2016/02/02

BIDIYO FILM DAKE BAYANIN AIYUKAN HADIMIN MASALLATAN HARAMI BIYU (SARKI FAHAD) NA KARIN MASALLACIN ANNABI MADAUKAKI






BIDIYO FILM; DAKE BAYANIN AIYUKAN "HADIMIN MASALLATAN HARAMI BIYU"
CIKIN SHEKARU 20 DON FAXAXA DA SAKE GINA MASALLACIN ANNABI MAXAUKAKI




TANADAR
 OFISHIN SHA'ANONIN MASALLACI MAI ALFARMA DA MASALLACIN ANNABI




TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
"Kawai, Mai raya masallatan Allah shi ne, Wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, kuma ya tsayar da sallah, ya bada zakkah, kuma bai ji tsoron kowa ba face Allah, To, akwai tsammanin Waxannan su kasance daga shiryayyu" [Tauba: 18].



Yana faranta mini rai; Na sanar da ku, -daga Madinar Manzo Mai karimci (Salati da sallama su qara tabbata a gare shi)-, kan wata buqata matsananciya da ta dabaibaye zuciyata, Wanda kuma itace Na karvi jagorancin wannan qasa Maxaukakiya, Tare da canza laqabin da za a riqa kirana da shi; daga SAHIBUL JALALAH (wato: shugaba ma'abucin girma), zuwa wani Laqabin da Nake sonsa, kuma amfani da Shi zai xaukaka Ni, Shine: MAI HIDIMAR MASALLATAN HARAMI BIYU MAXAUKAKA (khadimu alharamaini as-sharifaini).

(Sarki Fahad)


Masallacin Annabi Maxaukaki; Wato masallacin Manzon Allah; (صلى الله عليه وسلم) wanda ya ke garin Madinatul Munawwarah: Ya samu babban matsayi a zukatan Musulmai, da Maluman tarihi.
Sai mu koma, ga kwanakin da tarihi ya rubuta, Don mu yi qoqarin  gano farkon yadda garin Madinatul Munawarah ya fara, wanda ta bi matakai masu sauqi wajen bunqasarta, har zuwa lokacin da aka fari aikin ginin Masallacin Annabi maxaukaki, -kamar yadda za a gani cikin zanen misaltawa- don Madinatul Munawwarah ta wayi gari, a matsayin cibiyar da take jagorantar Musulmai, kuma take tsara duk sha'anoninsu, na lamuran da za su tabbatar da walwalar duniya, da samun ni'imar lahira.

A shekarar farko ta hijira: Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya tsayu wajen gina MasallacinSa maxaukaki, Sai aka yi aikin rufinsa da tankar Dabino.

Sa'annan sai aka yi aikin faxaxa shi, a shekara ta bakwai bayan hijira, a inda Masallacin ya wayi-gari, yana da kusurwa guda huxu, Tsayinsa kuma kusan zira'i xari, Wanda kuma ya qunshi: Gurbin Sallan Annabi, da MinbarinSa, da Raudha maxaukakiya.

Daga nan, sai Himmar khalifofi, da sauran jagororin Musulmai na aikin faxaxa Masallacin Annabi Maxaukaki, ta biyo baya.
Haka, masu sarauta da sarakunan musulmai, suma suka biyo bayansu; Ta yadda suka qara, hasumiyoyi, da qubbobi, aka kuma shafa zinari a jikin katangu, da usxuwanoni, da qofofi, a wani yanayin da yake nuna gwanancewar musulmai a fannin aikin gini mai kyau.

A qarshen shekarun daular Usmaniyyah, Sai aka qawata wannan masallaci da aikin qara shi; Wanda khalifan daular Usmaniyyah mai suna: As-sulxan Abdulmajid, ya aiwatar, wanda ya kai kimanin mita 2293, a lissafin murabba'i.  Kuma ya gama wannan aikin, a shekarar hijira ta 1277h, a inda aka canza qubbobi, a rufin masallacin, maimakon katakai.

Shekaru kamar 90 sun shige, bayan qarin da khalifan daular Usmaniyya; As-sulxan Abdulmajid, ya yi, Sai Musulmai su ka yi mubaya'a wa shugaban da ya haxe wannan qasa; mai suna Abdul'aziz xan Abdurrahman; Alu-Sa'ud, Sai ya baiwa masallatan harami guda biyu maxaukaka muhimmanci, a tsawon mulkinsa; kuma ya yi umurnin ayi masa qarin daular Saudia ta farko, a shekarar hijira ta 1372h, Sai aka sayi gidajen da suka kewaye da Masallacin, aka rushe su, aka kuma daidaita su da qasa, Sai kuma aka sadar da qarin da daular Saudia ta farko ta yi, da wanda As-sulxan Abdulmajid ya yi, a wani yanayi da yake nuna gwanancewa a fannin gini, mai kyau.
Wannan qarin da aka yi, wanda kuma aka kamala shi a shekarar hijira ta 1375h, ya kai mita 6024 a lissafin murabba'i.
Sai faxi ko girman Masallacin, da dukkan aikin faxaxa shi da aka yi ta yi, (lokaci bayan lokaci) ya fi mita 16327 a lissafin murabba'i.

A farkon zamanin mulkin HADIMIN MASALLATAN HARAMI GUDA BIYU (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye shi- sai ya tafi akan takun Mahaifinsa;  wanda ya assasa wannan qasa, Jagora; Abdul'aziz  xan Abdurrahman (Allah yayi masa rahama) wajen bada kulawa ga masallatan harami biyu maxaukaka.
Kuma a cikin shekaru ashirin (20) na bunqasawa da samar da manyan aiyuka, a dukkan vangarorin rayuwa, Batun masallatan harami guda biyu suna daga abu na farko da basu muhimmanci (Allah ya daxa kare shi).
Mai HADIMIN MASALLATAN HARAMI GUDA BIYU (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye shi-  ya xora tubulin farko, na qara aikin faxaxa Masallacin Annabi maxaukaki, a garin Madinatul Munawwarah, ranar Juma'a, 9 ga watan Safar, ta shekarar 1405 daga hijira, domin Madinatul Munawwara ta ga, Shima Masallacin na Annabi, ya samu mafi girman aikin faxaxawa, da ya tava samu, a tsawon tarihi.
Sai aikin rurrushe ginin da suke kewaye da masallacin ya fara, bayan an gama biyan waxanda aka saya daga wurinsu.
Daga nan, sai aikin ginin faxaxawan da yafi girma ya fara, wanda faxinsa shine: mita 82000 a lissafin murabba'i, domin a wannan karon, faxaawan yafi duk abin da ya gabace, ta fiskar kyautata gini, da faxi, da qarfi, da kyale-kyale, Tare da sanya ko riskar da duk abinda Masallacin zai buqata, saboda an samar da kayan aiki na qarshe, wanda ilimin fannin gine-gine da qere-qere, ya kai izuwa gare su; kamar QUBBOBI masu motsi; waxanda ake aiki da su, a karo na farko, da kuma manya-manyan LEMOMI waxanda aka qirqiro, kuma babu irinsu, da MATAKALAI na lantarki a tsakanin hawan beni da na qasansa; waxanda suke saukake kai-komon dubban xarurrukan Mutane, da wassu irin RUMFUNA ko LEMOMI da suka qunshi dubban FILOLI, da dogayen HASUMIYOYI, wanda sune mafi tsawo da aka tava yi a tsarihin musulunci, da kuma HARABA mai faxi, wanda ba a tava samun irinsa ta fiskar faxi ba, a tsawon tarihi, waxanda kuma aka shumfuxe kasansa da blok xin fulon da ya ke tsote zafin rana, da kuma HIDIMOMI mabanbanta na gyaran abinda ya lalace, madawwami wanda baya yankewa, qarqashin kulawan Babban ofishin sha'anonin masallatan haramin Makkah da na Annabi. Da kuma sauran wassu abubuwan na daban; waxanda za su sanya masallacin Annabi maxaukaki, ya zama wata alama ce bayyananniya akan doron qasa.

HADIMIN MASALLATAN HARAMI GUDA BIYU (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye shi-  ya bada kansa da dukiyarsa domin hidiman masallatan harami guda biyu maxaukaka, da kuma kula da mahajjata da masu ziyara da masu umrah.
Don, kuma a kiyaye lamarin addini da yanayinsa, Sai (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye shi- ya yi umurnin ayi amfani da tsare-tsare da suka dace, da yadda aka gina masallacin annabi da irin yanayin ginin musulunci. Sannan ya yi umurnin a zrtar da wannan aikin faxaxawan tare da ci-gaba da gudanar ibada a cikin masallacin; ba tare da aikin da ke gudana ya tsayar da komai ba.

Harsashin da aka gina qarin da (Sarki Fahad) mai hidimar masallatai guda biyu maxaukaka, ya yi wa masallacin Annabi maxaukaki, sun dogara ne akan FILOLI guda 8500 masu dungu uku na FOLABIY, wanda aka kafa sashinsu a cikin qasa, kamar tsawon kimanin MITA 30 zuwa 50.
Kuma idan aka haxe waxannan filolin tsayinsu zai kai, kamar KILO MITA 30.
Kuma a wajen gino harsashin masallacin (faundation) an yi amfani da kusan buhun siminti musallah 100000.
Kuma haqiqa an qulle filoli na FOLABIYYA  da qarfen yin fila da manara da tushe, wanda yawansu ya kai tushe guda 1877. Tsayuwansu kuma akan mita 70000 ne na fila mai dungu uku, wanda aka yi shi da siminti musallah.
            Faxin ginin da (Sarki Fahad) mai hidiman masallatai biyu ya qara, a masallacin Annabi = ya kai mita 82000 na lissafin murabba'i. Wannan faxin kuma zai baiwa Mutane  kusan 170000 damar yin sallah. Kuma an shirya saman wannan ginin don a iya yin sallah a kansa, da faxin da aka qaddara shi da mita 67000 na lissafin murabba'i, wanda kuma Mutane 90000 za su iya yin sallah.
            Kuma wannan qarin da ya yi, ya haxa da, tanada ko shirya harabar da take kewaye da wannan masallacin, wanda faxinsa ya kai mita 235000 da lissafin murabba'i.
            Sai faxin cikin masallacin Annabi maxaukaki, bayan wannan qarin, idan aka dunqule shi ya wayi gari, ya kai mita 98500, a lissafin murabba'i, wato: qarin kawai, ya kai ninkin tsofon Masallacin Annabi (gabanin qarin) har sau biyar.
A, haka, sai wuraren da za a iya yin sallah ya zama kusan gurbin masu sallah mutum miliyan xaya (1000000), a watan ramadana mai albarka, da kuma lokacin hajji.
Qarin hadimin masallatan harami guda biyu (Sarki Fahad), wanda ya aiwatar a masallacin Annabi, Ya haxa da RUMFUNA; waxanda suka qunshi fiye da FILOLI guda 2100, waxanda su kuma a samansu, akwai wasu baka; waxanda a lokacin sana'anta su, da tsatsara su an kula da tsarin da zai kawo daidaito ko ya sanya su, su zama abu xaya tare da qarin da ake masa laqabin: Qarin daular Saudia na farko.  
Shi kuma rufin wannan qarin ya kasu har zuwa yanki 95, waxanda aka lulluve su gabaxayansu. In banda yanki guda 27 waxanda su kuma aka keve su da QUBBOBI masu motsi.
Qarin da mai hidimar masallatan harami guda biyu maxaukaka (Sarki Fahad) ya yi, ya samar da sabin HASUMIYA guda shida akan hasumoyoyin da ake da su a masallacin Annabi maxaukaki; waxanda tsayin kowannensu shine:  mita 104.
Kuma guda huxu daga cikinsu, suna nan ne a kusurwan wannan qarin guda huxu, su kuma sauran guda biyun suna jikin mashigan sarki Fahad xan Abdul'aziz, ta vangaren arewa.
Kuma a saman hasumiyoyin akwai hoton jinjirin wata, wanda aka leleye shi da ruwan zinari, nauyin kowani xaya daga cikinsu shine ton huxu.
Sai yawan hasumiyoyin gabaxaya su ka zama guda goma (10), suna haskaka sararin samaniyar Madina da alamar Imani, wacce ta cika da kevantacciyar alama ta kyau.   
Qarin ginin da mai hidimar masallatan harami guda biyu maxaukaka yayi wa masallacin annabi, ya qunshi MASHIGA GUDA BAKWAI manya-manya, ta vangaren gabas, da arewa da yamma, kuma kowani mashiga yana da qofofi guda biyar a kusa, da kusa, tare kuma da wassu qofofin guda biyu a ta gefensu.
Sannan kuma akwai manya-manyan mashiga guda biyu ta vangaren arewa na wannan qarin, kowanne daga cikinsu yana da qofofi guda uku a wuri xaya, a ta gefensu kuma akwai qofofi guda huxu.
Kamar yadda wannan qarin ya qunshi qofofi guda goma (10), a matsayin mashiga da mafitan matakalai masu motsi na lantarki; domin yin hidima ga hawa na sama na wannan qarin. Qari akan matakalai guda goma sha takwas (18 ba masu motsi ba) ta cikin masallaci.
Kuma a qarshen arewacin masallacin akwai qubbobi guda bakwai (7) da hasumiya guda biyu a saman mashigan sarki Fahad xan Abdul'aziz, domin wannan mashigan ya banbanta da sauran, kuma domin ya yi nuni kan zanen kalmomin musulunci masu kyau.
Kuma a saman ginin da mai hidimar masallatan harami guda biyu (sarki Fahad) ya yi, akwai qubbobi guda 27 masu motsi, Nauyin kowanne xaya daga cikinsu ton 80 ne, tsayinsa ta sama kuma mita uku ne da rabi (3 1/2) daga tudun rufin, kuma fiye da mita 16 daga kan qasa. Kuma faxin qubba xaya shine mita 14 da uku bisa huxun mita (3/4), kuma an yi amfani da ton 40 ne wajen sana'anta kowace qubba. Kuma ana bubbuxe qobbobin ko a rufe su ne ta hanyar na'ura; domin a amfana da iska ta xabi'a a wassu yanayin da suka dace.
Mai hidiman masallatan harami guda biyu maxaukaka (Sarki Fahad) –Allah ya kiyaye shi- shi da kansa, da kuma tunaninsa ya ke bibiyar matakan zanen aikin da qirqiransa, da zartar da shi, a inda ya riqa miqa dukkanin abinda zai sauqaqe aikin, musamman idan wani abu ya gitta ko ya so ya tsaya a gaban wannan aiki mai xan karen girma na wahalhalu ko abinda zai hana ruwa gudu.
Kamar  yadda ya bada muhimmanci mai girma –Allah ya qara kiyaye shi- wajen yin hidima da kawo kwanciyar hankali ga masu ziyartar masallacin annabi maxaukaki; Sai aka qirqiri lemomi guda 12 don kare masallata daga zafin rana, a wurin da ake ce masa, HASWATU BIYU, daga cikin wuraren da aka qara, a lokacin qarin ginin da daular Saudia ta farko ta gabatar. A matsayin misalin da bashi da makamanci.
Kuma ana bubbuxe waxannan lemomin, ana kuma rurrufe su da na'ura, duk da girman kowanne daga cikinsu. Kamar yadda a lokacin sana'anta su an lura da abinda zai kawo haske, da kyautata iska, da kawo sanyi a jikinsu. Kuma girman kowace lema ya kai mita 306. Sannan ana sana'anta lemar daga sejintiplon wanda gobara ko wuta bata qona shi, haka kuma, da wassu layukan na haske qanana; waxanda da ido kawai ba za a iya ganinsu ba.

Su kuma gine-gine da hadimin masallatan harami biyu maxaukaka ya yi don hidimomi mabanbanta ya haxa da; Gini guda 15, wanda kowannensu ya qunshi: hawa huxu (a cikin qasa); Kuma a cikin waxannan gine-ginen akwai: wuraren alwala guda 6214, da kuma banxakai guda 2432, da mataka guda 116 na latarano wanda aka yi su, a wurare talatin mabanbanta (30), qari akan matakalolin da basa motsawa suma guda talatin (30).
Kuma wannan qarin ya qunshi gini guda 27 don wassu kevantattun hidimomi; kamar cibiyoyin lafiya, da cibiyoyin kunne-kunne, da kashe-kashe (control), da cibiyoyin gyaran na'urori,  da cibiyan kashe gobara, da xakin kula da aiyukan tsaro.
Qarin da mai hidiman masallatan harami maxaukaka ya yi, ya qunshi: Kevantacciyar tashan wutan lantarki, domin samar da wutan wucin gadi ko kar ta kwana , wanda mashuna ko injuna guda biyar suke yin aiki a cikin wannan tashar; don su iya wadatar da vangarorin da aka qara na masallacin, da kuma wani injin guda xaya na daban don ya bada wuta a wuraren fakin xin motoci. Sannan sai aka qaro wassu injunan guda biyu; domin wutan da ake samu idan aka haxa shi, ya iya kaiwa wanda zai haskaka birni guda cikakke.
Shi kuma aikin kawo sanyi (A C) a masallacin Annabi maxaukaki yana dogara ne, akan cibiyoyin kawo sanyi guda shida (6), wanda suke aiki da injunan wuta; qarfin xaya daga cikinsu qisan dubu bakwai (7000) ne, Kuma a cikinsu akwai babban abin sanyaya ruwa, a duniya. Kuma tashar sanyayawar ta qunshi galan 17000 na ruwan da ake sanyaya shi a kowani minti xaya. Kuma tafiyan ruwan da aka sanyaya shin yana farawa ne daga tashar sanyaya shi; wanda nisanta –zuwa da komawa- shine: kilomita bakwai daga masallacin Annabi, kuma ruwan ya kan kasance ne, cikin wani hanyar tiyo na musamman, wanda ya ke bi ta cikin hanyar da aka yi a cikin qasa; wacce aka mata suna da NAFAQUL KHADAMAAT.
Kuma a nan za mu ga cewa, hanyar wannan aiki da aka bunqasa, wajen kawo sanyi, wanda bashi da makamanci a duk duniya, Ta yadda a cikinsa ake: Tace iskar da za a riqa shaqarta, tare da sanyaya ta, sai watso ta, ta wassu kafofi ko vuli-vulin da aka samar da su a jikin qasan filolin masallaci; wannan kuma ba don komai ba; sai domin yanayi mai sanyi (da daxi) ya game xaukacin masallacin Annabi maxaukaki.

(Ruwan zamzam): Shi kuma ruwan zamzam ana xauko shi ne, daga cibiyar tashar da ake cika gorunan zamzam; wacce take Makkatul mukarramah, zuwa cibiyar tashar sanyayawa ta garin Madinatul munawwarah. Kuma aikin dako, ko xauko ruwan zamzam yana ci-gaba a cikin wassu tankunan da aka tabbatar da su akan motoci, a tsawon duka kwanakin shekara.

2016/01/28

HUDUBAR MADINA, ta Juma'a 19 RABIYU AS-SANIY 1437h daidai 29 janairu 2016m, ta As-sheikh Abdulmuhsin Alkasim










HUXUBAR MASALLACIN ANNABI
 (صلى الله عليه وسلم)
JUMA'A, 19 /RABI'U AS-SANIY/1437H
Daidai da 29 / 01 / 2016M




LIMAMI MAI HUXUBA
DR. ABDULMUHSIN XAN ABDURRAHMAN XAN MUHAMMADU ALQASIM







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da kuma munanan aiyukanmu.
Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi.
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Ina kuma shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara tabbata a gare shi, da iyalanSa da sahabbanSa; da sallamar amintarwa mai yawa.

            Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah      -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa,         saboda taqawar Allah haske ne ga basirori, kuma da ita ne zukata da zuciyoyi suke samun rayuwa.

            Ya ku musulmai …
Yin bauta wa Allah shi kaxai itace hikimar samar da halitta, da basu umurni,   Kuma don samar da ita aka turo dukkan Manzanni, aka kuma saukar da littatafai, kuma da ita ne kawai waxannan halittun za su samu xaukaka, su rabauta, su kuma ci nasara su tsira.   Kuma lallai matsayin bayi a wurin Allah zai kasance ne gwargwadon matsayinsu cikin bauta. Allah (تعالى) yana cewa:
"Lallai wanda yafi karama daga cikinku a wurin Allah shine wanda ya fi ku aiki da taqawa" [Hujuraat: 13].

            Kuma yana daga cikin FALALAR ALLAH da KARRAMAWARSA: Yadda ya sanya ibadodi suka zama nau'i-nau'i; domin ya sanya jin daxin bayi shima ya zama nau'i-nau'i, kuma domin ya xaukaka darajojinsu da waxannan ibadodin.
            Kuma akwai wata ibada a cikin addini mai girma, wacce –a koyaushe- take yin rigaye ga dukkan ibadar da ba ita ba, sannan ta inganta sauran ibadodi  (ILIMIN ABINDA AKE YIN BAUTA DA SHI), Wanda ya rabauta da ita ya ci nasara, Wanda kuma yayi sakaci da ita zai yi nadama. Allah ya yi yabo ga ma'abutanta. Kuma ya fifita wassu halittu saboda sun mallake ta. Tana shiryar da Bawa zuwa ga UbangijinSa, kuma tana haskaka hanyoyin rayuwarsa. Kamalar Mutum da tsirarsa a cikin rayuwarsa da bayan mutuwarsa yana rataya ne akanta. Kuma ba a bauta wa Ubangiji da wani abu kwatankwacinta ba; Saboda da wannan ibadar ne ake sanin Allah, kana a bauta masa, Ariqa yin yabo a gare shi, a riqa ambatonSa, a riqa girmama shi. Kuma ake sanin haqqoqin Mahalicci da halittu, da kuma banbance tsakanin halal da haram, da kuma gaskiya da varna, da kuma ingantacce daga lalatacce, da mai amfani daga mai cutarwa, da mai kyau daga mummuna. Ita ce kuma ke xebe kewa ga wanda ke cikin kaxaici, kuma take abota da shi idan yana wurin da ya kevanta, ta riqa tunatar da shi yayin gafala. Nemanta (ibadar ilimi) biyayya ne ga Allah, Bayar da ita kusanci ne zuwa gare shi. Kuma (ilimi) qawa ne ga ma'abutansa, kuma kariya ne ga sahibinta, Tana haskaka zukata da basirori, kuma tana qarfafa kwakwale da zukata. Kuma ma'abutanta a bayan qasa kamar taurari ne ga sama (wajen haskakawa); saboda da Su ne, a ke samun shiriya. Kuma Su ne, ado ga Halittu, kuma mafi kyanSu, Kuma Su ne, kariya ga al'umma da kuma garkuwanta. Kuma ba don Su ba, da alamomin addini sun shafe. Kuma da wannan ibadar al'umma take gyaruwa, kuma ta xaukaka. Da kuma daidaituwan rayuka da samun tsarkinsu. Da kuma shiriyar 'yan Adam da samun rabonsu. Kuma itace ke bada kariya ga al'ummai kuma ta basu salama. Buqatuwa izuwa gare ta yafi dukkan wata buqata. Kuma idan aka rasa ta duniya zata wargaje kuma ta lalace.
Imam Ahmad (رحمه الله) yace:
"Mutane sun fi buqatar ilimi fiye da buqatarsu zuwa ga abinci da abin Sha; saboda Abinci da abin Sha ana buqatarsu ne, a cikin yini sau xaya ko sau biyu. Shi kuma ilimi ana buqatuwa zuwa gare shi a kowani lokaci".
Kuma farkon ayar da ta sauka ta kasance tana kwaxaitarwa ne kan wannan ibadar (ta neman ilimi):
"Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda yayi halitta" [Alaq: 1].
Kuma al'ummarmu (ta Musulmai) al'ummar ilimi ce, da rataya ga Allah.
Ibnu-Kasir (رحمه الله) yana cewa:
"Kuma farkon abinda ya sauka na alqur'ani shi ne: Waxannan ayoyin masu karimci, masu albarka. Kuma sune farkon rahamar da Allah ya yi ga bayi, kuma farkon ni'imar da ya yi akansu".
            Allah ya sanya wa zatinSa sunan AL-ALIMU (wato: Masani).
Kuma ya siffanta kansa da siffar ILIMI. Sa'annan Allah ta hanyar ILIMI ne ya sanu a wurin halittunSa, Yana cewa:
"Wanda ya sanar (da Mutum) game da alqalami * Ya sanar Mutum abinda bai sani ba" [Alaq: 4-5].
            Kuma Manzanci gabaxayansa ILIMI ne da AIKI, Kuma ilimi shine rabinsa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Shine Wanda ya aiko manzonSa da shiriya (wato: ILIMI) da kuma addinin gaskiya (wato: AIKI NA KWARAI)" [Taubah: 33].
            Babu wani abu da yafi daxi ga bawa, kuma yafi kawo gyara ga zuciyarsa fiye da son Allah, Saidai kuma babu hanyar da za a kai izuwa ga hakan sai ta hanyar ILIMI.
            Kuma ilimi shine HIKIMAR da Allah ke bada ita ga wanda ya nufa daga cikin bayinSa; Allah (سبحانه) yana cewa:
"Yana bada hikima ga wanda ya nufa, Kuma duk wanda aka bashi hikima to an bashi alheri mai yawa. Babu wanda yake wa'aztuwa face ma'abuta hankula" [Baqarah: 269].
Mujahid (رحمه الله) yace hikima cikin ayar itace: "Ilimi da fiqihu".

            Allah yayi baiwa da ILIMI ga Annabi Adamu  (عليه السلام) kuma ya bayyanar da falalarSa da ILIMI akan sauran Mala'iku,  "Kuma ya sanar da Adamu sunaye dukkansu, sa'annan ya bijiro da su ga Mala'iku, Sai yace: Ku gaya mini sunayen waxannan idan kun kasance masu gaskiya" [Baqarah: 31].
            Kuma Allah (سبحانه) ya zavi wanda yaga dama daga cikin AnnabawanSa da ManzanninSa da duk wanda ya nufa daga cikin halittunSa; Sai Mala'iku su ka yi busharar samun Is-haqu; yaro MAI ILIMI ga matar Annabi Ibrahima.
Shima annabi Yusufu (عليه السلام) Allah yana faxa akanSa:
"Kuma lokacin da ya kai cikan qarfinsa sai muka bashi hukunci da ilimi" [Yusuf: 22].  Kuma shi annabi Yusuf ya faxi wannan falalar ga karan-kansa, a inda yace:
"Lallai ne Ni mai tsarewa ne, Masani" [Yusuf: 55].
            Kuma shima annabi Musa (عليه السلام) an karrama shi da ILIMI ,Sai ya ce:
" Lokacin da ya kai cikan qarfinsa, kuma ya daidaita sai muka bashi hukunci da ilimi" [Qasas: 14].
            Kuma Allah ya faxa dangane da annabi Dawuda da Sulaimana (عليهما السلام):
"Kowanne mun bashi hukunci da ilimi" [Anbiya'i: 79].
            Kuma Allah ya tunatar da annabi Isah (عليه السلام) da ni'imar ILIMI, a inda yake cewa:
"Ka tuna ni'imomina akanka, da kuma ga mahaifiyarka, a yayin da na qarfafe ka da RUHUL QUDUSI, kana yin magana wa Mutane a cikin shimfixar jariri, da kuma kana dattijo. Da kuma a lokacin da na sanar da kai littafi da hikima, da attaura da injila" [Ma'ida: 110].
Kuma shima Alkhadir, annabi sukutum daga cikin ulul-azmi yayi tafiya zuwa gare shi, saboda abinda yake da shi na fifikon ilimi; "Sai suka sami wani bawa daga bayinMu, Mun ba shi wata rahama daga wurinMu, kuma Mun sanar da shi wani ilimi daga gunMu" [Kahf: 65].
Kuma rundunar annabi Sulaimanu (عليه السلام); Wanda yafi ilimi daga cikinsu shine wanda yafi qarfi a cikinsu; "Sai wanda yake a wurinsa akwai wani ilimi daga littafi ya ce: Ni zan zo maka da shi gabanin kyaftawar ganinka ta koma gare ka" [Naml: 40].
Kuma lallai Allah ya qididdige ni'imominSa ga ManzonSa (صلى الله عليه وسلم) sai ya sanya ilimi, ya zama ya fi sauran ni'imomin matsayi, a inda yace:
"Kuma Allah ya saukar da littafi da hikima a gare ka, kuma ya sanar da kai abinda ba ka kasance ka sani ba" [Nisa'i: 113].
            Kuma bai nemi annabinSa ya nemi qarin wani abu ba, face ilimi, Ya ce:
"Kuma ka ce: Ya Ubangiji ka qara mini ilimi" [Xaha: 114].
            Kuma ilimi shine kayan gadon annabawa, kuma wanda suka gaji iliminsu suna daga mafi alherin Mutane a bayansu, kuma sune mutanen da suka fi kusanci da su; Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:  
"Malamai sune magada annabawa, kuma lallai annabawa ba su gadar da Dinari ko Dirhami ba, kawai! Sun gadar da ilimi ne, kuma duk wanda ya same shi to lallai ya samu cikakken rabo". Attirmiziy ya ruwaito shi.
            Kuma lallai Allah ya kafa ma'abuta ilimi a matsayin masu shaida kan Uluhiyyar Allah, a inda ya ce:
"Allah ya shaida cewa: Lallai babu abin bautawa face shi, Kuma Mala'iku da ma'abuta ilimi sun shaida" [Ali-imrana: 18].
            Kamar yadda Allah ya kafa ma'abuta ilimi a matsayin masu shaida kan vacin maganar kafirai, a inda ya ce:
"Kuma waxannan da aka baiwa ilimi da Imani suka ce: Lallai haqiqa, kun zauna a cikin abinda Allah ya rubuta, har zuwa ranar tayarwa, to, kuma wannan itace ranar tayarwar, kuma amma ku kun kasance ba ku sani ba" [Rum: 56].
            Kuma da ilimi ne, ake jin tsoron Allah; sannan ayi masa biyayya, "Kawai, Malamai ke tsoron Allah daga cikin bayinSa" [Faxir: 28].
Az-zuhuriy (رحمه الله) ya ce:
"Ba a bauta wa Allah da wani abu kamar ilimi ba".
            Samun ilimi alheri ne, da rabauta; saboda "Duk wanda Allah ya nufe shi da alheri ya kan fahimtar da shi a cikin addini", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
            Zavavvu a cikin Mutane sune waxanda suka fi ilimi, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم):
"Zavavvunsu a jahiliyya sune zavavvunsu a cikin Musulunci idan suka yi fiqihu", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
            Ilimi ma'aunin fifikon aiyuka ne da darajojinsu, Kuma da ilimin ne, aiyuka ke inganta, ko su tsarkaka. Kuma aqidar Mutum ba za ta zama garau, ya kuma samar da ikhlasi ga UbangijinSa, tare da yin koyi da annabinSa ba face ta hanyar ilimi, Allah (سبحانه) yana cewa:
"Sai ka sani, cewa: Babu abin bautawa da cancanta face Allah…" [Muhammadu: 19], Sai Allah ya fara ambaton ilimi –a cikin ayar- gabanin zance da aiki.
            Ilimi shine shugaba ga aiki, kuma shine yake masa jagora, kuma duk wani aikin da babu ilimi a cikinsa to ba zai amfani ma'abucinsa ba, hasalima cutarwa ne a gare shi. Wanda ya yi bauta wa Allah ba tare da ilimi ba to varnarsa tafi abinda zai kawo na gyara, yawa. Kuma shirka da bidi'a basu shigo wa Mutane ba, sai saboda qarancin ilimi da kuma nisantar ma'abutansa. Shi kuma vata abokin tafiyar jahilci ne; wannan ya sanya Allah ya umurce mu da neman tsarinsa daga hanyar ma'abuta vata, a cikin kowace raka'a daga cikin raka'oin sallolinmu.
            Kuma, Allah ya kore daidaito tsakanin ma'abuta ilimi da wassunsu, saboda haka; ba za su daidaita ba saidai idan rayayye zai yi daidai da matacce, da kuma makaho da mai gani, Allah (تعالى) yana cewa:
"Ka ce: Shin waxannan da suke da sani, suna daidaita da waxanda ba su sani?" [Zumar: 9].
            Kuma da ilimi ne bayi ke rayuwa, kuma suke samun haskensu, "Shin, kuma wanda ya kasance matacce, sa'an nan muka rayar da shi, kuma muka sanya wani haske dominsa, yana tafiya da shi a cikin mutane, zai zama kamar wanda misalinsa yana cikin duffai, Shi kuma ba mai fita ne daga cikinsu ba" [An'am: 122 ].
            Lallai Kyakkyawan nitsuwa da samun fahimta a  cikin addini suna daga cikin sifofin da muminai suka kevanta da su, Sai zukatansu suka haskaka da ilimi "A'a, Shi ayoyi ne bayyanannu a cikin qirazan waxanda aka baiwa ilimi, Kuma babu  mai musun ayoyinmu face  azzalumai" [Ankabut: 49].
 Kuma a cikin alqur'ani mai girma akwai misalai da aka buga, su guda arba'in da wani abu, kuma da ilimi ne, ake hankalta, kuma ake riskar ma'anonisu, "Kuma waxancan misalan muna buga su ga mutane, kuma babu mai hankalta da su, sai masu ilimi" [Ankabut: 43].
Kuma  wassu daga cikin magabata sun kasance idan suka bi ta kan, misalin da basu fahimce shi ba, sai suyi ta kuka, sai kuma ya ce, "Ni ban kasance daga masu ilimi ba".
            Rahama tana lulluve majalisosin ilimi da ma'abutanta, Nitsuwa kuma tana sassauka akansu, Kuma Mala'iku suna kekkewaye su, kuma suna fakewa a cikinsu, "Kuma lallai Mala'iku suna sanya fuka-fukansu, saboda yarda da xalibin ilimi", Attirmiziy ya ruwaito shi.
Ibnu-Alqayyim (رحمه الله) ya ce: "Idan babu wata falala ga ilimi, sai kusantar da mutum zuwa ga Allah, Ubangijin talikai, da kuma riskar  halittar Mala'iku, da yin abota da maxaukakan Mala'iku, to da hakan ya ishe shi falala da xaukaka. To, yaya kuma, alhalin xaukakar duniya da lahira an rataya ta da ilimi ne, kuma an sharxanta mata samuwansa".
            A majalisosinsu ake samun hikima, kuma su masu ilimi ga al'umma sune mafi alherin abin koyi. Amfanin masu ilimi yana isa zuwa ga waninsu bayan amfanar da kansu, Wannan kuma shine dalilin da ya sa kowa yake yin yabo a gare su, kuma yake musu addu'a, Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Lallai Allah da Mala'ikunSa, da ma'abutan sammai, da qassai, har tururuwa a cikin raminta, da kuma kifi, suna yin addu'a ga wanda yake koyawa Mutane alkhairi", Attirmiziy ne ya ruwaito shi.
            Yin tafiya don neman ilimi yana daga cikin aiki akan hanyar Allah (fi-sabili Allah), Abu-Addarda'i (رضي الله عنه) yana cewa:
"Duk wanda ya ga fita da safe, ko kuma da yamma, zuwa ga ilimi baya cikin jihadi (fiy-sabili Allah), to lallai ya samu tawaya cikin hankalinsa da ra'ayinsa".
            Rigaggeniya a cikin ilimi abin godiya ne, kuma babu hassada sai cikin abubuwa guda biyu, Mai kyautatawa a cikin iliminsa, da Mai kyautatawa a cikin dukiyarsa, Waxanda ba su ba, kuma ba a yin (GIBXA) a cikinsu, saboda qarancin amfaninsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Babu hassada sai cikin abubuwa guda biyu; Mutumin da Allah ya bashi dukiya, sai kuma ya rinjayar da shi akan rowarsa, a cikin lamarin gaskiya. Da kuma mutumin da Allah ya bashi hikima sai yake hukunci da ita, kuma yake karantar da Mutane ita", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
            Kuma lallai dalilai na shari'a, da abinda aka qaddara sun nuna cewa: Lallai sakayya ta kan zama daga jinsin aiki, Don haka; Duk wanda ya bi hanyar ilimi to ya bi hanyar aljannah, kuma lallai ilimi shine hanyar zuwa aljannah da ta fi sauqi, kuma tafi daxi, "Duk wanda ya bi wata hanya da yake neman wani ilimi akanta, to Allah zai sauqaqe masa hanyar aljannah da ita", Muslim ya ruwaito shi.
            Ilimin shari'a garkuwa ne daga fitintinu da musibobi, Imam Malik (رحمه الله) ya ce:
"Lallai wassu mutane sun nemi ibada sai suka tozarta ilimi, daga qarshe sai suka fice da takobi ga al'ummar annabi Muhammadu (صلى الله عليه وسلم), Saidai da sun nemi ilimi da ya katange su, daga hakan".
            Kuma don girman amfaninsa sai umurni ya zo cewa a isar da shi, a kuma yaxa shi, a faxin duniya, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Ku isar mini koda da aya xaya", Bukhariy ya ruwaito shi.
            Allah ya yi umurnin a riqa tambayar ma'abutansa, ana komawa zuwa gare su, "Sai ku tambayi ma'abuta ilimi idan kun kasance ba ku sani ba" [Nahl: 43].
            Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya yi addu'ar hasken fiska ga ma'abuta ilimi, wanda kuma shine, walwala da kyan fiska, da farin ciki, da buxawan qirji, a inda yake cewa:
"Allah ya kyautata fiskan mutumin da ya ji daga gare mu, sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, Dayawa wanda aka isar masa yafi kiyayewa daga wanda ya ji (daga farko)", Attirmiziy ya ruwaito shi.
            Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya yi addu'a ga wanda ya ke so, da cewa ya kasance daga cikin ma'abutan ilimi, sai ya faxa akan Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما), "Ya Allah ka fahimtar da shi addini", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
            Da ilimi ne ake xaukaka darajoji, a cikin rayuwa, da bayan mutuwa, Allah (تعالى) yana cewa:
"Allah yana xaukaka waxanda suka yi Imani daga cikinku, da waxanda aka baiwa ilimi wassu darajoji masu yawa" [Mujadilah: 11].
Ibnu-Alqayyim (رحمه الله) yana cewa:
"Duk wanda ya yi ilimi sai ya yi aiki, to irin wannan ana kiransa babba, a cikin mulkin sammai".
            Kuma amfanin ilimi yana riskan ma'abucinsa a bayan mutuwa, matuqar ana amfana da iliminsa, Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yana cewa:
"Idan Mutum ya mutu aikinsa ya yanke sai guda uku, Saidai sadaka mai gudana, ko ilimin da ake amfana da shi, ko xa nagari da yake masa addu'a", muslim ya ruwaito shi.
            Mafificin ilimi da yafi girma, wanda kuma shine abin yabo a cikin nassoshin Alqur'ani da hadisi, shine ilimin da ya vuvvugo daga cikin littafin Allah da Sunnah, Wanda kuma yafi qololuwa shine ilimin sanin Allah da sunayenSa da sifofinSa, kuma wannan ilimin shine (GAYAR) da ta sanya Allah ya yi halitta, kuma ya bada umurni, "Allah, Wanda ya halitta sammai bakwai, kuma daga qasa kwatankwacinsu, Umarninsa yana ta sauka a tsakaninsu, domin ku SAN lallai Allah mai iko ne akan dukkan komai, kuma lallai Allah yana kewaye da dukkan komai da SANI" [Xalaq: 12].
            Kuma wajibi ne akan kowani Musulmi ya nemi sanin gwargwado na farilla daga cikin ilimi, wanda kuma da shi ne zai inganta tauhidinsa, da sallarsa da azuminsa. Kuma ya bada wani zamani daga cikin lokacinsa don ganin samuwan hakan. Kuma kada ya riqa jin nauyin zuwa halqoqin ilimi da majalisosinsa, saboda Annabi Musa; wanda Allah ya yi magana da shi (كليم الله), kuma yana daga cikin manzanni na ulul-azmi, ya yi tafiya kuma ya haxu da gajiya a hanyarsa ta neman ilimi, haka kuma ya faxi tausasan Magana wa Alkhadir, yana mai cewa:
"Shin ba zan bika, don ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya?" [Kahf: 66]. 
            Kuma wajibi ne akan mai nemansa ya riqa girmama matsayinsa tare da roqon Allah akan ya bashi mai amfani daga cikinsa, da kuma kyautata masa zato, dalazimtar taqawa, saboda kasancewarta mafi alherin abinda zai taimake ka wajen samun ilimi. Kuma wajibi ne niyyarsa ta kasance an tsantsance ta ga neman ganin fiskar Allah, kada kuma ya nemi ilimi don ya riqa alfahari ga wawaye, ko don  jayyaya da malamai, da shi. Kuma lallai duk wanda ya yi aiki da abinda ya sani, sai Allah ya gadar masa da ilimin abin da bai sani ba.

BAYAN HAKA, YA KU MUSULMAI!
            Lallai Allah ya yi alqawari ga wanda ya xau hanyar neman ilimi da cewa: Zai sauqaqe masa shi, kuma zai bashi abinda bai yi zato daga cikinsa ba, a inda ya ce:
"Ka yi karatu, kuma Ubangijnka shi ne Mafi karimci" [Alaq: 3].  
            Kuma hanyar neman ilimi tana da sauqi, kasancewarta hadda ne ga littafin Allah Mai girma, da wani abu na hadisan annabi (صلى الله عليه وسلم), da wassu zavavvu daga cikin littatafan ma'abuta ilimi, tare kuma da fahimtar abinda suka gabata (na ayoyi da hadisai da littatafai). Kuma da haka ne Mutum zai samu yardar Allah, da maxaukakan aljannonin ni'imah.
           
A UZU BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIM:
"Kuma baya kasancewa ga muminai su fita zuwa yaqi gabaxaya, To don menene wata jama'a daga kowane vangare daga gare su ba ta fita (zuwa neman ilimi ba) domin su nemi ilimi ga fahimtar addini, kuma domin su yi gargaxi ga mutanensu idan sun koma zuwa gare su, tsammaninsu za su yi taka-tsan-tsan" [Taubah: 122].

            ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA. …
             

HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa;  godiya kuma tasa ce bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya;      Ina mai girmama sha'aninSa.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi daxin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.

Ya ku musulmai…
Malaman wannan al'ummar; daga cikin waxanda suka yi rigaye, da waxanda suke riskansu: Ba a ambatonsu sai da kyakkyawan ambato, saboda haqqinsu akan wannan al'ummar yana da girma, ta fiskar sonsu da girmama su, da darajanta su, da komawa izuwa gare su, da xaukan ilimi a gare su. Kuma lallai girmama ma'abuta ilimi yana daga girmama addini; saboda kasancewarsu waxanda suke dauke da shi, kuma waxanda aka basu amanar kiyaye shi. Kuma dukwanda ya karkace bai yi irin wannan mu'amalar da sub a, to lallai ya vace; ya bar hanya. Shi kuma qin ma'abuta ilimi da yin adawa da su tawaya ne cikin hankali, kuma karkacewa ne daga fixira. Wannan yana shelanta masa yaqin Allah da kuma cewa zai masa uquba, Allah a cikin hadisin Alqudusiy yana cewa:
"Wanda ya yi adawa da waliyyina to lallai na shelanta yin yaqi da shi", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.   
           
            Sannan ku sani;         Lallai  Allah ya umurce ku da yin salati da kuma sallama ga Annabinsa
Sai yace, a cikin mafi kyan abinda aka saukar:
"Lallai Allah da Mala'ikunSa suna yi salati ga wannan annabin, Yak u waxanda suka yi Imani, ku yi salati a gare shi, da sallamar amintarwa" [Ahzab: 56].
            Ya Allah! Ka yi salati da sallama da albarka, ga annabinmu Muhammadu,
            Kuma Ya Allah! Ka yarda da khalifofi shiryayyu, waxanda suka yi hukunci da gaskiya, kuma da shi, su ka kasance suke yin adalci, Abubakar da Umar da Usman da Aliyu, da kuma sauran sahabbai gabaxaya, Ka haxa da Mu tare da Su, da kyautarka da karamarka, Ya Mafi kyautar masu kyauta.
            Ya Allah! Ka xaukaka Musulunci da Musulmai, ka qasqantar da shirka da Mushirkai, kuma ka ruguza maqiyan addini, Kuma ka sanya –Ya Allah!- Wannan qasar cikin aminci da nitsuwa, da wadaci da walwala, da kuma sauran qasashen Musulmai.
            Ya Allah! Ka gyara halin Musulmai a kowani wuri.
            Ya Allah! Ka mayar da su izuwa ga addininka, mayarwa mai kyau.
            Ya Allah! Ka sanya qasashensu su zama garurrukan aminci da zaman lafiya, Ya Mai qarfi, Ya Mabuwayi!
            Ya Allah! Ka tabbatar da rundumarmu, Ya Allah! Ka tabbatar da dugadugansu, Ya Allah! Ka daidaita jifansu, kuma ka azurta su da yi don kai (ikhlasi), Ya Ma'abucin girma da Baiwa.
            Ya Allah! Ka datar da shugabanmu, kuma ka sanya aikinsa ya zama cikin yardarka. Kuma ka datar da sauran jagororin Musulmai wajen yin aiki da littafinka, da hukunta shari'arka, Ya ma'abucin girma da yin baiwa.
            "Ya UbangijinMu ka bamu mai kyau a duniya, ka bamu mai kyau a lahira, kuma ka kare mu daga azabar Wuta" [Baqarah: 201].
            Ya Allah! Lallai ne Mu muna roqonka ilimi mai amfani da kuma aiki mai kyau.
            Ya Allah! Lallai kai ne abin bautawa; Babu wani abin bauta face kai, Kai ne Mawadaci, mu kuma mune Faqirai, Ka saukar mana da ruwan sama kada ka sanya mu daga cikin masu xebe tsammani, Ya Allah! Ka bamu ruwan sama!
            Ya Allah! Ka bamu ruwan sama!!
            Ya Allah! Ka bamu ruwan sama!!!
            "Ya Ubangijinmu lallai ne Mu mun zalunci kayukanmu, idan har baka gafarta mana, ka yi rahama a gare mu ba, za mu kasance daga cikin masu hasara" [A'araf: 23].
            Bayin Allah!!!
            "Lallai Allah yana yin umurni da adalci, da kyautatawa, da baiwa makusanci, kuma yana yin hani akan alfasha da abin qi, da zalunci, Yana muku wa'azi da fatan zaku zama masu tunawa" [Nahli: 90].
Ku riqa ambaton Allah Mai girma da daraja zai ambace ku, ku gode masa akan ni'imominSa zai muku qari, kuma ambaton Allah shine mafi girma, kuma lallai Allah ya san abinda kuke aikatawa.
,,,          ,,,          ,,,

,,,          ,,,          ,,,

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...