2015/09/10

HUDUBAR MASALLACIN ANNABI 27 ZULKIIDAH 1436h TA SHEIKH ABDULMUHSIN ALKASIM











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 27 /ZUL QI'IDAH/1436H




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI ABDULMUHSIN ALQASIM







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Lallai yabo na Allah ne; muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarin Allah daga sharrin kayukanmu, da kuma munanan aiyukanmu.
Duk wanda Allah ya shiryar to babu mai vatar da shi, Wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya.
Kuma ina shaidawa lallai annabi Muhammadu bawanSa ne manzonSa ne.
Salatin Allah su qara tabbata a gare shi, da iyalansa da sahabbansa; da sallama mai yawa.

            Bayan haka;
Ku kiyaye dokokin Allah      -Ya ku bayin Allah- iyakar kiyayewa,         saboda Ubangijinmu (Allah) baya karvar aiki sai wanda aka yi shi da taqawah,    Kuma baya yin rahama sai ga ma'abotanta

            Ya ku musulmai …
Allah yana zavan wanda ya so daga cikin halittunSa
"Kuma Ubangijinka yana halittar abinda ya nufa, Sai kuma yayi zavi"  [Qasas: 68].

Sai Allah ya zavi manzanni daga cikin Mala'iku, haka kuma daga cikin mutane.       Daga cikin maganganu kuma sai ya zavi ambatonSa,         Daga dukkan qasa kuma = masallatanSa,    Sai kuma daga cikin watanni,   ya zavi watan ramadhana, da kuma watanni huxu masu alfarma.
            Kuma lallai mutanen jahiliyyah sun kasance su kan yi qarin kwanaki a cikin watanni, ko su jinkirta wassu, suna masu bin son zuciyarsu;         Sai azuminsu ya kasance ba a lokacinsa ba,     Hajjinsu shima ba a zamaninsa ba.
Har Allah yayi rahama ga wannan al'ummar; da tayar da Manzon da ya tsayar da wannan addinin;      Sai ya aikata hajjinsa (صلى الله عليه وسلم) hajjin bankwana, bayan zamani ya juya ya daidaita kamar yadda ya kasance;       Sai hajjinsa ya auku a cikin watan zulhijjah,      ya kuma bayyana haka a cikin huxubarSa:
"Lallai zamani ya juya ya koma kamar yadda yake, a ranar da Allah ya halicci sammai da qassai", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Da wannan,       Sai qidaya ta cika,       lissafi kuma ya inganta,    Lamari shi kuma ya koma kan abinda ya kasance akansa a farko,           kamar yadda littafin Allah ya bayyanar.
           
            Kuma fifikon da aka sanya a tsakanin darare da yini yana hukunta a tsayu wajen ribatar alherin da yake cikinsu.  Kuma lallai Annabinmu (صلى الله عليه وسلم) ya kwaxaitar kan ribatar ni'imomi guda biyar, gabanin gushewarsu; a inda yake cewa:
"Ka ribaci biyar gabanin abubuwa biyar; Samartakarka gabanin tsufanka,   Da lafiyarka gabanin cutarka,   Da wadacinka gabanin talaucinka,   Da damar lokaci; gabanin shagaltuwarka,  Da rayuwarka gabanin mutuwarka",     Alhakim ya ruwaito shi.

                     Kuma lallai kwanaki goman zulhijjah sun nufo wannan al'ummar, kuma suna daga cikin kwanakin Allah masu alfarma,     kuma sune cikamakon watannin nan sanannu; waxanda Allah yake faxi akansu:
"Aikin hajji watanni ne sanannu" [Baqarah:  197].   Waxanda kuma sune: Watan shawwal, da zulqi'idah da kwanaki goman zulhijjah (na farko).      Kuma saboda girman matsayinsu ne mafi yawan aiyukan hajji suke aukuwa a cikinsu.       Kuma Allah yayi rantsuwa da dararensu; a inda yake cewa:
"Ina rantsuwa da alfijir * Da kuma darere guda goma" [Alfajr: 1-2].
Kuma yininsu yafi girman falala akan yinin kwanaki goman qarshe na watan ramadhana.   Kuma Annabi (عليه الصلاة والسلام):
"Mafificin kwanakin duniya sune: Yinin kwanaki goma", Ibnu-hibbana ya ruwaito shi.

Kuma darajar kwanaki goman zulhijjah tayi fifiko saboda haxuwar manya-manyan ibadodi a cikinsu,     kamar sallah, da azumi, da zakkah, da kuma aikin hajji. Wanda hakan kuma baya kasantuwa a wassu kwanakin waxanda ba su ba.

            Kuma kowani aiki managarci a cikin waxannan kwanakin (guda goma) yafi soyuwa a wurin Allah, fiye da irin wannan aikin; idan ya auku a cikin wassu kwanakin waxanda ba su ba.      Annabi (عليه الصلاة والسلام) yace:
"Babu waxansu kwanaki da aiki managarci yafi soyuwa a cikinsu a wurin Allah fiye da waxannan kwanakin guda goma. Sai suka ce: Koda jihadi ne fiysabilillah?     Sai yace: Koda jihadi ne fiysabillahi,       Saidai mutumin da ya fita da ransa da dukiyarsa, sai kuma bai koma da komai ba",   Bukhariy ya ruwaito shi.
Malam Ibnu-rajab (رحمه الله) yace:
"Lallai wannan hadisin yayi nuni cewa: Yin aiki a cikin kwanakin nan guda goma shi yafi soyuwa a wurin Allah, akan yin aikin a sauran kwanakin duniya, ba tare da an togance wassu kwanaki ko an ware su daga ciki ba".

            Kuma lallai magabatan kwarai (رحمهم الله) sun kasance suna yin bakin qoqarinsu wajen aikata kyawawan aiyuka a cikin kwanakin nan guda goma;     Sa'idu xan Jubair (رحمه الله) idan kwanaki goman zulhijjah suka shiga ya kan qara zagewa wajen aiki tuquru, har kamar ba zai iya ba.

            Kuma yana daga falalar Allah da kyautarsa    Sai dangogin aiyukan biyayya wa Allah a cikin kwanakin nan suka yawaita;
Kuma yana daga cikin abubuwan da aka shar'anta a cikin kwanakin nan:  YAWAITA AMBATON ALLAH, kamar yadda Allah yake cewa:
"Kuma su ambaci sunan Allah a cikin wassu yini sanannu" [Hajji: 28].
Abdullahi xan Abbas yace:
"Sune: Yini guda goma".
            Kuma ambaton Allah (سبحانه) a cikin waxannan yinin guda goma yana daga cikin mafificin dangogin nau'ukan biyayya wa Allah;        Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) ya ce:
"Babu wassu yini da yafi girma a wajen Allah, ya kuma fi soyuwa a wurinsa ayi aiki a cikinsu fiye da waxannan guda goman;     Sai ku yawaita faxin: La ilaha illallahu a cikinsu, da yin kabbara, da hamdala",  Ahmad ya ruwaito shi.
Imam Annawawiy (رحمه الله) yace:
"Mustahabbi ne yawaita zikirori a cikin waxannan kwanakin guda goma,       qari akan waxanda ake yi a wassu kwanakin.     A ranar arafah kuma mustahabbi ne a yawaita yin zikirori fiye da sauran kwanakin guda goma".

            Mafifici kuma daga dangogin zikiri shine KARATU KO TILAWAR LITTAFIN ALLAH;     Wanda kuma shine shiriya da haske mabayyani.

            Yin kabbarori kuma ko-yaushe a kowani lokaci yana daga cikin ibadun da suke banbance waxannan yini guda goma;      Abdullahi xan Umar da Abu-hurairah (رضي الله عنهما) suna fita zuwa ga kasuwa, a kwanaki guda goma; suna yin kabbara; mutane kuma suna yin kabbara da kabbararsu. Bukhariy ne ya rawaito shi.

            Kuma an shar'anta yin kabbarori qayyadaddu a bayan sallolin farilla, daga sallar asubar ranar arafah, ga mahajjata, da waxanda ba su ba.        Sheikhul Islam (Ibnu-taimiyyah رحمه الله):
"Maganar da tafi inganci dangane da kabbarar da magabatan kwarai da faqihai da sahabbai da manyan maluma ita ce: Mutum ya fara yin kabbara daga sallar asubar ranar arafah,      har zuwa qarshen kwanakin busar da nama (ATTASHRIQ; 13 ga wata),      Bayan kowace sallah".

            Yana kuma daga cikin abubuwa mustahabbai YIN AZUMIN KWANAKI GUDA TARAN FARKO, DAGA CIKIN GOMAN ZULHIJJAH    Imam Annawawiy (رحمه الله) yace:
"Azumtar hakan mustahabbi ne; abun so mai tsanani".

            BADA SADAKA shima aiki ne mai kyau managarci;     Kuma da bada sadakar ake yaye baqin ciki,      sannan wahala ta gushe.        Kuma mafi alherin sadakar da aka bayar itace wacce ta kasance a lokacin buqatarta,     da kuma wacce aka bada ita a cikin wani zamani maxaukaki.

            Ita kuma TUBA  matsayinta a cikin addini maxaukaki ne,       Kuma ita sababin tsira ne da rabauta.       Allah ya wajabtata akan al'umma gabaxaya daga dukkan zunubai;     Sai yace;   akan mutanen da suka riya cewa Allah yana da mata, wai kuma yana da xa:
"Shin baza su tuba zuwa ga Allah ba ne, suna masu neman gafararsa" [Ma'idah: 74]. 
Kuma ya faxa dangane da muminai:
"Kuma ku tuba zuwa ga Allah gabaxaya ya ku muminai, da fatan zaku samu rabo" [Nuur:  31].
  Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya kasance yana roqon Allah a cikin yini xaya sau xari cewa ya karvi tubansa;     Yana cewa:
"Ya ku mutane ku tuba zuwa ga Allah;      saboda ni nakan tuba a cikin yini xaya sau xari", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.

Kuma lallai mune muka fi buqatar tuba,        Kuma lallai mafi alherin yini ga bawa shine yinin da ya tuba a cikinsa,     Annabi (عليه الصلاة والسلام) yace wa Sahabinsa Ka'ab xan Malik (رضي الله عنه):
"Ina yin albishir a gare ka da mafi alherin yinin da ya tava shigewa a gare ka tun ranar da mahaifiyarka ta haife ka", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma me yafi kyau fiye da mai tuba ya yi tubansa a mafi soyuwan kwanaki a wajen Allah!
Duk kuma wanda ya yi gaskiya cikin tubansa to zai samu xaukakan darajoji,      Allah kuma zai canza masa munanan aiyukansa da masu kyau.

            Kuma a cikin kwanaki goma na farkon zulhijjah ake yin HAJJIN XAKIN ALLAH MAI ALFARMA, Wanda kuma xaya ne daga cikin rukunnan musulunci, masu girma waxanda musuluncin ya ginu akansu,     Allah (سبحانه) yana cewa:
"Kuma lallai Allah ya wajabta wa mutane yin hajjin wannan xaki; ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi" [Ali-imraana: 97].
Kuma Annabi (عليه الصلاة والسلام)  yace:
"Ya ku mutane an farlanta hajji akanku; Ku yi aikin hajji", Muslim ya ruwaito shi.
Kuma aikin hajji yana daga cikin aiyuka masu fifikon falala a wurin Allah;       An tambayi Annabi (صلى الله عليه وسلم) cewa:
"Wani aiki yafi falala? Sai yace: Yin imani da Allah da manzonSa,    Sai aka ce: Sa'annan sai me? Sai yace: Sai jihadi fiysabilillahi, Sai aka ce: Sa'annan sai me? Yace: Sai hajjin da aka yi biyayya a cikinsa. Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma lallai lafiyayyen hajji (mabruur) bashi da wani sakamako sai aljannah,     kuma ana kankare zunubai da shi, da kura-kurai,    Annabi (عليه الصلاة والسلام):
"Wanda yayi hajjin wannan xakin;  bai yi kwarkwaso ba, bai yi fasiqanci ba, zai fita daga  zunubansa kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi", Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.       Kuma lallai Allah yana yin alfahari da waxanda suka halarci tsayuwan arafah, ga halittunsa na sammai (mala'iku).

            Kuma lallai hajji yana da hikimomi masu girma, da manufofi masu kyau manya-manya, a addinance, da a duniyance, a wannan rayuwar da kuma a lahira;      Kuma na farko daga cikin waxannan hikimomin shine: TABBATAR DA TAUHIDI,     saboda Kalmar da take bakin mahajjata ko-yaushe itace:
"لَبَّيْكَ اللَّهُمَّ لَبَّيْكَ ، لَبَّيْكَ لا شَرِيكَ لَكَ لَبَّيْكَ ، إِنَّ الْحَمْدَ وَالنَّعْمَةَ لَكَ وَالْمُلْكَ لا شَرِيكَ لَكَ".
Ma'ana: "Mun amsa maka ya Allah, muna amsa maka, mun amsa baka da abokin tarayya, mun amsa, Lallai yabo, da ni'ima naka ne, da mulki;    baka da abokin tarayya".
            Yana kuma daga cikin hikimomin aikin hajji:  TSANTSANTA NIYYAR AIKI (wato: IKHLASI) GA ALLAH SHI KAXAI, da kuma   YIN KOYI DA MANZON ALLAH,     Allah ta'alah yana cewa:
"Kuma ku cika hajji da umrah ga Allah",  [Baqarah: 196].
Manzon Allah (عليه الصلاة والسلام) yace:
"Ku koyi aikin hajjinku daga gare ni", Muslim ya ruwaito shi.
            Yana kuma daga cikin hikimomin aikin hajji:  "Domin su halarci amfaninsu" [Hajji: 28],  a nan duniya, da abinda suke samu na alkhairori,    da kuma a lahira ta hanyar shiga aljannoni.

"Sai su ambaci sunan Allah a cikin kwanaki sanannu", [Hajj: 28] … .
Kuma lallai hajji yana tunatar da mutane cewa za a bar wannan duniyar;      kuma lokacin aiwatar da hajji shine qarshen kwanakin shekara,        Kuma Annabi (عليه الصلاة والسلام) ya aiwatar da aikin hajjinsa ne a qarshe-qarshen rayuwarsa;    wanda kuma a cikinsa yayi bankwana da sahabbansa,     Allah ta'alah kuma a cikin wannan hajjin ya cika wa al'umma addininta; ya kuma saukar masa da faxinSa a ranar arafah: "A yau na cika addininku a gare ku,   na kuma cika ni'imata akanku", [Ma'idah: 3].

Wanda kuma ya gaza yin hajj saboda wani uzuri to zai yi tarayya da mahajjata a cikin lada;     idan har yayi gaskiya cikin niyyarsa,        kasancewar ta kan yiwu masu tafiya da zuciyarsu,    su rigayi waxanda suka je kawai da jikikkunansu.

Kuma a cikin waxannan kwanaki goman ake samun YININ ARAFAH;  Wanda azumtarsa yake kankare zunuban shekarar da ta wuce, da wacce zata zo,             Kuma "Babu wani yini wanda Allah yafi 'yanta bayi a cikinsa daga wuta fiye da yinin arafah", Muslim ya ruwaito shi.     Kuma mafi alherin addu'a shine addu'ar da aka yi ta a ranar arafah.

Kuma a cikin waxannan kwanaki goman ake samun YININ LAYYA; Wanda shine yini mafi girma daga cikin kwanakin da ake aiyukan hajji a cikinsu, kuma shi yafi xaukaka a cikinsu,      kuma shi yafi tattara aiyukan hajji dayawa a cikinsa,      don haka shine: RANAR AIKIN HAJJI DA YAFI GIRMA,    Allah yana cewa:
"Kuma, Yin shela daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutane, a ranar hajji wanda yafi girma…" [Taubah: 3].
Kuma wannan yinin (na layya) shine mafi girman kwanaki a wurin Allah;     Annabi (عليه الصلاة والسلام) yace:
"Lallai mafi girman yini a wurin Allah shine ranar layya, sa'annan sai ranar goma sha xaya; wanda mahajjata suke tabbata a Minah",    Abu-dawud ya ruwaito shi.
Kuma yinin layya xaya ne daga cikin idi guda biyu na musulmai;     ranar farin cikinsu; saboda sun sauke wani rukuni daga cikin rukunnan musulunci (wato hajji).

            Saidai mutane a yanayi na farin-cikin idi zasu iya gafala, su bar tsayar da ambaton Allah (zikiri),     A irin wannan yanayin yin zikirin yafi falala;       Allah yana cewa:
"Ku ambaci Allah a cikin kwanaki qididdigaggu" [Baqarah: 203].      Waxanda kuma sune kwanakin idi (waxanda ake busar da nama a cikinsu; AT-TASHRIQ).
Annabi (عليه الصلاة والسلام) yace:
"Kwanakin ATTASHRIQ –ma'ana: kwanakin idi- kwanaki ne na ci, da sha, da kuma ambaton Allah",    Muslim ya ruwaito shi.
Ibnu-hajar (رحمه الله) yace:
"Lallai falala ta tabbata ga kwanakin nan guda goma,     don haka sai ta tabbata ga kwanakin idi (Attashriq)".

            A kwanakin layya da na shanya nama (attashriq) ake yin ibada ta dukiya da jiki (wato: layya), wacce kuma take cikin ibadodin da Allah yake sonsu dayawa; (kuma saboda girmanta) Allah ya haxa ambatonta tare da sallah a cikin faxinsa:
"Ka yi sallah wa Ubangijinka, kuma kayi sukan (raqumi) a gare shi", [Alkausar: 2].
Kuma lallai Allah ya kwaxaitar kan tsantsanta niyya cikin yanke-yanke ko suka, da cewa: Bawa ya nufi Allah shi kaxai cikin layya, ba alfahari ko riya, ko don aji labarin mutum yayi, ko ayi layyar don tsagwaron al'ada ba,       Allah yana cewa:
"Naman dabbobin layya ko hadayanku baya samun Allah,   haka jinanensu,     Saidai taqawarku ce take samunsa" [Hajj: 37].
Kuma Annabi (صلى الله عليه وسلم ) yayi layya da raguna guda biyu, masu baqi-baqi, masu qaho, ya yanka su da hannunsa" Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.
Kuma ragon da ake masa laqabi da AMLAH: Shine baqin da a saman gashinsa akwai fari.
"Aqranaini" kuma a cikin hadisinma'abota qaho.

            Babu laifi Mutum ya ci bashi don ya sayi abin layya, sai kuma ya jira samun mayewar abinda ya kashe daga Allah.

            Kuma bai dace mutum yayi ta qorafin tsadar kuxin dabbar layya ba; saboda ladanta a wurin Allah yana da yawa.

            Kuma duk wanda yayi nufin yayi layyah haramun ne akansa ya aske gashinsa ko ya yanke wani abu na farcensa, Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace
"Duk wanda yake da abin yankan da zai yanka; to idan jinjirin watan zulhijjah ya kama to kada ya aske gashinsa ko wani abu na farcensa, har zuwa lokacin da zai yi layyan",      Muslim ya ruwaito shi.

            Bayan haka,            Ya ku musulmai….
            Lallai wanda ya rabauta shine wanda ya ribaci muhimman watannin lokutan ibada da kwanakinsu,      ya kuma kusanci masoyinsa Allah da aiyukan xa'a da biyayya,      da fatan wata rahama daga cikin rahamomin Allah ta lulluve shi;      sai ya samu rabo  ya kuma tsira tare da aminta daga babbakuwa ko faxawa cikin wuta,       sa'annan ya samu rabauta da shiga aljannar da faxinta shine faxin sammai bakwai da qassai.           Wanda kuma a can ne zai yi daddaxar rayuwa ta har abada;        Kuma don neman samun haka mutanen kirki (masu rigaye zuwa ga aikata alkhairi) suka zage damtse.

A UZU BILLAHI MINASH SHAIXANIR RAJIM:

"Ku yi gaggawa zuwa ga wata gafara daga Ubangijinku, da samun aljannar da faxinta shine faxin sammai da qassai;        wacce aka tanade ta ga waxanda suka yi imani da Allah da Manzanninsa,     Wancan kuma falalar Allah ce da yake bayar da ita ga wanda ya nufa,   kuma lallai Allah shine ma'abocin falala mai girma" [Alhadid:   ].

            ALLAH YAYI MINI ALBARKA NI DA KU CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA.
             

HUXUBA TA BIYU
Yabo ya tabbata ga Allah kan kyautatawarSa;  godiya kuma tasa ce bisa ga datarwarSa da kuma ni'imominSa,
Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya;      Ina mai girmama sha'aninSa.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa ne.
Allah yayi daxin salati a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da kuma sallama mai ninnukuwa.

Ya ku musulmai…
Aikata dangogin savo da laifuka sababi ne na samun nisa daga Allah,      kamar yadda kuma yin biyayya a gare shi yake sabbaba samun kusantarSa;      saboda yin zunubai yana da shu'umci da matsala ga xaixaikun jama'a da kuma al'ummai,     Allah (سبحانه) yana cewa:
"Kuma ku nisanci zunubin bayyane da kuma wanda ya vuya;     lallai waxanda suke aikata savo to da sannu za a sakanta musu da abinda suka kasance suke aikatawa" [An'aam: 120].
            Kuma lallai hatsarin savo yana qara girma idan aka aikata su a lokutan rahama da alkhairori,      Allah ta'alah yana cewa:
"Lallai qidayar watanni a wurin Allah watanni sha biyu ne, a cikin littafin Allah, tun ranar da ya halicci sammai da qassai,    Daga cikinsu akwai guda huxu masu alfarma,   Wannan shine addini miqaqqe kada ku zalunci kayukanku a cikinsu" [Taubah; 36].
Qatadah (رحمه الله) yace:
"Yin zalunci a cikin watanni masu alfarma yafi girman zunubi da kuskure fiye da yin zalunci a cikin wassu watannin; waxanda ba su ba,    tare da cewa yin zalunci a kowani hali yana da qirma,      Saidai kuma Allah yana girmama abinda ya so daga al'amarinSa".         

            Kuma kamar yadda yin zunubai a cikin watannin nan laifi ne mai girma,       to haka aikata kyawawan aiyuka na biyayya a cikinsu shi kuma akwai alheri babba.

            Sai ku ribata da lokutan samun rahamomi, da xaukaka darajojin bayi,         kuma ku nisanci duk abinda zai shamakance samun gafarar Allah,      a irin waxannan lokutan,    ko a wassunsu.


            Sannan ku sani;         Lallai  Allah ya umurce ku da yin salati da kuma sallama ga Annabinsa …   …   …  

2015/09/04

HUDUBAR JUMA A DAGA MASALLACIN MANZON ALLAH 20 11 1436h TA SHEIKH SALAH ALBUDAIR











HUXUBAR MASALLACIN ANNABI (r)
JUMA'A, 20 /ZUL QI'IDAH/1436H




LIMAMI MAI HUXUBA
SHEHI SALAH ALBUDAIR







TARJAMAR
ABUBAKAR HAMZA
بسم الله الرحمن الرحيم
HUXUBAR FARKO
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah wanda ya haskaka basirar muminai da shari'arSa,      Ya kuma bayyana halal daga haram ga mukallafai (masu hankali, baligai),    Kuma ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai ya ke, bashi da abokin tarayya, kuma bashi da mai taimako.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu annabi Muhammadu bawan Allah ne kuma manzonSa; da ya bayyanar da hukunce-hukunce, da qa'idodin musulunci ga masu bi; sannan yace:
"Wanda Allah yake nufinsa da alkhairi ya kan fahimtar da shi addini".
Salatin Allah da sallamarSa su qara tabbata a gare shi, da iyalansa da sahabbansa; khalifofin addini, waxanda suka cika da yakini.

            Bayan haka;
           
Ya ku musulmai …
Ku kiyaye dokokin Allah,    saboda taqawar Allah itace mafificin aiki,    Yi masa xa'a kuma shine mafi xaukakar nasaba, ko danganta;
"Ya ku waxanda suka yi imani ku kiyaye dokokin Allah iya kiyayewa, kuma kada ku mutu face kuna musulmai",  [Ali-imraan: 102].

            Ya ku musulmai …
Aikin hajji xaya ne daga cikin rukunnai guda biyar waxanda aka gina musulunci akansu,            Kuma yana wajaba akan balagagge mai hankali (mukallafi) da yake da iko, sau xaya a rayuwa.

Kuma duk wanda hajji ya wajaba akansa, kuma yake da ikon aikata shi   =  To dole ne a kansa ya gaggauta aiwatar da shi;          Ya zo daga Abdullahu xan Abbas    (رضي الله عنهما) yace:     Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Duk wanda ya nufi aikin hajji to ya gaggauta shi;       saboda rashin lafiya ka iya bijirowa,       ko hanya ta gurvace,      ko wata buqatar ta bijiro".     Ahmad da Ibnu-Majah suka ruwaito shi.

            Wanda kuma ya mutu gabanin ya sauke farillar hajji,     sawa'un yayi sakaci cikin hakan, ko bai yi sakaci ba,      kuma daidai ne yayi wasicin cewa a yi hajjin a gare shi ko bai yi wasici ba   =   To sai a fitar da kimanin abinda zai yi masa hajji da umrah daga cikin abinda ya bari na dukiya;         Saboda hadisin Abdullahi xan Abbas  (رضي الله عنهما) Lallai wata mata daga qabilar juhaina ta zo wajen Manzon Annabi (صلى الله عليه وسلم) sai tace: Lallai uwata tayi bakancen zata yi aikin hajji, sai bata samu ta yi hajjin ba, hart a mutu; Shin zan mata hajjin?       Sai yace: Na'am kiyi mata hajji;    Shin idan akwai bashi akan mamarki; zaki biya mata?     Ku biya Allah bashinSa;     saboda Allah shi yafi cancantar a biya shi". Bukhariy ne ya ruwaito shi.

            Wanda kuma ya samu ikon yin hajji da kansa to bai halatta ya wakilta wani mutum ya yi hajjin a gare shi ba.

            Wanda kuma sharuxan wajabcin hajji suka tabbata akansa,          Sai kuma ya gaza yinsa da jikinsa;      saboda wani uzurin da aka xebe tsammanin gushewarsa;     kamar gurguntaka da cutar da ta jima, ko dai wani rashin lafiyar da ba a tsammanin warkewarsa, ko kuma ya kasance ba zai iya tabbata akan abun hawa ba; sai da matsananciyar wahalar da ba za a iya jure mata ba,    ko kuma ya kasance tsofo ne da qarfinsa ya qare     =   To wajibi ne akansa ya samar da wanda zai yi hajji da umrah a gare shi;           Ya zo daga Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما) lallai wata mata tace:         Ya ma'aikin Allah!       Lallai farillar Allah akan bayinsa na hajji ta riski babana yana dattijo mai yawan shekaru;      Ba zai iya tabbata akan abin hawa ba;      Shin zan iya yin hajji a gare shi?      Sai yace:     E; na'am".      Bukhariy da Muslim suka ruwaito shi.

            Kuma duk lokacin da mutum ya wakilta wani yayi masa aikin hajji,     sa'annan sai ya samu lafiya   =  To ba wajibi ba ne akansa ya yi wani hajjin na daban;    saboda ya aikata abinda aka umurce shi da shi;    sai ya fita daga zargi.

            Shi kuma wanda yake fatan zai samu ikon yin hajji da kansa,     ko kuma ana tsammanin gushewar cutarsa,    to lallai baya halatta a gare shi ya wakilta wanda zai yi hajji a gare shi;     Idan kuma ya aikata haka    to bai isar masa ba.

            Shi kuma faqirin da bashi da kuxin aikin hajji to hajjin baya wajaba akansa,     kuma ba zai nemi wani ya wakilce shi ba,      haka ba za a yi masa hajjin ba.     Saidai babu laifi; Wani ya bashi kuxin hajjin.

            Wanda kuma aka biya masa kuxin hajji,     sai kuma ya zama baya tsoron idan ya karva za a yi masa gori, ko a cutar da shi,  to babu laifi ya karva; yayi hajjinsa da shi.

            Kuma wanda bai yi hajjin musulunci na wajibi ba to bashi da damar yayi hajji ga waninsa;     Idan kuma ya aikata hakan to hajjin ya zama nasa;      wannan kuma saboda hadisin Abdullahi xan Abbas (رضي الله عنهما) lallai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yaji wani mutum yana cewa:     Ya Allah na amsa maka zan yi hajji wa Shubruma, Sai Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) yace:
"Wanene Shubruma? Sai yace: Dangina ne makusanci. Sai yace: Shin ka tava yin hajji?   Sai yace: A'a!  Sai yace:  Ka mayar da wannan ta zama taka,   Sa'annan daga baya kayi hajji wa Shubrumah".    Ahmad da Abu-dawud da Ibnu-Majah suka ruwaito shi.

            Halal ne mutum ya karvi wani lada, idan ya wakilci wani cikin hajji.
Saidai abinda yafi ga mai wakiltar waninsa shine ya karbi kuxin da zai biya buqatunsa na hajji,  amma kada ya karvi lada.

            Yin haramar hajji ga mutane guda biyu baya qulluwa;   Don haka duk wanda yayi haramar hajji xaya ga mutane guda biyu, ko kuma ga kansa da waninsa   =  to haramarsa ta auku ne wa kansa kaxai.       Idan kuma ya yi haramar yin umrah ga wani, sannan yayi aiyukanta har ya kammala.       Sa'annan yayi haramar aikin hajji ga wani mutum na daban    to hakan ya inganta;    saboda a wannan yanayin ibadodi guda biyu ya aikata.

             Kuma mustahabbi ne mutum yayi hajji ga iyayensa guda biyu;    in dukkansu sun mutu,    ko kuma sun gajiya;     Amma sai ya fara yin hajjin wa mahaifiyarsa;  kasancewar itace abar gabatarwa cikin biyayyarsa.     Saidai kuma zai gabatar da hajjin da zai yi wa mahaifinsa na wajibi, akan wanda zai yi wa mahaifiyarsa na nafila.

            Kuma namiji bashi da haqqin ya hana matarsa yin hajjin musulunci (na wajibi);  matuqar ta samu muharrami;     Kuma muharrami ga mace yana daga ikonta na hajji.
Saidai kuma Imamu Maliki (رحمه الله) yace:   Mace zata iya fita hajji cikin taron mata ko tawagarsu.

            Duk kuma matar da mijinta ya mutu to baza ta fita zuwa ga hajji ba a cikin kwanakin iddar mutuwa;   saboda idda lokacinta yana qarewa, shi kuma hajji lokacinsa baya qarewa.       Kuma idan labarin rasuwarsa ya iske ta;   alhalin bata yi nisa daga gida ba   to sai ta dawo; don tayi iddarta a gidanta.       Idan kuma tayi nisa to sai ta cigaba da tafiyarta.

            Kuma duk wanda akansa akwai bashin da wajibi ne ya biya shi; saboda shigar lokacin biyan    to sai ya gabatar da shi akan hajji;        Saidai idan mai bashin yayi masa izinin tafiya hajji.      Wanda kuma bashinsa ya zama biyansa kucul-kucul ne,  kuma ya zama ya mallaki kason kowani lokaci; wanda zai biya idan lokacinsa yayi to sai ya tafi hajjinsa, ba tare da an sharxanta neman izinin wanda yake bin bashin ba.

            Ya ku musulmai …
            Barin yin hajjin nafila, ko umrah ta nafila a lokacin tsananin cunkoson jama'a     da nufin yalwatwa masu rauni da mata da marasa lafiya da tsofaffi masu yawan shekaru; waxanda suka zo don sauke hajjin farilla    =    barin haka shine yafi kusa da xa'a da alheri da samun lada da sakayya a wurin Allah;     Saboda yin hajjin nafila, da umrah ta nafila sunnah ne,      yayin da qoqarin kiyaye cutar da musulmi kuma wajibi ne;           Ya zo daga Abdurrahman xan Auf (رضي الله عنه) yace:     Annabi (صلى الله عليه وسلم) yace da ni:    
"Yaya ka aikata lokacin tava hajarul aswad?      Sai nace:    Na kan tava,       Na kan bari.     Sai yace:     Ka aikata daidai".   Ibnu-hibbana ne ya ruwaito shi.
Ma'anan wannan shine: Ya tava a lokacin da babu cunkoso,      ya kuma bar tava dutsen a yanayi na cunkoso,    Sai Annabi (صلى الله عليه وسلم) ya bayyana cewa ya dace da shari'a.

            Bada sadaka shima yafi falala akan yin hajjin nafila, da umrah ta nafila;      idan har akwai danginsa da suke da buqata, ko kuma ana cikin wani zamani na yunwa,  ko kuma aka samu wassu daga cikin musulmai suna da matsananciyar buqatar sadakarsa, ko kuma buqatar ciyarwarsa;        Wata rana Abdullahi bn Almubarak ya fita zuwa ga hajji sai yaga wata budurwa tana xaukar maceccen tsuntsun da aka jefar da shi a bola,   Sai ya tambaye ta,     Sai tace: Ni da 'yar'uwata a wannan wurin bamu da abinci, sai abinda aka jefar a wannan bolar,    Sai Abdullahi ibnul Mubarak ya yi umurnin a mayar da raquman da suka yi lodin kayansa, ya kuma bata duka abinda ya ware don buqatar hajjinsa,     sa'annan yace: Yin haka shi yafi falala fiye da muyi hajji a wannan shekarar. Sa'annan ya koma garinsa.


            Ya ku musulmai…
            Duk wanda ba a bashi takardar izinin yin hajji ba, daga hukumomi     to wajibi ne ya jinkirta hajjinsa, a magana ingantacciya, har zuwa lokacin da zai samu izinin fita;    saboda maslahar shari'a ta hukunta iyakance adadin waxanda za su yi hajji da umrah;     domin tunkuxe matsalolin cunkoso da turarreniya,   da kuma hana yin aikin kara-zube.

            Ya ku waxanda kuke bin hanyar qarya, da algus, da wayo wa hukumomi ko mutane, da rashawa,      domin su guje wa dokokin da suka kawo tsari a aikin hajji      !!!

                 
            Ya waxanda kuke bin hanyoyi masu sarqaqiya, da hatsari;     domin ku gudu daga wuraren 'yan sandan kan hanya masu kula da aminci; waxanda ba a sanya su a wuraren aikinsu ba sai don maslahar hajji da samun aminci a cikinsa, da kuma don samun lafiyar mahajjata  !!!


            Ya ku waxanda kuke sava wa shari'a, kuke kuma qetare dokokin Allah (تعالى), kuke aikata haram, sannan ku wuce miqaatai, da wuraren 'yan sanda ba tare da sanya ihrami ba  !!!

            Wani irin hajji kuke nufi ?!
Kuma wani lada kuke fatan samu?!

Alhalin kuma kuna yin qarya, da wayo, da sava wa dokoki !!!


Ya ku waxanda kuke tsallakar da waxanda suke sava wa dokoki, da kuma xauka ko tsallakar da waxanda suke nufin su yi hajji ba tare da sun haxa takardun izini ba   
Ku sani!   Ladan kwadagonku dukiya ce mai dauxa, kuma kuxi ne na haram, wanda aka samu ta hanyar savo!

Gabaxayanku!   
Ku hanu daga waxannan aiyukan abun zargi,     Sannan ku yi dubi zuwa ga al'amuran da idanu na hankalta, da hikima, da kuma qoqarin sauke nauyi.

Kuma ku nisanci kafa hujja da hujjoji rusassu; waxanda suka fi gidan sauro sakwarkwacewa idan za a tattauna akansu,    irin hujjojin da suke sanya wanda ya yi riqo da su a wajen tattaunawa dalilansa su qare yayi shiru ya kasa wata magana   !!!

Ya Allah ka nuna mana shiriyarmu,
Ka kuma kare mu daga sharrin kayukanmu
Ya Mai karamci,      Ya Mai girma,    Ya Mai rahama!


HUXUBA TA BIYU
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah;  wanda ya ilmantar da bayinSa, ya kuma sanar da su, sannan ya basu fiqihu a cikin addininsu ya fahimtar.
Kuma ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah; shi kaxai yake bashi da abokin tarayya.
Kuma ina shaidawa lallai annabinmu kuma shugabanmu Muhammadu bawansa ne, kuma manzonSa.
Allah yayi daxin salati da sallama a gare shi, da iyalansa da sahabbansa, da waxanda suka tafi akan turbar gaskiya, har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka:

Ya ku musulmai…
Ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku kula da su,   kuyi masa biyayya, kada ku sava masa, "Ya ku waxanda suka yi imani ku kiyaye dokokin Allah,   ku kasance tare da masu gaskiya",     [Taubah: 119].

Ya ku musulmai…
Ku lazimci sunnonin da suke da madogara,      waxanda malamai tabbatattu amintattu suka ruwaito su,      Sannan ku kiyaye bidi'oi da qirqirarrun al'amura,

Ka yi mamakin yawan waxanda suka tattaru akan bidi'oi,

Ko kuma suka karkace suka bar sunnoni, suka ware

Kuma ina suke da sunnah MUTANEN DA suka karkata zuwa ga kaburbura suna fatan samun alheri daga waxanda suke kwance a cikinsu ?!

Suka kuma fiskantar da zukatansu zuwa gare su, harma da fiskoki,

Suka riqi kabari abin dogaro, da wurin yaye bala'i,

Da mafaka,     da qofar samu,   da Katanga daga sharri,   da wurin fata !

Har suke sujjada akan qofofinsu,
Suke yanka abun yankansu a bakin qofofin,
Suke kuma yin xawafi da kewaya kaburburan,

Wai !!! suna fatan samun yaye matsaloli daga gare su, da albarka, da kwararan alheri.

Bidi'oi masu girma da ake kiransu bautar kaburbura.

Wanda kuma tushensu shine bautar gumaka,

Jiga-jigan maluma masana, da shehunan musulunci duk sun yi ijma'i da ittifaqi,   kan cewa hakan yana cikin bidi'oi masu muni, waxanda suke cin karo ko warware musulunci da shari'ah.   Kamar su Abu-hanifata da Malik da Shafi'i da Ahmad.


Shi kuma Ubangijinmu Mai karamci yana kwararo kyauta,      yana kuma jin addu'ar bawa,     ba tare da masu ceto, ko wassu da za a riqa a matsayin tsani ba;    daga cikin annabawa ne ko daga cikin waliyyai.


Ku ziyarci masallacin Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)… 
Kuna masu nisantar shafa katangun masallacin ko qofofinsa, da minbarinSa, da mihrabin sallarSa;    Domin ita albarka ba a nemanta cikin shashshafa daskararrun abubuwa.

Sannan ku nisanci neman albarka da qasar da take kan kaburbura,     ko neman waraka da ita,      ko kuma jejjefa abinci, da kwayoyi hatsi da kuxaxe akan kaburbura,      ko kuma roqon waxanda suke kwance a cikinsu;     saboda aikata hakan yana cikin aiyukan jahilai na jahiliyyah.


Aikinku Allah ya gama shi da karvuwa, da kuma bada lada,

Addu'arku kuma ya gama ta da yarda da kuma amsawa.

Ya kuma jawo muku arziqi, 
ya kuma bubbuxe muku qofofinsa.
 انتهت

Kuma kuyi salati ga Ahmad mai shiryarwa,
Mai kuma ceton mutane gabaxaya,

Saboda
Duk wanda yayi masa salati guda xaya
To lallai Allah zai yi masa guda goma,

Zuwa ga halittu aka turo shi, don ya zama rahama, mai tausasawa
Kuyi masa salati, da sallama masu tarin yawa;

Ya Allah kayi salati da sallama ga bawanka kuma annabinka Muhammad,
Kuma ya Allah ka yarda da dukkan iyalansa da sahabbai,
Ka haxa da mu, Ya Mai karamci, Ya Mai yawan baiwa,

Ya Allah ka xaukaka musulunci da musulmai,
Kuma ka qasqantar da shirka da mushirkai,
Kuma ka halaka azzalumai, da masu kasha bayinka, mavarnata, masu qetare iyaka,   Ya Ubangijin halittu!

Ya Allah ka tunkuxe yaquka da fitintinu da savani da rashin kwanciyar hankali, da jayayya    
daga qasashen musulmai gabaxaya,   Ya Mai karamci!

Ya Allah ka dawwamar wa qasarmu;  ta Saudiyya
Amincinta, da wadacinta, da xaukakarta, da kwanciyar hankalinta,
Kuma ka datar da shugabanninta zuwa ga abinda akwai alkhairi a cikinsa da gyaruwan musulmai,
Ya Allah ka datar da shugabanmu; Mai hidimar masallatai biyu; harami, maxaukaka,   da na'ibansa guda biyu
Zuwa ga abinda xaukakar muslunci yake cikinsa da gyaruwar musulmai,   Ya Ubangijin halittu!

Ya Allah ka warkar da marasa lafiya daga cikinmu,
Ka yaye ma waxanda aka jarrabe su daga cikinmu,
Kayi rahama ga mamata daga cikinmu,
Kuma ka fitar da waxanda suke cikin kurkuku,
Ka taimake akan wanda yayi adawa da mu,
Ya Ubangijin halittu!

Ya Allah ka kiyaye mahajjata,
Da masu ziyara, da masu umrah,

Ya Allah ka karvi aiyukansu
Kuma ka tsarkake musu, su
Ka kuma xaga darajarsu,
Ka xaukaka su,

Qarshen addu'armu ita ce:
ALHAMDU LILLAHI RABBIL ALAMINA !     

            

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان)

TSAWATARWA DAGA SHAN TABAR SIGARI (التحذير من شرب الدخان) Na Shehun Malami Abdul’aziz dan Abdullahi bn Baaz Allah ya yi masa rahama...