya kasance al'adar Annabi ne –صلى الله عليه وسلم- da sahabbansa.

Kuma yana daga sifofin bayin Mai rahama: TAUSHIN GEFE, DA KAWAR DA KAI DAGA JAYAYYA DA JAHILAI, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma bayin Mai rahama su ne waxanda ke yin tafiya a kan qasa da sauqi, kuma idan jahilai su ka yi musu magana, sai su ce: salama (a zauna lafiya)" [Furqan: 63].

Kuma yana daga sifofin bayin Mai rahama: TSAKAITAWA WAJEN CIYARWA, saboda babu varnatarwa, kuma babu kwauro (ko mammaqo), Allah ta'alah yana cewa: "Kuma sune waxanda idan za su ciyar, basu varnatarwa, kuma ba su yin kwauro, kuma ciyarwarsu ta kan kasance a tsakanin wancan, tsakaitawa" [Furqan: 67].
Kuma varnatar da dukiya a cikin watan azumi da wanin wannan watan, abu ne da aka yi hani akansa, domin kashe dukiya wajen sayan waxannan ni'imomin, sa'annan a tuntsurar da su (ba tare da sun amfanar ba), lamari ne da shari'a ta yi inkarinsa, kuma ta haramta shi, Allah ta'alah yana cewa: "Kuma ku ci, kuma ku sha, kuma kada ku varnatar; lallai ne shi (Allah) baya son mavarnata" [A'araf: 31].
            Sai ku yi salati, -Ya ku bayin Allah- ga Manzon shiriya, sabodaAllah ya umurce ku da aikata haka, a cikin littafinsa; a inda yake cewa:
"Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yin salati ga wannan annabin, Yaku waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallama na aminci" [Ahzab: 56].
,,,          ,,,          ,,,

,,,          ,,,          ,,,

2017/06/01

hudubar 07 Ramadan 1438h daidai da 02 Yuni 2017M daga Dr Husain AlusSheikh Masallacin Annabi SAW











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
(صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 07/RAMADHANA/1438H
daidai da 02/YUNI/2017M




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEIKH HUSAIN BN ABDUL'AZIZ ALUS-SHEIKH





TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
TTT
Shehin Malami wato: Husain bn Abdul'aziz Alus -Sheikh –Allah ya kiyaye shi- ya yi hudubar juma'a mai taken: TTT, Wanda kuma a cikinta ya tattauna, akan

بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO

Bayan haka:
Ya ku Bayin Allah… !!
Lallai abin neman da ya fi xaukaka, kuma buqatar da ta fi girma, ita ce: BAWA YA YI GAGGAGWAR AIKATA ALKHAIRORI, YA KUMA RIBACI LOKUTAN ALKHAIRI; TA HANYAR SAMAR DA KYAWAWAN AYYUKA, "Da waxanda su ka yi rigaye. Su waxanda su ka yi rigaye * Waxannan su ne waxanda aka kusantar …" [Waqi'ah: 10-11].
Kuma a cikin watan ramadhana akwai, damammakin yin guzuri, na kyawawan ayyuka, da kusantar Allah da dangogin xa'oi, kuma ya zo cikin hadisi, cewa: "Wanda ya azumci watan ramadhana cikin imani da neman lada, an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa. Wanda kuma ya yi tsayuwar ramadhana (wato, sallar dararen watan) cikin imani da neman lada, to an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubansa" An yi ittifaqi kan ingancinsa.

Ya ku Taron musulmai … !!!
Wanda aka masa taufiqin dace, shi ne wanda ke kiyaye gavvansa, daga aikata ababen da aka hana, da kuma laifuka masu halakarwa,
Kuma lallai yana daga cikin hasara, da tavewa ko halaka, Musulmi ya yi aikin tara ko samun lada, tare da gaggawar aikata xa'oi, sai kuma ya sake gaggawa wajen warware abinda ya qulla, da rushe abinda ya gina, saboda talauci na haqiqa (a lahira), shi ne, wani ya bayar da kyawawan ayyukansa, ga waninsa, sakamakon sakaci ga lamarin haqqoqin halittun Allah, da zaluntarsu da kala-kalan nau'in zalunci, da cutar da su, da dangogin cutarwa, ko yin ta'addanci akansu da na'uka mabanbanta na ta'addanci, wanda Ubangijin halittu ya haramta, kuma annabinmu Muhammdu –صلى الله عليه وسلم- ya tsawatar,   "Shin kun san wanene fallasasshe?
Sai su ka ce: Fallasasshe a cikinmu shi ne wanda bashi da dirhami ko kaya. Ya ce: Sai Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: Lallai fallasasshe daga cikin al'ummata, shi ne wanda zai zo a ranar qiyama, da salloli, da azumi, da zakka, sai ya zo alhalin ya zagi wannan, ya yi qazafi ga wannan, ya ci dukiyar wannan, ya zubar da jinin wannan, ya doki wannan, sai a baiwa wannan daga kyawawansa, wannan daga kyawawansa, idan kyawawan nasa su ka qare, gabanin a gama biyan abinda ke kansa, sai a xauko daga zunubansu, a lafta akansa, sai a jefa shi cikin wuta" Muslim ya rawaito shi.
Nawawiy ya faxa –a inda ke sharhin wannan hadisin-: "Haqiqanin fallasasshe shi ne wanda zai halaka cikakkiyar halaka, kuma shi ne aka rasa, rashin da babu samuwa a bayansa, ta hanyar xaukar ayyukansa kyawawa ga masu binsa bashi, idan kuma kyawawan nasa su ka qare, to sai a kwaso munanan ayyukansu, a lafta masa, sai kuma a wurga shi cikin wuta, a nan ne kuma; Sai hasararsa da halakarsa da talaucinsa su gama cika".

Don haka; ka ji tsoron Allah –Ya kai musulmi-, kana mai kiyaye ranka, daga dukkan laifuka, kuma ka nisantar da ita, daga sabbuban halaka, da kuma dalilan yin hasara.

'Yan'uwana musulmai … !!!
Tsira, tana nan a cikin kiyaye gavvai, samun sa'ada kuma a cikin lazimtar xa'oi, da kiyaye su daga dukkan abinda zai gurvata su, ko kuma ya vata tasirinsu, Annabi –صلى الله عليه وسلم- ya ce: "Wanda a wurinsa akwai zaluncin da ya yi wa xan'uwansa; cikin mutunci ne, ko dukiya, to ya nemi warwarewa daga gare shi, gabanin ya zo a qiyama, a inda babu dinari ko dirhami, kawai za a xauka ne daga kyawawan ayyukansa, idan kuma babu; to sai a xauki munanan sahibinsa, sai a qara su akan munanansa, sai kuma a yi wurgi da shi cikin wuta", Bukhariy ya rawaito shi.
A cikin riwayar waninsa kuma, Ibnu-Hubairah ya ce: "Xaukar fansar qisasi, yana shiga cikin kowane kyakkyawa, har ya zama babu wani abu daga cikinsa da zai saura".
            Sai ka kiyaye –Ya kai Musulmi- daga faxawa cikin halaka, kana mai cikakken kiyayewa, dangane da haqqoqin halittu, Annabi –صلى الله عليه وسلم- kuma, yana cewa: "Lallai za a bada haqqoqi ga ma'abutansu, a ranar qiyamah, har sai an xau fansa ga akuyar da bata da qaho, daga akuya mai qaho". Muslim ya rawaito shi.
            Ma'anar hadisin shi ne, lallai Allah zai xau fansa ga wanda aka zalunta, daga wanda ya zalunce shi, kamar yadda hadisan da su ka gabata su ka bayyanar.

            Daga wannan ne kuma, (za mu ce:)
            Shi mai azumi yana cikin lokaci muhimmi; wanda a cikinsa xa'oin muminai su ke yawaita, sai ya zama wajibi, musulmi ya riqa tuna cewa, lallai haqiqanin azumi tarbiyya ne, kan samar da taqawa, "Ya ku waxanda su ka yi imani an wajabta azumi a kanku, kamar yadda aka wajabta shi ga waxanda su ka zo gabaninku, tsammaninku za ku samu taqawa" [Baqara: 183].
            Kuma cikin faxakarwar Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- tabbatattu, akwai mafi girman tsawatarwa, kuma mafi girman wa'azi, saboda Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Kuma idan ranar azumin xayanku ta zo, to kada ya yi kwarkwasa, kuma kada ya yi Shewa (ihu), idan kuma wani ya zage shi, ko ya aibanta shi, sai ya ce: Ni mai azumi ne…".

            Sai ka kiyaye kyawawan ayyukanka –Ya kai musulmi-, kuma ka kasance a kan, bada kariya ga labulan ayyukan xa'arka, kana mai bayyanar da matsanancin kwaxayi a kan hakan, kuma mafi girmansa, saboda Manzon Allah –صلى الله عليه وسلم- yana cewa: "Wanda bai bar faxin zancen qarya, ko aiki da shi ba, da kuma jahilci, to lallai Allah bashi da buqatar ya bar abincinsa da abin shansa".

,,,          ,,,          ,,,
,,,          ,,,          ,,,

HUXUBA TA BIYU
            Ya ku waxanda su ka mallaki kafafen sadarwa!!!, Ya waxanda aka jarabbe su, da rubutu a kafafen sadarwa, da na'ukansu dayawa!!!,
Ku ji tsoron Allah mabuwayi da xaukaka, kuma ku kiyayi yaxa dukkan abinda ya sava wa wannan addini da falalolinsa, ko ya ke yin suka kan tabbacin wannan addinin, ko kuma yaxa abinda zai kai ga aukawa ga bolar ababen kyama, kuma munana, Saboda ya zo cikin qa'idodin shari'a, cewa, duk wanda ya zama sababin faxawar halittu cikin savo, to lallai yana da kwatankwacin zunubinsu, Allah ta'alah yana cewa: Kuma lallai za su xauki kayan nauyinsu (na zunubi), da waxansu nauyayan zunubai, tare da kayan nauyinsu" [Ankabut: 13].
Kuma Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa: "Wanda ya sunnata mummunan sunna a cikin musulunci, yana da zunubinta, da zunubin mutumin da ya yi aiki da ita, ba tare da an tauye komai daga zunubansa ba".
Kuma Allah ya yi rahama ga Shaxibiy, a inda ke faxar maganarsa mai muhimmanci, cewa: "Madalla da mutumin da ya mutu, sai zunubansa su ka mutu tare da shi, Bone kuma ya tabbata ga wanda ya mutu, sai zunubansa su ka cigaba da wanzuwa, shekaru xari, ko shekaru xari biyu, ana masa azaba da su a cikin qabarinsa, ana kuma tambayarsa, har zuwa lokacin qarewarsu".


,,,          ,,,          ,,,

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...