2016/02/16

AIYUKAN FADADA MASALLACIN HARAMI TARE DA BAYANIN AIKIN FADADAWA SABO DA AKE ZARTARWA (توسعات المسجد الحرام، ومشروع التوسعة الجديدة)






AIYUKAN FAXAXA MASALLACIN HARAMI
TARE DA BAYANIN
AIKIN FAXAXAWA SABO DA AKE ZARTARWA
(توسعات المسجد الحرام، ومشروع التوسعة الجديدة)



AIKIN FAXAXA HARAMIN MAKKAH MAXAUKAKI
DAGA/ HADIMIN HARAMI BIYU MAXAUKAKA;
SARKI ABDULLAHI XAN ABDUL'AZIZ ALU-SA'UD
(توسعة خادم الحرمين الشريفين الملك عبد الله بن عبد العزيز آل سعود للحرم المكي الشريف)




TANADAR
 OFISHIN SHA'ANONIN MASALLACI MAI ALFARMA DA MASALLACIN ANNABI


TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
Allah ya halitta Mutum domin ya raya wannan duniyar, ya kuma kevance wani kwari mai girma dakasancewa wurin da ya fi tsarki; wanda shine: MAKKAH.
Kuma a cikin garin Makkah akwai XAKI NA FARKO da aka gina a bayan qasa, don bautar Allah Shi kaxai.
Matakai dayawa Xakin Allah mai alfarma ya bi ta kansu, har zuwa, ganin Hadimin Masallatan Harami Guda Biyu; (Wato: Sarki Abdullahi) don shima –a tarihance- ya dangwala hannunsa (wajen yin hidimar qara faxaxa Masallacin), kuma don ya bar wata alama da zata dawwama, wacce 'ya'ya da jikoki za su riqa tuna shi da ita, suna kuma addu'ar sakayya da lada a gare shi (su riqa, shi masa albarka).

Cikakkiyar surar da zata nuna muhimmacin wannan lokacin zata bayyana ne idan aka xauko bayanin; daga farkon aikin faxaxawa da aka yi wa MASALLACI MAI ALFARMA, a zamanin khalifancin Alfaruq; khalifa Umar xan Alkhaxxab (رضي الله عنه);

a lokacin da ya iyakance filin masallacin harami ta hanyar gina katanga wacce tsayinta shine: qafa shida (6, wato: qama xaya), a shekara ta goma sha bakwai (17) daga hijira.  

   Bayan kaman shekaru takwas (8) kuma, Sai Khalifa Usman xan Affan (رضي الله عنه) ya qirqiro wani qarin na daban, wanda ya qara wax akin Allah kwar-jini, da xaukaka.

   Sa'an nan Sai gwamna Abdullahi xan Az-zubair (رضي الله عنه) ya qara faxaxa wurin sallah da xawafi ta vangaren gabas.

   Haka kuma khalifan daular Abbasiyya; mai suna: Abu-Ja'afar Almansur shima ya qara wani fili wa masallacin ta vangaren arewa da yamma.

   Haka kuma, Xansa; Muhammadu Almahdiy shima ya bi mahaifin, ta hanyar qara wani filin ta kowani vangare (gabas da yamma, kudu da arewa).

   Sa'an na sai khalifa mai suna: Mu'utadhid shima ya yi wani qarin ta arewa.

  Amma shi kuma sarki Muqtadir, a shekara ta 306 na hijira shi kuma ya yi qarinsa ne ta yamma.     

Kuma da haka ne, faxin masallacin Makkah, da kuma filin xawafi; wanda daxaxxun runfunan da aka yi a zamanin khalifancin daular Abbasiyya suke kewaye da shi = suka tabbatu akan wannan yanayi har tsawon shekaru 1069, Wanda a cikinsu babu wani qarin gini da aka yi a masallacin haramin Makkah,  Saidai aiyukan gyare-gyare da kwaskwarima (a lokuta mabanbanta), da kuma sanya qubbobi akan waxannan rumfunan, a lokaci, da kuma umurnin sarkin daular Usmaniyya; Salim Na-biyu.

A ZAMANIN SARAUTAR SAUDIYYA, Sai (Wanda muke neman gafarar Allah a gare shi) wanda kuma shine ya assasa daular saudiyya; wato: Sarki Abdul'aziz, Alu-Sa'ud = ya dasa harsashen fara aiyukan qarin farko na daular Saudiyya;  kuma shine farkon qarin da ya haxe wurin sa'ayi (na Safa da Marwa); ya kuma jona shi da masallaci mai alfarma, kamar yadda aka qara hawan sama (na beni) wanda ya ninka faxin masallacin gabaxaya, tare kuma da samar da masallacin cikin qasa. Kuma a nan ne, aka qara wurin yin xawafi, kamar yadda ya ke a yanzu.
Sa'an nan sai sarki Sa'ud xan Abdul'aziz, da sarki Faisal (Allah ya yi rahama a gare su) suka qarisa abinda babansu wanda ya assasa daular saudiya ya farar.

A lokacin qarin da daular saudiya na biyu kuma ga haramin Makkah maxaukaki a zamanin mulkin mai hidimar harami guda maxaukaka; wato sarki Fahad xan Abdul'aziz (Allah yayi rahama a gare shi) sai aka yi qarin wani wuri daga vangaren yanma, wanda aka haxa shi da harami, sannan aka daidaita su har ta fiskar tsari ko yanayin gini.
Kamar yadda aka shirya saman rufin masallacin, ga masu sallah, aka kuma faxaxa harabar da ta kewaye masallacin domin haramin Makkah maxaukaki ya xauki masu sallah kamar Mutane dubu xari shida (600, 000) da dukkan qare-qaren da aka yi masa.  

Saidai a shekarun qarshe-qarshe an samu qaruwar da ba a tava samun irinta ba; na adadin mahajjata da masu umrah da ziyara, saboda ci-gaban da aka samu da bunqasa a hanyoyin tafiye-tafiye, da kuma qaruwar yawan musulmai wannan ya sa masallacin ya wayi gari cikin matsananciyar buqatar neman qari, Sai qoqarin warware matsalar da samar mata da mafita ya zama babban abinda mai hidimar harami biyu maxaukaka ya himmatu da shi (Sarki Abdullahi), Sai kuma ya bada aikin faxaxa wurin sa'ayi (na Safah da Marwah); wanda aka gama aikinsa a shekarar da ta wuce, ta yadda faxinsa ya ninku har zuwa sau huxu.  Sai kuma aka qara wani hawan, a sama, da kuma wani a cikin qasa, tare kuma da ninka filin sa'ayi; daga mita 20 zuwa mita 40, domin sabon wurin Safah da Marwah ya ishi qarin masallata kamar 70000.  Sai kuma aikin qara nazari mai zurfi na yadda za a warware matsalar cunkoson ya ci-gaba, wanda ya haifar da bada umurnin bunqasa masallacin; wanda a tarihi ba a tava yin irinsa ba wajen girma, ta yadda idan an gama ta, a dunqule; filin masallacin harami, tare da wannan qarin zai wayi gari ya kai ninki ukun girman filin a yanzu, don sabon qarin shi kaxai xinsa ya iya xaukar masallata kimanin Mutane miliyan xaya (1000000), shi kuma masallacin gabaxaya ya iya xaukar masallata fiye da Mutane miliyan xaya da dubu xari shida (1,600,000), ba a kwanakin cunkoso ba.  Amma a lokacin hajji da sauran kwanakin tsananin cunkosu nan kuma sabon qarin zai xauki adadin mahajjata da masu umrah wanda yafi haka. Wannan kuma sharar fage ne ga wassu qare-qaren da suke tafe (nan gaba), don su zama hidima wa garin Makkatul makarramah da kuma baqin (Allah) mai rahama.    
Kuma shi wannan qarin da yafi na bayansa girma, zai kasance ne ta vangaren arewacin masallacin harami, kuma wannan aikin zai qunshi: abubuwa guda shida manya; (1) Ginin sabon qari. (2) Filayen wajen masallaci (harabobi). (3) Gadodi (4) Ginin sama (harabar sama, mai gangarowa), (5) Wuraren shigewan masu tafiyar qafa (6) da kuma nau'ukan gine-gine don hidimomi dayawa mabanbanta, waxanda sun haxa da:  Cibiyoyin lafiya, da ofishin 'yan kwana-kwana, da asibiti, da cibiyar tashar sanyaya iska (A C), da kuma samar ko bada wutan lantarki (ihtiyaxi; kar-ta-kwana, na wucin gadi). Waxannan vangarori (guda shida) sashinsu yana qarfafa ko kammala sashi ne, don samar da masallaci na zamani wanda yake da gamewa, da kuma yin amfani da mafi kyan kayayyakin zamani da takanolaji,   don kawo aminci da hutu ga mahajjata da masu umrah, da kuma isowarsu cikin sauri da sauqi zuwa masallaci mai alfarma.

Tunanin kama wannan aikin wanda ya fara da rushe ko shishirya vangaren da ake kiransa: Almanxiqatu As-shamiyyah (da ke arewa) na aikin qarin gini wa masallacin haramin Makkah ya xauki shakali ne irin na haske, wanda ya fara daga: cibiyar Ka'abah  ta dukkan vangarorin gabaxaya, domin fiskantar da xaukacin masallata gabaxaya zuwa ga vangaren alqiblah.
Kuma wannan wurin da ake aikin ginin qara shi a jikin masallaci ta qunshi babbar qofa, mai suna: QOFAR SARKI ABDULLAHI, wanda a saman qofar akwai hasumiya manya-manya guda biyu, domin hasumiyoyin harami su wayi gari sun zama guda goma sha xaya (11).
Kuma saboda sauqaqe kai-komon masallata, ta hanyar da ta fi tsari, da yawan aminci, da kuma saboda kai-komon nasu cikin jagoranci, da taqaita cunkoso Sai aka qara yawan gadodi; waxanda za su qulle  tsakanin harabar da take sama ta arewa da kuma ginin harami na yanzu, wanda kuma su gadodin za su tsaga; kana su bi ta cikin ginin sabon qari gabaxayansa. Tare da shirya harabar qasa da take tsakanin sabon masallacin da aka qara da kuma harabar sama da take a can baya, wanda za ta xauki sahu masu yawa na qarin masallata.  

Wannan tsararren wurin da aka gina ta vangaren arewa, a cikin harabarsa manya-manyan lemomin da ake buxe su da na'urori suna qawata shi,  Wannan kuma don su bada kariya ga masallata daga zafin rana, da kuma ruwan sama.

A qarqashin harabobi kuma an samar da banxakai da wuraren alwala, da kuma wassu wurare da ofisoshi masu gamammen amfani.

A wajen samar da harabobin sama da suke vangaren arewa, ta can baya kuma, an lura da matakai guda shida da suke bin juna, waxanda suke dacewa da yanayi ko xabi'ar duwatsun da suka kewaye wurin, wanda kuma za a yi amfani da rufinsu a matsayin qarin wuraren da za a riqa yin sallah, a wani yanayi mai qayatarwa.
Kuma, a qasan waxannan harabobin sama: An samar da banxakai, da wuraren alwala, qari akan xakunan kunne-kunne da ofisoshi, da kuma cibiyoyin lafiya.
Kuma hanyar da ta yi zobe (ring road) wa masallacin harami ta farko, tana kutsawa ta cikin ginin harabar baya, wacce take sama ta arewa, daga gabas zuwa yamma. Tare da qulluwa da tashoshin motocin… da aka tanada don kai-komo, domin sauqaqe lamarin shigi da fici zuwa ginin sabon masallaci. Qari akan hanyoyin shigewan masu tafiyan qafa; waxanda suke faraway daga harabar qasa na masallaci, suke kuma tafiya vangaren arewacin masallaci mai alfarma; inda aka tanadi asibiti da gine-ginen 'yan sandan kar-ta-kwana, da jami'an tsaro, a ta wannan vangaren.
Haka nan kuma, ginanniyar hanyar cikin qasa (NAFAQU KHIDIMAAT) itama take kutsawa ta cikin ginin harabar baya da take sama, don ta haxe babbar tashar motoci da kuma masallacin harami.
Daga Qofar Mai Hidimar Harami Biyu Maxaukaka (sarki Abdullahi) muke shiga ginin sabon masallaci, domin mu samu mashiga maxaukaki mai girma (الممر الشرفي) wanda qubba mai girma da take buxewa tana qawata shi.
A geffan wannan qubbar kuma guda biyu akwai wani hol (قاعة) don yin sallah, wanda aka yi shi akan matakai huxu waxanda tsakiyansu ya sha banban, a hawa na xaya da na biyu, waxanda kuma suka kasu zuwa manya-manyan hol da qanana, tsakaninsu kuma akwai filaye ta ciki, a tsawon wannan ginin, wanda kuma aka yi aikin rufin kansu da rufi na gilashi mai buxewa, da kuma qubbobi guda huxu waxanda basa motsawa.
            Wannan shine zamanin wannan sarki (sarki Abdullahi) Mai Hidimar Masallatan Harami Biyu Maxaukaka, wanda yak e cika abinda ya alqawarta wa al'ummarsa na cika abinda khalifa shiryayye; Umar xan Alkhaxxabi (رضي الله عنه) ya fara (Na aiki a masallacn harami).
            Kuma abin mamaki ba ne, a wurinku irin wannan kyautayin da masarautar larabawa ta Saudiya take rayuwa a cikinsa, a irin wannan mataki da masallacin harami yake rayuwa a cikinsa, wanda tarihinsa ya sha banban.

            Ya Mai Hidimar Masallatan Harami Guda Biyu, da irin umurnin da kuka bayar ne maxaukaki mai karamci, Wannan aiki na-azo a gani yake wanda kuka yi umurnin a kammala aikinsa, a cikin shekaru biyu masu zuwa, da izinin Allah maxaukaki da sannu aikin ganin an qare shi zai ci gaba tuquru, dare da rana.


"Ya ku waxanda suka yi imani idan kuka taimaki Allah sai ya taimake ku, kuma ya tabbatar da dugaduganku" [Muhammadu: 7].

2016/02/14

LADDUBAN MASALLACIN ANNABI (من آداب المسجد النبوي )







LADDUBAN MASALLACIN ANNABI
(مِن آداب المسجد النبوي)

TANADAR
Ofishin FAXAKARWA DA NUSARWA
Da ke qarqashin
Ofishin WAKILCIN GAMAMMIYAR MA'AIKATA,
DAKE WAKILTAR SHA'ANONIN MASALLACIN ANNABI (s.a.w)




FASSARAR
Abubakar Hamza



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. Salati da sallama su qara tabbata ga annabinmu Muhammadu, da kuma iyalansa da sahabbansa gabaxaya.
Bayan haka:

Xan'uwana Musulmi!
Ka gode wa Allah Ubangijinka; wanda ya kawo ka Masallacin AnnabinSa (صلى الله عليه وسلم), wanda kuma Allah ya fifita shi, sannan ya sanya yin sallah a cikinsa ya zama yafi salloli dubu a wani masallacin wanda ba shi ba; in banda Masallaci mai alfarma (da ke garin Makkah), kuma ya sanya wanda ya zo wannan masallacin don koyan wani alheri ko ya koyar, a matsayin mai jihadi fiysabili Allah.

Sai ka qara kwaxayi –Ya kai wanda nake xan'uwantaka da shi don Allah- wajen yin sallah a masallacin Annabi, da neman fahimtar addini, ta hanyar halartar halqoqin ilimi, domin ka bauta wa Allah akan basira, sannan ka riqa yin tambayoyi kan dukkan abinda ka jahilta, Allah ta'alah yana cewa:
{فَاسْأَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِنْ كُنْتُمْ لا تَعْلَمُونَ} [سورة النحل: 43].
"Kuma ku tambayi ma'abuta ilimi, idan kuka kasance ba ku da sani" [Nahli: 43].

          Ka sani, Wannan Masallacin yana da LADDUBAN da ake kula da su, da wassu HALAYYA; waxanda ake aiki da su.
Anan, Za mu tunatar da kai, sashinsu:

1) Musulmi namiji da musulma mace su zo (Masallacin) cikin nitsuwa da ladabi, da kuma tsarki, da kyakkyawan shiga, da qamshi mai daxi, tare da nisantar nau'ukan wari ababen qi, kamar taba, da albasa, da waninsu, wannan kuma saboda Mala'iku suna cutuwa da abinda 'ya'yan-Adam suke cutuwa da shi.
2) Idan  za ka shiga Masallacin; Ka gabatar da shigar da qafarta ta hagu, Sai kuma ka ce: "BISMILLAHI, WASSALATU WASSALAMU ALA RASULILLAH, A'UZU BILLAHIL AZIM, WA BI WAJHIHIL KARIM, WA SULXANIHIL QADIM, MINASH SHAIXANIR RAJIM, ALLAHUMMA IFTAH LIY ABWABA RAHMATIKA", Daga nan sai ka yi sallah raka'oi biyu, (mai suna) gaisuwar Masallaci. Sai kuma ka yi qoqari wajen ambaton Allah, da ibada, da karatun alqur'ani.
3) Idan ka zo yin sallama wa Annabi (صلى الله عليه وسلم) Sai ka tsaya ta fiskar qabarin, cikin ladabi, da qanqan da sauti, Sannan ka ce: "ASSALAMU ALAIKA WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU, ASSH'HADU ANNAKA BALLAGTA ARRISALAH, WA ADDAITA AL'AMANAH, WA NASAHTA AL'UMMAH, WA JAHADTA FIY ALLAHI HAQQA JIHADIH, FA JAZAKA ALLAHU ANNIY WA ANIL MUSLIMINA KHAIRAL JAZA'I".
Sa'annan ya yi sallama wa Abubakar da Umar, ta hanyar ambaton sunayensu (رضي الله عنهما).
Sa'an nan ka tafi duk wurin da ka so a cikin wannan masallacin, ka kuma roqi dukkan abinda ka so, daga cikin ababen roqa waxanda suka halatta a shari'a.
Kuma  a cikin zuciyarka ka sanya aqidar cewa, lallai janyo wani amfani da tunkuxe cuta basa kasancewa face daga Allah maxaukaki; Sai ka yi ta neman buqatunka daga wurinsa shi kaxai, na duniya da lahira, ba tare da sanya wani tsani ba, kamar yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"إِذَا سَأَلْتَ فَاسْأَلْ اللَّهَ وَإِذَا اسْتَعَنْتَ فَاسْتَعِنْ بِاللَّه".
Ma'ana: "Kuma idan za ka yi roqo ka roqi Allah, haka idan za ka nemi taimako ka nema a wurin Allah".
Kuma ka da ka shafi, ko ka sumbaci katanga ko waninsa.
Kuma ka da ka yi sallama wa qabarin alhalin kana cikin yanayi irin na mai sallah.
Kuma ka da ka yi sallaman alhalin kana nesa da qabarin; saboda hakan savanin abinda magabatan kwarai suka kasance akansa ne (رضي الله عنهم).
4) Ka ribaci samuwarka a wannan masallacin; Idan ka yi sallar nafila sai ka zauna a wurin zamanka, kana TASBIHI wa Allah, kana AMBATONSA, kuma ka yawaita karatun alqur'ani.
Kuma ka zavar wa kanka wurin da ya yi nesa da cunkoso; tsoron ka da ka yi tarayya cikin samar da cunkoson da zai cutar da 'yan'uwanka Musulmai.
5) Yi kwaxayin tottoshe kafa a cikin safu, tare da yin qoqari wajen samun safun farko-farko; domin falalarsu, idan hakan ya yiwu ba tare da haifar da cunkoso ba.
Kuma ka nisanci zama a wuraren shigewa, da mashigan masallaci; don kada ka cutar da 'yan'uwanka Musulmai, ko ka quntata musu.
Kuma kada ka yi gaba da liman, a lokacin da aiwatar da sallah ya kama ka a harabar masallaci (ta gaba).
6) Ka girmama littafin Allah maxaukaki; ka da ka yi rubutu a jikinsa, kada kuma ka riqa wasa da fefofinsa, Sannan ka da ka sanya takalminka a gefensa.
7) Ka kiyaye tsaftar Masallacin, da kuma harabarsa, daga dukkan abinda zai cutar, ko kuma kaki.
Kuma ka karantar da 'ya'yanka ladduban masallaci, ka kuma kiyaye su daga yin wargi da wasa, ko xaxxaga sauti (da shewa).
8) Yi qoqarin rage cunkoso, a lokacin fita daga masallaci; ta hanyar jinkirta fitanka na wani lokaci xan kaxan, har zuwa lokacin da cunkoson zai ragu.
9) Kuma ka sani cewa, lallai masallaci ba wurin barci ba ne, ko yin roqo, ko cikiyar kayayyakin da suka vace.
10)                  Ka da ka yi alwala da ruwan da aka tanada don sha, kuma ka da ka sanya shunfuxan masallaci su zama ababen tada kai (filo), ko mayafan rufuwa; saboda an ajiye su ne a matsayin WAQAFAN da za a riqa sallah a kansu, ba don masallata su riqe su a matsayin shumfuxai ba.
Haka kuma, ka da ka sanya katakon xora qur'anai su zama a qarqashin kanka don tada shi (filo), saboda an ajiye su ne a matsayin WAQAFI don xora Qur'anai kawai.

Daga qarshe kuma; Muna tunatar da kai cewa, lallai taimakawarka ga ma'aikatan da suke masallacin Annabi (s.a.w), da sanar da su, dukkanin abinda yake wurinka na shawarwari, ko gyare-gyare zai taimaka wajen bunqasa irin hidimar da ake aiwatar da ita ga masu ziyarar wannan wuri mai tsarki; Don haka; kada ka yi taraddadi wajen qaddamar da duk abinda ke tare da kai na hakan.

ALLAH YA KARVA MAKA, KUMA YA NINNIKA LADANKA.

Wassalamu alaikum wa rahmatu Allahi wa barakatuhu.

Tanadar: Ofishin FAXAKARWA DA NUSARWA
Da ke qarqashin
Ofishin WAKILCIN GAMAMMIYAR MA'AIKATA,

DAKE WAKILTAR SHA'ANONIN MASALLACIN ANNABI (s.a.w).

2016/02/09

FADAKARWA DA NASIHOHI GA MAZIYARTA MASALLACIN ANNABI MATA (توجيهاتونصائح لزائرات المسجد النبوي الشريف)







FAXAKARWA DA NASIHOHI
GA
MAZIYARTA MASALLACIN ANNABI MATA
(توجيهات ونصائح لزائرات المسجد النبوي)


TANADAR
Ofishin Faxakar Da Mata Da Nusar da Su, 1434h




FASSARAR
Abubakar Hamza



BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.
Salati da sallama su qara tabbata ga shugaban manzanni, da kuma iyalanSa da sahabbanSa gabaxaya.
Ya wacce ta ziyarci masallacin Annabi !
Ya wanda Allah ya yi baiwa a gare ki da ziyartar masallacin Annabi (صلى الله عليه وسلم) domin yin salla, da zikiri, da ibada.
Zuwa gare ki nake fiskantar da waxannan wasiyyoyin da faxakarwa:
Muna faxakar da ke, kuma muna cewa:
Ke (a yau), kina masallacin Annabi ne (صلى الله عليه وسلم), Masallacin da zukatan muminai suke begen zuwansa, kuma rayukansu suke cike da begen gamuwa da shi.
Tayin murnar samun damar sallah da kika yi a cikinsa; saboda yin sallah a cikin wannan masallacin yana daidai da yin sallah dubu (1000) a waninsa, kamar yadda ya zo daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) cewa:
((صلاةٌ في مسجدي هذا خيرٌ من ألف صلاةٍ فيما سواه، إلا المسجدَ الحرامَ)).
Ma'ana: ''Sallah a masallacina wannan yafi salloli dubu alheri; a waninsa in banda masallaci mai alfarma", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
            Taya ki murnar samuwarki a wannan bagiren mai albarka; bagiren da imani ke fakewa a cikinsa, kamar yadda macijiya ke fakewa a cikin raminta, Imamul Albukhariy –Allah yayi rahama a gare shi- ya fitar da hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه) cewa lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم), yace:
((إنَّ الإيمان ليَأْرزُ إلى المدينة كما تأرز الحَيَّةُ إلى جُحْرها)).
"Lallai imani zai tattara a garin Madina kamar yadda macijiya take tattara a cikin raminta".
            Taya ki murnar halartar halqoqin ilimi; waxanda suke cikin wannan masallaci (mai albarka); domin ki samu ladan Mai yin jihadi fiysabil Allah, kamar yadda ya zo cikin hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه), ya ce: Na ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:  
((مَن جاء مسجدي هذا لم يأتِهِ إلا لخيرٍ يتعلَّمُه أو يُعلِّمُه، فهو بمنزلة المجاهدِ في سبيلِ الله، ومَن جاء لغير ذلك فهو بمنزلة الرجل يَنظرُ إلى مَتاعِ غيره)).
Ma'ana: "Wanda ya zo masallacina wannan; bai zo masa ba sai don wani alherin da zai koye shi, ko ya koyar da shi, to yana da matsayin mai jihadi fiysabil Allah. Wanda kuma ya zo ba da wannan manufar ba to kamar mutumin da yake kallon kayan waninsa ne". Ibnu-majah ya ruwaito shi. Kuma Albaniy ya inganta shi.
            Taya ki murnar samun damar yin sallah a raudha, wanda Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yake faxa a kanta:
((ما بين بيتي ومِنبري روضةٌ من رياضِ الجنّة)).
Ma'ana: ''Tsakanin gidana da minbarina dausayi ne daga cikin dausayin aljanna'', Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
             Taya ki murnar jiran sallah, bayan sallah a wannan masallaci (mai albarka), domin ki samu ladan mutumin da yake aikin ribaxi fiysabil Allah, kamar yadda Imamul Muslim –Allah yayi rahama a gare shi- ya fitar da hadisin Abu-hurairah (رضي الله عنه) lallaiManzon Allah (صلى الله عليه وسلم), ya ce:
«ألا أدلُّكم على ما يمحو الله به الخطايا، ويرفع به الدرجات؟ قالوا: بلى يا رسول الله. قال: إسباغ الوضوء على المكاره، وكثرة الخُطى إلى المساجد، وانتظار الصلاة بعد الصلاة، فذلكم الرباط».
"Shin ba zan nuna muku abin da Allah ke share kura-kurai da shi ba, kuma ya xaukaka darajoji da shi? Sai suka ce: Na'am, Ya ma'aikin Allah! Sai ya ce: Cika alwala, a lokacin qi (sanyi), da yawan taku izuwa masallatai, da kuma jiran sallah bayan sallah; Wannan kuma kamar yin ribaxi ne".
          Taya ki murnar samun sallar gawa (jana'iza); saboda a cikin yin ta akwai lada mai girma, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
((مَن شَهِد الجنازة حتى يُصلَّى عليها فله قيراطٌ، ومَن شهد حتى تُدفن كان له قيراطان. قيل: وما القيراطان؟ قال: مثل الجبلين العظيمين)).
"Duk wanda ya halarci sallar janaza har aka yi mata sallah, to yana da qiyraxi guda xaya, Kuma duk wanda ya halarce ta har zuwa a bunne ta zai samu qiyraxi guda biyu. Sai aka ce, menene qiyraxi biyu? Sai ya ce: Misalin duwatsu guda biyu masu girma ", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.

            YA KE WANDA TA ZIYARCI MASALLACIN ANNABI Yi qoqarin, zuwan da kika yi don ziyara ya zame miki dama ta yin hisabi wa kanki, da samun qarin imani, da yawaita aiyyukan xa'a.
   Kuma ki yi kwaxayin aikata kyakkyawan aiki, da neman lada, da yin ikhlasi ga Allah ta'alah cikin dukkan aiyukanki.
   Ki kasance Mai girmama wuraren bauta wa Allah na harami guda biyu; saboda taqawar Allah itace take sanya a riqa  girmama waxannan wuraren, kuma duk zuciyar da ta ke girmama Allah, to zata bada dalili ne akan ita mai taqawar Allah ne ta hanyar girmama wuraren da Allah ya nemi a girmama su, Allah ta'alah yana cewa:
{ذَلِكَ، وَمَنْ يُعَظِّمْ شَعَائِرَ اللَّهِ فَإِنَّهَا مِنْ تَقْوَى الْقُلُوبِ} [الحج 32].
"Saboda, Duk wanda ya girmama wuraren bautan Allah, to lallai hakan yana daga cikin taqawar zukata" [Surat Alhajj: 32].
   Kuma kada ki riqa xaga sauti a cikin masallacin, ta yanayin da za ki takura wa sauran mutane, kuma ahir xinki da yin tafi, da guxa a cikin masallaci, saboda yin haka mummunan aiki ne abun kyama.
    Abu ne mai kyau, ki girmama wannan masallacin; ta hanyar rufe wayar hannu, a lokacin sallah; don kada ki takura wa 'yan'uwanki masallata da qarar waya; sai ki tafiyar musu da kushu'insu.
   Kuma abu ne mai kyau, ki girmama wannan masallacin da rashin shagaltuwa da xauke-xauken hotunan sasaninsa da vangarorinsa; saboda ba ki yi dogon tafiya kika zo wannan garin ba, sai don ki samu lada mai yawa, ki kuma amfana da alkhairi mai yawa.
   Kuma abu ne mai kyau, ki girmama masallacin; ta hanyar kiyaye tsaftarsa; wannan kuma zai tabbatu ta hanyar nisantar yin rubutu akan katangun masallacin da abubuwan da ake sanyawa don hana shigewa. Kuma kada ki yi amfani da ruwan da aka tanada don a riqa sha; wajen yin alwalanki, a cikin wannan masallacin, saboda aikata hakan zai tauye ko rage ruwan da aka tanadar ga masu ziyara don sha, tare da abinda zai janyo na cutar da mutumin da ya bi ta kansa; alhalin kuma banxakai da kuma wuraren da aka tanada don yin alwala suna nan, a kusa, kuma suna xauke da dukkan abinda zaki iya buqatarsa.
   Kuma abu ne mai kyau, ki girmama masallacin a yayin tafiyanku zuwa ga Raudha; ta hanyar tafiya cikin nitsuwa da kwanciyar hankali, kuma ki kasance cikin rufi da cikakken yanayi na sutura.
    Kuma abu ne mai kyau, ki koyar da xanki LADDUBAN MASALLACI,             kina mai shuka son masallaci da girmama alamomin da ake yin bautar Allah a wurinsu, a cikin zuciyarsa.
Sannan ki sani cewa, lallai wurin karatun da aka tanada wa yara (laburarin yara) ya himmatu wajen karantar da yara ladduban da suke da alaqa da masallatai da wassunsu, sai ki yi qoqarin xanki ya samu rabonsa na ziyartar wannan laburaren.

            Sai kuma ki yi qoqari wajen cike lokutanki a wannan masallacin da yin tilawar littafin Allah (Alqur'ani), da ambatonsa maxaukakin sarki, da halartar halqoqin ilimi. Kuma ki yi guzuri, ki amfana da littatafan da aka ajiye wa masu ziyara a laburaren da suka kevanci Su, da kuma muhadarorin da aka yi rakodin, daga ofishin xaukan karatu cikin sauti, tare da kuma amfana da littatafan da ake bayar da su kyauta ga masu ziyara.
            Kuma ki yi qoqari, wajen daidaita sahun mata masu sallah; saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
((سَوُّوا صفوفكم؛ فإنَّ تسوية الصفوف مِن إقامة الصلاة))
Ma'ana: "Ku daidaita sahu; saboda daidaita sahu yana daga tsayuwar sallah", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma hadisi   ya zo daga Jabir xan Samurah (رضي الله عنه) ya ce:
«أَلَا تَصُفُّونَ كَمَا تَصُفُّ الْمَلَائِكَةُ عِنْدَ رَبِّهَا؟ فَقلنا: يَا رَسُولَ اللهِ! وَكَيْفَ تَصُفُّ الْمَلَائِكَةُ عِنْدَ رَبّها؟ قَالَ: يُتِمُّونَ الصّفَّ الْأُوَلَ، وَيَتَرَاصُّونَ فِي الصَّفِّ».
Ma'ana: "Shin ba za kuna yin sahu kamar yadda Mala'iku ke yin sahu a wajen Ubangijinsu ba? Sai muka ce: Ya ma'aikin Allah! Ta yaya Mala'iku ke yin sahu a wajen Ubangijinsu? Sai ya ce: suna ciccika sahun farko sai wanda ke biye da shi, kuma suna hadewa; sashinsu zuwa sashi a cikin sahu", Muslim ne ya ruwaito shi.

            Kuma abu ne mai kyan gaske, ki zama babbar misali da ke aiki da musulunci wajen kyautata mu'amalantar tsare-tsaren da aka sanya ga mata masu ziyartar masallacin Annabi; waxanda ba don komai aka sanya su ba sai don kowa ta yi aikin ziyararta cikin qoshin lafiya, tun daga lokacin shigowarki ta qofofin masallacin, har zuwa fitarki daga wannan masallacin.

            Kuma abu ne mai kyan gaske, ki siffanta da halaye masu kyau, da ladduban musulunci. Kuma ki taimaki 'yan'uwanki mata masu ziyara, a lokacin cunkoso. Sai kuma ki ji, kana ki bi, faxakarwar masu nusantarwa; waxanda suke aikin faxakarwa zuwa ga abinda alkhairi ya ke a cikinsa.

             Ya wacce muke fatan kariyar Allah a gare ta ! Tafiyarki zuwa ga Raudha ya zama da tsanaki da nitsuwa, ba tare da ke kin wahala ba, ko kuma sauran masu ziyara sun wahala ba. Kuma ki sani, lallai tafiya raudha, da yin sallah a cikinsa alheri ne da lada, in sha Allah. Saidai kuma ba wajibi ba ne, kuma bashi da alaqa da umrarki da hajjinki, don haka kada ki tsananta wa kanki, wajen shiga wurin da ya yi cunkoso.

Ya wacce muke fatan kariyar Allah a gare ta ! Lallai addinin musulunci addini ne cikakke, da ya game dukkan maslahohinmu na duniya da lahira, kuma ya zo da alkhairori ga musulmai; mazansu da matansu. Kuma lallai ya bada muhimmanci ga mace, ya kuma sanya ta a wurin karramawa da girmamawa; matuqar ta yi riqo da shiriyarsa, ta kuma yi ado da siffantuwa da falalolinsa.
Yana kuma daga cikin haka: Lallai musulunci ya mata izinin halartar masallatai, domin ta yi tarayya da mutane cikin alkhairi, da yin sallar jam'i, da halartar majalisosin ambaton Allah (zikiri); cikin wassu dokoki da qa'idodi waxanda za su nisantar da ita daga fitina, su kuma kiyaye mata mutuncinta. Allah ta'alah yana cewa:
{يا أيها النبي قل لأزواجك وبناتك ونساء المؤمنين يدنين عليهن من جلابيبهن ذلك أدنى أن يعرفن فلا يؤذين وكان الله غفورا رحيما} [الأحزاب 59].
"Ya kai wannan Annabin! Ka gaya wa matanka da 'ya'yanka mata, da matan muminai su kusantar da jilbabinsu qasa, wannan shi yafi kusa da a sansu ba za a cutar da su ba, Kuma Allah ya kasance Mai gafara Mai rahama" [Ahzab: 59].
Ya zo daga Ummu-Salmah (رضي الله عنها) ta ce:
((Yayin da ayar
{يا أيها النبي قل لأزواجك وبناتك ونساء المؤمنين يدنين عليهن من جلابيبهن}.
Ta sauka (wato, ayar umurnin matan muminai da sanya hijabi), Tace: Sai matan Al'ansaar, kai ka ce akan kayukansu akwai hankaku, na daga tufafi)), Abu-dawud ya ruwaito shi, kuma Albaniy ya inganta shi.

            Ya budurwar da take rayuwa cikin musulunci! Ki sani! Lallai shi hijabi yana kare mace daga idanun mutanen banza.
Kuma lallai waxanda suka xanxani xacin bayyanar da ado da ballagaza, suka kuma quna da wutar qazantar cakuxuwar maza da mata sun tabbatar da hakan.
Kuma ki yi kwaxayin nesantar yin ado da sanya turare a lokacin fitanki daga gidanki; Ya zo daga Zainab matar Abdullahi xan Mas'ud (رضي الله عنه) ta ce: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya gaya mana:
«إِذَا شَهِدَتْ إِحْدَاكُنَّ الْمَسْجِدَ فَلاَ تَمَسَّ طِيبًا».
"Idan xayanku za ta halarci masallaci to kada ta shafa turare", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma ki yi kwaxayin nisantar cakuxuwa da maza akan hanya; saboda ya zo daga Hamza xan Abiy-Usaidu Al'ansaariy, daga Babansa (رضي الله عنه), lallai shi ya ji Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) alhalin yana fita daga masallaci, sai Maza suka cakuxa da Mata, a hanya, Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
«اسْتَأْخِرْنَ؛ فَإِنَّهُ لَيْسَ لَكُنَّ أَنْ تَحْقُقْنَ الطَّرِيقَ، عَلَيْكُنَّ بِحَافَاتِ الطَّرِيقِ». فَكَانَتِ الْمَرْأَةُ تَلْتَصِقُ بِالْجِدَارِ، حَتَّى إِنَّ ثَوْبَهَا لَيَتَعَلَّقُ بِالْجِدَارِ مِنْ لُصُوقِهَا بِهِ.
Ma'ana: "Mata Ku koma qarshe; saboda ba haqqinku ba ne ku kasance a tsakiyar hanya, Ina horonku da bin geffan hanya", Daga nan Mace sai ta kasance tana mannewa da katanga, har ya zama tufafinta yana maqalewa da katanga; saboda yadda ta ke mannewa da shi . Abu-dawud ya ruwaito shi, kuma Albaniy ya ce: hadisi ne hasan.

            Me ya fi kyau, kuma me yafi xaukaka, fiye da ki kasance abar koyi ga wassunki, wajen aiki da ladduban shari'a, waxanda suka zo a cikin littafin Allah mabuwayi da xaukaka, da sunnar ManzonSa (صلى الله عليه وسلم).

            Muna roqon Allah, ya karva miki aiyukanki na kwarai, ya kuma datar da ke zuwa ga dukkan alkhairi; wanda ma'auninki zai nauyaya da su; don ki kasance cikin rayuwa yardaddiya; a ranar tashin qiyamah; ranar da mutane za su tashi zuwa ga Ubangijin talikai.
30/04/1437h
Wanda ya yi daidai da
09/fabarairu/2016m

A Madinar Manzon Allah (SAW)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...